Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rike da hannu Habeeb tana wasa da yatsu sa taji ya matsi hannuta da k'arfi a firgici tad'ago taga ya runtsi idanu had'e da cije lebb'e tace yaya Habeeb ciki ne kuma"?
K'asa magana yayi faman juyi yakeyi duk da haka hannaye su na sark'e da juna, Hasheem da ke zaune a gefen bisa kujera roba yana _chat_ a waya shi ya mik'e nufi wurinsu gani yadda Habeeb ke birgima yasa yafita da gudu yakira _Nurse_ da sauri tashigo da kyar ta6an6are hannushi daga rik'o da ya yiwa Haleesa, tafara dubashi gani abun yafi k'arfinta yasa takira _doctor_
Haleesa na dur'kushe a k'asa tana kuka mai matuk'ar ban tausayi _doctor_ yadaka mata tsawa ta hanyar cewa ke! Tashi kifita k'asa tashi tayi saida Hasheem yakamata suna kaiwa bakin k'ofa tajuya, ta kalli Habeeb sai kawai ta ji yana kalma shahada.....


```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```


Jeeddah Aliyu🌹
[27/08 6:20 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [27/08 9:39 am] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```20```

Wasu yawu masu d'aci da masifar zafi suka cika bakin Haleesa saida taja dogon numfashi tayi nasara had'iye su kaitsaye suka, ratsa mak'oshinta suka dira cikin hanjinta nan take cikinta yafara k'ugi tamkar wance tayi _breakfast_ da fate wake Sam Haleesa bata lura da cewa sun fito d'akin ba saida ta ji sautin murya Ammi da kyar tad'ago kanta ta k'arewa Ammi da inna mairo da kuma zainab kallo ta ga kowane hawaye na zuba daga idanu sa, tsoro da zallumi had'e da tashin hankali Wanda tsawon rayuwa Haleesa bata ta6a gani irin sa ya ziyarce zuciya da gangar jikinta jin take wani irin mashahuri sanyi yasoma ratsa k'assa jikinta sai kawai jikinta yafara rawa kamar mazari da sauri inna mairo ta rik'e ta salman yak'araso daf da su muryasa na rawa yace Ammi meya faru naga kuna kuka"?
Kafin Ammi ta bashi amsa d'an tsamurare likita da ke cikin d'akin Habeeb yafito yana sharar gumi da _handkerchief_ da alama tak'are masa, cikin yanayi na tashin hankali Haleesa da yaya salman suka nufi sa a lokacin d'aya suka watsa masa rikitaciya tambaya _doctor ya jikinsa"?_
_doctor yaya Habeeb ya ji sauki koh"?_
Doctor ya girgiza 'kok'o kansa sai kace kadangare daga bisani yace _I'm sorry to say Habeeb is gone_
Sai Ku yi hank'uri mutuwa rigar kowa ce.
_innalillahi wa'inna illahi raji'um_ kalma da su salma ke ta mai-maitawa sabani Haleesa da ke tsaye kamar an shuka ta, ba k'arami jajircewa tayi wurin gani ta dai-daita numfashinta da ke barazana rabuwa da gangar jikinta, da kyar ta iya lala6o kalmar k'arya ce wallahi k'arya kake yi likita ya za'ayi yaya Habeeb ya mutu"? _you are bloody liar doctor_
Doctor ya yi murmushi yajuya yanufi office d'insa da alama su doctor sir an sha gani mutuwa kala-kala.
A hanzarce Ammi ta rik'o ta Haleesa tace ki sakeni Ammi girgiza mata kai Ammi tayi cikin hargowa tace kisakeni Ammii a tsorace Ammi tasaketa a hankali tafara ja da baya yanayi ta kamar na mahaukaciya sabon kamu, daga bisani tajuya da gudu ta afka d'akin yayinda Su Ammi suka Mara mata baya Habeeb ta hango tun daga tafin k'afarsa har izuwa kansa lullube da farin zani ta'karasa daf da gadon hannuta na rawa ta yaye zani idanu sa na lumshe tamkar mai bacci fuskarsa d'auke da murmushi kamar ka kira shi ya amsa, goshinsa na kyalli, Haleesa ta rik'o hannusa cikin sark'ewa halshe tafara magana _baka mutu ba yaya Habeeb Dan Allah katashi karka yi min irin wannan wasa I can't take it's any more please yaya Habeeb wake up don't do dis to me please yaya Habeeb I beg you proved 2 dis stupid doctor you are still alive ta'karasa magana had'e da rushewa da kuka mai k'arfin gaske_
A wannan Karo yaya salman ne ya yi yunkuri rik'ota ya mannata a 'kirjinsa, yace ki daure Haleesa ki danne zuciyarki domin ke aka yiwa wannan mutuwa saboda irin tsintsa _so da sha'kuwa_ da ke tsakani Ku amma hakan ba shi zai ba ki dama kin manta da cewa ubangiji da yaba mu Habeeb shi ya kar6i abinsa duk ma rai sai yad'and'ani mutuwa Habeeb ya riga mu gidan gaskiya Allah ya gafarta masa salman yak'arasa magana had'e da fashewa da kuka yayinda Haleesa ta 'kank'anme shi tasaki kuka mai matuk'ar ratsa zuciyar mai karatu, salman yaja ta suka fito daga d'akin.
Hasheem ya kira baffa da baba yafad'a musu Habeeb yarasu dama sun tafi gida domin su yi shiri zuwa masallacin juma'a kasancewa yau ranar juma'a ce.
Kukan Haleesa takeyi kamar ita ma za ta bi Habeeb sai faman sabbatu take yaya salman! _Haleesa ta kira shi cikin dasashiyar murya_
Na'am Haleesa shima ya amsa mata cikin murya tausayi
_Shikenan yaya Habeeb yatafi ya barni na tabbata nima nayi ban kwana da farin ciki wallahi yaya salman ba zan iya rayuwa babu yaya Habeeb mutuwa zan yi domin ban ga amfani rayuwata k....._
Da sauri yaya salman ya toshe mata baki yahanata k'arasa abunda ta je fad'a
Haleesa ta rik'o hannu salman ta aza bisa 'kirjinta tace ka saurara yaya salman ka ji yadda zuciyata take bugawa wani duhu nake gani wallahi mutuwa zan yi.
Yayinda numfashinta yadauke chak salman yad'ago fuskarta nan yagano cewa suma tayi, k'ara rungume ta yayi domin tashin hankali da yake ciki ya fi k'arfin tunani sa.
Har su baffa suka iso _hospital_ salman yana rungume da Haleesa, shi bai fad'awa jama'a a some take ballatana akawo masa agaji kuma shi bai nemo abunda zai farfad'o mai da ita shi kanshi a lokacin in aka tambaye shi, waye shi ba zai fad'a saboda tsanani tashin hankali da yatsince kanshi ciki.....
[27/08 11:35 am] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```21```

```Da misali 'karfe 1:15pm```

Su baffa suka kar6i gawar Habeeb har zuwa lokacin Haleesa bata farfad'o ba yaya salman yasauke ta chak, yanufi k'ofar fita _reception_ da ita Zainab ta d'auko mata takalminta da suka sa6ule daga 'kafafuta sai lokacin baffa yalura da halin da Haleesa take ciki, kafin yacima salman har yasakata cikin _taxi_ ya shiga ya zauna yak'ara rungume ta baffa k'araso ya rik'e k'ofar mota yace salmanu yarinya nan suma tayi"?
Salman yad'aga kai alama eh! Baffa yak'ara cewa ya kamata kabarta asibiti domin tasami kulawa likitoci salman ya girgiza kai had'e da cewa mu tafi gida kawai baffa.
Batare da baffa yace komai ba yajuya.
Kaitsaye gida aka wuce da gawar Habeeb a d'akin inna mairo aka ajiye shi, salman yanufi gidansu da Haleesa ya debo ruwa tukunya laka masu sanyi gaske ya kwara mata a fuska, a firgici ta mik'e zaune sai faman zazzare ido takeyi tayi wuk'i-wuk'i numfashinta na fita da k'arfi tadafe 'kirjinta tace _innalillahi wa'inna illaihi raji'un Ya ubagiji mahalici sammai da kassai kasa wannan abun da nagani a mafalki kar yakasance gaskiya_
Tana d'ago idanuta suka sauka bisa fuskar yaya salman ras, ras! Gabanta yafad'i sakamako gani yana kuka da sauri ta mik'e tsaye ta dank'i hannu salman cikin rikitaciya murya tace yaya salman da gaske ne yaya Habeeb yarasu"?
Da gaske ne Haleesa ba mafalki ba Habeeb yatafi ya barmu da kewarsa, tsakaninmu da shi sai addu'a Haleesa ta fashe da kuka tsawon _6 minutes_ suka dauka suna kuka babu mai rarrashin wani daga bisani salman ya yi k'arfi halin share hawaye shi, yace Haleesa ki yi hank'uri ki yak'i zuciyarki tasoma rungumar babban rashi da mu ka yi ki share hawaye ki ki zo mu tafi ki yiwa masoyinki addu'a had'e da yi masa kallon k'arshe domin daga wannan gani da za k yi masa, ba za ki 'kara ganinsa ba sai a photo.
Haleesa ta tsagaita kukan da takeyi had'e da feto majina ta goge a hijab d'inta zuciyarta cike da 'kunci tace _ya ubangiji kai bani yaya Habeeb a yau kuma ka k'ar6i abinka ya Allah ka gafarta masa ka sada shi da haske kabari kasa kyawawan halayesa nagari su bi shi ya ubangiji talikai k'asa mini juriya da hank'uri rashin sa_
Da sauri salman yace _Ameen Haleesa_
Haleesa ta girgiza kai jin takeyi ina ma ace mutuwar Habeeb mafalki ne ba gaskiya ba tasaki mai matuk'ar ci rai har shed'ewa take numfashinta yafara k'auracewa gangar jikinta, a hanzarce salman ya rungume ta yana bubuga bayanta tsawon dak'i'ka uku Haleesa ta d'auka kafin tasamu ta dai-daita natsuwarta salman ya cireta daga 'kirjinshi yarik'o hannuta suka nufi gidansu Habeeb ko da suka shiga gidan har anyi masa sutura yana kwance cikin makara lullube da farin likkafani, Haleesa tanufi wurinsa ta dur'kusa gaban makara so take tayi masa addu'a amma tarasa abunda za ta karanto masa, tsanani tashin hankali da firgici sun hanata kawai sai tafashe da kuka, Ammi da inna mairo da ke tsaye a bakin k'ofar d'akin suka soma tayata kukan.

```k'arfe 2:30pm```

Bayan an sauko daga masallacin juma'a jama'a suka dinga barkowa a k'ofar gidan mal Audu mai kifi domin su hallaci sallah jana'izza Habeeb, samari unguwar kowane su ka kalli fuskarsa idanu sa za ka hango sunyi jajir musanman 'yan _team's_ d'insu na _ball_ da kuma yaranshi na shago kuka sukeyi abin gwani ban tausayi domin kowasan Habeeb mutumi kirki uwa uba hank'uri Habeeb akwai hankuri sanyi hali da kyar ka ga yayi fad'a ga wasa da dariya Habeeb gwanin barkwaci ne shiyasa kowa yakeso sa mutuwa Habeeb tayi masifar girgiza d'ibin jama'a kamar yadda mutuwa ```marigayi Ahmad s Nuhu ta girgiza d'ibin al'ummah, Ya Allah ka gafartawa Habeeb da Ahmad s Nuhu Allah kasa aljana Firdausi ce makomarsu ```

_Ameen ya rabbi_

```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[27/08 6:21 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [27/08 4:08 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB ```💝

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```22```

```Note:-``` _Assalamu Alaikum masoya Jeeddah Aliyu ina mai matuk'ar ba Ku han'kuri kashe yaya Habeeb da nayi da yawanku reader's za kuce wannan karo wane irin labari Jeeddah Aliyu ta zo mana da shi ga shi tace suna littafi ta Ni da yaya Habeeb kuma ta kashe Habeeb ina so kusani yaya Habeeb bashi bane star d'in littafi kuma in har ban kashe Habeeb ba ta yaya za Ku fahimce sak'on da labari yake d'auke da shi Nima ba'a son raina yaya Habeeb ya mutu wannan karo reader's dole Ku yi han'kuri kamar yadda Hafsat Shehu da Ali Nuhu sukayi hank'uri rashin Ahmad s Nuhu Ku ma sai Ku yi han'kuri rashin yaya Habeeb abu d'aya Jeeddah Aliyu za tace da Ku kutanadi handkerchief had'e da tissue domin goge hawaye da majina_

_I love you all my fans_


Haleesa ta 'kurawa gawar yaya Habeeb da ke kwance cikin makara ido gani abu take kamar Almara ko mafalki cikin zuciyata tace shikenan yaya Habeeb yatafi barni bari na har abada, shikenan ```NI DA YAYA HABEEB ``` sai a mafalki ko kuma a photo kamar yadda yaya salman yafad'a ta sulele k'asa tayi kwance tacigaba da rera kuka mai 'kunar zuciya yaya salman da Hasheem had'e da baffa da baba suka shigo d'akin domin d'aukar gawar Habeeb Haleesa nagani haka ta mik'e zubar muryarta na rawa jikinta na makyarkyata tace baffa da baba ina za kutafi da yaya Habeeb"?
Dan Allah karku tafi da shi ina sonshi wayyo yaya Habeeb katashi ba zan iya rayuwa in ba kai karka manta da alqawali da kayi min za ka sani farin ciki har karshen rayuwata, shine za ka mutu ka barni, da sauri inna mairo tashigo ta fito da Haleesa daga d'akin a lokacin guda baffa da baba suka share hawaye salman kuma kifa Kansa yayi a jikin bango yana kuka rija-rija kamar mace yayinda Hasheem yake tsungune gaban gawar Habeeb, hawaye na tsiyaya daga idanu shi baba Audu ya katsi musu hanzari jimamin da sukeyi ta hanyar cewa Ku kama mu fita da gawar, ba yadda dole suka iya dole suka Kama makarar suka fito da gawar daga cikin d'akin Haleesa na kyalla ido ta ga an fito da gawa Habeeb ta kurma ihu mai matuk'ar karar gaske inna mairo tak'ara rik'eta gam bata 'kara shiga tashin hankali ba saida su baffa suka kai zaure d'auke da gawar Habeeb hakan ya tabbata mata da tarasa yaya Habeeb wani gwaron numfashi mai tsayin gaske taja daga bisani tasauke nan take ta sulele jikin inna mairo a some nan take hankalin mutane gidan yak'ara tashi.
A k'ofar gida kuma bayan a sallace gawar Habeeb aka saka ta cikin mota, aka nufi mak'abarta da shi{Allahu Akbar rayuwa duniya kenan lokacin da kake cikin ganiyar jin dad'inta mutuwa ta riske ka ka shirya ko ba shirya ba tadauke ka Allah yasa mu yi kyakyawan karshe Amin}
Ruwa aka dinga kwarawa Haleesa da kyar aka samu tafarfad'o.........
[27/08 6:20 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```23```

Haleesa na zaune a d'akin inna mairo ta buga tagumi da hannuta na hagu hannuta na dama rik'e da casbi, tana ja lokacin-lokacin tana sharar hawaye, yayinda jama'ar da ke d'akin suke ta faman bata hank'uri ita dai Haleesa jin su kawai take domin ita kadai tasan zafin da rad'ad'i da takeji, bayan an dawo daga kai Habeeb gidansa na gaskiya abokai sa suka shigo domin yiwa su inna mairo ta'aziyya suraj abokin Yaya Habeeb sai faman sharar hawaye yake yi, da kyar ya iya bud'e bakinsa yace inna ina Haleesa"?
Inna mairo tace Ku k'arasa d'aki tana ciki suraj ya mik'e yashiga d'akin, Ya zube gaban Haleesa cikin rawar murya yace sannu Haleesa Allah yajik'an Habeeb Allah ya gafarta masa.
Haleesa tad'ago rinani idanu ta tace _Ameen suraj Allah yabada lada_
Yadda suraj yaga idanu Haleesa sun kode had'e da kumburi tsanani tausayinta yakama shi, yafashe da kuka yayinda Haleesa ta taya shi da sauri d'aya daga cikin ayarin abokai Habeeb da suka shigo tare da suraj yarik'o suraj had'e da ya tayarda shi tsaye yace haba! Suraj ya za ka K'ara k'arya mata zuciya"?
A halin yanzu Habeeb addu'armu yake bu'kata ba kuka ba yajuya wurin wani d'an lukuti saurayi yace Abbas kayi masa addu'a nan take Abbas yafara kwararo addu'a jama'a da ke d'akin har ma da na waje suna amsawa da _Ameen_ daga bisani Abbas yacika da fatiha aka Shafa addu'ar sannan suka fice daga d'akin Haleesa ta kifa kanta bisa cinyoyi zainab tacigaba da shasshekar kuka.

```k'arfe 4:15pm```

Bayan 'yan zaman ma'kok'i masu yin sallah daga cikin su sunyi sallah la'asar aka fara rabon abinci kowane gugun na mutane in kaduba sai ka gansu da _plate_ d'in _jallof rice_ suna yayak'a gidan ma'kok'i ya koma gidan biki.
Haleesa na zaune bisa sallaya da tayi sallah a hankali tabin mutane d'akin da kallo gani yadda suke ta ruguzar shinkafa idanuta suka cik'o da hawaye ta girgiza kai tasoma tausayi kanta kowace irin rayuwa za ta fuskanta anan gaba, domin yaya Habeeb yariga yasaba mata da cin abinci tare da shi _through out_ ba abunda tasaka a cikinta ko ruwa ta kasa sha kamar daga sama ta ji murya wata 'yar gajeriya mace mai kama da Rukayya Dakaratu tace wai lami kinada labari malam idi yasaki kubra saki uku"?
Lami ta zaro idanu had'e da cewa kai jama'a anyya ladiyo za ta shiga aljanna kuwa"?
Ae ko ubanta kara6o ta ba za ta shige ta ba domin yanzu kubra ita ce mace ta takwas da mallam idi yasaka kuma kowace su lami ladiyo ce tayi sanadi sakinta 'yar gajeriya tak'arasa magana had'e da samk'ama loma shinkafa abaka abin zai ba ka haushi da dariya yadda ta cika bakinta da shinkafa.
Tsanani haushinsu da takaici ya kama Haleesa cikin zuciyata tace wallahi na tsani wannan al'ada ta mallam bahaushe ta zaman mak'o'ki zaman mak'o'ki ko zaman gulma da tsugudidi, domin ni da na ke jini yaya Habeeb ko ruwa nakasa sha amma su wadanan bayi Allah bayan sun narki shinkafa sun kuma buge da gulma.

```BAYAN SATI D'AYA ```

Yau satin yaya Habeeb d'aya da rasuwa Haleesa na zaune bisa katifarta ta kurawa photo sa ido hawaye na zuba akan fuskarta nan take tasoma tuna rayuwa da sukayi a baya, kamar wance aka mitsina ta mik'e zubar ta nufi k'ofar fita Ammi na _kitchen_ ta ga wucewa ta da sauri tafito daga _kitchen_ tasoma kwadawa Haleesa kira tuni Haleesa tafice daga gidan a tsorace Ammi tanufi k'ofar fita tale'ka ko 'kura Haleesa bata hango ba d'an kwalin kanta ta yafa tashiga gidan inna mairo da zainab tafara cin karo tana wanki a bakin famfo, Ammi tace zainabu Haleesa tashigo gidanan kuwa"?
Zainab tace a'a Ammi fita ta sakeyi"?
Eh! Ina kitchen naga wulgawarta ko da nafito na nemi ta narasa da sauri zainab ta wanke hannuta ta d'auko hijab d'inta inna mairo tafito daga band'aki{bathroom} hannuta rik'e da buta tace garin yaya fateema kika yi sake tasake tafita"?
Ammi tace narasa yadda zanyi mairo da wannan al'amari na Haleesa yarinya sai kace mai iskokai tana fitowa na biyo bayanta a tunani na gidanan tashigo ashe ta haura gaba, zainab tace bara naje shago ko filin makaranta watakila tana chan don ko jiya a filin makaranta na kamota tak'arasa magana had'e da ficewa daga gidan......


```DEDICATED TO SHEHU ALIYU FAMILY'S ```

Jeeddah Aliyu🌹
[28/08 9:57 pm] Jeeddah Aliyu🌹: [28/08 2:26 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```24```

Duk Inda zainab take sa rai za ta ga Haleesa taje amma bata ganta ba, yaya salman da ke biye da Zainab a baya sai fad'a yakeyi wannan wane irin rashin takwali ne na Haleesa"?
Sai kace akanta aka fara mutuwa in kuma ciwo hauka ne yakamata yayi a nemo k'ato _padlock_ a rufe ta a d'akin don ni nagaji da wannan masifa.
Zainab tace han'kur za ka yi yaya salman kai kanka kasan dole Haleesa ta tsince kanta a wannan yanayi addu'a za mu cigaba da yi mata Allah yakawo mata Wanda zai maye mata gurbin yaya Habeeb.
A tsakiya gida suka tararda Ammi da inna mairo suna jimami wannan al'amari na Haleesa Ammi nagani su batare da Haleesa ba cikin rauni murya tace ba Ku ganta ba koh"?
Salman yace Eh! Ammi ni wannan al'amari na Haleesa yafara bani haushi, in an mutu ba'a dawowa ballatana tasa ran Habeeb zai dawo.
Hasheem ne yayi sallama yashigo janye da Babur yanufi _part_ d'in da marigayi yaya Habeeb ya ginawa Haleesa dama _parlour d'aya da bedroom ne sai bathroom had'e da d'an 'karamin kitchen_ cikin filin tsakiyar gini Hasheem yake _parking_ Babur d'insa har juya sai kuma yadawo sakamako hango mutum da yayi a tsakiyar _parlourn_ kwance da sauri yak'arasa waje mamaki mai d'auke da tausayi Yakama shi Haleesa ce kwance a k'asan _parlour_ tana bacci Hasheem yafice da sauri yana kwalawa Ammi da inna mairo kira Ammi da Inna Ku zo Ku gani kada nagani ni kadai da hamzari suka nufi wurin Hasheem, da yatsa yanuna musu Haleesa da ke kwance tana sharar baccin gaba d'aya su Ammi suka d'auki salati Wanda yayi sanadi falkawa Haleesa kwayar idanu ta sunyi jajir Ammi ta tashi ta tsaye tace haba, haba! Haleesa wane irin hali kikeso jefa kanki"?
Habeebu yatafi wannan abu da kikeyi bashi zai sa yadawo gareki ba da ana mutuwa adawo Haleesa da yanzu mu ma muna tare da iyayye mu amma ina! Tsakani mu da su sai addu'a kafin mu ma tamu mutuwa ta riske mu a kullum addu'a mu Allah yagafartawa Habeebu ke kuma ya musaya miki da Wanda yafi shi Wanda zai so ki fiye da son da habeebu ya nuna miki.
A tsorace Haleesa tad'ago dara-dara idanuta ta dube Ammi daga bisani ta girgiza kai hawaye na fita a idonta tace har abada Ammi ba zan sami Wanda zai maye gurbi yaya Habeeb a zuciyata.
kafin Ammi tabata amsa inna mairo ta garita ta hanyar cewa Haleesa Dan-Adam baya fidda rai da Rahmar Allah in ki kayi tawakalli da mik'a kukanki wurin Allah sai ki ga yakawo Wanda zai mantar da ke rayuwa da kike yi da Habeebu yabaki so da kulawa fiye da Wanda Habeebu yabaki.
Haleesa ta runtsi idanu cikin zuciyarta tace na fahimce wad'annan tsofafi guda biyu har abada ba za su gano manufar ta ba.

```BAYAN WATA 6```

Bayan watani shidda da rasuwa yaya Habeeb a yanzu Haleesa tarage damuwa saidai tayi matuk'ar rama kamar ka hura mata iska tafadi tadawo _so silent_ abunda yake firgita iyayye ta bai wuce wata d'abi'a da ta tsiro da ita za ta yini guda cur batare da tayi doguwar magana ba
Kasancewa kowa yasan wannan d'abi'a ba halinta bane domin Haleesa na da surutu ga yawan tsokana da kyar ka zauna da Haleesa bata tsokana ka ba koda yaushe fuskarta na d'auke da murmushin sa6ani yanzu da murmushin yake mata wuya.
Haleesa tafito daga d'akinta tana sanya da atamfar _Java wax orange da touch's d'in brown_ d'ikin Riga da siket bata d'aura d'an kwali ba ta yafa _kashkha veil brown colour_ tayi matuk'ar kyau jikinta na fitarda k'amshin _explore white body splash_ kaitsaye d'akin Ammi tashiga Ammi nagani ta ta zaro ido had'e da cewa Haleesa ke ce kuwa"?
Haleesa tayi murmushin mai sauti daga bisani tace kinga wani sabon sauyi a tare da ni Ammi"?
Ammi tak'ara bud'e baki da hanci tace ba sauyi d'aya ba Haleesa sauye-sauye
Haleesa ta kyalkyale da dariya tace kai Ammi dama fa ina wanka.
Miye amfani wanka da ko _versiline_ ba ki shafawa Kai Alhamdulillahi! Allah ya kar6i addu'a da muka share tsawon watani muna yi, Allah ya yi miki albarka Haleesa Allah yakawo miki miji nagari tamkar Habeebu ki.
_Ameen Ammi Haleesa tafad'a idauta cike da kwalla_
Da sauri tadanne hawayeta saboda bataso Ammi tagano cewa har yanzu da sauran rina akaba cikin sanyi murya tace Ammi _N100_ za ki bani na siyo awara,
Ammi tasaki murmushin farin ciki tace awara kuma Haleesa"?
Haleesa tad'aga kai Ammi tace bara kamal yadawo yasiyo miki
Dan Allah Ammi ki barni naje da kaina so nake na d'an mik'a 'kafata.
Ammi ta bud'e kwano samira ta d'auko _N200_ ta mik'a mata had'e da cewa kidawo mini da chaji kuma in kinje kin tararda layi ki bar kudi kidawo in kamal yadawo ya kar6o miki.
"Haleesa tace to! Ammi sai nadawo adawo lafiya Ammi tafad'a had'e da bin ta da kallon tausayi......
[28/08 5:17 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love❣_

```®NWA```

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```25```

Haleesa na fitowa gidan baba Audu tashiga inna mairo na zaune tana yanka kunbewa, ta ji sallama Haleesa ta amsa had'e da d'agowa saura kiris inna mairo ta yanke yatsanta kasa hank'uri tayi saida ta furta abunda idanuta suka hasko mata wa nake gani haka kamar Haleesa"?
Haleesa ta rufe fuskarta da tafin hannuta tace ba kama bace inna nice'
Ikon Allah Haleesa sai yau aka fita daga takaba"?
Na ga anci kwalliya abunda muka jima bamu gani ba, masha Allahu _Allah yasa karshen damuwarki kenan_
Haleesa ta sada kai k'asa had'e da cewa _Ameen._
Inna ina zainab"?
Zainab na aike ta
To inna na tafi tajuya had'e da ficewa yayinda inna mairo ta share hawaye tausayin Haleesa da suka zubo mata.
A hankali Haleesa take tafiya tana sharar hawaye tasoma tunani rayuwar da tayi da yaya Habeeb abaya tun da da yaya Habeeb ya fahimce Haleesa na matuk'ar son awara, duk yamma sai yasiyo mata awara taci tun lokacin da yarasu ta daina cin awara don kawai yaya salman yafaranta mata duk yamma sai yasiyo mata kamar yadda Habeeb yake mata amma ta k'i ci ta aza kuka dalilin da yasa salman yadaina siyowa kenan.
Yau d'in ma da tayi wanka har da su kwalliya tayi ne don ta faranta ran Ammi, domin ta fahimce irin damuwa da Ammi take shiga a duk lokacin da taganta cikin damuwa.
Tana kaiwa dai-dai _Ni da yaya Habeeb teilorings center_ ta ja tayi tsaye ta tsurawa shagon ido kuka na 'ko'kari kunbce mata da sauri ta bar bakin shagon tana tafiya batare da tasan Inda take jefa k'afafuta sai da tayi tafiya mai nisan gaske sannan tagano har tafita cikin unguwar su ga kuma duhun magariba yayi domin a wasu masallatai an gama

Please Login or Register in order to submit comment