na gaji" Meema ta fad'a cikin shagwab'a.
"Is OK Meema, ba ri in je gidan Momi in dawo" Dr ya fad'a.
Cikin marairaicewa Meema ta ce "Yanzu yaya Sadik fita za ka yi ka bar ni".
"Yanzu zan je in dawo" Dr ya fad'a.
"Ka tawo min da ice cream da baked chicken" Meema ta fad'a cikin shagwab'a.
"OK zan tawo miki dashi, sai na dawo" Dr ya fad'a yana mik'ewa.
Waving din hannun ta tayi kana ta koma ta kwanta.
Dr kuwa yana fita gidan mu ya tawo.
Tun a hanya yake jin gaban shi na fad'uwa saboda tunanin yanda zai tunkare ni.
Har ya k'araso gidan yana tunanin yanda zai fuskance ni.
Ya dad'e zaune a motar kana ya d'akko wayar shi yayi dialling din numba ta amma is not reachable.
Hakan yasa ya fito daga motar ya yi knocking din gate din.
Mai gadi ne yazo ya bud'e mai.
Ganin Dr ne yasa cikin girmamawa ya gaishe shi saboda ya gane shi.
Bud'e mishi k'ofar yayi ya shigo.
Dr ne ya sanar dashi ya shiga ya sanar da ni nayi bak'o.
Main parlour mai gadi ya yi sallama Ummu ta amsa mishi.
Sanar da ita ana sallama da ni.
Ni kuwa tun da na idar da sallar magrib ina zaune ina lazimi ban tashi daga sallayar ba har San da nayi sallar isha'i ina zaune.
Ummu ce tayi sallama na amsa mata.
Sanar da ni tayi na yi bak'o kana ta fita daga d'akin.
Tun da Ummu ta sanar dani ana sallama da ni nake tunanin Wanda yake kira na a wannan lokaci.
Mik'ewa nayi na fito dan ganin mai kira na.
Ban gane wanene ba kasancewar ban k'arasa inda yake zaune a d'aya daga cikin kujerun dake gurin shak'atawa ba.
K'arasawa nayi had'e da sallama ta.
Juyowa yayi ya amsa min sallama ta had'e da murmushi a fuskar shi.
Mamaki ne ya kama ni ganin Dr da nayi a lokacin wanda har hakan ya nuna a fuska ta.
Wai Dr na ke gani a gaba na ko ido na ne yake min gizo?.
Tabbatar da cewa shi d'in ne yasa na cire mamakin ganin shi da nayi.
Gani nayi ya rame ya k'ara haske da alama kamar yayi fama da rashin lafiya.
Tambayar da na fara yi wa kaina shine me ya kawo Dr gidan mu?.
Ganin tambayar ba ta da wani amfani a guri na sai ma b'acin rai da hakan zai haddasa min yasa nayi saurin kawar da wannan tunanin a raina.
"Fatima Zarah" Dr ya kira suna na.
Ba tare da na mishi magana ba ko amsa kiran suna na da yayi na juya da niyyar komawa cikin gida dan ina ganin babu wani amfanin tsayawa in saurare bayanin abin da ya kawo shi gidan mu.
Mik'ewa yayi ya kira suna na "Zarah".
Ko alamar juyowa ban yi ba na ci gaba da tafiya ta na bar shi a gurin.
Bi na yayi da kallo har na b'ace wa ganin shi yana nan a tsaye.
Ganin tsayuwar ba ta da wani amfani a gare shi yasa ya fara tunanin tafiya.
Yasan hakan daman za ta iya faruwa in har yazo waje na dan yasan raina a b'ace yake game dashi.
Ya zama dole yayi hak'uri da duk abin da zan mishi.
Fatan shi shine ya samu in saurare shi.
Jiki a sanyaye Dr yayi ma mai gadi sallama ya bar gidan.
[10/16, 19:54] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*ššš
š¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āā
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*šKAINUWA WRITERS ASSOCIATION*š¤š½
www.maryamahmadpaki.blogspot.com
facebook: Kainuwa Writers Association
*TUNATARWA*
*Magana Uku Ce Magabata Suke Yawan Maimaitawa:*
*(1) Idan Ka/ki ka Gyara Sirrin ka/ki, Allah Zai Gyara Zahirinka/ki..*
*(2) Idan Ka/ki ka Gyara Abinda Ke Tsakanin Ka Da Allah,, Allah Zai Gyara Abinda Ke Tsakaninka/ki Da Mutane!!*
*(3) Idan Kuwa Ka/ ki ka Dage Wajen Neman Lahira,, Allah Zai Sawwake Maka/mi ki Samun Duniya.*
*Allah Yasa Mudace Duniya Da Lahira!!*
103-104
Tun da Dr ya shiga mota yake mamaki na da tunanin yanda ban yi maraba dashi ba san da na gan shi.
A tunanin shi in dai ya tako yazo inn da nake zan yafe mishi abin da ya min tare da manta komai da ya faru a tsakanin mu, sai gashi na bashi mamaki ban ma kula shi ba bare yayi zaton samun sassauci daga guri na.
Yasan abin da ya min dole ne in kasance cikin fushi dashi tare da dāaukan dukkan matakin da na ga shi yafi dacewa wajen hukunta shi.
Hakan ba zai dame shi ba in har zan yafe mishi in manta komai sannan mu kāara dasa wata sabuwar soyayya da tafi ta da dadāi da gamsarwa dan a yanzu ne wani tsimin soyayya ta ke taso mishi a cikin zuciyar shi.
Da wannan tunanin ya samu ya kāarasa gida.
Side dāin shi ya wuce ba tare da ya shiga side dāin Meema ba.
Bedroom dāin shi ya wuce dan a yanzu yafi so ya kadāaita shi kad'ai ko ya samu sassaucin yanda yake ji a zuciyar shi ga me da ni.
Yana shiga ya samu Meema kwance akan royal bed dāin shi.
Yayi mamakin ganin ta saboda ba ko wane lokaci ba ne take zuwa side dāin shi ta kwanta.
Cire kayan shi yayi ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito.
Motsin shi da Meema ta ji ne yasa ta budāe idon ta cikin bacci ta ce "Yaya Faruk ashe ka dawo, ina ice cream dāin".
Ran shi ne ya bāaci da tambar da Meema ta mi shi, daman ga yanayin yanda ya bar gurin na, dan haka yayi shiru kamar bai ji ta ba ya ci gaba da sa pyjams dāin shi.
Kāara jefo mishi tambayar tayi da cewa "Yaya Faruk na ce ina ice cream dāin, tun dāazun na ke ta zaman jiran ka ba ka dawo ba, shi yasa ma ban ci komai ba".
Wani banzan kallo ya watsa mata kana ya ce "donāt disturb me Meema ban siyo ba, ke ba ki san ki lura da yanayin da mutum yake ciki ba, za ki dame ni da shirmen maganar ki".
Tabāe baki tayi kana cikin shagwabāa ta ce "yanzu yaya Sadik mi ye laifi na a nan dan na tambaye ka ko ka tawo min da ice cream dāin, since I was waiting for you amma na ga ba ka dawo ba, ban ci komai ba ina ta jiran dawowar ka, kasan ba na son heavy food da daddare".
Ganin yanda Meema ke son takura mishi da surutun ta wanda ba abin da yafi bukāata da ya wuce ya kasance shi kadāai ko ya samu saukāin yanda yake ji a zuciyar shi, hakan yasa cikin fad'a ya ce "Meema leave me alone, am not in a good mood, za ki iya koma wa side dāinki ki kwanta, a yanzu na fi bukāatar zama ni kadāai, idan ina bukāatar ki zan zo in sa me ki ko in kira ki".
Mamakin Dr ne ya kamata ganin da ga mishi magana ya fara mata fadāa, tasan fitar da yayi ne aka bāata mishi rai shine yake son hucewa akan ta, kāarin takaicin ta shine yanda ya ce mata ta koma side dāin ta dan ya ga ta zo gurin shi.
Cikin bāacin rai Meema ta sakko daga kan bed dāin ta fita daga dāakin ba tare da kāara yin magana ba.
Kwantawa yayi akan gadon yana kallon P O P dake saman ceiling dāin dāakin ya fadāa cikin kogin tunani.
Tunanin yanda na nuna mishi halin ko in kula san da yazo gidan mu shine ya dinga mishi yawo a ran shi.
Bai yi tunanin cewa in har ya taka kāafar shi ya zo in da na ke ba zan mishi haka ba saboda yasan irin son da nake mishi sai gashi na mishi bazata.
A yanzu ba abin da yafi wahalar da shi irin soyayya ta da ke dāawainiya dashi a ko da yaushe.
A yanzu ne ya tabbatar da irin zazzafar soyayyar da yake min wanda a da bai min irin ta ba.
Tunanin yanda zai shawo kaina da irin soyayyar shi da yake saurin jawo hankali na yake yi.
Haka ya ci gaba da sakāa da warwara yanda abin zai zo mishi da saukāi ganin mun daidaita dashi ba tare da jan wani tsawon lokaci ba.
A yanzu babban burin shi shine in amince mi shi mu kāara dasa wata tsaftatacciyar soyayya wacce ba muyi ta a da ba.
A shirye yake da ba da dukkan kulawar shi gare ni da min hallaci da soyayyar shi wanda bai min ita a da ba.
Da wannan tuanin Dr ya samu bacci ya dāauke shi ba tare da ya shirya yin baccin a lokacin ba.
A bāangare na kuwa tun san da na koma dāaki na fara mamakin zuwan Dr gidan mu wanda a yanzu sama da tsawon shekara dāaya da ya wuce bai neme ni ba ko ya tako ya zo gidan mu sai a yau da yayi niyyar yin haka.
Tuananin abin da ya kawo shi gidan mu shi yafi dāawainiya da ni a cikin zuciya ta.
Tunanin da na fi yarda dashi duk da ban tabbatar ba cewa Dr yazo gidan mu ne dan ya nemi sulhu a guri na mu daidaita saboda takāamar ko wani lokaci yazo zan yi marhabin dashi.
Sai dai in haka ne tunanin shi zan bashi mamaki domin zan nuna mishi cewa Fatiman da ya sani a da wacce ta nuna mishi makauniyar soyayya ba ita ba ce a yanzu.
A yanzu na fito daga cikin duhun da a da nake ciki na soyayyar shi wanda ba na ji ba na gani amma a yanzu ina cikin haske ne domin a yanzu zan iya fuskantar shi da duk abin da yazo saboda na riga na ajiye soyayyar shi a gefe na zabāi hanyar da tafi dacewa da ni.
Sai dai har yanzu nasan duk yanda Dr ya bāata min ban daina jin son shi a raina ba.
Nasan hakan ba ya rasa nasaba da sharrin so.
Soyayyar da na nuna ma Dr a baya ita na fara tariyowa zuwa rayuwar auren mu da irin sakamakon da ya min da irin kāaunar da na nuna mishi ta hanyar yin min abubuwa da dama.
Wanda yafi tsaya min a rai shine saki na da yayi wanda a yanzu na ke neman sama da shekara dāaya a gidan mu ba tare da Dr ya nuna damuwar shi akan hakan ba.
Hawaye ne ya fara zubo min a idanu na dāaya na bin dāaya.
Ban damu da in share ba saboda nasan shi kan shi hawayen rahama ne a gare ni.
Tunanin da zuciya ta ke yawan yi shine daman Dr kuwa yana so na kamar yanda na ke son shi kuwa?
Amsar da zuciya ta tafi karkata da ita shine Dr yana so na duba da yanda ya nuna min kulawar shi da irin soyayyar shi tun kafin in aure shi har zuwa rayuwar auren mu, sai dai nafi gamsuwa da cewa na fi son Dr akan son da yake min.
A halin da ake ciki yanzu shine soyayyar yaya Faruk da take son hana ni sukuni ga kuma soyayyar Dr dake gefe dāaya a cikin zuciya ta.
Sai dai a yanzu na fi marhabin da soyayyar yaya Faruk in har zan samu kāarbāuwa a wajen shi duba da yanda ya so ni a da sannan ga halayen shi nagari da su ka kāara bayyanuwa a gare ni.
Fata na shine in bar wa Allah zabāi ya zabāa min cikin yaya Faruk da Dr wanda zai fi zama akhairi a gare ni.
Ina cikin wannan tunanin ne na ji sallamar Ummu ta shigo dāakin.
Saurin goge hawaye na nayi kana na yalwata fuska ta da murmushi a fuska ta na amsa mata sallamar.
Kallo na tayi ta zauna a gefen bed dāina ta fuskance ni.
"Fatima me ya same ki, tun da kika dawo kiran ki da aka yi a waje na lura da yanayin ki ya canza, shi yasa lokacin da kika dawo na ga kin wuce dāakin ki ban takura miki ba wajen sanin me ya faru".
Shiru na yi ina sunkuyar da kaina kana ina wasa da yāan yatsun hannu na.
Har lokacin hawaye ne ke kāokāarin ci gaba da zubowa a idanu na.
Ummu ce ta jefo min da tambaya "Fatima wanene ya aiko a ka kira ki a waje?".
Cikin sanyin murya na ce "Dr Sadik ne".
Kallo na Ummu tayi tana nazari na kafin ta dāaura da cewa "Kenan shi yasa yanayin ki ya canza ki ka zo dāaki kina tuani" Ummu ta fadāa.
Amsa mata nayi da cewa "Aāah Ummu, ban ji dadāin jiki na ne".
Girgiza kai Ummu kawai Ummu tayi ba tare da ta yarda da abin da na fadāa ba.
Shiru Ummu tayi kana ta dāaura da cewa "Fatima ya dai kamata ki san abin da ya dace da ke dan shekaru sun ja, ya kamata ki tsaya ki natsu wajen tantance wanda ya kamata ki zabāa a matsayin mijin ki saboda ba na so ki kāara kwatanta kuskuren da kika yi a baya sannan ki dage wajen mikāa wa Allah bukāatun ki Allah ya zabāa miki abin da yafi zama alkhairi a gare ki, nima zan ci gaba da taya ki da adduāa".
"Na gode Ummu" na fadāa cikin sanyin murya.
Mikāewa Ummu tayi ta ce "Fatima ina so ki fahimci cewa duk abin da ya sami bawa rubutacce ne daga wajen ubangiji, kowane mutum da kike gani yana tare da kāaddarar sa, duk abin da kika ga yayi farko ta yana da kāarshe, saboda haka ina so ki mikāa dukkan lamarin ki zuwa ga Allah subhanahu wata aāla akan ya saman miki mafita a rayuwar ki, ba na jin dadāin yanda wani lokacin na ke ganin ki cikin tunani, ni kaina hankali na ba ya kwanciya in na ganki a wannan halin, ya kamata ki daina sa ma kan ki damuwa kin ji ko auta ta" Ummu ta kāarasa maganar da wasa.
"Zan kiyaye insha Allah Ummu" na fadāa.
Murmushi Ummu tayi ta ce "Yawwa auta ta, haka na ke son ji, Allah ya kawo miki miji nagari".
Murmushi nayi na sunkuyar da kaina kana na amsa da "Amin Ummu".
Fita Ummu tayi daga dāakin.
Bayan fitar Ummu ne na fara tunanin maganar da ta fadāa min.
Nasan duk wannan maganar da Ummu take yi tana yin abin da hausawa ke cewa kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke iya gane wa, maganganun ta suna nuni da cewa kar in yi saurin amincewa da Dr duba da yanda ta faru a tsakanin mu, Ummu ba tasan nima a yanzu na ma kaina karatun ta natsu ba, a yanzu na dawo daga rakiyar makauniyar soyayya wacce ba za ta bāille da ni hanyar da nake so ba sai dai ta bar ni a tashar nadama, a yanzu abin da na fi bukāata shine duk wanda zan aura ya zama soyayya mai tsafta muka gina a tsakanin mu dan samun ribar soyayya ga duk wanda suka kāulla ta a hanyar da ta dace.
Ganin yanda tunani yake so ya takura min yasa na tashi na fito falo na kunna kallo dan in rage ma kaina tunanin da ke son addaba ta.
Ina cikin kallo ne Ummu ta fito daga side dāin ta tazo ta zauna muka ci gaba da kallon kana mu tabāa hira jefi-jefi.
Na ji dadāin kasancewa a wannan yanayin domin hakan ya cire min damuwar da nake ciki da tunanin da ke son takura min.
Yau ranar ta kasance ranar Talata.
Na dawo daga aiki na shigo da mota ta cikin layin mu na ga wata mota a gate dāin gidan mu wanda ban gane mai mamallakin motar ba.
Kusa da motar na zo nati parking kasancewar ba hanyar da zan wuce.
Ganin wanda ya fito daga motar ne yasa na bi shi da kallo dan ban yi tunanin zuwan shi a wannan lokacin ba duba da yanda muka rabu dashi.
Dr ne na ga ya nufo mota ta.
San da ya kāaraso ne ya min nocking dāin kāofar mota ta amma ban budāe ba.
Dāaure fuska ta nayi ina jiran jin shi da me yazo.
Sai da ya min nocking kusan sau 4 sannan nayi wining dāin glass dāin motar.
.
Sallama ya min na amsa mai kana ya dāaura da cewa "Fatima pls in ba damuwa ina so ki ara min time dāin ki muyi magana, dāazun na zo mai gadin ku yake fadāa min kin je gurin aiki, shi yasa ma na tambaye shi lokacin da za ki dawo aikin ya fadāa min".
Tabāe baki na nayi na ce "Kash! Gashi kuma yanzu ban da time saboda yanzu na dawo daga aiki ina bukāatar hutawa, za ka iya dawowa next time in kana bukāar hakan".
Kallon mamaki Dr ya bi ni dashi saboda ba yi tunanin hakan daga gare ni ba.
Ran shi ne ya bāaci da maganar da na mishi wanda hakan ya nuna a fuskar shi, sai dai yayi kāokāarin controlling dāin fushin shi.
"pls Zarah ko yaya ne ki bani time dāin ki, maganar da za mu yi da ke is very important a tsakanin mu, ba zan ja maganar tayi tsawo ba tun da kina bukāar ki huta" Dr ya fadāa.
"Ina ganin na riga na fadāa maka tun farko ban da time da zan tsaya sauraron ka a yanzu saboda ina bukāatar hutawa, maganar da ka ke yi wai maganar na da mahimmanci ina ganin a gurin ka ta ke da mahimmanci domin ni in dai ta bāangare na ne ba na bukāatar jin ta, in kuma maganar da mahimmanci a gurin ka kamar yanda ka fadāa za ka iya dawowa next time amma ba yau ba" cewa ta.
Kallo Dr ya bi ni dashi kamar yau ya fara gani na, nasan hakan bai rasa nasaba da mamaki na.
Nasan bai yi zaton zan mishi haka ba saboda yasan irin son da na ke mishi, sai gashi na bashi mamaki wajen fadāa mishi magana kai tsaye.
San da yazo na kāi sauraron shi ya dāauka wannan hukuncin na tanazar mishi, sai gashi yau ma na zo da wani salo na kora da hali.
Ganin Dr bai da niyyar matsawa daga gurin yasa na kunna karatun alkāurāani a cikin motar cikin suratul Rahaman kana na dāakko waya ta ina pressing.
Nasan hakan ne kadāai zai sa Dr ya tafi ba tare da mun yi musayar yawu dashi bad an nasan a cikin abin da Dr ya tsana shine shariya da kāyaliya.
Ran Dr ya bāaci da abin da na mishi wanda hakan ya bayyana a fuskar shi sai dai yana kāokāarin bāoyewa.
Bai kāara ce min komai ba ya girgiza kai kana ya tafi ya shiga cikin motar shi.
A 360 ya ja motar ya bar layin.
Kāaramin tsaki nayi kana nayi wa mai gadi horn ya zo ya budāe min na shiga da mota ta ciki.
Ko da na shiga ciki ban yi realising abin da na wa Dr ba, a gani na Dr ya cancanci in mishi fiye da haka.
Hakan ya tabbatar min da cewa a yanzu na dawo daga rakiyar makauniyar soyayya da na ke wa Dr.
Nasan in da a da ne da yanzu ina nan cikin damuwa ganin na bāata wa Dr rai amma a yanzu hakan bai dame ni ba duba da yanda a da na nuna mishi soyayya mara misaltuwa wanda ban ji ban gani.
Yanzu na fi samun natsuwa a cikin zuciya ta saboda ajiye wahalalliyar soyayyar Dr da a da ta azabtar dani.
Ranar haka na kasance cikin walwala dan nasan ko ba komai na bāata wa Dr rai.
Dr kuwa tun da ya fara driving yake tunanin abin da na mishi wanda bai za ci hakan daga gare ni ba.
Soyayya ta dake wahalar dashi a yanzu ita take kāokāarin cire mai duk wani walwalar shi da farin cikin shi.
Wani irin so yake min da shi kanshi ba zai iya fasalta yanda yake ji na a zuciyar shi ba.
A da yana ganin zai iya rayuwa ba tare da ni ba, sai a yanzu ne ya kāaryata zuciyar shi cewa ba zai iya ci gaba da gudanar da rayuwar shi ba tare da ni ba.
Zuciyar shi ce ta fara harbawa da sauri-sauri a lokaci dāaya kāirjin shi ya ji ya fara mishi wani irin ciwo.
Dafe kāirjin shi yayi ya rintse ido saboda yanda yake jin ciwon a cikin jikin shi.
Jinginar da kanshi yayi a jikin sitiyari yana maida numfashi.
Sai da ya dāauki lokaci kafin ya samu kāirjin ya lafa mishi amma har yanzu yana jin sauran ciwon.
A haka ya samu ya ja motar har ya kāaraso gida.
Side dāin Meema ya shigo hadāe da sallama ya zauna in da ya same ta a kujerar 2-sitter tana kwance tana buga game a wayar ta.
Meema kuwa tun da ta amsa mishi sallamar ta mishi sannu ta maida hankalin ta akan game dāin da take bugawa ba tare da ta lura da yanayin da Dr yake ciki ba.
Ciwon kāirjin ne ya kāara dawowa Dr wanda ya fi lokacin da yake cikin mota.
Yanda ya fara numfashi ne yasa Meema tayi saurin maida hankalin ta gare shi.
Ganin halin da Dr yake ciki yasa ta yar da wayar da ke hannunta ta nufo gurin shi.
Rikāe shi tayi tana tambayar shi in da yake mishi ciwo a lokaci dāaya tasa kuka mai ban tausayi.
Dr bai samu damar yin magana ba saboda yanda yake ji a jikin shi.
Da kāyar Dr ya samu ya budāe baki ya fadāa ma Meema in da maganin shi yake a bedroom dāin shi.
Da gudu Meema ta nufi bedroom dāin shi ta dāakko maganin ta bashi ya sha.
Jingina yayi da kujerar da yake zaune yana maida numfashi a hankali.
Bai wani jima da shan maganin ba ya fara jin bacci.
Hakan yasa ya kwanta akan kujerar 3-sitter dāin da yake zaune.
Meema ce ta zo ta zauna kusa dashi tana kallon shi.
Wani irin tausayin shi ne ya kamata ganin yanda ciwon yake wahalar da Dr.
Ji take yi kamar ta cire ciwon daga jikin shi ko ya samu saukāin wahalar da yake sha.
Hawaye ne ya fara zubowa a idanun ta na tausayin Dr.
Hannun ta takai kanshi tana shafa mi shi a hankali.
Haka Meema ta ci gaba da zama tana jiran tashin Dr.
Dr sai da ya dāauki fiye da awa dāaya kana ya tashi daga baccin da yayi.
A hankali ya budāe idon shi yayi tozali da Meema kusa dashi.
Mamaki ne ya kama shi ganin Meema kusa dashi.
Hakan ya tabbatar mi shi da cewa tun san da ya fara bacci ta ke zaune a gurin.
Shi kan shi yasan Meema na son shi sai dai alāadar yahudawa da take koyi dasu da wasu halayen ta na cewa tana da freedom dāin kanta ba ta cika bin abin da zai fadāa mata ba a matsayin shi na mijin tab da wasu hakkāokāin ta da ba ta saukewa a matsayin ta na matar shi, wannan shine matsalar da suke fuskanta da ita Meeman.
Shi kan shi wani lokacin tana bashi tausayi saboda son da take mishi, yana ji a ranshi zai iya ci gaba da zama da ita matukāar za ta gyara halayen ta ko dan darajar son da take mishi da kuma Momin shi.
Yasan so dāaya ne tak ya kuma riga ya mallaka min, sai da ya na kāokāarin ganin ya sa son Meema a ranshi ko yaya ne saboda yanda ta dāauki lokaci tana dāawainiya da son shi a cikin zuciyar ta kuma gashi yanzu tana matsayin matar shi ta sunna.
Katse mi shi tunanin shi Meema tayi da cewa "Ka tashi yaya Sadik, ya jikin?".
Kāasaitaccen murmushi ne ya bayyana a fuskar shi ya ce "Na tashi Meema, naji saukāi, thanks".
"Thanks for what" Meema ta fadāa.
"for your caring" Dr ya ba ta amsa.
"you deserve more than that" cewar Meema.
Murmushi yayi ya rungume ta kana ya rikāe mata hannu yana wasa dashi.
A haka suka ci gaba da hira da Meema.
Dr ne ya bata umarnin ta dafa mishi shayi wanda ya ji kayan kāamshi a ciki.
Ba a dāau lokaci ba Meema ta dafa shayin ta kawo mishi ya sha.
Ranar kam zaman su abin burgewa da ban sha'awa saboda yanda su ka tarairayi junan su.
[10/21, 11:46] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*ššš
š¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āāš¤¦š½āā
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*šKAINUWA WRITERS ASSOCIATION*š¤š½
Facebook: Kainuwa writers Association
www.maryamahmadpaki.blogspot.com
*TUNATARWA*
_Rayuwa haske ce_
_Mutuwa kuma aya ce_
_Arziki jarrabawa ne_.
_Talauci kuwa misali ne_
_Hankali makaranta ne_
_Ilimi kuwa jagora ne_
_Jahilci kuwa duhu ne_
_Duniya gida ce_
Qabari daki ne_
_Allah ka sa mu dace_
105
Ni kuwa ta bāangare na ban san halin da Dr yake ciki ba, gudanar da rayuwa ta nake cikin nishadāi ba tare da wata matsala ko damuwa ba.
Matsala ta ba ta wuce yanda zan kāara tunkarar yaya Faruk ba tun da ya min gargadāi akan in kāara tunkarar shi da maganar ina son shi.
Gashi ko na kira shi a waya bai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 46 Chapter of 50