Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a yi ba. Ya ja ƙaramin tambulan ya tsiyaya a ciki sannan ya janyo ruwa shi ma ya ɗan tsiyaya a kai kana ya ɗauka. Duk abin da yake Hero kallansa kawai yake yi. Se da ya ga yana shirin kaiwa baki sannan yace

"Wait Friend.. Me nake gani? Kana nufin.."

"Yeap!" Bad ya katse shi da faɗin haka. Wani ihu Hero ya saki hadda miƙewa tsaye. Se kuma ya koma ya zauna yana dariya yace

"Shege Bad Man.." shi dai be bi ta kansa ba ya soma kai cup ɗin bakinsa ya shanye abin da ke ciki tass. Be jira ba ya sake ƙara wata cikin cup ya sake kaiwa bakinsa, shi kuma Hero se zuga shi yake yi cike da farin ciki. Ana cikin haka, zuwa lokacin ya ɗan soma jin kansa na ɗaure masa, dan be tsaya tunanin komai ba ya fara afata a cikinsa. Se dai sam tsadarta ba ta kai wadda yake amfani da ita ba, shi yasa ma ya ji ta kamar wani sabon abu. Wayarsa da ke ajje ta soma ringing. Da idanunsa da ke a lumshe ya ɗan buɗe ya kalli wayar, shi sam be saba jin irin yanayin nan dan ya sha wani abun ba, ya dai buɗe idanun nasa yana gyara zamansa. Ɗaukar wayar Hero yayi yana faɗin

"Noo Bad. Ba zaka iya answering call ba a wannan yanayin.." Ɗan tsuke face yayi yana watsa masa idanunsa duk da har lokacin kansa sake yi masa nauyi yake. Yace bayan ya ɗan janyo iska daga huhunsa

"Give..me.." yayi maganar a ɗan rarrabe yana miƙa masa hannu. Babu musu ya miƙa masa wayar, ba tare da ya kalli me kiran ba ya ɗaga. Daga can ɓangaren Aunty (ƙanwar Mom) tace

"My son.." sarai ya gane muryar wace duk kuwa da yanda yake jinsa kamar ba shi ba. Cikin ƙarfin hali yace

"Yes Aunt.."

"Ya na ji muryarka haka? Ko har yanzu baccin gajiya ka ke?" Auntyn ta tambaya

"Uhmm" kawai ya faɗa har lokacin idanunsa a lumshe. Fahimtar bacci yake yi ne ya sanyata faɗin

"Olright i will call u later.. Sleep well.." Daga haka ta yanke kiran ba dan ta so ba, dan ta so ne su ɗan gaisa sosai saboda yadda wata muhimmiyar tafiya ta kamata a ranar da ya dawo daga California.


.. A nutse ya saka kansa cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Ummeey ta amsa sallamar tana kallansa. Se ya ƙaraso ya nemi waje ya zauna kusa da Ummeeyn. Sanye yake cikin wani tattausan yadi me kyau wanda ya matuƙar yi masa kyau, kansa babu hula, se kwantacciyar baƙa ƙirin ɗin sumar kansa kamar ta larabawa. Yau ne karon farko da na soma ganin kansa a buɗe, ni se na ga ma kamar yafi kyau a hakan. A nutse ya kalli kan gadon da Abeey ke kai a kwance yace

"Ummeey bana son fita. Ki bari na soma kai shi asibiti tukunna." Kallansa Ummeey tayi yanda ta ga damuwa ƙarara a kan kyakkyawar fuskarsa. Se ta maida dubanta kan Abeey tace

"Ka bari ya kai ka a dubaka mana." Girgiza kai Abeey yayi yana ɗan murmushin ƙarfin hali kafin ya buɗe baki yace

"Haba.. haba.. ciwo ne fa kamar na ko da yaushe. Duk kun bi kun damu kanku kamar yau na fara irin wannan ciwon? Kai Affan.." ya dakata yana kallan Gwani

"Na'am Abeey."

"Tashi ka tafi makaranta. Ka bar ɗalibai na jiranka."

"Abeey!" Gwani ya faɗa yana kallan Abeeyn da kana kallansa ka san baya jin daɗi.

"Affan! Ni nace maka ka je koh?" Abeey ya faɗa yana kallansa. Se ya jinjina kai a nutse kafin ya miƙe jikinsa a sanyaye. Duk da be so hakan ba, amma tunda Abeeyn yace ya tafi gwara ya tafi ɗin. Dan haka ya juya ya kalli Ummeey yace

"Ummee bari na je.. Abeey Allah ya ƙara maka lafiya."

"Ameen_Ameen ɗan albarka. Allah ya tsare." Abeey da Ummeey suka kusan haɗa baki wajen faɗar hakan.

"Ameen." Ya amsa a nutse, kafin ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya koma ya sake shiryawa kamar yanda ya saba fita, ya naɗe kansa sannan ya fice zuwa makarantar.




.... "Wato Afaaf baki da kirki koh? Ni zaki zubarwa da mutunci a idon duniya?" Da sauri ta ɗaga kanta cike da mamakin jin furucin Abban. Se dai ta riga ta san halin Abban, idan yana faɗa baya so a ce komai. Hakan ne ya sanyata yin shiru, ta maida kanta ƙasa, kamar mutuniyar kirki ta gaske.

"Tunda har suka kirani suka faɗa min laifinki, hakan ya nuna ba tun yau kika soma ba. Wato kin daɗe kina nuna musu rashin daraja, se da kika kaisu bango sannan suka faɗa min. Ni ba ma su burgeni ba da basu zane min ke ba, sannan kuma ki dawo ni nan na ƙara miki da wani sabon, shashashar yarinya." Sosai Abba ya cigaba da mata faɗa, wanda a yadda na ga yanayinta kamar ya shigeta. Se daga ƙarshe Abba ya ƙare da faɗin

"Ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki ji, ka da ki bari, ka da ki sake a sake kawo min ƙararki daga makarantarku, ko bokon ko islamiyyar. Idan ba haka ba wallahi zan saɓa miki Afaaf, zan saɓa miki kin ji na faɗa miki." A hankali ta ɗaga kai alamar "Ehh" sannan ta buɗe baki a hankali tace

"Ka yi haƙuri Abba."

"Ka da ki sake." Ya faɗa kawai yana soma takawa dan ficewa daga ɗakin.

"Cewa en uwanki su fito mu tafi, yau da kaina zan kai ku." Bata kawo komai a ranta ba, ta miƙe ta koma cikin ɗakinsu, inda Didi ke zaune duk da ba jin faɗan take ba, amma duk a dame take kamar ita aka yiwa faɗan. Da sauri ta kalli Lulun, se dai yanda ta ga fuskarta ne babu yabo ba fallasa ya sanyata ɗan jin sanyi tace

"Lulu!"

"Uhmm! Abba yace ku fito ze kaimu." Tun kafin ta ƙarasa faɗa Little har ya miƙe ya fice daga ɗakin a guje. Didi ta miƙe cikin sanyin nan nata ta riƙo hannun Lulu tace

"Sorry." Ta faɗa fuskarta a ɗan narke. Ɗauke kai Lulu tayi sannan tace

"A'ah. Ai dama haka kike so." Waro manyan idanunta Didi tayi sannan tace

"Nii! A'ah fa.. Ni kawai so nake ki chanja daga wannan Lulun kin ji?"

"Tohm" Lulu ta faɗa.

"Dat's my baby gurl." Didi ta faɗa a ranta tana fatan Allah ya sa daga yanzun Lulun ta chanja gaba ɗaya. Kai tsaye compound ɗin gidan suka nufa. Abba na cikin motar har ya tayar da ita ma. Babu ɓata lokaci suka shige bayan motar dan Little ya shekara a gaba. Se da suka shiga sannan Abba ya tayar da motar suka bar gidan. Kai ba zaka ce Abban ne yanzu ya gama faɗa ba, yanda ya saki jiki yana jan 'ya'yan nasa da hira. Hakan ba ƙaramin kwantar da hankalin Lulu yayi ba, ko babu komai ta san ya sakko. A ƙofar makarantar Abba yayi parking motarsa. Se dai ga mamakinsu su duka, se ya sauka daga motar shi ma. Kallan juna Didi da Lulu suka yi, Lulu ta ɗan karkatar da kanta alamar tana tambayar Didin ko ta san dalilin Abban na yin haka? Girgiza kai Didi tayi. Ganin babu wanda ze amsa musu tambayar ya sanya su saukowa daga cikin motar.

"Abba a dawo lafiya." Suka haɗa baki wajen faɗa.

"Allah ya sa. Mu je ciki, ina son ganin malaminku." Haka kawai dukkansu suka ji jikinsu yayi sanyi, amma se suka basar suka bi bayan Abban dake riƙe da hannun Little zuwa cikin makarantar.

"Afrah kama hannun Little ku shige. Zamu ga Malam Affan." Abba ya faɗa yana miƙawa Didi hannun Little. Karɓar hannun nasa tayi tana faɗin

"Toh Abba." Se ta kalli Lulu da ke tsaye kamar wadda aka dasa. Dan tunda Abba yayi maganar ta kasa cewa komai. Ɗan lumshe mata idanu Didi tayi tana jinjina mata kai dan ta bata ƙwarin gwuiwa. Se itama ta lumshe idanun tana ɗan sauke ajiyar zuciya. Haka nan kawai se ta ji a ranta ba se ta tambayi Abban dalilin tsayawarsu ba, dan ta san zuwa yayi kawai ya gaisa da Gwanin. Malam Ahmad ne ya ƙaraso wajen Abban, ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan Abba yace

"Malam Affan be shigo ba ne?" Jinjina kai Malam Ahmad yayi kana yace

"Wallahi kuwa. Amma na tabbatar wani babban uzuri ne ya riƙe shi. Zaka iya jiransa idan ba sauri kake ba."

"Ehh toh.. da yake dai akwai inda zan je ne, ina ga zan tafi, se na dawo." Wani irin sanyi Lulu taji yana ratsata jin furucin Abban. Sosai hakan ya mata daɗi dan dama bata so a ce Abban da kansa su gaisa da Gwanin. Se dai tun kafin Malam Ahmad ya kai ga cewa komai Gwani ya shigo cikin makarantar cike da takun nan nasa na nutsuwa.

"Aff, ka gan shi ma ya zo." Malam Ahmad ya faɗa yana murmushi. Cikin jin daɗin ganinsa Abba yace

"Toh madallah." Suka sake gaisawa sannan Malam Ahmad ya bar wajen. Se da suka gaisa da Gwani ya faɗa masa Abba wajensa ya zo sannan ya wuce. Wani irin takaici ya zo ya cika Lulu, ta ji kamar tayi kuka dan haushi, ta faki idanun Abba ta watsa masa harara sannan tayi saurin ɗauke idanunta kada ko shi ko Abban wani ya ganta. Sallama yayi sanda ya ƙaraso wajen Abban. Abba ya amsa sallamar yana miƙa masa hannu suka gaisa cike da girmama juna.

"Amm Malam Affan, idan babu damuwa ga Afaaf nan na dawo da ita. Ina kuma sake baka haƙuri don Allah kayi haƙuri, In Sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Nauyin maganar da ke fitowa daga bakin Abban ya sanya Gwani ɗago kai yana girgiza kai sanda wani ɗan murmushi ya suɓuce a kan fuskarsa yace

"Ka dena bani haƙuri don Allah.." Shi ma murmushin Abba yayi kafin yace

"Toh shi kenan. Amma ga ta nan na kawota ta baka haƙuri!" Da wani irin sauri ta ɗaga kai ta kalli Abba tana so ta tabbatar da gasken abin da taji a kunnenta, hakan Abba ya furta? Kallan gargaɗin da taga Abba ya jefeta da shi ne ya sanyata shan jinin jikinta. Shi kuwa Gwani se a lokacin ma ya san da wanzuwarta a wajen.

"Babu komai, kaje kawai, zuwanka ma ya wadatar." Gwani ya faɗa. Girgiza kai Abba yayi be ce komai ba se sake kallan Lulu da yayi kafin yace komai ta fahimci abin da yake nufi. Dan haka ta ɗan lumshe idanunta tana jin yadda bugun zuciyarta ke cigaba da ƙaruwa. Narkakkun idanunta sun cika taff da ƙwallar baƙin ciki ta soma takowa zuwa inda suke. Da ƙyar ta iya tausar zuciyarta ta tattaro kalmar haƙuri, se dai bata kai ga furtata ba ta jiyo muryar Abba na faɗin

"Tsuguna ki ba shi haƙuri." Yayi maganar fuskarsa a haɗe, dan kuwa shi kansa ya soma fuskantar take_taken Lulun, shi kuma ba ze yi sake ba wajen kula da tarbiyyarta. Dan haka idan ma tana tunanin tafi ƙarfin kowa ciki kuwa hadda malaminsu, toh yau ɗin zata gane malamin nasu ya fita matsayi. Sosai taji kanta ya wani irin juya mata, idanunta a rufe na tsawon sakanni, ƙafarta na wani irin rawa, tana jin maganar da Abba ya faɗa ɗin kamar wata wuƙa aka saka aka yanketa. Ita a wajenta ma har gwara a yanketa ɗin da a ce ta tsugunawa Gwani wai ta bashi haƙuri. Kallanta Abba yayi a ransa yana fata kada a ce Lulun ta sake nuna halinta tun ba a je ko ina ba, dan idan hakan ta faru toh babu shakka yau me raba shi da ita se Allah. Cikin rashin sanin mafita ta zube a kan gwuiwoyinta, zuwa lokacin tuni hawayen da suka cika mata idanu sun gama zuba a kan fuskarta. Wani irin sanyi na kaɗa ilahirin jikinta. Ba dan taso ba, ba dan kada ta wulaƙanta Abbanta a gaban mutane ba, da babu abin da ze sanyata tsugunawa ta bawa Gwanin haƙuri, ko da kuwa korarta za a yi daga makarantar. Duk yadda zuciyarta ke mata ƙuna, tana hanata aikata abin da mahaifin nata ya umarceta da yi, haka ta take, ta cije, ta buɗe baki da ƙyar tace

"Ka yi haƙuri.." ta faɗa wasu sabbin hawaye masu ɗumi na kwaranyowa a kan fuskarta, lokaci ɗaya tana ji har abada mutuncinta da kuma ajinta ya gama tsiyayewa a bainar nasi..



*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_11


___"Allah ya kiyaye gaba." Shi ne abin da Gwani ya faɗa yana maida dubansa kan Abba da ya soma faɗin

"Toh Malam Affan, na gode." Ɗan murmushi ne ya wanzu a kan fuskar Gwanin ba tare da yace komai ba, se miƙa masa hannu da ya yi suka sake gaisawa. Daga haka Gwani ya yi hanyar ajinsa cikin nutsuwa. Kallan Lulu Abba ya yi da har yanzun take tsugune a wajen, ta kasa ko da motsa wa ne ballantana ta miƙe. Har kuma lokacin idanunta a rufe suke, ta kasa buɗe wa dan ji take yi kamae tana buɗe wa ɗin za ta ga idanun kowanne ɗalibi a kanta wanda hakan ze tabbatar mata da cewa kowa ya ga wannan dizgin da ya faru da ita.

"Afaaf.." Abba ya faɗa yana kallanta, ganin har lokacin ba ta tashi ba. Se a lokacin ta buɗe idanun nata, se dai har lokacin ba ta tashin ba, saboda yanda take jin ƙafafunta har lokacin na rawa.

"Kee!!" Abba ya sake faɗa. Se a lokacin ta yi saurin tattaro duk wani kuzari da ya rage mata, ta soma miƙewa a hankali, har ta miƙe a kan ƙafafunta.

"Na'am Abba.." ta yi ƙarfin halin faɗar hakan. Duk da ya lura da yadda idanunta suka yi ja, hakan be sanya shi tambayarta dalili ba, dan ya san dalilin. Dan haka se cewa ya yi

"Maza ki wuce aji. A yi karatu lafiya, Allah ya ba da sa'a."

"Ameen." Nan ma ta yi ƙarfin halin faɗa. Se da ya ga ta soma takawa zuwa hanyar da za ta kaita ajinsu sannan Abban ya fice daga makarantar. A hankali ta cigaba da taka wa, tana ɗan lumshe idanunta ko za ta samu ƙwallar da ta rage cikin idanunta ta koma. A haka har ta ƙarasa ajin nasu. Ba tare da ta kalli inda yake zaune ba ta shige cikin ajin lokaci ɗaya ɓacin ranta na ƙaruwa, tana jin wata irin tsanarsa na ratsata. Kai tsaye waje ta samu ta zauna, ba tare da ta lura ma da inda ta zauna ɗin ba. Tunda ta shigo Didi ke kallanta, ta ɗauka yanzun da ta shigo za ta ga canji daga gareta, se dai ba ta gani ba. Ta ɗan lumshe idanunta tana fatan a ce za ta ga ranar da Lulun za ta shiryu.

Wani murmushi Abida ta saki lokacin da Lulu ta zauna a kusa da ita. Se ta saka hannu ta riƙota tana faɗin

"Subhanallahi, masoyiyarta me ya faru?" Ta yi maganar tana kallanta. Hannu Lulu ta saka ta janye hannun Abidar sannan ta ɗauke kai tana jin kamar ana ƙara mata ɓacin rai ne. Ba ta haƙura ba ta sake kai hannunta za ta riƙo na Lulun. Da sauri Lulu ta juya ta watsa mata wani kallan gargaɗi ranta a matuƙar ɓace tace a hankali

"Malama ki bari mana.." ta faɗa muryarta a cunkushe. Jinjina kai Abida ta yi, ashe kenan duk yanda take tunanin Lulun ta wuce haka? Lallae kam akwai aiki babba a wajenta. Ita tunda ta zauna a cikin ajin ba ta san me yake magana a kai ba, saboda takaicin yanda muryarsa ke ratsa cikin ajin cike da nutsuwa, kamar me tantance kowacce kalma. Hakan ne ya sanya gaba ɗaya en ajin suka nutsu, kowanne na saurarar bayaninsa. Kasancewar yau ɗin ba ranar hadda bace ya sanya littafai suka dinga yi babu sanya.


... "Wai me ya faru ne?" Didi ta faɗa tana zama a kusa da Lulu. Girgiza kai Lulu ta yi sannan tace

"Babu komai fa Didi, kawai dai kaina ke ciwo.." Da sauri Didi ta miƙe tun kafin ta ƙarasa maganar

"Kuma na sha magani." Shi ne abin da Lulu ta ƙarasa faɗa kafin Didi ta fita daga ɗakin. Dawowa Didi ta yi tana ɓata fuska, se da ta zauna sannan tace

"Kin tabbatar kin sha?" Da sauri Lulu ta jinjina kai lokaci ɗaya tana faɗin

"Ehh fa.."

"Me ƙarya.?"

"Ɗan aljanna.." in ji Lulu. Se suka yi dariya dukansu, kafin Didi ta miƙe tace

"Se na faɗawa Ammi kuwa.." da sauri Lulu ta riƙo hannun Didi tana narkar da fuska tace

"Ni fa da wasa nake. Kawai dai.." ta faɗa tana cigaba da yamutsa fuska.

"Kawai dai me..?" Didi ta tambaya

"Abin da ya faru a makaranta ne.."

"Oh my goodness.. Lulu me yasa kike son ɗorawa kanki damuwa ne babu gaira babu dalili? Me Gwani ya miki? Me ya tsare miki? Shi fa mutum ne me kirki da sanin ya kamata, me ze sa ya miki wani abun da ba za ki ji daɗi ba? Ya fa san me yake yi, wallahi idan dai har kika bi abin da yake so shi kenan zaku koma zaman lafiya. Mutumin kirki ne.." ta ƙarasa faɗa a gajiye, dan bata san kuma me za ta cewa Lulun bayan haka ba. Dan kuwa ba yau ce ranar farko da ta zauna tana fahimtar da ita kirkin Gwani ba, ba kuma ta san sanda za ta gane hakan ba.

"Tohm Didi na ji.." ta faɗa cike da ƙosawa. "Gwani mutumin kirki ne" ita har ta gaji da jin wannan maganar. Kowa haka yake faɗa a lokuta da dama, se dai ita har yanzun ba ta gani ba. Ita a wajen ta ma ba ta taɓa ganin mutum mara kirki, me girman kai irinsa ba. Kuma abin da ke sake ƙona mata rai da shi, yanda yake taƙama da wata izza bayan shi ba ɗan kowa ba ne. Harara Didi ta jefawa Lulu ba tare da tace komai ba, ta sauka daga kan gadon ta wuce zuwa inda wardrobe ɗinsu take. Kai tsaye wardrobe ɗinta ta buɗe ta soma dubawa da alama wani abun take nema. Zuwa can anjima ta rufe tata. Se ta koma kan ta Lulu ta soma dubawa, duk abin da take Lulu na kallanta, har ta zo za ta ɗauke kai se kuma ta maida kanta wajen Didin da sauri. Babu ɓata lokaci ta diro daga kan gadon ta ƙaraso wajen Didin tana faɗin

"Wai me kike nema ne? Je ki zauna zan duba miki.." ta faɗa tana tuna wayar da Mami ta ajje mata a ƙasan kayanta. Da mamaki Didi ta kalleta, ta riga ta san halin Lulun da kan son jiki, amma yau ita ce ke cewa ta je ta zauna ta bincika mata abu? Lallae. Se ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya tace

"Anya kuwa Lulu? Yau waye ne ya miki faɗa haka?"

"Abba mana." Ta faɗa cikin basarwa tana ƙaƙalo wani murmushi ta yi. Dan ta san idan har ta yi murmushin yaƙe toh Didin kan iya ganota cikin lokaci ƙanƙani.

"Tohm.." Didi ta faɗa tana harɗe hannunta a ƙirji ta koma ta zauna tana kallan Lulun.



.. Da sauri Mommah ta miƙe tana kallan Bad Man ɗin da ya shigo cikin ɗakin. Murmushi ya suɓuce a kan fuskarta. Se ta ƙarasa tana faɗin

"Areef..!"

"Mommah.." ya faɗa da wannan kakkaurar muryar tasa me daɗin sauraro. Babu ɓata lokaci ya cigaba da takawa zuwa cikin ƙaton parlourn har zuwa sanda ya ƙarasa inda jerin kujerun suke, ya nemi waje ya zauna ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan ɗaya. Neman waje itama Mommah ta yi ta zauna, duk da yanda ta ji daɗin ganinsa amma ba ta son abin da ze janyo tashin hankali tsakaninta da Mom. Dan ta san daga wannan ɗan zuwan da ya yi idan har ta sani za ta iya tayar mata da hankali.

"Areef.. Mom ta san za ka zo nan ɗin?" Da mamaki ya kalli Mommahn jin tambayar da ta fito daga bakinta. Se ya ɗauke kai kawai ba tare da ya amsa mata tambayar ba yace cikin er basarwa

"Gud evening.." Ta riga ta san halinsa. Ta san sarai ya ji ta, amsar ce dai ba ze bayar ba. Hakan ne ya sanyata yin murmushi sannan tace

"Ka na lafiya? Ya hutu?" Ɗan murmushin gefen baki ya yi kafin ya ɗan taɓe bakinsa yace

"Uhmm.. Cool.." Murmushi Mommah ta sake yi lokaci ɗaya tana miƙewa ta wuce ƙatuwar freezer da ke can wani ɓangare a cikin ɗakin ta buɗe. Kafin ta kai ga ɗauko komai ta jiyo muryarsa yana faɗin

"I don't need anything Mommah.." ya faɗa yana miƙewa lokaci ɗaya yana gyara zaman hular kansa.

"Haba Areef, ka tsaya ko ruwa mana ka sha.." Mommah ta faɗa sanda take kallansa. Se ya girgiza kai yace

"Not dis tym gaskiya."

"Ohk se yaushe?" Mommah ta faɗa. Kamar me tunani ya ɗan tsaya se kuma yace

"Ahmm bye.." ya yi maganar yana soma takawa ya fice daga ɗakin. Se ta bi shi da kallo, duk da be ci komai ba, amma ta ji daɗin zuwansa sosai.

Kai tsaye bayan fitarsa daga ɗakin part ɗin Daddy ya wuce, dan ba tun yanzu ya ke kiransa a kan yana nemansa ba. Zaune kan kujera yana kallo a Al_jazeera, kan kujerar da ke gabansa kayan marmari ne reras waɗanda suka sha haɗaɗɗen yanka me ɗaukar idanu. Se kuma juice shi ma da ke ajje, wanda har ya tsiyaya shi a cikin tambulan yana ɗan sipping lokaci zuwa lokaci. Kai tsaye shigewa yayi kawai ya nemi waje ya zauna yana kallan T.Vn shi ma, daidai kuma lokacin da suka gama labaran. Ɗaukar remote Daddy ya yi ya kashe T.Vn sannan ya juya ya kalli Bad Man yace

"Haka ya kamata ɗan musulmi ya shigo ɗaki?" Daddy ta faɗa yana kallansa. Ɗan yamutse fuska ya yi sannan ya zamo daga kan kujerar da yake kai yace

"Sorry Dad.. Assalamu alaik.." sosai muryarsa ta yi daɗi sanda ya furta sallamar kamar wani balarabe. Daddy ya yi murmushi yana faɗin

"Ko kai fa..Wa alaika assalam." Gaisawa suka yi sannan Daddy yace

"Yaushe za ka fara aiki? Ko se ka huta?"

"Yes Dad.." ya faɗa kamar me jiran tambayar Daddyn da ma.

"Ba lokaci me tsayi dai za ka ɗauka ba.." Daddy ya faɗa.

"But.. zan ɗan soma ziyatar en uwa da abokan arziƙi, idan na gama se na fara aikin.." Kallansa Abba ya yi jin abin da ya faɗa ɗin. Se da ya girgiza kai yana murmushi kafin yace

"Kamar gaske.. kai ɗin..?" Shi ma murmushin ya yi kamar ba shi ba amma be ce komai ba har zuwa sanda Daddy ya sake faɗin

"So abin da nake so da kai.. ka zauna a gida ka yi hutunka. Ban son fice_ficen nan.."

"Ohk.." Sallamar Mom cikin ɗakin ita ce ta sanya Daddy kallanta, ya amsa sallamar sanda take cigaba da takowa cikin ɗakin. Kai tsaye kusa da ɗanta ta je ta zauna tana murmushi. Se da ta saka hannu ta kamo hannunsa sannan ta kalli Daddy tace

"Barka da wannan lokaci Yallaɓai.." ta kira shi da sunan da Mommah ke kiransa da shi a lokuta da dama. Hakan ne ya sanya shi murmushi, kafin shi ma ya amsa mata da sunan da ya saba kiran Mommahn da shi a duk lokacin da ta kira shi da 'Yallaɓae'

"Barkanki dai Ranki ya daɗe.."

"My boy.."

"Mom.." ya faɗa tana kallanta can ƙasa. Maida dubansa Bad Man ya yi kan Abba yace

"Abba ka faɗa wa Mom, ta de na kirana da Boy, look at me fa.." ya yi maganar yana kallan kansa. Murmushi Abba ya yi shi ma se ya kalli Bad Man ɗin, duk da ba wasu shekaru na azo a gani ke gare shi ba amma da ke ƙaƙarfa ne shi, me murɗaɗɗen jiki da kallo ɗaya za ka masa ka gane ya horu da ɗaga ƙarfe ya sa ba za ka iya ƙiyasta shekarunsa a yanayin jikinsa ba.

"Gaskiya dai.. ki dena kiransa da Boy.."

"Oh my gosh.." Mom ta faɗa tana girgiza kai, fitinar Areef ɗin yawa gareta. Amma dai ta san idan har ba denawar ta yi ba ba ze dena mata mita a kan hakan ba. Dan haka tace

"Noted Sir.." ta faɗa tana kallan Daddy da murmushi kan fuskarta. Shi ma murmushin ya yi. Daga haka se suka ɗan cigaba da hira, Bad Man na gefensu yana danna waya, dan shi sam be saba da wata hira ba, yanzun nan za ta ginshesa. Dan ma ya ga suna

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment