Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin Hamlabi mai kama da kwarya.
Hamlabi ya farka a firgice.
Koda yaga zarata a gaban sa riƙe da takubba tsirara,sai ya taƙarƙare zai ƙwalla ihu.
Cikin sauri Bagwan ya toshe masa baki da hannu yace,
"Kada kayi ihu ya kai Hamlabi kayi sani cewa nine Bagwan maƙocinka, waɗannan kuwa su jarumi Nazmir ne abokaina da kuma sauran dakarun nan waɗanda sarki ya haɗamu da su don zuwa dauko gimbiya Luzaiya a can ƙasarsu."
Koda jin wannan batu sai jikin Hamlabi ya kama karkarwa alamun tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarsa.
Cikin sanyin jiki Hamlabi ya miƙe
tsaye ya je ya dauko fitila,sannan ya zauna ya dubi Bagwan yace,
"Yakai maƙocina ya ya akai kamanninka suka sauya haka gaba ɗaya?
Na rantse da darajar tsufana ko kaɗan fuskarka ba ta yi kama da ta makocina Bagwan ba,haka kuma suma waɗannan abokan tafiyar taka basu yi kama da su jarumi Nazmir ba,amma kuma gaskiya na ji cewar muryarka na nan kamar
yadda na santa."
Koda jin wannan batu sai Bagwan ya yi murmushi,nan take ya ɗebi ruwa ya wanke fuskar tasa,sai ga kamanninsa sun bayyana ƙarara.
Al'amarin da ya jefa tsoho Hamlabi cikin matuƙar mamaki kenan,ya buɗe baki galala yana kallonsa.
Daga can kuma sai yayi ajiyar zuciya ya dubi Bagwan ya ce,
"Haƙiƙa kun yi babbar hikima,in ba don kun ɓatar da kamaninku ba da tuni yanzu kun daɗe da zama gawarwaki."
Koda jin haka sai mamaki ya kama su Bagwan.
Nazmir yace,
"Yakai wannan tsoho wai shin meke faruwa ne?
Ka sani cewa mun je gidajenmu mun iske su a kulle,kuma dakarun
sarki na gadinsu."
Yayin da tsoho Hamlabi ya ji wannan tambaya sai ya gyara zama gami da gyaran murya,kuma
ya saita muryarsa tasa ƙasa-ƙasa yace,
"Bayan tafiyar ku izuwa birnin su gimbiya Luzaiya wani hatsabibin boka ya bayyana a ƙasar nan, kuma ya nunawa sarki duk abin da ya faru gareku a cikin wani madubin tsafi.
Duk yaƙin da kuka yi har da yadda mahaifin gimbiya Luzaiya ya sallama kansa gareku,ku ka sare kansa,ku ka taho mun gani a wannan madubin tsafin.
Kai na taƙaice muku labari dai har lokacin da gimbiya ta faɗa ƙasan tsaunin nan don kashe kanta jarumi Nazmir ya bita kawo izuwa haɗuwarku akan dutsen nan inda Nazmir ya harbe barewa duk kowa a garin nan ya gani a cikin madubin
tsafin can a fadar sarki.
Bayan an gama ganin hakan ne boka Sharmadu ya sanar da sarki
cewa kada ya kuskura ya bar iyayenku daku a raye.
Muddin yayi haka kuwa har abada ba zai auri gimbiya Luzaiya ba, kuma ku ne zaku zama sanadiyar ajalinsa.
A dalilin haka ne sarki ya sa aka kamo iyayenku gaba ɗaya aka kai su cikin turakarsa aka ɗaɗɗauresu da sarƙoƙi,yanzu haka ana jira ne
ku iso a kamaku a hada da su a kashe ku lokaci guda dan haka dokar boka Sharmadu ta kasance.
Bisa wannan dalili ne na yi mamaki
matuƙa da na ganku a cikin gidana don nasan cewa an saka matakan tsaro masu tsauri akanku,wai shin ma ya akai kuka shigo nan ba
tare da an kama ku ba?
Ina mai yi muku ta'aziya bisa rashin abokanan ku,kuma masoyanku waɗanda kuka taso tare tun yarinta."
Sa'adda tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka ciko da ƙwalla,domin tausayin su jarumi Nazmir ne ya turnuke shi.
Jarumi Nazmir ya dafa kafaɗar tsoho Hamlabi yace,
"Yakai wannan tsoho haƙiƙa ka
taimakemu da ka sanar damu halin da ake ciki.
Yanzu wacce irin shawara zaka bamu domin mu tsira da rayuwarmu da kuma rayuwar
danginmu?"
Tsoho Hamlabi yayi shiru bai ce komai ba yana tunani.
Nan take Bagwan ya shiga tunanin
matarsa Muslaiya,wacce ya tafi ya bari da tsohon ciki wadda a halin yanzu bai san halin da take ciki ba.
Shi kuwa Bardil sai ya shiga nasa
tunani.
Jarumi Nazmir ya katse musu tunani da cewa,
"Ba mu da isasshen lokaci na tunani mai zurfi.
Ya kai tsoho Hamlabi me zaka iya cewa damu yanzu?"
Hamlabi ya yi ajiyar zuciya yace,
"Shawarar da zan ba ku guda daya ce kacal.
Lallai kada ku je gidan sarki sai kun tabbata kun fara zuwa ɗakin bauta inda boka Sharmadu yake kun riske shi kun kashe shi.
Muddin yana raye ba za ku iya
kuɓutar da iyayenku da danginku ba daga gidan sarki.
Ku yi sani cewa kashe boka Sharmadu daidai yake da neman jaki mai ƙaho.
Babu wani abu da zan iya sake fada muku face na yi muku fatan samun nasara,kuma ina roƙo a gareku daku hanzarta barin gidana don kada ku shafa mini kashin kaji."
Yayin da tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa,sai su jarumi Nazmir suka yi tsuru-tsuru suka hau duban juna.
Bardil ya yi ajiyar zuciya ya ce,
"Haƙiƙa anan nahiyar bamu san irin ƙarfin bokaye ba,amma ga yadda nake samun labarinsu sun kasance ababan tsoro.
Kai an ce ma idan boka ya bunkasa yana zama ubangijin mutanensa,saboda tsananin tsoro da girmamawa a gare shi.
Ashe kuwa faɗa irin waɗannan mutane ba ƙaramin bala'i ba ne."
Koda jin haka sai jarumi Nazmir yace,
"Ai kuwa komai bala'insa ba zamu kasa tunkararsa ba.
Ai dama yanzu haka rayuwarmu na cikin ɗaya-biyu.
Kodai mu mutu ko kuma mu rayu.
Tsakaninmu da sarki sai gaba,sai yaƙi.
Ko dai yaga bayanmu ko mu ga bayansa.
Ku tashi mu tafi ɗakin bauta don mu riski wannan shegen,tsinannen boka mu fara ƙaddamar dashi, sannan mu tunkari gidan sarki. Gimbiya Luzaiya kuma ba zamu
bayar da ita ba face ɗayanmu baya numfashi a doron kasa."
Jarumi Nazmir ya ɗaga takobinsa sama ya ce,
"Waye zai bi bayana?"
Take Bagwan da Bardil suka ɗaga nasu takubban suka kara a jikin takobin Nazmir.
Cikin haɗin baki suka ce,
"Muna tare da kai,komai wuya, komai dadi,mutuwa ce kaɗai zata raba mu."
Sa'adda sauran baradan suka ga haka sai suma suka ɗaga nasu takubban suka yi iƙirarin abinda su Bardil suka yi.
Nan take jarumi Nazmir ya wuce gaba ya kama katanga ya haura.
Bardil,Bagwan,Luzaiya da sauran baradan suka yi yadda ya yi.
Sannu a hankali su jarumi Nazmir suka yi ta kutsawa cikin gari,suna masu laɓe-laɓe su shiga nan,su fita can,har suka sami nasarar shiga cikin ɗakin bauta inda boka Sharmadu yake.
Da shigarsu suka hau yin sanɗa da laɓe-laɓe,suna duddubawa don su yi masa kwaf ɗaya.
Sai da suka duba ko'ina a cikin ɗakin bautar,amma ko ƙuda ba su gani ba.
Al'amarin da ya fusata su kenan, kuma hankalinsu ya yi mummunan tashi.
Ba zato,ba tsammani kuma sai suka ji an bushe da dariya.
Dariyar ta cika ɗakin bautar gaba daya, babu dadin ji.
Cikin fushi da kakkausar zuciya jarumi Nazmir yayi tsawa yace,
"Yakai baƙin la'ananne in ka isa namiji ka fito fili mu yi gaba da gaba.
Ai ba a san maza da ɓuya ba.
Na rantse da darajar iyayena muddin za mu yi fito na fito sai na kai ka kushewa."
Koda gama faɗin hakan sai aka sake bushewa da dariya.
Lokaci guda kuma dariyar ta ɗauke,sai ga boka Sharmadu ya bayyana a tsakiyarsu jarumi Nazmir riƙe da wata isgar tsafi wadda aka yi da jelar zaki.
Boka Sharmadu ya kasance matashi,ɗan kimanin shekara talatin da bakwai.
Garjejen ƙato ne,mai ƙirar sadauki. Hannayensa biyu a cike suke da layu.
A ƙugunsa akwai wani gurun tsafi
ja,babu takalmi a ƙafarsa.
A kansa babu gashi ko sili da ɗaya, kuma a aske yake ban da sheƙin salsal babu abin da kan ke yi.
Idanunsa manya-manya ne,kuma ƙwala-ƙwala ababan tsoro.
Bashi da gemu ko saje sai wani murtukeken gashin baki tamkar tsumma aka nannada masa.
Yana da ƙaton hanci,mai faɗin ƙofofi.
Bakinsa kuwa wangameme ne, cike da wargatsatstsun haƙora marasa kyan gani.
Kai duk inda ake neman mummuna da an ga boka Sharmadu an gama neman,don shi ne ƙarshen muhawara.
Sharmadu ya dubi jarumi Nazmir yace,
"Kai samari iya bakinka kada kuruciya ta dubeka,ta ɗebe ka,ta jefa ka cikin bakin kura ka halaka a
banza.
Ka yi sani cewa nine boka Sharmadu shiryayyen da ya shirya tun masu neman shiri basu farka daga barci ba.
Nine dodan mazajen duniya,kuma nine sa gudu maganu ƙi gudu.
Nine ɗaya tamkar dubu."
Nazmir ya sake daka masa tsawa yace,
"Ƙarya kake ƙaramin barde yau ka hadu da gwarzo,ɗaya maganin gwarzaye dubu.
Yau sai takobina ta sha jininka sannan ta je ta sha jinin mai gidanka,wannan azzalumin sarkin wanda ya daɗe yana cutar da iyayenmu da sauran talakawa."
Koda jin wannan batu sai boka Sharmadu ya turɓune fuska, muninsa ya ƙaru kamar an shaƙe
alade.
Kafin wani daga cikin su Nazmir ya yi wani yunƙuri tuni Sharmadu ya nuna jarumi Nazmir da wannan isgar tsafi da ke hannunsa,kawai sai wata irin iska mai ƙarfi ta ɗaga Nazmir sama ta rinƙa makashi a jikin ginin ɗakin.
Koda ganin haka sai Bardil,Bagwan da sauran barade suka ruga kan boka Sharmadu da nufin gididdiba shi.
Kawai sai ya juyo ya dube su.
Take wani haske ya fito daga cikin idanunsa ya buge su duk suka ƙame,suka zama gumaka.
Sharmadu ya ci gaba da ƙyalƙyala dariya.
Har a yanzu iskar nan bata daina gwara jarumi Nazmir ba a jikin ginin dakin.
A wannan lokaci gimbiya Luzaiya na daga gefe guda a tsaye ita kaɗai tana ganin abinda ke faruwa. Koda ta ga halin da Nazmir ya shiga ya zamana kansa ya fashe jini na zuba kuma ya ji raunika a sassan jikinsa,harma hankalinsa ya fara gushewa sai hankalinta ya dugunzuma,bata san sa'adda idanunta suka cika da ƙwalla ba,ta fara kuka. Nan take ta tuna lokacin da jarumi Nazmir ya sallama rayuwarsa ya bita cikin ramin nan mai tsananin zurfi.
Haka kuma ta tuna sa'adda ya ceci rayuwarta sa'adda kura ta kawo mata farmaki.
Ta tuna da irin kulawar da yayi mata yayin zamansu a cikin jeji. Nan take gimbiya Luzaiya ta ji cewa duk duniya babu abin da take so sama da jarumi Nazmir.
Cikin zafin nama ta daka tsalle ta dirga a gadon bayan boka Sharmadu ta ɗane wuyansa.
Kawai sai ta kama isgar tsafin dake hannunsa ta matseta.
Ba zato sai taga boka Sharmadu ya kurma ihu.
Gaba ɗaya sassan jikinsa suka kama karkarwa ya hau layi kamar wanda ya sha gida ya bugu. Ba shiri ya ƙwalawa aljaninsa kira. Kawai sai Luzaiya taji an figeta daga kan wuyan Sharmadu an jifa da ita,tamkar tsakuwa aka wurgar. Luzaiya ta faɗi can gefe ɗaya sumammiya.
Wani gabjejen aljani ya bayyana mai kama da goggon biri,jikinsa gaba ɗaya gashi ne mai kauri da tsini tamkar ƙayar bushiya. Kuma ya kasance baƙı wuluk,muninsa ya linka na boka Sharmadu sau ɗari. Boka Sharmadu ya miƙe tsaye da ƙyar yana tangaɗi,sannan ya dubi aljanin yace, "Yakai Dumudulmus na umarce ka da ka kwashe mu nan gaba ɗaya ka kaimu fadar sarki yanzu-yanzu."
Dumudulmu yayi sujjada ga boka
Sharmadu yace, "An gama sarkin bokaye."
Kamar ƙiftawar ido,ya kwashe su gaba đaya ya ɓace tare da su. Bai bayyana a ko'ina ba sai a fadar sarki Fahalul Bahafus inda suka iske fada ta cika maƙil ana fadanci. Boka Sharmadu ya risina a gaban sarki ya kuwashi gaisuwa sannan yace, "Ya sarkin duniya ga masoyiyarka gimbiya Luzaiya,kuma ga manyan abokan gabarka na kawo maka kamar yadda na ɗauki alƙawari. Don haka sai ka gaggauta hallakar da su ta hanyar da na sanar maka."
Koda jin haka sai farin ciki ya lulluɓe
sarki Fahalul Bahafus. Nan take ya sa aka je aka fito da su sadauki Halufa,a cikinsu harda Muslaiya matar Bagwan da kuna Lamiz da sauran iyayen abokan nan su jarumi Nazmir.
Koda Lamiz ta ga ƙyallenta a goshin jarumi
Nazmir sai ta fashe da kuka don ta san cewa yayanta ya mutu. Shi kuwa Bagwan yaga wani kyakkyawan yaro a hannun matarsa Musalaiya. Da shi da yaron kamanninsu ɗaya tamkar an tsaga kara.
Nan take farin ciki ya kama Bagwan ya yunƙura da nufin ya ruga wajen su amma damar hakan bata samu ba,don boka Sharmadu ne ya nuna shi da isgar tsafi. Take wata baƙar sarƙa murtukekiya ta ɗaure hannayensa da kafafunsa. Suma sauran iyayen abokanan su Nazmir da basu ga 'ya'yansu ba,sai suka fashe da kuka. Nan take aka tusa ƙeyar su jarumi Nazmir izuwa tsakiyar fada aka tsaida su gaban wasu manyan turakan gini inda aka saba kashe mutane waɗanda suka yi laifi ga sarki.
Yayin da sadauki Halufa da jarumi Nazmir suka dubi juna sai Halufa ya murtuke fuska. Lokaci guda idanunsa suka ciko da ƙwalla ya dubi jarumi Nazmir cikin fushi yace, "Ya kai ɗana haƙiƙa kaci amana ta da kaje ka kashe mahaifin gimbiya Luzaiya don kawai ka biya buƙatar wannan azzalumin sarki namu. Kayi sani cewa har abada ba zan yafe maka ba,face ka hana auren sarki da Luzaiya,kuma ka kuɓutar da rayuwar mu nan gaba ɗaya."
Yayin da jarumi Nazmir ya ji wannan batu daga bakin mahaifinsa sai ya durƙusa ƙasa da ƙyar bisa gwiwoyinsa sakamakon raunikan da
ke jikinsa kuma har yanzu jini na zuba a kansa,kuma jiri na ɗibarsa. Cikin ƙarfin hali ya dubi sadauki Halufa a lokacin da idanunsa ke rufewa da buɗewa tamkar mai jin barci yace,
"Yakai Abbana ka yi mini aikin gafara,ka sani cewa ban aikata wannan mummunan aiki ba bisa sani da son zuciyata. Lallai wannan sarki namu yayi mana dole ne kamar yadda ka sani idan kuwa muka saɓawa umarninsa rayuwarmu da taku na iya salwanta. To yanzu ma dai ga shi kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba,tunda dai mun sha wahala mun biya buƙatar tasa,amma kuma sakamakonnu shi ne kisa. Haƙiƙa wannan sarki ya cika azzalumi."
Gama faɗin hakan ke da wuya sai ga
sarki ya fito. A ɓangaren hannunsa na dama gimbiya Luzaiya ce a tafe ta sha kwalliya,kuyangi na biye da ita. A wannan lokaci duk 'ɗa' namijin da ya ƙyallara ido ya ga gimbiya Luzaiya dole ne ya ruɗe,ya ɗimauce saboda tsananin kyawunta da ya bayyana a fili ƙarara.
Fuskarta na ta sheƙi da annuri,amma cikin zuciyarta baƙin ciki ne a lulluɓe, kamar zata
fashe. Hawayen takaici yayi sintiri bisa kyawawan kumatunta,ta hanga, ta dubi inda jarumi yake ta ganshi cikin mawuyacin hali,kuma cikin sarƙa a ɗaɗɗaure. Kawai sai ta fashe da kuka.
Nan da nan sarki ya sa aka zaunar da ita,shima ya zauna akan karagarsa,sannan yasa aka fara shirye-shiryen ɗaura aurensu. Su kuwa su jarumi Nazmir sai aka jera su a gaban wani ƙaton basamuden bawa baƙin fata wanda ya riƙe wata zabgegiyar adda. Shirin da aka yi shine da zarar an gama ɗaura auren sarki da gimbiya Luzaiya sai wannan baƙin bawa ya sare kawunansu jarumi Nazmir ta yadda jininsu zai zuba cikin wata ƙatuwar tukunyar tsafin boka Shamradu.
A kowanne ɓangare na fadar gabas da yamma,kudu da arewa dakaru ne birjik tsaitsaye cikin shirin yaƙi,shi kuwa boka Shamradu na tsaye a tsakanin karagar sarki da ta gimbiya Luzaiya yana murmushin farin ciki, don ya san cewa saura ƙiris buƙatarsa ta duniya ta cika.
Tsakanin boka Shamradu da sarki akwai wata yarjejeniya ta cewar idan ya taimaka masa yaga bayan maƙiyansa,shi kuma zai bashi kyautar babban gari daga cikin ƙasarsa ya mulke su,kuma zai zama makusanci a fadar sarki.
Lokacin da aka ci gaba da harkokin ɗaurin aure, sai gimbiya Luzaiya ta dulmiya a
cikin kogon tunani, inda take cewa da kanta,tabbas idan ta kuskura ta auri wannan sarki
rayuwarta ta gama gurbata gaba daya. Babu
wani abu da zai sata farin ciki a duniya face ta auri Jarumi Nazmnir masoyin da shi kadai ne zai iya mayar da ita kasarsu ta sadu da mahaifiyarta,
kuma ta hau kan karagar mulkin da ta gada. Ta
ya ya za ta sami wannan nasara? Babu wata
dama face ta tsaida wannan daurin aure, kuma ta
ceci rayuwar su jarumi Nazmir.
To wai shin me za ta yi ta tsaida ɗaurin auran, kuma me za ta yi ta iya ceton rayuwarsu
Nazmir din? Wannan tanbaya ce wadda gimbiya Luzaiya ta yiwa kanta, kuma ta kasa
gano amnsarta. Tana cikin haka ne ta tuno da abin
da ya faru dazu a dakin bauta tsakaninta da boka
Sharmradu.
Koda ta tuno wannan al'amari sai ta mike zumbur cikin zafin nama ta shammaci boka
Shamradu ta fisge isgar tsafinsa daga hannusa ta
cauɗa masa ita a wuyansa. Kawai sai aka ga boka
Shamradu ya kankance ya zama ƙanƙanin dutse.
Nan fa sarki ya zabura ya faɗa bayan karagarsa
ya ɓoye dakaru suka yi ca kan gimbiya ita kuwa ta nunu su da isgar tsafin nan suma sai suka
kuma suka zama gumaka. Nan fa fada ta hargitse aka hau guje-guje da iface-iface.
Gimbiya Luzaiya ta ruga inda su jarumi Nazmir suke ta nuna sarkar da ta ɗaure su da
isgar tsafi, take sarkar ta narke ta zama ruwa.
Koda ta ga sun kuɓuta sai ta miƙawa jarumi Nazmir isgar tsafin, ta ce rike wannan ta zama makaminka, kai ne namiji ni kuwa macece ban
saba da gumurzu ba. Cikin hanzari Nazmir ya karbi isgar.
A daidai wannan lokaci ne sarki ya fito daga maboyarsa koda ya hango iskar tsafi a
hannun jarumi Nazrnir sai ya dakawa dakarunsa
tsawa ya ce, "Maza ku raba shi da wannan isgar
tsafin ku kawo mini ita nan."
Gaba daya dakarun wajen suka yi caa kansa, shi kuwa ya rinka nuna su da ita sai dai
ka ga tsawa na dira kansu, suna zubewa kasa matattu. Wani lokacin kuma wuta ce
jikinsu su kone kurmus. Wani lokacin kuma dai kawai aji wuyansu na karyewa rakakas, ko
kuma a ga kibiyoyin
tsafi na jukunansu. Anan fa yaki ya yi yaki, Nazmir
zubar da maza, amma sai ka waɗansu na daɗa
shigowa cikin fadar kamar ba za su kare ba.
A wannan yaki sadauki Halufa ya taimakawa jarumi Nazmir matuka, domin shi ma
tsohuwar jarumtarsa ce ta motsa, ya dunga girbar
maza kamar yana sassabe a gona. Haka ma su Bagwan sun taka muhimmiyar rawa a wannan
yaki. Yayin da aka shafe sa'a uku ana wannan yaƙi amma ya ki karewa sai hankalin su jarumi
Naznir ya tashi. Don haka sai sadauki Halufa ya bada shawarar a bude hanya da ƙarfin tsiya a fice daga cikin fadar don a fita daga garin gaba
daya.
Ai kuwa haka aka yi, ámma duk da haka sai da sarki ya ja tawagar miliyoyin mayaka aka
bi bayansu Nazmir har aka riske su a daji,sannan aka ci gaba da yaƙi. Yayin da gumurzu
ya yi gumurzu,bala'i ya yi bala'i sai isgar tsafin nan ta subuce daga hannun jarumi Nazmir ta
fadi ƙasa. Ai kuwa tana faduwa sai kasa ta tsage ta fada ciki. Take kasar ta rufe kanta tamkar an binne gawa a kabari. Koda sarki da dakarunsa suka ga babu isgar tsafi a hannun jarumi Nazmir sai suka yi kukan kura suka afka musu. Nan fa
aka buɗe sabon lale,aka ruguntsume da mummunan yaƙi.
Wannan yaƙi dai ba'a gama shi ba,sai
bayan wata shida. Ma'ana bisa dole aka rinką tsayawa ana ja da baya musamman idan dare yayi.
Da safe kuwa sai a sake gamuwa a filin daga a ci gaba da rubdugu. Tsakanin mutanen sarki da mutanan su jarumni Nazmir. A wannan yaƙi ne
sadauki Halufa da dukkanin iyayen abokan Nazmir suka rasu,Bagwan ma a wannan yaki ne ya rasa rayuwarsa ya zamana jarumi Nazmir,gimbiya Luzaiya, da Bardil ne kaɗai suka rayu,
suma ba su tsira ba sai da taimako ya zo musu daga birnin gimbiya Luzaiya na dakaru miliyan dubu huɗu. Jarumi Nazmir ne ya kama azzalumin sarkin garinsu da ƙarfin tsiya ya đaga sama ya fyaɗa da ƙasa. Take sarki ya sume.
Kafin ya farfaɗo Nazmir ya kama wuyansa ya karya ya yar da gawarsa anan ƙasa.
Bayan an gama yaƙi ne aka koma birnin gimbiya Luzaiya inda aka ɗaura auren jarumi
Nazmir da gimbiya Luzaiyà ya zauna tare da ita a ƙasarta. Mutanensa suka so ya koma gida ya zama sarki,amma ya ƙi yace ya bar gida har abada,tun da ba shi da iyaye a garin bashi da kowa sai Bardil. Don haka sai aka baiwa Bardil sarautar ƙasar."

Lokacin da sarki Dujalu ya zo nan labarinsa sai ya yi shiru ya dubi boka Hajurul Mukurus,tsoho Rafkanagu da Ruziyal yace,
"yanzu ya ya kuka ji wannan hikayar ina fatan dai kun ji daɗinta?"
Ruziyal yace, "Ƙwarai kuwa ai na ji daɗinta,musamman yadda na ji ƙarshen wannan azzalumin sarki sai dai kuma na ji tausayi
matuƙa da ya zamana iyayen jarumi Nazmir sun mutu har da sauran abokansa ya rage mutum ɗaya jal daga cikin su, wanda hakan ne ya sa ya ji garin nasu ya fita daga ransa."
Tsoho Rafkanagu yace, "Ƙwarai kuwa nima haka na ji a raina, amma fa gaskiya wannan hikayar ta cika tsawo ina fatan ta gaba ba ta kai wannan yawa ba?"
Sarki Dujalu ya bushe da dariya yace, "Ai hikayar da zan ba ku nan gaba ta ninka wannan
sau biyu a tsawo,kuma akwai abubuwan al'ajabi da yawa a cikinta,sai ku gyara zama ku kasa kunnuwanku don ku ji ta."
Caraf sai boka Hajarul Mukursu yace,
"Ranka ya daɗe zai fi kyau dai kasa a sake kawo mana sihirtaccen shayin nan naka mu sha, don mu ƙara kimtsawa tun da dai ka ce hikaya ce mai tsawo."
Sarki Dujalu ya sake bushewa da dariya yace, "Wannan babu laifi."
Nan take ya ce, aje a gayawa kuyanga mai shayi ta kawo. Cikin hanzari wani bafade ya miƙe ya shiga cikin gida. Wannan shi ne abin ya faru a fadar sarki Dujalu bayan ya gama basu labarin hikiyar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya.

*********

Al'amarin su jarumi Hubairu kuwa,bayan sarki Lu'umanu ya sace gimbiya Sima ya ɓace da ita a cikin sararin samaniya,sun neme shi sun rasa, sai hankalin Hubairu ya ƙara dugunzuma,
ya rasa abin da ke masa dadi, a duniya. Koda ganin halin da ya shiga sai sai aljani Abtarul
Hudes ya shiga rarrashinsa yana mai kwantar masa da hankali cikin daɗaɗan kalami, da nuna
masa mubimmancin rungunar ƙaddara.
Hubairu ya yi shiru bai ce komai ba. Daga bisani sai ya dubi Abtarul Hudes yace, "ya kai
Abtarul Hudes ka yi sani cewa shi SO cuta ce,wadda in dai ta shigi mutum har abada ba zai
warke ba,face ya sadu da masoyinsa. Ka yi sani cewa sarki Lu'umanu va zama babban maƙiyi na a duniya, tun da yana son ya raba ni da masoyiyata, kuma yana son ya abin da nake so kuma yana son daƙile addinina.
Abinda nake so da kai kawai shine ka ƙara azama don mu isa birnin Teheren da wuri
kafin Mushrikin nan ya samu damar aurar
masoyiyata.
Idan hakan ta faru zan kasance cikin baƙin ciki. Da yardar Alah zamu sami nasara akansa,kuma tsafinsa ba zai sami tasiri akan mu ba."
Yayin da aljani Abtarul Hudes ya ƙara ƙarfin kaɗawar fukafukansa, ya zamana suna masu tsananin gudu sai keta gajimare suke tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya.
A can birnin Teheren kuwa tuni sarki Lu'umanu ya sauka da gimbiya Sima har ma ya tashe ta daga wannan barci da ta daɗe ta na yi,amma bai tashe tan ba, sai bayan ya tsafanceta ya juyar da tunanin ƙwaƙwalwarta ya zamana ta mance da duk abubuwan da suka faru gareta a
baya. Wato ƙwaƙwalwar ta zama sabuwa tamkar ta jaririyar da aka haifa yau babu komai a cikinta face abin da za'a sa mata.
A cikin turakar sarki Lu'umanu bisa wani ƙasaitaccen gado na alfarma. Gimbiya Sima ce a zaune fuskarta cike da murmushi da annuri,kuyangi na ta shige da fice a ɗakin ɗauke da kayan marmari iri-iri da kuma sauran nau'in abinci da abin sha. Duk suna kaiwa gimbiya
Sima ne don ta zaɓi abin da za ta ci amma har yanzu ba ta zaɓi komai ba. Daga ƙarshe dai naman ɗawisu ta ci,sannan ta sha ruwan inibi.
Bayan ta gama kimtsa cikin ta ne,kowa ya fita ya barta,sannan sarki Lu'umanu ya shiga ciki ya risketa,da shigarsa ya ƙare mata kallo sama da ƙasa ya ga irin tsananin kyawunta sai farin ciki ya turnuƙe shi ya ji kamar an bashi duniyar nan gaba ɗaya. Sarki Lu'umanu ya zauna a gefen gadon kusa da gimbiya Sima suka dubi juna suna masu murmushi,mai nuna tsantsar so da bege. Lư'umanu yace,
"Yake masoyiyata ki yi sani cewa gobe i yanzu kin zama matata,ina nufin an ɗaura mana
aure,yanzu me kike so a cikin faɗin duniyar nan na baki shi,koda kuwa yana ajiye a can bangon ƙarshen duniya?"
Gimbiya Sima ta ƙyalƙyale da dariya tace,
"Bana son komai daga gareka ya masoyina face ka yawata dani ko'ina da ina acikin gidan sarauta don na marewa idanuna da kallo."
Koda jin wannan batu sai sarki Lu'umanu ya bushe da dariya sannan yace ai wannan bukata taki a komai sauƙi ce a wajena. Nan take Lu'umanu ya nuna tagar ɗakin da hannunsa kawai sai tagar ta buɗe daddumar tsafinsa ta shigo ta cikin tagar.
Daddumar ta sauko ƙasa ta dira a gabansa kawai sai ya kama hannun Gimbiya suka hau kan daddumar suka zauna.
Zaman su ke da
wuya daddumar ta tashi dasu sama ta ringa shiga dasu saƙo saƙo lungu lungu na gidan sarautar kai har cikin kurkukun nan na ƙarƙashin ƙasa inda aka taɓa tsare aljani Markahul sabus sai da suka shiga. Anan né suka riski waziri kuddaru a ɗaure cikin sarƙa an ajiye abinci a gabansa ya zubawa abincin idanu yana kuka,koda ya ɗago kai yaga
Gimbiya Sima tare da sarki Lu'umano bisa

2 Comments On MATSATSUBI Book 2
avatar
idris-idris-abubakar

1 year ago

Reply

Hausa

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to idris-idris-abubakar

Eh na hausa ne

Please Login or Register in order to submit comment