Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BUSA A MUTU 💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part A💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing by AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ (ALKAWARIN MU NA NAN DANI DAKU IN KUN LATSA MANA LIKES & COMMENTS KUNA ZUCIYATA 🎧🎤🎷🤓🤓🤓) Labari Ya Isowa Shagala Cewa... DA JARUMI IMRAN DA JARUMI MURAISU DA SU MAHAIFIYARSA HUSNAILA SUKA SHAFE SAMA DA SA'A UKU SUNA FAFATA YAKI, AMMA DAYANSU BAI SAMI NASARAR KODA KWARAZANAR JIKIN DAYA BA. Al'amarin da ya fusata kOwanncnsu ke nan. Da kansu suka ja da baya, suka yi cirko-cirko suna haki da kallon juna. Kawai sai jarumi Imran ya mai da takobinsa cikin kufe yai jifa da ita, sannan ya dubi Muraisu da Husnaila ya ce, "Tun da dai iya yakinmu ya zo daya me zai hana mu jarraba amfani da tsagwaron karfin dantsen mu amma bisa sharadi guda," Cikin alamun fishi da mamnaki jarumi Muraisu ya ce, "Wanne irin sharadi ke nan kake nufi?" Jarumi Imran ya ce, "Sharadin shi ne, idan na sami sarar kaiku kas za ku janye dukkan nufinku ku kar6i addinina. Idan kuma ku ka sami nasara a kaina zan kyaleku ku ci gaba da yin abinda kuka sa a gabanku. Na yi haka ne domin na kawo karshen gardamar da ke tsakaninmu". Koda jin wannan batu sai jarumi Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila suka dubi junansu sannan suka koma gefe daya domin su yi shawara. Muraisu ya dubi Husnaila ya ce, "Ya ke Ummina yanzu ke a ganinki mene ne abinda ya kamata mu yi?" Koda jin wannan tambaya sai Husnaila ta sunkui da janta kas tana tunanı har 1zuwa tsaWon 'yan dakiku, daga can sai ta dago kai ta dubi Muraisu cikin alamun tsananin damuwa ta ce, "Ya kai dana, ka yi sani cewa da dadewa tun ina yarinya Karama na taba ji daga bakin mahaifina cewar ma'abota addinin Musulunci suna da matukar sa'a da nasara bisa duk abinda suka sa a gabansu. Tabbas Biri ya yi kama da Mutum, tunda gashi mun gani a zahiri, ta yadda mu biyu muka kasa samun nasara akan wannan bakon jarumi duk da mun hada KARFI DA KARFE ni da kai. Ni ina ganin cewar zamanmu a cikin wannan daji na Kirzufa yanzu ya kare, domin na fuskanci cewa sihirin da ke cikinsa ya daina aiki tunda gashi KAHONKA na BUSA A MUTU ya daina BUSUWA. Kuma ga dukkan alamu wannan jarumi da ya z0 sai ya fita daga cikin dajin nan lafiya kuma a raye, ka ga ke sihirin dajin ya karye tunda a ka'ida duk mahalukin da ya shigo bai isa ya fita a raye ba. Yanzu idan har muna son wannan KAHO na BUSA A MUTU ya sake BUSUWA, dole ne mu nemo wannan Gashin SIHIRI wanda dan uwana Sarki Imras ya Boye domin bisa binciken da na yi, na gano cevwa da wannan gashi ne kadai zamu iya dawo da karfin sihirin kahon BUSAA MUTU da kuma sihirin wannan daji na KIRZUFA. Ka ga ke nan yanzu zamanmu anan cikin dajin Kirzufa bashi da wani amfani, dole ne mu fice daga cikinsa mu tafi neman GASHIN SIHIRIN. Sabo da haka, yanzu dole ne mu janye yaki da Wannan bakon jarumi tunda ba shi bane abokin gabarmu ba, ko addininsa gaskiya ne ko karya ne ba ta tashi mu ke yi ba. Dole ne mu san hanyar da zamu bi yanzu mu gujewa wannan bakon saurayi da abokan tafiyarsa". Cikin alamun tsananin damuwa Muraisu ya dubi mahaifiyarsa Husnaila ya ce, "To yanzu wacce dabara zamu yi mu gujewa wannan bakon jarumi?" Husnaila ta yi murmushi ta ce, "Kar ka damu, zo mu je mu yi magana da shi". Nan take Muraisu da Husnaila suka koma inda jarumi Imran da su jaruma Suzaila ke tsaye suna saurarensu. Da zuwansu sai Husnaila ta dubi Imran ta ce, "Ya kai wannan GWARZON MAYAKI, ka yi sani cewa mu yanzu amince zamu bayar da gaskiya ga addininka, amma sai idan mun zauna tare da kai mun yi maka wadansu 'yan jarrabobi da za su tabbatar mana da gaskiyarka da addininka. Yanzu za mu je mu debo 'yan kayayyakinmu mu biku mu tafi mu bar dajin nan gaba daya har abada ba zamu dawo ba. Amma ka sani cewa Sarki Imras da Sarki Huraisu su ne manyan abokan gabarmu wadanda in dai zamu hadu da su babu abinda zai rabamu da su face KAIFIN TAKOBI! Don haka, kada ka kaimu izuwa garuruwansu". Koda jin wannan batu sai jarumi Imran ya dubi Husnaila cikin alamun damuwa ya ce, "Ya ke wannan 'yar Sarki, ki yi sani cewa koda zamu hadu da su Sarki Imras ba Zan bari su cutar da ku ba, wannan alkawari ne tsakanina da ku. AA Misau ke Magana Ku sani cewa ni ina s0 ne na yi sulhu a tsakaninku domin an riga an yi kuskure tun a baya, tunda dai akwai nasaba ta jini a tsakaninku, ya kamata a yafi juna". Koda jin haka sai hawaye ya zubowa jarumi Muraisu ya ce, "Ta ya ya kake tsammanin zan iya yafewa Sarki Huraisu wanda ya kashe mahaifina, ya jefa mahaifiyata a cikin rayuwar kunci da wahala, rayuwar daji inda babu abinci da abin sha mai dadi, kuma babu makwanci mai kyau, alhalin ada ta saba da rayuwa mai dadi? Kamar yadda nima ba zan iya yafewa Sarki Huraisu ba, haka ma mahaifiyata ba za ta iya yafewa Sarki Imras ba, tunda ya so ya lalata rayuwarta ya hanata yin aure da haihuwa, kuma gashi da shi aka hada kai aka kashe mijinta. Ka yi sani cewa tun dazu mahailiyata ta yi bincike ta gano cewa Sarki Imras da Sarki Huraisu sun yi gagarumin shiri sun taho izuwa nan dajin Kirzufa bisa kan wani aljani domin su hallakamu. Yanzu mene ne abin yi?" Koda jin wannan tambaya sai jarumi Imran ya sunkui da kansa Kas ya yi dan guntun tunani sannan ya dago kai va ce, "Yanzu abinda za a yi, akwai wani Kauye wanda muka ci su da yaki muka kafa addinina a cikinsa, zamu je can mu zauna tare da ku a can. Amma ina son ka gaya mini iva tsawon kwanakin da za ku yi ku gama jarrabani don tabbatar da gaskiyata da adalcina". Koda jin haka sai jarumi Huraisu da mahaifiyarsa Husnaila suka dubi juna, sannan Husnaila ta ce, "Muna son ka barnu kwana ashirin da daya kawai." Koda jin haka sai jarumi Imran ya gyada kai ya ce, "Shi ke nan, kamar yadda kuka yi shawara kai da mahaifiyarka nima akwai bukatar na je na yi shawara da Lushaira, saboda ta zama tamkar 'yar uwata ta jini yanzu tunda ta karbi addinina". Gama fadin hakan ke da wuya sai jarumi Imran ya juya ya koma inda su Husnaila ke tsaye , wato in da ya shata musu layi ya ce kada su kuskura su ketara. Da zuwansa sai ya dubi Lushaira ya ce, "Ya ke 'yar uwata matso kusa da ni donin mu yi shawara a matsayinki na 'yar uwata musulma". Koda jin wannan batu sai jaruma Suzaila taji ta kamu da tsananin kishi, ta jìi kamar ta hana Lushaira zuwa wajen Imran, amma sai ta kanne. Ba tare da 6ata wani lokaci ba Lushaira ta tako Kafafunta ta gota wannan layi wanda jarumi Imran ya shata musu, ta z0 daf da shi ta tsaya yadda har suna iya jin numfashin juna. Al'amarin da ya kara tunzura Suzaila ke nan, jikinta ya kama tsuma. Ita kanta sai taji tana mamakin kanta, na vadda take jin tsananin kishi akan mutumin da bai san ma tana sOnsa ba. Nan take Imran ya kwashe labarin duk abinda suka tattauna shi da su jarumi Muraisu ya zaiyanewa Lushaira. Kuma ya nemi shawararta bisa abinda take ganin zai fishshesu". Koda jin haka sai Lushaira tayi dan shiru tana nazari. Daga can sai ta fago kai ta dubi Imran ta ce, "Ka amince da wannan sharadi da suka zo da shi. Amma fa dole ne mu zuba ido sOsai akansu domin alkawarin duk mutunin da bai addinin Musulunci ba, alkawari ne mara tabbas. Ka sani cewa wadannan mutanc za su iya yaudararmu su gudu su karya alkawarin da ke tsakaninmu. Abu na biyu kuma, dole ne mu kula da alakarsu da su jaruma Suzaila da tamu ni da dan uwana Husnalu, saboda za su iya huce haushinsu akanmu. Ma'ana za su iya kokarin hallaka Suzaila a matsayinta na 'yar Sarki Huraisu ko kuma su yi yunkurin hallakamu ni da Husnalu a matsayinmu na 'ya'yan Sarki Imras, domin su đauki fansa." Sa'adda jarumi Imran yaji wannan batu sai ya jinjina kai ya ce, "Kada ki damu za mnu sa ido sosai akansu ni dai kawai fatana shi ne Allah Ya sa su gane gaskiya kuma su karbcta. Koda gama fadin hakan sai ya koma wajen su jarumi Muraisu ya ce, "Na gama shawara da 'yar uwata kuma na amincc da sharadin da ku ka zo mini da su. Don haka sai ku je ku dcbo kayanku ku zo mu tafi". Cikin farin ciki jarumi Muraisu da Husnaila suka juya da sauri suka nausa izuwa cikin dajin Kirzufa. A kan hanyarsu ne Muraisu ya dubi Husnaila cikin alanun tsananin damuwa ya cc, "Haba ya ke Ummina ya ya ke da muka gama magana akan cewa guduwa zammu yi amma kuma yanzu kı ka sauya magana kika ce zama za mu yi tare da su? Ta ya ya ke nan za mu sami nasarar ganin bay an wadannan abokan gaba namu idan jarumi Imran ya sami nasarar yin sulhu tsakaninmu da su?" Koda jin wannan tambaya sai Husnaila te yi murmushi ta ce, "Ya kai dana kai yaro ne har yanzu baka san cewa yaki dan zamba banc. Tunani na yi na ga cewa idan ma muka gudun ba za mu cimma nasara ba bisa bukatarmu. Idan kana son ka ga bayan makiyinka dole ne ka kusanceshi ka san sirrinsa tukunna, ta haka ne za ka sami lagonsa ka kawar da shi cikin ruwan sanyi. Tunda dai zamu zauna tare da su Husnaila a Kauyen da zamu je har tsawon sati uku, ka yi kokari ka sace zuciyarta ta fada cikin tarkon sonka ta kowacce hanya. Kana da kyau, kuma ka ga jarumi na gaske, wadannan abubuwa biyu da kake da su yana matukar jan hankalin 'ya mace Sai ka yi amfani da wannan dama ka dinga dukan cikin Husnaila har ta sanar da kai inda mahaifinta ya boye kwalbar da ya sanya wannan GASHIN SIHIRI. Da zarar ka sami nasarar hakan sai mu sulale mu gudu mu bar Kauyen da zamu je domin tafiya neman gashin sihiri. Da zarar mun mallaki wannan gashi zamu iya hallaka Sarki Huraisu da Sarki mras cikin sauki tamkar cire silin gashi a cikin tandun mai. Nan dai suka garzaya cikin sauri suka dcbo kayayyakinsu a cikin kogon dutsen da suke kwana. Muraisu ya dauko kahonsa na BUSA A MUTU ya ratayashi a bayansa. Koda suka fito daga cikin kogon dutsen rike da 'yan kayayyakinsu sai suka ga gaba dayan dabbobin dajin sun taru a waje daya sun kura musu idanu sun yi zugum- Zugum. Kai da gani ka san cewa dabbobin suna cikin tsananin bakin ciki da alhini na rabuwa saboda sun fuskanci cewar ranar rabuwa ce ta z0 alhalin AA Misau ke Magana an yi sabo da juna tsawon shekara da shekaru. Nan take zuciyar Muraisu da Husnaila ta karaya, har idanunsu suka ciko da kwallah suka kama zubar da hawaye. Wasu daga cikin dabbobin sai suka taho wajensu suna kwanciya a jikınsu suma suna rungumesu suna shafar jikinsu. Kawai sai Muraisu ya fashe da kuka yana cewa , "Ku Yi hakuri ya ku abokan zama zarmu rabu yanzu, amma zan dawo gareku nan ba da dadewa ba." Nan dai Muraisu da Husnaila suka yiwa dabbobin dajin bankwana suna kuka suka juya suka koma inda su jarumi Imran suke. Nan dai suka dunguma gaba dayansu suka fice daga cikin dajin Kirzufa suka durfafi hanyar da za ta kaisu wannan Kauye wanda suka yi niyyar zuwa domin a zauna tsawon sati uku kamar yadda aka yi alkawari. fitarsu: dajin. daga cikin dajin ke da wuya kamar da tsawon rabin sa'a sai ga su Sarki Imras sun sauka a bakin dajin Saukaisu ke da wuya sai suka sauko daga kan aljanin, Sannan Sarki huraisu ya dauk0 madubin tsafinsa ya shafeshi da hannun hagu. Koda takarkare ya gama ganin abinda yake son gani sai ya Takarkare ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki, har kwallar takaici ta ciko masa idanu. Cikin firgici Sarki Imras ya dubeshi ya ce "Ya kai abokina me ka yani ne a cikin wannan bincike naka? Shin ba za mu iya shiga cikin wannan daji bane?" Sarki Huraisu yai ajiyar zuciya ya ce "Ai wannan bakon jarumi ma'abocin addinin Musulunci ya ruguza mana shirinmu gaba daya. A yanzu haka ya daukc jarumi Muraisu da 'yar uwata Husnaila ya tafi da su izuwa can wanı Kauye inda za Su 7auna tsawon kwana ashirin da uku. Babban tashin hankalina shi ne wannan ne kadai lokacin da za mu iya amfani da shi mu ga bayan Muraisu da mahaifiyarsa amma idan muka bari har suka karbi wannan sabon addini, to fa ba zamu iya ganin karshensu ba. Ni yanzu ma kaina ya daure, ban san ma abinda zamu yi ba. Idan muka ce zamu bi bayansu a yanzu ba zamu iya yin komai ba don jarumi Imran ba zai bari mu taba su ba". Koda jin haka sai Sarki Imras yai ajiyar zuciya kuma yai tunani na tsawon 'yan dakiku, sannan ya dubi Sarki lHuraisu ya ce, "Ya kai abokina, ka kwantar da hankalinka ka sani cewa hanyar kashc makahon Kare yawa gareta. Yanzu abinda zamu yi shi ne mu koma can kasarka nu zauna akwai dabarar da nake so mu yi". Sarki Huraisu ya jinjina ya ce "Me zai hana ka gaya mini dabarar da kake da ita yanzu?" Sarki Imras ya ce, "Ai shirin zaune ya fi na tsaye". Koda jin hakan sai Sarki Huraisu ya koma kan aljani ya zauna, shima Sarki Huraisu sai yą hau, nan take aljani ya bude fuka-fukansa ya tashi da su sama ya nufi hanyar da za ta kaisu Birnin Hutaira. Kallo daya za ka yiwa sarakan biyu ka fahimci cewar suna cikin tsananin tashin hankali da bakin ciki. su jarumi Imran kuwa, lokacin da suka iso Kauye sai Wannan mutanen Kauyen suka karbosu hannu biyu cikin tsananin farin ciki, saboda basu taba tsammanin cewa za su sake ganinsu ba. Shugaban mutanen Kauyen ne ya zo da kansa ya shigar da su har cikin farfajiyar gidansa aka kawo musu abinci da abin sha suka kimtsa. Bayan sun nutsu sai jarumi Imran ya dubi shugaban Kauyen ya zaiyane masa abinda ya kawo su, sannan ya tambayeshi ya ce, "Mencle ne abinda ya fi kawo muku arziki a wannan Kauye?" Da jin wannan ambayà sai shugaban Kauyen ya yi murmushi ya ce, "Ya shugabana babu abinda yake kawo mana kudi sama da cinikin fatocin dabbobi da kuma harkar su (kamun kifi) saboda muna da wani babban kogi da ke can karshen gari, har ta kai cewa baki daga hauren kauyuka da birane sun fara zuwa suna siyayya. Kwatsam! Sai wata matsala ta taso mana wacce ta firgita bakin suka daina zuwa. Matsalar dai guda biyu ce. Matsala ta farko ita ce; Dajin da muke zuwa farauta yanzu ya gagaremu shiga Saboda wadansu mugayen dabbobi uku_da suka wanzu a cikinsa suka hana shiga, Dabba ta farko, wani rikakken Zaki ne mai tsananin Karfi, girma da sihirin da komai yawan mafarauta sai ya tarwatsasu. Sau bakwai ana yin taron manyan mafarauta masu takama da kansu suna shiga cikin dajin domin su kashe wannan Zaki amma dayansu baya dawowa a raye. Mafarautar sun canfa fatar Zakin da cewa duk wanda ya dinka sutura da ita ya sanya a jikinsa, to babu wata dabba da za ta iya gumurzu da shi komai girman ta da karfinta. Dabba ta biyu kuwa, wata narkckiyar Macijiya ce da ke yammacin dajin wacce makami baya tas iri a jikinta, kuma tsawonta ya kai kamu dari uku da sittin, haka ma Ko dutse ta kewaye komai girmansa idan ta matseshi sai dai ka ga yana rugurgujewa. Itama wannan Macijiya sau uku ana jarraba kasheta amma abu ya gagara. Har gudunmawar Dakarun Yaki muka nemo daga manyan birane uku amma duk a banza. Dabba ta uku kuwa, wata Doddanniya ce wacce ke zaunc a arewacin dajin. Ita dai wannan Dodanniya tana da hannaye guda goma sha biyu, shida a hagu, shida a dama. Hannayen na ta suna da wani irin sihiri na karawa kansu tsawo babu iyaka. Kuma da hannu daya Jal tana iya hallaka dakaru dubu a lokaci guda. Hannayen na ta suna da tsananin kaifi tamkar zabira kuma ko ina a jikinsu wadansu abubuwa ne masu kama da Rahonni wadanda ke da tsinin gaske, idan ta soki mutum da su a ciki ko a kirji sai sun hudo ta gadon bayansa saboda tsawonsu. Ko bishiya ko dutse Dodanniyar ta buga da hannun na ta sai dai ka ga ya ragargaje bare jikin mutum. Wadannan mugayen abubuwa uku basu ta ba fitowa ba daga cikin wannan daji amma fa in dai mutum ya kai kansa cikin dajin sunansa gawa. Shi kuwa wancan kogi da ke karshen gari cibiyace ta teku, akwai kifaye masu yawan gaske a cikinsa tamkar idan za'a shekara dubu ana diba ba tsayawa ba za su kare ba. A cikin wannan kogi akwai wata katuwar kada wacce tana iya hadiyar mutum ashirin a lokaci guda kuma da jelarta tana iya yakar mutum dubu saboda tsawon jelar da kaurinta. Sara da suka basa tasiri a jikin kadar kuma duk abin da ta gatsa da hakorata sai ta fasashi koda karfe ne kuwa ba ma dutse ba." Lokacin da Shugaban Kauyen yazo nan a zancensa, sai jarumi Imran da su Muraisu suka yi a jiyar numfashi suka jinjina al'amrin, sannan jarumi Imran ya ce, "Hakika wannan al'amari babba ne, to amnma da izinin Allah zamu magance wannan matsala da ta addabe ku. Karfinmu ko iya yakin mu ba za su sa mu kawar da wadannan abubuwa hudu ba, amma dai za mu ncmi taimakon Ubangijin Musulunci." Ko da gama fadin hakan sai jarumi Imran ya juya ya dubi Muraisu, Husnaila, Suzaila da sauran abokan tafiyar ya ce, "To kun ji dai. matsalar da muka zo muka riska a wannan Kauye wacce bamu san da ita ba sai yanzu don haka ina son mu yi amfani da wannan dama ta zuwanmu wannan Kauye mu taimakawa jama'a. Ni kam nayi alkawari zan sallama raina da jikina don taimakon wadannan mutane don haka wanda duk vake Kaunata ina son ya bayar da gudunmuwarsa. Imran ya dubi Muraisu da Husnaila ya ce, ban ce kuma ku taimaka ba tun da al'amari ne da ya shafi 'yan uwana Musulmai amma dai ku sani cewa duk sa'adda zamu tafi wannan aiki na kawar da abubuwan hudu dola pe mu tafi tare da ku saboda ina tsoron idan muka barku a cikin Kauyen nan makiyanku za su iya kawo muku hari kuma idan suka sameku a yanzu za su iya samin nasarar hallakaku tunda sihirin tsafinku ya daina tasiri, na su kuwa yana yi Alhakina ne na kula da lafiyarku da rayuwarku tun da nine naje na lalata sihirin tsafinku dana dajinku. Ba zan daina tsaron lafiyarku ba har sai bayan na tabbatar da sulhu tsakaninku da abokan gabar taku. Me kuka ce kuna ganin za ku iya hakuri ku bimu izuwa cikin wannan daji?", Koda jin wannan tambaya sai Muraisu ya budi baki domin ya ce, wani abu amma sai Husnaila ta tari numfashinsa ta ce. "Mun amince za mu bi ka izuwa cikin wannan mugun daji da wannan mugun kogi kuma zamu baka gudunmawa da karfin jikinmu iya kar abinda zamu iya." Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullu6e jarumi Imran ya yi godiya gasu Husnaila sannan ya dubi jaruma Suzaila ya ce, "Ku kuma fa? Ku ma kun amince za ku bini izuwa cikin wannan daji da wannan kogi?" Da Karfi AA Misau Yace Mun Amince Zamu biku wannan Kogon hhh kunsan Nima ai Jarumi ne ko Saboda haka Zamu dakata Anan Sai wani lokaci kuma Admin AA Misau ke Magana WhatsApp group https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU 💕 Littafi Na Bakwai (7)🩸 Part B💎 Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴 Typing by AA Misau ke Magana ✍️⭐⭐⭐ (Hallau Yau Ma Dai Ina Dauke Muku Da cigaban Wannan Littafi Ku Bamu Aron Kunnuwanku Kucigaba da antaya manaa likes and comments domin Samun cigabansu akan lokaci) SANNAN INA GABATAR MUKU DA WANI GROUP DA ZAMU RINKA DORA MUKU LITATTAFAN DA KUKENEMA DA MA WANDA KUKA DADE DA KARANTAWA KUKE NEMAN SAKE KARANTAWA https://facebook.com/groups/1511287118906332/ SAIKUNZO KU MA KUN AMINCE ZA KU BINI IZUWA CIKIN WANNAN DAJI DA WANNAN KOGI?" Da jin haka sai Suzaila tayi murmushi ta ce, "A shirye nake da na sallamna raina da jikina don taimakonka, " Koda jin wannan batu sai kuwa ya cika da mamaki domin ba a ga dalilin da zai sa Gimbiya Suzaila ta ce za ta sallama ranta da jikinta ba don taimnakon jarumi Imran tun da shi ba a ga wani abu ba wanda ya yi ma ta wanda ya kamaci ta yi masa wannan hallacci. Ita kuwa Gimbiya Lushaira lokacin da ta ji batun da Gimbiya Suzaila tayi sai kishi ya turnuketa ta rasa abin da ke ma ta dadi Kamar jarumi Imran ya san abin da ke ranta sai ya dubeta ya ce, "Ya ke Lushaira ku kuma fa ke da dan uwanki, shin kuma za ku bini izuwa cikin wadannan wurare guda biyu masu hadari?". Lushaira tayi murmushi ta ce, "Nima a shirye na ke na sallama raina da jikina don taimakonka, sai dai ban san abin da ya ke cikin ran dan uwana ba". Da jin haka sai Hasnalu yai caraf ya ce, "Ai duk inda 'yar uwata ta sa kafarta sai na sa tawa domin ko mutuwa za ta yi ina son mu mutu tare. Sa'adda jarumi Imran yaji haka sai ya sake kamuwa da farin ciki ya dubi gaba dayan abokan tafiyar ya ce a Cikinmu nan akwai jarumai wasu kuma suna da basira gami da hangen nesa saboda haka ina son mu hada kai kuma mu hada KARFI DA KARFE wajen ganin mun sami nasarar kawar da wadannan masifu da suka dakushe kasuwancin wannan Kauye. dan mutum ba zai iya taimakawa ba da karfin damtsensa sai ya taimaka da shawara." Garna fadin hakan ke da wuya Imran ya dubi Muraisu da Husnaila ya ce, "Da izinin Ubarngijina za ku gasgata gaskiyata da adalcina kafin ma cikar sati ukun a cikin gwagwarmayar da fuskanta a cikin wannan daji da wannan kogi. Ya yin da Muraisu da mahaifiyarsa Husnaila suka ji haka sai suka yi murmushi mai nuna rashin gamsuwa domin ko kadan ba sa tunanin cewa jarumi Imran zai iya yin wani abin al'ajabi ko jarumtaka wacce za ta sa su gamsu da cewar addininsa gaskiya ne kuma suna ganin cewar jarrabawar da za su yi masa bai isa ya iya tsallaketa ba. Wannan shi ne abin da ya faru gasu jarumi lmran bayan sun sauka a wannan Kauye. alamarin su Sarki Huraisu kuwa lokacin da suka iso Birnin Hutaira sai suka shiga cikin gidan saruatar suka zauna suka huta aka kawo musu abinci da abinsha na alfarma suka kimtsa. Bayan sun nutsu sai Sarki IHuraisu yai shiru ya fada cikin kogin tunani mai zurfi. Koda Sarki Imras ya lura da halin da yake ciki sai ya dafa kafadarsa ya ce, "Ya kai abokina ka kwantar da hankalinka ka sani cewa yanzu ne ma muka sami hanya mafi sauki wacce zamu iya kawar da su jarumi Muraisu ta banya mai sauki." Koda jin haka sai Sarki Huraisu ya cika da mamaki va ce, wacce hanya ce mai saukI haka wacce kake ganin bukatarmu zata biya?". Imras yai ajiyar numfashi ya ce, Tun da dai yanzu Muraisu da Husnaila sun fito daga cikin dajin

Chapter 1 of 4