Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi na dena rashin ji. Ah toh. Ban faɗa ba idan na dawo ya yankani.."

"Amma ba kya tsoron ya sanarwa da Abba?" Fatima ta faɗa tana kallan Lulu.

"Ke ba ze faɗa ba dallah. Kema me ye na damun kanki ne wai?"

"Masoyiya ka da fa ya dake ki.."

"Duka kuma? Aou dama yana duka ne?" Girgiza kai Fatima ta shiga yi kamin tace

"A'ah ba ya yi amma dai kar ya sake miki abin da ya saba yi ki ce ya dizga ki.."

"Masoyiya wai me ye haɗinku da wannan mutumin ne na ga kina ta wani kare shi? A'ah kin ga faɗa min wallahi ba wanda zan faɗawa.." Lulu ta ƙarashe maganar a hankali tana kuma gyara zama. Duka Fatima ta kai mata a fusace tana faɗin

"Ban sani ba.." Dariya Lulu ta yi tana faɗin

"Ah toh.. ai yanzu dai kya ƙyale ni na sarara.."

"Allah ya shirya min ke Masoyiya.."

"Ameen in da gaske ki ke.." Lulu ta faɗa tana yamutse fuska.

"Wai kin san mene ne?" Fatima ta faɗa tana gyara zamanta.

"A'ah se kin faɗa.."

"Abida ce ta zo gidanmu ɗazun.."

"Abida kuma?" Lulu ta tambaya da sauri tana kallan Fatiman. Se ta jinjina kai, kafin ta kai ga sake cewa komai Lulu ta sake faɗin

"Karki faɗa min da gaske ne? Me ta zo tace miki? Yi maza ki faɗa min plss." Taɓe baki Fatima ta yi kafin tace

"Ke ba fa komai. Ba abin da tace min, kawai dai gaisawa muka yi, ban da nan ba komai.."

"Ohk toh idan ta kuma zuwa ki faɗa min plss.."

"Tsaya.. wai me ya faru ne haka na ga duk kin tsorata? Wani abu?" Girgiza kai Lulu ta yi tana faɗin

"Nop babu wani abu fa.." Daga haka suka cigaba da hira. Zuwa can Fatiman ta tafi bayan ta je ta yiwa Ammi sallama. Ba ta daɗe da fita ba Didi ta shigo cikin ɗakin hannun Little ɗauke da wata babbar leda da kaya cike a ciki. Da sauri Lulu ta miƙe tana faɗin

"Zo mu gani, me aka baka?" Baya ya yi da ita da sauri yana faɗin

"A'ah na wa ne fa.." Tsaki Lulu ta ja kafin tace

"Kai ba ci maka zan yi ba, kawai gani zan yi.." Se a lokacin sannan ya miƙa mata ta kama hannunsa suka nemi waje suka zauna. Didi ma neman waje ta yi ta zauna kawai. Buɗe ledar Lulu ta yi ta shiga fito da abubuwan da ke cikinta. Tarin chocolates ne kala kala kamar za su yi magana masu daɗi, aji da kuma tsada.

"Awwwn Didina ta girma wallahi. Duk wannan namu ne?" Ta yi maganar tana kallan Didi. Murmushi kawai Didi ta yi tana maida dubanta kan Little da ke faɗin

"Hmm Uhmm Jamm! Allah kuwa na wa ne.." Kumatunsa Lulu ta kama ta ja tana faɗin

"Duka wannan za ka shanye wai?"

"Ehh mana. Ai Yah Kaseem ɗin ne yace na wa ne duka tunda Didi ba ta so.."

"Iyee!! Yah Kaseem! Wa ya ɗora maka sunan a bakinka haka raɗau?" Lulu ta faɗa tana riƙe haɓa.

"Didi ce.." ya faɗa yana karɓar ledar daga hannun Lulu. Se ta maida dubanta kan Didi daidai lokacin da ya nufi ɗakin Ammi hannunsa ɗauke da ledar.

"Didi.."

"Kee.." Didi ta faɗa tana murguɗa baki.

"Ba shakka.. kin san me? Faɗa min gaskiya Didina.." Lulu ta ƙare maganar tana dawowa kusa da Didi, sannan ta ɗora da faɗin

"Ki na sonshi koh?" Shiru Didi ta yi tana ɗan wani juya kai kafin can tace

"Na ji ina son hira da shi. Da ze tafi ma na ji ba daɗi.." Tsalle Lulu ta yi kafin ta koma ta zauna a kan kujerar tana faɗin

"In faɗawa Ammi kin amince koh? Don Allah don Allah kar ki ce a'ah.." Lulu ta faɗa cikin zaƙuwa.

"Tohm.." shi ne abin da Didi ta faɗa tana murmushi. Kawai se Lulu ta rungumeta cikin matuƙar farin ciki.



.. "Kema fa kanki kamar na Hero ne yana ja wallahi.." Ladi ta faɗa tana kallan Abida. Murmushi Abida ta yi kafin tace

"Wallahi kam irin aikin nan akwai wahala. Amma idan buri ze cika ai babu matsala."

"Bayan kin tura hotunan kin goge amma?" Ladi ta tambaya. Shiru ta yi na en wasu sakanni se kuma can ta shiga girgiza kai sannan tace

"Gaskiya dai ban goge ba. Amma ai babu damuwa, za ta yi tunanin kawai hoton ne ya birge ni shi ya sa na tura. Kuma ma shi ne dalilin da yasa ban tura wanda ita Afaaf ɗin take ita kaɗai ba. Se na tura wanda suke tare ita da masoyiyarta ta. Kin ga ko da ta gani ba na tunanin wani abun ze zo kanta.."

"Hakane kuma" Ladi ta faɗa tana jinjina kai.

"Bayan nan kuma na samo mana wani information ɗin.." Abida ta faɗa tana neman waje ta zauna. Da sauri Ladi tace

"Yi maza ki sanar min me ya faru?"

"Na ji tace gobe akwai inda za su je. Se dai duk abuna ban ji inda za su je ɗin ba."

"Aiki me kyau Abida. Maza miƙo min wayata.." ta yi maganar tana nuna mata wayarta da ke ajje a kusa da Abidan. Babu musu ta miƙa mata ta shiga nemo number Hero ta kira shi.

"Albishirinka!!" Ladi ta faɗa tana murmushi.

"Goro.." shi ma ya maida mata yana murmushi.

"Idan kana da lokaci ka ɓillo dan an samu cigaba. Idan kuma ba ka da shi faɗa min kana ina yanzun nan ka ganni a wajen.."

"Shegiyar mata.. ba se kin zo ba, ki jira ni zan ƙaraso.." Hero ya faɗa

"Toh godiya nake.."


.. Kowaccensu cikin hijab ta shirya me kyau. Sun fito a Malaman Addini sun yi kyau abinsu. Se da ta gama ɗaura niƙab ɗinta sannan ta kalli Ammi tace

"Ammi mun gama.."

"Toh.. gashi nan. Idan ki ka kai se ki taho ki zo ki wuce makaranta tunda dai ke ba ki sanar da ba za ki je ba. Dan haka se ki barsu su su je aiken Umman Fatiman. Allah ya tsare.." Ammi ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙawa Didin ledar hannunta.

"Ameen ya rabbi Ammi.." suka amsa a tare, sannan suka fito zuwa compound. Drivernsu Lulu ne ya ɗauke su kai tsaye zuwa gidan da Ammi ta aikesu. Babu laifi sun ɗauki mintuna masu ɗan dama a gidan, saboda da farko ma da suka je matar bata nan, se da suka jirata ta dawo suka bata saƙon, sannan suka yi mata sallama suka fito.

"Didi toh ki zo kawai mu tafi tare mana. Gobe se mu je makarantar duka.." girgiza kai Didi ta yi tace

"A'ah ni kam. Na san Gwani ze shigo yau ɗin nan, kuma ban faɗa masa ba.." Taɓe baki Lulu ta yi sannan tace

"Ai shi kenan.."

"Toh se kun dawo. Amma fa kar ku saki jiki magribh ta yi muku a waje.."

"In Sha Allah Didi.." suka amsa a tare. Har ta fara tafiya se kuma ta juyo tace

"Toh Baban na jiranku, ko me za ku jira anan?"

"Ahh haba Didi ki hau ya maidaki gida mana. Ta baya zamu ɓilla ne, akwai hanya me sauƙi, anan za mu samu mota ta kaimu unguwar.."

"A'ah ni dai na samu abin hawa kawai.." Didi ta faɗa.

"Ba komai fa Didi.."

"Shi kenan toh. Allah ya tsare.. Se kun dawo"

"Ameen.." nan ma suka amsa a tare. Motar Didi ta shige yayin da su kuma suka yi baya kamar yanda suka faɗawa Didin. Tafiya kaɗan ce kuwa ta kaisu titin. Babu daɗewa kuwa suka sami abin hawa suka hau. Da yake gidan na en uwansu Fatima ne ya sanya babu laifi sun ɗan jimawa matar. Se dai kafin gabatowar magribh suka suka soma shirin tafiya. Babu yanda ba ta yi da su a kan su zauna ba su ka ce an ce ka da su kai magribh. Babu yadda ta iya haka suka mata sallama suka tafi. Suna tafiya suna hira abinsu har zuwa sanda suka ƙaraso titi.

"Laaa pls Masoyiya zo mu je yau dai na siyi wannan popcorn ɗin. An daɗe ana tallarsa amma ban taɓa ɗanɗana irinsa ba duk sona da popcorn." Lulu ta faɗa tana kallan wani haɗaɗɗen wajen saida gugguru wanda ke kusa da wani hamshaƙin restaurant.

"Ai kin ji kuma kwaɗayi. Ni wallahi ma yunwa nake ji. Ki bari kawai mu tafi gida.."

"Amma er uwakkun nan tace ki zauna ki ci ki ka ƙi ci?" Taɓe baki Fatima ta yi kafin tace

"Abincin na su ne be min ba." Dariya Lulu ta sheƙe da ita tace

"Wallahi na bar abin ne kawai a raina saboda er uwakku ce. Ashe ke ma da kanki haka za ki ce. Kai jama'a!" Ta ƙare tana saka hannu a baki ta kare tana cigaba da dariyarta.

"Kya ji dai da shi.." Fatima ta faɗa tana yin gaba.

"Aou wai nufinki ba za a siya ba?" Lulu ta faɗa tana riƙo hannunta.

"Masoyiya wallahi na gaji. Don Allah ki taho mu tafi.."

"Kin ga ki ce dai yunwa kawai ki ke ji. Ga restaurant nan ki zo mu shiga na san za a samu wainar shinkafa, ki yi kodimonki da ita kin ga kowa an yi abin da yake so kenan.." Se da ta ambaci wainar shinkafar kuma sannan ta yi murmushi, dan kasancewarta me son wainar shinkafa sosai. Se suka taka zuwa wajen saida popcorn ɗin. Se da ta siya sannan suka shiga restaurant ɗin da ya gaji da haɗuwa. Abin da ya kawo su kawai shi suka yi. Aikuwa cikin sa'a suka samu wainar shinkafar. Ita dai Lulu da yake ba yunwa take ji ba, kuma wainar shinkafa ba ta wani daɗata da ƙasa ba ya sanya ba ta ci komai ba, se kawai ta jira Fatiman ta ci abincin.

"Masoyiya wallahi ko ba yunwa nake ji ba na ga abincin nan se na ci.. Chaaɓɓ kin ji daɗi kuwa?" Ta faɗa tana cigaba da cin abincinta.

"Ke mu dai ki yi sauri wallahi. Nima na gaji.."

"Ehh tunda kin samu abin da ki ke so ba?" Ta faɗa tana watsa mata harara.

"Oho dai.. Ai kema kin samu.." Se da ta ci yanda take so sannan ta kora da lemo, kana suka miƙe a tare dan barin wajen. A daidai sanda suka gama fitowa daga inda ya kasance nan ne mutane ke zaune suna cin abinci da sauransu, a daidai lokacin da Lulu ke kallan Fatima suna magana, se kawai ji ta yi kamar ta bugi wani abu, kafin ta gama tantance mene ne se ji ta yi an zagayeta da hannaye guda biyu. A daidai kuma wannan lokacin ne sautin ɗaukar hoto ya daki dodon kunnena "Ƙyaras.." daga haka Hero ya saki Lulu ba tare da ya bari ta kalli fuskarsa ko shi ya kalleta ba ya yi ciki da saurin da cikin sakannin da ba su wuce a ƙirgasu ba ya ɓacewa ganina. Cikin tsananin ɓacin rai, haushi, takaici gami da baƙin ciki ta ɗaga hannunta da niyyar tunkuɗe wanda ta ke tunanin rashin hankali ne ya saka ya zo wucewa ze mata irin wannan bangazar, se dai cikin sakanni ta ji an riƙeta alamar ba da gangan aka yi hakan ba. Kafin kuma ta ɗauki wani mataki se ji ta yi an saketa. Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar gangar da ake kaɗawa. Fararan manyan idanunta sun cika fall da ƙwallar baƙin ciki, se dai har wani huci take fitarwa saboda ɓacin rai. A fusace ta juya dan ɗaukar matakin da ya dace tun kafin ma hankalin wasu ya dawo kansu, ballantana a san abin da wani dabban ya yi mata ba. Daidai lokacin da Bad Man da ke sanye cikin wasu tsadaddadun kaya en ubansu ya kalli Hero sanda ya wuce da gudu kamar wanda aka kaɗo, ganin be fahimci dalilinsa na yin hakan ba, ya sanya shi juyawa fuskarsa kamar ko yaushe babu walwala dan dubawa ko wani abin ne ya faru? Se dai yana juyawar ita kuma fusatattun idanunta da ke cike da fushi suka sauka a kansa, kasancewar shi kaɗai ne ta gani a wajen wanda ya ke kusa da su, se waɗanda ke nesa da su. Ta kuma riga ta san wanda ya mata wannan haukan be ci a ce sun samu tazara da yawa ba, dan haka ganin Bad Man kusa da su ya sanyata sake tabbatar da cewa lallai shi ne ɗan iskan da ke ƙoƙarin yi mata akuyanci. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba ta ɗaga hannunta ta sauke masa lafiyayyuyan yatsun hannunta guda biyar reras a kan farar hamshaƙiyar fuskarsa..



https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*


By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_


*CHAPTER ONE*

Page_20


___"Ɗan iska kawai.." ta faɗa fuskarta ɗauke da zallar ɓacin rai, har kuma lokacin ƙwallar da ta taru a idanunta na nan. Kyawawan ianunsa da basu da yalwar girma ya sake ƙanƙancewa yana kallanta cikin yanayin da na kasa fahimtar wane iri ne. Cikin lokaci ƙanƙani ya ɗaga hannunsa a nutse ya shafa kyakkyawar fuskarsa. Kafin ya kai ga yin wani yunƙuri saboda yanda man kansa ya tsotse da wannan al'amarin, so yake ma ya gama tabbatar da da gasken abin da ya faru ya faru. Wace ce ita? Fatima ta yi saurin riƙo Lulu tana faɗin

"Zo mu tafi ke.." kafin Lulun tace komai Fatima ta saka hannu ta jata da ƙarfi suka wuce. Daidai lokacin da Hero ya ƙaraso dab da Bad Man yace a hankali

"Ka da ka yi wani yunƙuri. Za ka jan yo hankalin mutane.." Hannunsa ya saka ya tunkuɗe Hero, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, har wani huci yake fitarwa, angry face ɗinsa ta sake haɗewa waje ɗaya. Saboda yadda ya tura Hero ɗin da ƙarfin gaske ya sanya shi yin gefe kamar ze kifa, dan Bad Man ɗin ba daga nan ba wajen ƙaƙƙarfan jiki. Da wani irin sauri ya sake yin gaba yana faɗin

"Plss Bad. Ka da ka yi haka. Babu wanda ya gani, idan ka yi wani yunƙuri kowa ze san abin da ya faru.."

"Heyy leave me. I said leave me.. Me ye ka ke faɗa ne? Waye kai da kake tunanin za ka faɗa min magana na ji? Na ce who are you?"

"Ni ba kowa bane Bad. But abin da kake ƙoƙarin yi ne nake ganin kamar be kyautu ba, ace kamar Areef Matawalle da kansa ya tsaya yana sa'insa da er gidan talakawa.."

"Er gidan talakawa.. Er gidan ko uban waye ba damuwata bane.."

"Don Allah ka zo mu je mu zauna mu yi magana. Ba dan halina ba don Allah.." Hero ya faɗa kamar mutumin arziƙi. Da ƙyar ya samu Bad Man ɗin ya yadda suka koma suka zauna bayan ya tabbatar masa da cewa ko ɓurɓushin en matan be gani ba.

"Ka santa ne?" Bad ya tambaya har lokacin a kufule.

"Noo ban santa ba. But abin da ta maka ze sanya ni nemota in ɗauki fansa.."

"Fansa? Har na yi wannan lalacewar?" Bad ya katse shi da faɗin hakan. Kafin ya ɗora da

"Ka nemo min wace ce ita. Ina ne gidan ubanta.. ban san dalilinta na marina ba but zan nuna mata true colour ɗina.."

"Amma Bad har yanzu na kasa gane dalilinta na marinka fa? Anya kuwa lafiyarta ƙalau?" Ɗan runtse idanunsa Bad ya yi yana jin kamar lokacin ne en yatsunta suka sauka a kan fuskarsa. Da sauri ya buɗe idanunsa ya saukesu a kan Hero ɗin daidai lokacin da yake shafa fuskarsa yana kuma hasaso irin wulaƙantaccen marin da ze yi wa yarinyar da tafi kama da mara hankali. Jin be ce komai ba ya sanya Hero sake faɗin

"Anya kuwa lafiyarta ƙalau? Ko kuma tana ɗaya daga cikin maƙiyanka, shi ya sa ta zaɓi tozartaka a cikin jama'a. Da ka biye mata kuma ka ga kai ta janyowa zubewar mutunci ba kowa ba.."

"Hero!!" Ya faɗa a zafafe yana watsa matsa rikitattun idanunsa. Babu shiri ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya

"Sorry Bad.. Yanzu dai me kake so a yi?"

"Just ka binciko min gidan ubanta.. Wallahi ko waye ubanta ba ze hana ni shiga har cikin gidan, kai har cikin ɗaki zan shiga na bata wulaƙantaccen mari da kuma tarin gargaɗi. Haters??" Ya ƙare a mamakance. Shi har yanzu abin mamaki yake bashi. Ajiyar zuciya Hero ya sauke yana jinjinawa rashin ji irin na Bad Man. Ya riga ya san tunda ya faɗa hakan ze cika ne, ko me kuwa za a yi se ya cika abin da ya faɗa. Lallai yarinyar ta janyowa kanta ruwan dafa kanta. Daga tarkon Ladi ta janyowa kanta na Bad Man.

"Shi kenan.. ka bani kwana ɗaya zan bincika maka.." ya faɗa a ransa yana saƙa yanda ze jewa da Ladi maganar nan. Shi har ya ma gama tsara yanda komai ze tafi, tabbas shigowar Bad Man cikin wannan tafiyar shi yafi komai daɗi, shigowarsa ciki za ta ƙarawa abubuwan armashi. Koma yace shigowarsa ce ma za ta gyara komai.



... "Wallahi Allah ya isana.." Lulu ta faɗa tana share ƙwallar da ta ƙi tsayawa a kan fuskarta.

"Masoyiya ni fa kina bani tsoro wallahi. Yanzu duk girman mutumin nan, kwarjini da sauran abubuwa ki ka kasa jin kunyar marinsa cikin jama'a? Ba kuma ya rama fa?" Da sauri Lulu ta juya ta kalli Fatima.

"Shi be ji kunyar taɓa jikina ba, se ni zan ji kunyar marinsa? Ɗan iskan banza kawai, mugu, azzalumi.." ta sake faɗa tana kuma ɗauke ƙwallar idanunta.

"Haka ne kuma.." Fatima ta faɗa. Har suka isa gida Lulu bata dena mita ba, tun Fatima na bata haƙuri har ta gaji ta yi shiru. Se da suka kusa shiga gida sannan Fatiman ta kalleta tace

"Amma dai ya kamata ki tsaya ki saita kanki in case kar Ammi ko Didi su fahimci wani abun.." Shiru ta yi kamar ba zata amsa ba. Se kuma can tace

"Na ji.."

"Yawwah ko kefa.." da ƙyar dai ta tsaya ta nutsu ɗin sannan suka shige cikin gidan. A parlour suka tarar da Little da Didi da dawowarsu kenan daga islamiyya.

"Sannunku da dawowa." Didi ta faɗa tana murmushi.

"Yawwah Didi.." Fatima ta faɗa, yayin da Lulu ta nemi waje ta zauna a kan kujera. Didi ta kalleta tace

"Ke kuma lafiya?"

"Ƙishirwa nake ji.." ta faɗa tana turo baki. Jinjina kai Didi ta shiga yi tace

"Lallai Lulu kullum taɓararki ƙara gaba take yi, wai ƙishirwa kike ji.." Fatima ba ta daɗe ba ta yi wa Ammi sallama sannan ta wuce gidansu bayan ta yi wa Lulu sallama.


... Cikin takun ƙasaita ta shigo ɗakin, tana tafiya tana yauƙi kamar wata budurwa, hannunta ɗauke da tire da ke ɗauke da wani glass jug da cups ɗinsa a gefe. A hankali ta ƙaraso ta aje a gaban Daddyn sannan ta koma ta zauna tace bayan ta ɗan yi fari

"Barka da hutawa Yallaɓai.." Murmushi ya yi yace

"Barka dai.. Kina lafiya?"

"Lafiya ƙalau nake.."

"Toh madallah.."

"Bari na zuba maka.." ta yi maganar tana miƙewa ta tsiyaya juice ɗin cikin glass cup ɗin sannan ta miƙa masa. Babu musu ya karɓa daidai lokacin da Mommah ke faɗin

"Barka da wannan lokaci.." kamar ba za ta amsa ba, se kuma can tace

"Barka.. Yawwah Yallaɓai dama magana ce na zo mu yi a kan ɗana.." Se da Daddy ya ɗan kurɓi juice ɗin sannan yace

"Toh ina jin ki.." Kallan Mommah Mom tayi sannan ta maida shi kan Daddy tace

"Ai na ga akwai baƙuwar fuska ne.."

"Baƙuwar fuska kuma? A ina?" Daddy ya faɗa yana kallan cikin ɗakin. Yamutse fuska Mom ta yi kafin tace

"Dole nace baƙuwar fuska mana Yallaɓai, tunda dai magana ce da ta shafi tsakanin iyaye biyu a kan ɗansu.." Se a lokacin ya fuskanci abin da take nufi, se ya girgiza kai cike da takaicin halinta yace

"Amma dai kin san ɗa na kowa ne koh?" Se ta girgiza kai da sauri tana faɗin

"In ji hausawa ba? Amma ɗa ai na me shi ne.."

"Ranka ya daɗe, a huta lafiya.." Mommah ta faɗa tana murmushin yaƙe. Amsa mata Daddy ya yi yana binta da kallo cike da tausayawa har ta fice. Se a lokacin ya dawo da dubansa kan Mom yace

"Ki dena wannan abin da kike, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba na sha yi miki faɗa a kan irin wannan halin, amma kin ƙi dainawa. Se yaushe ne za ki dena?" Ya yi maganar yana kallanta.

"Tom.." ta faɗa dan so take kawai a bar maganar, kafin ran Daddyn ya sake ɓaci, yanzun nan ya chanja mata fuska bayan magana take so su yi.

"Dama magana ce a kan Areef.." ta faɗa a tausashe.

"Ina jinki.." Daddyn ya bata amsa a taƙaice. Se da ta sauke ajiyar zuciya sannan tace

"Dama so nake na roƙi alfalmar ko za a samar masa aiki a wata ƙasar na ga yafi sabawa da can ɗin.." Kallanta Daddy ya yi kamar me nazarin wani abu daga fuskarta. Ba tace komai ba ta yi shiru tana jiran ta ji amsar da za ta fito daga bakinsa. Murmushi Daddy ya yi yana girgiza kai yace

"Aiki a wata ƙasar, ke ba ma a wata ƙasar ba matsala ce a wajen Areef. Dama ya lafiyar kura bare ta yi zawo? Idan dai har aiki na samar masa, toh ya zame masa dole ya dinga zuwa kodayaushe. Idan kuwa kasuwanci ne babu ruwansa, ze iya ɗora wani a kan wani abun idan ya yi niyya. Ko kuwa kin fi so ya dogara ne da gwamnatin nan tamu? Idan hakan ki ke so shi kenan. Amma dai ki tabbatar kin fara tuntuɓar ɗan naki, dan idan dai har na yanke hukunci ba zan chanja ba.." Numfashi Mom ta ajje kana tace

"Ai Yallaɓai ba ina nufin aiki gama gari ba.."

"Duk wani aiki sunansa aiki ne.." Daddy ya katseta da faɗin hakan.

"Shi kenan.. Zan tuntuɓe shi na ji daga bakinsa.."

"Hakan ma ya yi.." Daddy ya faɗa yana kai juice ɗin hannunsa baki ya kurɓa.



... Tare suka fito daga asibitin shi da Abbati kamar ko yaushe, da yake shi ɗin amintaccen Abeey ne ya sa se ya zama kamar shi ne mataimakin Gwani a duk wasu al'amuran da suka shafi rashin lafiyar Abeey ɗin. Abbatin ke ɗauke da ledar maganungunan Abeey haka suka fito titi. Gwani yana cikin favourite shigar nan tasa da ke matuƙar yi masa kyau, wadda kodayaushe ba a iya ganin sumar kansa da ke a rufe, se zahirin kyakkyawar fuskarsa da ke a buɗe, shigar da a lokuta da dama idan mutane suka kalle shi kafin ya yi magana kai tsaye suke kiransa da balarabe, saboda babu wani abu da ya banbanta shi da su. Fari, kyau, shiga da komai da komai irin nasu ne. Kai Gwani fa na daban ne a komai.

"A'ah Malam Affan, yau ma dai mun sake haɗuwa.." Abba ya faɗa yana murmushi. Shi ma murmushin ya maida masa yana miƙa masa hannu suka gaisa. Suka gaisa ma da Abbati, sannan Abba yace

"Ya me jikin?"

"Alhamdulillah.." Gwani ya faɗa cikin nutsuwa.

"Madallah.. Allah ya ƙara afuwa.." Abba ya faɗa

"Ameen" Gwani da Abbati suka haɗa baki wajen faɗar hakan.

"Dama ina so na sake ganin jikin nasa. Se dai yanzu ina sauri ne, akwai inda zan je.. Ka saka min numberka, idan na shirya zan zo na duba jikin Malam.." Abba ya faɗa yana miƙawa Gwani wayarsa. Karɓa ya yi a nutse ya shigar da numbersa sannan ya miƙawa Abban. Daga nan Abba ya yi musu sallama ya shige inda ya zo.

"Malam wannan mutumin na da kirki wallahi.." Jinjina kai Gwani ya yi kamin yace

"Tabbas.."

"Allah ya saka masa da alkhairi, ya ƙara zumunci... ko shi ma dai ɗalibin Malam ne?" Girgiza kai Gwani ya yi daidai sanda suka tare adaidaita yace

"A'ah.."


... Allah Allah take kawai ya gama abin da ze yi ya fita ba tare da ya tashi waɗanda suka yi fashi ba. Babu daɗewa ya gama littafin, sannan ya rufe shi. Se kowa ya shiga mayar da littafan cikin jaka ana jiran ya yi addu'a a tashi. Se dai me? Abin da dai ba ta son ji shi ne abin da ya faɗa wato

"Wanda duk ya yi fashi ba tare da ya sanar min ba, ya fito.." Kamar kar ta tashi, se kuma ta tuna irin wannan abin da take yi ma fa yana janyo raini. Cikin ikon Allah yau se ya kasance su biyu ne suka yi fashin. Kallanta Didi ta yi sanda ta miƙe a mamakance. Ƙasa_ƙasa tace da Fatima

"Dama ba ku faɗa ba?" Girgiza kai Fatima ta yi kunya na kamata se kawai ta yi shiru tana kallan Lulu da ta fita zuwa wajensa. Da ɗayar er ajin tasu ya fara, fuskarsa a tamke, dan shi ba ya son raini, idan yace ba ya son abu kawai ba ya so. Babu daɗewa suka

2 Comments On A JINI TAKE (IZZATA) CHAPTER 1
avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

avatar
abubakar-sunusi

1 year ago

Reply

Please Login or Register in order to submit comment