Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
Kirzufa kuma mun san inda suke to mu tashi mutum daya masanin kissa da tuggu mu turashi izuwa wannan Kauye da su Muraisu suka sauka a matsayin Hamshakin dan kasuwa domin ya yi mana leken asiri ya gano mana inda Muraisu da mabaifiyarsa suka kwana. Da zarar mun gano haka sai mu tashi zakwakuran mayaka wadanda suka kware a aikin kisa suje cikin dare kuma a cikin 6ad-da-kama su kashe Muraisu da mabaifiyarsa, sai dai kawaia wayi gari aga gawarsu ba tare da an san wanda ya kashesu ba. Ka ga faruwar bakan ma za ta haddasa rashin fahimtar juna a tsakanin jarumi Imran da su jaruma Suzaila wadanda yake kokarin janyo ra'ayinsu su karbi addininsa. Ka sani cewa idan suka karbi addinin Musulunci mulkinmu ya karye." Koda Sarki Imras yazo nan a zancensa sai Sarki Huraisu ya bushe da dariyar farin ciki ya cc, "Ya kai abokina hakika yanzu na dada gamsuwa cewar karfin damtse da karfin sibiri basu kadai bane abubuwan da suke kai mutum izuwa nasara ba. Tunani, hange da basira sune akan gaba. Tabbas zamu gaggauta amfani da wannan shawara ka amma dola nc na za6o gawurtaccen jarumi wanda zan d ya yi wannan aiki saboda koda asirinsa ya tonu ya ZAmana cewa zai iya kare kansa". Haka dai Sarki Imras da Sarki Huraisu suka ci gaba da tattaunawa bisa wannan matsala har izuwa lokaci mai tsawo sannan suka yi sallama aka kai Sarki Huraisu izuwa masaukin sa. a can suka tattaunawa a tsakaninsu sai aka rabu akan cewa gobe da safe za'a dugunzuma a tafi izuwa can bakin kogi da ke karshen gari domin a yaki wannan katuwar masifaffiyar Kada wacce ta hana mutunen Kauyen gabatar da sana'ar kamun kifi. Nan take aka masaukinsu. Kauyen kuwa bayan su jarumi Imran Sun gama aka kai Muraisu da mahaifiyarsa Jaruma Suzaila da tawagarta ma sai aka basu nasu masaukin dabam, shi kuwa jarumi Imran shi kadai aka bashi masauki a wani gida da ke makwabtaka da shugaban Kauyen. Lokacin da jarumi Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila suka shiga cikin nasu masaukin suka kwanta domin suyi barci sai barcin ya gagara domin domin kowannen su Zuciyarsa a cike take da tunani gami da wasi- wasin anya burinsu na ganin abokan gabarsu zai cika?". Koda Husnaila ta fahimci cewar duk su biyun suna cikin damuwa ne iri daya sai ta dubcshi ta ce, "Ya kai dana na san duk abin da yake damunka, kana tunani ne akan yadda za mu sami nasarar ganin bayan abokan gabnmu. Shin kamanta da duk shirin da mukayi a baya?" Na gaya maka cewa abu na farko da zamu yi shi ne mu tura a Sato mana wannan kwalbar sihiri wacce wannan gashi ke ciki a wajcn Sarki Huraisu tun da indai muka mallaki gashin ni na san hanyar da zamu bi mu dawo da sihirin da ke jikin kahon BUSA A MUTU, dana dajin Kirzufa." Koda jin wannan batu sai Muraisu ya dubi Husnaila cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Ya ke Ummina yanzu ta ya ya Zamu iya zuwa mu sato wannan gashin sihiri albalin gashi muna tare da jarumi Imran kuma kin san cewa ba zai taba yarda ba dayanmu ya tafi wani wajen ba?". Da jin wannan tambaya sai Husnaila ta yi murmushi ta ce, "Ya dana kayi sani cewa babu abinda kudi ba zai siya ba. AA Misau ke Magana A can Birnin Lairuf akwai wani mutum dana sani wanda ake kira da suna Zaitar ibini Mazwan wanda ya kasance shahararen barawo wanda yake yin sata ta ban al'ajabi. ba. Duk satar da zai yi in dai ba zai samu kudi sama da Dinare dubu dari ba, ba ya yin ta. Kuma a tarihin sana'arsa bai taba samun bacin rana A can gidan sarautar Birnin Lairuf na san wurare uku inda Sarki ya ke ajiyar dukiyarsa kuma ni kadaice na san Sirrin yadda za'a iya bude inda kudin suke a đebo minsu. Zan tura a kirawo Zaitar Ibn Mazwan na bashi kwangilar sato mini wan can gashin sihiri a gidan sarautar Sarki Muraisu bisa sharadin biyansa lada guda biyu Lada na farko kafin ya yI aiknsa zan sanar dashi dala misan tsafin da zai karanta ya bude ma'adanar farko va debo dukiya wacce adadinta ya kai Dinare dubu dari uku. Bayan yaje ya kawo mana kwalbar dake dauke da gashin sihiri zan gaya masa dalamisan isafin da zai karanta ya bude ma'adana ta biyu wacce ke dauke da Dinare dubu dari shida. " Koda jin wannan batu sai Muraisu ya cika da tsananin mamaki da farin ciki ya ce, "Hakika kin zo mana da shawara mai kyau to amma yanzU Wa za ki tasa ki aike shi izuwa Birnin Lairuf don ya kirawo miki Sarkin barayi Zaltar Ibn Mazwar kuma shin kina da ladan da za ki iyar biyan manzon da zai je ya isar miki da sakonki ga shi Zaitar din?". Da jin wadannan tambayoyi guda biyu sai Husnaila ta yi murmushi ta ce, "Kada ka damu ya kai dana ai shckaruna a duniya ba za su tashi a banza ba, kuna amfanin ilimi da hankali aiki da su. Yanzun nan za ka ga aiki da cikawa don masu iya magana sun ce, "Da zafi - zafi akan bugi karfe'" Koda gama fadin hakan sai Husnaila take ta bude wata tsohuwar Akwatunta ta karfe waccec tun kan Muraisu ya girma take ajiye da ita a cikin dajin Kirzufa ta dauko kudi kimanin Dinare ashirin, ragowar Dinaren da ke cikn Akwatin kuwa ya kai dubu uku. Nan take ta daure wannan Dinare asbirin a cikin tsumma sannan kuma sai ta dauko alkalami, Tawada da takarda ta rubuta wasika. Bayan ta gama rubuta wasikar ta nannadeta sai ta mike tsaye ta dubi Muraisu ta ce, "Ka jirani zan je gidan shugaban Mutanan Kauyen nan na dawo. Ko kala Muraisu bai ce da ita ya bita da kallo kawai. Lokacin da Husnaila ta isa gidan shugaban Kauyen ta sami ganawa da shi, sai ta ce da shi tana bukatar manzo wanda zai kai ma ta wasika izuwa Birnin Lairuf cikin abin da bai wuce kwana uku ba," Da jin haka sai shugaban ya yi ajiyar numfashi ya ce, "Tabbas ina da wani zakwakurin bawa wanda zai iya yi miki wannan aiki, amma dole ne ki biyashi ladan kudi a kalla Dinare goma sha biyar." Koda jin haka sai Husnaila ta yi murmushi ta ce, "Zan iya bashi Dinare ashirin ma amma ina son ka tabbatar mini da gaskiyarsa da amanarsa". Shugaban ya ce, "Ai tun kafin ma addinin Musulunci ya zo mana wannan bawa nawa ya sami shaidar gaskiya akan aikinsa a wajan gaba dayan mutanen garin nan. Sama da shekaru arba'in yana wannan sana'a ta kai sakonni izuwa birane da kauyuka ba'a taba samunsa da ha'inci ba". Da jin haka sai hankalin Husnaila ya kwanta, nan take ta fiddo wannan Dinare guda ashirin gami da wannan wasika ta mikawa shugaban Kauycn tà ce, "Gashi ka Kirawo wannan bawa naka ka bashi wannan sak0 amma akwai bukatar na gana da wannan manzO". Shugaban ya ce, "Ai wannan mai sauki ne". Nan take shugaban ya kwalawa wani bawansa kira ya shigo cikin harabar gidan ya dubeshi ya ce, "Ma za ka je ka kirawo mini Ashtar manzon sako. AA Misau ke Magana Bawan ya risina ya ce, "An gana ya shupabana" Nan take bawan ya fita da gudu ya tafi cika umarni Jim kadan kuwa sai ga Ashtar manzon sako ya iso Da zuwansa sai ya yi sallama. Shugaban ya amsa masa sallamar sannan ya shigo cikin harabar gidan ya iske Husnaila tare da shugaba a Zaune. Cikin ladabi manzo Ashtar ya isina ya kwashi gaisuwa sannan ya zauna a gefe guda. Nan take shugaba ya dubi Ashtar ya ce, "Wannan ita ce Husnaila matar marigayi Sarki Muraisu na Birnin Lairuf Yanzu za ta ba ka sako izuwa Birnin Lairuf kuma zata biyaka ladan aiki". Koda gama fadin hakan sai shugaban ya mike tsaye ya basu wuri. Nan take Husnaila ta mikawa Ashtar kudi da wasika ta dubeshi ta ce, "Ga ladan aikinka Dinare goma, wannan wasika kuma idan ka isa Birnin Lairuf sai ka nemi Zaltar ibini Mazwan ka bashi". Sa'adda Ashtar yaji wannan batu sai ya yi dan jimn yana tunani cikin alamun 'yar damuwa. Ilusnaila ta dubeshi ta ce, "Lafiya, tunanin me ka ke yi haka? Ko kana gantn cewa ba za ka iya wannan aiki bane?" Ashtar ya yi murIushi ya cc, "Ai gabatar da wannan aiki mai sauki ne a gareni tamkar Cire silin gashi ne daga cikin tandun mai. Kawai inda matsalar take shi nc, wannan mutum da kika aikeni wajensa barawo ne shahararre kuma gagararre. A matsayina na ma'aboci addinin Musulunci a yanzu laifi ne na taimaki mai laifi ya sami nasarar cutar da wani." Koda jin wannan batu sai Ilusnaila ta yi murmushi ta ce, "Kada ka damu ai ba dukiya na umarceshi da satowa ba, rantse da darajar iyaycna abinda zai samo min ko dinare daya ba za a iya siyansa ba domin wani silin gashi ne guda dava na kan bil'adama, kuma ni da dana kadai gashin zai yiwa amfani". Koda jin wannan batu sai hankalin manzo Ashtar ya kwanta. Nan take ya karoi sakon Ilusnaila sannan ya yi ma ta alkawarin cewar lallai a cikin abinda bai wuce kwana uku ba zai dawo. Ba tare da bata wani lokaci ba Ashtar ya yiwa Husnaila sallama ya tafi, itama sai ta yiwa shugaban Kauyen sallama ta nufi masaukinta. Lokacin da Husnaila ta iso masaukin na ta sai ta iske jarumi Imran tsaye a kofar gidan da aka saukcsu fuskarsaa murtuke babu alamar annuri. Nan take taji zuciyarta ta buga da karfi, tsoro ya dabaibayeta saboda kwarjininsa. Cikin alamun ashin gaskiya lHusnaila ta karaso kusa da jaruni Imran ta tsaya tana mai sunkui da kanta kas. Shi kuma sai ya dubeta cikin biyayya da girmamawa ya ce, "Ya ke Ummul Muraisu kin sani cewa rayuwarku a cikin hadarí take ke da danki saboda me kuma za ki dinga fitowa daga cikin masaukinku kina yawo a cikin garin nan? Hakkina ne na kula da lafiyarku da rayuwarku a yanzu tunda ni ne na baroku da inda babu wanda ya isa yaje har can ya cutar da ku. Ki sani cewa tun dazu ina biye da ke na ga saadda kika fito daga cikin wannan gida da aka saukeku har kika isa gidan mai garin nan. Bani da sha'awar sanin abinda ya kaiki can, amma hakkina ne na san duk inda za ku je ke da danki a ko yaushe, don haka in dai kuna bukatar za ku je wani wuri to ku fara sanar da ni". Lokacin da jarumi Imran ya zo nan a jawabinsa sai lHusnaila ta dubcshi cikin alamun nadama bisa abinda ta aikata ta ce, "Ka gafarceni ya kai wannan jarumi mai ban al'ajabi, ka yi sani cewa daga yanzu duk inda zamu je ni da dana sai mun sanar da kai". Koda jin haka sai jarumi Imran ya yi ma ta guntun murmushi ya ce, "Shi kenan, kOmai ya wuce sai da safe", Yana gama fadin hakan sai ya yi tafiyarsa ya nufi nasa masaukin, amma yana waige-waige da kalle-kalle don tabbatar da tsaro. Dama kuma tun kafin akai kowa masaukinsa sai da ya sa shugaban Kauyen ya samo dakaru aka baza su suka kewaye gidajen da aka saukesu don tabbatar da tsaro don kada mekiyan su Muraisu su kawo harin sumame ba a sani ba. Kai hatta gidan da aka ajiye Muraisu da mahaifiyarsa a ciki sai da jarumi Imran ya karanta addu'o'in tsari a cikinsa ya tofa a gabas da yamma, kudu da arewa. Wannun shi ne abinda ya faru a can Kauyen jarumi lmran suka sauka. AA Misau ke A can Birnin Hutaira kuwa, kashe gari da sassafe Sarki Imras ya sa aka yi masa iso a wajen Sarki Huraisu. Bayan sun gaisa sai Sarki Imras ya dubeshi ya ce, "Ina labarin Bafataken da za mu tura izuwa Kauyen da su Muraisu suka sauka, shin ka samo wanda ya dace ya yi wannan aiki?" Koda jin wannan tambaya sai Sarki Huraisu ya yi murmushi ya ce, "Ai tun a darcn jiya na gama shirya komai. Yanzu haka ina tare da wanda zai yi mana wannarn aiki." Yana gama fadin hakan sai ya tafa hannayensa sau uku, kawai sai Sarki Imras ya ga wani dogon mutum ma'abocin kwarjini ya fito daga cikin wani daki. Kallo daya mutunn zai yi masa ya gane cewa Attajiri ne kuma sadauki ne saboda yanayin tufafin da yake sanye da su da kuma yanayin siflar jikinsa ta sadaukai. Mutumin ya risina ya gaishe da Sarki Imras ya kame kamar gunki. Shekarun mutumin ba ra su yi kasa da arba'in ba. Sarki huraisu ya gabatar dt mutumin ga Sarki Imras ya co, "Wannan shi ne attajiri AMLAS IBINI BALMARU Kwararre ne shi a iya kasuwanci. Gwani ne shi a iya batar da kama kuma kasurgumi ne akan yaudara da cin amana. Tabbas Amlas ne kadai zai iya aiwatar da wannan aiki da muke bukata komai irin tsaron da za a sa a wannan Kauye sai ya san hanuyar da yabi ya gano a inda Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila suke kwana. Nan take Sarki IHuraisu ya kawo dinare dubu arba'in va baiwa Attajiri Amlas a matsayin guzurinsa na wannan tafiya da zai yi sannan aka yi masa alkawarin ninki uku na abinda aka bashi idan ya cika aikin nasa bida yadda aka umarceshi cikin nasara." Cikin tsananin murna Amlas ya karbi wannan dirhami dubu arba'in yana ta godiya sannan ya yiwa Sarki Huraisu sallama ya tafi. Fitarsa ke da wuya daga cikin turakar sai Sarki Imras yai ajiyar numfashi cikin murna ya ce, "Sai yanzu hankalina ya kwanta. Amma tsawon wane lokaci kake ganin cewa attajiri Amlas zai iya kammala wannan aiki domin mu tura Dakarun da za su kashe abokan gabar tamu akan lokaci?" Sarki I luraisu ya ce, "Zai isa can Kauycn a cikin kwana hudu kuma ya yi alkawarin kammala aikin a cikin kwana goma sha hudu, wato mako biyu kacal. Ka ga ke nan a cikin kwanaki goma sha takwas kacal zai gama". Da jin wannan batu sai Sarki Imras ya bushe da dariyar farin ciki har yana faduwa kasa daga kan kujerar da yake zaune saboda murna. Shima Sarki Huraisu sai ya tayashi yin dariyar har sai da dariyar ta gundurcsu sannan suka daina. Lokaci guda kunna sai Sarki Imras ya fashe da kukan bakin ciki har da hawaye Al'amarin da yai matukar girgiza Sarki Huraisu ke nan ya cika da tsananin mamaki ya dubeshi ya ce, "Ya kai abokina ina dalilin zubar wannan hawaye na ka?" Surki Imras ya cc, "Ya kai abokina ka yi sani cewa ba wani abu bane ya saņi wannan kuka ba face tsananin takaici bisa yadda har yanzu bamu sami nutsuwa ba ta jin dadin Daular Mulkin da muke kai bayan bakar wahalar da muka sha ta neman duniya tunda bamu da kwanciyar hankali sakamakon fargabar abokan gaba. Yanzu dai ka ga ni sai da na shafe sama da shekara goma a cikin daji tare da DAKARUN TAWAYE muna shirya yadda zamu yiwa dan uwana Sarki Muraisu juyin mulki amma abu ya gagara har sai da na hada kaj da kai. Ina ji ina gani muka kashe dan uwan nawa wanda muka kasance jini daya ni da shi kuma shí kadai ya rage mini a duniya don dai kawai na sami wannan duniya. Ga shi na sami duniyar amma ina ji ina gani zama akan karagar mulkin ya gagareni. To wai shin yaushe ne zan sami wannan kwanciyar hankali har dukkan tsoro da fargaba su kau duga cikin zuciyata?" Koda Sarki huraisu yaz0 nan a zancensa sai shima Sarki Imras idanunsa suka ciko da kwallah ya ce, "Ai duk irin ciwonmu daya. Ka tuna cewa fa nima akan na sami wannan duniya Ne na hana 'yar uwata yin aure alhalin babu wata mace mai kyanta a gaba daya wannan Nahiya, amman kuma har gobe ana farautar rayuw:rta duk da cewar ita ce kadai sauran dangina jinina a doron kasa. Hakika yanzu ne na tabbatar da cewa dukiya da mulki su ne babbar masifa ga bil'adama, domin a kansu babu abinda mutum ba zai iya aikatawa ba. Ni kaina AA Misau Akan neman Dukiya ne Yasa zan dakata anan naje nemansu Mai Magana Ko Kuma Nace Naku Akullum Admin AA Misau ke Magana WhatsApp group Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q Facebook page https://www.facebook.com/profile.php?id=100063661782295BUSA A MUTU 💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part C💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing by AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ ( kuciGaba dayi mana likes and comments domin Samun cigabansu akan lokaci) MULKI SU NE BABBAR MASIFA GA BIL'ADAMA, DOMIN A KANSU BABU ABINDA MUTUM BA ZAI IYA AIKATAWA BA. Ai kuwa yadda zuciyoyin nan namu suka kekashe ban ga abinda zai sa mu ja da baya ba ko mu ji tsoro bisa ida nufinmu". Sarki huraisu ya ce, "Kwarai kuwa! Koda kuwa sama da kasa za su hade sai mun cimma burinmu. lokacin da manzo Ashtar ya iso Birnin Lairuf bai zame ko ina ba sai kasuwa. Dama a wannan lokaci ya jagoranci wata tawaga ne ta Fatake wadanda adadinsu ya kai mutum dubu biyu suna janye da rakuma sama da guda dubu uku tare da dakarunsu masu bada tsaro. Bayan wannan tawaga ta sauka a kasuwa kowa ya ncmi hanyar gidan da zai kwana, sai manz0 Ashtar ya kira mai kula da gidan da ya sauka ya dubeshi ya ce, "Samari ina da tambaya. Shin, ko ka san gidan Zaitar ibini Mazwar?" Koda jin wannan tambaya sai saurayin ya guntse bakinsa da hannayensa biyu ya dubi Ashtar cikin álarmun Tsoro ya ce"Ya shugabana akan wane dalili kake neman mutumin da ya zama tamkar dodo a garin nan? Ka sani cewa Zaltar ibini Mazwar baya harka da kowa face manyan Sarakai da manyan Attajirai wadanda suka mallaki dukiya ta gaban kwatance. Ina mai tabbatar maka da cewa baka da abinda Sarkin barayi Zaltar zai saurarcka". Koda jin wannan batu sai manzo Ashtar ya yi murmushi ya ce, "Na san cewa ni bani da kudin da zan iya hulda da Zaltar, amma idan har na yi arba da shi na mịka sakon da aka bani a hannunsa dole ne ya karbeni hannu biyu kuma ya yi hulda da ni. Ni kawai abinda nake da bukata shi ne ka rakani gidan Zaltar domin na gana da shi". Koda jin wannan batu sai mai kula da gidan ya kama noke-noke yana kokarin ya yi tafiyarsa. Nan take Ashtar ya zura hannu a cikin aljihunsa ya dauko dinare biyu ya mika masa ya ce, "Ka rakani inda nake bukata yanzu". Jikin mai kula da gidan na rawa ya karbi wannan kudi ya ce, "Mu je zuwa Mahaukaci ya hau Kura". Nan take Ashtar ya fice mike tsaye ya bi yaron gidan suka Suna fita suka kulle kofar gidan sannan suka kama hanya suka yi ta tafiya har suka iso cikin gari. A sannan ne Ashtar ya ga sun fara wata sabuwar tafiyar. Su kutsa nan su fita can, sai da suka shafe kusan rabin saa suna tafiya kamar ba za su je inda suka dosa ba, sannan suka iso Karshen gari inda suka yi kicibus da wani dankareren gida wanda in banda gidan sarautar garin ba wani gida wanda ya fi shi kyau da kawatuwa. Daga nesa kadan da gidan dan rakiyar ya coge ya Dubi Asbtar ya ce, "To ni fa nan ne iyakata, don haka kai sai ka karasa. Lan jira ka anan idan ka dawo a raye sai mu koma cikin gari tare." AA Misau ke Magana Lokacin da Ashtar yaji wannan batu, sai nan ta ke shima tsoro ya baibayeshi, zuciyarsa ta buga da karfi. musamman da yaji dan rakiyar tasa ya ce sai ya dawo a raye sannan za su koma tare. Amma da ya tuna tafiyar da ya shafe a baya mai hadari ya iso nan Birnin Lairuf sai ya ga ai duk irin hadarin da zai fuskanta yanzu mai sauki ne tunda dai ga shi ya iso inda zai bayar da sakon. Nan take Ashtar ya yi kundumbala ya durfafi wannan kerarren gida wanda sama da Dakaru dubu ke kewaye da shi suke gadi. Tun kafin Ashtar ya karasa daf da kofar gidan, Dakaru kimanin mutum đari uku suka rugo da gudu izuwa gareshi suka yi masa kawanya suna masu zare makamai. Kawai sai daya daga cikin Dakarun ya dubi Ashtar ya ce, "Wane ne kai kuma mene ne ya kawoka nan gidan mai girma Zal tar?" Maimakon Ashtar ya budi baki ya bayar da amsar tambayoyin da aka yi masa sai kawai ya zaro wannan wasika wacce Husnaila ta bashi, ya mikawa wanda ya yi masa tambayoyin ya ce, "Ka kaiwa maigidanku wannan wasika zai gane ko ni waye, kuma zai san daga inda na fito," Mai tambayar ya karbi wasikar ba tare da wata gardama ba sannan ya juya ya nufi wannan gida ya bar ragowar yan uwansa zagaye da Ashtar din suna muzurai, kawai jira suke su ga Ashtar ya yi wani yunkuri na rashin gaskiya su afka masa su hallakashi. Bayan kamar shudewar dakiku dari uku da tamanin da tafiyar wannan badakare sai gashi ya dawo fuskarsa cike da annuri ya dubi Ashtar ya ce "Maigidana yana yi maka barka da zuwa, kuma ya ce na yi maka jagora 1zuwa gareshi". Nan take dakarun da suka yiwa Ashtar kawanya suka Ja da baya suka bude masa hanya ya bi wanann Badakare a bayaa suka durfafi wannan kerarren gida. Koda suka iso kofar gidan aka bude musu suka shiga sai Ashtar ya zamo cikakken dan Kauye ya kama kalle- kalle saboda a iya yawon duniyar da ya yi a rayuwarsa bai taba ganin gidan da aka kawatashi ba kamar wannan. Duk inda suka gifta baya ganin komai face kyawawan kuyangi, furanni da kayan ado iri-iri, wadansu sun isa su yayewa mutum duk irin bakin cikin da yake ciki a rayuwa. Sai da suka wuce manyan fadoji guda shida sannan suka iso fadar Karshe ta bakwai wacce Sarkin 6arayi Zaltar yake zaunc bisa wata kujerar mulki ta alfarma. Hadimai maza da mata sun kewayeshi tamkar wani Serki. Koda shigowar Ashtar cikin wannan fada sai Zaltar ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune cikin matukar farin ciki ya taryeshi yana mai rike hannayensa Karmar wanda ya sadu da dan uwansa wanda suka dade bass hadu ba. Zatar ya ja Ashtar har izuwa kan kujerarsa suka tare yana yi masa lale marhaban Zamansu ke da wuya aka kawo muSu abinci da abin sha suka ci suka yí hani'an, kai ka ce dama sun dade da sanin Juna. Bayan sun kanmala cin abincin sun nutsu sai Zaltar Ya dubi Ashtar ya ce, "Ya kai wannan bakon alheri ka yi sani cewa ban taba yin farin ciki ba irin na yau saboda muhimmnancin wannan sako da ka kawo mini domin kuwa sako ne wanda na dade ina jiransa tsawon shekara da shekaru. Yanzu zan sa a kaika masaukinka ka kwanta ka huce gajiyar taliya in ya so gobe da safe sai na sallameka ka koma izuwa Kauyen da ka baro mai girma Husnaila." Nan take Zaltar ya sa aka tafi da Ashtar izuwa masaukinsa inda aka shigar da shi cikin wani kasaitaccen daki mai dauke da luntsumcmen gado. Akan gadon a kwakkwance wadansu kyawawan kuyangi ne su shida sun ci ado suna ta faman kamshi. Koda Ashtar ya yi arba da wadannan kyawawan kuyangi sai ya daka tsalle ya fada tsakiyarsu ya yi kwanciyarsa, su kuwa suka shiga yi masa tausa kai ka ce shi ne maigidan. Kashe gari kuwa da safe Sarkin barayi Zaltar ya kawo amsar wasika ya bai wa Ashtar sannan ya bashi tukuici na dinare dubu goma kuma ya hadashi da Dakaru hamsin ya ce su yi masa rakiya har izuwa Birnin Lairuf don tabbatar da cewa ya isa gida lafiya saboda kasancewar babu fatake abokan tafiya da za su koma tare da shi tunda ba su kammala harkokin kasuwancin su ba. Farin ciki a wajen Ashtar a wannan rana ba zai misaltu ba domin a iya rayuwarsa ta duniya bai taba mallakar dinare dubu daya ba ma nasa na kansa, amma yau gashi shi ne da dinarc dubu goma nasa na kansa. Wannan shỉ ne abinda ya faru a Birmin Lairuf bayan manzo Ashtar ya sadu da Sarkin barayi Zaltar ibini Mazwar. A can Kauyen da su jarumi Imran suke kuwa, lokacin da gari ya waye sai kofar gidan maigari ta cika makil da jama'a saboda murna da đokin gagarumin aikin da za a fita a yau na zuwa bakin kogi domin a kawar da wannan katuwar Kada wacce ta hana yin sana'ar su a garin. A wannan lokaci ne jarumi Imran, Suzaila, Muraisu da Husnaila tare da Dakarun Gimbiya Suzaila suka fito a cikin gagarumar shigar yaki kowannensu na rike da makamai. Kawai sai jarumi Imran ya dubi shugaban Kauyen wato maigari ya ce, "To mu zamu tafi izuwa can bayan gari inda kogi yake domin kawar muku da wannan muguwar Kada wacce ta hanaku yin su. Abinda nake bukata da ku shi ne, ku tayamu addu'a Allah ya bamu sa'a akan wannan Kada". Koda jin haka sai gaba dayan mutanen Kauyen suka yi kabbara da karfi, Imran da Lushaira ma sai suka yi Koda hasnalu da Muraisu suka ji Lushaira ma tayi kabbara sai suka cika da tsananin mamaki suka kura ma ta Idanu domin su dai a saninsu basu san lokacin da ta musulunta ba don haka akan wane dalili za ta yi wannan kabbara?" AA Misau ke Magana Koda Lushaira ta fabimci cewar tayi subud-da-baka ta tonawa kanta asiri sai ta sunkui da kanta kas tana basarwa. Ba tare da 6ata wani lokaci ba jarumi Imnran ya dubi Maigari ya ce, "Kada wanda ya ce zai biyomu a baya don ya ga irin gumurzun da zamu yi da wannan Kada. Mu kanmu bamu da tabbacin zamu sami nasarar hallaka wannan Kada sai abin da Allah Ya zaryar, don haka idan kunne yaji to gangar jiki ta tsira. Yanzu zamu tafi da zarar kun jiyo bushin kaho daga can bakin kogi to mun sami nasarar, idan kuwa kuka ji shiru mun hallaka." Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya juya ya wuce kan gaba izuwa hanyar da ta nufi kogi, suma sauran jaruman da abokan tafiyarsa sai suka bishi duu! a baya aka bar gaba dayan mutanen Kauyen a tsaitsaye tare da maigari a kofar gidansa suna masu binsu da kallo. Da yake Lushaira na biye da jarumi Imran daf da daf sai ya faki idanun kowa ya rada ma ta addu'ar da za ta dinga karantawa a ranta don kariya ba tare da kowa ya ji ba. Sai da suka shafe kusan sa'a daya da rabi suna tafiya sannan suka iso bakin wannan kogi sannan suka tsaya suka yi cirko-cirko suna kallon kogin kawai a

Chapter 2 of 4