Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ajiyar zuciyar da take sauke wa a jejjere . Da sauri tasa hannu ta goge fuskarta , Kafin ta ‘dago , Ko kallon su Bata yi ba tadan matsar da ‘kafar ta gefe domin su samu damar wucewa , Tanajin dayar tace ‘’Allah ya kyauta Kowa de yanada damuwar nan daurewa kawai akeyi ‘’. Bata da lokacin su Dan zuwa yanzu abunda yake kanta ma ya ishe ta yayi mata yawa Tunda gashi yau har da kuka tukuru a aji tayi . Hakanan ta ‘dan juya ta sunkuya ta dauki ko’da’d’diyar Jakarta Ta mike Bata yadda ta kalli kowa ba haka tanufi ‘kofa. Hakanan ragowar students din suka bita da kallo wasu ta na basu tausayi wasu Tana basu mamaki Dan tashi daya in ka kalli fuskarta xaka san kuka tayi Gaba daya duk se taji wani iri Ganin kallon da ake mata , Taji saukin ra’da’din zuciyar ta tabbas Amman kuma duk se taji takaicin kukan da tayi a aji dan haka Tana fita ta wuce Ko ABBAKAR Bata tsaya jira ba . Tana fara tafiya ta ji yo shi ya biyo ta yana kiran ta Manu ! Manu !! Manu!!!. Se da ta dan gyara fuskarta wai ita ala dole kar ya gane kuka tayi Tukunna ta ‘dan tsaya ba tare da ta juya ba . A haka ya ‘karaso ya sameta yana dan haki Da alamun ya ‘dan ha’da da gudu ne yace ‘’Hope dai Bakiyi attendance ba Kar sir najeeb yaga sunanki biyu Naga kin sunkuyar da kanki Su kuma na gefen ki dasuka gama basu tashe ki ba Shiyasa na rubuta miki ‘’ Jinjina kanta tayi alamun yes Sannan tasa hannu ta ‘dan goge fuskarta Sam taki yarda ta kalleshi ita ala dole kar ya fahimci kuka tayi Ahankali tace ‘’nagode abbakar ‘’ Murmushi ya yi Kafin yace ‘’oh com on Manu Nasan fa kuka kika yi ’’ Girgixa Kai tayi kafin tace ‘’Banyi komai ba ‘’ Murmushi yayi me ‘dan hade da dariya Kafin yace ‘’Look at me ‘’ Bata ‘dago ‘dinba Dan haka ya zagayo ya tsaya a gaban ta ya tsare ta da idanu Yana kallonta kawai kafin A hankali ya samu bakin shi ya sake futar da Sentence din ‘Manu look at me ‘ Yanzun ma Bata ‘dago ba Har Wani ‘dan ajin su yazo yace ‘’Yauwa ku nake nema Sir Najeeb yana kiran ku ‘’, Har yayi gaba se kuma ya dawo yace ‘’ I mean ,yana Kiran ta dan ita yace in Kira but nasan tare zaku je Shiyasa nace muku yana Kiran ku ‘’ Ya fadi hakan yana dariya kasa kasa Sannan ya ‘daura da cewa ‘’Ku yi sauri yana ajin har yanzu’’ Kafin yace musu ‘’se anjima ‘’ Daga haka ya juya ya wuce .. Addua MANUBIYA tashiga yi Allah yasa ba wani abu serious bane ba Dan inde kaji kiran sir Najeeb Tou ba alkhairi bane , Dan haka tashi daya ta ‘dan tsure Wanda hakan yasan ya har Bata ma Jin Abbakar har seda ya sake cewa ‘’Manu. Kar yaji haushi fa ‘’ Tukunna suka jera su biyun suka nufi ajin da suka gama lectures din … Waya suka sameshi yanayi dan haka suka tsaya jira , Yafi minti hudu Kafin yayi sallama da Wanda yake wayar tukunna ya mike ya fara harhada takardun shi .. Yana hada takardun ba tare daya kallesu ba yace ‘’Next time ,In kinsan kuka da rashin maida hankali xakiyimin a aji Karki sake shigowa ‘’ Daga haka ya sa kai ya fice , Ko hak’urin da suka fara bashi bai tsaya ya saurara ba…. MANNUBIYA O3 Na Humayrah Bulama ELEGANT online ✍️ Yana fita Abbakar ya fesar da iska yace ‘’Allah ya taimake mu, We got lucky’’. Dan tabbas shi kan sa ya ‘dan tsorata kuma ya san ba ‘karamar sa ‘a suka ci da ya bar Manubiya a iya warning bai ce kar ta sake shigar mishi aji ba.” A hankali itama Manubiya ta fesar da iska,bata gama tunani ba ta ji ya ce ‘’Nima ina son ganinki, Bismillah zauna.” Ya fad’i hakan yana nuna mata wajen zama Sannan shima ya nemi seat ya zauna dan yanzu ba kowa a ajin. Shiruu tayi kamar baza ta zauna ‘din ba, sai kuma ta nema seat ‘din kusa da ita row din farko taja ta zauna Kafin tace ‘’Ina jinka.” Cikin rashin jin da’di yace ‘’Manu,bana jin da’din b’oye b’oyen da kike yi min kwana biyun nan, In akwai wata matsalar da ban san da ita ba Talk to me, ki gaya min mu nemo mafita mana, Ko kin dena trusting ‘dina ne?” ya Kara’she tambayar tashi a hankali yana mai kallon ta . Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce ‘’Ba haka bane.’’ Cikin tarar numfashin ta yace ‘’To yaya ne?’’ Girgixa kai kawai ta yi tana jin wani takaici yana sake lullu’beta, kafin tace “Kaka mallan ne yake so ya b’ullo da sabon issue.” A hankali ta ‘dan sauk’e ajiyar zuciya kafin tace ‘’Sannan Baraka ta gaishe shi Sai kuma ta ‘dan yi shiru , chan kuma tace ‘’kaka mallam ne yace wai in bar makarantar In yi aure.” Da sauri Abbakar yace ‘’what? Saboda me wai?” Ahankali tace ‘’Nima ban san dalilin sa ba , Kawai yaga kwana biyu ciwon Inna ya motsa shine yake son sake d’aga mata hankali ita da Baba,In ba haka ba meye na ‘bullo da wani case d’in? Ai y’a san Baba bayaso ace baza mu yi karatu ba,kuma ya san baya son yawan yin jayayya da su.” ‘’Ya kamata ayi wani abun akan wannan tsohon fa ‘’. Abbakar din ya fa’da cikin rashin jin da’di, ‘’me Baba yace ?‘’ Ya jeho mata tambayar a jere. Cike da damuwa tace ‘’Shiru yayi ,kuma ni harga Allah ina jin tsoron shirun na sa , Ina Jin tsoro kar ya amince kasan shi bayason hayaniya dasu.” Da sauri Abbakar yace ‘’ Bana jin Baba zai yarda su hana ki karatu, No matter wat ‘’ Cikin gyara zaman sa da bata dukkan nin attention d’in sa Ya ce ‘’Ki nutsu ki daina d’aga hankalin ki Pls,ki kwantar da hankalin ki kar ki damu inshaaAllah sai kinyi har PhD ,karki bari tsohon nan ya hanaki walwala ya saka ki a damuwa , kalli yadda kike kuka a aji fa.” Ya k’arashe maganar cikin rashin jin dad’i. Jin jina kai kawai tayi Daga haka ta fara ‘ko’karin mi’kewa . A hankali yana kallonta yace ‘’ Ita kuma Baraka mai tayi?” Sai da ta ‘dan kalle shi da kyawawan rinannun idanuwan ta tukunna ta kauda kai gefe ta ce ‘’Ba komai ‘’ Daga haka ta mi’ke tsaye . Da sauri shima ya mi’ke ya ‘karasa gareta sannan yace ‘’Ya jikin Inna?An ha’da kud’in kaita asibitin ?’’ Da sauri tace ‘’An ha’da ‘’ daga haka ta juya ta nufi ‘kofar fita . Tun dazu dama ya riga ya gano a inda main problem d’in daya saka ta kukan yake , Yanzu kuma yadda tayi ya tabbatar mishi …. Ya riga Yasan ko me zai yi bazata yarda ta kar’bi sisi a wajen sa ba , Sannan ya fahimci Baraka ta kuma yin abunda tafi komai ‘kwarewa akai wannan karon ma Duk yadda akayi ta ‘bullo da wani abun ta amshe ku’din hannun Ya musbah kakaf , Ya rasa gane dalilin daya sanya Baraka take wannan rashin imanin ,baisan meyene a kanta ba Bai kuma san dalilin daya sanya Baba da Ya musbah suke biye mata suke ‘daga mata k’afa take tsula duk tsiyar data ga dama ba . Ganin dayayi Manubiya har ta fice ne yasa shima ya bi bayan ta da ‘dan sauri ,a ranshi kuwa ya riga ya gama yanke shawarar abunda ya kamata yayi wajen taimaka mata a samu a kai Innar Asibiti,Satin ta kusan ‘daya tana fama ciwon ta ya motsa ya kamata ace taga likita . Yana fita ya hango ta har ta ‘dau hanyar da zai sada ta da gate , Dan haka ya k’arasa suka nufi gate din tare shi da ita . Ba gida zai yi ba shiyasa basu tafi tare ba amman sai da ya sanya ta a adaidaita sahu ya biya ku’din kmr kullum tukunna ya juya shima ya tari tashi adaidaita sahun ya shige yayi gaba. Anguwar su ‘daya da Abbakar shine best frnd d’inta tun daga secondary skul suka fara abota sosai hakan ya sanya tun suna yara suke shiri , Abokanayen sa har dariya suke ma sa , tun yana ‘dan mitsitsi yake wanke k’afa ya tafi gidan su Manubiya wasa , tun Inna tana hanawa har ta zo ta daina . Har kawo yanzu kuwa shi ka’dai ne Abokin ta Tun da ita Ba kula en unguwar su take yi ba saboda munafurce munafurcen su , a makarantar ma ta’ki yarda tayi k’awaye ana son ta sosai da ‘kawance kawai dai itace ta’ki yarda , Duba da yadda yaran suke en gayu a ganin ta In ta biye su sai ta kasa godewa ubangiji na na’imomin daya yi mata gashi kullum in aka je cafeteria sai dai suyi ta biya mata , bawai suna complain bane kawai dai itace ba ta feeling comfortable kuma ta san yau da gobe sai Allah shiyasa ta ke dodging . Tun suna mata naci tana zille wa har suka ha’kura suka rabu da ita .Su suna ganin girman kai gare ta Ita kuwa a ganinta bai kamata ta ‘daura wa kanta abunda yafi k’arfin ta ba , Matsalar ta ma ta isheta . Tana wannan tunanin mai Adaidaita sahun ya k’araso cikin layin nasu dake a Anguwar ‘Gadon’Kaya’, Ita ta nuna ma sa ‘kofar gidan yayi parking daga haka ta fito ta nufi ‘kofar gidan bayan tace mishi ta gode . Kallo ‘daya zaka yiwa gidan ka san cewa ya da’de kuma yanayin ginin zai sanya ka fahimci bai ma san ma menene renovation ba , Katangar gidan both side sun tsatstsage yayin da fentin ya goge gabad’ayan shi baka ganin komai sai jar k’asar bulo din ginin ta k’asa k’asan ta sama kuma ragowar farar k’asar fentin da bata gama gogewa ba Sai zanen yara na shirme wanda akayi da bak’in gawayi . Normal k’aure ne a gidan sai dai shima ya ji jiki matuka …… Tana k’arasawa jikin k’yauren ta kama ta tura k’ofar ta kutsa kanta cikin gidan ,Dama tun daga waje za ka gane babban gida ne ,sakamokon yanayin tsayin katangar both side .. Ta wani dogon soro tabi kafin ta k’arasa ainihin cikin farfajiyar gidan A ta farko farko gefen dama babban kitchen d’in gidan yake wanda murhu da kurfeti suka cika shi taf Wanda hakan zai nuna maka kowa girkin shi yakeyi a daban. Farfajiyar asalin cikin gidan kuwa d’auke yake da part part wajen guda takwas , Wasu sabbi k’al ginin zamani wasu tsofaffi tukuf ginin k’asa Wasu manya ne domin ko baka shiga ba zaka fahimci wajen d’akuna uku ne ma a ciki da parlourSai kuma masu ciki da parlour,Yayinda wasu kuma d’aki daya ne kawai sai band’aki….. Ginin dayafi ko Wanne tsufa da k’ank’anta ta nufa ,tana zuwa dai dai bakin k’ofar ‘dakin ta sa hannu ta d’aga labulen ta shiga ciki da sallama. Babban d’aki ne Sosai Da manya manyan taga guda biyu suna kallon juna sai k’ofar bandaki data ke a chan kusurwar d’akin . K’atuwar katifa ce kawai a yashe a gefen d’akin, Sai babban wardrobe d’in katako ,Laidar d’akin bata wani yage ba ammanfa taji jiki dan tayi laushi matuk’a, Kana gani kasan takatsantsan da kula ne ya kawo ta war haka ba tare da ta fatattake ba . Wata farar budurwa fara k’al wadda bazata wuce shekaru sha bakwai ba ce zaune a kan katifar gefen wata dattijuwar mata tana yi wa matar datake a kwance fifita, Tashi d’aya yanayin matar zai baka tausayi dan kana ganin ta zaka san tana jin jiki matuka . Setin su kuma wani dattijon tsoho ne zaune da wani Yaro a gefen shi wanda ba zai wuce shekaru sha d’aya ba . Kai kana ganin tsohon kasan ba wai shekarun shi ne suka kai ya Kai haka tsufa ba Kawai dai yanayin rayuwa. Fuskokin su gaba ‘daya babu walwala Kowa ka kalla a cikin su yayi jigum bama su san Manubiyan ta d’aga labulen ba saida sukaji sautin muryarta data shiga da sallama . Jidda wadda ke a zaune kusa da Inna ce ta d’ago ta kalle ta Ahankali tace ‘’har kin dawo ? Sannu da zuwa.’’ Jinjina kai kawai Manu ta iya yi kafin ta juya ta kalli Muhsin wanda yake mata sannu da zuwa shima ta yi ma sa d’an guntun murmushi ,ahankali ta k’arasa ta durk’usa a gaban Baba tace ‘’Baba Ina wuni.’’ Kmr ba zai yi mata magana ba sai kuma yace ‘’Mai yasa baki ‘dauki kud’in motar dana ajjiye miki ba? Bana ce miki munada ku’din abun karyawa ba? Mai yasa kike da taurin kai ne?’’ ya jero mata tambayoyin a jere kafin ya ‘daura da cewa ‘’Ce miki akayi nan da b.u.k ‘din tafiyar wasa ce?” Ya k’arasa tambayar ta sa ta ‘karshe cike da rashin jin da’di da takaici . Ahankali ta sunkuyar da kanta ‘kasa Tace ‘’Kayi ha’kuri baba bazan ‘kara ba .’’ Sai da ya’dan fesar da iska tukunna ya kauda kai gefe ya ci gaba da tunanin dayake yi kafin ta shigo . Su Jidda ta juya ta kalla kafin tace ‘’Ya jikin nata‘’? Dakyar sai da ta had’iye wani abu daya tokare ma ta a ma’koshi tukunna tace ‘’Da sau’ki ,Alhamdulillah .’’ Ahankali tace ‘’Allah ya ‘kara sauki.’’ Kamr muhsin zai fashe da kuka haka ya ‘dago ya kalli Manubiyan kafin yace ‘’Adda Manu ,sai da fa ta kuma suma da kika tafi makaranta dazu’’. Shiruu tayi chan kuma sai ta sunkuyar da kanta ‘kasa , Wanda hakan ya bawa hawaye damar fara gangaro mata , Haka ita ma Jidda ta sunkuyar da kanta ‘kasa ta fara nata kukan , Ganin hakan ne ya sanya shima Muhsin ya fara nashi kukan. Haka suka tusa Baba a gaba kowa yana hawaye . Ahankali ya zaro wayar sa daga aljihu ya danna kiran Ya Musbah , Kamar dazu ,yanzu ma wayar a kashe dan haka ya ‘dago ya kalla Jidda bayan ya maida wayar cikin aljihun malun malun din sa ,yace ‘’Maijidda kikace dazu yace miki Mu jira shi zai zo ko?’’ Sai da ta ‘dan yi shiru tukunna Ahankali ta gyada mishi kai sannan tace ‘’Eh, Baba.’’ Tsaki yayi daga haka ya mi’ke tsaye yace ‘’Muhsin taso muje .’’ Dasauri Jiddan tace ‘’Baba ka bari ni in sake komawa in dubo sa ba sai kaje ba.’’ Kallon ta yayi kamar bazai ce wani abun ba Sai kuma yace ‘’kar ki damu yanzu zamuje mu dawo InshaaAllah Ina son ganawa da shi .’’ Daga haka ya juya ya fita Bayan ya nunawa manubiya gurasar ta da suka ajjiye mata a cikin kwano yace ta tabbatar ta ‘dauka taci . Yanayin yadda ya mi’ke , da kuma tafiyar ta sa ce zai sanya ka fahimci ashe k’afa d’aya gare sa , Domin tashi ‘daya zaka gane ‘dayar ta roba ce . Tare suka fice shida muhsin wanda ya fita da sauri , domin shi kan sa yaron hankalin sa a mugun tashe yake,Allah Allah yake a san yadda za a yi a kai innar tasu asibiti dan jikin nata ya tsorata kowa Babba da Yaro . Suna fita Manubiya ta mi’ke ta cire hijabin jikinta , Daga haka ta karasa inda su Innar suke itada jidda, Sai da ta tabbatar innar bacci takeyi tukunna ta kalli Jiddan tace ‘’Mai ya faru dazu da kika je gidan , kin gan sa ?’’ Ahankali Jidda ta share hawayen da suka xubo mata Kafin ta shiga koro mata yadda sukayi Da yadda ya Musbah yace kawai tazo gida su jira sa , Gashi kuma har yanzun bai zo ba . Shiruuuuu Duk su biyun sukayi Ko wacce zuciyar ta babu dad’i Suna kuma tunanin a ina zasuje su samo ku’di Dan sun san tunda ya musbah ya fara wasar er buya dasu Tou shima bashi da yadda zai yi ne. A take zuciyar Manubiya ta fara bata shawarar ta cire kunya kawai ta gayawa Abbakar gaskiya,tasan zai taimake su…. A bakin ‘kofar gidan sa su Baba suka hango sa , in ba an gaya maka ba bazaka yi tunanin yara yi auren fari ba, fari sol kyakkyawan gaske bai cika tsayi ba Amman yanada fad’in k’ashi. cikin sanyin jiki Baba da muhsin suka k’arasa inda Ya Musbah yake Alwallar sallar magrib Dan ta k’arato ,tare da wani makwafci kuma Abokin sa Mai suna ‘ Nafi’u’. Cike da girmamawa shi da Abokin na sa suka gaida Baba. Kafin Abokin yace wa Ya Musbah ‘’Bara in wuce In fara karatun kafin ku kammala .’’ Jin jina kai kawai Ya Musbah yayi Dan gaba ‘daya hankalin sa a mugun tashe yake , gashi yaga Baba sai wani irin kallo yake ma sa wanda ya kasa gane ma’anar. Rashin sanin abun yi da kame kame ne Ya sa shi cewa ‘’Bismillah Baba Mu shiga daga ciki ko ?’’ Sai da Baban ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace ‘’Naa shiga kuwa ?’’ Ahankali Ya Musbah yace ‘’to ko soro ne ka shiga dan Allah Akwai bayanin da nake so Inyi maka ne ‘’. Ba dan Baba yaso ba Ya Kama hannun Muhsin suka bi bayan ya Musbah. Anan soron kuwa ya shimfide musu tabarma Dan ayanzu bai isa shigar dasu cikin gidan ba Yanzun nan makwafcin sa kuma Abokin sa Nafi’u ya gama musu shara’ah da Baraka Saboda kawai Jidda ta zo dazu. Tunda Jiddah ta zo ta ta tafi take ta faman bambami Wai tazo har gida tayi mata rashin kunya Sarai yasan k’arya takeyi Kawai tana neman hanyar da zata bi ta datse zuwan en uwan na sa gidan ne Gaba d’aya Bayan a yanzu kamata yayi ma ace shi yake rik’e da Jidda ko Manubiya….. ‘’Tunanin mai kake yi???’’ Muryar Baba ta Katse ma sa tunani. Ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya Yana shirin yin magana Baban ya sake katseshi ta hanyar cewa ‘’Innar ku har yanzu tana kwance Ba kud’in magani babu na zuwa asibiti Musbahu!kai ne ka hanani aikin k’arfi Sannan kace k’annen ka mata baza suyi Aikatau ba , Badaban haka ba nasan da yanzu mun san yadda mukayi aka kai ta asibiti . Tun shekaran jiya muke tsammanin ka Ka kashe wayarka kuma Kak’i ka yarda kazo inda muke Idan kud’in ba su samu ba ai yakamata ace ka zo ka duba mahaifiyar ka ko ?’’ Ahankali cikin yin kasa da murya Ya musbah yace ‘’Baba, kalli fa k’afar ka bazaka iya aikin k’arfi da ita ba In ka saka mata nauyi dayawa kar muje Itama Kwaya d’ayar data rage maka ya zamana itama ta samu matsala , Su Manubiya kuma ba wai girman Kai bane ya sanya na ce baza suyi aikatau ba A ganina bai kamata ace ina raye muna zaune a unguwa ‘daya Amman ace k’anne na mata wai su zasu na kula da iyaye na,ba. Dan Allah Baba kayi ha’kuri ka bar maganar dakon dakake so kayi da duk ma wani aikin k’arfi , Zan yi k’ok’ari in San yadda zanyi InshaaAllah zan iya kula da kowa . Kud’in ma na nemo bawai ban nemo ba Amman sai jikin baba k’arami yadan mot……’’ Shiru yayi Kafin yaci gaba da cewa ‘’Amman karka damu Nafi’u yayi wa ‘dan uwan da magana kuma d’an uwan yace za’a san yadda za ayi Mu jira shi zai kawo kud’in , Shiyasa ma kaga ban zo ba bana so in zo muku ba tare da kud’in ba , Shi nake ta jira nafi so in yazo ya bani sai inzo a kaita asibitin ‘’. Sai a Sannan Baraka data lab’e musu tun dazu ta shigo cikin soron , Ahankali ta k’arasa inda suke ta zauna Cikin Ladabi ta gaida Baba, Da Kulawa ya Amsa yana tambayar ta ‘ Ina takwaran sa ‘ tace ‘mishi yana ciki yana bacci ‘. Da ladabi muhsin ma ya gaida ita ta amsa Daganan soron ya d’auki shiru kafin a hankali sautin kukan Baraka ya fara tashi . Da sauri Baba yace ‘’Subahanallah Baraka lafiya? mai ya faru ? . Cikin kukan dakyar tace ‘’Ba komai Baba ba komai Kuyi hkr Subuce min yayi.’’ Tana gama fad’in haka ta fara k’ok’arin mik’ewa . Cikin d’an tsare gida Baba yace ‘’Koma , koma Baraka Koma ki zauna’’. Ya Bata umarni ran sa duk babu dadi . Ahankali ta koma ta zauna tana d’an satar kallon Ya musbah wanda ya hade rai Yana ji kmr ya rufe ta da shegen duka. Ahankali Baba ya shiga rarrashin ta, Har sai data yi shiru tukunna yace ta fad’a masa Meke faru wa ,m Cikin yin k’asa da murya tace ‘dama kwanakin baya ne Ya musbah ya karb’i kud’in ta kuma itama kud’in ba nata bane ba Na k’awar Maman ta ne So Maman tata ta biya rabi, amma ta kasa biyan rabi shine k’awar ta ta tace xataje da en sanda ta tafi da ita ‘. Tun jiya take bin sa ya bata kud’in shikuma yak’i ya bata , yanzu gashi en sandan sunje za’a tafi da Maman ta ‘.. Shiruuu Baba yayi da jin batun Baraka , Kafin ya mik’e tsaye ya kama hannun muhsin, Ahankali ya kalli Ya musbah ya ce ‘’Musbahu , in an kawo kud’in da akayi maka alkawari ka bata.’’ Dasauri Ya musbah yace ‘’Amman fa baba..’’ Cikin katse sa yace ‘’Bana son musu Sannan banason ja’inja Ka bata kawai Karka damu zan san abun yi ‘’. Ahankali ya kalli Baraka wadda tayi kalar tausayi yace ‘’Karki damu ba za a tafi da maman ki ba Inada mara lafiya a gida , shiyasa bazan iya bin ki muje inga komai ya lafa ba , yanzu kiyi sauri ki je wajen ta Musbahu zai biyo ki da kud’in InshaaAllah, In basu cika ba ma In na san yadda nayi na ha’da kan en kud’ad’e na kashe wutar gaba na Ki yi min magana sai in cika miki ‘’. Yana gama fad’in haka yaja hannun muhsin suka fice daga soron . Cikin bacin rai ya Musbah ya kalle ta kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya juya ya fice Ya bi bayan Baba ranshi a mugun bace . Yaso ya fahimtar da Baba akan yayi ha’kuri ya karb’a kud’in ya bar batun Baraka Amman furr Baba ya’ki sauraron sa karshe ma fadd’a ya rufe sa da shi Sannan yace ya koma kar Wanda zai kawo ma sa kud’in ya zo bai same sa ba kuma Wallahi in ya sake karb’arwa Baraka kud’in ta kuma ya hana ta ran sa sai yayi mugun b’aci. Ganin yadda ran Baba ya b’aci Sosai ne yasa kawai ya Musbah ya ha’kura Sannan ya ba sa ha’kuri Daganan Ya juya ya nufi hanyar gidan sa . Bai shiga ba direct masallaci ya wuce ana idar da sallar ‘dan uwan Nafi’u ya kawo kud’i kamar yadda yayi alk’awari , Ya musbah Ji yake yi kamar yace wa ‘dan uwan Nafi’un kawai ya bar kud’in ya fasa ranta , Domin yasan in yasa hannu ya karb’a kud’in ya baiwa Baraka To bai san ranar biya ba , gashi yana tsananin jin kunyar Nafi’u Dan yana bin sa bashin kusan dubu d’ari kuma bai san ranar biya ba Yanxu kuma gana d’an uwan sa ya fara hawa kan shi, Dama saboda yaga na asibitin mahaifiyar sa ne Shiyasa kawai zai karb’a . Kamar Nafi’un ya san me yake tunani Ahankali ya dafa Abokin na sa da suka taso tare tun k’uruciya yace ‘’Ka kwantar da hankalin ka Kar ka damu Ko yaushe ne in ka samu kana iya biya ‘’. Sai da ya d’an sauke ajiyar zuciya Tukunna Ahankali yasa hannu ya kar’ba kud’in Wanda ko bai k’irga suba yasan basufi naira dubu goma ba Yaso

Chapter 3 of 32