Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan
faɗi abu ɗaya da za'a yi mu sami nasara."
Koda jin haka sai Faltuz tace, "Ai dama ku maza kaidin ku yafi namu masifa,kawai dai ƙaurin suna muka fiku.
Maza sanar damu dabarar da zamu yi don mu hallakar da wannan basarake cikin ƙanƙanin lokaci."
Murkubalu ya yi murmushi, sannan kuma ya ƙyalƙyale da dariya har da doka ƙafarsa guda ƙasa,yana mai yiwa kansa kirari da cewar,
"Nine Murkubulu tsuliyar dodo, kuna nine baƙin annamimi uban munafukai.
Nine sharri kayan kwalba,kakan mugayen aljanu,masu baƙar zuciya da mugun nufi da baƙin tanadi."
Murkubalu ya ci gaba da cewa,
"Abin da
za'a yi shi ne,wace ce tafi kowa rashin tsoro a cikinku?"
Nan da nan su duka suka nuna Lulaija suka ce,
"Gata nan kuma ita ce wawiya don an bata sandar girma akan hakan,kuma an tabbatar da cewa a cikin gaba ɗayan al'ummar aljanun garinsu babu mai iya sai da rai kamarta."
Murkubalu yayi murmushi,a karo na uku yace,
"Yauwa ke nake so ki juye kamanninki izuwa na matar wannan waziri,ki kasance cikin suturu mai shara-shara wato wadda ke nuna surar jikinki sai ki gifta ta gabansa,yayin da yake wannan aikin bauta na gunkinsa.
Tabbas yana ganinki sha'awarsa zata motsa ya tashi ya bar bautar ya bi bayanki.
Mu kuma sai mu yi amfani da wannan damar mu cim masa."
Koda jin wannan batu sai Lulaija tace,
"Tabɗijam amma kun zo mini da rainin hankali,to ku tsaya ku ji don fa an ce ni wawiya ce kuma bani da tsoro baya nufin cewa bana son na cigaba da rayuwa a duniya,shin ka mantane cewa an ce kada mu kusance su yayin da suke aikin bauta ko tsafi?
Ko kuwa kana so ne na halaka a banza."
Murkubalu yace,
"Ai ba so nake ki halaka ba,kuma bana ce ki kusance shi ba,nesa da shi
zaki gifta,buƙata dai kawai ya ga giftawar taki cikin wannan yanayi."
Yayin da Lulaija ta ji haka sai tayi murmushi tace,
"An gama."
Kafin wani daga cikinsu ya ƙara cewa wani abu tuni ta ɓace ɓat,bata sake bayyana a ko'ina ba sai akan tagar turakar wannan waziri a matsayin tsuntsun kanari.
A wannan lokaci waziri,ya tsugunna gaban gunkinsa bisa gwiwoyinsa yana bauta.
Cikin hanzari tsuntsun kanarin ya sauko ƙasa ya tsaya ya zamana tsakaninsa da waziri ya kai taku arba'in.
Kawai sai tsuntsun kanarin ya rikiɗa ya zama matar waziri wadda ta kasance ɗanyar budurwa mai tsananin kyawun fuska da kyawun surar jiki.
Sanye take cikin wata irin doguwar riga mai launin shuɗi kuma shara-shara.
Daga ƙasanta an yi mata beza da adon dutwatsen lu'ulu'u.
Koda ta yi tafiya taku biyu sai ƙarar duwatsun lu'u lu'un suka janyo hankalin waziri ya ɗago da kansa da sauri don yaga komene ne.
Ai kuwa sai ya yi arba da kyakkyawar matarsa tana mai bayyanar da surar jikinta kuma ta faɗa cikin ɗakin da sauri.
Cikin kiɗemawa waziri ya miƙe zumbur har ma yana dungure gunkin nasa,wato abin bautar tasa.
Gunkin ya tuntsure ya faɗi
ƙasa,amma san bai lura ba.
Kawai sai ya ɗaga ƙafarsa ya shallake gunkin ya nufi ƙofar ɗakin da matar tasa ta shiga.
Har ya jefa ƙafarsa ta dama cikin ɗakin ya ɗago ta hagun kenan sai yaji wani irin abu ya shiga jikinsa gaba ɗaya,wanda ya haddasa sandarewar jijiyoyin jikinsa na tsagin ɓangaren hagu.
Kawai sai ji yayi komai na rabin jikinsa ya daina aiki.
Take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa,yana mai kurma ihu.
Al'amarin da ya janyo farkawar gaba ɗayan mutunen gidan kenan,suka rugo inda yake a firgice.
Koda suka zo suka ga halin da yake ciki sai duk suka kama kuka suna cewa,
"Shi kenan ta faru ta ƙare,annobar da ake faɗi ta sauka."
A can gidan sarkin Kisra kuwa lokacin da Tazibul Luhucul ta sauka a tsakiyar harabar gidan sai ta iske sarki a kishingiɗe yana gyangyaɗi,amma hannunsa guda na kan irin wannan gunki wanda wazirinsa ke bautawa.
Koda ganin haka sai hankalin Tazibul Luhucul ya dugunzuma don ta san cewa ba zata iya yi masa komai ba,muddn hannunsa na kan gunkin.
Nan fa ta tsaya tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta da tunanin mafita.
Sai daya zamana alfijir ya kusan ketowa anma bata sami mafita ba.
Ta ɗauko mudubin tsafinta ta shafe shi da
hannun hagu,take taga duk abin da ya faru tsakanin hadimanta da 'yan mnajalisar wannan birni wato taga cewar gaba ɗaya sun sami nasara akan 'yan majalisar birnin cikin sauƙi,waziri ne kawai ya basu wahala amma shima ɗin a ƙarshe sun gama dashi.
Kuma taga cewa tuni hadiman nata sun koma can bayan gari sun tsaya ita kawai suke jira.
Gashi kuma saura baifi daƙiƙa ɗari uku da sittin ba lokacin tafiya yayi.
Nan fa Tazibul Luhucul ta ji zuciyarta ta cika da mugun baƙin ciki tace a ranta,
"Haƙiƙa abin kunya ne ace hadimaina sun sami nasara amma ni na kasa.
Ya zama dole nima nayi tunanin dabara kafin ƙarewar ƙanƙanin lokacin da nake da shi."
Tana gama aiyana hakan ne,wata kyanwa ta zo giftawa ta gabanta.
Cikin fushi Tazibul Luhucul ta kaiwa kyanwar duka da hannunta na dama,ai kuwa kyanwar nan sai ta tsorata tayi tsalle ta faɗa kan sarki.
Ba shiri sarki ya farka a firgice,ya miƙe tsaye gami da zare takobinsa ya kama leƙe-leƙe da dube-dube.
Ba zato,ba tsammani,sai ya ji komai na tsagin rabin jikinsa ya daina aiki.
Take ya faɗi ƙasa,kawai sai jin dariyar Tazibul Luhucul yayi tana mai cewa na gama dashi,na gama da shi.
Ƙiri ƙiri ta baiyana
a gabansa tana ta yin wannan furuci.
Shi kuwa sai ya kurma ihu yana mai kiran sunan ɗansa jarumi yarima Lubaika wanda tuntuni yayi nisa akan hanyarsa ta zuwa dajin dulmus
don saduwa da boka Hulumul Makahur.
Kafin mutanen gidan sarautar su kawo wani ɗauki tuni Tazibul Luhucul ta ɓace ɓat sai zuwa akayi aka iske sarki a kwance ya zama naƙasasshe.
Kamar yadda Tazibul Luhucul tare da hadimanta suka sami nasara a birnin Ƙisra haka ma Saubatul Azwas da nata hadiman suka sami nasara a birnin Rum wato dai suma sun mai da sarkin garin da 'yan majalisarsa naƙasssu masu mutuwar jiki.
Bayan wannan gagarumar nasarane suka sake haɗuwa a wata mahaɗa dake tsakanin biranen biyu,nan take suka ƙyalƙyale da dariyar farin ciki.
Saubatul Azwas tace,
"Yauwa yanzu mun gama da ƙasa biyu saura guda huɗu.
Yake ƙawata yanzu sai ki tafi ƙasar Hindu da Farisa ni kuma ki barni da Misra domin itace ƙasa mafi haɗari tunda sun kasance ma'abota addinin musulunci,waɗannan mutane suna iya hallakar da aljanu ta hanyar ƙonesu da wuta irin
sihirtacciyar wuta yayin da suke kiran sunayen Ubangijinsu wato abin bautarsu.
Koda jin haka sai Tazibul Luhucul tace ai dama babban kaya
sai amale,dole ne na barki dabirnin Misra,babu abinda zance dake sai fatan sa'a." Saubatul Azwas ta fashe da mahaukaciyar dariya tana mai
buɗe fukafukanta ta tashi sama cikin sauri hadiman dake tare da ita suka bi bayanta,nan da
nan suka cilla izuwa ƙololuwar sararin samaniya suka nufi birnin Misra.
Tazibul Luhucul da nata hadiman ma suka tashi sama suka nufi ƙasar Hindu da Farisa.
Wannan shine abinda ya faru gasu Tazibul Luhucul bayan sun
fara samun nasara bisa gagarumar buƙatarsu ta duniya wacce itace mallakar mutane da aljanu dakuma haɗa sinadarin gano inda wani sirin tsafiwanda shine kacal ya rage musu su mallaka a taskarsu ta tsafi.
Al'amarin yarima Sammaru kuwa lokacin daya kama hanya ya nufi dajin Dulmas saida yayi tafiyar sa'a bakwai cif ba tare da ya yada zango ba,kuma bai haɗu da wani tsautsayi ba ko mugun abu face namun daji iri-iri waɗanda ko guda ɗaya bata tare shi ba ko afka masa.
Yayin da rana ta take sai zafi ya yawaita a jejin,duk da cewa akan doki yake tafiyar sai daya jiƙe sharƙaf da gumi.
Da yake zuciyarsa a harzuƙe take ko kaɗan bashi da niyyar tsayawa a ko'ina har sai ya riski kogon da boka Hulumul Makahur
yake,dama ya sani cewar tafiyar sa'a goma sha huɗu ce zata kaishi wannan wuri daga cikin
birnin Sin.
Wato a ƙa'ida in dai mutum ya taso da sassafe tabbas zai isa bayan magariba.
Babu zancen yunwa,ƙishirwa ko gajiya a tare yarima Sammaru domin yayi watsi da su a ransa burinsa kawai ya ganshi a gaban kogon tsafin boka Hulumul Makahur.
Bisa rashin sa'a sai yaga dokinsa ya fara nuna alamun sarewa domin baya iya sauri sosai kamar da farko,sannu a hankali kuma sai dokin ya fara tafiyar sassarfa,wannan al'amari ya fusata shi amma daya fuskanci cewar dokin ya gaji ne kuma yana buƙatar ruwa da abinci sai ya rungumi ƙaddara ya tsaya ya sauka.
Sammaru ya duba gabas da yamma,kudu da arewa don ya hango inda za'a sami fadama.
Ai kuwa sai ya hango wata ƙorama wadda ke kwaranya bisa wasu ƙananan duwatsu.
A gefenta wasu ciyayine masu tsawo da duhuwa,koda ganin wannan wuri sai murna ta kama shi cikin sauri yaja dokin ya nufi inda wannan ƙorama take.
Abin da bai sani ba shine wannan wuri wata mafakace ta waɗansu gungun muggan 'yan
fashi.
Adadin waɗannan 'yan fashi ya kai dubu biyar,duk suna nan a kwance cikin ciyawa mai duhuwa sunyi lamɓo.
Tun sa'adda yarima
Sammaru yazo wajen suna ganinsa amma shi bai gansu ba kuma bai ji motsin komai ba a wajen,kai ko kaɗan ma bai taɓa zaton wani mai rai zai iya zama a cikin wannan duhuwa ba in dai kasance ire-iren su kifi,kwaɗo da makamantansu ba.
Sammaru ya kai dokin nasa cikin ƙoramar,dokin yasa bakinsa ya sha ruwa ya ƙoshi sannan ya nufi cikin duhuwar nan inda doguwar ciyawa take ya kama cin ciyawar,shi kuwa yarima Sammaru sai ya cire takobinsa da sauran kayan yaƙinsa ya ajiye a gefe guda sannan ya tuɓe kayan jikinsa gaba ɗaya ya ajiye,ya faɗa cikin ƙoramar ya kama wanka.
Faruwar hakan keda wuya 'yan fashin nan suka yi fitar burtu gaba ɗayansu suka kewaye ƙoramar duka.
Waɗannan 'yan fashi sun kasance gabza-gabza masu ƙirar samudawa kuma suna ɗauke da muggan makaman yaƙi,komai rashin tsoron mutum in yayi arba dasu sai zuciyarsa ta harba,cikin tsananin mamaki Sammaru ya ɗaga kai sama ya dubesu,to amma shi dai yasan duk bala'in da za'ayi sai dai ayi amma ba zai yarda su kämashi ba su wulaƙantashi bare su ɓata masa lokaci bisa saurin daya keyi na isa kogon tsafin boka Hulumul Makahur.
Wani garjeje daga cikin 'yan fashin wanda
shine mafi girma,kwarjini da ban tsoro ya matsa kusa da Sammaru yace ɗan nema samamme fito kayi gaisuwa gaban sarkin ɓarayin jejin Dulmas tun gabanin banyi fishi da kai ba,ka ware ido kana kallon mu kamar mutum đa mutum.
Wannan kalma ta ƙarshe ba ƙaramin ciwo ta yiwa yarima Sammaru ba domin shi a ganinsa anyi matuƙar muzantashi,wai shin ma me
wannan ɗan fashi yake nufi da kamar mutum da mutum,lallai akwai raini a cikin wannan batu,wato yana nufin su sune mutane shi kuwa ba mutum bane,cikin tsananin fushi Sammaru ya dubi sarkin ɓarayin ya daka masa harara gami da tsawa yace,
"Kai ƙaton banza,la'anannen wofi,shin bakusan ko ni waye ba,kake bani umarnı,kuma har kake ƙasƙantani.
To kasani cewa idan kana yi mini kallon jaki ne ni kuma ina yi maka na harawa ne.
Babu wani đan da ya isa ya ɗaga hannu a gabana ba tare da na ladabtar da shi ba,nine yarima Sammaru ɗa ga sarki Alyasil Buhus na birnin Sin,duk wani abu daya kwana ya tashi acikin jejin nan ƙarƙashin mulkina da iko na yake."
Koda jin wannan batu sai sarkin ɓarayin ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da gogen tsumma.
Nan fa sauran yaransa suka
karɓa,ma'ana suka taya shi yin dariyar.
Lokaci
guda kuma ya tsuke bakinsa ya sake murtuke mummunar fuskarsa mai kama da tatsilallan man shanu yace,
"Kai yaro sarauta acikin gari ake yinta banda cikin daji,babu sarki a jeji sai mai ƙarfi,mune sarakan dawa maganin 'yan' dawa da baƙindawa,babu mai shiga dajin nan ya fita lafiya face mun tatseshi ya zama talaka fitik,koda kuwa shine ya fi kowa dukiya,sai mun
kwankwashe shi ya zama tamkar ƙwaryar molo kuma sai mun ragarjeje shi ya fatattake tamkar yayin iska."
Sammaru yace,
"Ai kuwa ƙaryarku tasha ƙarya daga yau kun dena wannan ƙazamar sana'a ta zalunci domin na kasance mala'ikan azzalumai mai mai dasu turɓaya a doron ƙasa."
Kafin Sammaru ya gama rufe bakinsa sarkin ɓarayin ya bada izinin a ragargaza shi.
A guje mutum hamsin sukayi caaa a kansa da nufin su daddatsashi suyi gunduwa gunduwa dashi a cikin ƙoramar.
Kash,rashin sani yafi dare duhu inda waɗannan barade hamsim sun san abin da zai biyo baya da basu haiyakewa Sammaru ba farat ɗaya.
Lokacin da baraden hamsin suka yi caa kansa kowa ya kai sara da mugun nufi sai Sammaru ya yi nutso izuwa ƙarƙashin ƙoramar ya lume a cikinta suka nemeshi suka rasa.
Cikin ƙaraji sarkin ɓarayin yace dasu suma suyi nutso
ƙasa,nan take suka bi umarni.
Ai kuwa tunda suka nutse,đayansu bai ɗago ba sai bayan gajeren lokaci sannan aka ga gawarwakinsu na tasowa sama kuma ko kaɗan babu alamar yanka ko tsini ko kaifi a sassan jikinsu.
Al'amarin da ya ƙara harzuƙa sarkin ɓarayi da yaransa kenan.
Kafin ɗayansu yayi wani yunƙuri sai ga Sammaru ya taso sama daga cikin ƙarƙashin ƙoramar riƙe da takobin ɗaya daga cikin 'yan fashin yana mai ƙaraji.
Nan fa 'yan fashin nan suka yi caa kansa gaba ɗaya wuri ya yamutse ya shiga saransu suma suna mai da martani.
Sai gashi Sammaru yana kutsawa ta cikinsu,in yaso yayi gabas ko yamma,wani lokacin kuma yayi kudu da arewa.
Amma yin hakan baisa ya sami nasaran kai guda ɗayansu ƙas ba suma kuma ɗayansu bai samu damar saransa ko sukarsa ba,nan fa aka ci gaba da artabu da ɗauki ba daɗi.
Shi dai Sammaru ya kasance mai tsananin zafin nama da jarumta su luma sun kasance masu juriya da ƙarfin damtse.
Duk da cewar yana saransu a sassan jiki jinı na zuba basu kai ƙasa ba kuma amma suma sun kasa kai shi ƙasan.
Nan fa ya zame masu alaƙaƙai suma suka zame masa alaƙaƙai.
Tofa! yau ga ƙarfi ya haɗu da naci,juriya ta haɗu da dakakkiyar zuciya kuma zafin nama ya haɗu da
yawan aiki.
Abin dai da yarima Sammaru ke gudu sai da ya faru domin sai da rana ta faɗi duhu ya soma ana wannan masifafen faɗa.
Ana cikin haka ne wata ƙatuwar inuwa ta lulluɓe filin fafatawar gaba ɗaya suka ɗaga sama,cikin kaɗuwa 'yan fashin nan suka ɗaga kawunan su sama gaba ɗaya,ai kuwa sai suka yi arba da wata ƙatuwar halitta,wannan halitta dai ba komai bace face aljani Labagaza,zaune akansa yarima
Yauhana ne da boka Karluz.
Nan take aljani Labagaza ya sauka gefe guda,Yauhana da
Karluz suka sauka daga kansa.
Koda 'yan fashin nan su kaga cewar aljani Labagaza bai taso kansu ba sai kawai suka ci gaba da kaiwa Sammaru farmaki,cikin hanzari yarima Yauhana ya kai masa ɗauki aka ci gaba da fafatawa.
Aljani Labagaza kuwa da boka Karluz sai suka zama 'yan kallo,yaƙi yayi yaƙi,gumu yai gumu kuma wahala tai wahala ya zamana gumurzun ya zama
kare jini biri jini.
Ko da ganin haka sai ran boka
Karluz ya ɓaci,kawai sai ya dubi aljani Labagaza yace gama mini da waɗannan 'yan fashi domin suna nema su ɓata mana lokaci.
Kafin Karluz ya gama rufe bakin sa Labagaza yasa yatsunsa biyar ya tsince 'yan fashin gaba
ɗayansu su dubu biyar ya mutsitsikesu cikin tafin
hannunsa.
Kawai sai ya yarfe hannun ya zubar dasu ƙasa a rugurguje tamkar an dakesu a cikin turmi.
A dai dai wannan lokacine yarima Sammaru ya dubi Yauhana da Karluz cikin ɗumbin mamaki sannan kuma ya dubi aljani Labagaza wanda babu abin da ya burgeshi da shi face tsananin girmansa da fadin tafin hannunsa,cikin yanayin mamaki Sammaru ya dubi Yauhana da kyau yayi nazarin suturar dake jikinsa ya tabbatar da cewa ɗan sarkine sai yace,
"Yakai wannan ɗan sarki wane ne kai kuma ina dalilin taimakonku a gareni?
Kafin Yauhana ya buɗe baki yace wani abu sai boka Karluz ya tari numfashinsa gami da shan gabansa sannan ya risina a gaban Sammaru ya kwashi gaisuwa yace,
"Gaisuwa a gareka ya kai yarima Sammaru 'đa' ga sarki Alyasil Buhus na birnin Sin,kayi sani cewa wannan ɗan sarkin dake gabanka yarima Yauhana kenan 'đa' ga sarki Jamshul na birnin Rum.
Ya kai Sammaru ka sani cewa bamu taimake ka don komai ba sai domin muna kan tafarki guda na buƙatar riskar boka Hulumul Makahur wanda zai samu akan turbar zuwa kogon Muddarul ikisina inda taskar tsafi take don deɓo tsumin tsafin da sarakunanmu zasu sha su warke daga muguwar cutar mutuwar rabin jiki.
Ni da
nake maka wannan bayani sunana boka Karluz,hadimi ga mutanen Rum."
Yayin da yarima Sammaru ya jı wannan jawabi sai murna ta kamashi nan take ya miƙa musu hannu suka yi musabiha yace,
"Ina murnar haɗuwa da abokan tafiya kuma abokan share hawaye tare,lallai ina mai yi muku bushara da cewar muna daf da isa wajen boka Hulumul Bakahur."
Koda jin haka sai boka Karluz yayi murmushi yace,
"Nasan da haka.
Yakai wannan ɗan sarki zaifi kyau ka rabu da dokinka anan domin mu tafi tare akan bawanmu aljani Labagaza gashi tsaye yana jiranmu."
Sammaru ya ƙarewa Labagaza kallo sama da ƙasa yace,
"Haƙiƙa kaci sunanka don tun da nake ban taba ji ko ganin aljani mai girmanka ba sai yau."
Labagaza ya ƙyalƙyale da dariya yace,
"Haba yaro ai duniyar nan da faɗi take inda kasan aljani Shamharu shahararre da baka faɗi haka ba."
Cikin mamaki Sammaru yace,
"Wane ne kuma Shamharu shahararre?"
Labagaza yace,
"Ai wannan labarine mai tsawo sai dại ka nemi littafin tarihi mai suna KUNDIN TSATSUBA a cikin sane zaka sha labarin Shamharu shaharare.
A taƙaice dai wani taƙadirin aljanine da ya gallabi duniya a zamaninsa ya zama alaƙaƙai ga komai da kowa."
Yayin da aljani Labagaza yazo nan a zancensa sai boka Karluz ya daka masa tsawa yace,
"Kai malam ba hira muka zo yi ba,maza ka đaukemu ka kaimu fadar boka Hulumur Makahur."
Cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗaya ba aljani Labagaza ya suri Sammaru,Yauhana da Karluz ya azasu a gadon bayansa har ma yayi tafiyar zango biyu,sai gasu sun iso kofar kogon tsafin boka Hulumul Makahur.
A hankali kuma a tsanake aljani Labagaza ya sauke su ƙasa.
Koda suka dubi kogon sai suka
ga ashe siffar mutumce dashi,wato mutum ne a zaune ya tanƙwashe ƙafafunsa kuma ya buɗe tafin hannayensa.
Akan tafin hannunsa na dama wata farar kwatanniyace.
Akan tafin hannun hagu kuwa jar kwatanniyace.
Boka Karluz,Sammaru da Yauhana suka ɗaga kai sama suna kallon wannan gunki cikin al'ajabi da rashin gane ma'anarsa.
Yauhana ya dubi Karluz yace,
"Shin kuwa kasan ma'anar wannan kwatanniya guda biyu?"
Karluz yai ajiyar zuciya yace, "Haba yarıma ya za'ai na sani ai munzo inda sanina bai kai ba.
Kasan ance Baba da Babansa,haka kuma malam da malaminsa,ni kam almajirine anan,neman sani nazo biɗa."
Karluz na gama faɗin
hakan suka ji an bushe da dariya.
Dariyar ta cigaba tsawon ɗan lokaci daga bisani ta ɗauke ɗif,kawai sai hannun daman mutum mutumin mai siffar kogon ya sauko ƙasa gabansu.
Bakin mutum mutumin kuma ya buɗe yace,
"Lale marhaban daku 'ya'yan sarakai ku sanya hannayenku a cikin wannan kwatanniya."
Koda jin haka sai boka Karluz ya fara kai hannunsa zai sa acikin kwatanniyar,cikin tsawa mutum mutumin yace,
"A kul kasa hannunka idan baso kake ya ruɓurɓushe ba.
Domin wannan kwatanniyace ta 'ya'yan sarakai kawai."
Cikin tsoro boka Karluz ya janye hannunsa jikinsa na karkarwa yaja da baya Yauhana da Sammaru suka sa hannayensu acikin kwantanniyar kawai sai suka zama farin haske suka ɓace.
Mutum mutumin ya sake sauko da ɗaya hannun nasa na hagu mai jar kwatanniya yace,
"Saka hannunka aciki ya kai Karluz domin wannan kwatanniya ta bokaye ce kaɗai.
Lallai babu mai shiga wannan kogo face sarakai da bokaye."
Cikin azama Karluz ya sanya hannunsa a cikin kwatanniyar take ya zama jan haske ya ɓace.
A cikin wata ƙasaitacciyar fada mai ginin dutsen jauhar ruwan ɗorawa suka tsinci kansu.
Komai dake cikin fadar akan iska yake
yawo babu wani abu dake ajiye a ƙasa.
Kai irin iskar dake kaɗawa a cikin kogon ma ba irin wacce mutum ya saba shaƙa da ji bace.
Abubuwan al'ajabi kuwa gasu nan birjik kaka-kala irin wanda idanu basu taɓa gani ba ne.
Nan fa Karluz,Yauhana da Sammaru suka zama cikakkun 'yan ƙauye kuma suka cika da al'ajabi domin su kansu yawo suke yi akan iska kuma tafiya ake yi dasu a cikin kogon ana ƙara nutsawa da su ba akai madakata ba.
Har yanzu kuma basu ga mutum ko aljan ba.
Babu komai face dabbobi iri iri daga irin halittun ruwa da kuma na jeji masu siffofin al'ajabi.
Wani lokacin sai kaga mitsitsin kifi da ƙaton kai mai girman tsauni ko kuma kaga kazar ruwa mai kawuna dubu da silin ƙafa đaya.
Haka dai suka yi ta ganin abubuwan mamaki har suka gaji da ganinsu.
Ba zato ba tsammani sai gasu acikin wata fadar dabam wacce tafi ta baya kyau da tsaruwa sau dubu.
A cikinta aljanu barkatai suna ta aiyuka iri iri na hidimar tsafi.
Komai a wannan fadar ma akan iska yake yawo har su kan su aljanun masu hidima.
Haka kuma abubuwan al'ajabin dake wajen sun ninka waɗanda ke fadar farko.
A cikin wannan fadar ne boka Karluz ya cire rawaninsa ya sake shi don ya ga abin da zai faru
Shin rawanin zai faɗo ƙasa ne,ko kuwa zai tsaya a cikin iska?
Ai kuwa yana sakin rawanin sai ya tsaya a cikin iska,kuma yayi sama ya naɗa kansa akan boka Karluz.
Take boka Hulumul Makahur ya bayyana a gabansu bisa wata karagar mulki.
A kansa akwai hular sarki ta
zinariya.
Hannunsa na hagu na riƙe da farar sandar tsafi.
Karagar zinariyar tana tafiya ne akan iska.
Yana sanye da wata doguwar jar riga.
A wuyansa akwai murjanai kimanin guda arba'in da bakwai,kuma kowanne đaya an yi shine daga abu dama,daga dangin zinare,sai lu'u'lu'u,jauhar, zubarjadi,demon,yaƙutu da dai
sauransu.
Wani abin ma ko sunansa mutum bai taɓa ji ba.
Boka Hulumul Makahur ya dubi boka Karluz yace,
"Iskar dake cikin fadar nan tamu ba irin iskar duniyar ku bace.
Wannan iska mun samo tane daga duniyar wata."
Hulumul Makahur ya waiga ya dubi yarima Sammaru da yarima Yauhana yace,
"Ina yi muku barka da zuwa fadar sarkin bokaye.
Haƙiƙa kun zo inda za'a share muku hawaye bisa babbar buƙatar dake gabanku,amma ku sani cewa za ku yi shirin nada gammo don
đaukar abin da yafi duniyar nan da abin dake cikinta nauyi."
Yayin da su Yauhana suka ji wannan batu sai hankalinsu ya tashi,gaba ɗayansu suka ƙurawa boka Hulumul Bakahur idanu,shima sai ya zuba musu ƙwala-ƙwalan idanunsa masu kama dana mujiya.
Bisa mamaki sai suka ga ya
tuntsire da dariya.
Lokaci guda ya haɗe fuska,kuma sai ga hawaye daga cikin idònsa guda.
Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin fargaba da ruɗewa kenan.
Yarima Sammaru ya dube shi cikin nutsuwa yace,
"Ya kai wannan boka ina dalilin
yin dariyarka,kuma ina dalilin yin kukanka?"
Boka Hulumul Makabur yai ajiyar zuciya yace,
"Ya kai wannan ɗan sarki kayi sani cewa yau shekarata casa'in da tara a cikin wannan kogo.
A cikin nan uwata da ubana suka yi rayuwa,ina da 'yan uwa guda bakwai dukkaninsu mata ne,nine kaɗai namiji.
Mahaifina gawurtaccen matsafi ne,ba wani abu bane ya zama sanadin aljalin mahaifina da mahaifiyata da kuma 'yan uwana face bincike akan yadda za su mallaki sirrikan tsafi guda
miliyan dubu tara da casa'in da tara,irin wanda bokanya Tazibul Luhucul ta mallaka,kuma ta
ɓoye su a cikin taskar tsafinta,wadda ke kogon Maddarul ikisina.
Sun sha ƙoƙarin zuwa kogon Muddaril ikisina,amma da sunje gaban ƙofar kogon sai shiga ta gagarasu.
Dawowa da baya ta gagara,anan suke rasa rayuwarsu.
Ɗaya bayan ɗaya da haka 'yan uwan nawa bakwai suka rasa rayukansu.
Ni kaɗai ne yanzu nayi saura. Daga tsawon lokacin mutuwar 'yar uwata ta ƙarshe,kawo iyanzu shekara arba'in kenan.
Tsawon wannan lokaci bana komai face bincike da gano yadda zan iya shiga cikin kogon Muddaril Ikisina na sato waɗannan sirikan tsafi kuma na
fito lafiya har na dawo nan cikin kogona.
Har yau kawo yanzu maganar nan da nake muku ban gano mafita ba,kuma na rantse da darajar rayukan iyayena da 'yan uwana ba zan fasa wannan aiki ba,har ajalina ya riskeni.
Wannan shine dalilin da ya sa nace daku kun naɗa gammo don shirin ɗaukar abinda yafi duniya da abinda abin cikinta nauyi domin abu ne wanda ya gagari dukkanin matsafan duniya."
Sa'adda boka Hulumul Bakahur yazo nan a zancensa,sai su yarima Sammaru suka yi ajiyar zuciya,cikin zulumi da juyayi yarima Yauhana yace,
"Ya kai wannan boka yanzu mun
gamsu cewar wannan aiki dake gabanmu gagarumine,to amma ka sani cewa har abada mai rai baya fitar da rai ga samun rabo.
Tuni mun sallama rayuwarmu bisa wannan al'amari,don haka babu gudu,babu ja da baya,walau mu dace,walau ba mu dace ba.
Yanzu muna so ka sanar damu hanyar da za mu bi mu je wannan kogo na Muddaril Ikisina,inda taskar tsafi take don ceto rayuwar iyayenmu."
Boka Hulumul Makahur yayi murmushi yace,
"Yaro man kaza,lallai inda ka san bala'in dake cikin wannan al'amari daka rungumi ƙaddara amma koda yake ance ba'a ƙwacewa yaro garma.
Zan faɗa muku matakan da za ku bi ku je wannan wuri,amma sai abokan tafiyarku sun iso."
Cikin yanayin namaki yarima Sammaru yace,
"Su wanene kuma abokan tafiyarmu?"
Boka Hulumul Makahur yace,
"Abokan tafiyarku mutum uku ne.
Akwai gimbiya Ashwarya 'yar sarki Bahacal na birmin Hindu,wadda ta kasance gagarumar jaruma mace,mai dakawa maza gumba a hannu.
Akwai yarima Lubaika 'dan' sarki Marluzil Hauras na birnin Ƙisra,sai kuma yarima Larbuz ɗan sarki Katimul Barhul na birnin Farisa,wanda shima
gwarzon mayaƙi ne,wanda yayi

2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

1 year ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment