Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MANNUBIYA O 1 NA Humayrah Bulama Daga k’ungiyar ELEGANT ONLINE ✍🏽 __________________ A shekarar 1990, A garin Kano. A hankali yake tu’kin motarsa k’irar Daewo Nubira. Kamar ba Ya so ya k’arasa inda Zai je saboda yanayin tuk’in na sa daya ke yi a gefen titi a hankali, a hankali. Sannu sannu Bata hana zuwa… in ji malam bahaushe don A hakan ya samu ya k’arasa gidan shi dake unguwar sharad’a. Ko da ya k’arasa bakin gate din bai yi horn ba sai da mai gadin da kan sa ya ji tsayuwar mota ya lek’o Tukunna ya koma da sauri ya wangale gate d’in Madaidaicin flat house d’in. Jikinsa na rawa Sakamakon ganin uban gidan nashi ne ke tsaye a waje. Ko da ya shiga ya k’arasa yayi parking Kashe motar kawai ya yi ya d’aura kanshi a jikin sitiyarin motar ba tare da ya fito daga motar ba. Yafi minti talatin a haka yana tunani shi ka’dai Kafin tashi d’aya gaban sa ya yanke ya fa’di. Ransa ya sake b’aci Sakamokon Jin fitowar ta . Ko ba a fadi mishi ba ya San Khadijah ce ,tunda basu da me aiki a gidan daga shi sai ita sai mai gadi Wanda yake musu har wankin kayansu da guga. Shiruu kawai ya yi yana jin ta ta rufe k’ofar parlourn data bu’de ta fito ta tunkaro motar Da yake ciki a zaune. As he expected, tana zuwa Ta banka’da k’ofar motar da k’arfi. Ko sannu da zuwa babu Cikin fushi ta ce “Shine sai da ka kira Abba ko? Cin fuska da rashin adalcin da ka kusan aikatawa bai isheka ba. Shine an kashe magana an gyara komai zaka wani wuce ka kira Abba, Me kenan kake so Yanzu? So kake ya goya maka baya ko me?” Bata jira Jan numfashi ba a hassale ta d’aura da cewa “Tou bari kaji ,Ko ya Goya maka baya abinda kake so ba zai tab’a faruwa ba Wallahi, Tunda in kana tunanin Abba yana bayan ka ni kuma daddy yana baya na. Ta k’arashe maganar Tata cikin tsananin bacin rai da takaici. Tun lokacin data iso ta fara magana Shima ya Ha’de rai , Fuskar nan tamau kamar bai tab’a dariya ba. Ba tare daya kalle ta ba ya zare key d’in motar Ya d’auki abubuwan buk’atar shi ya mik’e ya fito daga motar. Ko kallon inda take bai yi ba Ya fara k’ok’arin wuceta . Da dan karfi Sannan da sauri Ta rik’o hannunshi Cikin tsananin bacin rai ta ce “IMAM ,Wallahi na fi k’arfin ka wulak’anta ni , Ai so ba hauka bane,bar ganin wai Ina sonka Wallahi idan baka janye maganar nan ba zan maka abinda sai ka yi daka sanin ha’duwa da ita kanta khadijar zan Baka mamaki zan sanyaka ……..” “Sannu Uwarsa” Suka ji Muryar Abba daga sama Wanda ba su san lokacin daya shigo ba ta daki dodon kunnuwansu . Tabbas ,ta sha jinin jikinta amman sam Kishi da Bak’in cikin da yake a kwance a kan kyakkyawar farar fuskarta be Kau ba Sannan zuciyarta banda turnik’i da tafarfasa ba abunda take yi. Ganin yanda Abban ya kafeta da idanuwa yana me K’arasowa inda suke ne Yasa ta d’an sunkuyar da kanta k’asa da sauri kuma ta cikawa Imam din hannu . Abban yana k’arasowa Imam ya durk’usa har k’asa ya gaida shi ,bayan sun gaisa Ya ‘dora da cewa “Abba ai da ka bari mun k’araso Don Yanxu nake shirin in yi wanka mu karaso wajen naka.” “kada ka damu ai Babu nisa Kuma Ina buk’atar yin tattaki din dama” Haka kawai Abban yace Yana kallon khadija wadda take gaishe shi “ ina wuni” Cikin d’an russunawa . Bai amsata ba,ya juya ya bi bayan Imam Wanda ya juya ya nufi k’ofar parlourn nasu da d’an sauri yana ce wa “Bismillah Abba. Da kansa Imam ‘din ya shiga ya kawo masa lemo mai sanyi da ruwa sai ‘d’an snacks a Gefe.” Dan khadija Bata riga ta shiga parlourn ba . Tabbas yanda taga abba tasan ba ze bi bayan ta ba Sannan ba ‘daga mata kafa Zai yi ba yau ,kuma tasan Abban nasu Baya tolerating nonsense da tirjiya . Zata iya cewa Bata tab’a ganin soyayyar ‘ya da uba irin ta Abban ta da sister din ta ba Amman tunda tayi mishi lefi ya fita harkarta Ya yafe ta Yanxu hatta ita kanta Bata San inda yayar ta ta take ba . Ayanxu Tsoron ta daya Shine kar ya goyawa Imam baya kuma ya turje Akan se ta bi ta yarda da abunda Imam din yake so Dan inde haka ta faru Tou wallahi ta shiga ukun ta . Ko da ace ba Imam ta aura ba , Bata jin zata iya zama da kishiya , Ballantana kuma Imam din ne , Ayanda take masifar sonshi Bata Jin xata iya jurar ganin wata ‘ya mace a matsayin matar shi bayan ita .Watan ma kuma Khadija , Yarinyar data san yana tsana nin so Domin ko Satin daya gabata Haka ya fito kiri kiri ya ce mata albarkacin sunan su yaxo daya ne yasanya yake mata raha yake dan kulata ……. Tasan rashin shigarta Akan lokaci Ka iya sake hasssala Abba,don haka ta yi ‘ko’kari ta tsayar da kukan nata da kyar Ta goge hawayen ta Ta nufi parlour itama . Abba yana zaune a kan kujera Imam a gefen shi A zaune a kasa A Haka ta shiga ta samesu , Dan haka itama ta karasa ta zauna a kasa dayan gefen kafar Abban. Ba tare daya kalleta ba yace ‘’Se yanzu kika ga daman shigowa kenan ‘’ Be Bata damar cewa komai ba Ya sake cewa ‘’Inaso ki nutsu kiji abunda xan fada miki yanxu Na farko shawarace Na biyu ma kmr shawarar ce Na uku kuma umarnine Kuma dole kiji, Sannan kiyi . Still be dau lokaci ba ya daura da cewa ‘’In mata uku Imam yace xe k’aro baki da hurumin shiga Kice A’a ‘’. ‘’Ki zauna a matsayin ki Sannan ki yiwa mijinki biyayya ki bashi goyon baya , Ni ma a matsayina na mahaifinki Kiyimin biyyayya ki yi abunda nace ‘’. ‘’Khadija,! Imam ze Kara aure Banason in ji wata matsala ta kuma kunno Kai daga gareki Har ayi auren nan a gama Ina ba haka ba Wallahi …..’’ Kukan data rushe dashi kmr Ana yanka ta ne yasa duk suka xuba mata ido kawai , Suna kallon ikon Allah . Cikin kukan tace Haba Abba Ko Wata na biyu ban gama rufawa a cikin gidan nan ba ace za ayimin kishiya Kuma Kuce inyi hakuri inyi shiru ?, Shi meyasa ba zai hakura ba , Daddy fa yace be yadda ba bayason ya sake Jin maganar. Cikin katse ta Abban yace ‘’That was when daddyn besan cewa ita wachchar khadijan ya fara so ba Kuma itace budurwar sa tun asalin farko ba , Bari kiji tun Kafin shi Daddyn ya fara maganar ku ke da Imam Already Imam yayi min maganar khadija , Maganar aurenki ce ta sanya ya daga kafa Dan haka yanxu Banga dalilin da zai sanya ya fasa aurenta saboda ke a karo na biyu ba Wallahi ‘’. Cikin kuka tace ‘’Abba har fa ciki ta zubar Kuma tsabar cin fuska Har gidan nan ya kawo min ita Lokacin ko sati biyu ban yiba a chan boys quarters din akayi jinyar ta Saboda Bata da kowa , Taya za a hadani kishi da wadda ta gama shigomin gida ta San sirrina Wadda Bata da iyaye Me yawo a titi suna tallan Nono …..’’ ‘’Ya Isa haka ,khadija ‘’! Abban ya daka mata tsawa cikin tarar numfashinta Kafin yace ‘’Tashi ki tafi ki bani guri ‘’ Zata yi magana ya kuma daka mata wata uwar tsawar dan haka taja ta mike ta wuce ta shige daki tana wani irin kuka . Ko da ta shiga dakin ma ta jima tana kukan Kafin daga karshe ta Yanke shawarar Neman ‘Larai ‘ Saboda ta Lura Hatta mahaifiyarta ita ma bayan Abban take bi . Iyayen ta sunada matukar kawaici ta San Imam baya son ta Biyayya ce ta sanya ya aureta, Shiyasa su kuma iyayenta baxasu taba goyon bayan ta ba Saboda Gudun Samun matsala da ‘family frnds ‘d’in nasu . Shiyasa gwara ta nemawa kanta mafita Tun Kafin kawaicin fulanin iyayenta ya cutar da ita . A nata lissafin kamata yayi a ce an barta da Imam ta juyo da hankalinshi gareta , Bawai a hadata kishi da wata chan daban wadda zata zo ta lalata komai ta kuma janye mata hankalin masiyo ba …. Khadija Tana shigewa ciki Abba ya dan gyara zama ya kalli Imam kafin yace ‘’Naji Khadija ta fadi wani Abu wanda ban san dashi Akan khadijan da kake son ka auro ba Ina fatan zaka cemin ba Dede bane ba .’’ Lumshe idanu Imam yayi Kafin ya shafa farar fuskarshi da tafin hannunshi , wanda tayi jajir zuwa yanzu tsabar shiga tashin hankali . Abba. Is his only hope yasan shi kadai ze iya convincing su daddy su barshi ya auri khadija. Abunda yaketa tsoro dama shine kar su san kaddarar data afka wa khadijan dan yasan Muddin suka sani da wuya Abban shima ya yarda Seda yaji Abban ya sake cewa ‘’Imam ,kayi shiru ‘’ Tukunna Ahankali ya bude idanunshi Cikin sanyin jiki yace ‘’am Abba Kmr yanda na gaya maka Khadija Bata da kowa Ita da Y’ar uwarta na sani tun farko suna kawo mana Nono office Se kuma wani Uncle din su data taba hadani dashi Wanda suke a gidanshi , A halin yanzu Shima ya rasu Kuma dama matar tashi azabtar dasu takeyi Tun a lokacin dayake a raye ma . Shiyasa Yana rasuwa ta tartara ta barsu ta yi gaba . Su sunce min Uncle din nasu da Baban su kawai suka sani Ba su taba xuwa garin suba bama su dan garin ba har Baban ya rasu yanxu gashi shima kawun nasu ya rasu . Shiyasa tun a lokacin naso in auri khadijar saboda itama yayar ta miji ya fito mata ta auri wani me mata uku da yara ashirin a layin nasu Amman yace ba zai rike Khadijah ba Nasan zaman ta ita kadai akwai hadari Shi kuma Daddy ya dage Akan sede ayi auren mu da Khadija tunda an Riga an gama magana Ko uzurina be tsaya yaji ba Gani yake yi kamar turjiya nake shirin mishi Shiyasa na hakura A wannan lokacin kmr yanda kace inyi hakurin . Itama ba yadda Banyi da ita Akan ta biyo ni ba Amman tace Zata iya zama ita kadai Ni kuma abubuwa sun sha min Kai A wannan lokacin Ga hidimar biki Ga aiki A wannan tsakan Kanin ne aka samu wani Mara Imani yaje yayi mata fyade Sam ba laifinta bane Saboda seda tayi kwana biyu a asibiti Batasan ma a ina kanta yake ba Tun daga lokacin naki amincewa taci gaba da xama a gidan ita kadai Laifina daya dana kawota nan Nasan be kamata in kawota nan ba Tunda gidan aure na ne Amman banida choice Tunda su daddy baxasu Bari in Kai musu ita Chan ba Ba tare da sunsan wacece ita ba Gashi cikin data samu ata dalilin kaddarar data afka mata Yaxo da matsala Ana yin sati biyu ta fara bleeding muna xuwa asibiti ya zube. Ga rashin lafiya ga rashin safety da shelter, Shiyasa na kawota nan ita da nurse Kuma tunda khadija tayi bincike ta gano asalin gaskiya ta fatattakesu Se da nayi kwana uku tukunna na nemota da kyar ‘’. Shiruu ya danyi Kafin ya daura da cewa ‘’Dan Allah Abba ka duba Lamarin nan Mu taru ni da Kai mu ceto rayuwar baiwar Allah ‘’. ya karashe maganar cikin hade hannuwanshi kamr xe fashe da kuka . Numfashi Abban ya fesar Bayan dogon Nazari Kafin ya kalli Imam din yace ‘’Zan ha’daka da driver gobe ku je ayi duk wasu gwaje gwaje da suka kamata Allah ya sanya alkhairi Allah yayi maka albarka , Zanyiwa daddyn naku magana Karka damu ze fahimta .’’ Wani tsananin sanyi ne ya lullube Imam ,har seda wasu hawayen farin ciki suka wanke mishi fuska . Murmushi kawai Abban yayi , Daga haka ya mike da shirin tafiya . Tsakanin uba da ‘ya se Allah Yasan abunda yayi Yake kuma shirin yi Tabbas shine Dede , Amma kuma a take tausayin ‘yar shi se ya lullubeshi , Dan Tabbas yasan tunda har Imam ya rufe ido ya sake mishi zancen wata Bayan ya aura mishi ‘yar shi Ko watanni biyu ba a rufe ba , Tou fa ba karamin so yakeyiwa Wachchar bafulatanar me tallan Nono ba . Har ga Allah Da ya ji shiru bayan wata daya da auren su Imam din ya dauka ya hakura ne , Ashe abun yananan . Tabbas rayuwar ‘yar shi khadija Tana cikin garari . Saboda tun shekara daya da ta gabata A lokacin da aka fara maganar aurensu har kawo yanxu Be taba ganin digon son ‘yar tashi a cikin idanun Imam ba . Daddy is his best frnd Tun yarinta ,Ba da ban haka da yanda yaga Daddyn ya nace da son yaga ya kulla aure a tsakanin su ba Da babu dalilin da zai sanya ya yarda da auren khadjan shi da Imam, Tunda ya San ba sonta yakeyi ba . Yana fatan su samu su da sasanta ya so ta wata rana Tou Yanxu kuma gashi xe auri wadda yakeso . Fatanshi daya Allah yasa khadijan tayi hankali ta kwantar da hankalinta tayi biyayya ta zauna lafiya Watakila ta samu matsugunni a xuciyar mijinta In ba haka ba kuwa Bayajin tanada rabo a xuciyar Imam …….. An dan Kai ruwa rana Kafin Daddy ya yarda aka daura auren khadija da Imam a cikin sati daya , Ba kalar haukar da Khadija batayiba Har kalanzir ta Barba’da a gidan yana bacci Lokacin ana ‘I gobe ‘daurin auren Allah ya taimaka ya ji warin kalanzir din ya farka da wuri . Yana xuwa ya tarar da ita tana kokarin kyasta ashana Da kyar ya samu ya karbe Yana jefar wa ta rarumo wuka, Ganin fa dagaske kishi ya haukatata in ya barta kashe shi zatayi Ne Yasa ya fincikota dakyar ya fitar ya saka ta a mota . Iyayenta kamar iyayenshi ne Dan ze iya cewa Shi da ‘dan uwanshi especially ma shi in particular kusan a hannun maman ta ma ya girma Amman ya kamata a takawa haukar ta burki Tun Kafin tayi ‘barna . Ba dan yaso ba Haka ya Kai ta gidansu ya fadawa su Abba duk abunda takeyi mishi Har kokarin kashe shi data fara yau dinnan . Sallamar shi kawai Abba yayi Bayan ya bashi hakuri Daga haka ya wuce ya barta a wajen su Abban don yace a bar mishi ita . A tunanin ta fada kawai Xa ayi mata Daganan a maida ita A ranar Amman se taji Abba ya Hana ya Hana ma a Barta fita ko kofar gida . Tana ji Tana gani haka aka daura auren Imam da amarya Khadija . Ba abunda yafi daga mata hankali irin yadda Abba yace ‘’baxata koma Kwata Kwata ba ‘’ Gashi auren datayi hauka akai ya Riga ya Kara Dan haka A take ta fara data sani Hankalin ta ya sake tashi Dan gani tayi kmr ma ta bawa Imam damar cin amarcin shi hankali Kwance . Ko sati ‘daya Ba ayi ba ta fita a haiyyacinta kamar mahaukaciya haka ta koma Ba da ban larai datake Bata Baki da mahaifiyarta ba Da tuni ta xauce …. Seda ta sha wahala ta fita a haiyyacinta tukunna Dakyar su mama mommy daddy suka takurawa Abba ya Kira Imam yace ya xo ya dauketa . A Lokacin khadija amaryarshi Watan ta daya Har da ‘dan cikinta ….. Tare da Larai suka koma gidan nata saboda itama a lokacin an dan samu matsala da ita a kauyensu Taki ta koma Ba karamin mamakin yanda khadija ta chanxa lokaci guda Imam yayi ba ba kishi ba hauka Sannan taja abokiyar zaman ta a jiki kmr zata cinye ta dan so , Cikin jikinta kuwa ko ita uwar iyaka yadda zata kula dashi kenan Komai Nan nan. Ko abu me nauyi Bata ta’ba Bari ta dauka , Bata girki su sukeyi ita da larai Ko ruwa taje tafasawa haka khadijan zata amshe Ita ko larai wata ta tafasa Ta Kai mata har daki Wani Abu da Imam yayi noticing Shine kullum fuskar khadija uwar gida da idanunta a kumbure suke Yayi tambayar duniya tace mishi kawai ciwon ido ne yake damunta . A yadda suka hade kansu gidanshi kullum cikin xaman lafiya da lumana Shiyasa ya kauda duk wasu negative thinking Ya rungumi matanshi . Shima a bangarenshi yana ‘ko’kari Sosai wajen Kwatan ta adalci Shi kan sa yasan yana namijin ‘ko’kari wajen ganin yayi adalci a tsakanin matan na sa Duba da yadda yakeji game da ko wacce a cikin zuciyar sa A yadda uwar gidan sa take kula da amaryar Ya kamata ko Albarkacin haka ne Ace taci ta samu guri a zuciyar sa Amman har gobe ya kasa bata Ko da kaso daya a cikin Dari na zuciyar sa . Saboda Amaryar ta riga ta hade ta mamaye gaba daya kaso Dari din Itace zuciyar tashi ma gaba daya . Amman kuma dukda haka sam baya Bari a gane Yana iyakar bakin ‘ko’karin sa sa wajen boye hakan. Abu daya yake yi wasu lokutan yake tonawa kam sa asiri , Kasancewar sa mutum me masifaffen kishi yasa yadda yake kishin amaryar su kansu su larai sun fahimci baya yi wa uwargidan ta sa . Tsananin kishin sa ya San ya ko abokan shi ba ya Bari su gaisa da amaryar sa , In xa a fita ya dinga gyara mata xaman hijabinta yana rufe koina Ko Gaisuwar me gadi in ta amsa se ta hadu da fushin sa na en kwanaki . Sa’banin yanda yakeyiwa uwar gidan sa . Shiyasa ko ba a fa’da ba ko ya boye su sun Riga sun sani Ba tare da shi kanshi yasan sun gama gane wa ba …… Cikin khadija amarya yana wata biyar Imam ya tattara gaba daya dukiyarshi ya damkawa babyn Mace ko namiji be damu ba kawai de shi yasan ya gama yanke shawarar in aka Haifa mishi baby na farko a rayuwarshi to ya bada komai nashi . Khadija har kuka ta dinga yi Akan ya janye wannan ‘kudiri nashi Dan xe janyo mata bakin jini , Amman furr yaki Daga karshe de ya tilasta ta ba yadda ta iya tayi shiru Sannan suka tsaya akan cewa Maganar zata tsaya iyaka su biyu , In ta haihu shi zai ci gaba da kula da dukiyar har se yaron ko yarinyar ya Kai minxalin aure tukunna xa a damka mishi komai A cewarshi a yanda ya fada mata Saboda farin cikin Samun haihuwa ne Shiyasa ya shirya hakan a ‘dan shi na farko Kuma ko da ace uwar gidan shi ce ta Haifa tou hakan zai yi . Amman a cikin xuciyarshi Har ga Allah yayi hakan ne saboda tsananin so da kaunar da yakeyiwa amaryar tashi , Saboda yanda yake sonta ya kwallafa rai a kanta haka yake ji da cikin jikinta kmr ranshi . Wani sabon abu daya fara lokacin da cikin yakai wata bakwai shine Rashin godewa abunda su larai sukeyi , Duk irin ‘ko’karin da sukeyi da khadija se ya Dena gani , Ko maganinta ne Bata sha a kan lokaciba Ranar se anga abun mamaki Ya dinga masifa har washegari . Kuma inde khadija tayi missing magana tou it’s either wachchar khadijan girki take mata ko wani Abu makamancin haka Ganin rigima Tana shirin fara kunno Kai yasa ita da kanta amaryar ta kar’bi magungunan nata daga hannun abokiyar zaman nata Akan zata dinga sha dakanta Dan ita kanta abubuwan da Imam din yakeyi Bata Jin da dinsu , Duba da yanda su khadijan suke namijin ‘ko’kari wajen Bata kulawa Amman Sam baya gani. Abunda Imam yake yi Akan cikin nan zaka dauka akanshi aka fara haihuwa a duniya , Abu daya da uwar gidanshi tayi shine Kauda Kai Ta dauke kanta Ta rufe idonta Sam ta’ki yarda ta biye mishi, Kuma Sarai tasan da maganar yanda ya bawa ‘dan cikin khadija dukiyarshi kakaf Amman shima Bata ce ‘kala ba , Ita yanxu babbar damuwarta Shine yanda har yanzu ta gagara daukar ciki, Dan haka ta du’kufa addua Ta bar Imam yanata kinibibin shi ‘Kar’kari in yace batayi wa khadija Abu ba Ta bashi hakuri A wuce wajen Ko yana mita bata biyeshi . A kwana a tashi …. edd din khadija ya cika har ya wuce Amman Sam Bata jin ko alamun labour Dan haka Suka nufi asibiti . suna xuwa a gwajin farko aka fahimci Babyn babu rai yama dade da mutuwa dan har kmr ya fara dagargajewa . Sumewa Imam yayi a wajen da Jin wannan mummunan batu, Dan xe iya cewa be taba shiga tashin hankali kwatankwacin wannan ba . Har aka yi aikin aka gama aka cire babyn aka mata wankin ciki be farfado ba . A tare sukayi jinya a asibiti Dan ba kadan ba jinin shi ya hau A bangaren khadija ma abun ba sauki Dan bayan kwana biyu dayi mata wankin ciki Yayarta ma ta

Chapter 1 of 32