Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
lokacin da tazarar su da kogin ba ta wuce kamu ashirin ba. Ko alamar Kadan ba su gani ba kuma babu wani bakon sauti a cikin kogin face na gudun ruwa. A dai-dai wannan lokaci ne jarumi Imran Muraisu ya ce, "Yanzu ta ya ya kuke ganin zamu iya ya dubi su tsokano wannan Kada ya fito?" Koda jin haka sai kowa ya yi shiru aka kama kallon juna aka rasa wanda zai bashi amsar tambayar. Koda ganin haka sai Imran ya yi murmushi ya ce, "Kada fa ku manta baya na gaya muku cewar ba wai tsagwaron karfin lan senmu banc zai bamu sa'a dole sai mun yi amfani da basirarmu da hikimarmu sai kuma taimakon Ubangijin grskiya." Koda jin wannar batu sai jarumi Muraisu ya numfasa va ce, "Ni ina ganin cwa dabarar da zamu iya yi mu sa Kadan nan ya fito tbu daya ne, dole ne mu samo fatsa mu jefata a cikin wannan kogi mu fara su. Tun da dai Kadan ya san an daina zuwa yin su a wannan kogi, to wata kila kamun Kifin ne baya so don haka da zarar mun fara zai fito don ya hallakamu". Koda jin wa wanr an batu sai jarumi Imran ya yi murmushi ya ce, "Tabbas ka amsa tambayata dai-dai. Na yaba da tunaninka da lasirarka". Nan take jarumi imran ya bude wata jaka da ke rataye a kafadarsa ya fiddo fitsa guda daya tal ya ce, "A cikinmu waye zai jarraba shiga wannan kogi ya yi su?" Nan fa kowa ya kama muzurai aka rasa wanda zai ce zai iya. Kawai sai iarv mi Imran ya yi murmushi ya ce, "Ni Zan shiga cikin kogin na jarraba. Amma gaba dayanku ku zauna cikin shiri". Koda gama fadin hakan sai jarumi Imran ya durfafi cikin kogin yana inai karanta wata addu'a a cikin ransa, kuma yana rike da vvannan fatsar da hannu daya, daya hannun nasa kuwa ya dafe kufen takobinsa. Imran ya shiga cikin kogin sai ya jefa fatsarsa a ciki ya fara yin su. Ai kuwa sai gashi nan da nan ya fara kamo wadansu manyan kifaye. Haka dai ya ci gaba su yana waige-waige da kalle- kalle a cikin ruwan domin ya ga ta inda Kadan za ta bullo masa, amma shiru kamar Malam ya ci Shirwa. Su jaruma Suzaila da ke tsaitsaye a can bayansa a gabar tekun kamar ka ce kyat su fita da gudu sai kyarma jikinsu yake duk da kasancewar su manyan sadaukai masu dakawa maza gumba a hannu. Ashe duk wannan abu da ke faruwa tun dazu Kadan ya ga sa'adda jarumi Imran ya shigo cikin kogin sa'adda ya yi lambo a can karkashin kogin, amma da zarar ya durfafi inda jarumi Imran din yake wannan su sai yaji kamar gagarumar wuta ya durtafa wacce ke barazanar narkar da dukkan jikinsa. Wanann ta faru ne albarkacin addu'ar da jarumi Imran ke karantawa a cikin ransa. Lokacin da jarumi Imran ya sami dan lokaci mai tsawo yana karanta wannan addu'a kuma yana ta yin su abinsa ya zamana cewa komarsa ta fara nauyi saboda ta cika da Kifi, sai ya tsaida yin su din domin ya fito daga cikin kogin. A sannan ne ya sha'afa ga barin ci gaba da karanta addu'ar da ke bakinsa. Ai kuwa sai wannan mugun Kada ya sami damar da ya durfafi inda jarumi Imran ya ke. Sai da ya rage bai fi saura kamu uku ba Imran ya iso bakin gabar kogin sai kawai ya yi arba da wannan Kada daf da shi ya taso sama yana mai wangame bakinsa da nufin ya hadiyeshi. Cikin tsananin zafin nania Imran. ya goce Kuma ya Zare takobinsa ya afkawa Kadan suka kacame da azababben yaki. Duk sa'adda takobin Imran ta hadu da jikin Kadan sai dai ka ga tartsatsin wuta na tashi tamkar karfe da karfe ne suka hadu. Babban abinda ya dagulewa Imran lissafi shi ne, Takobin tasa ba ta iya yiwa Kadan lahanin komai kuma dakushewa take dada yi. Abu na biyu kuma shi ne tun da Imran yake gumurzu da mutane , aljanu da dabbobi bai taba haduwa da halitta tmai zafin nama ba kamar wannan Kada. Saí da aka shafe kusan rabin sa'a ana artabu tsakanin jarumi Imran da Kadar ya zamana cewa Kadan ya kasa hallakashi, shima kuma ya kasa cutar da Kadan. Duk wannan abu da ke faruwa su jarumi Muraisu na tsaye a bakin gabar kogin suna kallo kawai an rasa wanda Tai kaiwa Imran đauki. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face firgicewar da jaruman suka yi sakamakon ganin girman wannan Kada yami da kwarjininsa. Ya yin da Imran ya fara gajiya shi kuwa Kadan yaci caba da kai basa mugaycn hare-harc yana neman hallakashi, ai hankalin Lushaira ya dugunzuma ainun, ba ta san sa'adda ta fashe da kuka ba. Ita kuwa jaruma Suzaila sai ta fusata ainun, bata san sa'adda ta zare takobinta ba ta falfala da gudun tsiya izuwa Cikin kogin tana mai rusa ihu ta kaiwa jarurni Imran dauki. Koda ganin haka sai Muraisu da sauran jaruman ma Suka sani kwarin guiwa suka uga izuwa cikin kogin suka kaiwa jarumi Imran dauki gaba dayansu. Koda Kadan ya ga an yi masa rubdugu sai ya fusata ainun ya rinka kai mugayen hare-hare ta ko ina da bakinsa da jelarsa. Duk sa'adda ya daga katuwar jelar tasa ya kai duka da ita, idan jaruman suka goce jclar ta fado cikin kogin sai ka ji gaba dayan Kauyen ya yi girgiza saboda nauyin jelar Kadar da karfin dukan ruwan da tayi. Wani irin mugun ruri kuwa da Kadan ke yi sai da ya firgita duk wani abu mai rai wanda ke bisa doron kasa da karkashinta a wannan Nahiya. Babu shiri mutane suka rinka toshe kunnuwansu, dabbobi kuwa suka rinka shigewa cikin ramuka suna buya. Ai kuwa ba a dade da fara wannan wumurzu ba Kadan ya fara yiwa jarunan mummunar barna ya rinka yi musu munanan raunika da jelarsa tamkar takobi aka sa ana saransu, sai dai ka ga jikinsu na darewa jini na fallatsi suna ihu suna zubcwa kasa Sumammu. Kafin cikar wani lokaci gaba dayan dakarun da Gimbiya Suzaila ta z0 da su sun zama gawa har da wadannan tagwayen sadaukai. Koda jaruma Suzaila ta ga mummunar barnar da Kadan ya yi sai ta fusata ainun ta kurma uban ihu tana mai Fashewa da kuka. Ba ta san sa'adda ta daka uban tsalle ba sama ta dira akan gadon bayan Kadan ta daga takobinta sama da hannu biyu da nufin ta soke Kadan. Maimakon takobin ta nutse a cikin gadon bayan Kadan sai ta 6alle ta rabu gida biyu. Kafin Suzaila ta yi wani yunkuri tuni Kadan ya sa jelarsa ya dokoto ta baya. Saboda karfin AA Misau ke Magana dukan sai da ta yi sama ta fado wajen kogin ta baje a kasa sumammiya. Al'amarin da ya firgita jarumi Muraisu da Husnaila ke nan, zuciyoyinsu suka karaya, jarumi Imran ne kadai bai karaya ba ya ci gaba da yakar Kadan ba tare da ya gaji ba ko ya ja da baya. A wannan lokaci Lushaira, Hasnalu na can gefe daya a bakin gabar kogin suna kallon ikon Allah. Lushaira tana ta karanta addu'ar da jarumi Imran ya bata, shi kuwa Hasnalu jikinsa na ta karkarwa saboda tsananin tsoro. Gashi dai yana hango jaruma Suzaila a kwance can gefe daya a sume, amma ya kasa kai ma ta dauki. Ana cikin haka ne Kadan ya sake mangare Muraisu da Husoaila, su ma suka sulale kasa sumammu, kuma suka nutse izuwa karkashin kogin. Koda jarumi Imran ya ga sauran shi kadai jal! a gaban Kadan suna fafatawa sai ya kwalla kabbara da karfi yana mai neman taimakon Allah. Ai kuwa sai ji ya yi ya sami wani irin gagarumin karfi irin wanda bai taba ji ba a jikinsa. Take ya daka tsalle sama tamkar an cillashi daga cikin baka ya soke idanun Kadan duka biyu da tsin in takobinsa a lokaci guda. Ai kuwa sai ga jinı yaa feshi la cikin idanun Kadar tamkar idaniyar ruwa ta 6alle. Nan fa Kadan ya kama mata-gun-gun yana birgima akan kogin yana ruri Nan da nan jinin Kadan ya yawaita akan kogin. Sai da Kadan ya shafe kusan rabin sa'a yana wannan mata-gun-gun sannan ya sandare ya zama gawa. A sannan ne jarumi Imran ya yi nuts0 izuwa kasan kogin ya dauko Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila ya fito da su daga cikin kogin ya zubesu a bakin gaba ya shiga danna cikinsu da bayansu ruwa na ta fitowa ta cikin bakinsu. A wannan lokaci ne su Lushaira na suka ruga wajen jaruma Suzaila da ke kwance a sume suka kai ma ta dauki suka fara tsayar da jinin da ke zuba a jikinta sannan suka kama yi ma ta fifita. Cikin ikon Allah kuwa ba a jima ba Suzaila da su Muraisu suka farfado daga dogon suman da suka yi. Koda ganin haka sai jarumi Imran ya mike tsaye cikin murna ya daga kansa sama ya yiwa Allah godiya bisa wannan nasara da ya samu. A dai-dai wannan lokaci ne gawar wannan Kada ta taso saman ruwa, kuma igiyar ruwa ta kadota izuwa bakin gabar kogin. Kawai sai jarumi Imran ya mike tsaye ya dauko wani kaho da ke cikin aljihun igarsa ya busashi. Take sautin karar kahon ya cika Kauyen gaba daya yana amsa kuwwa izuwa cikin dazuzzuka. Koda mutanen Kauyen suka jiyo sautin wannan kaho sai suka zabura, maza da mata, nanya da yara suka rinka falfalowa da gudu izuwa bakin kogin. Duk wanda ya ZO ya ga gawar Wannan Kada sai ya cika da tsananin al'ajabi ya kama yin kabbara yana godiya ga Allah kuma yana yiwa jarumi Imran jinjina. Sannan shima AA Misau aka shiga yi masa jinjina Saboda shine ya Fara saran wannan kada da har aka samu galaba akanta hhhh Zamu dakata anan saikuma wani lokaci idan Allah ya kaimu rai da lafiya Admin AA Misau Ke Magana Ku bibiyemu a wannan shafukan Dandalin Litattafan Yaki By Al'ameen Ahmed Misau DANDALIN LITATTAFAN YAKI BY REAL AA MISAU BUSA A MUTU💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part D💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing by AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ DUK WANDA YA ZO YA GA GAWAR WANNAN KADA SAI YA CIKA DA TSANANIN AL'AJABI YA KAMA YIN KABBARA YANA GODIYA GA ALLAH KUMA YANA YIWA JARUMI IMRAN JINJINA. Al'amarin Muraisu, Suzaila da husnaila kuwa. lokacin da suka farfado daga dogon suman da suka yi, suka ga jarumi Imran a gaban gawar wannan Kada kuma suka ga takobinsa ta yi faca-faca da jini sai suka cika da tsananin mamaki suka sallama masa. Duk su ukun sai jikinsu va yi sanyi kuma zuciyoyinsu suka kama wasiwasin anya kuwa addinin Imran ba shí ne addinin gaskiya ba? Lokaci guda duk su ukun suka mike tsaye suka z0 gabansa suka yi masa jinjina. Suzaila ta dubi gawarwakin jama'arta sai ta fashe da kuka cikin tsananin takaici. Ganin halin da ta shiga ne ya sa kowa ya kamu da tausayinta har jarumi Imran ya zo daf da ita ya shiga rarrashinta yana bata baki. Wannan abu da jarumí Imran ya yi ma ta ba karamin dadi da farin ciki ta ji ba, don haka sai ta daina kukan ta dubeshi cikin murmushi mai taushi ta c, "Godiya a gareka ya Sarkin jaruman duniya." Cikin matukar mamakí Imran ya dubeta ya ce, "Haba ya ke wannan 'yar Sarki saboda me za ki bani wannan matsayi wanda ban cancanta da shi ba? Ki sani cewa ita fa duniya fadi gareta, haka ma abin cikinta yawa yareshi. Ina mai tabbatar miki da cewa akwai jarumai da yawa a cikin duniyar nan wadanda suka fini karfi da jarumtaka nesa ba kusa ba, Suzaila ta sake yin murmushi mai taushi a karo biyu ta e, "Ai ruwan da ya doki mutum shi nc ruwa. Ban ga jarumtakar sauran jaruman da kake fadi ba, ammna na ga ta ka jarumtakar. Na rantse da darajar iyayena ban taba ganin irin taka jarumtakar ba. Lokacin da aka fara gumurzu da wannan katon Kada na ga ka shafe sama da rabin sa'a kana artabu da ita ba tare da ta sami nasarar koda lakutar jikinka ba sai na tsorata da al'amarinka kuma na sallama maka". Koda jin wannan batu sai jarumi Imran ya yi dan guntun murmushi ya ce, "Ai duk wannan jarumtaka da kika ga na yi ba kokarina banc, taimako ne kawai daga Ubangijina. Shin yanzu wannan gagarumar nasara da Ubangijına ya bani na sami nasarar hallaka wanann Kada ba ta isa ta sa ku yi imani ba ku karbi addinina?" Sa'adda Suzaila taji wannan tambaya sai ta yi shiru tana mai sunkui da kanta kas ta ce, "Hakika wannan hujja ta isa ta sa na yi imani da Ubangijinka, amma dai sai mun gama jarraba gaskiyarka da adalcinka kamar yadda Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila suka kuduri niyya. Adalcinka na farko da nake son na gani shì ne, yadda za ka karôi soyayyata kamar yadda ka karbi ta Gimbiya Lushaira. Shin za ka sota nc fiye da ni? Yadda duk kake tunanin cewa Lushaira ta kamu da Sonka, to ni nawa son ya ninka na ta, kuma nima a shirye nake da na kar6i wannan addini naka muddin za ka yi alkawarin aurena. Ka sani cewa kaine irin namijin da na dade in farauta wanda nake mafarkin ya zamo abokin rayuwata. Kai ne kadai wanda na ga ya dace da ni, kuma ina ganin ccwa idan na rasaka hakura da aure ke nan har abada" Koda gama fadin hakan sai jaruma Suzaila ta tafi ta bar jarumi Imran cikin tsananin damnuwa da fargaba bisa kalmomin da ta gaya masa. Muraisu da mahaifiyarsa kuwa, lokacin da suka koma gefe daya, sai Muraisu ya dubeta ya ce, "Ya ke Ummina yanzu dai kin ga irin gagarumar jarumtakar da Imran ya yi da idanunki, kuma kowa ya tabbatar da cewa wannan jarumtaka tasa ta fi karfin ta karfin dantse zallah dole sai dai aga taimako daga wani Ubangiji. Shin me kika yanke hukunci a cikin zuciyarki? Shin Zamu karbi addinin jarumi Imran nc ko kuwa ba zamu karba ba?" Sa'adda IHusnaila taji wannan tambaya sai tayi ajiyar Zuciya ta ce, "Ai ko zamu karbi addinin Imran sai bayan mun cika burinmu mun kashe Sarki Imras da Sarki Huraisu kuma ka hau karagar mulki ta Birnin Lairuf. A sannan ne zamu sami nutsuwa da kwanciyar hankali" Koda jin wannan batu sai Muraisu ya gyada kai ya ce, "Ya ke Ummina da furko kin ce na sami soyayyar Lushaira domin na ji inda mahaifinta ya boye wannan kwalba kum yanzu gashi mun sanıt wanda zai je ya sato mana kwalbar, me ya kamata na yi akan wannan al'amari?" Koda jin wannan tambaya sai Husnaila tayi murmushi ta ce, "Ka janye batun neman soyayyar Lushaira tunda mun sami mafita. AA Misau ke Magana Yanzu kawai abinda muke jira shi ne dawowar manzo Ashtar a gobe ko jibi domin mu ga amsar wasikar da na aikawa Sarkin 6arayi Zaltar ibini Mazwar." Koda Husnaila ta zo nan a zanccnta sai suka ga maigari ya sa an datse kan wannan Kada an ciccibeshi an tafi da shi izuwa cikin gari. Nan take masunta suka yi ta shiga cikin kogin suka kama sana'arsu ta yin su cikin tsananin farin ciki da mnurna. Lokacin da jarumi Imran tare da maigari da sauran jama'a suka iso ko far gidan maigari, sai Maigari ya sa aka kafe kan wannan Kada domin ya zamana cewa ko daga can nesa mutum ya durfafo Kauyen babú abinda zai fara atba da shi face wannan kan Kada saboda ya zamo abin tarihi abin tunawa. A sannan ne jarumi Imran ya yi jawabi mai ratsa zukata ga mutane bisa wannan nasara da Allah Ya bayar aka kawar da mugun kadan, sannan kuma ya tabbatarwa da mutanc cewar gobe kuma za a yı shiri a shiga dajin farauta domin a kawar da wadannan mugayen abubuwa guda uku. Ya ce za a fara ne da yakar wannan muguwar Dodanniya mai hannaye guda goma sha biyu." Nan dai aka sallami kowa, jama'a suka watse, suma Su jarumi Imran sai suka tafi masaukinsu. Har jaruma Suzaila ta Juya za ta tafi izuwa na ta masaukin sai Gimbiya Lushaira ta dubeta cikin alamuin matukar tausayi ta ce, "Ya ke kawata bai kamata ki tafi masaukinki ba ki zauna ke kadai saboda kadaici-da tunani Zai yi miki yawa tunda gaba dayan jama'arki sun hallaka Saura ke kadai. Zai fi kyau ki bimu namu masaukin ni da dan uwana domin mu dcbe miki kewa" busa a Koda jin wannan batu sai hasnalu ya kamu da matukar farin ciki. Ita kuwa Suzaila sai ta dubi jarumi Imran cikin damuwa, amma sai ya yi ma ta nuni da ta amince. Imran ya dubi Lushaira ya ce, "Ya kamata fa ki bi Ka'idojin addini. Kin sani cewa Suzaila ba maharramar Hasnalu ba ce, don haka kada ki bari su rinka kebanta ba tare da ke ba kuma kema kanki bai kamata kí rinka kwana a daki daya ba tare da hasnalu duk da ya kasance dan uwanki. Abinda za a yi yanzu, ke da Suzaila ku rinka shiga cikin daki kuna kwana tarc, shi kuma ya kwana a falo", Gama fadin hakan ke da wuya sai jarumi Imran ya juya ya nufi nasa masaukin. Da isar Imran cikin dakinsa sai ya iske an kawo masa abinci da abin sha. Imran ya zauna ya sa abincin a gaba, amma sai ya kasa ci duk da cewar yana jin yunwa. Ba komai ne ya haddasa hakan ba face tunanin kalmomin da jaruma Suzaila ta gaya masa. Nan fa ya fara zancen zuci yana mai cewa; nan" "To ni yanzu ya Va zun yi da soyavyar mata biyu ke Baya ga wannan kuma sai tunanin gumurzun da zai yi gobe ya fado masa a rai, ya tuno da irin masifar dabbobi ukun da aka yi masa bayani a cikin dajin farautar, sai ZACiyarsa ta karaya sabodą ya tabbatar da cewa karfinsa da dabararsa basu isa su sa ya sami nasarar kawar da mugayen abubuwan uku ba sai dai taimakon Allah. Lokacin da dare ya raba Kauyen yai tsit! ba a jin sautin komai face na gyare da sauran tsuntsaye, sai ga wadansu Dakaru su biyu kacal sun bayyana a cikin garin sun yi shigar bakaken kaya kuma sun rufo fuskokinsu, idanunsu ne kadai a bude. Da yake dare ne mai duhu, ko kadan babu hasken farin wata, sai wadannan dakaru suka saje da duhun gari, in dai ba haskesu aka yi ba babu yadda mutum zai iya ganinsu a lokacin da suke sanda suna durfafar gidan da aka sauki Muraisu da mahaifiyarsa. Wadannan dakaru biyu dai ba wani bane ya turoSu, kuma ya nuna musu gidan da su Muraisu suke ba face Attajiri Almas ibni Balmaru, wanda ya Zo Kauyen a matsayn dan kasuwa ya kama cinikin fatu da yawa har jama'a suka aminta da shi a cikin kwana daya da yini daya. A haka ne ya sami damar gano gidan da aka sauke su Muraisu. A wannan yammaci ya yi amfani da karfin sihirin tsafi ya aikawa su Sarki Muraisu bayanin komai, su kuma suka aiko da wadannan kwararrun dakaru wadanbda suka kware a iya kisa. Lokacin da Dakarun biyu nasu bakaken kaya suka iso kofar gidan da su Muraisu ke ciki sai suka daka Tsalle sama tamkar tsuntsaye suka dira akan saman rufin gidan sannan suka diro kasa a farfajiyar gidan, suka kama sanda da dube-dube. Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda dakarun suka sami damar shiga har cikin harabar gidan ba farc da. masu gadin gidan Sun gansų ba alhalin masu gadin sun kewaye giden ne kuma adadinsu ya kai goma. Koda dakarun biyu suka isa kofar dakin da su Muraisu ke ciki sai suka cika da mamaki domin sun iske kofar ne a bude ba a kulle ta ba. Kawai sai suka kunna kai ciki. Suna shiga suka iske shimfidu guda biyu alamar mutane ne a kwance sun lullube jikinsu da mayafai. Nan take dakarun biyu suka daga takubbansu biyu suka caka a cikin shimfidun. Bisa mamaki sai su ka ji sun caki tudun matasan kai. A fusace suka waigo, sai suka yi arba da jarumi Imran tsaye a gabansu rike da fitilar ice da kuma takobi a hannunsa, sannan suka hango Muraisu da mahaifiyarsa a can gefe daya suna ta shara barci abinsu basu ma san abinda yake wakana ba. Cikin zafin nama suka sake yunkurawa za su kaiwa su Muraisu hari, amma sai Imran ya taresu aka ruguntsume da azababben yaki. Karar haduwar takubbansu ne ya sa Muraisu da Husnaila suka farka daga barcin a firgicc. Koda suka ga jarumi Imran yana yaki da wasu bakin dakaru da suka 6oye fuskokinsu sai su ma suka mike tsaye zumbur! Suka dauko takubbansu da nufin su taimaka masa, amma sai ya yi musu nuni da su bari Nan fa su Muraisu suka zuba ido suka zama 'yan kallo. Shi kansa jarumi Imran bai taba haduwa da kwararrun mayaka irin wadannan masana sarrafa takobi ba, domin wani irin rubdugun har suke kai masa cikin bakin zafin nama ta sama da kasa, gefe da gefe. In ba don shima yana da matukar zafin nama ba da tuni sun sassarashi. Tun ana yin wannan artabu a cikin daki sai da aka fito waje cikin harabar gidan aka ci gaba da masifaffen yaki ya zamana cewa dakarun biyu sun kasa koda lakutar jikin Imran, shima ya kasa lakutar jikin dayansu, sannan kuma ya hanasu zuwa kusa da su Muraisu bare su sami damar hallakasu. Muraisu da Husnaila suka fito daga cikin dakin suka ci gaba da kallon wannan gumurzu suna al'ajabin irin jarumtakar wadannan dakaru biyu. Koda aka dan jima ana wannan dauki ba dadi ba tare da fuskantar wata nasara ba sai dakarun biyu suka fusata suka sauya salon fadan ya zamana cewa suna hadawa da kai naushi da bugu hannu da kafa bayan kai sara. Ai kuwa nan take daya daga cikinsu ya sami nasarar naushin jarumi imran a fuska. Yai baya taga-taga kamar zai fadi amma sai ya tirje ya tsaya daram da kafafunsa. Kawai sai Imran ya ji danshi akan lebensa. Yana shafe leben da hannunsa sai ya ga jini. Al'amarin da yai matukar fusatashi ke nan, shima sai ya sauya salon yakin ya koma yin irin nasa salon. Faruwar hakan ke da wuya sai fadan ya dada rikicewa ya zamana cewa kowa yana jin jiki. Suna bugunsa shima yana bugunsu. A haka ne dakarun biyu suka sami nasarar yankar Imran a lokaci guda. Yankan farko akan damtsen hannunsa na hagu, yanka na biyu a kafadarsa. Amma saboda juriya da jarumtaka irin ta Imran ko yi gezau bai ba, kawai sai ya dan ja da baya ya gyara tsavuwa a lokacin da jini ke diga a jikinsa. Su kuwa dakarun a jikin takubbansu ne jinin Imran ke điga. Koda dakarun biyù suka ga sun sami wannan nasara sai suka yi murmushi, a tunaninsu sun samo lagon jarumi imran, don haka za su iya hallakashi yanzu farat daya. Kawai sai dakarun biyu suka yi kukan Kura suka sake afkawa Imran aka ruguntsume da sabon azabbaben yaki. Wannan karon sai suka ga zafin naman Imran ya ninka nasu, don haka da kyar suke iya kare harin da yake kawo musu. Nan da nan Imran ya rudasu kuma ya shammacesu ya daka tsalle sama ya shallake tsawonsu. Kafin su waigo baya su fuskanceshi tuni ya dankarawa kowannensu sara a gadon bayansa. A tare dakarun suka tsandara ihu suka fadi kasa lokacin da jini ke zuba a bayan nasu. Ba zato ba tsammani sai suka mkie tsaye zumbur! Suka daka tsalle sama suka doki kirjin jarumi Imran yai tsalle sama ya fadi can gefe daya. Kafin ya mike tsaye sai suka cika wandunansu da iska suka falfala da azababbcn gudu domin su tsere. Ai kuwa sai Muraisu da Husnaila suka bi bayansu a guje, aka kasa tscre. A lokacin da dakarun da ke tsaron su Muraisu suka farga da abinda ke faruwa suma sai suka bi bakin a guje. Koda dakarun suka ga sun kasa cimma bakin dakarun sai suka fara sakar musu harbi da kibiyoyi. AA misau ke Magana Cikin sa'a kuwa aka sami daya daga cikinsu a kafa ya kurma ihu ya fadi kasa. Har dayan ya tsaya da nufin ya janye wanda aka harba din, sai ya ga shima za a kamashi sai ya take da gudu don ya kai labari. Lokacin da Badakaren wanda aka harba da kibiya ya ga ba zai iya mikewa ba ya gudu kuma ya ga sauran kiris su Muraisu su iso kansa sai ya zare wata wuka a jikinsa ya kirba a cikinsa ya kashe kansa. A dai-dai wannan lokaci ne su Muraisu suka iso kansa tare da dakaru aka kewaye gawar Badakaren aka tabbatar da cewa ya mutu. A sannan ne ma jarumi Imran ya karaso wajen a guje. Koda ya iske gawar wannan Badakare mai bakaken tufafi sai ya kamu da tsananin bakin ciki da takaici. Kawai sai ya hawaye fuskar Badakaren ya ga bai ma taba ganin mai irin kamanninsa ba. Imran ya caje jikin gawar da aljihunan rigarsa da wandonsa, amma bai sami komai ba. Kawai sai ya mike tsaye ya dubi Muraisu da Husnaila ya ce, "Hakika kuna da sauran kwana a duniya da tuni wadannan Dakaru sun hallakaku in ba don Allah Ya sa na shigo gidan ba a wannan lokaci. Wai shin waye ku ke zaton ya aiko wadannan kwararrun masu kisa domin su hallakaku?" Koda jin wannan tambaya sai Husnaila ta yi shiru tana tunani. Daga can sai ta dubi jarumi Imran ta ce, "Babu wanda ya tanadi irin wadannan kwararrun mayaka a Nahiyar nan kaf face Sarki Huraisu, saboda ya dade yana tanadi akan cikar burinsa." Imran yai ajiyar zuciya ya ce, "Na godewa Allah da wadannan dakaru basu sami nasarar hallakaku ban Da jin haka sai Muraisu da Husnaila suka durkusa a gaban jarumi Imran bisa guiwoyinsu suka kama yi masa godiya bisa ceton ransu da yi. Imran ya yi murmushi ya ce, "Ai mutuwarku a yanzu ba karamar asara ba ce a gareni, kuma rayuwarku za ta kaini ga cimma babban burina". Koda jin haka sai Muraisu da Husnaila suka cika da mamaki, domin basu gano abinda yake nufi da wannan jawabi nasa na karshe ba. Nan dai dakaru suka dauke gawar wannan bakon Badakare suka tafi da ita. Jarumii Imran ya dubi su Muraisu ya ce, "Dole ne mu kara karfin tsaro a Kauyen nan domin makiya ba za su daina yunkurin kawo hari ba." Nan dai kowa ya kama gabansa aka watse. Kashe gari da safe bayan kowa ya kimtsa an yi shirin tafiya Dajin Farauta sai aka taru a kofar gidan maigari kamar yadda aka saba. A sannan ne mai gari ya dubi jarumi Imran, Muraisu, Husnaila da Suzaila ya ce, "Ya ku wadannan manyan Jarumai ku yí sani cewa har abada ba zamu taba mancewa da. ku ba bisa gudunmawar da ku ka

Chapter 3 of 4