You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
maganar
" Khaleed !!!!!!! Ta fada cikin wata iriyar murya
" Calm down mana beb ! Ya fada yana nupo ta
" Kada k Matso kusa dani Khalid " tana fada tana matsawa baya ,
" k fadamin mena maka k dakkoni k kawoni nan mena maka ?
" Kinga beb xauna kiji magana xamuyi ta fahimta " inji Khalid
" Banda lokacin ka kwae k fadamin abinda yasa k kawoni nan "
Tuntsirewa yayi d dariya yana fadin
" Kinga ni kua ina d lokacinki ae beb kinsan ynx kua ina cikin tarko akan dakko ki d nayi ?
Bata ce masa komae b illah binsa d take d kallo
Neman waje yayi y xauna yana cewa
" kinsan menene ki tsaya muyi xance na fahimta Idan kuma kika qi xan nuna miki true colour dina ! ga waje nan ki xauna " y fada yana nuna mata kusa dashi
A hankali ta tako ta xauna nesa dashi so kwae take taji mexe ce mata
Gyara xamansa yayi yana fadin
" beb wato tun b yau b nake qaunarki nake sonki nake muradinki amma kinqi bani dama na bayyana miki shys na yanke shawarar kawoki nan na fadamk dan naga wadancan shashashan sun fara huremk kunne
xaki iya yin watsi dani idan a can ne ! kina sona ? Y fada yana mata wani shu'umin kallo
Kanta gabadaya y kulle tama rasa abinda xatayi sam bata san sanda ta fara fadin
" wae me kuka maedani ne ? Kowa so so so ni kadae ce mace ne a duniya ?
Shin meyasa bakunan ku basu d kunya wajen furta wannan kalmar ne ?
Ku qyaleni haka don Allah na huta na gaji dajin wannan Kalmar daga bakin maza daban daban , enough is enough pls
" Kinga beb duk wadanda suka fada mk daban suke dani ni ynx kwae ki bani amsata kina sona koh ?
Cikin daga murya tace
" Khalid bana sonka "
Baya yayi sosae
" kikace bakya sona ?
" Ehh " ta fada tana jijjiga kae alamar tabbatarwa
Wata muguwar dariya y saki kapin yce
" well dama na fadamk d choice is yours
so tunda bakya sona xan riqeki anan ki xama matata dukda ba'a mana aure b ! Nayi niyyar in haqura d marin d kikamin eyee ko kin manta ne ?
toh ni ban manta b dole ne in fanshe marin d kikamin beb "
" Tirrrr d irin wannan rayuwar Khalid Allah y kiyashe ni Allah y tsareni d sharrinka Khalid
" Fitarki daga hannuna kwae shine ki amsa xaki aure ni fine ! yau dinnan xan maedaki gida inje in nemi aurenki kamar yadda yke a addini se a dauramana aure idan kuma kinqi seki xama dadirona " y fada yana kashe mata ido
Cikin rufewar ido tace
" Khalid da in aureka gwara na mutu banyi aure b wlh baxan aure k b !! Amsar dk keso kaji kenan koh toh gata nan kaji ta k qyaleni in tafi gida "
" Ya dae en mata har kin saka ran fita daga gidan nan kenan ?
Kin manta za6i 2 na baki kuma kinqi amincewa d ko guda 1
toh ni kua na xa6ar miki guda 1 ba shikenan b ? Khalid y fada yana kallanta
" Khalid " inji 1 daga cikin su
Maeda hankalinsa yayi gunsa kapin ya masa alama d suje
babu musu duk suka fice daga dakin
Xubewa tayi a tantagaryar dakin tana sakin wani kuka me tsuma xuciya
wace irin rayuwa ce wannan ? Yanxu rayuwar d Khalid y dauka me 6ullewa ce ?
B shiri ta faara janyo duk wata addu'a d tazo bakinta.
Tana nan xaune aka sake turo qofar shi dinne dae y sake shigowa
sedae a wannan karon fuskarsa babu annuri sa6anin yanxu
Qafarsa y dora kan table din dake gabanta kapin yace
" ba xaki aureni b koh ?
Toh kije kiyi auren mu gani
kije ki auri duk wanda kika fiso a fadin duniyar nan
amma sedae ki sani duk ranar d kika sake kika auri wanin da vani b toh daga ranar ki faara irga kwanakin takabarki !!!
A razane ta dago ido tana kallansa kana a hankali ta fara girgiza kae
" A'ah qarya yake duk wani rae a hannun Allah yke duk wanda kikaga y mutu toh lokacin sa ne yayi wani banza khalid babu abinda xe iya yi "
taji xuciyarta na raya mata
Sosae ta yadda da hakan
Khalid y katseta d fadin
" yah en mata da sarewa d wuri haka ? Ae baki gama jin sharadin nawa b
" Xan barki kije gida amma ki cigaba d tunawa d abinda na fadamk
amma wlh wlh kika sake kika fadawa wani ko wata cewar nine na kawoki nan abinda xanyi se yafi ta6aki akan kowa dan wlh wlh sena kashe ARMAN !!
B barazana nake miki b wlh xan aekata ne saboda haka bakinki qanin qafarki
Kallansa kwae take xuciyarta na wani irin bugawa da qarfi d qarfi
" baby pah baby pah xe kashe ? kuma tasan a yadda ya fada din tabbas xe iya aekawata
A hankali taji wani irin sanyi na ratsata alamar zazza6i na iya kamata a kowanne lokaci.
***********A can bayan layin nasu suka ajjiyeta ta fara takawa wani irin jiri na dibarta
tafiya kwae take bata gane gabanta seda tayi da gaske ta iya karya kwanar street dinsu
kapin ta faara knocking gate din gidannasu
D sauri sojojin d suke tsaye a gate din suka bude
Bata tsaya b ta cigaba d tafiya tana harhada hanya
Yana xaune a motar he have no thing to do kwae y xauna yayi shiru
Kamar ance y kalli compound din y hangota tana tafiya cikin sassarfa
Kamar an tsakure shi y bude motar cikin xafin nama y fito
daedae lokacin d jirin y kwasheta ta tafi luuuuuiii xata fadi
D qarfi y furta
" baby !!! Kuma cikin xafin nama y qarasa
Qarasowar tasa yai daedae d xubewarta inda yae maza y tallafota ta fada jikinsa
Gabadaya y dagata kamar baby se part din mamama
kae tsaye bed room din mamaman dake sama y wuce d ita yana qoqarin kwantar d ita
Fitowar mamama kenan daga toilet tayi alwala kamar a mafarki ta hangi sanah
Cikin sauri d sassarfa ta qarasa shi kuma lokacin y koma toilet din y debo ruwa a qaramin cup y daawo
Mamama ce t tallapo kan sanah din inda shi kuma y dinga shafa mata a fuska
kapin a hankali cikin en second ni taja wata gwauruwar ajjiyar xuciya
Ajiyar xuciya mamama tayi qwallar data maqale ta samu damar xubowa kan fuskarta tae sauri ta daukesu dan bata so arman ya gani
" Alhmdlh " y furta akan la66ansa yana sake maeda hankalinsa kan sanah da take qoqarin miqewa hannunta dafe d goshinta
A hankali Mamama ta furta " SANAH !
Gyada kanta kwae tayi b tare d tce komae b dan ji take kanta kamar ze fado
Mamama ta zare hearing aid din kunnenta ta ajjiye gefe kapin ta maeda ta kwance bayan ta gyara mata kwanciyar
B musu kua ta kwanta din dan itama tana buqatar hutun
Mamama ta dubi arman d akwae buqatar aje asibiti ne ?
" A'ah mamama yau d gobe throughout ina gida insha Allah xan kula d ita snn akwae kayan aeki anan kinga b se anje can b "
Mamama tce
" tohm ae shknn ynx dae mu bata waje tae bacci inta tashi seka dubata sannan duk wata magana ma se a yita dg baya "
Da " toh " y amsa yana ficewa dg dakin itama tabi bayansa.
Ta kwashi wajen 5 hours tana bacci kapin ta farka
sanda ta farka dinma d xaxxa6i me xafi ta tashi
Mamama ce ta taemk mata tayi wanka snn tayi sallah ta daawo kan gadon
tana shirin kwanciyar mamama ta dakatar d ita ta hanyar fadin
" baccin y isa haka sanah kwanciyar m ta isa bari n kira arman yaxo y dubaki "
Ji take kamar tace a'ah a kirawo yah imam y dubani amma ta kaasa
5mins back se gashi y shigo hannunsa dauke d qatuwar jaka yae mata mazauni a dakin
tare suka shigo d afrah ita kuma nata hannun dauke d plate d alama abinci ne a ciki
Kae tsaye yaja bed side drawer y xauna yana kallanta
sedae ita sam taqi kallansa hasalima wani side din daban take kalla
Wayar afrah ce tae ruri dae dae lokacin data kema sanah sannu cike d tausayawa er uwarta ta
Kallan arman tayi tace
" Yah arman bari naje ynx xan daawo "
Harara y jefa mata
" ina xakije ?
" Mama ke kirana " ta fada tana sake riqe wayar
" Ohk tohm saura inji b haka b " y fada yana dauke kae kamar bashi yayi maganar b yayinda ita kuma ta fice
Mamaki sanah tayi sosae
kenan yana nupin b ita kadae yke ma takura akan kula maza b ?
Toh wae shi babynnan me yke nupi ne jiqa su xasuyi susha in basuyi soyayyar b ko mene ?
Bata kae ga qara wani tunanin b ta jiyo muryarsa
" Me ke miki ciwo ynx ?
Sake kauda kanta tayi kapin a hankali tace
" kae na d xaxxa6i "
" Ohk toh tashi kici abinci sannan kisha magani " y fada yana bude plate din abincin
Ta6e baki tayi dan harga Allah bakinta babu dadi ko kadan
" bakina b taste pah " ta fada kamar xatayi kuka
" Yes na sani in kika ci ae xe daawo "
" Nidae a'ah " ta bashi amsa d sauri kuma a gajarce
" Well toh bari kwae na mk allura seki fi samun taste din "
Ae b shiri ta zabura
" aah don Allah baby karka min kaaji "
Be kula ta b sema janyo allurar d yayi y fara qoqarin hada ta
D sauri ta janyo plate din ta faara danna abincin d sauri d sauri fuskar nan kamar me cin magani se 6atawa take
Dariya taso qwace masa amma seya dake
Seda tayi wajen 10 spoon sannan ta ajjiye tana sauke ajjiyar xuciya ta tureshi gabanta tana turo baki
" ohyah take water " y fada yana turo mata rubber water
Dauka tayi tana sake kallansa hadda aekin harara
Sarae y ganta amma seya dauke kae
Maganin y faara 6allowa b tare daya kalleta b
" Eyyah nafa ci abincin "
Be saurare ta b y miqa mata maganin
" Yi maza ki shanye dukka " y bata umarni kae tsaye
"Nidae bana sha" itama ta bashi amsa tana kauda kae
"Ohk ae b damuwa bane bari n baki injection ae daama tafi sauqi...."
Tun kapin y gama maganar ta riqo hannunsa ta kwashi maganin ta jefa a baki ta kora d ruwa tana sauke ajiyar xuciya a jere ajere
Cikin ikon Allah kua sae gashi y xauna ........
Mhiz Innocent ce.....✍️
.
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent 😻
Page 15
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻
Fitowa yayi xuwa parlourn qasa
Mamama ce xaune ita d daddy d alama magana suke me muhimmanci dan hatta t.v dke aeki volume dinta a mute yke
Neman waje yayi y xauna yana fadin
" Sannu d dawowa daddy "
" Yawwah arman y jikin qanwartaka ? Daddy y fada yana kallansa
" Jiki alhmdlh "
Mamama tace
" bacci take ynx ne ?
Arman yce
" Aah ynx dae xata samu tayi insha Allah tunda tasha magani "
Daddy yce
" toh bari in ta samu baccin ta tashi se asan maganar d xaayi.
Fafurr aka ta mata tambayar wanda y dauketa tce ita bata sani b kwae dae tasan an dauketa ynx kuma an dawo d ita
Aunty ( maman Khalid ) ce tce
" Kinga malama kwae ki fadi gskia kinje kinbi wani tanbadadden ne ynx km y dawo dake "
B ita kadae b duk wadanda suke dakin seda suka dago suna kallanta
Cikin xafin rae daddy yce
" Abeedah ! Wannan xancen ba naki bane karki sake saka mana baki a magana "
Wata uwar harara arman y jefawa auntyn dan yanda yaji xuciyarsa na xafi
Abba ( Abban souban ) ne y katse masa tunaninsa t hanyar fadin
" Ke sanah kin tabbatar baki san ko 1 daga ckn wadanda suka daukeki b ? kuma babu abinda suka mk ?
" Ehh Abba " ta fada kanta a qasa
Kallanta kwae yke yana naxartar ta Sam be yadda d ita b
be yadda d yanda take sum sum d kae b
yanayinta gabady y nuna alamun rashin gskia hakan ys y cigaba d kallanta
Cikin sa'a kua ta dago kae
Idanunsu suka sarqe cikin na juna
B shiri ta janye ganin yanda ya jefe ta d wani irin kallo data gaza ganeshi ga bugun qirjinta y qaru fiye d nada.
Baffa ne yayi gyaran murya kapin y fara fadin
" Toh alhmdlh alhmdlh
ynx abinda y rage kwae semu godewa Allah tunda Allah y dawo d ita cikin qoshin lpia
kuma babu abinda y sameta
haqiqa Allah shine abin godia "
Haka taro y watse bayan ansha addu'oi.
**********Hira suke sosae cikin farinciki kana ganinsu kaga masoya wadanda suke ji d soyayya
Fuska t rufe kana tce
" Yah souban kallan pah y isa haka mana "
" Uhmm sanah baki san bana gajiya d kallan ki b
ke ni kwae so nake ki qarashe wannan level din in kae xancen wajensu Abba " y fada yana kallanta
Qasa tayi d kanta tana murmushi daedae lokacin d wayarta tayi ringing
" Yah Imam "
Y bayyana kan screen din wayar
Souban y kar6i wayar
" Nipah Allah ma ya gani na gaji d ganin kiran imam xuwa cikin wayarki wae me yake nupi d ke ne ?
Kallansa tayi ganin yanda y haqiqance tce
" Ba pa abinda yke nupi banda matsayinsa na yayana " ta fada kanta tsaye
" Toh kuwa xan fada ms abinda ke tsakanimmu " inji souban
" A'ah nidae ina jin kunya pah ! T fada tana 6ata fuska
Dariya yayi yana fadin
" Sanah rigima "
Itama murmushin tayi har madaedaeciyar wushiryarta na fitowa sannan gefe d gefen kumatunta suka lotsa.
Se a lokacin ta samu damar wucewa tana kada kae hadda qwafa
Kae tsaye sashen su souban din ta wuce tayi sa'a kua maman na xaune parlour tana kallo
Qarasawa tayi ta xauna tana fadin
" Maman souban ba dae kina xaune anan kina kallan banxan nan b baki san abinda ke faruwa b "
" Haba maman Khalid ni wlh kin tsora tani me yake faruwa a gidan ne ? Inji mama
Aunty ta gyara xama tana fadin
" Aekam dae lokacin tashin ki tsaye ne yaxo ! Ynxn nake ganin souban d waccan yarinyar ke alamu ma dae sun nuna soyayya suke "
Xabura mama tayi tana fadin
" Ke ki bari dan manzo "
" Wlh kua ke ni bama rashin kasancewarta cikin family dinnan bane damuwar
kwanakin bayan nan d akace an sace ta wae kin yadda ?
Gwauron numfashi mama taja kapin tace
" Ke ni ina na yadda
kinsan dae en gidannan ba son gskia suke b ynx k fadi gskia ace qin mutum kke
amma ace wae yarinya an sace ta kuma ta dawo tace batasan su waye b
ae kinsan d sake
toh wama y sani ko yawan ta ta tafi "
" Toh ae dama a juri xuwa rafi d tulu wataran Seya fashe
wlh ina ganinta na karanci rashin gskia a tattare d ita yanda take ta sum sum d kae kamar munafuka" inji aunty
" Ynx dae b wannan b meye mafita ? Mama ta fada tana me kallan aunty
Aunty tace
" Ahh wannan kuma ae y rage naki
kece xaki tashi tsaye karki sake ki hada xuri'a da irin wannan yarinyar wlh "
Mama tace
" kinsan abinda xaayi ki bani nan d sati 1 insha Allah xanyi wani abu
idan banyi nasara b xan nemeki se mu chanja zani "
" Ah toh ynx naji batu dadi na dake baki d sanya komae d xafi xafi kike " inji aunty
" Toh ke baki ji me ake cewa b d xafi xafi ake dukan qarfe "
Dukkansu suka saka dariya .
************ Mamama ta kalleta ganin ta miqe
" A'ah ba dae har kin qoshi b ?
" Ehh mamama na qoshi xanje inyi karatu ne " inji sanah
" Ohk tohm Allah y taemk "
Murmushi tayi kana t amsa d
" Ameen "
Ta wuce dakinta
gefen gado ta xauna ta janyo wayarta ta kunna data ta fada Instagram ganin sun nuno mata babban jaruminta Ram Charan yayi posting
ta shiga tana ganin posting din snn t danna lyk ta kashe datar .
Ta janyo Jakarta ta ciro buk ta fara dubawa
Daga parlour ta jiyo magana amma bata fita b har seda afrahn ta shigo dakin
Ta galla mata harara
" Er raenin hankali nasan kina jin muryata shine kikae shiru dan ace bacci kike " afrah ta fada tana hawa kan gadon ta xauna
" Kinga ni karatu xanyi wannan week din muna d test karki hanani yi "
" Ehh ae g sarkin surutu dole in hanaki karatu
ke nice ma ke " Afrahn ta fada tana sake harararta
" Ke Kinga ni ba wannan ba mama ce tace in kiraki !
Tun kapin t qarasa ta juyo tana kallan afrah
" Mama kuma ? ta fada a kan la66anta sedae bata san y fito fili b
" Ehh mama ke kiranki meye naga duk kin tsorata haka ne ? Ko akwae damuwa ?
D sauri ta girgixa kae
" a'ah b komae muje kwae " Sanah ta fada tana miqewa
Tare suka qarasa part dinnasu
Mama na xaune kamar koda yaushe tana kallo
Sanah ta gaeshe ta cikin girmamawa
Ta amsa mata tana maeda dubanta kan afrah
" Afrah jeki dora dinner ga yamma nan nayi "
" Toh " afrah tace tana wucewa kitchen din
Gyaran murya maman tayi tana kallan Sanah dke xaune qasan carpet kanta a qasa duk jinta take a muxance ta qagu taji kiran meye ne maman take mata .........
Inna ga comments dinku d yawa anjima xan qara muku page guda in na samu dama In Sha Allah 😻
Mhiz Innocent ce......✍️
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent 😻
Page 16
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻
Iya wannan kadae y isa y nunan yadda kuke son kasancewa d novel din nan 😻 naaji dadin comments dinku sosae 🥺
Allah y bar qauna 🥺😻🫶
Kamar kua maman tasan meke ranta a hankali t furta
" Kinga sanah b komae ys n kiraki b sedan in miki gargadi "
" Gargadi ? ta maemaeta a hankali
" Qwarae gargadi
inaso daga yau ki fita a harkar souban inma sonshi kike toh ki sani shi b auranki xeyi b
ki fita a harkarsa tun kapin allura ta tono garma
ki barmin dana dan baze ta6a auranki b indae ina raye a duniyar nan "
Jin kalaman maman take kamar wata guduma take qwala mata a tsakiyar ka
wannan hukunci nata yayi tsauri d yawa
bata tashi rabasu b seda sukayi mugun sabo haka
ta riga ta gama mallaka masa xuciyarsa sannan xatace ta rabu dashi ?
Me maman take nupi ne tabbas ta fahimci wasu xantukan nata amma ta kasa fahimtar wasu
xata so ace akwae wanda xe mata fashin baqi akan wasu maganganun nata...
Bata qarasa tunanin b mama ta katse ta d fadin
" Ki tashi ki tafi shine maganar dama amma ki tabbatar kin fita daga rayuwar souban "
Jiri taji yana so y kwasheta bayan ta miqe hakan yasa ta tsaya ta nutsu sannan ta nemi hanyar fita ta fice
Afrah dake tsaye bakin kitchen ta fito
" Haba mama me sanah tayi ne d bakya sonta don Allah ! kuma ba kyason hadin ta d yah souban "
" Toh sannu uwata tunda ke kika haefeni ae dole ki titsiyeni in fada mk dalili koh ?
Afrah da idanunta suka ciko d hawaye sosae tace
" mama don Allah ki bar yah souban d sanah wlh suna qaunar junans...
Wani wawan duka maman ta kawo mata
" Zaki yimin shiru ko sena fasa bakin rashin kunyar ? Shashashar banxa wadda bata san me take b
ki sake min wata magana akan wawiyar yarinyar can xaki ga yanda xanyi dake in baki shiga hankalinki b ni nan xan shigar dke "
**********Ta rasa gane meke mata dadi
me tayiwa mama ne hk d bata so ta auri danta ?
Menene aebun ta dan suna soyayya dashi shin akwae wani laefi ne a ck ?
Wayar ta dake kan side drawer ce tayi qara ta juya kana ta duba me kiran
souban dinne kmr yanda tayi tsammani dan bashi ne kiransa n farko a lokacin b
Namma dae sharewa tayi kamar bata gani b
Daga qarshe ma daya dameta seta kashe wayar gabadaya ta kwanta tana Jan blanket.
Wasa wasa ta fara fita harkar souban idan kiranta yayi a waya bata dagawa
haka messages in yayi mata babu reply
sannan ta guji duk wata hanya da xata hadata dashi
duk kua sanda taga suna shirin haduwa toh pah xata kawo uxurin d zesa ta kaucewa haduwar tasu.
Yau juma'a gabadayansu suna babban parlour kamar yanda suka saba lunch anan duk ranar juma'ar
sedae wadanda suke d uxuri ne kadae basa nan.
Se ynx souban y samu damar shigowa dakin sbd ynx y dawo daga court
yaje yae wanka so yke y hadu d sanah ba dan haka b da babu abinda xe kawoshi sedae y kwanta ya huta.
Kujera yaja y xauna akayi sa'a wadda take facing nata ne bayan y gaeda manyan dke dakin
Gabadaya seta kaasa sukuni kwae caccakar abincin tke d spoon shi kua souban kallonta kwae yke
yayinda daga gefe gogannaku yana ankare dasu duk wani motsi nasu
Baya tayi d kujerarta ta miqe
Baffa dake goge hannunsa d tissue yce
"Amaryata ba dae har kin qoshi b ?
" Ehh baffa dama bana jin yunwa ne " ta fada tana qaqalo murmushi sannan tayi wuff ta fice daga dakin
Souban y bita d kallo yana mamakin wannan chanjawar ta ta
Shi kuwa arman wani sanyi yaji yana ratsashi har seda ya saki wani murmushi Wanda y qarawa kyakykyawar fuskarsa kyawun gani.
Tana shiga daki ta fada kan gado xuciyarta tana wani irin harbawa
kwanciya tayi rub d ciki tana tunane tunane barkatae.
Mintuna kadan taji wayarta tayi qara alamar shigowar saqo
kamar katta duba se km taji tana so ta duba
hakanne y sanyata janyo wayar ta duba saqon souban ne y shigo wayar kamar hk
" Lurv pls karki hukuntani akan laefin d bansan nayi shi b
idan na mk wani abin ki taemkmin ki fadamin kapin xuciyata ta samu matsala
rashin ji daga gareki b qaramin illah yakewa xuciyata b plss "
Ta karanta ta maemaeta har seda taji hawaye na shirin xubo mata sannan ta jefar d wayar ta koma kwanciyar
Ta rasa gaane mecece mafita
mahaefiyarsa tace ta rabu d shi ba xata auram mata da ba toh menene abinda yafi kamata tayi ?
Rabuwa dashi din itace kwae mafita.
Tana nan har ta tashi tayi alwala tana karatu aka turo qofar dakin
seda takae qarshen ayar sannan ta amsa sallamar tana janyo hearing aid dinta ta saka
afrah ce d amrah suka qaraso suka xauna gefen gadon
Murmushi ne y su6uce mata suma suka mayar mata
Afrah ce ta faara magana
" Yah souban ne y aeko mu "
Gyara xama tayi tana kallansu ba tare d tace komae b
Aftah ta cigaba d fadin
" ba se kin fadamin komae b bana buqatar ji dan nasan komae
duk abinda y faru nasani
Kinga sanah bafa mama ce xata aurar d yah souban b ke ina ruwanki indae kina sonshi ?
" Don Allah ki dena wahalar mana d yaya " inji amrah
Dariya duk su 3n sukayi kapin amrahn ta Dora d fadin
" sanah wlh b ruwan yah souban shi be masan abinda y faru b
kece dae kike neman Dora masa laefi kuma kike wahalar masa d xuciya "
" Toh naji naji duk kun wani kalallameni wae ni zaku yaudara....
" Ke dallah b yaudara bace wlh yah souban ne y aeko mu d kansa " afrah ta katseta ta hanyar fadin hakan
" Tohm karku damu insha Allah zan duba " sanah ta fada tana janyo qur'anin data ajjiye kan side drawer
Amrah ta kalleta
" what nupinki ? Kinga just take ur phone ki kirashi "
Harara sanah ta watsa mata
" kiji mu d mata ce miki akae baxan kirashi b ? Ynx dae kinga karatu nake inna gama In Sha Allah xan kira uhmm ?
" Tohm shknn " suka fada a tare suna miqewa.
Fitowarta kenan dg dakinta taga Mamama na shirin hayewa step