Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
bamu a wannan Kauyen musamman jarumi Imran wanda ya fitar da mu daga duhu zuwa haske. Yanzu kuma gashi kun dawo mana da harkar kasuwancinmu na su daga jiya zuwa yau har baki sun fara cin kasuwarmu. Ni a tawa shawarar iya wannan kokarin da ku ka yi mana ya isa me zai hana ku hakura da shiga cikin wannan daji na farauta saboda mugun hadarin da ke cikinsa?" Koda jin haka sai jarumi Imran ya yi murmushi ya ce, "Ai tunda har muka yi alkawarin shiga babu abinda zaí sa mu janye. Abinda muke bukata kawai a wajenku shi ne ku tayamu da addu'a". Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya juya ya nufi hanyar da za ta kaishi cikin dajin Farauta. Ba tare da fargabar komai ba kuwa su jaruma Suzaila suka bi bayansa, Hasnalu da Lushaira ne daga baya. A Can Birnin Hutaira kuwa, Sarki Imras da Sarki Huraisu na zaune a fada cikin kaguwa bisa jiran dawowar wadannan dakaru masu bakaken tufafi wadanda suka je kashe Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila, amma shiru basu dawo ba a lokacin da ake sa ran dawowar tasu. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin sarakan ke nan suka kasa zaune ko tsaye. Kwatsam! Sai ga daya daga cikin dakarun biyu ya shigo cikin fadar yana layi kamar zai fadi, jini na zuba daga gadon bayansa. Cikin dimauta Sarki Imras ya tari Badakaren ya allafeshi da hannayensa biyu a lokacin da Badakaren ke Kokarin mutuwa ya daka masa tsawa ya ce, "Ina daya abokin aikin na ka? Shin kun sami nasarar kashe Muraisu da mahaifiyarsa kuwa?" Badakaren ya budi baki da kyar ya ce, "Ranka ya dadei wannan bakon jarumi ne ya ceci rayuwarsu lokacin da muka shiga har cikin masaukinsu, An kashe abokin aikina a can, nima da kyar na karaso nan". Garma fadin hakan ke da wuya sai idanun Badakaren suka kafe, jikinsa gaba daya ya sandare ya zama gawa. Koda ganin haka sai Sarki Imras ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki da fusata ya mike tsaye zumbur! ya dubi Sarki Huraisu ya ce, "Dole ne mu yi shirin karshe yanzu tmu tafi izuwa wancan Kauye domin mu yaki su Muraisu da shi kansa wannan bakon jarumi wanda ya ke karesu daga sharrinmu". Da jin haka sai Sarki Huraisu ya dubi Sarki Imras cikin alamun matukar danuwa ya ce, "Ta ya ya ka ke ganin zamu iya samun nasara akansu alhalin yanzu sun san cewa muna harin rayuwarsu tunda gashi mun tura a kashe su bamu sami nasara ba sun tsallake Rijiya da baya?" Sarki Imras ya yi guntun murmushin mugunta ya ce, "Ai yakin sumname zamu kai musu cikin MAMAYAR BAZATO. Tun daga nesa zamu sa ayi ta harbawa Kauyen kibiyoyin wuta yadda koda kibiya ba ta soki mutum ba bai isa ya tsallake masifar wuta ba, Topa Nima AA Misau jin wannan tuggu da su sarki huraisu ke shiryawa yasa zan tsaya nan Saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu Admin AA Misau Ke Magana Ku bibiyemu a shafukan nan Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAU Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q BUSA A MUTU 💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part E💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing by AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ (WANNAN SHINE KARSHEN POSTING DIN MU AKAN LITTAFIN BUSA A MUTU) TUN DAGA NESA ZAMU SA AYI TA HARBAWA KAUYEN KIBIYOYIN WUTA YADDA KODA KIBIYA BA TA SOKI MUTUM BA BAI ISA YA TSALLAKE MASIFAR WUTA BA, KA GA KE NAN komai da kowa da ke cikin Kauyen sai ya kone. Koda jin wannan batu sai Sarki Huraisu ya bushe da dariyar farin ciki saboda ya tabbatar da cewa wannan dabara da Sarki Imras ya zo da ita dole ne ma a sami nasara. Nan take Sarki Huraisu ya bada umarni aka fara shirye-shiryen yaki. Sai da aka tara mayaka sama da dubu dari biyar. Dubu dari uku daga cikinsu duk masu kwari da baka ne. Nan da nan aka gama kimtsa komai Sarki Imras da Sarki Huraisu suka yiwa wadannan dakarun yaki jagora suka fice daga cikin Birmin Hutaira. Duk wanda ya dubi yawan wannan runduna yaji cewa za su je su yaki dan karamin Kauye ne wanda gaba đayan mutanen cikinsa ma basu wuce mutum dubu ashirin ba dole ne ransa ya baci saboda kawai zalunci ne. _Kash! Rashin sani ya fi dare duhu,_ inda su Sarki Hutaira sun san abinda zai biyo baya da ba su yị wannan kuskure ba na bin bayan su Muraisu. Nan da nan su Sarki Huraisu suka ci gaba da durfafar wannan Kauye cikin tsananin sauri ta hanyar amfani da karfin sihirn tsafi don gajarce nisan tafiyar. Ai kuwa sai gashi sun iso Kauyen da safe, kuma tazararsu da su jarumi Imran bisa tafiyar da suka yi izuwa dajin farauta ba ta wuce ta rabin sa'a ba. Lokacin da tazarar da ke tsakanin rundunar su Sarki Imras da Kauyen ba ta wuce taku dari ba sai Sarki Huraisu ya baiwa masu kwari da baka umnarni su fara kunna wuta a jikin kibiyoyinsu. Lokaci guda aka sake basu umarnin harbi. Kaico! Mutuwa ba ta da lokaci. Nan fa aka fara yiwa Mutanen Kauyen ruwan kibiyoyın wuta. Sai dai ka ga kibiya ta soki mutum kuma wuta ta kama jikinsa. Take mutane suka rinka kalmar shahada suna mutuwa. Kauyen gaba daya ya yarmutse. Mutane maza da mata, yara da manya suka rinka guje-guje da iface-iface domin su tsira da rayuwarsu, amma babu wajen gudu, mutuwa ce kadai matserarsu. Allahu Akbar! Komai rashin imanin mutum idan ya ga yadda wuta ta kama Kauyen gaba daya tana ci ganga- ganga kuma ya ga yadda kananan yara, mata da tsofaffi suke mutuwa dole ne tausayi ya kamashi ya zubar da hawaye. Haka dai aka ci gaba da yiwa Kauyen ruwan kibiyoyi har sai da aka daina jin ihu da koke-koken jama'a, kuma sai da Kauyen gaba daya ya kone kurmus sannan aka daina harba kibiyoyin. A sannan ne rundunar ta su Sarki Imras ta karasa daf da Kauyen. Koda su Sarki Imras suka ga gaba dayan mutanen garin sun zama gawa kuma sun babbake sai suka kama dariyar mugunta da farin ciki. Sai da suka yi dariyar suka gaji a lokacin da komai ya gama konewa sai toka da hayaki da konannun gawarwaki sannan Sarki Imras ya bada umarnin a shiga cikin Kauyen a nemo masa gawar Muraisu, Husnaila da ta jarumi Imran domin su shaida da idanunsu su tabbatar da cewa sun mutu. al'amarin su jarumi Imran kuwa, lokacin da suka nausa cikin daji farauta suka durfafi inda wannan Dodanniya take. Sai da suka yi tafiyar rabin sa'a sannan suka hango tsaunin da aka tabbatar da cewa akansa Dodanniyar take rayuwa. Nan take jarumi Imran ya juyo domin ya dubi sauran abokan tafiyar, kawai sai ya hango alamun tururin bayakin vuta a can bangaren da Kauyen yake. Cikin tsananin kidimewa da đimauta ya nunawa su Muraisu hayakin da hannunsa. Suma a rude suka waiga baya suka yi arba da hayakin. Take jarumi Imras ya ce, "Tabbas babu lafiya an kawowa Kauyen can hari bayan tahowarmu." Cikin razani Suzaila ta duti Inran ta ce "To yanzu meye abin yi? Zamu karasa wajen wannan tsauni ne mu yaki Dodanniyar ko kuwa zamu koma can Kauyen ne mu kai musu agaji?" Imran ya ce, "Ai bashi da Wani amfani mu je mu yaki su Dodanniya a yanzu tunda wadanda za mu yi yakin dominsu suna cikin masifa. Kawa: ku zo mu ruga da baya", Imran na gama fadin hakats ai ya juya da baya ya falfala da azababben gudu. Nan take su jarumi Muraisu ma suka rufa masa baya. Birnin Hutaira kuwa, a dai-dai lokacin da su Sarki Imras suka kwashi dakarun yakin su ne suka fice daga cikin Birnin Sarkin Barayi Zaltar ibini Mazwar ya baiyana tsulum! A kofar gidan sarautar. a can Gashi dai gidan a kewaye yake da Dakaru masu tsaro amma ta gabansu ya wuce kuma ya shige har can cikin gidan ba tare da wani ya ganshi ba saboda karfin sihirinsa na bata. Sai da Zaltasr ya shiga har cikin turakar Sarki Huraisu asirinsa bai tonu ba, kuma duk inda ya iske kofa a rufe sai dai ka ga ya ratsa ta cikin bango ya wuce tamkar ratsawar danshi daga cikin karkashin kasa. Lokacin da ya tsinci kansa a cikin turakar Sarki Huraisu sai ya shiga laluben wannan kwalbar sibiri, amma sai da ya caje turakar gaba daya, ko ina da ina ko alamunta bai gani ba. Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalinsa ke nan ya fara tunanin cewa shi ke nan ya yi asarar makudan kudaden da ya dade yana mafarkin mallakarsu rayuwarsa. Har ya juya zai fice daga cikin turakar sai yai arba da wani dan karamin gunki da aka sokeshi a cikin wani dan rami da ke jikin bango. Kai tsaye ya je gaban gunkin yasa hannunsa don ya đauko gunkin. Yana janyo gunkin sai ya' ga wata kofa ta bude a JIkin bangon wacce ko alamunta babu da farko. Yana lekawa cikin kofar dakin sai ya hango tarkacen kayan tsafi iri-iri. Cikin tsananin farin ciki ya kunna kai cikin dakin ya ci gaba da neman wannan kwalba wacce aka sa gashin sihiri a cikinta. AA Misau ke Magana Ai kuwa bai dade ba yana dube-dube ya ga wata 'yar karamar kwalba a cikin wata bakar akwatin karfe. Babu alamar wata kofa a jikin kwalbar, amma kuma ga wani dan siririn gashi a cikinta. Cikin alamun tsananin tsoro Zaltar ya kai hannu zai dauki kwalbar amma sai ya kasa. Kawai sai ya karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku sannan ya dauki kwalbar. Bisa mamaki sai ya ga ya dauki kwalbar lafiya ba tare da wani abu ya same shi ba. Nan take ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya yi girgiza ya bace bat daga cikin dakin tamkar bai taba wanzuwa ba A wajen. Kauyen Zirmal kuwa, lokacin da su Sarki Imras suka sa a shiga cikin Kauyen a nemo musu gawar su Muraisu, sai da aka caje ko ina amma ba a ga gawar ta Su ba. Al'amarin da yai matukar dugunzuma hankalinsu ke nan ainun, Sarki Imras ya kurma uban ihu ya ce, "Tabbas mun yi babban kuskure da muka baro Birnina mu duka. Jikina ya bani cewa can Birnina su Muraisu suka tafi. Idan kuwa can din suka tafi lallai za su yi kokarin dauko wannan gashin sihiri ne. Da zarar sun daukoshi kuwa shi ke nan har abada ba zamu iya kawar da su ba sai sun sami nasara akanmu. Babu wani abu da zamu iya yi a yanzu face mu ruga izuwa Bimina domin mu hana faruwar hakan". Yana gama fadin hakan ya bayar da umarnin a bar Kauyen a koma izuwa Birnin Hutaira. Nan take gaba dayan tawagar ta juya da gudu ana zaburar dawakai aka đauki hanya. Tafiyar su Sarki Imras da kamar kusan rabin sa'a ke nan sai ga su jarumi Imran sun karaso Kauycn a guje Koda suka ga yadda aka kone Kauyen gaba daya kuma aka kashe gaba dayan jama'ar Kauyen maza a mata, sai dukkaninsu suka kamu da tsananin bakin ciki da tausayi suka fashe da kuka. Haka dai suka ci gaba da duba gawarwakin suna kuka saboda tsananin bakin ciki ma jarumi Imran bai san sa'adda ya kwarara uban ihu ba ya durkushe kasa. Daga can sai ya mike tsaye zumbur! a fusace ya zare takobinsa ya yunkura zai ruga da gudu ya bi bayan sawun dawakan su Sarki Imras, saui Suzaila ta yi wuf! Ta sha gabansa ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani cewa idan muka bi bayan abokan gaba a yanzu ba zanu sami nasara ba saboda bisa ganin sawun dawakansu suna da tsananin yawa kuina ka san cewa Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi." Da jin haka sai jarumi Imran ya dubi Sużaila a fusace ya ce, "Kawai kice ba kya so naje na yaki mahaifinki saboda na tabbatar da cewa shi da Sarki Imras ne suka zo suka yi wannan mummunar barna saboda sun turo a kashe su Muraisu basu sami nasara ba". Da jin haka sai hawaye ya zubowa Suzaila ta ce, "Ban taba goyon bayan mahaifina ba bisa duk irin zaluncin da ya yi a baya kawo i yanzu. Na hanaka zuwa ka tunkareshi ne a yanzu saboda na damu da rayuwarka da lafiyarka kuma a shirye nake na taimakeku ku yaki mahaifina da Sarki Imras domin a kawar da su. Abinda ba ran iya ba kawai shi ne ba zan iya kashe mahaifna ba da hannuna." Har jarumi Imran ya budi baki zai ce wani abu sai Husnaila ta tari numfashinsa ta ce,"Abinda wannan yarinyar ta fada maka gaskiya ne Idan har ka ce za ka bi bayan su Sarki Huraisu a yanzu ka yake su ba za ka tab:a samun nasara ba kumna babu wanda zai iya tserar da rayuwarka face Ubangijinka." Koda įin wannan batu sai jikin jarumi Imran yai sanyi, kuma ya dubi lusnaila cikin tsananin mamaki ya ce, "Yanzu kina nufin ki ce da ni kin yi imani cewar babu wani karfi wanda ya fi na Ubangijina?" Husnaila ta yi dan guntun murmushi ta ce, "Duk mai hankali, kuma mai son gaskiya idan ya yi la'akari da irin nasarar da ka sanu a bakin kogi ka kashe wannan katon Kada ya tabbatar da Kartin Ubangijin Musulunci. Na yi maka alkawari ni da dana Muraisu za mu karbi wannan addiní naka mai daraja da adalci, amma ba yanZu ba sai bayan komai ya lafa". Gama fadin hakan ke da wuya sai suka hango wanı AA Misau ke Magana mahayi bisa kan doki a sukwane ya durfafosu. Gaba dayansu sai suka zare takubbansu suka juyo suna kallon mahayin suna jiran karasowarsa. Koda ya kara matsowa kusa sai Husnaila ta shaida mahayin. Ba kowa bane face Sarkin barayi Zaltar ibini Mazwar wanda fuskarsa ke cike da annuri alamar cewa ya samu nasarar aikin da aka turashi yi. Cikin tsananin farin ciki Husnaila ta ruga izuwa wajen Zaltar ta tarcshi. Zaltar na isowa daf da ita ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak, kuma ya sauko daga kan dokin. Nan take Zatar ya dauko wannan kwalbar sihiri daga cikin aljihunsa. Koda HIusnaila ta yi arba da wannan kwalba sai ta kai hannu da nufin ta karba, amnıa sai Zaltar ya janye nasa ya dubeta ya ce, "Haba ranki ya dade ai da sauran magana. Ya za ki karbi wannan kwalba ba tare da kin bani cikon ladana ba?' Koda jin haka sai husnaila ta yi murmushi, nan take ta rafawa Zaltar wadansu kalmomin tsafi guda uku, sannan ta ce, "Sai mun hadu a Birnin Lairuf a ranar da dana ya hau karagar mulki." Nan take Zaltar ya risina ya yi godiya ga Husnaila sannan ya yi ma ta sallama ya ba ta wannan kwalba kuma ya hau dokinsa ya juya da baya ya zaburi dokinsa da gudu cikin tsananin farin ciki. Muraisu ya rugo da gudu wajen Husnaila ya ce, "Ya ke Ummina me ake ciki yanzu? Shin Sarkin 6arayi ya yi nasara?" Husnaila ta ce, "Kwara kuwa, bukatata ta biya. Yanzu mnu je wajen su jarumi Iriran na yi magana da shi" Nan take Muraisu ya takewa Husnaila baya suka dawo wajan su jarumi Imran. Da zuwansu sai Husnaila ta dubi Imran cikin nutsuwa ta ce, "Ya kai jarumin jarumai, ka yi sani cewa ni da dana yanzu mun sami abin dogaron da muka tabbatar da cewa sami zamu iya yakar abokan gabarmu mu hallakasu. Na sani cewa kaima yanzu ka yankewa su Sarki Huraisu hukuncin kisa tunda sun kashe yan uwanka Musulmai, zancen yin sulhu ya kare. Ina mai rokonka da ka bamu dama mu je mu kaddamar musu mu hutassheka yaki da su". Lokacin da Husnaila ta z0 nan a zancenta sai jarumi Imran yai shiru yana nazarin al'amarin. Daga can sai ya dago kai ya dubcta ya ce, "Dalili daya ne zai sa na baku wannan dama. Dalilin kuwa shi ne, kin yi min alkawarin za ki karbi addinina ke da danki. Na yi muku izini ku je ku yaki abokan gabar taku. idan har kun fuskanci wata matsala ko kuma kuna bukatar gudunmawa ku aiko mini. Ni yanzu zamu tsaya mu binne gawarwakin jama'ata da aka kashe a wannan Kauye, kuma mu yì musu addu'a gami da zaman makoki na kwana uku saboda bakin cikin abinda aka rasa. Bayan kwana ukun zanu wuce izuwa Birnin Lairuf domin na kai musu tallan addinina. Da zarar kun sami nasarar kawar da su Sarki Imras sai ku taho Birnin Lairuf mu hadu a can". Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya dubi jaruma Suzaila, Lushaira da Hasnalu ya ce, "ina tausaya muku bisa kasancewar yanzu iyayenku sun zama manyan abokan gabarmu. Ina mai shawartarku da ku dauki hakuri da dangana domin wannan al'amari mukaddari ne daga Allah. Ya kai Hasnalu yanzu kai mene ne matsayinka? Ka ga dai 'yar uwarka ta karbi addinina kai kuma fa?" Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa Hasnalu ya ce, "Ai yanzu na ga zahiri da idanuna don haka bani da sauran kokwanto akan addinin musulunci, a shirye nake na karbeshi yanzu. Mahaifinmu kuwa Sarki Imras duk abinda ya sameshi shi ne kaddararsa tunda Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa ke duka". Da jin haka sai farin ciki ya lullube jarumi lmran. Nan take ya biyawa hasnalu KALMAR SHAHADA va maimaita. Al'amarin da ya jefa Lushaira cikin tsananin murna da farin ciki ke nan bisa musuluntar dan uwanta Hasnalu Husnaila da Muraisu kuwa sai suka zagaya izuwa bayan wata bishiya suka tsaya. Take anan Husnaila ta karanta wadansu dalasiman na tsafi ta tofa akan wannan kwalba. Kawai sai kwalbar nan ta fashe, wannan silin gashi da ke cikinta ya tashi sama ya shige cikin bakin Muraisu. Faruwar hakan ke da wuya sai Muraisu ya ji wani irin azababben karfi ya shiga jikinsa. Kahon BUSA A MUTU kuwa da ke rataye a bayansa sai ya kama jijiga tamkar ruhi ne ya shige shi. Kawai sai Muraisu ya kwarara wani uban ihu, sannan ya ciro kahon daga bayansa ya kafa a baki ya busa. Karar busa kahon ta cika nahiyar gaba daya, ta firgita kowa da komai! Nima Kuma AA Misau jin wannan karar Kaho yasa zan dakata anan Saboda tsaro SHIN SU MURAISU ZA SU DAUKI FANSA AKAN SU SARKI IMRAS? TSAKANIN SUZAILA DA LUSIIAIRA WACE CE ZA TA ZAMA MATAR JARUMI IMRAN? WANE DAN SARKI NE ZAI MUTU YANZU SAKAMAKON BUSA KAIION BUSA A MUTU DA MURAISU YA YI YANZU? Mu hadu a busa a mutu 8 (Kashi na takwas) don jin karshen wannan kasaitaccen kayataccen labari. Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe Sarkin marubuta liutattafan yaki abdulaziz sani madakin gini SAIDAI KUMA KASH AN SAMU MATSALAR RASHIN SAMUN LITTAFI NA 8 DIN A WAJENA WANDA YASA DOLE MU DAKATA ANAN KODA BAMA SO AMMA A CIKIN MAKARANTA IDAN AKWAI WANDA YAKE DA SHI SAI YAMUN MAGANAA PRIVETE ADMIN AA MISAU KE MAGANA An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4