Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daukarta " a'ah arman bari tukun kaje k chanja uniform se kazo ka dauketa " dariya yyi sosae yce " amma inna fito a hannuna xatay ta xama ko ? daga yau babyna ce " y fada yana sake fadada fuskarsa d murmushi murmushi ta kuma masa tce " ehh amma dg yau b sunanta baby ba an saka mata suna sunanta SANAH !! yamutse fuska yyi kamar wani babba yce " da dadi " sannan y wuce dakinsa d yke kusa dana mamaman girgiza kae mamama tayi daedae lokacin d take amsa sallamar Alh alqaseem shima fuskarsa dauke d murmushi y qaraso y xauna yana kallan babyn yce " rahma y qarin haquri ? " Mungode Allah " ta fada tana gyara kwanciyar Sanah akan cinyarta wadda ke qoqarin tashi kallanta yyi ckn nutsuwa yce " rahma bani hankalinki nan " jin haka y sanya ta bada dukka hankalinta yce " ina fatan dae babu wata Matsala koh ? yanayinta kadae y nuna masa babu matsalar amma dukda haka seda yaji daga bakinta " tace ehh daddyn arman babu " ta fada fuskar ta dauke d murmushin dake nuna yadda taji dadin tambayar daya mata wadda ke dauke d tarin kulawarsa a garesu baki 1 Jinjina kae yyi sosae yana fadin " Masha Allah ! Allah y gafartawa fateema sannan y raya baby fateema " " Ameen " tace kana ta dora d " daddyn arman an xa6a mata suna pah " yce " ahh masha Allah wanne suna aka saka mata ? murmushi tayi tana kallan babyn kapin tace " SANAH ! tashi yyi ya kar6eta yana fadin " toh Allah y raya mana Fateema Sanah " daedae lokacin Arman y fito ckn qananan kaya y qaraso yn fadin " daddy kaga mamama ta samomin baby koh ? dariya y bawa daddyn nasa yce " ehh mana boy ae mamanka tana qaunarka shys ta samomk baby " qoqarin kar6arta ykeyi mamama tce " kaaga bakaci abinci b snn bakayi sallah b koh ? yce " aah mamama nayi sallah pah abinci ne banci b km ae itama baby bata ci b ! don Allah ki bani ita " y fada kamar me shirin sakin kuka daddy yce " toh jeka xauna " b musu y xauna daddy y dorams ita kan cinyarsa daedae lokacin km data faara kuka d sauri mamama ta tashi ta nupi kitchen ta hado mata madara t daawo kapin ta daawo harya tashi yana tafiya d ita a kafadunsa kamar y saba d raenon daddy kua binsa d kallo kwae yana murmushi mamama ta qaraso xata kar6i Sanah yae saurin fadin " pls mamama ki bani ni xan bata " tce " ohh ni ennan arman madarar ma kae xaka bata ? yce " ehh " aekuwa haka y sauko d ita kan cinyarsa mamama ta tallapo kanta ya dinga bata madarar a hankali mamama har mamaki take irin yadda arman din yke acting kamar y saba tana gama sha mamama ta kar6eta ta dorata kapada seda tayi gyatsa sannan ta bashi ita aekuwa y gane yanda akeyi din bayan an gama basu madarar ranar wuni yayi yana hidima da Sanah din islamiyya ma da qyar y tafi seda mamama ta masa Jan ido. Tun daga ranar pah duk wata kulawar Sanah din Arman keyin ta bata madara , sakata tayi bacci d sauran abubuwa wanka d tsarki d saka Pampers ne kwae mamama ke mata amma komae shike mata wata irin qaunar yarinyar yke kamar bashi d wasu en uwan wanda suke cousins kuma suke tare gida 1 bacci kwae ke rabasu se km in zeje makaranta. Yana xaune gefen qaramin gadon Sanah din d irin abin wasan yarannan a hannunsa yana karkada mata shi se kua 6al6ala dariya take shi km hakan na qaramasa qaemi daedae lokacin mamama ta shigo tana fadin " arman " " na'am mamama gani nan ! baby nakewa wasa " murmushi tayi tace " uhmm ae na gani arman toh seka dauketa k kaewa auntynka ( kishiyarta maman Khalid kenan yaron dt xo dashi gidan ) 6ata rae yyi kapin yce " mamama tana jin dadin wasan pah kar a sakata kuka " " A'ah kaaga babu wanda xe sakata kuka auntyn ce pah kwae " d hanzari y miqe yana fadin " yawwah dama banaso Khalid dinnan y dauketa kullum y dauketa setayi kuka " girgiza kae mamama tayi " arman banda rigimarka ita Sanah ina tasan waye ma ya dauketa ballantana tayi masa qwuiwa " bema jita ba dan harya dauki Sanah din y fice d ita binsa tayi d kallo kana ta miqe itama ta fito A gefe ta sameshi kusa d auntyn dke dauke d Sanah a hannu d alama jira yke ta kalleta shi km y kar6a abarsa su koma aekam ko minti 1 batae a hannun ta b ta miqa masa tana fadin " gata " d sauri y kar6a yana barin wajen auntyn ta juyo d kallanta kan mamama tce " ashe kuma abinda y faaru kenan ! toh Allah yji qan rae " " Ameen " mamama ta fada tana mamakin qarfin hali irin na auntyn lokacin d qanwarta ta ta rasu bata nan amma wata 1 d rasuwar ta daawo sedae yau sanah ta kusa wata 3 se ynx xataxo mata gaesuwa hadda neman iri na ganin 'yar da marigayiyar ta bari bayan gabadaya faccalolinta duk seda sukaje mata gaesuwa harcan gidan qanwarta ta bata qara mintuna 5 ba ta tashi tana fadin " toh Allah yaji qan rae y raya abinda aka bari nabar Khalid shi kadae bari in wuce " mamama tace " toh an gode. Tana nan xaune taga fitowar arman dauke d Sanah wadda a ynxn y sako mata rigar sanyi kallansa tayi kapin tace " ina kuma xakaje ? " Wajen baffa xanje yau basu gaesa d baby b " binsa tayi d kallo tana cewa " toh k gaeda baffan " " toh " yce yana ficewa daga 6angarennasu xuwa 6angaren former brigadier general Arab tsoho me ran qarfe y sameshi a kishingide kamar koda yaushe d jarida a hannunsa yana karantawa ( mazan jiya kenan har ynxn akwae idon ) ya qarasa y xauna yana fadin " baffa ga baby yau bata xo kun gaesa b " murmushi y wanxu akan kyakykyawar fuskar tsohon yana ajjiye jaridar hannunsa y kar6i Sanah yana fadin " ahh lallae abokina hala dae yau kae k shirya amaryartawa dan naga tafi kullum kyau " dariya arman yyi yana fadin " ehh baffa nine ae daama nafi mamama iyawa " haka suka cigaba d hirar dama sun saba kapin suka koma 6angarensu a hanya suka hadu d Abba ( qanin daddy ) yana shirin fitowa shida souban Abba yce " ahh arman sanah ce a hannunka ? yce " ehh Abba daga wajen baffa muke " " toh ka dena fitowa d ita a cikin sanyin nan saboda kar sanyi y kamata kaaji koh ? yayi maganar yana kar6arta arman yce " toh Abba " souban yce " Abba nima k bani sanah din in dauketa " " aah kaga mu wuce kaga sauri nake karka makarar dani ". Abba y fada kapin y juyo yana kallan arman " maza jeka kae sanah gida kazo mu wuce masallaci " kar6arta yyi yana fadin " toh. Tun daxu yke ta faman lallashinta taqi yin shiru ya bata madara taqi kar6a y jijjiga ta amma duk a banza mamama ta qaraso dakin d sauri dan idar d sallahrta kenan t jiyo kukan sanah din d sauri ta qaraso tana kar6arta " lpia kua arman meya sameta ? cikin yanayin kamar yana shirin kuka yce " Nima bansaniba tun daxu kwae naga tana kuka kuma taqi yin shiru duddubata mamaman tayi ko wani abunne y cijeta amma bata ga komae b ko wata alama sedae taga kamar yarinyar tana kae hannunta saetin kunnanta ta janye hannun amma se taga ta sake mayar d hannun tana qara sautin kukannata.......... Alqalamin Innocent ne ✍️ *♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story By Mhiz Innocent 😻 Page 3 ~08105359153~ Number dina d take always welcoming naku a DM 😍 but pls message me amfani couz number nan an tanade ta ne especially sbd ku 🌚😻 Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 😻 cikin tashin hankali ta fito daga dakin sedae daddy baya nan hakanne y sakata daukar mayafinta ta hau mota suka wuce asibiti ita d arman tashin farko aka kar6esu ana dudduba yarinyar. Mintuna wajen 20 kapin wani doctor yce d ita ta biyoshi office kae tsaye ta shiga ta ja kujerar ta xauna arman na gefe yana kallansu doctorn y xare glass dinsa sannan yce " hajiya daama yarinyar taki tunda kika haefeta tana d qarancin ji ne ? Kallansa take sosae d alamar tambaya dan sam bata fahimci xancen nasa ina y dosa b jin bata bashi amsa b y sanyashi fadin " ohh sorry hajiya na manta ashe pah baby ce nasan ba xaku gane ko tana ji ko bata ji b ! so ynx dae bayani 1 shine hajiya yarinyarki tana d qarancin ji ne kuma dan tayi ciwon kunne b wata damuwa bace saboda xe iya dinga tasar mata a kowanne irin lokaci ne amma ynx xamu san yanda xaayi insha Allah kapin babban likita yazo in yaso seya fadi abinda xaayi din gabadaya mamama ta kasa cewa komae jin wae sanah tana d qarancin ji " kenan kurma ce ? ko me wannan likitan ykeso ya fadamata. Magunguna y rubuta mata ba tare d tace masa komae b ta fito ta wuce pharmacy ta kar6i magungunan sannan suka wuce gida shidae arman be fahimci komae b ya daega babyntasa tayi shiru ita dae mamama bin sanah kwae take d kallo har wasu hawaye taji suna xubo mata cikin sauri ta gogesu kapin ta dudduba magungunan sannan ta saka mata na shafawa a kunnen ta bata nasha tana ta yamutsa fuska arman d bashi ke sha b shima se yamutsa fuskar yke tana gama bata y dauketa yaje y kwantar d ita. Gabadaya jin jikinta take babu qwari ta kasa yin komae tunanin sanah din y cika mata xuciya d ruhi ynx qaramarta d ita bata d lpiar kunne " yah salaam " ta fada tana dafe kanta daedae lokacin d umma ( matar baba qaninsu daddy d Abba kenan ) d sallama ta shigo dakin ganinta y sanya mamama daga ido tana fadin " umman amrah sannu d shigowa " " yawwah sannu dae maman arman ! dama shigowa nayi naji naaga dazu kin fita cikin sauri kamar babu lpia kuma ynx kin dawo ma kamar babu lpia ? Jinjina kae mamaman tayi kapin tace " wlh umman amrah kinga yarinyar nan ce taketa kuka tun daxu shine na kaeta asibiti suke tabbatar mana d cewar tana d qarancin ji shys yau d ciwon kunne ta tashi " " Yah salaam yah salaam " umman ta fada ta maemaeta " Eyyah Allah mae yadda yaso d bawansa Allah y bata lpia ! don Allah ki dena damun kanki kinji insha Allah idan d rabon warkewa kinga ae xata warke Mamama tace " haka ne insha Allah " nan suka cigaba d hira dan daama tasu tazo 1 a cikin matan gidan kansu a hade yake yayinda aunty ( kishiyar mamama d mama matar Abba ) Kansu a hade yke kuma sune masu baqin hali a cikin gidan. Dawowarsa kenan daga makaranta y shigo dakin yana kiran " baby ! baby " d qarfi sakamakon daga muryar d yke tana iya jiyoshi aekuwa ta fara xillo kan keken xaman d take d hanzari ya qaraso yana rungumeta " baby na daawo " se dariya take itama tana kallansa cikin gwarancinta itama tace " be..bi * ranar murna kamar xeyi me har rawa seda yayi yau sanah tayi magana yana nan yana murnarsa ya jiyo muryar souban daga parlour daukar sanah yayi suka fito ganinta ya sanya souban din qarasowa yana cewa " arman kawota na dauketa na kaeta suyi wasa da afrah " ta6e baki arman din yayi kamar wani babba " a'ah souban indae kanaso suyi wasa kaje ka dauko afrahn ka kawo ta nan se suyi wasan " " shikenan toh bari in daukota har amrahn baba ma xan dauko se suyita wasan tare " shi dae arman bece masa komae b har y fice aekuwa se gashi y kawo su duk akan kekunan xamansu dan duk xasuyi sa'anni sedae wannan ta bawa wannan wata ko watanni amma dae duk sun girmi sanah haka suka hadasu sukuwa sukaeta wasansu souban d arman suna kallansu suna dariya in sunyi abin dariya. Suna haka souban y jiyo muryar mamansu dga parlour tana fadin " souban rashin kirkin naka har yakae ka fito min d yarinya a cikin sanyin nan ! toh miqomin abata ni ba shashasha bace " a sukwane y janye keken d afrah ke kae y fita y kaewa maman ita kana y daawo arman yce " toh k dauki amrahn itama ka kaeta gidansu mana " dan shi kam Allah ma ya gani y gaji d wasan yafiso su 2 suyi abinsu haka souban y dauka amrahn itama y kaeta 6angarensu kapin y wuce nasu. Kwanaki suka cigaba d garawa satika na shudewa suka hadu suka bada shekaru 3 shaquwa me tsanani na sake shiga tsakanin arman d sanah yanxu haka indae xaka mata magana d qarfi xataji abinda kke fada amma indae a hankali kayi kamar yadda xakayi d mutum me normal kunne baxa taji b sedae kwae ta kalleka ta faara xuwa islamiyya tana fahimtar karatun sosae duba d yanayin karatun islamiyya ana yinsa ne d qarfi gata akwae qwaqwalwa ana yi musu karatu xataxo tana biyawa arman ko mamama ko daddynta. " Baby ! Baby ! Ta fada d qarfi yanda tasan xe jita d sauri y qaraso yana fadin " baby gashi pah na siyo miki sweet din " " me kace ? Ta fada cikin muryar ta na me koyo yce " ehh na siyomk sweet din " kallan bakinsa kwae takeyi hakan yasa ta gane abinda yake fada dukda ma seda ya daga murya tace " toh ina sweet en ? yce " ohyah close ur eyes " y fada yana kulle idansa ganin hk y sanya ta rufewa shi km y miqo hannunsa ya dakko hannunta y dora mata akan hannun ta bude ido tana kallan sweet din ta bude ido tana bude baki ( duk wani wayo d surutunsa ta dakko shi ) tace " baby duka ? yce " yes baby ! rungumeshi tayi tana fadin " kuma baxan sanwa amrah da afrah ba amma xan bawa mamama " ta fada tana ficewa daga dakin a parlour ta sami mamama d daddy ta qarasa wajen daddyn d gudu tce " daddy kaaga baby y siyo min " " ahh er gidan baby mu gani " daddy y fada yana kar6ar sweet din ita kua se dariya take mamama tace " daddyn arman bani sweet dinnan yaron nan na hanashi siyowa sanah kayan zaqi haka amma yaqi ji " daddy yce " aah ki barta in kikae haka baxa taji dadi b ki barta a hankali xata dena shan xaqin " y fada yana kallan Sanah d tayi rau rau d ido hade d ta6e baki Ba don taso b haka ta qyaleta shi km daddy y miqamata sweet din yana kallanta ita kuma seta kalleshi ta bada hankalin ta sosae dan so take ta fahimci abinda xe fada mata din yce " jeki daki " d gudu kuwa ta kwasa duka suka bita d kallo daddy yce " uhmm rahama so nake in saka yarinyar nan a makaranta amma kuma ga yanayin lalurarta y kike ganin xaayi ? Mamama tace " nima tunanin d nake kenan tunda dae karatun boko daban dana islamiyya " Jinjina kae daddy yyi kapin yce " Kina bata maganin kua ? mamama tce " ehh ina bata kwae dae Allah ne beyi xata dinga ji sosae din b har ynx " cikin nuna amincewa d xancennata yce " hakane amma akwae wata shawara dana yanke daama next week in Allah y kaemu xan je los Angeles toh insha Allah ki shirya se muje a duba kunnennata in d rabon warkewar se kiga an dace " Ba qaramin dadi mamama taji b dan tana matuqar jin dadin yanda yke nuna tsantsar kulawa game d sanah din ba xaka ta6a cewa bashi y haefeta b ................ Mhiz Innocent ce ✍️ *♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story By Mhiz Innocent 😻 Page 4 ~08105359153~ Number dina d take always welcoming naka a DM 😍 but pls message me amfani couz number nan an tanade ta ne especially sbd ku 🌚😻 Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 😻 Cikin sati 1 tsaf suka gama shirin xuwa Los Angeles . a wata safiya suka tashi xuwa can su 2 suka tafi bayan kukan d arman yasha kan xe bisu amma saboda makaranta yasa basu tafi dashi b . Dab d maghrib suka isa qasar me cike d sanyi dan haka d rigunan sanyinsu suke tafe. kae tsaye gidan d xasu sauka suka wuce gidan wani abokin daddy me suna " doctor Stephen " daama indae daddy yazo anan yake sauka amma shi abokinnasa baya gidan ynx haka shys y basu gidan ranar hutawa kwae sukayi . washegari kua sanah ta dinga musu kuka akan rashin ganin baby seda sukayi video call ta ganshi sannan ta sarara musu . Wajen 12 suka isa hospital bar kae tsaye doctor Stephen y kirawo a waya y shigar dasu ciki ba'a dauki wani lokaci b aka shiga d sanah dakin bincike suna nan xaune a harabar asibitin kowannensu addua yke ckn xuciyarsa tare d fatan dacewa daga can doctor Stephen din y buqaci ganin daddy suka koma dakin binciken tunda shima doctor ne Dr Stephen yce " doctor yarinyar nan xa'a iya mata aeki sannan kuma in Allah y yadda se kaga ta warke ! amma sedae ynx shekarunta sunyi qanqanta nasan kaema kasan hakan " daddy yce " qwarae Dr Nima n dauka xaa sami wata mafitar ne ba se an kae ga aeki b amma tunda haka ne inda akwae wani taemakon d xaka mana muna d buqatarsa tunda kaga yarinyar ynx haka inaso in sakata ne a makaranta ! so kaga ba lallae ta dinga fahimta sosae b a yanayin d take " jinjina kae Stephen yayi sannan ckn tabbatar d xancensa yce " doctor akwae taemakon d xaa mata kapin lokacin d xaa iya mata aeki yazo " ckn farinck daddy yce " doctor wanne taemko ne wannan ? " Hearing aid !! Stephen y fada yana murmushi " Wowwww ! Doctor kasan na manta d wannan ae d tuni an nemi wannan mafitar " dariya Stephen yyi yce " ae Nima nasan mantawa kayi so ynx xaku tafi dashi sannan se a kula dashi tunda yarinya ce " b qaramin godia daddy yayiwa Stephen b sannan y baro wajensa. Ko sati 1 basuyi a qasar b shima kuma daddy y gama abinda zeyi suka kamo hanyar dawowa kano bayan sun taho d hearing aid din amma basu fara mata amfani dashi b tukun . gabady sanah ta koma wani silent d ita sam bata san yin magana sedae tayi shiru tana tunani . Ranar d suka koma d maghrib ne dan haka duk en gidan suna nan lokacin d suka shiga gidan yyi daedae d fitowar baba (baban amrah) d Abba (abban souban) harma d baffa xasuje masallaci bayansu sojoji ne wajen guda 5 masu tsaron baffan cikin farinciki dukka suka tarbesu tare d fatan an dace sosae fara'ar daddy ta qaru hakan y nuna musu an dace din kenan nan yke sanar dasu yadda abin y kasance suma sunji dadi sosae kuma sun nuna farin cikinsu baffah yce " ohh ni yanxu wannan jaririyar er xaa maqalawa hearing aid kae Allah dae y kyauta y qaremu d lpia " dukka suka amsa d " ameen " sannan daddy yabi sahunsu suka nupi masallacin. A hankali ta tura qofar shiga dakin jinta a rufe y sanyata dakko mukulli ta bude hannun ta riqe dana sanah ae tun kapin su qarasa shiga arman y jiyo muryar su dan suna xaune a bayan harabar gidan shida souban suna alwala d gudu y qarasa dakin yana fadin " baby!! jin muryarsa y sanyata juyowa itama d gudu ta qaraso itama tana fadin " baby! rungume juna sukayi arman yana cewa " baby ynx kina jina ko nayi magana a hankali ? turo baki tayi kamar xatayi kuka dan bataji abinda yace b tce " baby shine k tafi koh ? Yce " aah pah baby kece kika tafi kuka barni ni kadae keda su daddy ni pah babu inda naje ina nan a gida kullum " kallansa kwae takeyi ba tare d tace uffan b . Ranar kuwa kapin kowannensu yayi bacci seda suka dade suna ta surutae tana bashi labari dukda wani abin ba ganewa yake b amma jinta yke yana ta dariya seda mamama taxo ta korashi sannan y tafi kana ta gyarawa sanah gado ta kwanta sannan ta koma dakin ta. Washe gari d safe qarfe 7 mamama tayi mata wanka ta shiryata cikin doguwar riga ta mata parking din gashinta sannan ta janyo hearing aid care kit din dake cikin wardrobe dinta ta ciro shi binta d kallo kwae sanah take ba tare d tace komae b a hankali ta kama kunnan sanah din ta saeta yanda ake sakawa ta duba wanda akae marking nasa d red colour sannan ta saka shi a kunnan dama dayan kuma me blue a jiki ta saka shi a kunnan hagu sannan tace cikin taushi " SANAH ! ae d sauri ta matsa baya tana fadin " mamama d qarfi pah kikae maganar " murmushi mamama tayi tana hamdala ga Allah sannan tae qasa d muryar ta Dan dole se an dinga mata magana a hankali kapin ta saba tunda ada daga can nesa take jiyo muryar sa6anin yanxu tce " jeki kiramin arman " tana fadin kapin ta rufe baki harta fice daga dakin ta nupi dakin arman " baby ! baby !! xo kaji " socks yake sawa amma jin muryarta yasa shi tasowa yana cewa " baby menene ? hannu takae kunnanta tce " d qarfi pah kake magana " se a lokacin y lura d abinda ke kunnanta y kama hannun ta suka fara rawa a dakin yace " yeahh baby ta faara jin magana ko a hankali akayi haka sukayi ta murnarsu sedae sunayi tana kae hannu kunnanta dan ji tayi kamar abin y takura ta tunda bata saba b se taji ma kamar ta cireshi amma kuma in ta cire din ko muryar baby ba xata dinga ji sosae b. A ranar kua aka kaeta makarantarsu arman ita dasu afrah d amrah aka sakasu a pre nursery yayinda souban d arman harma d Khalid yanxu haka suke a jss 3 . Suka faara karatunsu cikin amincewar ubangiji d nasarori masu yawa dan dukkansu su ukun ba a banxa b baya bane sedae duk sanah ta kere su b qaramin taemk mata hearing aid dinnan yke b tun batason saka shi har ta saba d kanta take kaewa arman ko mamama ko daddy su saka mata abinda yake rabata dashi bacci ne kwae in xatayi bacci mamama ke cire mata ta maeda cikin hearing aid care kit b qaramar kulawa sanah ke samu daga wajen iyayennata b uwa uba kuma arman kowanne lokaci nata ne komae y samu baby bashi d xance sena baby haka xalika wajen souban ma yana ji d ita indae zewa qanwarsa afrah abu toh ze hada d sanah din hadda amrah. Tana tsaye a qofar ajin su arman din ta cika tayi fam so take kwae ta samu wanda xata sakarwa kukan shagwa6ar aekuwa batafi minti 5 b arman din y fito shida souban d sauri duk su 2n suka qaraso arman y kamo hannunta " meya sameki baby ? Aekuwa dama qiris tke jira ta saki kukan tsugunnawa yyi y kamota yana fadin " yi shiru baby yi shiru ki fadamin menene ? shima souban din kallan ta yke yana cewa " meya faru sanah ? seda tayi me isarta sannan tace " ba yah khalid ne ba... " Arman yce " Khalid kuma ? Me Khalid din y miki " turo baki tayi tace " toh ba wata ce ta

Chapter 2 of 18