*BY*
*MARYAM AHMAD PAKI*
*šKAINUWA WRITERS ASSOCIATION*š¤š½
*TAāAZIYYA*
_Ina mikāa sakāon taāaziyya ta ga family dāin Murjanatu Alhassan wacce Allah ya ma rasuwa a āYar aduwa University a sanadiyar rashin lafiyan da tayi_.
_Allah nake rokāo ya jikāan ki ya gafarta miki, Allah yasa aljanna ce makomar ki_.
_San da naji labarin rasuwar ki ba kāaramin tashin hankali na shiga ba, nasan nayi rashi, ke kāawa ce ta gari da bazan mantaD dake ba_
ššš
_Ina mikāa sakāon taāaziyya ta ga Hussaina wacce Allah yayi wa mijin ta rasuwa_.
_Halima Mk ina kāara mikāa sakāon taāaziyyata gare ki na rasa mijin ki da kika yi_.
_Allah nake rokāo ya jikāan su baki dāaya ya kyautata makwancin su, ya sa aljanna ce makomar su, Allah mu ma ka kyautata kāarshen mu_
_Ina rokāon duk wanda ya karanta wannan page dāin yasa su a adduāa_
*QUESTION OF THE DAY*
_Wace surah ce take karantar da cewa duka abubuwan duniya suna da dangantaka da junansu, dangantaka bayyananna koāboyayya, Kuma zumuntarsu na gudana gwargwadon dangantakarsu da juna_
67-68
Su Abbu kuwa ba kāaramin fushi suka yi dani ba, yaya Khalil ma ya fisu shiga damuwa saboda yadda muka fi shakāuwa dashi, ba wani mai walwala a cikin su tun san da na bar gidan mu.
Dadin su Faruk ya bada cigiya ta a kafafen yadāa labarai, sannan ya kai report police station amma har yanzu shiru ba wani bayani a kaina.
Tsakanin Dadi da Abbu an rasa mai kāarfin gwiwar da zai iya tunkarar Hajiyan Wagini akan rashin gani na da ba ayi ba, tunanin fadāan da za tayi da halin da za ta shiga yasa suka āboye mata, sun barshi akan sai an ganni za a sanar mata da komai, a cikin su ba wanda tunanin shi ya kawo can zan tafi.
Yau kwana biyu kenan da wayar da yaya Faruk suka yi da Dadi sai gashi a Kaduna.
Tun san da Dadi ya kira shi yake tunanin dalilin kiran da Dadi ya mishi, yasan in akan biki ne zai sanar dashi a waya, ba sai yace yazo ba.
Bayan ya huta ne Dadi ya kira shi side dāin shi.
Samun shi yayi da Momi a zaune, alamun dake fuskar su na nuna kowa da abin dake damun shi.
Sallama ya musu ya nemi guri ya zauna.
Dadi ne yayi kāarfin halin amsa masa sallama.
Cikin ladabi yaya Faruk ya ce "Gani Dadi".
Dadi sai da saki ya gauron numfashi saboda tunanin abin da zai fadāa ma yaya Faruk ba mai dadāin ji ba ne kana ya kira sunan sa "Umar!
Cikin sanyi ya amsa "Naāam Dadi".
A ranshi kuwa jinjina abin da Dadi zai fadāa mishi mai matukāar mahimmanci ne tun da ya kira ainihin sunan shi.
Dadi ne ya nisa kafin yaci gaba da cewa "Faruk, dalilin da yasa na ce kazo Kaduna shine akan wata kāaddara da ta faru bayan tafiyar ka wanda yake da alakāa da kai, ka ga kenan āboye maka bai da wani faāida".
Tun kan Dadi ya fadāa mishi maganar da yake son fadāa mai, yaji jikinshi yayi sanyi, yanzu jikin shi ya fara bashi ba abu mai dadāi Dadi zai fadāa mai ba.
"Faruk abin da nake son fadāa maka shine yau kwana hudāu kenan ba a ga Fatima ba, ba a kuma san inda ta tafi ba, hakan kuma na da nasaba ne da auren da za a muku da kuma wanda take so shi wannan Dr dāin, ina son ka dāau hakan a matsayin jarabawar ka, shi Ibrahim saboda ranshi a ābace yake ya ce ko da ba ta dawo ba zai dāaura mata aure dakai, kuma ni na fahimci dan ya faranta maka zai yi, ni kaina nasan Ibrahim da Aisha suna nuna maka so kamar dāan da suka haifa,sun kansu yanzu suna cikin damuwa da abin da Fatima ta aikata, maganar a dāaura aure ba a ga Fatima bai taso ba, za a kāara ābata Alāamarin ne, gwara in ta dawo a san yadda za ayi, ba na so ka sa wannan matsalar a ranka dan guje ma kamuwa da wata cutar, kayi hakāuri Faruk, nasan Fatima ba ta kyauta maka ba" ya kāarasa maganar cikin lallashi.
Tun san da lokacin da Dadi ya fara labarta mishi wannan mummunan labarin kan shi yake a sunkuye ba tare da ya dāago kai ba.
Duk wannan maganganun da Dadi yake ma yaya Faruk ji yake kamar ana watsa mishi tafasasshen ruwan zafi ne a zuciyar shi, ran shi ba kāaramin ābaci yayi da jin wannan labarin ba, jijiyoyin kanshi duk sun tashi, idanun shi duk sun canza launi zuwa ābacin rai, bai taāba kawo wa a ranshi wannan mummunan labarin Dadi zai sanar dashi, ji yake ina ma mafarki yake yi ya samu ya farkar daga wannan mummunan mafarkin wanda bai fatan ya kāara yin irin shi, sai dai kash! Wannan mummunan labarin a zahiri Dadi yake sanar dashi, yau ya kāara tabbatar da maganar da Hausawa ke cewa idan wani yakāi ka wani sai yaso ka, shi da āyan mata ke son shi yana ja musu aji, nan ya tuno da Binafa yadda take mishi magiya akan ya so ta saboda yadda ta kamu da son shi, ya samu ya ba ta hakāuri ta hakāura da sauran āyan matan da suka fadāa mishi suna son shi bai kula su, sai gashi an samu a kanshi na gudu saboda kar na aure shi duk kuwa da irin son da ya nuna min amma ni ban ga hakan ba, na zaābi bare a kanshi, ba abin da yafi tsaya mishi a ranshi shine yadda na dinga mishi yawo da hankalin shi na kāin fitowa a fili na fadāa mishi ba na son shi da wuri, sai daga baya da ya sakankance da cewa ina son shi sannan na nuna mishi da ban yi naāam dashi ba, yanzu ba abin da yake mishi yawo a kāwakāwalwar shi shine guduwar da nayi wanda ba a san inda na tafi ba, a yanzu yana ganin ba abin da zai fi mai saukāi illah ya samar wa kanshi mafita kafin dawowa ta, shi kadāai yasan matakin da zuciyar shi ke fadāa mishi ya dāauka akan wannan curkudāadādāen alāamarin, yana ganin ba wanda yafi cancanta da ya nemo ni dan zartar min da hukuncin da ranshi ke ayyana mishi da ya yanke wanda yake ganin shi kadāai ne zai kawo kāarshen wannan abun da yake faruwa tsakani na dashi.
Momi da Dadi jikin su ne ya kāara yin sanyi ganin halin da yaya Faruk ya shiga tun a yanzu wanda ke nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki da kuma ābacin rai da ya mishi dabaibayi a lokaci guda.
Falon ne ya dāauki shiru ba tare da kowa ya sake magana ba, kowa da irin tunanin da yake ayyanawa a ransa.
Jin shirun da yayi yawa ne yasa Dadi ya kira sunan yaya Faruk cikin tattausan harshe.
Yaya Faruk ne ya dāago kan shi wanda yake mishi wani matsanancin ciwo, wani irin nauyi kan yake mishi saboda tsabar ciwon da yake yi mishi.
"Come close to me my son" Dadi ya fadāa cikin lallashi.
Ba abin da yaya Faruk yafi bukāata a yanzu da ya wuce yaji shi a kwance ko ya samu saukāin radāadāin da yake ji a zuciyar shi da kuma kan shi da yake mishi matsanancin ciwo.
Ba tare da musu ba ya matso ya kwanta a jikin Dadi, a lokacin ne yaji wani irin zazzafan hawaye na fita daga idanun shi, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi kamar wanda yaci kuka ya kāoshi, kāarshe ma runtse idon shi yayi ko ya samu saukāin halin da yake ciki, sai faman karanta *Inna lillahi wa inna ilaihir rajiāun* da *Allahumma ajirni fih musibatih, wa aklifni khairan minha* wannan adduāoāin su yake ta faman maimaitawa a cikin ranshi, a hankali yaji natsuwa ta fara shigar shi, ābacin ran da yake tare dashi ya fara raguwa.
Momi na ganin halin da yaya Faruk ke ciki ita ma ta fara zubar da hawayen tausayin shi, tasan daman hakan za ta faru, yaushe rabon da ta ga hawayen yaya Faruk, amma yau a dalili na yaya Faruk na zubar da hawaye.
Dadi na lura da hawayen da Momi ke yi, yasan dole ta shiga wannan halin in dai ta ga yaya Faruk a cikin wannan halin, shi kanshi kawai dauriya yake yi ba wai dana bun bai dame shi ba, a yanzu ba wanda yafi bukāatar lallashi sama da yaya Faruk.
Dadi ba abin da yake faman yi sai shafa kan yaya Faruk yake yi kamar yadda ake lallashin kāananun yara, a lokaci dāaya yana fadāa mishi sweet words masu kwantar da hankali.
Jikin shi da yaji ya dāau zafi wanda hakan ke nuna zazzaābi ne ya kama shi mai zafi.
Janyen jikin shi yayi daga jikin Dadi, hannun shi yasa ya rikāe kan shi wanda yake ji kamar zai tsage saboda ciwon da yake mai.
Tashi yayi da niyar tafiya, ya fara tafiya kenan, hannun shi na dafe da kanshi, jirin da yaji yana dāibar shi, nan ya fara tangadāi zai fadāi, da sauri Dadi ya taso dan ya rikāe shi kafin ya fadāi, ko kan Dadi ya kāarasa yaya Faruk ya fadāi a kāasa.
Momi ce ta taso da gudu tana kuka tazo tana jijjiga yaya Faruk.
Anisa ma wanda shigowar ta yayi daidai da fadāuwar yaya Farud da gudu ita ma ta kāaraso gurin yaya Faruk wanda yake kwance a kāasa.
Momi kuwa cikin kuka cewa take yi "Faruk ka tashi, ku kadāai gare ni, daga kai sai Anisa, ku kadāai Allah ya ba ni, kar ka mutu saboda āya mace, idan ka mutu ban san halin da zan shi ga ba".
Anisa ma cikin kuka ta kwanta a jikin yaya Faruk tana cewa "yaya Faruk dan girman Allah ka tashi, kai kadāai ne dāan uwana da nake kalla na ji sanyi a raina, kar ka tafi ka barni da maraicin ka, rashin ka zai sa in shiga cikin wani mawuyacin hali, yaya Faruk kaji tausayin mu ka tashi dan Allahā¦" nan ta kāara fashe wa da wani irin kuka.
Cikin Momi da Dadi an rasa mai lallashin wani a cikin su.
Dadi ne ya taāba yaya Faruk yaji yana motsi, hakan yasa ya fahimci suma yayi.
Da sauri ya wuce gurin dāan kāaramin fridge dāin shi ya dāakko faro water mai sanyi yazo ya yayyafa mishi a jikin shi.
Saukar ruwan da yaji a jikin shi yasa ya saki wata ajiyar zuciya.
Dadi ne da Momi suka samu suka kama shi suka kai shi side dāin shi.
Wayar shi Dadi ya dāakko ya kira family Dr dāin su ya fadāa mishi halin da yaya Faruk ke ciki.
Ba a dāau wani tsawon lokaci ba sai ga Dr yazo da kayan aikin shi.
Bayan gwaje-gwajen da Dr ya mai ne ya kalli Dadi ya ce "Alhaji a gwaje-gwajen da nayi na gano Faruk yana yawan tunani duba da yanda BP dāin shi ya hau, yawan tunanin da ya fara yi mishi yawa ne ya jawo mishi ciwon kai mai tsanani wanda hakan yasa temperature dāin jikin shi ya canza, ciwon kai da jirin ne ya hadassa mishi suma, sannan Alhaji pls a kiyaye fadāa mishi abin da zai sa ranshi ya ābaci don kiyaye lafiyar shi, yanzu zan mishi allurar da zai sakko mai da zazzaābin, zan kuma sa mishi drip da yaji kāarfin jikin shi, sannan zan ba da maganin da za a bashi yasha, in da hali a barshi ya huta don a yanzu bai bukāatar hayaniya".
"Za mu kiyaye insha Allah" Momi ta fadāa.
Bayan ya mishi allura ne yasa mishi drip kana ya musu sallama suka fita da Dadi.
Tun da aka sa ma yaya Faruk drip yake ta faman barci kasancewar har da allurar bacci Dr dāin yasa mai.
Momi ce ta koma side dāinta dan dafa wa yaya Faruk abincin da zai ci in ya tashi.
Anisa kuwa zama tayi a kusa dashi tana kallon yadda yaya Faruk ya koma a lokaci guda.
Ba abin da take furta wa sai "Fatima why, me yasa za ki sa yaya Faruk a wannan halin da yake ciki" a lokaci dāaya hawaye na ci gaba da zubowa a idanun ta.
Yaya Faruk sai da ya kwashe fiye da awa uku yana bacci kafin ya tashi daga baccin.
A hankali ya dinga budāe idon shi, Anisa ya gani a gefen shi tana rikāe da dāayan hannun shi wanda ba a sa ma drip ba, yayin da hawaye ke zubowa a idanun ta.
Ganin yaya Faruk ya farka yasa ta saki murmushi ta ce "yaya Faruk ka tashi, sannu ya jikin, yanzu ina yake maka ciwo, akwai abin da ka ke so ne, ko in kira Momi ne?".
Jin wannan jerin tambayoyin da Anisa ke jero mishi yasa ya girgiza mata kai.
Kāara rikāe hannun ta yayi yana kallon ta, idanun ta da ya gani ya canza kala ya tabbatar mishi da tayi kuka, hannun shi yasa yana goge mata hawayen.
Kwanciyar da ya ji ya gaji da ita ne yasa a hankali ya tashi ya zauna.
Da sauri Anisa ta kara mishi pillow a bayan shi ya jingina da gadon.
Drip dāin da taga ya kāare ne yasa ta cire mishi ta koma ta zauna.
"Me yasa ki kuka?" yaya Faruk ya tambaye ta.
Kamar jira take yi ta kāara sa wani kukan, cikin kukan take cewa āyaya Faruk dan Allah ka daina sa tunani ni a ranka, likita yace BP dāin ka ya hau kuma duk a dalilin tunani, plss ka cire tunanin Fatima a ranka".
A hankali ya ce "Kar ki damu Anisa, komai ya kusan zuwa kāarshe insha Allahu, ki daina kuka kin ji my lovely sister".
"Na daina yaya Faruk".
Momi ce ta shigo da foodflask a hannun ta da flask.
Ajiye wa tayi a kan centre table ta nufi yaya Faruk cikin faraāa ta ce "Ka tashi Faruk, sannu ya jikin".
"Da saukāi Momi".
"To Allah ya kāara saukāi".
"Amin Momi".
Niyar mikāewa yayi da niyar tashi amma har yau jikin shi ba kāarfi.
Momi ce ta ce "Ina zaka kuma".
Cikin muryar marasa lafiya ya ce "Ina so in je in watsa ruwa ne, jiki na ne nake jin shi ba kāarfi, ga shi ina so in yi sallah laāasar da ban yi ba".
Cikin tausayawa Momi ta ce "Ka bari kaci abinci zaka ji dadāin jikin ka, in yaso sai ka watsa ruwan kayi sallah".
"Bari in je in yi brush in dawo".
"Ok" Momi ta amsa mishi.
Tashi yayi a hankali yake takawa, da alama har yanzu bai gama jin kāarfin jikin shi ba.
Bandāaki ya shiga ya dāauraye fuskar shi kana yayi brush ya fito.
Dawowa yayi ya jingina da gadon.
Momi ce ta kalli Anisa tace "Je ki kan fridge ki dāakko plate da cup a zuba mishi ya ci".
Anisa ce ta hadāa mishi kakkauran Tea wanda yaji madara a ciki, dāayan plate dāin kuma farfesun kayan cikin ne a ciki.
Momi ce ta amshi tea dāin da plate dāin ta matsa kusa da yaya Faruk dāin.
Tea dāin take bashi a baki wanda yake shan shi kamar madāaci hakan yake jin shi a bakin shi, kadāan yasha tea dāin y ace ya kāoshi, ajiyewa Momi tayi ta fara bashi farfesun, yana shan farfesun ne ba wai dan yana jin taste dāin shi a bakin shi ba, sai don kar ran Momi ya ābaci yasa yake sha.
Dadi ne ya shigo dāakin yayi don ganin jikin yaya Faruk.
Samun shi da yayi ya farka har yana dāan cin abinci yasa yaji dadāi a ranshi.
A hankali ya kāaraso gurin su yana Murmushi ya kalli yaya Faruk ya ce "Jiki yayi saukāi kenan Faruk, Allah ya kāara afuwa da saukāi".
Amsawa yayi da "Amin".
Bayan ya gama cin abincin ne ya mikāe yaje ya watsa ruwa yayi alwala yazo ya rama sallolin da ake bin shi kana ya koma ya kwanta.
Dadi ne ya kira su Abbu ya sanar dasu rashin lafiyar yaya Faruk.
Da daddare sai gasu Abbu, Ummu da yaya Khalil sun zo duba shi.
Jikin Ummu ne yayi sanyi ganin da Momi take amsa musu maganar su kamar ba ta so, tasan hakan bai rasa nasaba da halin da yaya Faruk yake ciki wanda a dalili na hakan ya faru dashi, ko waye aka yi wa dāanta haka dole ne ranta ba zai mata dadāi ba.
Anisa kuwa tun bayan gaishe dasu da tayi ta tashi ta bar dāakin.
Shi kanshi yaya Faruk bai ji dadāin yadda Momi tayi ma su Ummu, da yadda yaga Anisa na share yaya Khalil, yana ganin wannan abin da ya faru tsakanin shi da ni ne, bai kamata su ābullo da wannan matsalar ba duk da yasan dan saboda shi suke yin haka, suna jin haushin abin da na mishi.
Yaya Khalil ne ya tashi ya bi ta dāakin ta amma ta kāi sauraren shi, a iya nazarin da yayi yasan ba abin da ya hadāa shi da ita bare yace fushi take yi dashi, duk wasu kalamai na lallashi da ya kamata ya fadāa mata ta saurare shi amma takāi, sai ma kuka da ta sa mishi.
Jikin shi ne yayi sanyi da kukan da yaga Anisa ta na yi, shi kanshi yanzu dauriya ce yake yi irin ta namiji, gashi kuma Anisa na so ta dāaga mishi hankali da kukan ta.
Cikin kukan take cewa "yaya Khalil ina rokāonka ka kāyale ni, ka barni na ji da halin da nake na halin da dāan uwa na yake ciki a yanzu wanda āyar uwarka ce silar shi shiga wannan halin, yaya Khalil tun da Fatima ta nuna ba ta son dāan uwa na to nima ina ganin babu wani faāida a ci gaba da soyayyar mu, nima ina kishin dāan uwa na kuma ina son sa, yaya Khalil ka fita na ce" ta kāarasa maganar cikin kuka.
Sai yanzu yasan akan abin da yasa Anisa take kāin kula shi, tana mishi haka ne saboda ta rama abin da Fatima ta yi ma dāan uwan ta, yasan ko mai zai fadāa mata ba za ta saurare shi ba, abin da ya fi shine ya bari ta sakko, hakan zai fi sa su fi fahimtar junan su.
Kallon ta kawai yayi ya girgiza kai ya fita daga dāakin.
Yana fita ta sake fashewa da wani kukan, wannan lokacin akan abu biyu take kukan, na son yaya Khalil da ke dāawainiya da ita a cikin zuciyar da rashin yi mishi adalci na hukunta shi da laifin da ba nashi da kuma tausayin halin da yaya Faruk yake ciki.
Haka su Ummu suka yi sallama da su Momi kowa da abin da yake damun shi a ranshi.
Ranar haka yaya Faruk ya kwana da tunanin in da na tafi.
Washegari jikin yaya Faruk yayi saukāi dan ya samu ya fito falo ya zauna, ganin yadda kowa ke nuna mishi kulawa yasa ya saki jikin shi duk kuwa da yadda yake jin zafi a cikin zuciyar shi na abin da na mishi.
Yaya Aminu ma yazo da Anty Jiddah sun zo sun duba shi, yaya Aminu haka ya ci gaba da kwantar mishi da hankali, ya nuna mishi shi kanshi halin da yake ciki na abin da na aikata.
Sun dāan jima a gidan kana suka koma gurin Momi suka mata sallama suka tafi.
Yau kwanan yaya Faruk biyu da zuwan shi Kaduna ya shirya zuwa Wagini gaishe ta, kiran ta da yayi a waya haka ma Dadi ya sanar dashi shima bai samun ta a wayar, hakan yasa ya shirya tafiyar.
Fito wa yayi cikin shigar wani yadi mai laushi kalar ash, in ban da kāamshin turare da yake tashi ba abin da falon yake yi.
Sallama yayi ma su Momi akan ya tafi Waginin, may be zai kwana a can ko ya dawo yau.
Fatan a dawo lafiya suka mishi.
Kasancewar ya sa wa motar speed yasa ya isa Wagini a da wuri.
Hajiya na zaune a tsakar gida tana sauraren radio taji shigowar yaya Faruk.
Sallama yayi yazo ya zauna kusa da ita akan tabarmar da take zaune.
Amsa masa sallamar tayi da faraāa a fuskar ta.
Hajiya ce ta ce "Maraba da mai gidana Soja na kaina, sannu da zuwa".
"Yawwa Hajiya, mun same ku lafiya".
"lafiya lau, ya aiki, ya wajen iyayen naka"
"lafiyar su lau, suna gaishe ki".
"Hajiya lafiya wai ba a samun wayar ki, su Dadi suna kiran ki ba sa samu, nima na kira ba ta shiga sai a ce min a kashe take".
Hajiya dama kamar jira take yi ta fara fadāa "Rashin samu na da ake yi ba zai rasa nasaba da wannan āyar buhun ubar ba, ba yadda banyi da ita ta gyara min wayar nan amma yarinyar nan takāi, idan na ce ta kira min ku a wayar sai ta ce ba ta shiga, haka na gaji na kāyale ta".
Murmushi kawai yayi yace "Wai wace yarinyar ce ki ke magana Hajiya".
"Au kai duk bayanin nan da nake yi ba ka gane wacce nake nufi ba, to amaryar ka nake nufi Fatimaā¦".
Da sauri ya katse da cewa "Wace Fatiman wai Hajiya".
Hajiya ce ta mishi dakāuwa tace "Ungo naka, kaji ni da shakāiyin yaro, yau Fatiman ce ba ka gane ba".
"Hajiya kina nufin Fatiman Abbu, dama tana nan ne".
"Yau kwanan ta kusan shida kenan, na ji kana tambayar dama tana nan ne, kana nufin ba a san tana nan ba ne".
"Tana ina ne Hajiya?".
"Tana can cikin dāaki, hala tana can ta kunna kururuwar shedāan tana saurara, yarinya ba ta da aiki sai kunna wakāokāin soyayya kamar a kanta aka fara".
Bai tsaya sauraren abin jin bayanin da Hajiyan Wagini ta ke mishi ba ya mikāe ya nufi dāakin.
Duk yadda na ābata mishi hakan ba zai hana shi jin dadāin tawowa ta nan Wagini ba, kowa tunanin shi bai kawo nan na tawo ba.
Ni kuwa ina kwance akan gado, earpiece ne a kunne na ina sauraren wakāar Hussaini Danko, sauraron wakāar na ke yi sannu a hankali kamar ni na raira ta, mai taken _SOYAYYA TA_
Bin wakāar na fara yi inda mai amshin take cewa _nima soyayya ta zan furta_
_ba a saka ni rana dāaya in yi gudun ka_, _so dāammara nayi ko za ya saka min hauka_, _ko mutuwa nai zan so a dalilin son ka , _so ajiya nayi ranar shi tazo zan dāauka_, _idan tafiya nayi an ce da gwani amsar ka_, _nace kai na zaāba_, _har zuci bazan canza ba_, _ba kuma zan kāosa baā¦_, _ni kaine burina ba a hana ni zuwa gurin ka_, _so ne jagora na shi ya dasa min kāimarka_, _amsar tambihi na je ka rabe min hujjar ka_, _ya zan yi in kāyale ka in ta zama a cikin cuta_, _so so soyayā¦_
Sauran baitin ne ya tsaya a iya baki na saboda idanuna da suka sauka akan wanda na gani a bakin kāofa yana kallo na.
A hankali ya tako ya kāaraso inda nake ya tsaya yana ci gaba da kallo na, a yanayin shi bazan iya gane halin da yake ciki ba.
Wata irin kunyar yaya Faruk ne ya kama ni da tsoron shi a lokaci guda, daskarewa nayi a zaune ba tare da na iya motsa ko da dāan yatsa na ba.
Wani irin murmushi ya min wanda na kasa fasalta mai murmushin yake nufi a gurin shi.
"Fatima kenan, ashe nan ki ka tawo a na ta neman ki a gida" ya kāarasa maganar yana min wani irin kallo.
A halin da nake ciki na firgici ba zai bani damar in iya budāe baki na in amsa wa yaya Faruk tambayar shi ba.
A yadda na lura ma bai da bukāatar amsawa ta a yanzu.
Ci gaba yayi da cewa "Fatima kamar yadda kike bukāatar in barki da masoyin ki wanda ku ke son junan ku ina ganin lokacin yayi, na yarda ke jaruma ce a soyayya da zaki iya fadāi tashi a kanta, in da kika ban kunya a soyayyar taki shine tsoron da kika sa a ranki har yakai ki ga barin iyayen ki wanda ki ka sa su a cikin halin damuwa, a matsayi kin a āya mace ina ganin ba mutunci ki ba ne barin gari dan ba kowa yasan nan za ki zo ba, hakan da kika yi zai sa mutuncin ki ya zube a idanun mutane, anyway ba dogon zance zanyi dake ba illa in sanar dake *FATIMA NI UMAR FARUK NA HAKāURA DA AURAN KI, FATIMA NA HAKāURA DA SOYAYYAR KI DUK KUWA DA SON DA NA KE MIKI*.
Sauri nayi na dāago kaina na kalle shi, banyi zaton jin wannan kalamen daga bakin yaya Faruk ba sanin son da yaya Faruk yake min ban yi zaton zai yi saurin yanke hukunci irin wannan ba na hakāura dani amma sanin halin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 50