Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rasu ta sanadiyyar haihuwa data xo yi Duk su biyun itada yaron ba Wanda yayi Rai . Shiyasa gabadaya khadijan ta kuma burkicewa Badaban karfin Imani ba da tuni ta xauce Imam ma yana nan Kullum kuka Seda mamanshi , Yahanasu , Ta tsawatar mishi ta nuna mishi ya rungumi ‘kaddara tukunna dakyar da taimakon Allah da addu’o’i ya dan dawo Dede . Ko a gidan nashi ma se da aka kwashe duk wasu belongings na babyn daya kashe uban kudi ya ware daki guda ya jibge Tukunna aka samu sa’ida Dan haka xe shiga dakin ya rungume Kayan Yaron yayita uban kuka kmr wani karamin Yaro abun tausayi Dama shi tun yana Yaro yanada masifar son yara Shiyasa ya kwallafa Akan cikin jikin khadija masoyiyar shi , sai de kuma ‘Kaddara ta riga fata ……….. Bayan wata uku , Kmr ha’din Baki a lokaci daya duk su biyun suka samu ciki Sede edd din uwar gidan ya fi na amarya Ita zata fara haihuwa da sati biyu Daganan amaryar ta haihu … Murna wajen imam ba a magana Amman kuma duk yanda yaso ‘boyewa kowa ya San yafi yin farin ciki da cikin amarya . Uwar gidan itama ciki gareta wannan Karon Shiyasa aka ‘karo me aiki me xuwa da tafiya Suka hadu itada Larai Sukayi ta kula dasu Kmr yadda Imam yayi wanchan Karon haka yayi wannan ma Ya kwashe komai ya damkawa dan cikin khadija . A nan ne kuwa yaga bacin ranta Dan burkice mishi tayi tace bazai yiu ba Ai itama yayar Tata ciki gareta . Har kuka tayi mishi Tace kar ya zama cikin Masu zalinci mana , Tunda take da khadija ba ta taba cutar da ita ba Abunda takeyi mata ko yayar ta Allah yaji ‘kanta Bata yi mata Taya xeyi mata haka Ita kam babu ruwanta kuma in ya matsa se ta je ta samu su Daddy ta fadi musu ba da ita xa ayi wannan zalincin ba …. Yanayin yanda cikin khadija yayi tsini kmr wanchan Karon na farko Yasan inshaaAllah namiji zata kuma haifa Sa’banin na uwar gidan sa daya bi jikin ta Sosai yasa tayi kiba Shiyasa ya yanke shawara Ya samu khadija ya lalla’bata Akan ya fasa bada duka dukiyar Instead ya rabata gida biyu Sannan Duk wadda ta haifi namiji a tsakanin su Tou shi za a bawa In kuma duk suka haifi maza tou se a rabata gida biyu a bawa kowa kashi daya Kuma shi zai ci gaba da kula da ita ne Har se Yaron ya kai eighteen years tukunna ze damka mishi abunshi A wannan Karon ma Yayi mata bayanin dalilin shi nayin hakan Na cewa Yaro namiji kuma nafarko ya kamata a bashi support sosai Sede ita khadija Sam Bata fahimci fa’idar yin hakan ba , Tun ba ma yadda ya ware ta ita kadai ita da take amarya ya gayawa ba A ganinta kamata yayi ya hade su duk su biyun ya yi shawara dasu , In ma hakan ne decision dinshi tou ya gaya musu a tare . Ganin da ta yi ranshi ya soma baci da tirjiyar ta ne ya sanya kawai ta hakura ta rabu dashi , Amman har ga Allah a chan kasan ranta addua takeyi Allah ubangiji ya sa uwargidan ta haifi namiji. Sarai tasan tana fahimtar wasu abubuwa na bambanci da Imam yake nunawa a tsakanin su Amman dukda haka ta kauda Kai kamar bata san me ke faruwa ba ,amma fa tasan ko zuciyar gwal gareta muddin akace sun haihu tare in ita ta haifi namiji aka bata rabin dukiya Tou fa Zaman lafiyar ta da abokiyar zaman na ta Wanda take matukar Jin dadi xe iya tabuwa , Ita kuma Bata son abunda xe hada ta da abokiyar zaman nata Dan ta yi mata abunda baxata taba mantawa ba Yanda ta kula da ita da ‘dan cikin ta a kwanakin baya Ba ko wa ce zata iya yin hakan ba , Ko dan uwanka na jini iyakar abunda ze yi maka kenan. A bangaren Imam Kuwa Yasan yanason khadija da cikin jikin ta fiye da komai a rayuwarshi Fiye ma da rayuwar tashi , Amma babban dalilin shi daya sanya yake son bawa babyn ta rabin dukiyar sa Shine Be san gawar fari ba Be San lokacin da zai mutu ba , babban tashin hankalin shi shine ,rayuwar da khadijan ka iya shiga ita da babyn su in baya raye Yasan su maman shi zasuyi kokari Amman ba kamar yadda shi xeyi in yana raye ba . Uwar gidan shi yasan tanada gata er Masu kudi ce , khadijan shi itace abar tausaya wa Gata ita ba karatu ba . Shiyasa yake kokari yake trying anything possible yaga ya Gina ta ta xama standard Tunda ba a San gawar fari ba ………… A kwana a tashi ..akace ba wuya a wajen Allah domin Watan haihuwa ya Kama , Har satin edd din uwargida ya shiga . Sam abubuwa basu tafi a yadda Imam ya tsara Ya kuma yi xato ba ,Domin amaryar mace ta Haifa Uwar gidan shi kuma ta haifi namiji . Wan da Sam be yi zaton hakan Ko tsammani ba . A ranar da suka haihun ma baya nan Yayi tafiya abuja , Kafin ya tafi sai da ya kai amaryar aka tabbatar mishi se nan da two weeks edd dinta xe cika A Yayin da ita kuma uwar gidan taketa fama da labour tun wayewar gari, Dan haka ya bar musu duk abun bukata Yace xasu dan fita shi da khadija su siyo ragowar Kayan baby Da ga siyayyar ne suka biya asibitin, Yaji dadi kuwa Da Jin bayanin doctor Wanda yake ce mishi Se nan da sati biyu xa a yi expecting haihuwar Tata . Saboda shi sati daya kawai xaiyi ya dawo Kuma yafi son amaryar tashi ta haihu yana kusa da ita . Dan haka ya maida ita gida Cike da farin ciki , Yayin da ita kuma ta ke ta faman kumbure kumbure Tana mishi wa ‘a zin ya dinga adalci. Cike da fatan alkhairi Da kuma tsananin kewar khadija ya tafi , Tare da fatan yana dawowa ita ma inshaaAllah zata haifa mishi sanyin idaniyar shi . Sede kuma Yana tafiya itama amaryar ta fara Samun contractions , Dan haka akayi asibiti dasu duk su biyun. Suna zuwa akace Sai de ayi wa amaryar cs dan baxata iya haihuwa da kanta ba , Ba tare da Bata lokaci ba Su Daddy da Mama suke cike takardar amincewa aka shige dakin tiyata da ita Itace kuwa ta fara haihuwa Aka ciro mata babynta mace katuwa Tubarkallah , larai ce ta mikowa su mommy da suke a waje Yarinyar Wadda sukayi tsananin farin ciki da gani , Basu gama murna ba Likitan ya fito musu da kyakkyawan Yaro me tsananin kama da uban shi Dan wajen khadija uwar gida . Kowa in ya kalleshi se ya ce MashaaAllah Saboda tsananin kyawun Yaron …… A ranar Imam ya biyo flight ya dawo A hargitse Da ‘doki ….. Tun a Chan ya gama yanke shawarar fasa bawa dan gidan uwar gidan ta sa Rabin dukiyar sa Da tunanin neman wata mafitar tunda ba kowa ya san da zancen ba dama ….. yana xuwa daya dauki yaron yaji duk duniya ba abunda yakeso sama dashi Dan har kuka yayi tsabar farin ciki Wata irin soyayya Allah ya dasa mishi ta Yaron Me tsayawa a rai , yana son itama dayar yarinyar da aka Haifa mishi amman ba kmr Yaron Ba Domin wannan Yaron is very very special and dear to him Wani irin kalar so kauna da tausayi na Yaron yake ji suna ratsa dukkan ‘bargo jini da tsokar dake jikin shi . ….. Beyi tunanin su maman sa sunsan maganar alkawarin daya dauka na raba dukiyar shi biyu ba , Seda yaji tayi mishi maganar. Ashe wannan Karon ma uwar gidan ta sani kuma ta gaya mata Tun farkon sanin xancen Da tayi , Sarai maman nashi ta fahimci son Kai yake shirin yi Ta kuma ji haushi Duba da yadda ya yanke shawarar a cikin amaryar na farko ba tare da ya tuntubi kowa ba , Shiyasa yanzun tace wa uwargidan ta yi shiru ta barta dashi xatayi Maganin shi . Yaso ya Zille , Tabbas yanason ‘danshi fiye da komai Amman kuma still yana duba khadijan shi Yaso ace ita ta Haifa mishi wannan babyn da tuni ya bayar willingly without thinking twice. Ganin khadijan nashi da maman shi Sun fara ganin kmr dama ba adalci yaso yi ba yasa kawai ya hakura ya bayar da rabin dukiyar tashi a danshi Ba dan yaso ………… Wani ikon Allah Tun daga wannan lokacin abubuwa suka sauya , Gabadaya soyayyar Imam ga Khadija tayi rauni , tama Lura kmr haushinta yake ji dan Ko kusa dashi bayaso taje . Itama uwar gidan nashi ba wani sake mata yakeyi ba , Amman de ya fi tsanar amaryar akanta . Inde kaga yana dariya tou ya dauki babies dinshi ne Amman baya ga haka ba shi da wata walwala . Tashi daya ya dawo wani iri mur’da’d’den mutum abun tsoro ma Dan har ga Allah itakam amaryar zuwa yanzu ya fara bata tsoro . Ga Hantara kyara da tsana wadda yake gwada mata kiri kiri. Ga wani irin masifaffen kishinta da yakeyi ,Ko dan yasan ya dena Bata attention maybe Shiyasa yake tunanin zata kula wani a waje . Gaba daya tashi daya duniya tayi mata zafi Da ga khadija se larai ne Kawai take dasu ta ke dan hira dasu ta ji sauki Se ko er jinjirar yarinyar ta Wadda ta Lura ‘Kiyayyar da Imam din yake mata ta fara shafar yarinyar da Bata ji ba Bata gani ba . Kafin ya ‘dauketa sau daya Ya dauki dan uwanta sau ashirin . Bata da yanda zatayi Tunda bama tasan laifinta gareshiba Ballantana ta gyara , Shiyasa ta dukufa addu’a Take kuma ‘ko’kari wajen holding kanta together , Amman fa ko ba ka santa tun farko ba Kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin tsananin tashin hankali . ……….. Bayan shekaru talatin …. MANNUBIYA O2 NA Humayrah Bulama ELEGANT ONLINE ✍️ Bayan shekaru talatin …… AUCLAND….. A Can tsakiyar ruwa Keb’ance daga dukkannin gidaje da al’ummar garin Na hango wani ha’da’d’den yatch me kyawun gaske. Kwata Kwata yatch din ba zai ‘dauki sama da mutane 70 ba Kasancewar ba wani girma gareshi ba.Walwali ta kalolin fitilun da suke haske ta cikin yatch din ne zai sa ka fahimci party akeyi. Tun daga nesa dasu ka’dan zaka san ba k’aramin ki’da ne ke tashi a cikin yatch ‘din ba , In kuwa ka k’arasa sai kanka ya fara juyawa, muddin ka kasance ba ma’abocin Son ki’de ki’de bane. Sama da k’asa ne kamar girman madaidaicin duplex. A k’asan ake gudanar da event d’in,wanda yanayin decoration da cakes din zai sanya ka fahimci birthday party ne …. Wata farar budurwa da ba zata gaza shekaru ashirin da bakwai a duniya ba sai wasu en mata guda uku ne a keb’antaccen d’akin dake a saman yatch d’in yayinda dukkan nin al’ummar cikin yatch d’in En mata da samari ne a ‘kasan sun cika Babban keb’antaccen parlourn tab harma da er varendar waje banda ki’da da rawa ba abunda ake yi, Wine rack na nan cike da kwalabe duk kalar abunda kake da buk’ata zaka je bar tender ya tsiyaya maka ka kora ta ma’koshin ka . Tana kwance Akan make ken Gadon dake a ‘dakin sanye da wasu matsatstsu Riga da wando, Rigar ko cibiyar ta Bata gama rufewa ba Fara ce tass Dan hasken fatar ta kamar na turawa tarr!! Ba za a kirata da kyakkyawa ba Ba kuma mummuna bace ba Tana da doguwar fuska, madaidaitan idanuwa dogon hanci da matsakaicin baki Gashin ta straight girarta a cike yake kamar yanda gashin kanta shima yake a cike taf ga kuma tsayi dan har ya kusan kaiwa gadon bayanta Doguwa ce Sosai sannan siririya ce ta gaske. ‘’KAUSAR!!!!’’ ‘Daya daga cikin en matan ta Kira sunanta,cikin nutsuwa sannan a hankali ta lumshe idanuwan ta ta bu’de Kafin cikin asalin jan aji da yau’ki ta mi’ke ta zauna a kan gadon. Sun san halin ta da yau’ki da rashin son takura shi yasa kowa ta ja bakinta tayi shiru basu sake tanka ta ba. Ta fi minti biyar tana ta yamutse fuska Kafin ta mi’ke kawai ta fad’a toilet. Ta jima Sosai a cikin ban’dakin Kafin ta fito . Kallon gadon ta yi Sakamokon ‘karar da taji wayoyinta data bari a kan gadon suna yi . Ko kallon wayoyin bata sake yi ba, ta nufi ledar da ta hanga dake nan gaban dressing mirrow tun d’azu, tana zuwa ta zaro wata 3 quarter gown black ,Ta jefar da ledar a k’asa tare da ragowar abubuwan ciki . Ba abinda ta shafawa fuskarta sai jan jambaki daga nan ta zura gown din ta feshe turarurruka,Ta saki gashin ta data d’aure gudun kar ruwa ya Jik’a mata shi garin yin wanka. Bata kalli kowa a cikin y’an matan da suke nan a shirye tun d’azu suna jiran ta ba… wayarta guda d’aya kawai ‘dauka ta kama hanyar fita , Suna ganin Haka suka mara mata baya duk suka fice kusan a tare …. Suna sauka ‘kasan wajen ya kara’de da ihu, masu happy birthday kausar’ ma suna yi , murmushi kawai tayi ta shiga hugging frnds d’in nasu da suka taru ana gaisuwar yaushe gamo Anayi suna bata gifts ita kuma tana mik’awa Frnds ‘dinta da suka sakko tare. Tunda ta sakko suka ha’da ido Amman sai ta ‘dauke Kai tayi kmr ma bata ganshi ba,bata ma yarda ta sake kallon direction d’in inda ta gansu shi da Abokanayen sa biyu ba ….. Direct inda babban cake ‘dinta yake ta nufa taje tayi cutting daganan tayi wa kowa godiya tare da basu uzurin ‘tanada important interview ‘ Daga haka tayi excusing kanta ta juya ta nufi sama inda ta fito , Party kuma ya ci gaba da gudana. Wata mahaukaciyar Dariya d’aya a cikin Abokansa ya kece da ita kafin yace ‘’Tunda nake Ba a ta’ba yin disgin daya bani tausayi da dariya at the same time kmr wannan ba ‘’. Kallon shi ‘dayan Abokin nasu ya yi Kafin yace ‘’Dude‘’!. Yana ‘dan mishi alamun ya yi shiru mana sannan ya nuna mishi YASIR da ido wanda kenan zaune a tsakiyansu su biyu. Tun lokacin da kausar ta sakko ya ‘dauke wuta, Ta saba wula’kanta shi dama those days. Amman Tunda suke Bata ‘taba mishi abun da yaji haushi irin wannan ba dukkan mutanen nan shi ya kwaso su wasu daga Nigeria wasu daga k’asar da suke duk shi ya musu ku’din jirgi saboda yana so taga frnds d’insù na school Altogether on her special day a inda relationship d’insu shi da ita ya soma sannan kuma favorite place ‘dinta. But it’s like Bama tayi farin ciki da surprise ‘din ba ko ka’dan. Wats wrong with kausar ne wai kwana biyu? Ya yi wa kanshi tambayar ran shi yana sake dagulewa . Ahankali ‘dayan abokin nasu yace “Yasir Magana ta gaskiya Yarinyar nan abun nata ya fara yawa You are better than this Pls move on, ga girls nan kala kala se wadda….” Kallon da yaga Yasir d’in ya d’ago yana mishi ne ya sanya shi kasa cigaba da maganar tashi, a hankali ya ‘dan sunkuyar da kanshi sai kuma ya juya ya bar wajen gaba d’aya dan tabbbas yadda yaga idanuwan Yasir d’in sun ka’da sun yi ja tsaf zai iya juye haushin sa akan sa. Shi kanshi ‘d’ayan Abokin nasu da yake ta mishi dariyar shak’iyanci shiru ya yi ya kauda kai be sake yun’kurin cewa komai ba….. Ya jima a wajen Kafin ya mi’ke ya nufi sama inda Kausar ‘din take. Yana k’arasawa bakin ‘kofar ‘dakin ya hango ta zaune gaban madubi ta sunkuyar da kanta sosai, kmr ma kuka take yi, A hankali ya ja ya tsaya a bakin ‘kofar yana k’ok’arin fahimtar yana yin ta daga nan inda yake tsaye “spying on lady are signs of a very poor manner !!’’ Yaji muryarta cikin yana yin kuka . Numfashi ya fesar Kafin ya Kutsa Kai ya ‘karasa cikin ‘dakin Idanuwanshi akanta ,duk Tsananin b’acin ran da yake ciki sai Ya ji yana Raguwa a hankali a hankali. A gefenta ya je ya tsugunna Kafin ya mi’ka hannu ya kamo nata, Bata kula shi ba sannan bata hana shi ba, tana jin shi ya shiga murza tafin hannun nata , a hankali cikin kwantar da murya ya ce ‘’Kausar abinda kika yi min yau banji da’din shi ba, I made this surprise for you Ga friends dinmu wasu na tabbatar rabon ki dasu tun a makaranta,amman sam it’s like kmr ma kashi na ‘debo na zuba miki,Ko arzikin kallo ban samu da ga gare ki ba,ballantana in ji how you feel about the surprise, Sannan nace miki tare zamu yanka cake but bama ki tsaya kin jira ni ba, u just went ahead and cut it by urself In wani abun nayi miki let’s work it out Wannan attitude d’in naki fa is a threat to our relationship,ba kya helping kwata- Kwata Sai de k’ok’arin lalatawa. I’m the only one trying fa anan kausar I ‘m doing a lot , Ko iyaka wannan birthday d’in Just to see u happy kinsan nawa na kashe kuwa?” Sai yanzu ta fesar da Numfashi Sannan ba tare da ta kalle shi ba ta mi’ke ta dan ja hannuta da ke cikin na shi da ‘dan ‘karfi ta bar wajen cikin takun ta ta nufi bed,Jakarta kawai ta ‘dauko ta zaro check ta fara neman biro. Tunda ta fara rubutun ya fahimci me take shirin yi dan Haka ya mi’ke shima ya ‘karasa da hanzari ya wafce takardar daidai nan ita kuma ta gama rubuta mishi ku’din . Cikin b’acin rai ya kalli Takardar Sannan ya maida dubanshi Gareta yace ‘’Cewa nayi ki biyani???’’ Ahankali ba tare data kalleshi ba Tace “Nop!,But Ina buk’atar space So zan yi ko me ne naga ya Kamata in dai zaka daina wannan jarababban naging din naka ‘’, Cikin takaici ta ‘daura da cewa ‘’Kuka fa ka shigo ka ga Ina yi Amman kawai kai matsalar ka ka sani,har ga Allah ka takura ni dayawa Yasir I feel suffocated around you !.’’ ‘Dan zaro ido yayi har zai yi magana da ‘dan ‘karfi Sai kuma ya runtse idanun shi da tafin hannunshi da ‘karfi, Ya d’an jima a haka Kafin Ya bud’e idanun Ya d’an sake matsawa inda take Tukunna A hankali cikin tsananin mutuwar jiki Yace “Kausar, Nagging na takura ki?” Shirun da yaga tayi ne ta kauda Kai Ya sanya shi sake matsawa Sosai gareta A hankali Ya ce ‘’Still,Akan incidence ‘din nan ne ki ke jin haushi na Ko?” Sai a sannan ta d’ago idanuwanta ta kalleshi A hankali itama tace ‘’Yasir Bana son yawan magana ayanzu Amman sai surutu kake saka wa Ina yi,In Kaga dama kaje ka nemi duk en matan duniyar nan, na fad’a maka ba damuwa ta bace ba. Sannan in dai cikin ka zai iya ‘daukar dukkan nin giyar duniyar nan Pls Fell free ka juye don wannan ma ba Matsala ta bace ba, All I want All I need daga gareka Shine space don Allah Yasir ka’dan ka ‘kyaleni for some time Ina bu’katar space.’’ Tana gama fa’din haka Ta juya ta shiga toilet da Sauri Ganin Yana shirin ruk’ota. Aikuwa har bakin kofar toilet din ya je yayi ta faman knocking Yana lallashin ta amman Sam ta’ki ta tanka shi. Ya jima tukunna da k’yar yaja k’afafuwan sa ya bar ‘dakin yana mamakin abun da yake damun kausar. Tun suna da shekaru 14 a duniya suke soyayya Yakuma San Tana tsananin ‘kaunar sa. Kawai dai be San me Ya faru kwana biyun nan gaba d’aya ta hargitse ba It’s like ko kallon shima Bata son yi ….. …. Sai da ta ji fitar sa Tukunna ta sauke wata nannuyar ajiyar zuciya ta bu’de k’ofar ta fito , Ba wai Bata son Yasir kwata kwata bane ayanzu m Tabbas akwai ragowar burbu’din soyayyar sa a cikin zuciyar ta har yanzu , Tun suna yara tasan Tana crushing Akan YASHJUB But Bata taba Sanin soyayyarshi zata iya yi wa zuciyarta mahaukacin kamu ba Sai da ta Ganshi after 10 years Sannan bayan soyayyar ta gare shi ba ta inda zaka ha’da yashjub da Yasir Kyau ilmi class ha’duwa Uwa uba ku’di Yashjub yafi Yasir ta ko Ina . Tabbas ta san zata sha fama . Ta san Da wuya Yasir ya ha’kura cikin sau’ki Sannan da wuya yashjub ya yarda cikin sau’ki ga kuma iyayensu wanda ta san ba ‘karamin rikici zata kunno ba,Amman yata iya ? Bata jin tanada sauran numfashi a gaba Muddin rayuwarta babu yashjub a ciki…. Duk yadda yaasir ya so daurewa kasa wa yayi A yanda yake jinshi tsaf zai fashe da kuka , Shiyasa Be kula kowa ba haka yazo ya wuce jamaar wajen ya shiga wani ‘dan karamin ‘daki anan ‘kasan , Yana shiga ko ida rufe ‘kofar beyi ba Hawaye ya wanke mishi fuska . Duk wani abu daya Ke breakable a cikin ‘dakin seda ya fasa shi . Wanda hakan ne ya janyo hankalin jamaar daya bari Har ta Kai ga Abokanan shi guda biyu shigowa Dama a yadda sukaga ya sa’k’ko sunsan ba lafiya ba Dakyar dayan ya kwace kwalbar hannu shi da tayi mishi jina jina Ya yar Cikin bacin rai yace ‘’Haba Yasir Kana hauka ne? Wai duk Akan mace kake wannan jahilcin A haka kana mata naci zata soka ? In Bata sonka ka hakura mana A Ina aka taba so dole ? Cikin tsananin fushi Yasir din ya sha’ko wuyan shi Wanda hakan yasa dayan Abokin nasu ya matso ya fara lalla’ba shi Dan ya Lura baya tare da hankalin sa Da kyar kuwa ya samu ya ya cika shi Abokin nasu ya juya yana wani irin huci da sau’ke ajiyar zuciya a jejjere Cikin tsananin ‘dacin zuciya yace wa ‘Dayan Ka shirya komai Kowa ya watse………. B U K Kano Bayani tu’kuru lecturer din yakeyi Gaba daya hankalin ‘daliban yana kan shi , Yanda ajin yayi tsit Sannan kowa ya nutsu ne Zai sanya ka fahimci Tabbas Ana Jin tsoron lecturer din, Kowa ya nutsu kana gani kasan babu me bukatar yin laifi. Tunda ya shigo ajin ya Lura da ita da kuma yanayinta Farar budurwa ce Sede ba kal ba Amman yanayin farin na ta me tsananin kyau da daukar hankali ne , Daga zaunen da take zaka fahimci tanada tsayi Sannan Bata da jiki amman baza ka kirata da er siririya ba Sakamokon ‘kirar da Allah yayi mata , Kyakkyawa ce ajin farko Dan ko mahaukaci in ya kalle ta se ya ‘kara …. Yauma kmr kullum bayajin hankali da tunanin ta suna ajin , Don Tun dazu Yaga Ta zabga uban tagumi da hannu daya Yana shirin ‘dauke idonshi daga kanta Yaga hawaye ya fara zubo wa ta idanunta , Wanda ita kanta yasan Batasan hawayen ya taho ba har seda ya samu nasarar sauka akan kumatunta tukunna taji dan haka da sauri ta sunkuyar da kanta ‘kasa , Kawai kuma seta fashe da kuka mara sauti . Har akayi lecture din aka gama aka ‘dauki attendance bama ta San an yi ba Saboda yau zage wa tayi ta zubar da hawayen da suka tarar mata a ‘kirji Suke bada gudunmmawa wa ‘karuwar ‘kuncin ta , Ta kuwa dan ji sanyi ba kadan ba ….. ‘’MANU!,xamu wuce ‘’ Muryar budurwar datake xaune a gefen ta ta katse mata hawaye da

Chapter 2 of 32