Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata ci ta rasa.
Koda suka yi ido-da-ido sai kuran nan ta taso a guje haikan don rashin haƙuri ma har tsalle take sama tana kara dirga gaba don gani take gudun bai isheta ba. Koda Luzaiya ta yunƙura don ga miƙe tsaye ta gudu sai ta ji ƙafafunta da hannayenta a ɗaure.
Nan take hankalinta ya dugunzuma jikinta ya kama karkarwa don tsananin tsoro ba ta san sa'adda
ta ƙwala uban ihu ba.
A wannan lokaci jarumi Nazmir ya deɓo kayan itatuwa niƙi-niƙi.
Koda ya jiyo ihun gimbiya Luzaiya sai ya yi watsi da itatuwan ya kece da tsananin gudu ya nufi inda ya baro ta.
Gudu yake iya ƙarfinsa kuma irin wanda bai taɓa yi ba a rayuwarsa.
Har yanzu bai daina jiyo ihun gimbiya Luzaiya ba,al'amarin daya ƙara fusata shi kenan ya ƙara
ƙaimi.
Kafin ya iso tuni kuran nan tayi tsalle sama ta dira gaban Luzaiya.
Nan take kuwa ta kaiwa gadon bayanta cafka da hakoran bakinta.
Cikin zafin nama Luzaiya ta mirgina baya amma duk da haka sai da haƙoran kurar suka yage
rigar Luzaiya kuma suka karce fatarta jini ya tsatstsafo.
Kurar ta sake kai mata cafka a karo na biyu bisa rashin sa'a sai ta faɗa hannun jarumi Nazmir ya shaƙe wuyanta,suka kama kokawa, su faɗi nan su tashi can.
A lokacin ne gimbiya Luzaiya ta zuba musu idanu kawai zuciyarta cike da tunani kuma hawaye na zuba a idanunta tace a ranta,
"Wai shin mene ne ma dalilin da ya sa na tsorata da wannan kura?
Ashe bani ce wadda ke neman
mutuwa ba?
Ya akai na kasance mai ƙoƙarin
neman tsira?
Haba Luzaiya me kike so ki yi a
duniya alhalin baki da kowa,ba ki da komai.
Haƙiƙa kin yi kuskure da kika yi ihu har jarumi Nazmir ya kawo miki ɗauki da wuri.
In da kin yi shiru da yanzu haka kin mutu kin huta da takaicin duniya.'
Tun da jarumi Nazmir yake bai taba haɗuwa da ƙatuwar kura irin wannan ba,a duk lokutan da ya sha arangama a jeji a yayin farautarsa.
Ita dai wannan kura ta kasance mai taurin kai,ƙarfi da jajircewa.
Sai da suka shafe kusan rabin sa'a
suna gumurzu ya zamana tayi masa rauni sosai da faratan hannunta amma da zarar ta kawo
masa cizo sai ya goce ya naushi bakin nata.
Saboda ƙarfin naushin nasa sai kaga ta zube ƙasa rikica amma kuma sai ta sake miƙewa cikin zafin nama,ta afka masa.
Yayin da jarumi Nazmir ya ga kurar nan tana so ta galabaitar dashi sai ya harzuƙa zuciyarsa ta yi baƙinƙirin kawai sai ya suri ƙafafunta biyu na baya ya dagata
sama ya rinka haji-jiya da ita tamkar wanda yake wasa da majajjawa.
Bayan ya wulwulata kamar sau arba'in a sama sai ya rinka rotsa kanta akan wani dutse har saida ya ga kan ya dagwargwaje sannan ya yi jifa da gawar kurar,shima ya tsugunna ƙasa yana haki da numfashi.
A sannan ne suka haɗa idanu
shi da gimbiya Luzaiya.
Koda ya ga raunin da kurar nan ta yi mata a gadon baya sai tausayinta ya kama shi.
Cikin sauri ya miƙe ya je ya buɗe
jakarsa ya ɗauko magani ya shashshafa mata a raunin,sannan ya kwance igiyar da ya ɗaure mata hannaye da ƙafafu,ya jinginar da ita a jikin bishiya.
Kawai sai ya juya mata baya yace,
"Idan kin so kina iya yin ƙoƙarin guduwa amma ki sani ba za ki iya tsere mini ba,a cikin jejin nan,duk
inda kika shiga kika ɓuya sai na laluboki."
Yana gama faɗin hakan ya tafi ya barta a wajen cikin tunani.
"Me kike jira ne ga dama ta samu?
Walau ki gudu ko kuma ki sami wani icen ki tsire cikinki ki mutu. Ko kya huta da baƙin cikin rayuwa."
Zuciyar Luzaiya ce ta saƙa mata waɗannan maganganu.
"Me yasa na rayu har na kawo i
yanzu?
Lallai akwai wani dalili a ƙarƙashin
wannan sanadi.
Zai fi kyau na tsahirta dan naga wannan dalili da idanuna tunda dai nayi iyakar ƙoƙarina akan na ga na halaka kaina,amma abu ya faskara.
Duk da kasancewar ban yi imani da
ɗaya daga cikin irin addinan zamani ba babu mamaki wani Ubangijin ne yake tsara rayuwata
saboda wani ɓoyayyen dalilin."
Luzaiya na cikin wannan tunani ne jarumi Nazmir ya dawo ɗauke da itatuwa.
Shi kansa yayi mamaki da ya iske ta har yanzu a zaune a inda ya barta,kuma hawaye bai daina zuba a idanunta ba.
Ban da karkarwar ɗari babu abinda take yi.
Nan da nan ya zube icen a gabanta
ya kunna musu wuta,sannan ya sake buɗe jakarsa ya fiddo wata riga wadda aka yi ta fatar damisa ya lulluɓawa gimbiya Luzaiya.
Shi kuwa dogon wando ne kaɗai a jikinsa na fatar zaki.
Nazmir ya zauna tsallaken wutar suna masu fuskantar juna.
Tsawon daƙiƙa biyar wurin yayi
tsit baka jin komai face kukan tsuntsaye da kuma kukan manyan namun dawa,da ke can nesa.
Nazmir ya katse shirun da cewa, "Me yasa ba ki yi ƙoƙarin guduwa ba sa'adda na kwance ki na tafi nemo itatuwa?"
Ba tare da ta ɗago kai ta dube shi ba,tace,
"Guduwa ta ba ta da wani amfani ko tasiri,domin na rigaya nayi kusure tunda har na yi ihu ka kawo mini agaji sa'adda kura ta afka mini."
Nazmir ya yi ɗan guntun murmushi sannan ya janyo maganin nan da ya shafa mata a rauni ya fara shafawa a nasa raunikan.
"Bai kamata ki yi ƙoƙarin kashe kanki ba,saboda baƙin cikin rashin mahaifinki,mulkinki da danginki,ki tuna cewa mai rai baya fitar da rabo,za ki iya sake saduwa da mahaifiyarki nan gaba,shin ba kya tunanin irin ɓacin ran da mahaifiyarki zata shiga idan ta sami labarin mutuwarki,ki sani cewa idan na kai ki ga sarkina ya aureki zaki ci gaba da rayuwa ne cikin tsananin jin daɗi da walwala."
Koda jin haka sai ta dubi jarumi Nazmir cikin ƙunar zuci tace,
"Shin jin daɗi da walwala zasu iya maishe da gurbin abokanka waɗanda ka rasa a wannan yaki da ka yi?"
Koda jin wannan tambaya sai idanun Nazmir suka ciko da ƙwalla,jikinsa yayi sanyi gaba ɗaya ya kasa cewa komai.
Luzaiya ta ci gaba da cewa,
"Babu wani farin ciki da zai iya gusar mini da đacin zuciyar da nake ji sakamakon kisan gillar da kuka yiwa mahaifina.
Ka yi sani cewa a duk sa'adda na dubi abokinka na kan ji kamar ana sukan zuciyata da tsinin masu. Inda zan kashe shi na yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsa izuwa sala-sala,mini-mini yadda tsuntsun kanari zai iya tsinta da bakinsa ya ci ba zan huce takaicin zuciyata ba.
Bani da wani masoyi a duniya wanda yafi ubana.
Na rayu a cikin ƙaunarsa,da begensa dare da rana,kuma cikinta zan mutu."
Sa'adda Luzaiya tazo nan a zancenta sai ta fashe da kuka.
Tausayi ya kara turnuke Nazmir yace,
"Na san har abada ba za ki iya yi mana afuwa ba,wato ni da abokaina amma ki sani bamu kashe mahaifinki don buƙatar kanmu ba sai don mu ceto rayuwarmu da kuma farin cikin iyayenmu.
Kowanne 'ɗa' na gari ba shi da wani buri wanda yafi na nunawa iyayensa tsantsar ƙauna kamar yadda suka nuna masa tun yana ƙarami kawo izuwa girmansa.
Tsantsar ƙaunar da nake yiwa mahaifina ce tasa na fito wannan
yaƙi,amma ba wai don tsoro da bin umarnin sarkina ba.
Hasalima a duniya babu mutumin dana tsana fiye da sarkin garinmu saboda zaluncinsa da rashin tausayinsa ga talakawa."
Koda gimbiya Luzaiya ta ji wannan batu daga bakin jarumi Nazmir sai ta cika da mamaki tayi shiru ba ta ce komai ba.
Daga can kuma sai ta dube shi tace,
"Ya kai wannan jarumi ina son nayi maka wata tambaya idan har ba za ka sami damuwa ba?"
Nazmir yace,
"Faɗi tambayarki in dai ina da
amsarta zan sanar da ke."
"Shin za ka iya gaya mini dalilin da ya sa mahaifina yace idan ya bari aka kashe ku ya ci amana?
Mene ne dalilin da ya sa ya kawo kansa gareku har ya umarce ka da ka sare kansa kuma ka kamani ka tafi da ni?
Kayi sani cewa zuciyata ta daɗe tana damuwar akan wannan al'amari,kuma ta shiga cikin bakin duhu babu mai fito da ita izuwa cikin hasken fahimta face kai."
Sa'adda gimbiya Luzaiya ta zo nan a zancenta sai jarumi Nazmir ya yi ajiyar zuciya yace,
"Ba komai ne ya sa mahaifinki ya yi haka ba sai don ya sakawa mahaifina abin da alherin da ya taɓa yi masa a baya kimanin shekaru da suka gabata."
Nan take jarumi Nazmir ya kwashe labarin abinda ya faru tsakanin sadauki Halufa da sarki Fahalul Bahafus ya zaiyane mata.
Koda ya ƙare labarin sai ta fashe da kuka tana mai cewa,
"Haƙiƙa mahaifinka masoyi ne a gareni da mahaifina lallai kai ba abokin gabata bane,domin ba don darajar mahaifinka ba da na girma
a cikin maraici.
Haƙiƙa mahaifina ya riƙe amana
kuma ya tabbatar da alƙawari.
Ya kai Nazmir kayi sani cewa daga yau na rungumi ƙaddara,kuma zan kasance mai bin umarninka har mu
isa ƙasarku ka danƙani a hannun sarkinku,domin yin hakan a gareni shi ne cikar riƙe amanar da ke tsakanin mahaifina da
mahaifinka.
Lallai kun yi halacci a garemu,lokaci yayi da zamu saka muku,ina mai roƙonka da ka yafe mini kura-kuran da na yi maka a baya."
Nazmir yayi murmushi yace,
"Ai duk abin da kika yi mini banga laifin ki ba,domin kin yi ne don sanin martabar mahaifinki."
Haka dai Nazmir da gimbiya Luzaiya suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai,ya umarce ta da yin barci,shi kuma yayi gadin lafiyarsu.
Koda jin haka sai ta miƙe tsam ta dawo inda yake ta kwanta tana mai ɗora kanta akan cinyarsa tace,
"Yanzu hankalina ya kwanta da kai na san cewa har abada ba zaka cutar da ni ba,domin kai masoyi ne ba maƙiyi ba."
A iya rayuwar jarumi Nazmir mace ba ta taɓa kusantar sa ba,irin yau sai dai a larura ko a wajen yaƙi.
Don haka lokacin da gimbiya Luzaiya ta ɗora kanta akan cinyarsa,sai gaba ɗayan tsigar jikinsa ta tashi,ya ji kamar ya ture
ta,amma da ya tuna cewar 'yar sarki ce fa mai mulki,kuma wadda ke cikin baƙin cikin rayuwa mai matuƙar buƙatar nutsuwa da kwanciyar hankali sai ya ƙyaleta.
Yayin da asuba ta fara gabatowa sai Luzaiya ta farka daga barci ta roƙi Nazmir da ya kwanta don shi ma ya dan rintsa. Nazmir yace,
"Ai gari ya kusan wayewa don haka kaima sai ka kwanta ba."
Nan fa gardama ta ƙarke a tsakaninsu da ƙyar ta shawo kansa ya amince ya kwanta,ita kuma ta ci gaba da tsaron lafiyarsu.
Luzaiya bata tashi Nazmir daga bacci ba sai da ta gari ya waye
sosai,rana ta ƙwale.
Koda farkawarsa kuwa yaga ashe gari ya daɗe da wayewa sai ya dubi
Luzaiya yace,
"Ya gimbiya me ya sa kika barni ina ta barci har tsawon lokaci haka?"
Yayin da Luzaiya ta ji wannan tambaya sai tayi murmushi tace,
"Saboda kaima ka bani dama na samu isasshen barci,kuma nasan cewa akwai bashin barci mai yawa a tare da kai,idan ba ka yi ba zaka iya samun matsala a lafiyar ka."
Wannan batu ba ƙaramin bashi mamaki ya yi ba,domin shi a tunaninsa bai ga dalilin da zai sa ta
damu da lafiyarsa ba.
Nazmir ya miƙe tsaye ya ɗauki kwari da bakansa da kuma takobinsa ya gyara musu zama a jikinsa.
Koda ganin haka sai Luzaiya ta dube shi cikin damuwa tace,
"Ina kuma zaka je?"
Nazmir ya maida mata murmushi yace,
"Zan je ne nayi farautar abin kalaci."
"Ai kuwa sai dai mu tafi tare, don ba zan yarda ka barni ni kaɗai ba a wannan mugun dajin."
Wannan batu ba ƙaramin mamaki ya baiwa jarumi Nazmir ba,domin a tunaninsa Luzaiya bata kasance matsoraciya ba,in da kuwa matsoraciya ce ai ba za ta hau doki ba,ta yiwa mayaƙa jagora a lokacin nan da ake gumurzun yaƙi tsakanin su Nazmir da baraden mahaifinta.
Jarumi Nazmir ya dubi gimbiya Luzaiya ya ƙyalƙyale da dariya yace,
"Haba ranki ya daɗe ai ni zatona ke jaruma ce daga cikin mata,ya kuma kike nuna gazawarki a fili haka?"
Luzaiya tayi murmushi tace,
"Ai ido ba mudu bane,amma ya san ƙima.
Tabbas ko kaɗan ban yi kama da jaruma ba,haka kuma ba ni da sura
irinta jarumai."
Ba tare da ɓata wani lokaci ba jarumi Nazmir ya nausa cikin jeji yana mai sauri-sauri, gudu-gudu.
Luzaiya ta bishi a baya duk in da ya ɗauke sawunsa sai tasa na ta,ko kaɗan bata yarda ya bata tazara ba.
Suna cikin dube-dube ne a jejin Nazmir ya hango wata barewa.
Ai kuwa yana ganinta ya ɗana baka akan kwari ya sai tata.
Koda ya saki bakar sai barewar ta ruga cikin dawa,kibiyar ta wuce ta saman kanta.
Koda ganin haka sai Nazmir ya bi barewar da gudu,itama Luzaiya sai
ta bi shi a guje iya ƙarfinta,don kada ya ɓace mata.
Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan gudu basu cimma barewar ba,ita kuma barewar bata ɓace musu ba.
Ya zamana Luzaiya ta jigata ainun sai haki take,kuma tana sassarfa kamar za ta fadi ƙasa,amma sai ta
jure.
Koda suka iso kan wani ƙaton dutse sai barewar nan ta fara ƙoƙarin isa karshen dutsen.
Anan ne jarumi Nazmir ya tsaya ya zaro kibiya guda ɗaya daga cikin kuttun kibbau ya aza akan bakar, sannan ya ja ya taɓe yana mai saita barewar nan.
Yayin da ya gama taɓewa da saitawa iya ƙarfinsa da iyawarsa sai ya saki kibiyar.
Cikin tsananin gudu da ƙarfi kibiyar ta tafi ta caki gadon bayan
barewar ta faso ta cikinta ta ɓulla waje.
Take barewar nan ta fadi ƙasa matacciya.
A sannan ne Nazmir ya waiga bayansa ya yi arba da gimbiya Luzaiya wacce ta zauna dirshan tana kallon abin da ke faruwa cikin nuna al'ajabi.
Nazmir yayi murmushi a gareta, itama ta yi masa fuskarta na nuna yabawa bisa jarumtakarsa.
Kawai sai Nazmir ya nufi inda wannan barewa ke kwance da nufin ya ɗaukota.
Ba zato ba tsammani sai ya gansu suna saukowa ƙasa daga saman wannan dutse.
Ba wasu ba ne face Bardil,Bagwan da kuma sauran baradan nan abokan tafiyarsa.
Koda su Bardil suka yi arba da jarumi Nazmir,kuma suka ga gimbiya Luzaiya a bayansa sai suka cika da tsananin farin ciki.
Nan take suka rugo gare shi shima ya ruga garesu take aka rungume juna,cikin murna mara misaltuwa.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka ɗauko barewar nan aka sauko daga kan dutsen.
Nan dai aka gasa barewa kowa ya yi kalaci,sannan aka shiga hira inda jarumi Nazmir ya baiwa su Bardil
labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu.
Al'amarin da ya ƙara jefa su cikin
matuƙar al'ajabi kenan.
Bayan nan sai Bagwan ya yi gyaran murya yace,
"Yakai abokina kayi sani cewa bayan rabuwarmu daku muma mun sha baƙar wahala sakamakon gamuwa da muggan namun jeji da
kuma nau'i-nau'in 'yan fashi,amma duk sai da muka fatattake su muka tarwatsa su.
A haƙiƙanin gaskiya bamu taɓa tsammanin zamu sake saduwa da ku ba,domin mun zata kai da ita duk kun hallaka a lokacin da kuka faɗo ƙarƙashin tsaunin nan mai kwazazzabo.
Tuni mun yankewa kanmu hukunci cewar ba zamu koma can ƙasar mu ba,muddin bamu ganku ba sai dai mu ci gaba da rayuwa a cikin jejin nan har ajalin mu ya riskemu, domin mun san cewa idan muka koma ba tare da biyan buƙatar sarki ba gaba ɗayanmu mun zama gawa."
Koda jarumi Nazmir ya ji wannan jawabi sai yayi ajiyar zuciya,sannan ya dubi Bardil da Bagwan yace,
"Ya ku abokaina ku yi sani cewa tabbas na ji a jikina cewa ɗayanmu ba zai sake mutuwa ba,har sai mun isa gida lafiya,tare da biyan buƙatar sarki sai dai baƙin cikin rabuwa da
abokanmu shi ne babban abin damuwarmu."
Yayin da jarumi Nazmir ya fadi haka sai idanun Bardil da Bagwan suka ciko da ƙwalla suka kama kuka,shima sai ya taya su.
Al'amarin da ya sa gimbiya Luzaiya ma ta tuno da mahaifinta,mahaifiyarta da kuma ƙasarsu kenan.
Itama dai bata san sa'adda ta fara zubar da hawaye ba,don haka sai ta miƙe ta koma gefe guda ta zauna ta ci gaba da kukanta.
Su kuwa sauran barada sai suka kamu da tausayi suka yi shiru da zugum cikin juyayi.
Nazmir ya kama hannun Bardil da Bagwan ya jasu izuwa gefe guda suka keɓe,sannan ya dube su ɗaya bayan ɗaya sa'adda yake goge hawayen idanunsa, yace,
"Yaku abokaina ku yi sani cewa jikina yayi sanyi,haka kuma zuciyata na bugawa ma'ana ina jin tsoro da faɗuwar gaba bisa abin da zai faru garemu bayan mun isa gida.
Jikina yana bani cewar akwai wani
mugun abu da zai faru a garemu dangane da sakaiyar azzalumin sarkinmu zai yi mana domin halinsa ne ya cutar da talakawansa waɗanda suka kyautata a gare shi."
Yayin da Bardil da Bagwan suka ji wannan batu sai duk hankalinsu ya tashi suka shiga tunani.
Nazmir ya katse tunanin nasu da cewa, ni kam a yanzu tausayin gimbiya Luzaiya ya shigeni har ina jin cewa kamar bazan iya danƙata ba a hannun azzalumin sarkinmu, to amma fa idan nayi tunani sai na ga cewa ba mu wata mafita don haka dole ne na miƙata in ba haka ba kuwa rayuwarmu da ta iyayenmu na cikin haɗari.
Yanzu ku mece ce shawararku bisa abin da kuke ganin zai fishshe mu?"
Lokacin da Bardil da Bagwan suka ji wannan tambaya sai hankalinsu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe duk suka yi shiru suna juya
al'amarin cikin zukatansu.
Bayan dogon nazari sai Bardil ya ɗago kai ya dubi jarumi Nazmir yace,
"Ya kai abokina haƙiƙa maganarka abin dubawa ce matuƙa,to amma ka yi sani cewa yanke hukunci a garemu yanzu yafi komai haɗari.
Ni a tunanina zai fi kyau mu bari mu isa gida in ya so sai mu yanke shawara bayan mun miƙa gimbiya ga sarki."
Koda jin haka sai Bagwan yace,
"Ƙwarai kuwa wannan shine abin da yafi cancanta a garemu."
Da wannan shawara aka yi amfani.
Wato daga wannan rana su jarumi Nazmir suka ci gaba da tafiya ba dare ba rana,sai dai kawai idan sun
gaji su yada zango.
Bayan wata da watanni ne suka iso ƙasarsu.
Yayin da suka iso bayan gari dare ya raba,don haka sai suka tsaya suna shawarwari akan shiga gari yanzu ko kuwa su bari sai gari ya waye?
Koda mahawara tayi yawa a tsakaninsu sai jarumi Nazmir yace,
"Wai shin wane ne shugaba a cikin tafiyar nan tamu?"
Bardil da Bagwan suka ce,
"Kai ne shugaba ya jarumin jarumai."
Nazmir yayi murmushi yace,
"Tunda haka ne ni yanzu nake son mu shiga cikin garin,kuma ba zamu shiga ba sai mun ɓatar da kamanninmu domin mu san sirrin abin da gari ke ciki,don kada mu faɗa cikin tarkon sarki.
Kamar yadda kuka sani cewar marigayi mahaifin gimbiya Luzaiya ya roƙeni da na fara nuna kansa ga
mahaifina tare da yi masa bayanin cewar ya sallama rayuwarsa don ceto tawa.
Don haka idan muka shiga cikin gari babu inda zamu fara zuwa face gidanmu don riskar mahaifina.
In yaso da safe sai mu tafi gidan sarki mu miƙa masa gimbiya Luzaiya."
Yayin da jarumi Nazmir ya zo nan a zancensa sai gimbiya Luzaiya ta dube shi idanunta cike da hawaye tace,
"Yanzu da hannunka zaka danƙani a hannun azzalumin sarki wanda ya zamo sanadiyar mutuwar abokanku,waɗanda kuka shaƙu ainun tun yarinta?
Ka tuna fa cewa a sanadin wannan azzalumin sarki ne mahaifina ya mutu,kuma a sanadinsa ne aka yi asarar dubannan rayuka, kuma a sanadinsa ne kuka rabu da iyayenku da danginku tsawon lokaci,kuka jefa kanku cikin muguwar rayuwa mai mugun haɗari.
Nikam da dai na zama matar wannan sarki gwara na mutu tsuntsaye su cinye gawata,ya zamana an mance da tarihina a duniya har abada."
Lokacin da gimbiya Luzaiya tazo nan a zancenta sai hankalin su jarumi Nazmir ya tashi,suka yi shiru cikin matuƙar damuwa da kokwanto.
Bayan ɗan gajeran tunani,sai jarumi Nazmir ya dafa kafaɗunta a karo na farko tun haɗuwarsu,suka tsurawa juna ido yace,
"Yake gimbiya,sarauniyar kyawawan duniya ki kwantar da hankalinki ki sani cewa ni jarumi
Nazmir na yi miki alƙawari cewar har abada ba zan bar rayuwarki ba a cikin ƙunci da baƙin ciki,lallai zan kuɓutar dake,kuma na mayar da ke
kasarku don ki sadu da mahaifiyarki ki ci gaba da rayuwarki ta sarauta,kamar da a cikin ƙasarki ta haihuwa."
Koda jin haka sai gimbiya Luzaiya tayi murmushin yaƙe sannan tace,
"Duk wannan ba zai burgeni ba face ka hana faruwar aure a
tsakanina da azzalumin sarkinku."
Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba, domin ya san cewa shi kam bai isa ya hana wannan aure ba.
Yayin da Luzaiya ta ga jarumi Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba sai zuciyarta ta karaya ta cigaba da zubar da hawaye tace,
"Shi kenan kuyi duk yadda kuka so, amma ku sani cewa na gama yanke shawara cewa lallai a ranar da aka ɗaura aurena da sarki zan kashe kaina."
Daga wannan furuci Luzaiya ta tsuke bakinta bata ƙara cewa komai ba.
Kawai sai ta koma gefe guda ta ci gaba da kuka abinta.
Nan fa su jarumi Nazmir suka shiga cikin sabon tsahon hankali da matuƙar damuwa,sai da suka shafe rabin sa'a suna masu tunanin mafita,amma babu.
Kawai sai jarumi Nazmir ya bada umarnin kowa ya sauya kamaninsa.
Nan take aka bi umarnin.
Ita kanta gimbiya Luzaiya sai da aka ɓatar da kamanninta duk da
tsananin kyawun nan nata ya dishashe aka mai da ita mummunar gaske.
Bayan an gama wannan shiri ne suka hawa dawakansu suka nufi ƙofar gari.
Da zuwa suka ƙwanƙwasa ƙofar,maigadi ya leƙo ta cikin wata mitsitsiyar taga ya dube su yace,
"Su waye ku?kuma daga ina kuka fito,har da kuke ƙoƙarin shigowar a tsakiyar dare haka?"
Jarumi Nazmir ya make muryarsa yace,
"Mu manzanni ne daga ƙasar Maskur mun zo da saƙo na musamman ga sarki daga hannun
sarkinmu."
Koda jin haka sai maigadin ya rufe wannan mitsitsiyar taga.
Jim kaɗan sai suka ji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar gaba ɗaya.
Ita dai wannan kofar shiga gari ta kasance ƙatuwar gaske,domin tsawonta ya kai kamu ɗari shida haka kuma faɗinta ya kai kamu ɗari bakwai.
An yi ta ne da zunzurutun ƙarfe mai kauri da nauyin tsiya.
Mutum arba'in ne ke buɗe ƙofar waɗanda suka kasance ƙarti majiya ƙarfi.
Bayan an gama buɗe ƙofar sai su jarumi Nazmir suka ga dakaru sama da mutum dubu ɗari a tsaitsaye bisa dawakai sun yi sahu a gabansu,kuma gaba ɗayansu cikin shirin yaƙi suke.
Ba a bar jarumi Nazmir sun wuce ba sai da aka kawo fitila aka haske fuskokinsu aka yi nazarinsu sosai.
Bayan hakan ma sai aka haɗa su da wasu dakarun mutum hamsin don su wuce dasu kai tsaye izuwa gidan sarki.
Yayin tafiya gidan sarki ne zuciyar jarumi Nazmir da ta abokan tafiyarsa ta cika da mamaki domin
ba su san dalilin wannan tsatstsauran matakin tsaro ba da aka ɗauka a garin.
Haka kuma sai suka kasance cikin fargaba,domin idan suka bari aka kai su gidan sarki kai tsaye an tarwatsa shirinsu gaba ɗaya.
Nan fa suka fara tunani da saƙe-saƙen zuci.
Dabara dai bata faɗo musu ba,har suka shigo wata siririyar hanya matsatstsiya.
Sai da suka zo tsakiyar hanyar sannan jarumi Nazmir ya dubi Bardil da Bagwan ya yi musu wata irin inkiya,suma sai suka yiwa sauran baradensu.
Cikin gaggawa Nazmir,Bardil, Bagwan da baradensu suka zare takubba suka afkawa waɗannan
barade hamsin masu yi musu rakiya izuwa gidan sarki.
Cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗari da ashirin ba,suka karkashe su gaba ɗayansu ba wanda ya tsira.
Nan da nan suka kwashe gawarwakin suka jefa cikin wata tsohuwar rijiya wacce babu ruwa a
cikinta suka rufe,sannan suka sauya hanya suka nufi gidan mahaifin jarumi Nazmir wato sadauki Halufa.
Abin ka da 'yan gari duk inda suka bullo suka ga dakarun tsaro sai su sauya hanya.
Haka dai suka ta kauce-kauce da raɓe-raɓe har suka iso gidan sadauki Halufa ba tare da wani ya gansu ba.
Koda suka hango gidan a kulle kuma suka ga dakarun sarki a kofar gidan a tsaitsaye suna kai-komo sai suka laɓe suka tsaya suna mamaki.
Jarumi Nazmir ya dubi su Bardil yace,
"Yaku abokaina ku yi sani cewa ruwa baya tsami banza.
Lallai akwai wani mugun abun da
wannan azzalumin sarki namu ya shirya a kanmu.
Yanzu mene ne abin yi?"
Bardil yayi gajeran tunani,sannan yace,
"Bai kamata mu yi komai ba face mun gano abin da aka shirya a kanmu,ina ganin zai fi kyau mu je
gidana da kuma gidan Bagwan don muga halin da suke ciki tun da mun ga halin da gidanku ke ciki.
Ba tare da wata gardama ba suka tafi gidajen biyu.
Abin da suka gani a gidan su jarumi Nazmir shi suka gani a gidan su Bardil da Bagwan.
Nan fa hankalinsu ya dugunzuma
ainun suka rasa abin da zasu yi.
Daga can sai dabara ta faɗo musu suka haura gidan wani maƙocin Bagwan wanda ya kasance tsoho ɗan shekara tamanin da huɗu ana kiransa Hamlabi.
Lokacin da suka shiga,Hamlabi na ta sharar barci har da munshari kai ka ce wata dabbar ce ke gurnani.
Sai da suka zo kansa suka tsaya bai sani ba.
Nan take Bagwan ya bugi tulelen

2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

1 year ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment