Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ac.
"Sai lokacin Bala da Hannah suka k'araso suka ta tattara da Haleesa tsaye tana rabon idanu, Hannah ce tanufi wajenshi ta durk'usa saitin fuskarshi idanunshi a rufe ta yi k'asa da murya ta hanyar cewa sannu yaya Habeeb"!
''Sautin muryarta ce tayi sanadin da ya bud'e idanu, harara yafara zuba mata me yakawo ki wurina"?
Yaya Habeeb z....shut up ya katsi ta bakida wani amfani da za ki yi min anan ki tashi ki kama gabanki
"I'm sorry Yaya Habeeb nasan za ka ji zafina sosai amma wallahi ba laifi na bane mom tace ko ka kira phone d'ina kada na d'aga domin tasan dalilin Haleesa ka ke kira amma ka yi hak'uri a kira Dr saleem ya duba ka zama da ciwo ba shi bane solution d'in matsalarka.
"Tsaki Habeeb ya ja cike da takaici yace a
tunani Hannah koda sweetheart da leesa sun had'e min kai ke za ki ji tausayina ashe kema bakyaso na.
''Wallahi ina sonka yaya Habeeb karka kamanta tun lokacin da muka rasa mahaifin mu kai ne ka maye mini gur6inshi.
"Habeeb ya yi shiru kamar mai nazari daga bisani yafara magana cikin murya mai ban tausayi Hannah inason Leesa sosai amma ita batasona ta tsaneni Hannah ki gayamin yadda zan yi Leesa tasoni.
''Hannah ta mik'e ta zauna kusa da shi har zuwa lokacin baisan cewa Haleesa tana cikin d'akin ba saboda ya ba wa k'ofa baya.
"Yaya Habeeb kadaina wahalarda kanka saboda Haleesa tana sonka kamar yadda kaima ka ke sonta tuni guguwar sonka tayi nasara tafiya da ita duk abunda take yi maka tana yi a dalilin irin wulaqancin da kadinga yi mata ni sheda ce akan irin matsanancin son da Haleesa take maka yaya Habeeb.
" A rikice Habeeb ya mik'e zaune yarik'o kafad'ar Hannah ya girgiza ta da k'arfi "omg! I can't believe da gaske ki ke yi Hannah Leesa tanasona ko kuma kina ne don kawai ki faranta mun rai"?
''Da gaske nake yi yaya Habeeb Leesa tana sonka ko ranar da ka mare ta zancenka ne mu ke yi ba na margayi yaya Habeeb ba tuni ka ture gwannatin margayi yaya Habeeb a zuciyar Haleesa.
"Habeeb ya rud'e yarasa indan zai jefa kanshi don dad'i nan take farin ciki ya mamaye shi yace ta ya ya zan amince da abunda ki ke fad'a gaskiya ne"?
"Hannah ta yi murmushi ta juyarda fuskar Habeeb zuwa da Haleesa take tsaye zaro ido Habeeb ya yi tamkar ya ga abun tsoro muryarshi a sark'e ya furta Hannah da gaske Leesa ce nake gani ko kuma gizo take mun"?
''Ba gizo bane a zahiri ka ke ganinta. Habeeb ya washe hak'ora kamar gonar auduga yak'ara mayarda ganinshi wurin Haleesa wance ta sadda kanta k'asa hawaye na zuba daga idanunta.
Cikin tsananin farin ciki Habeeb ya rungume Hannah yayinda Hannah keta faman yi mishi dariya.
''Haleesa tad'ago had'e da share fuska ta dubi Bala tace Bala kira Dr ya duba shi.
Da sauri Bala yaciro waya gaban aljihunshi ya kira Dr saleem.
'Hannah ta mik'e tana dariya tanufi wurin Haleesa ta rad'a mata wannan tsayin na menene"? ki k'arasa wurinshi mana yad'an ji d'umin jikinki tak'arasa magana had'e da ficewa.
''Haleesa ta zaro ido tabi ta da kallo daga bisani tajuya ta dube Habeeb suka had'a ido kasa d'auke idanunta tayi akanshi wani irin kwarjini ya yi mata.
''k'ayatacen murmushi yasake mata, ta lumshe idanu ta koma jikin bango talafe Habeeb yayi k'asa da murya yace zo ki ji Leesa naa"!
''Mak'e kafad'a ta yi had'e da turo baki.
"Ni koh"?
''Eh! Kai! Tafad'a tana murgud'a baki.
Habeeb ya langwa6e kai yana kallonta ya mik'e da kyar jiri yana d'ibarshi yanufi wajenta hannunshi ya aza a har6arta yad'ago fuskarta da sauri ta runtse idanunta gam... Leesa abunda Hannah tafad'a min gaskiya ne ni anan"? yana magana ne had'e da aza hannunshi a k'irjinta.
"Yarrr..... Haleesa taji tak'ara runtse idanunta Habeeb ya yi murmushi yarad'a mata _I love you leesa"!_
A hankali Haleesa ta ware idanunta akan kyakyawar fuskarshi wani irin kunyarshi take ji ta ture hannunshi ta ra6a gefenshi za ta wuce ya rik'o hannunta kamar za ta yi kuka tace yaya Habeeb ka je ka kwanta naji jikinka da zafi sosai kafin Dr saleem ya zo ya duba ka.
''Leesa ke ce magani ciwona ganinki kadai ya ye mini duk ciwo da nake ji a jikina yanzu kin yarda inasonki ba pretending nake yi ba"?
Murmushi ta yi had'e da gyad'a kai.
"yasaki Hannunta ya ware hannayenshi yace _oya come here & give me a big hug_
Cikin jin kunya ta girgiza kai tana murmushi.
"Leesa please"! Yafada kamar zai yi kuka a kunyace tanufi fad'add'e k'irjinshi tashige ya rungumeta tsanm.....kamar zai shigarta da ita cikin k'irjinshi yashiga sinsinar k'amshinta daga bisani ya lalla6o bakinta ya had'e da nashi karo na farko da Haleesa taji tanaso tanunawa Habeeb ita ma fa takamu ta zira mishi halshenta gaba d'aya Habeeb yarud'e tsayuwa tagagare shi gani haka yasa taciro bikinta daga nashi tanufi gefen gado ta zauna tana kare fuskarta da tafin hannunta.
"Habeeb yana murmushi yanufi wajenta ya zauna yacire hannayenta daga fuskarta cikin tautasan lafazi yafara magana _Leesa inasonki sosai kece farin ciki ruhina, kece annuri zuciyata a lokacin da ki ka juya min baya sai naji kamar zan yi hauka I love you so much Leesa"_
"Dad'i ya lullu6e Haleesa ta yi wani fari da idanu cike da jin kunya tace _I love you too my Handsome don_
"Kyakyawar runguma Habeeb ya yi mata da kyar ta zare jikinta daga nashi ta janyo masa pillow yaya Habeeb please ka kwanta.
Ture pillow ya yi bana kwanciya akan pillow leesa amma zan iya kwanciya anan yana magana ne had'e da aza kanshi a cinyoyinta.
"A hankali take Shafa sumar kanshi knocking akayi Haleesa tashiga ture kan Habeeb yayinda yak'ara gyara kwanciyarshi a jikinta ba yadda ta iya dole ta zuba masa ido a haka Dr saleem Yashigo yatarar da su yashiga duba Habeeb fad'a yayi masa sosai akan yarage tunani kuma yadinga cin abincin daga bisani yace Bala ya biyo shi ya kar6o magani, Hannah da ke tsaye a gefe tace Zan bi Bala ya ajiye ni a gida da sauri Haleesa tace ni fa"?
"Ke kuma ki zauna ki kula da mijinki har sami sauki"
"Habeeb yace kinga Hannah yi tafiyarki kyalleta kawai so take ta 6ata mun rai.
Hannah tana dariya tafice Habeeb yak'ara shigewa jikin Haleesa ture shi tayi ta kwanta kusa da shi ya matsa ya aza kanshi bisa cikita yashiga zuba mata hira mai dad'i hannunta na cikin sumar kanshi tana ya motsawa.

_some hours later_

Cikin shagwa6a Haleesa take magana wai yaya Habeeb kana nufi anan zan kwana"?
"Ae ya ma wuce wai my Leesa ke yanzu in na barki ki koma chan gida ae ba za ki iya bacci mai dad'i ba.
Ni gaskiya tsora nakeji kada mom tagane.
Ba za ta gane ba my Lessa please karki tafi ki barni kinji"?
Shikenan zan kwana amma gobe da sassafe Bala zai maida ni ka amince"?
"Uhm.....na amince yafada had'e da Jan karan hancinta ya mik'arda ita tsaye yace bacci nakeji leesa mu je mu yi wanka"
"Ido ta zaro uhm.....uhm...ka je ka yi wankanka nima nayi nawa.
Cak.....yadauketa yanufi bathroom da ita sai faman yi mishi magiya take ya ajiye ta ya yi biriss.... Da ita yadireta cikin bathtub.....

Jeeddah Aliyu🌹
[9:57PM, 17/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [17/12 4:44 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```95```

~~ihu taje kurmawa ya toshe mata baki da hannunshi yacire kayan jikinshi yashiga bathtub yana lek'e fuskarta da ta tufe da tafin hannunta da k'arfin tsiya yashiga cire mata kaya wanka da za'ayi cikin d'an k'ank'ani lokacin amma saida suka share tsawon lokacin suna wasa da ruwa sai kace k'anana yara.
"Habeeb yarigata fitowa daga bathtub idanuta na rufe ruf ita a dole kunya take ji towel ya mik'a mata sannan yafita tafito daga bathroom tana kare fuska kasa karasawa cikin d'akin ta yi.
''Ta ciki mirror Habeeb ya hangota tsaye ya ajiye, comb d'in hannunshi yanufi wajenta, towel d'in jikinta ya ja a rikice ta ware idanuta masu d'auke da tsoro.
Kyakkyalewa da dariya ya yi har yana dafe ciki Haleesa ta yi sororo hannunta na dafe da towel d'in jikinta tana masa kallon mamaki.
''Ya tsagaita da dariyar da yakeyi still fuskarshi na d'auke da murmushi yace ya akayi ne 'yan matanaa naga kin kura min ido"?
''Murmushi ta yi had'e da juyawa tanufi dressing mirror tace dariya tana matuk'ar k'ara maka kyau yaya Habeeb kadinga dariya kadaina wannan had'e da fuska da ka ke yi.
''Yana murmushi yak'arasa daf da ita ya rungumeta ta baya suna hango fuskokinsu cikin mirror _soyayyarki ce ta yi nasara canza ni har nake iya dariya Leesa ke Alkhairi ce a rayuwana banta6a zan tsanmani zan so wata 'ya mace ba sai gashi kin shigo rayuwana kin dasa min sonki da k'aunarki a zuciya ban tabbata da sonki ya mun Illah ba sai da ki ka juya mun baya nadaina jin Qamshinki nadaina jin d'umin jikinki I miss your hot body_
Murmushi Haleesa ta yi ta mik'a hannunta tattaro jik'ak'en sumar kanta ta yarfa masa a fuska da sauri ya lumshe idanu, tace Uhm.....ba ma ni kayi missing ba koh"?
Juyo da ita yayi suna facing d'in juna cak yad'aga ta ya zaunarda ita akan mirror I absolutely miss you my Leesa"!
"Ta turo baki cikin shagwa6a tace _I miss too my handsome don_
" ya kashe mata ido d'aya very slowly yafurta da gaske"?
"Gira ta d'aga mishi
_Oya shown me baby you miss me_ peck tayi mishi a goshi yatsine fuska yayi No.....Leesa ba irin wannan ba.
Tak'ara masa wani a kumatu ya ka ji wannan"?
"Shi ma bai yi ba yafad'a yana 6ata fuska
Zaro ido ta yi had'e da cewa uhm.....uhm...ni ka saukeni na shafa mai.
''Saida ya sumbace lips d'inta sannan yasauketa yanufi gefen gado ya zauna yana aikin kallonta, ta Shafa lotion a fatarta ta kwashe sleeping dress d'inta tanufi bathroom Yayinda Habeeb ya bita da dariya.
"Tana fitowa ya kafeta da ido yi tayi kamar bata ganshi ba tanufi mirror tad'auki perfumes tafashe logun da sak'o na jikinta ta yi tsaye jikin mirror tana kallon Habeeb tana murgud'a baki.
''Zo ki ji Leesa naa!
Harararshi ta yi had'e da mak'e kafad'a ya mik'e tsaye yanufi wajenta tun kafin yakarasa tafara ihu _Wayyo yaya Habeeb karka ta6ani Allah banaso_
In ke bakyaso ni inaso ya sunkuce ta sai ihu take tana zillo k'afafu ya jefata bisa gado ya kashe light.
"Dare ranar sai ya zamewa Habeeb tamkar shine first night d'insu saboda da amincewa Haleesa suka raya daren sa6ani first night d'insu da shi kadai ya yi kid'ansa ya kuma taka rawarshi.

_8:00am_
Habeeb ya falka yashiga tashe da Haleesa ta bud'e idanuta da kyar saboda baccin bai isheta ba tak'ara shigewa jikinshi cikin muryar bacci tace ni kabarni nayi bacci na.
wane irin bacci kuma Leesa"? Kinsan yanzu karfe nawa kuwa"?
Oho....ni bansaniba ka kyalleni nayi baccina"!
Yacire ta daga jikinshi yanufi bathroom ya yi wanka baya buk'ata yin alwala domin wankanshi na had'e da alwala yafito sanye da bathrobe kaitsaye ya sunkuce ta sai tsintar kanta ta yi cikin bathtub ihu ta kurma had'e da wartsakewa.
"Habeeb yana dariya ya dungure mata kai oya ki yi wanka idan ki yi sallah sai ki kwanta ki cigaba da baccin naki sleeping sickness kawai yana magana ne had'e da fita daga bathroom d'in.

_15 minutes later_

Haleesa tana tsaye gaban dressing mirror tana make up duk abunda take yi Habeeb yana mik'e akan gado yana kallonta yana murmusawa abinsa ya cize lips d'inshi na k'asa ya lumshe idanu shi kadai yasan mugunta da yake shirya mata.
"Ta cikin mirror ta hangoshi yana murmushi tabe baki tayi tace wai wannan murmushi na menene"?
''Kashe idonshi d'aya ya yi yace na sonki ne.
Huh.....I see tafad'a had'e da k'ara tabe baki ta d'auki veil d'inta mahadin baqar Jallabiya da ke sanye a jikinta ta yi rolling sannan tajuya ta dube shi tace "my handsome am ready call Bala to pick me up.
''Okay...yafad'a had'e da danna waya yakara a kunne yashiga magana Bala wai ina kashiga ne ga Leesa tana jiranka ka maida ta gida"?
Ya d'an yi shiru daga bisani yace what's! Kana nufi baka dawo bane"? shikenan ka yi sauri please tana jiranka kasan banaso 6acin ranta. Yak'arasa magana had'e da kashe wayan yajuya ya dube ta yace Bala bayanan yafita zai dawo nan da 4-6 hour's.
Whats 4-6 hours gaskiya I can't wait tak'arasa magana had'e da yatsine fuska.
"Ya tabe baki tell me yanzu ya ki ke so ayi"?
''Taxi zan bi tun da kai ba driving ka iya ba balle ka kaini.
"Murmushi ya yi yana kallonta ta k'asan ido
"My handsome bani k'udin taxi na wuce Allah na matsu na bar gidanan.
Harara ya zuba mata banida k'udi sai kitafi a 'kafa.
Murmushi ta yi tace "you most be joking tanufi bedside inda wallet d'inshi yake ajiye takai hannunta za ta d'auka shima yakai hannunshi cikin zafin nama tariga shi d'auka tana dariya ta 6alle wallet din.
"Leesa karki sake ki bud'e min Wallet kinji koh"?
Gwalo ta yi mishi tak'arasa bud'ewa taciro 5k ta mayarda wallet d'in inda ta d'auko ta sunkuya ta yi pecking lips nashi I've to go my handsome ka tabbata ka yi taking medicine naka in time nasan halinka da rashin son magani ka ci abinci sosai is that clear"?
"Ya ja karan hancinta yana murmushi yace yes ma!
Ya tashi zaune yarik'o hannunta yana mata kallo mai cike da zalla so in a cool voice ya furta thank you very much leesa for your love & care!
"It's my pleasure. duk lokacin da mom tasake tafiya I will surely get back to you okay"?
"Okay my love am gonna miss you"
Me too tafad'a kamar za ta yi kuka tajuya har takai k'ofa ta tsaya tajuyo yana zaune yana kallonta still fuskarshi d'auke da murmushi rass-rass gabanta yafad'i tashiga tunani what's does means he said he wanna miss me but now he's was smile"?
"I thinks there has something wrong with this guy cike da fargaba tace yaya Habeeb are you okay"?
"Yes am absolutely fine
Tayi ajiyar zuciya tace bye take care ta bud'e k'ofa tafita yad'aga murya yace you too baby ya kwanta yadauki phone d'inshi kira number Bala yakara a kunnenshi _Bala ka yi gudun bala'i ka je d'akin Rahul da Rita kafito da su ka kawo su dai-dai k'ofar fita main palour kasake su_
Banaso tambayar banza kaje ka yi abunda nasaka. Ya yi hanging up yana murmushi
"Haleesa tana jefa k'afarta waje taci karo da black police dog's sai fama zazzago halshe suke yawu na zuba wani d'an uban tsalle tadaka had'e da zunduma ihu tajuya parlour da gudu yayinda dogs d'in suka Mara mata suna "barking ihu take had'e da kwad'awa yaya Habeeb kira a rikice ta haura staircase a hargitsi ta afka d'akin Habeeb ta rufo k'ofa da k'arfi.
''Habeeb da ke kwance da sauri ya rufe idanu kamar mai bacci yana dariya k'asa- k'asa saboda yasan tsiyar da ya qula mata.
"Da gudu tafad'a kanshi ta k'amk'ame shi _Wayyo Yaya Habeeb wa'annan 'yan Iskan karnuka za su cinye ni_
K'ara rungumeta ya yi yace oh! sorry baby ki barni da su sai naji dalilin da yasa suka tsorata mun ke.
''Ba wani dalilin kawai ka fitarda su daga gidanan narasa laifi da nayi musu suka tsaneni ko Imaan da ke yarinya k'arama basa yi mata barking sai ni da suka rena ni dai kafitarda su tak'arasa magana tana hawaye.
"Habeeb ya hadiye dariyarshi yace gadi suke min baby kinga kuwa bai kamata na fitarda su ba.
Harara ta galla masa duk wad'annan securities da ke gidanan ba su isa gadi ba sai Wa'annan bak'ak'e"?
Murmushi ya yi suna da amfani sosai bagashi yanzu sun koro mun ke kinga sai ki cigaba da jinyar mijinki.
''Tasa mishi Kukan shagwa6a haba yaya Habeeb kana nufi zan k'ara kwana anan"?
"To meye a ciki dan kin k'ara kwana anan"?
"Mom nake tsoro kar taji labari na zo wajenka.
Kidaina jin tsoro Sweetheart ba za ta dawo ba sai nan da
3 day's.
A shagwa6e tace uhm..uhm...ni ban yarda ka tashi ka rakani
Haba! My Leesa Dan Allah ki yi hak'uri ki zauna kinga hankalinmu a kwance cikin 3 day's d'inan za mu sha soyayarmu kafin sweetheart ta dawo ta datse mana jin dad'nmu.
Hmm...Haleesa tafad'a had'e da kai mishi duka ya kyalkyale da dariya phone d'inshi ya yi ringing yadauka yakara a kunnenshi yace _Hello Maryam_
"Rass....gaban Haleesa yafad'i nan take ta tuna da yadda ta ta6a ganin Habeeb da Maryam a Sokoto wani irin kishi ya lullu6e ta ta mik'e da k'arfi tanufi k'ofar fita.......

Jeeddah Aliyu🌹

[8:05PM, 19/12/2016] Hafsat Yau Abdullahi: [19/12 12:39 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*


```96```

~~Ta bud'e k'ofa tafita da mugun mamaki Habeeb ya bita da kallo ya mik'e da sauri ya bi bayanta a parlour yatarar da ita ta kifa kanta a hannun kujera tana shasshek'a kuka a rikice ya furta _Maryam I'II call you later_ batare da ya jira jin abunda Maryam za ta fad'a ba ya yi hanging up jikinshi na rawa ya zauna kusa da ita ya rungumo kafad'arta, tashiga ture shi in tears tafara magana _don't touch me kai mayaudare ne yanzu nan ka gama tsara ni kana fad'ar I'm the only woman you love shine don wulaqancin da kwarewa da yaudara in front of me kana cheating nawa_
Zufa ta soma tsattsafo wa Habeeb in shock yake kallonta da kyar ya tattaro yawun bakinshi ya yi nassara lalla6o kalma da zai furta mata Leesa please karki d'aga mun hankali akan abinda bakida tabbacin akansa ki yarda da ni nothing between us banta6a son Maryam ba kuma bana tunanin zan so ta.
"Ta galla masa harara baka sonta amma naganka kana, tsotsar bakinta.
Zaro ido yayi karki yi mun sharri Leesa Maryam fa Qanwata ce Kamar Hannah take a wurina me zai kaini da bakinta"?
Cikin murya ta kwashe lokacin da taganshi da maryam a Sokoto yana busa mata ido Wanda har tayi tunani sumbatar ta ne yake yi.
"Dariya sosai Habeeb ya yi gani yadda yake dariya yasa tafashe da kuka mai k'arfi gaske da sauri ya hadiye dariyarshi ya rungume ta yana bubbuga bayanta cikin rarrashin ya sanarda ita abinda yafaru tsakaninshi da Maryam.
"Ba wani photo boyfriend d'inta da za ta nuna maka sau nawa tana kashe min gargad'in akanka.
"A da kenan amma a yanzu yayanki ya yi nassara saye zuciyarta Leesa Maryam yaya salman takeso, saidai Hajiya khareema tak'i amincewa a cewarta 'yarta ba za ta aure talaka ba.
Mamaki ne lullu6e ya Haleesa tad'ago daga jikinshi yaya salman fa kace"?
Gyad'a mata kai yayi yace ni kaina lokacin da ta gwada min pic nashi nayi mamaki, sai take fad'a min wai d'ikin takai shagonshi anan suka had'u har suka qula soyayya da na sanarda ita cewa yayanki ne sosai kunya ta lullu6e ta tadinga rok'ona kada na sanarda ke.
Da kaina naje gidansu wajen Hajiya khareema na rok'eta tabar Maryam ta aure Wanda takeso tun da ta hak'ura da ni da kyar na shawo kanta ta amince a halin yanzu Maryam in-law d'inki ce don haka kidaina kishi da ita Habeeb Lamido naki ne ke kadai.
Yak'arasa magana had'e da d'ago fuskarta halshenshi yasa ya tsotse hawaye kumatunta banaso na k'ara gani hawaye akan wannan kyakyawar fuska.
"Ta yi murmushi had'e da 6oye fuskarta a k'irjinshi.

_some hours later_

Habeeb yana kwance akan kujera Haleesa tana tsaye wajen k'afafunshi ta na Jan k'afafun nashi da k'arfi tana magana cikin shagwa6a ni fa ba zan
yarda ba sai ka goya ni katashi ka goya ni nace tak'arasa magana cikin ihu.
"Habeeb ya mik'e zaune yatsunshi yasa toshe kunnenshi yana dariya ta k'asan ido yake kallonta yace Leesa please ki barni na huta mana ni narasa dalilin da yasa ki ka zama stubbornly"?
"Kukan shagwa6a tasa mishi babu shirri ya duk'a ta dalle bayanshi yadinga zagaye parlour da ita suna kyalkyalar dariya abinsu rayuwa ta yi musu dad'i a koda yaushe za ka, tararda su manne da juna ko kitchen Haleesa tashiga Habeeb yana rungume da ita har ta kamalla musu girki, ita kanta Haleesa wasu lokuta tana mamaki yadda Habeeb Lamido yake haukar sonta.
Cikin kwanaki 3 kacal so da shak'uwa mai k'arfin gaske yashiga tsakaninsu, har basa son dai-dai da 1 second su nisanta da juna.

_Monday morning_
{ around 9:30am}
"Leesa yanzu tafiya za ki yi barni"? Habeeb Yafad'a kamar zai yi kuka.
"A sanyaye ta zauna kusa da shi tarik'en hannunshi, nima ba'ason raina zan tafi na bar ka ba saidai tafiya ya zame mini dole.
"Ba dole bane Leesa in kinso za ki iya zamanki ba abunda sweetheart za ta yi ita kanta farin ciki za ta yi in tadawo ta tarrarda mu a tare.
''Tabe baki tayi ni dai wannan abin kunya ba da ni ba sai ka jira har zuwa lokacin da mom taga dama tadawo maka da ni.
Shikenan ni dama can! Nasan ba wani damuwa ki ka yi da ni ba ae sai kitashi na mayarda ke yana magana ne had'e da mik'ewa tsaye.
Girgiza kai ta yi ta mik'e tsaye tak'ara rik'on hannunshi karka yi, fushi da ni my handsome don ba zan iya tsallake umarnin mom bane.
Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba ya wani kauda fuska shi kadai yasan irin rad'ad'i da yake ji Sam bayaso abunda zai nisata shi da ita.
A shagwa6e tace my handsome don bakace komai ba naga ka wani kauda fuska kamar bakaso kallona"?
"Ya ja iska had'e da zare hannunshi daga nata, da sauri tafad'a k'irjinshi tasa mishi kuka duk duniya ba abunda ya tsana irin kukanta a rikice yad'ago fuskarta Leesa please kidaina banason kukanki yana d'aga min hankali ki barni da naji da kewarki.
To ba kai bane ka yi fushi ni kuma banaso fushinka, tak'arasa magana cikin muryar shagwa6a.
Yatsashi yasa ya zagaye lips d'inta daga bisani ya lalla6o bakinta ya had'e da nashi, tsawon lokacin suka dauka manne da juna daga bisani Haleesa ta zare jikinta daga nashi tanufi k'ofar fita ya Mara mata baya.
"Direct parking lot suka nufa Habeeb ya kwadawa Bala kira Bala da ke zaune a main gate ya amsa had'e da tasowa yanufo wajensu.
"Kai Bala bani car key zan kai 'yar yarinya nan gida gaba d'aya tafitine ni da rigima yak'arasa magana had'e da dungure mata kai.
''Tsalle Haleesa ta daka ta dire a gefe d'aya tana

Please Login or Register in order to submit comment