Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ace sun d’an fi haka da sai ya bawa Baraka dubunta goma ragowar kuma ayi hidimar asibiti da shi … Godiya Sosai yayi har sai da ya bawa ‘dan uwan nafi’un kunya ma Daganan yayi musu sallama ya burga mashin d’in sa ya wuce ya barsu anan a tsaye Kafin suma su juya su nufi k’ofofin gidajen su . Har suka k’arasa k’ofar gidanjen nasu guda biyu Ya musbah tunani yake yi , tausayin sa Nafi’u yake ji sosai dan yasan in ba matsalar Baraka ba tou matsalar rashin lafiyar mahaifiyar su ce ta sanya shi a damuwa haka Yana shirin yi ma sa magana yaji Ya musbah ya ce ‘Nafi’u kud’in nan fa Baraka zan bawa ‘’. A d’an fusace nafi’un yace ‘’Saboda ka zama mijin tace ?’’ Ya musbah Bai boye wa Abokin na sa komai ba haka ya zaiyyane ma sa abunda ya faru Sannan ya ‘kara da cewa ‘’ Ba wata maganar en sanda , Biki ne take da shi tsabar bala’i wai ankon super za suyi Me sunan baba kan sa tayi mishi kaya Masu kyau da tsada sama da kala uku Amman saboda Allah ace mahaifiya ta Bata da lafiya amma sam Baraka Bata damuba ….’’ Ya karashe maganar hawaye suna silalo masa Da kyar Nafi’u ya iya danne fushin sa gudun kar ya sake tunzura Abokin nasa, Sai da yad’an daidaita kan sa daga takaicin Baraka Tukunna Ahankali ya dafa shi Kafin yace Kayi hkr Musbah Komai yayi zafi maganin sa Allah , Tunda tayi maka haka kuma Baba yace a Bata kawai a Bata din , Ita ta sani Inde duniya ce Dede take da ita, Kawai yanzu matsalar shine inda zamu nemo wani kud’in Saboda Nima Wallahi babu a waje na da ace ina da shi Wallahi dana baka, kasan lokacin biyan kud’in gida yayi Mutumin nan Sam kasan baya tab’a d’aga min k’afa har gara kai Yakan ce ai yasan baka aiki Gashi wannan term din khairat ta shiga makaranta shiyasa nima duk na zama a matse ,bani da shi .’’ Shiru ya d’an yi kamar me tunani kafin yaci gaba da cewa ‘’kuma kaga yaya na guda daya tak a duniya na tambaya maka shi shima amma bara muga ko akwai….’’ Dasauri Ya musbah ya katse sa ta hanyar cewa ‘Nafi’u Karka damu Na gode Wallahi ban san da wanne baki zan maka godiya ba Banajin akwai Aboki irinka har yanzu a duniya In kuma akwai tou tabbas baku da yawa Nagode nagode ka kwantar da hankalin ka bara inje in bata kud’in dole haka zan hak’ura in lek’a Innar babu ko sisi In naje sai a san yadda za ayi’’. ‘’Ok’’ Nafi’un yace Cikin rashin Jin dad’i Kafin ya sake cewa ‘’Nima bara in duba gida In komai normal sai mu tafi tare wajen Innar ….. MANNUBIYA O4 Na Humayrah Bulama ELEGANT Online ✍️ Babu kunya ba tsoron Allah haka Baraka tasaka hannu ta amshe kud’in nan,duk da kuwa ragowar kwallar data gani a idanun mai gidan nata wanda hakan ya tabbbatar mata da kuka yayi , Sannan ga jijiyoyin kan sa sun fito rad’au ga kuma farar fuskar sa tayi jajawur wanda haka yake sake nuna tsananin tashin hankalin da yake a ciki. Tana amshe kud’in ta shige cikin parlourn su mai ‘dauke da d’akuna biyu ,dama fitowarta daga band’aki kenan ta tarar da shi yana jiran ta . Ya dad’e a tsaye , kafin ya samu ya ja Kafafuwan sa ya juya ya fice daga gidan, gabadaya . Sai a Sannan tabar bakin window inda ta lab’e tana kallon sa tana mai tab’e baki a ranta tace ‘’Haka kurum in bada kud’ina akai uwar wani ba tawa ba asibiti,bayan ga biki a gabana , In na biyeka Musbahu naga alamun sai na gagara shiga k’awaye na wallahi,da mutunci na ka auro ni amma iyakar inda ka ajjiye ni da suturun daka jeremin a lefe ya sanya yanzu ko hamshak’in taro za’ayi k’awaye na basa gaiyyata ta.’’ Hakanan tayita mita a cikin ranta daga karshe ta shiga kasafta mai da me zata siya da kud’in…… Tun lokacin da suka rabu da Ya musbah ,Baba’ yake tunanin ta Ina zai samo kud’i , duk inda ya duba ya zaga ya zagayo babu hanya , shiyasa gaba d’aya hankalin sa ya sake tashi , ahaka sukayi alwallah sukayi salla daganan suka fito daga masallacin suka zauna akan d’an dakalin k’ofar gidan da shi da muhsin. Yana cikin tunani yaji wasu zafafan hawaye suna zuba akan kyakkyawar tsohuwar fuskar sa ,sai da ya faki idon Muhsin wanda yayi shiruu shima ya sunkuyar da kan sa k’asa tun dazu Tukunna yasa hannu ya share hawayen nasa Kafin a hankali ya fad’a duniyar wani tunanin na daban ………Yanzu haka , a tsakiyar en uwan sa yake Babban yayan su BABA HABU da matan sa biyu Umma DIJE da umma KULUWA Umma dije yaranta mata uku Zainab ,Hauwa sai Maryam , gaba d’ayan su sunyi aure. Sai Umma kuluwa tanada Yaro d’aya namiji ‘Ya Yusuf ‘ya girmi Ya musbah da shekara d’aya amma shi bai yi aureba . Sai d’ayan yayan nashi UTHMAN Wanda kowa yake kiran sa da UNCLE Uncle yanada mata uku Kasancewar yana aiki a banki yasa duk ya ‘dan fisu rufin asiri Matarshi ta farko FATIMA Umma Fati Yaro daya tak ta Haifa Ya iliya (yayi aure)daganan ta samu matsala Bata sake haihu wa ba ta biyun sunan ta khadija Itakam ko b’atan wata ma Bata tab’a yi ba , Sai ta ukun Anty RUMASATU Anty amarya tanada yara biyu mata twins Shamsiyya da Salaha masu shekaru goma a duniya. Sai yayar sa Anty umma (Binta),wadda mijin ta ya rasu ta komo gidan da zama Yaranta biyu mata ta farkon sunan ta Fiddausi tana aure a illorin sai autar ta wadda ta ke tare da ita ‘Siyama’ Siyama ta girmi Jidda Manubiya kuma ta bata shekara d’aya . Sai shi Baba (MUSA) Matarshi d’aya Aminatu (Inna) Da yaran su hudu Musbahu mai shekaru 27 Sai Manubiya mai shekaru 22 Sai Maijiddah mai shekaru sha bakwai Da auta Muhsin wanda bai k’arasa rufe shekaru sha d’aya ba . Duk a cikin y’an uwan nan na sa da suke zaune tare a gida d’aya babu wanda zai tambaya kwandala a cikin su yau ace ya d’auka ya ba sa , In ana maganar asalin rashin had’in Kai Tou shine definition d’in rayuwar Baba da y’an uwan sa , Ba hassada babu fad’a babu hayaniya amma fa kowa na sa kawai ya sani ,hatta Anty umma , ba mai ciyar da ita a tsakanin yayyun nasu maza biyu Masu rufin asiri , sai dai ta ci da kanta ta ci da y’arta Da taimakon y’ar sana’ar siye da siyarwar da takeyi , sai kuma sistern siyaman itama tana taimakawa ba laifi. A takaice dai kowa ta kan sa yake yi a gidan, kowa nasa ya sani sannan babu ruwan kowa da kowa , yanayin zaman sam babu dad’i ,ga baki ga hanci compound d’aya amma in ba su Manubiyan ba babu wanda wani abun zai faru ace wai ya lek’a d’an uwansa yaji halin da ake ciki. Mai k’ananun maganganu ,rigima da son had’a fad’a a gidan mutum d’aya ne Kaka Malan , Wani d’an uwan mahaifin su da Allah bai ba sa haihuwa ba Suka d’auko suka bashi d’aki mai bandaki a cikin compound d’in nasu, Wanda shima sai yayi da gaske tukunna suke kula sa su zuba ma sa abinci,dan Kaka Mallan irin tsoffin nanne masu tijara ,gulmace gulmace,shishshigi da zalama. Sukam a tsakanin su babu jita jita Sai dai Sam basa tausayin juna basa kuma taimakawa juna Idan d’an uwan ka zai kwana bai ciba Babu ruwan ka ba abunda ya shafeka . Tun suna yara su uku ,mahaifin su ya zaunar da su ya tambaye su abun da kowa yake son yayi a rayuwa, Yayyun Baba biyu Uncle da Baba Habu suka zab’a karatu Shi kuma ya zab’a Sana’a Kamar yanda mahaifinsu yayi alkawari Karatu har sai da sukace sun gaji Shi kuma aka damk’a ma sa mak’udan kud’ad’e aka ce yaje ya yi Sana’a. Abun nashi kamar sa hannu duk sana ‘ar daya soma bata Al’barka A haka har jarin na sa ya k’are tass. Uncle Baba habu da Anty umma mahaifiyar su d’aya Yayinda shi kuma ya kasance d’an gidan amarya Mahaifiyarsu Uncle ce ta fara rasuwa kafin tashi mahaifiyar wadda ta rasu wajen haihuwar sa. Tun suna yara sun taso basu da wani had’in kai ,tun lokacin da iyayen su mata suka rasu mahaifinsu bai k’ara aure ba shima har ya bar duniya. Hakanan suka tashi a wannan gida da suka gada kowa yayi auren shi yake rayuwar sa daga shi sai iyalin sa Duk cikinsu shine mai d’an karamin waje Sakamokon siyar musu nashi portion d’in daya dinga yi saboda ya samu ya sake jan wani jarin sannan kuma aci abinci a gidan sa . Ko da ya haifi musbahu,ya kai minzalin hankali Yaso ya d’aura shi akan layin Sana’a shima,har rantar kud’i ya dunga yi yana bashi jari amma shima Sam sanar tashi batayi Albarka ba Ganin sanaar baxata yiu ba yasa suka hak’ura Da ragowar en kudin hannun su da bai kai ya kawo ba suka fara makanikanci dan a lokacin shekarun Musbahu sun Kai sha bakwai ba damar komawa makaranta A wannan lokacin ne kuma Allah ya ‘daurawa baba Musa tsananin son yaga yaran shi sunyi karatu Shiyasa ya tsaya tsayin daka akan karatun nasu , Dan bai yi k’asa a guiwa ba sai da ya sanya su a makaranta, A lokacin Manubiya har dariya akeyi mata dan tayi girma a ajin yara Tare ya saka su a aji daya Manubiya muhsin da jidda Duk a aji ‘daya Hatta jidda a lokacin tayi girma a ajin,amma Sam yaran basu wani damu ba Dan suma suna tsananin son karatu Sannan sunada tsananin k’ok’ari da naci akan karatun Dan cikin ikon Allah hazak’ar su ta sanya aka dinga yi musu double promotion wanda har ta kaisu ga taddo sa’o’insu Da farko private suka fara Amman yanayin rayuwa ya sanya dole Baba ya maida su ta gwamnati Wanda duk gidan su kad’ai ne suke zuwa makarantar gwamnati Jamb ne ya so bawa manubiya matsala Amman waec d’inta da neco har mamaki ya dunga bawa mutane Saboda yanda ta fito da flying colours.Rashin cin jamb d’in ne yasa ta shiga poly tayi diploma Ta shiga BUK da D E ,yanzu haka Tana level 3 suna karantar English tare ita da Abbakar Tun a poly suke tare ita da Abbakar Bata da kawa mace Saboda yanayin rayuwarta Kullum Kayanta a kode , Gashi ko kudin handout wani lokacin sai dai ta ara tayi karatun a iya makarantar Sannan in anzo tafiya cafeteria sai dai ta gudu Dan inde Anje sai dai a siya mata tasan rayuwa bazata yiwu a haka ba shiyasa ta shafawa kanta lafiya, Abubakar ne kawai Abokin ta anan unguwar tasu yake bayan layin su Maman shi k’awar Maman Baraka ce Tare suka bude gidan abincin su Tun shekaru baya da dad’ewa . Jidda kuma wannan Shekarar ta zana waec ,taci itama kuma cikin Ikon Allah taci har jamb yanzu saura mata post utme . Muhsin kuma yana js2 tun last year ,yanayin rayuwa yasa ya kasa ci gaba da karatun. ……. ‘’Baba Ina wuni,’’ Muryar Abbakar ta katsewa Baba tunanin sa. Ahankali sannan a d’an boye ya sake goge idanuwan sa tukunna ya juya yana kallon su shi da Muhsin. Da kulawa ya amsa shi yana tambayar sa ya Maman sa shi kuma yace Mishi ‘’tana lafiya’’ kafin Cikin yin k’asa da Kai yace ‘’Baba dazu a aji ana ta bayani amma sai na lura sam hankalin Manubiya baya a ajin daga baya ma sai na fahimci ashe ma kuka takeyi naso in taimake ta dan nasan akan rashin lafiyar Inna ne amma sam sai tak’i yarda, Dan Allah Baba ga kud’i na bawa muhsin a kai Innar asibiti dasu Kar kace a’a , nima kamar uwa Inna take a waje na ’’ Ahankali ya d’aura da cewa Allah ya bata lafiya ya kawo mata sauk’i’’ Yana gama fad’in haka ya musu sallama ya juya ya wuce… MANNUBIYA 05 Na Humayrah Bulama ELEGANT Online ✍️ Sai da Muhsin ya d’an tab’a Baba tukunna yayi firgigit yace ‘’Na’am.’’ Neman Abbakar ya fara yi amma sai yaga babu shi babu alamun sa Ahankali yace wa Muhsin d’in ‘’kaje gidan su kace ma sa na gode Sam banga wucewar sa ba ‘’. ‘’To’’ Muhsin yace daganan ya mik’a ma sa kud’in yace ‘’gashi.’’ Sai da kwallah ta zubo wa Baba kafin yasa hannu ya karb’a kafin ya mik’e ya wuce cikin gidan da sauri Muhsin kuma ya wuce gidan su Abbakar. Kusan karo sukayi shi da Manubiya wadda ta fito da gudu Suna had’a ido da Baban nata ta fashe da kuka ta fara waiwaye tana nuna ma sa d’akin tana juyowa tana kuka wiwi tama kasa magana. Da sauri suka d’unguma zuwa d’akin. Abunda yayi tunani d’in ne kuwa Dan haka ya durkusa ya fara k’ok’arin kinkimar Inna wadda ta sank’ame idanuwan ta suka k’ak’k’afe dai dai nan ya musbah ya shigo ….. Allah ya taimake su Nafi’u ya taho da motar sa 206 dan haka aka saka ta a ciki suka wuce da Baba da Ya musbah da Nafi’u wanda ke driving da innar rashin gurin zama da kuma jiran Muhsin ne ya sanya su Manuniya suka hak’ura ba don sun so ba ,Amman har waje bak’in k’ofa suka biyo su kowa tana kuka,sai da suka ga wucewar su tukunna suka fara k’ok’arin komawa ciki dakyar. Anan bakin k’ofar suka had’u da Baba habu shi da Uncle wanda dawowar sa kenan daga parking motar sa a gidan makwafcin su inda yake ajjiyewa. Gaisuwarsu kawai ya iya amsa wa daganan ya shige ciki ya barsu tsaye su da Baba habu,shima kamar bazai tambaye su ba Sai kuma ya ce musu ‘’lafiya kuwa?’’ Jidda ce ta iya bashi amsa dan ita Manubiya haushin sa takeji, ba sa shiga harkarsu sannan ba sa taimaka musu amman ya tashi ya tsaya yana k’ok’arin k’ulla aure tsakanin Jidda da Ya yusuf,bai damu da yadda jiddan bata son Ya yusuf d’in ba kawai shi dai farin cikin d’an sa yake dubawa…. A tunanin Jidda zai bi bayan su Baba tunda ta lura tunda aka fara maganarta da Ya Yusuf ya na d’an kula su amma sai taji yace ‘’Allah ya Bata lafiya’’ Daganan shima ya ja k’afafun sa ya shige ciki. Yana wuce wa dai dai nan Muhsin yana k’arasowa dan haka suka wuce ciki. Sai chan dare tukunna ya Nafi’u yazo yace su kwantar da hankalin su jikin innar da sauk’i. Yanayi sa yasa tashi d’aya suka fahimci ya fad’a musu hakan ne kawai dan su d’an kwantar da hankalin su. Daman basuyi girki ba Tashin hankali yasa suka kasa ma jin yunwar,jugum ranar haka suka kwana ita da Jidda sam basu runtsa ba Muhsin ma barcin d’an kad’an yayi,safiya tana yi zazzab’i mai zafi ya rufe Manubiya dan yau kwanan ta na uku kenan batayi bacci ba …… Tun lokacin da Yasir ya fita daga d’akin da kausar take ciki bata sake ganin sa ba Hada hadar komawa ma Abokin sa ya d’aura akan komai shi kuma yayi wucewar sa. Banda addua ba abunda takeyi a ranta akan Allah ubangiji yasa Yasir zuciya yayi Sannan ya hak’ura da ita har abada,shaka ta kwana Tana wannan adduar tare da tunani barkatai a ranta washegari itama suka had’a komai itada k’awayenta suka nufi airport …… da safe around 8 flight d’insu yayi landing a gida Nigeria, Suna fitowa suka tarar da Sister d’inta ’Yasira’ ta na jiransu …. Sai da suka fara ajjiye k’awayen nata da suka dawo tare tukunna suka d’auki hanyar gidan su dake a sultan road,shiru motar ta d’auka ba mai cewa komai kafin chan Yasira tayi murmushi tace ‘’tun jiya daya dawo dama nasan fad’a kukayi, yanzu kuma mood d’inki ya tabbbatar min da hakan, Did u tell him?’’ Ta karashe maganar tata da tambaya tana me d’an waiwayowa ta kalle ta kafin ta maida hankalin ta akan tuk’in da takeyi. Kamar kausar d’in bazata amsa ta ba sai kuma tace ‘’Na ce ma sa bana son sa, yayan sa nake so???’’ Wata er siririyar dariya Yasirar tayi kafin tace ‘’Noo!ki dai san ta yadda zaku yi breaking up tunda wuri kuma cikin sauk’i domin in kika bari kukayi baram baram,to fa ki tabbatar auren ki da Ya Yashjub ba mai yiuwa bane ba So find a way out soon, rikitacciyar zuciyar ki data d’auko mana aiki mai zafi , ta nemo mana mafita,a samu a rabu cikin sauki.’’ Wata nannauyar ajiyar zuciya kausar ta sauk’e kafin tace ‘’Abun da nake ta so inyi kenan shi kuma Yasir nacin bala’i ne da shi kamar maye haka yake,yak’i ya bani had’in kai, ban….’’ Ganin yadda Yasirar tayi Shiruuu ta d’an b’ata fuska ne yasanya Kausar d’in yin shiru kafin ta d’an yi gyaran murya Ahankali tace ‘’Sorry.’’ Murmushi kawai Yasira tayi kafin tace ‘’Kausar,inda ace zanji haushin ki akan issue d’in Yasir, tou da tuni tun farko da kika gayamin yanda feelings d’inki sukayi bouncing daga kan Yasir zuwa kan Ya yashjub da naji haushinki But You are my best friend hakan ne ya sa nayi supporting d’inki,kasancewar Yasir twin brother d’ina ba zai sanya in zuba ido Inaji Ina gani , ki cuce sa ki cuci kanki ba domin nasan tunda har Kika iya kallon ido na kika cemin bakya son Yasir tou tabbas bakya kaunar sa Kuma in kukayi aure a haka akwai babbar matsala, dan haka ,ko da ace baki samu Ya yashjub ba bazan so ki auri Yasir ba ….’’ A hankali Kausar d’in tace ‘’InshaaAllah Allah zan samu Ya Yash da izinin Allah I just need your support Yasira.’’ Ta karashe maganar ahankali tana kallon Yasirar abun tausayi. Murmushi Yasira tayi Kafin tasa hannu ta kamo na Kausar d’in tana Murmushin tace ‘’Zan taimake ki har sai inda k’arfi na ya k’are InshaaAllah, tun yarin ta kin kasance k’awata y’ar uwata da take tsayamin tsayin daka akan komai In na k’i inyi miki wannan taimakon kwaya d’aya danasan shine farin cikin ki ai na zama butulu.’’ Cike da Jin dadi Kausar tace ‘’Thankyou’’ tana Murmushi. Daganan suka shiga tattaunawa akan yadda za suyi da Yasir saboda sun fahimci sai sunyi da wayo da dabara tukunna zasu ci nasara domin sai yanzu suka fahimci ashe su sunyi underestimating soyayyar dayake yi wa kausar d’in…. Kamar yadda sukayi zato A compound d’in dank’areren mansion d’in suka tarar da mommy tana jiran su,murmushi Yasira tayi kafin ta juya ta kalli kausar wadda ta had’e rai tace ‘’Your guarding angel, ai na san ta daina fushin dake,gashi har ta zo tarbarki, Jiya da Daddy yace mata zai dawo yau,bakiga yadda hankalin ta yayi bala’in tashi ba gudun kar ya dawo bai tadda ki ba, Tun jiyan take tambaya ta Flight din naku dai 8:00am ne ko ?in tabbatar naje na dauk’o ki da wuri Kar Ya Yash ma ya fahimci bakya kasar kuma kar Daddy yazo bakya nan.’’ Duk da yadda kausar ta shirya k’in yin murmushi sai da wata y’ar siririyar dariya ta subuce mata A Chan k’asan ranta tana mamaki da yaba tsantsar k’aunar da momyn nata takeyi mata But bazata bari taga lagonta ba In ba hakaba tasan yau sai ta sha fad’a , Dan haka ta sake had’e rai ta turb’une fuska kamar bata tab’a dariya ba tukunna ta murza handle d’in ta fito. Duk yadda mommy ta so sauk’e wa kausar ruwan bala’i suna hada ido sai taji fushin nata yana d’an sauk’a,tabbas ita kanta ba zata iya fad’in adadin k’aunar da take yi wa Kausar ba.Ganin yanayin fuskar Kausar d’in kuma sai ya sanya ta tad’an fara d’ar d’ar amman dukda haka yau kam ba zata bari kausar ta ga lagon ta ba,Ita ce uwa Ita yakamata subi bawai ita ta dunga binsu ba. Tana cikin wannan tunanin kawai taga Kausar d’in tazo ta wuce ta ba tare data ko gaida ita ba. A fusace mommyn ta juya ta shiga kwala mata kira, d’aga mata hannu kawai Kausar d’in tayi tana wani yatsine fuska kamar irin kin isheni d’in nan daganan ta wuce ta bi takan had’ad’d’iyar Barandar dake kewaye da main door d’in ta murza handle d’in ta tura ta shige abunta. Ba mommy ba hatta Yasira sai da ranta yad’an baci kamar zata bi Kausar d’in tayi mata magana sai kuma ta tuna yadda suke ita da mommy ba’a shiga fad’an su yanzun sai su shirya su barta tana fushinta ita kad’ai. A mugun fusace gudu gudu sauri sauri mommy tabi bayan Kausar,a bakin stairs ta hange ta tana shirin fara hawa Dan haka ta tafi da gudu ta finciko ta ta dawo da ita gaban stairs din ta fara fada baki da kumfa ‘’Kiyi laifi , kuma ki dawo min da wannan attitude d’in?mai kike nufi kenan ? Tou bari Kiji wallahi zan barki da Daddyn ku wannan karan dan naga abun naku daga ke har Yasir d’in fitina yake k’ok’arin zamewa mutane, In auren kuke so ku fad’a ayi muku kowa ya huta dan Wallahi na gama rufa muku asiri. Bazai yiu ace kina bin sa kuna yawo k’asa k’asa ba mu kuma muna gida a shantake, Banda iskanci wanne irin birthday celebration ne da baza a yi miki a Nigeria ba Sai ya d’auke ki kuntafi wata uwa duniya..’’ A hankali Yasira ta d’an matso ta tab’o ta Kafin tace ‘’Mommy.’’ Cikin fada ,mommyn Ta ture hannun Yasirar kafin taci gaba da cewa ‘’Rabu dani Yasira Kausar ta kaini bango Wallahi, A gaban ki na ce mata ban amince su tafi ko Ina ba ai amma dayake ta raina ni shine ta wanke k’afa da bi sa, to kuwa kamar yadda ta wanke kafa haka nima zan wanke hannaye na daga rufa musu asiri tund…’’ A karo na biyu Yasira ta sake katseta ta hanyar cewa ‘’Mommy!!!’’ Da d’an k’arfi Juya wa mommyn tayi a fusace zata rufe Yasirar da fad’a amma sai tagan ta duk a d’imauce tana kallon ta tana waiwayawa tana kallon k’ofar shigowa .. ….Giant,ne sosai mai fad’in k’ashi Sanye yake da riga da wando ‘pyjamas ‘farare tass masu ratsin silver,skin colour din sa light brown ne Kamar na half cast mai tsananin kyau ,shek’i da daukar ido Normal lowcut da tsadadden gyaran fuska yayi Amman yanayin yanda sumar tashi yadanyi coiling dukda kankantar sumar da aka bari ne zai sanya ka fahimci,lallausar suma gare sa Fuskarnan tasha gyaran fuska .. Wanda Hakan ya taimakawa ba’kak’irin d’in sumar ta sa sake haskaka kyakkyawar fuskar sa Kasancewar ba sa da sank’o ko kad’an ne ya taimaka wajen sake fitowa da k’awata matured handsome face d’in sa wadda k’awataccen saje da d’an siririn gashin baki,had’e da d’an mitsisin tudun gemun sa da ko hannun yara bazai iya kamawaba suka yiwa fuskar ta sa k’awanya. Dogayen idanuwa gareshi,manya kamar na maijin bacci wanda yayi dai dai da tsararriyar girar sa, Hancin sa dogo ne sosai,har baka Wanda yad’an bud’e Kad’an ta k’asan ya bada shape d’in M, Sai d’an mitstsin light nude lips d’in sa… ……. Ita kanta Kausar sai yanzu ta lura da YASHJUB,tsaye a bakin k’ofar, Wani irin sanyi takeji yana ratsa ta tun daga tsakiyar kanta har izuwa babban d’an yatsar kafarta.Duk da

Chapter 4 of 32