Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama da ita, ashe mamansu da kanta ta zo ta sanarwa da Malam Ahmad a kan rashin zuwan nata, saboda Gwani da bata samu ba. Dan haka se ya sallameta, sannan ya maida dubansa kan Lulu yace

"Me ya hanaki zuwa?" Shiru ta yi a ranta tana tunanin abin da ya kamata ta faɗa. Se kawai ta yi shiru tana ɗan motsa jikinta. A karo na biyu ya sake maimaita tambayar tasa. Se a wannan karon sannan ta ɗan soma motsa baki fuskarta a haɗe kamar me faɗar wani abun.

"Babu dalili kenan?" Ya faɗa ransa a ɗan ɓace.

"Toh Ya Sayyadi ƙarya zan yi?" Ta fada tana ɗan yamutse fuska a kuma gajiye.

"Hafsa! Karɓo min bulala.." ya faɗa yana kallan Hafsa Abba da ta kasance Monitor. Da mamaki gaba ɗaya en ajin ke kallan Gwanin jin abin da ya faɗa, dan a iya saninsu, tun zuwansa makarantar ba ya taɓa shiga aji da bulala, a gaba ɗaya makaranta ma babu wanda ya taɓa ganin sanda ya yi duka.

"Toh Ya mu'allim.." ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ajin. Tunda ta ɗaga kai ta kalli Hafsa Abban dan tabbatar da da gasken bulala ya aika a karɓo masa ta kasa saukewa. Dukanta ze yi bayan an tabbatar da cewar ba ya duka? Kenan ita yake so ya wulaƙanta a cikin ajinsu? Shi ya sa ze daketa? Wayyo Allah, me ya sa ta bari hakan ke shirin faruwa? Daga lokacin da ya daketa da bulala kuma ai shi kenan ita kuma tata ta ƙare. Duk wani mutuncinta da en ajin ke gani ta san tsiyayewa ze yi tass ya bi rariya. Kallan banza da yake mata shi kuma se dai ya ƙaru tunda dai har ya daketa. Se ta yi ƙasa da kanta tana jin wata ƙwalla na taho mata, anya kuwa ba za ta bi zugar da take ji zuciyarta na mata ba? Anya kuwa za ta jure zama ya daketa kamar jaka? Ba kuwa za ta bi abin da zuciya ke saƙa mata ba, idan ya so ko hakan ne ze zama sanadiyyar korarta daga makarantar, a koreta ɗin. Ta san dai Abba da Ammi za su mata faɗa, idan ya kama ma su daketa, amma dai ta san ba za su karyata ko su kasheta ba, kuma dai koma mene ne daga ƙarshe dai ta tsira da mutuncinta a wajen Gwanin.


... "Haba Hero. Ya mun gama magana da kai kuma za kace min ka fasa ka samo wata zazzafar hanyar? Ni dai tunda ka fita kuma ban san me za ka ce min ba, dan wallahi jikina ya yi sanyi.." Ladi ta faɗa cikin rashin jin daɗi.

"Kin ga zauna anan ki ji.." ya yi maganar yana riƙo hannunta ya zaunar da ita gefensa.

"Ki tsaya ki saurare ni. Na gama aikina na farko ba tare da an samu wata matsala ba. Ina shirin gabatar da na biyun na ga wata hanya da idan muka bi ta za ta ɓillar da mu hanya ɗoɗar. Kin san Areef Matawalle? The only son of Alhaji Matawalle..?

"Ni kuwa na san shi. Duk da dai ban san shi a gaske ba, amma na san shi a hoto.."

"Gud.. Toh abokina ne.."

"Abokin ka kuma? How?" Ladi ta tambaya cike da mamaki. Ɗaga kafaɗa ya yi yana taɓe baki kafin yace

"Manta da wannan.. Ke dai ba kin gane a kan wanda nake magana ba?"

"Ehh na gane.."

"Toh garin aikina na farko, akasi ya saka yarinyar ta ɗauka shi ya rungumeta, tsausayi ya sakata sharara masa mari.. Toh tsausayi mana, dan kuwa Bad Man ba ya yafiya, wannan kamar a rubuce yake.."

"Kai ka bari Hero. Na shiga uku. Mari kuma? Lallai na sake tabbatar da rashin kunyar yarinyar nan. Amma dai me ze yi mata?" Dariya Hero ya sheƙe da ita kafin yace

"Ke ai mu aiki ya zo mana cikin sauƙi.. Ni ɗin nan ba ɗan gidan uban kowa bane." Ya yi maganar yana nuna kansa. Dariya Ladi ta yi tace

"Kuma a haka fa se a ɗauka kai ɗin ɗan gidan wani shegen ne.."

"Ah toh ya za a yi?" Ya faɗa yana sakin dariyar gefen baki. Se ya ɗora da faɗin

"Sunan mahaifin yarinyar can Alhaji Muhammad Aji. Duk da dai ba wani shahararren me kuɗi bane amma dai yana da rufin asirin da ze iya kai ƙara.Ke kin san ko ba shi da hali ma ze ɗauki mataki ne, kin san talakawa da buri. Idan dai har na aikatawa ɗiyarsa wani abun na san ze ɗauki mataki a kaina ni ɗin da ba ni da kowa.." ya ƙare cike da izgili yana wani rausayar da kai. Har se da hakan ya sanya Ladi sheƙewa da dariya. Se dai kafin tace komai ya ɗora da faɗin

"Shi kuwa Bad Man ɗan gidan Alhaji Matawalle ne, kina tunanin akwai wanda ze iya shari'a da shi bayan wannan shegen kuɗin da yake da su? Bar shi ma a wani me taurin kan ze iya, amma kina tunanin duk wanda ze yi shari'a da Matawalle ze yi nasara a kansa ne?" Ɗan shiru Ladi ta yi tana nazarin maganar Hero ɗin. Can dai tace

"Fito min a mutum. Me ka ke so ka ce?" Gyara zama ya yi sannan ya soma faɗin

"Yace ze je har gidansu a kan mari kawai.. ya ki ke gani idan al'amarin da nake ƙoƙarin aikatawa ya koma kansa? Komai ze zo da sauƙi dan na riga na san Bad Man ba ze yi zaman kurkuru ba. Kin ga ba a saka ni a matsala ba ke kuma kin samu cikar burinki.." Murmushi Ladi ta shiga yi cike da gamsuwa da maganar Hero ɗin. Se kuma can tace

"Amma kuma idan aka samu matsala aka riƙe abokin naka a gidan yari fa?" Ɗan taɓe baki Hero ya yi sannan yace

"Ehh toh.. duk can za ta ƙare musu. Ke dai ba kin samu abin da kike so ba?" Dariya Ladi ta yi sosai, jin yadda Hero ɗin ya zame kansa daga wannan al'amarin cikin ƙanƙanin lokaci.

"Lallai Hero ban san da abin da zan biyaka ba. Kai ɗin na daban ne Hero. Duk wanda ya samu kwanya irin taka ya godewa Allah, dan wallahi ba duk kai ba.." Dariya ya yi jin yanda take ta fasa masa kai.

"Amma tsaya? Kamar na san halin Alhaji Matawalle fa a kan ra'ayin riƙau, da son gaskiya, har ma da kula da tarbiyyar wasu bare nasa. Kana nufin kace min duk waɗannan halayen nasa da suka janyo masa baƙin jini a wajen wasu mutanen ɗansa guda ɗayan nan yana neman mata?" Shiru Hero ya yi na tsawon sakanni, kafin can yace

"Gaskiya dai a'ah.. Amma a wannan karon ze fara..!!"


https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_21~22


... Babu daɗewa Hafsa Abba ta shigo ajin hannunta ɗauke da bulalar. Da sauri Lulu ta kalleta ganin da gasken karɓowa ta yi. Babu ɓata lokaci ta ƙarasa ta miƙawa Gwani. Karɓa ya yi, ita kuma ta koma wajenta ta zauna. A hankali ta ɗan kalli Gwanin se ta ga yana ƙoƙarin miƙewa. Cikin rawar murya tace

"Ya Sayyadi Fatima fa ta faɗa maka.." ta faɗa dan ganin mafita ta ƙwace mata. Ɗan shiru Gwani ya yi a ransa yana saƙa abin da ya kamata ya yi wa Lulun. Dan kuwa shi kansa ya san ba dukan ze yi ba, saboda ba ya jin har abada ze iya kai hannunsa jikin mace, gani yake kamar wani saɓo ne ze aikata. Be fasa miƙewar ba hannunsa ɗauke da bulalar da tun shigowarsa makarantar be taɓa riƙewa ba yace bayan ya kalleta fuskarsa a ɗaure

"Ka da ki sake zuwa makarantar nan, se bayan kwana biyu.." Ya faɗa, daga haka ya fice daga ajin. Duka en ajin bin Lulu suka yi da kallo, masu mata kallan mara tarbiyya na cigaba da yi. Masu mata kallan wadda ba ta jin magana na cigaba da yi. A hankali kuma se kowa ya fara zamewa daga cikin ajin, har kuma lokacin Lulu na tsugune kamar wadda aka dasa.

"Ki tashi mu tafi.." Fatima ta faɗa tana riƙota. Se a lokacin ta miƙe jikinta a matuƙar sanyaye se dai fuskarta kamar wadda aka yi wa mutuwa. Ta sauke numfashi tana hararar iska sannan ta kalli cikin ajin. Didi na tsaye tana jiransu su wuce, se dai ba ta ko kalli inda Lulu take ba. Ganin da tayi ta miƙe ne ya sanyata ficewa daga cikin ajin, se suma suka bi bayanta.

"Aikin kawai. Ka daɗe ba ka ba ni suspension ɗin ba mana.." Lulu ta faɗa sanda suka fito. Kallanta Fatima ta yi tace

"A'ah Masoyiya.. Idan kika je gida me za ki cewa Ammi?"

"Uhmm me basirata take yi? Cewa zan yi ba ni da lafiya. Ai ni wallahi ma ya ba ni lasisin da zan ji daɗin rayuwata na kwana biyu ba tare da na gan shi ba"

"Hmmm.." Fatima ta faɗa. Bayan shuɗewar wasu sakanni tace

"Amma dai Masoyiya ya kamata ki dinga sassautawa. Wannan abin ya yi yawa wallahi. Kuma su Abba za ki janyowa, don Allah ki bari.."

"Toh.." Lulu ta faɗa kawai. Har suka je gida Didi ba tace da Lulu komai ba, ta barta ta yi abin da ta ga dama, tunda ba ta jin magana. Itama kuma Lulun se ta share Didin, dan ka da ta mata magana ma ta tuna abin da ya faru, ballantana ma har ta faɗawa Ammi ko Abba. Dan haka se ta mata shiru, idan kwana biyun suka wuce se ta kulata.

... "Ki tashi ki fito mu ci abinci koh?" Ammi ta faɗa tana kallan Lulu da ke cikin blanket ita a lallai dole mara lafiya.

"Ammi na ƙoshi. Wallahi bacci nake ji.." Ƙarasowa Ammi ta yi cikin ɗakin zuwa kan gadon ta nemi waje ta zauna. Yaye blanket ɗin ta yi sannan tace

"Lafiya kike kuwa? Me ke damunki?"

"Ammi zazzaɓi ne a jikina.." ta faɗa tana runtse idanu.

"Zazzaɓi a jikinki kuma shi ne ba za ki faɗa min ba? Wannan ai shashanci ne. Tun yaushe kike jinsa?" Ammi ta faɗa tana taɓa goshin Lulun. Jin sanyi ƙalau ya sanyata faɗin

"Ikon Allah! Kuma babu zafi jikinki.."

"A cikin jikina nake jinsa.." Lulu ta faɗa tana rungumo bargo. Miƙewa Ammi ta yi tace

"Kin ga tashi maza ki shirya mu wuce asibiti.." Waro idanu Lulu ta yi tana jin yadda hantar cikinta ta kaɗa. Da sauri tace

"Ammi ba se mun je ba don Allah. Zan warke ne wallahi.." Ɓata rai Ammi ta yi tana kallanta tace

"Ki tashi nace koh?"

"Don Allah Ammi, don Allah kar mu je.."

"A wane dalilin zamu ƙi zuwa wai? Za ki tashi mu wuce koh se na zo na saɓa miki duk da baki da lafiya?" Ammi ta faɗa tana yaye blanket ɗin gaba ɗaya. Se a lokacin Lulu ta miƙe lokacin da ƙwalla ta cika idanunta taff. Haka ta miƙe ta buɗe wardrobe ta fito da hijab ta zura. Haka tana ji tana gani Ammi ta sakata a gaba suka fito parlour.

"Didi idan Little ya tashi ya ci abinci plss. Zan kai Lulu asibiti ba ta jin daɗi.." Kallan Lulu Didi ta yi, ta galla mata harara tana ɗauke kai. Ita kuwa Lulu se ta langaɓar da kanta kamar da gaske.

"Toh Ammi. Allah ya tsare.." Didi ta faɗa tana jinjina kai, hadda ƙwafa, dan so take ƙaryar Lulun ta ƙare a yau ɗin. Bata daɗe zaune a wajen ba bayan fitar su Ammin Abba ya shigo.

"Sannu da zuwa Abba.." ta faɗa tana kallan Abban.

"Yawwah.. Afrah. Ina Ammin taku?"

"Ta fita kai Lulu asibiti."

"Toh Subhanallahi.. Me ke damunta?"

"Wai zazzaɓi.."

"Aou wai ne ma Didi?" Abba ya faɗa yana kallanta. Se ta tura baki tace

"Toh Abba haka na ji tace.."

"Kenan ba haka ba ne?" Shiru ta yi tana tunanin anya kuwa ta faɗawa Abban? Se dai tana so ne Lulun ta koma kamar kowacce ɗiya dake son janyowa iyayenta yabo, ba kamar yadda take a yanzun ba, da take janyowa iyayensu zagi.

"Abba suspension aka bata fa."

"Suspension kuma?" Abba ya faɗa cike da mamaki. Jinjina kai ta yi kafin tace

"Ehh fa Abba. Laifi ta yi wa Gwani Affan shi ne ya bata. Amma Abba ka yi haƙuri, na faɗa ne ba dan komai ba, se dan ko za a yi haƙuri kawai a cire Lulu daga makarantar nan Abba. Wallahi bata so ne kawai, kuma Abba ka da ta janyo a zageku.." Numfashi Abba ya sauke yana ɗan jujjuya kai.

"Wannan yarinya, wannan yarinya.. Kai!!" Abba ya faɗa. Se kuma ya miƙe yace yana kallan Didi

"Bari na je na dawo kafin su dawo.."

"A dawo lafiya Abba.." ta faɗa tana bin Abban da kallo. A ranta tana fatan Allah ya sa ya yadda ya cire Lulun daga wannan makarantar. Kai tsaye Abba wayarsa ya ɗauka ya kira Gwani, se da ya tabbatar masa yana gida sannan ya katse wayar, bayan ya ji kwatancen gidan.

"Ya ya me jikin?" Abba ya faɗa yana kallan Gwani.

"Alhamdulillah.." Gwani ya faɗa da murmushi kan fuskarsa, dan ba kaɗan ya ji daɗin zuwan Abban ba.

"Fita za ka yi ne?"

"Wallahi kuwa.. Amma Abeeyn na ciki.." Gwani ya faɗa.

"Toh babu damuwa. Dama zuwa biyu ne ya kawo ni. Na farko na duba jikin Malam, na biyu kuma na ba da haƙuri a kan abin da ya faru.." Kallan Abba Gwani ya yi dan be fahimci abin da yake magana a kai ba. Dan haka da mamaki yace

"Haƙuri kuma?"

"Ƙwarai kuwa. Wato Malam ka san yaran yanzu ka haifesu ne amma ba ka haifi halinsu ba. Na ji duk abin da yarinyar nan ta yi, shi ya sa na ɗauko jiki na zo na ba ka haƙuri don Allah ka yi haƙuri ka yi haƙuri kamar dai kodayaushe.." Girgiza kai Gwani ya yi yace bayan ya ɗan yi murmushi

"Ban so ma ka shiga cikin maganar nan ba. Babu komai In Sha Allah. Allah ya shirya.."

"Ameen ya rabbi. Na gode.."

"Haba babu komai."

"A ƙara haƙuri dai don Allah.." Murmushi kawai Gwani ya ƙara yi, mutuncin Abban na ƙaruwa a cikin idanunsa. Ba Abba ne ya bar gidan ba se da ya shiga ya gaishe da Abeey sannan ya baro gidan. Sosai Abeeyn ma ya ji daɗin zuwan nasa, da ze tafi kuwa ya masa godiya dan lokacin ma ya ji sauƙi Alhamdulillah.


.. A kwance yake kan gadon idanunsa a lumshe, kansa a kan hannayensa, yana ɗan bubbuga ƙafarsa dake sauke a ƙasan gado. Ya kasa sukuni tun jiyan, gaba ɗaya hankalinsa na kan Hero ne, yana jira ya zo masa da labari a kan yarinyar nan. Kamar daga sama ya ji wayarsa na ringing. Da ɗan sauri ya buɗe idanunsa da suka ɗan kaɗa saboda ɓacin rai. Ya miƙe zaune sannan ya ɗaga wayar.

"Ya?" Ya faɗa tun kafin Hero ɗin yace wani abu.

"Komai ya kammalu.."

"Kana ina?" Bad ya faɗa bayan ya miƙe tsaye.

"Tun yau za ka je ne?" Iska ya ɗan fesar yana lumshe idanunsa da ɗan ɓacin rai yace

"Just tell me kana ina?"

"Ohk..." Be ajje wayar ba se da Hero ɗin ya sanar da shi inda yake, sannan ya jefata cikin aljihunsa kana ya ɗauki shegiyar hularsa me kyau ya ɗorata a kan kwantacciyar sumar kansa ya fice daga ɗakin. Cikin sa'a Daddy baya nan, hakan ne ya sa be samu tsaiko ba ya fice daga gidan bayan ya kartawa masu tsaron rashin kirki. Dan kuwa idan dai Daddyn na nan shi ne kawai suke aikinsu, dan ma dai shi ɗin idan Daddy na nan be cika fita sosai ba. Idan kuwa Daddyn baya nan, daga ya yi musu magana a kan ze fita za su ƙyale shi ya fice jiki na rawa, ba tare da lura da amanar da Daddyn ya basu ba.

"Tafiyar za ta ɗauke mu minute nawa?" Ya faɗa sanda yake kallan Hero.

"30 minute.."

"Ohk let's go.." ya faɗa yana shirin miƙewa.

"But Bad. I think ya kamata ka ɗan sha wani abun, ina me tabbatar maka da rashin kirkin da za ka yi se yafi wanda ka shirya masa.." Wani wulaƙantaccen kallo ya bi cup ɗin da Hero ya miƙo masa da shi sannan yace bayan ya ɗan ja ƙaramin tsaki

"Ba na buƙatar komai dan zan yi rashin kirki.. Idan za ka je ka miƙe mu tafi.. Idan kuma ba za ka je ba just give me the address.."

"Toh juice fa?" Ya faɗa yana kallansa. Jin be ce komai ba ya sanya shi sake faɗin

"Sorry my man. Mu je.." ya faɗa yana miƙewa. Se kuma ya cigaba da faɗin

"Ina fatan za ka koyawa yarinyar hankali, yanda ko da wani ne ya sake sakata aiki a kan kowanne game gari ne ba za ta karɓa ba ballantana a kanka.. Mari fa..?"

"Heeyy!!!" Bad ya faɗa cikin ɗaga murya yana kamo Hero kamar ze dake shi.

"Na bar maganar.." Hero ya faɗa. Komawa Bad ya yi ya zauna jin kansa ya ɗan sara masa. Se ya saka hannu ya ɗauki sassanyan Juice ɗin da Hero ya zuba masa ya kai bakinsa ya shanye tass sannan ya ajje yana ɗan sauke numfashi idanunsa a lumshe. Wajen sakanni talatin sannan ya buɗe idanun nasa, ya kalli Hero yace

"Let's go.." ya faɗa yana miƙewa. Babu musu a wannan karon Hero ya yi gaba yana faɗin

"Ohk Sir.." Ko da suka isa wajen motar Bad Man, Hero har da saka hannu ya buɗe masa ƙofa, ya shiga ya zauna har lokacin fuskarsa babu fara'a saboda ɓacin ran da ya kwana da shi. Zagayawa Hero ya yi ya tayar da motar kai tsaye suka wuce gidan na Muhammad Aji.

... Se da ya ɗaga kai ya kalli motar lokacin da ta shiga cikin layin. Be kawo komai ba suka cigaba da ciniki da me saida ɗatar. Har ƙofar gidan Hero ya yi parking na motarsa, ya kalli Bad Man yace

"Ga gidan nan.." Hero ya faɗa yana nuna gidansu Lulu. Bin gidan ya yi da kallo kamar me nazari, se kuma ya ɗan yi murmushi yace

"Well done. Za ka iya tafiya.." Babu musu yace

"Allah ya bada sa'a.." ya faɗa yana murmushi. Daga haka ya sauka daga motar, shi ma Bad ɗin ya sauka. Shi Hero se ya fice daga layin yayin da Bad Man ya yi cikin gidan. Hannunsa ya saka ya tura ƙofar gidan. Da wani banzan kallo yake bin gidan da shi. Be dakata ba har se da ya durfafi inda ɗakunan gidan suke. Ƙofar ɗakin a buɗe take, hakan ne ya sanya shi shigewa ciki kawai. A nutse ya soma jefa idanunsa cikin ɗakin ko ze hango fuskarta. Ko ma ba tata ba ya hango ta wata, se dai be hango kowa ba. Hakanne ya sanya shi ɗan soma takawa zuwa cikin ɗakin. Motsin da ya ɗan ji a ɗakin da yake shirin gettawa ne ya dakatar da shi. Se ya dawo da baya ya saka hannunsa ya tura ƙofar ɗakin. Daidai lokacin da ta fito daga toilet. Se ta ɗauki hijab ta saka, dan ta riga da ta saba, ko da tana gida ne ta zauna da hijab. Kamar a mafarki ta ji an turo ƙofar ɗakin. Se ta ɗaga kai da sauri, ta ma ɗauka za ta ga ki Little ne, se dai me? Cikin lokaci ƙanƙani idanunta suka sauka a kan Bad Man dake tsaye bakin ƙofar hannayensa saye cikin aljihu, fuskarsa a ɗinke kamar wanda be taɓa dariya ba. Ba ta san lokacin da ta saki ƙara ba jikinta na ɗaukar rawa. Se ta yi hanyar banɗaki cikin matuƙar tsoro, firgici da rikicewa. Se dai me? Se ta ji toilet ɗin a rufe, ta manta ita da kanta ta cire key ɗin ta ajje shi kan drawer. Kallan wajen ta yi kamar za ta ɗauko, se dai Bad ɗin ya soma matsowa. Se kawai ta fashe da kuka tana kallansa.

"Tsoro kuma kike ji yanzu? Wace ce ke? Waye ya aikoki?" Ya yi tambayar duka a lokaci ɗaya kyakykyawar fuskarsa kuma har lokacin a haɗe.

"Wace ce ni kuma?" Ta tambayi kanta cikin mamaki. Se dai ba ta san tambayar ta fito fili ba.

"Tambayata ki ke? Ina iyayenki suke? So nake na mareki a gabansu na ga abin da za su iya yi.. Ba so kike ki zubar min da mutunci ba? A banza.." ya ƙare yana murmushin takaici. Ita ba ma saurararsa take ba, kawai ta yi shiru ne kamar tana jinsa amma tana kallan gefensa ne tana tsara yanda za ta yi tsalle ta fice daga ɗakin. Se dai har kuma lokacin "Waye shi?" ta ƙi barin ƙwaƙwalwarta. Jin da ya yi ta yi shiru ne ya sanya shi sake kufula, se kawai ya cigaba da takawa, daidai lokacin da ta yi iya ƙoƙarinta wajen yowa gaba dan ficewa daga ɗakin. A fusace ya kai hannunsa kan lallausar fuskarta ya shimfiɗa mata wani gigitaccen mari. Se dai aka samu akasi be sameta ba, saboda yanda ta kauce, hakan ne kuma ya yi sanadiyar faɗuwarta gefe, tsausayi ya sanyata buguwa da gefen drawer. Nan take ta zube a wajen. Ɗan runtse idanunsa ya yi da ƙarfin gaske bayan hannunsa ya taɓa fuskarta. Cikin sakannin da basu wuce 10 ba ya ji gaba ɗaya kansa ya wani irin juyawa, gangar jikinsa ta soma rawa, jiri ya kwashe shi. Kansa ya yi masa wani dumm kamar an ɗora masa wani ƙaton gini a kan nasa. Gaba ɗaya gidan ya shiga juya masa, ya soma ganin sama na komawa ƙasa, se ya riƙo kan nasa da sauri. Se dai duk da haka da wani jiri ya kwashe shi se gashi zube a tsakar ɗakin har kuma lokacin jikinsa be dena wata muguwar karkarwa ba. Daidai lokacin da Habu Driver ya shigo cikin ɗakin. Da sauri ya yi watsi da ledar hannunsa, ya ƙarasa yana kallan Didi da kuma saurayin dake kwance shi ma a tsakar ɗakin. Tsoro duka suka cika shi a lokaci ƙanƙani. Se dai ya riga ya san daga lokacin da ya ga motar ta shigo layin be ci ace har ya aikatawa Didin wani abu ba. Ta yiwu dai wani abun suka shaƙa ya sumar dasu dukansu. Gaba ɗaya saboda tsabar rikicewa se ya rasa ma abin da ze yi. Ya dinga musu fifita zuciyarsa na bugawa. Se daga baya da ya ga Bad bayan en sakanni ya kan ɗan jijjiga da jikinsa sannan ya miƙe ya fita daga ɗakin a guje. Se kuma ya tsaya, tunawa da ya yi idan har ya kira wani daga cikin en unguwar za su iya zargar wani abu. Hakan ne ya sanya shi komawa ciki. Da taimakon Allah ya yi ƙoƙari ya fito dasu ya sakasu cikin mota sannan ya hau ya tasheta ya fice daga gidan. Kai tsaye asibiti ya wuce da gudu, yana addu'ar Allah ya sa basu mutu ba. Yana kuwa zuwa aka karɓesu hannu bibbiyu. Da yake akwai mutane da dama da suka san Bad har sun fara ƙus ƙus cikin asibitin suna faɗawa junansu suma suna munafunci. Shi dai Habu Driver yana tabbatar da an shigar dasu babu ɓata lokaci ya ɗauki waya ya kira Abba.


.. Babu daɗewa se ga Abba cikin asibitin hankali tashe. A lokacin ne kuma likita ya nemi ganin wanda ya kawo Bad Man ɗin da kuma Didi. Abba da kansa ya je, dan lokacin ma be fahimci abin da Habu Drivern ke faɗa masa ba. Dan haka ya nemi waje yana jiran cewar doctor.

"Wato ita yarinyar buguwa ta yi da wani abu a gefen kanta. Wanda hakan ya janyo mata suma saboda yanda ta bugu ɗin. Shi kuma Yaron bisa rashin sani, ko kuma da saninsa ya sha wasu ƙwayoyi ne da suka yi wa ƙwaƙwalwarsa girma sakamakon rashin saninsu da ta yi. Se ta kasa karɓarsu saboda ba ta saba da su ba. Hakan ne ya janyo masa fita daga hayyacinsa. Se dai cikin ikon Allah ita yarinyar ta riga da ta farfaɗo. Shi kuma yaron gaskiya dai har yanzu be farfaɗo ba, se dai muna saka ran nan da dare ya farka ɗin In Sha Allah.." Ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin yace

"Na gode.."

"Amma yana da kyau ku kira mahaifin yaron.."

"Mahaifin yaron kuma? Ka san shi ne?" Abba ya faɗa yana kallan Doctor ɗin.

"Yeap. Ɗan gidan Alhaji Matawalle namu ne fa.."

"Alhaji Matawalle?" Abba ya faɗa cike da mamaki.

"Ƙwarai kuwa.." Likitan ya faɗa cike da tabbarwa. Miƙewa Abba ya yi ya miƙawa Doctorn hannu suka yi musabaha sannan yace

"Thank u.." daga haka ya fice daga Office ɗin.

... Har

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment