Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rigar zip yak'i rufewa sai fama gunguni take yayin da yaya Habeeb ke tsaye a k'ofar kitchen suna fira shi da Ammi tun kafin tafito daga d'aki take kwada masa kira yaya Habeeb! Wannan wane irin d'iki ne ka yi min zip yak'i rufewa"?
"Yaya Habeeb yadafe bakinshi yana dariya tak'araso daf da shi yaya Habeeb ina magana ka kyalle ni tafad'a cikin shagwa6a ya sauke hannunshi daga dafe bakinshi da ya yi ya k'ura mata ido ba ko kiftawa a shagwa6e tace me ye haka yaya Habeeb ya ina maka k'orafi akan zip d'in riga na yak'i rufewa kai kuma kana aikin kallona"?
Ya yi murmushi had'e da cewa babylove rigar nan ta yi masifar yi miki kyau, muddin nayi sake kika fita da ita ba k'aramin "accident za ki had'a dad'i ya lullu6e Haleesa ta kada kwayar ido ta kyalkyale da dariya Ammi da ke kitchen tace Allah yaraba mu da masifa duk abunda kyau shi ya zama masifa abun gudu ne yaya Habeeb ya dube Haleesa suka kyalkyale da dariya Ammi tace au ni ku ke yiwa dariya to maza ko bace min da gani gaba d'aya kun toshe k'ofar kitchen kun hanawa iska shigowa sai fama shak'ar hayaki nake Yaya Habeeb yarik'o hannunta zo mu je d'aki mu yi sirri banaso Ammi ta ji abunda za mu fad'a a bakin k'ofar d'akin Haleesa ya ja birki ya yi k'asa da murya kada Ammi ta ji abunda yakeso fad'a babylove ina matuk'ar sonki shiyasa nake kishinki wallahi banaso kowane d'a namiji ya kalli kyakyawa surarki na rok'e kada ki saka rigar nan ki barta sai mu yi aure ki yi min kwalliya na dinga gani ni kadai kinji babylove"?
Murmushi Haleesa ta yi tace yaya Habeeb rigima ina lissafi kusan kala 4 ka yi min d'iki kana hanani sakawa kace na ajiye sai mu yi aure ni fa hijab nake sakawa ba haka zan fita ba tak'arasa magana had'e da turo baki yaya Habeeb yak'ara narkewa sai kace manshanu na amince ki sakawa wad'anchan amma wannan ki ajiye ki yi min kwalliya amarci dariya sosai Haleesa ta yi daga bisani tace shikenan amma bana iya rufe zip din rigar da kaina cikin sigar jin dad'i yace wannan ba matsala bane ranarda da duk kika saka rigar ni da kaina zan k'arasa rufe miki zip da sauri Haleesa tarufe fuskarta da tafin hannunta yaya Habeeb yayi dariya yace bara na koma shago salman yana jira na in nadawo da dare zan ji dalilin wannan rufe fuska yajuya yafice Haleesa tadawo daga dogon tunani da ta afka tafashe da matsananci kuka "Allah sarki yaya Habeeb Allah ya yi nufi bara maka kwalliya da wannan rigar wance na d'auki tsawon lokacin ina adana ta kuka sosai Haleesa ta yi mutuwar yaya Habeeb tadawo mata sabuwa dal tsawon lokacin tadauka tana kuka duk ta6ata kwalliya da ta yi saida tagaji don kanta ta yi shiru, cikin sanyi jiki tanufi bathroom ta wanke fuskarta tasake Shafa powder da kwalli duk da haka kallo d'aya za ka yi mata kagano ta yi kuka har ta linke rigar ta mayar a trolley sai kuma tafasa domin bata ga amfani ajiyar ta da take yi tasaka inner wears ta zura rigar ta yi tsaye gaban dressing mirror tana kallo yadda rigar ta yi matuk'ar yi mata kyau hawaye suka ciko mata ido da sauri ta mayarda su ta rufe zip amma yak'i rufewa duka kamar yadda ya yi a wance lokacin kasancewa Haleesa bataso d'a kwalli shiyasa ta yane kanta da d'a k'aramin mayafi zuciyata a chukushe tafice tunawa ta yi da dokokin da Habeeb Lamido ya gindaya mata gabanta na fad'uwa tasoma haura upstairs karon na farkoda k'afarta ta ta6a takawa bedroom d'in shi......


Jeeddah Aliyu🌹


[04/11 7:06 pm] Jeeddah Aliyu🌹: ```💝NI DA YAYA HABEEB💝```

_❣the sweetest love_❣

Na Hauwa Shehu Aliyu🌹

```®NWA```

°°°°```In Dedication```°°°
*To Shehu Aliyu family's*

```64```

Da sauri-sauri Haleesa ta sauke numfashi ta hadiye yawu Habeeb yak'ara dank'e yatsunta yana wani lumlumshe idanu "am sorry baby bara k'ara fita na barki ke kadai kinji"?
Haleesa tayi murmushi yak'e tasada kai k'asa zuciyarta cike da mamakin Habeeb lalle Habeeb Lamido cikakken d'an duniya ne, kallo d'aya tayi mashi ta gano duk abin da yakeyi mata"pretending ne, muryar imaan ce ta katsi mata zance zuci "Daddy aunty Maryam tace "new mommy da ka kawo min 'yar talakawa ce bata dace da kai ba kum..."shut up Imaan bana hanaki irin wannan surutu maras kan gado ke fa da bakinki ki ka ce kinaso na kawo miki "new mommy ba"?
"Imaan ta gyad'a kai
Duk ranarda na K'ara jin irin wannan magana a baki ki bara k'ara siya miki "Ice cream
Rau-rau da idanu Imaan ta yi kamar za ta yi kuka tace, "Daddy na daina Habeeb ya shafi cheek in ta ya juya wurin Maryam da ke tsaye tana fama da tafarfasa zuciya ya dank'ara mata harara mai dauke da gargad'i ya mik'e tsaye ya sunkuce Imaan ya dube Haleesa yace baby in kin sallame visitors in ki ina jiranki a sama bai jira amsar da Haleesa za ta bashi ya haura upstairs cikin d'aga murya Maryam tace kadawo da imaan tafiya za mu yi batare da yajuyo ba yace za ki iya tafiya Co's imaan tadawo gidan ubanta
A tsoroce Maryam tace wannan wane irin d'aye hukunci ne yaya Habeeb"?
Cikin isa da tak'ama yace saboda ni nake iko da imaan
Maryam tak'ara harzuk'a Duk tsawon wannan lokacin da imaan ta dauka a tare da mu baka ta6a nuna kanada iko da ita sai yanzu ba yadda za'a yi muna raye imaan ta zauna a hannun kishiya uwa in har kai baka sonta to mu munasonta matuk'ar ka ga imaan ta zauna a gidanan ka tabbata cewa ka rataya mini igiyoyi aurenka Inda har hakan bata kasance ba wallahi imaan bara ta zauna a hannun wannan 'yar Matsiyata, Habeeb ya bud'e baki da d'ibin mamaki yana kallonta cike da takaici yadawo cikin parlour ya sauke Imaan yanuna Maryam da yatsa yasoma magana cikin b'aci rai banaso iskanci banza da wofi maryam har ni za ki fadawa magana banza zai fiye miki alkhairi ki tattara k'afafu ki ki bar min gida tun kafin ki kaini bango nayi miki rashin mutunci nasha Fad'a miki bana sonki na tsane ki da yake ke dak'ik'iya ce kin kasa gane hakan zeely ta janyo hannun Maryam tace zo mu tafi Maryam sannu-sannu bata hana zuwa saidai ajima ba'a kai ba lokacin na zuwa da za kiyi fatali da gwannati 'yar Matsiyata ki mulki yaya Habeeb son ranki "Habeeb yak'ara harzuk'a yanufi wurinsu da gudu suka fice daga parlour da Ku tsaya na nuna mu Ku yadda za Ku yi mulki na 'yar Matsiyata nan da Ku ka rena tafi Ku daraja da k'ima a wurina'yan iska tarkace tsiya marasa tarbiyya, kuma duk ranarda na k'araji d'aya daga cikinku ta kira matata da suna 'yar Matsiyata dai na gwaje mata baki Haleesa ta tsura masa ido tana mamaki yadda kalamai nan suke fitowa daga bakinshi yana juyowa suka had'a ido ya watsa mata harara ke! daina kallona kin wani tsareni da idanu sai kace mayya da sauri ta sada kai k'asa yak'araso daf da ita saida yak'are mata kallon wulak'anci ya ja tsoki ke! Ina son ki bud'e fakanfakan kunneye ki masu kama da na zomo ki saurare abunda zan Fad'a miki domin banaso asami akasi ki ce baki fahimce abunda nake nufi duk magana da Habeeb yakeyi Kai Haleesa na sunkuye tana murza zobe yatsanta saida yaja iska sannan yacigaba da cewa ina matuk'ar son imaan banida buri da yawuce naga rik'o ta yadawo hannuna musanmman da na fahimce irin rik'o sakainiya kashi da akeyi mata a duk lokacin da na je ganin Imaan raina na matuk'ar sosuwa a yadda nake tararda ita Sam bata samu kyakyawa kulawa gaba d'aya tarbiyyar ta na wurin 'yar aiki Imaan na buk'atar wance za ta maye mata gur6i mahaifiyarta da tarasa, dalili da yasa lokacin da mom ta yi min tallarki na amince zan aure ki, ina fatar za ki rik'e Imaan da amana sai lokacin Haleesa tad'ago tasauke ajiyar zuciya, cikin sanyi murya tace insha Allah zan bawa Imaan kyakyawa kulawa bara ka ta6a samu na da aikata ba dai-dai a gareta ae d'a na kowa ne yadda zan kula da 'yar da na haifa haka zan kula da ita tak'arasa magana had'e da sada kai k'asa "Habeeb Lamido ya ja wawa tsoki ya wani zare idanu ke! Ba dai ni kike tunani zan miki ciki har ki haihu"?
A tsorace Haleesa tak'ara d'agowa tasauke "eye's ball d'inta akan fuskarshi yadda ya murtuk'e fuska ya yi mugun kad'a anta cikinta cike da takaici yace kidaina yaudara domin ni ba abunda zan tsinta a jikinki yanuna jikinta da yatsa shi yana yatsina yacigaba da cewa na mafalki ma da kike samu da ina da yadda zan datsi shi da tuni na taka miki birki da fatar kin fahimce inda na dosa"?
" Batare da Haleesa ta fahimce abunda yake nufi ba ta gyad'a kai ya tabe baki had'e da cewa ki bani aro hankalinki na karato miki dokoki zaman gidana idan kika kiyaye su za ki ji dad'i zama da ni doka ta farko na tsani k'azanta shiyasa bana sha inuwa d'aya da k'azami in har bakida tsafta ki fara koyo in kuma kinada sai ki k'ara bisa ga wance kike da saboda ni mutum ne mai tsanani kyakyame gaske doka ta biyu ya zame miki dole duk wani abu da kika yi amfani da shi ki mayarda shi a muhallinsa hatta da "toothpick yana da muhallinsa a gidanan, sai kuma doka ta uku dole ki girmama ni domin ni mutum ne mai matuk'ar so girma daga yau za ki dinga gyara mini sitting room da kuma bedroom dole ne kullum ki wanke mini bathroom amma ban amince ko "Noodles ki dafa da sunana, da sauri Haleesa ta dube shi fuskarta d'auke da d'inbi mamaki yak'ara zare mata shegu idanunshi masu masifar tsorata ta kidaina mamaki domin ba ki kai matsayi da ki za ki dafa mini abinci shi ma gyara rooms in da kika ji nace kidinga yi min ba wai kin Kai matsayin shiga d'akina bane kawai banaso kidinga cinye min abinci a wofi sai ki kiyaye dokoki da na shinfida miki domin shine kwaciyar hankalinki a gidanan ya sunkuce Imaan suka haura upstairs yabar Haleesa sake da baki hawaye masu masifar zafi suka wanke mata fuska tasaka bayan hannunta ta goge, bayan "10 minutes da fitar Habeeb sai gashi yadawo yana rik'e da hannun Imaan jin karar footstep in shi yasanya Haleesa tajuya yasauya kaya zuwa dark blue Jean's da white shirt ya sha stocking da belts mai tambari D&G ko kallon gefen da Haleesa take zaune bai yi ba yafice yayin da Haleesa ta bi su da kallo haka tacigaba da zama a parlour tana sak'e-sak'e kiran sallah magarib ne ya mayarda ita bedroom in ta ta yi wanka had'e da alwala ta yi sallah tana gama sallah tasoma lazimi har akayi kiran sallah isha'e ta mik'e ta gabatarda sallah bayan tagama sallah tanufi "dressing mirror ta yi simple make up tasanya yaloluwa night gown pink colour ta fashe jikinta da designer perfume ta tufke gashin kanta da k'ato ribbon pink colour kaitsaye tanufi downstairs parlour peter ta hango a dining area yana jera abinci a table tanufi wurinshi peter na ganinta ya rusuna ya gaida ta cikin sakin fuska ta amsa masa ya ja mata kujera ta zauna cikin gur6ataciya hausar shi yace mah me za'a zuba miki"?
Haleesa ta yi shiru daga bisani tace zan yi serving da kaina za ka iya tafiya Peter yajuya yafice ta bud'e warmers pounded yam ta zuba had'e da egusi soup ta sha smoked fish tana ci tana gyada kai alama abinci ya yi mata dad'i bayan ta cika cikinta tanufi parlour ta kwanta akan 3 star tasoma tunani wance irin rayuwa za ta yi da Habeeb Lamido.

_9:00pm_

Sai misali k'arfe 9:00pm Habeeb yadawo yana sa6e da Imaan a kafad'arsa ta yi bacci, yana shigowa parlour Haleesa ta mik'e da sauri tanufi wurinshi sannu da zuwa yaya Habeeb Imaan ta yi bacci ne"?
Kallon sama da k'asa ya yi mata ya ja d'an siriri tsoki cikin husky voice in shi, yace ba ki ga alama bane ko ke makauniya ce"?
Murmushi ta yi ta lamgwabe kai dallah matsa ki bani wuri ki yi wani tsare da tambayoyinki na shirme Allah ya ba ka hankuri kawo ta na kaita bedroom kamar ba zai mik'a ta ba saida ya yi mata kallon da ta tsana sannan ya mik'a mata Imaan garin amsa ta hannushi ya goge k'irjinta saura kiris Haleesa tasaki Imaan cikin zafin nama yarik'e Imaan jikin Haleesa yadauki rawa sai fama zarar ido take wani mugun kallo ya watsa mata had'e da daka mata tsawa ke! Wance irin mahaukaciya ce"?
Don kawai hannuna ya goge k'irjinki shine za ki sake min yarinya Allah yaso ki da tafad'i Allah da sai na 6arar da ke Humm! Haleesa tasauke ajiyar zuciya cikin tsanani jin kunya tasada Kai k'asa ya ja tsoki ya ra6a gefenta ya haura upstairs bedroom in shi ya wuce da Imaan ya shinfid'e ta had'e da sauya mata kayan jikinta zuwa sleeping dress ya kwa6e kayan jikinshi yadaura "bathrobe towelling yanufi bathroom yacika bathtub da ruwa masu dumi-dumi ya zuba bath perfumes masu k'amshin gaske ya yi kwance cikin bathtub ya d'auke remote control ya yi switch on in TV ya murd'o BBC channel ya murza liquid soap mai k'amshin "guava fruit a skin in shi saida ya share "20 minutes yana wanka sai kace zai sauya skin colouring d'inshi daga bisani yafito daga bathroom d'in ya yada zango a gaban dreesing mirror ya shafe jikinshi da lotion ya bi lungun da sak'o na jikinshi da perfumes yasaka pajamas sky blue colour ya fice zuwa downstairs parlour Haleesa na zaune ta rafka tagumi kallo d'aya ya yi mata yadauke kai yanufi dining area Haleesa tad'ago ta sace kallonshi ta tabe baki ga ni zai yi serving in kai shi yasa ta tuna da nasiha da baffa da Ammi suka yi mata akan ta bi Habeeb lamido sau da 'kafa domin aljannata tana k'ark'ashi k'afarshi bai kamata furuci shi yayi tasiri akanta tak'i yi masa biyayya da sauri ta mik'e tanufi dining area har ya yi nufi ya bud'e warmers kamar daga sama ya ga hannun Haleesa ta dafe murfi ta wani lamgwabe kai tadawo kala tausayi "please yaya Habeeb ka bani dama nasamu wannan lada kallon hadari kaji ya yi mata ya murtuk'e fuska ya janye hannunshi ke! Ban Fad'a miki a rayuwa na banaso shishigi ni za ki yi wa kilinbibi da kissa da kisisina shine don tsabar iskanci har da su saka "transparent night gown don ki ja hankalina wallahi ki yi a banza ki yi yawo nicked a gidanan ko dar bara ji ba Co's bana kallonki a matsayin mace, ki gaugauta ki bace mini da gani na tsani kallon wannan "ugly face naki duk k'ok'ari Haleesa ta yi ta danne hawaye ta ta k'asa shar hawaye suka tsiyayo akan fuskarta ke! Dallah bace min da gani banza 'yar k'auye "classless kawai da gudu Haleesa tanufi bedroom in ta tafad'a bisa bed tasaki kuka mai tsunma zuciya dama ga Haleesa da kuka banza marigayi yaya Habeeb ya riga ya sagarta ta abun d'a k'ank'ani ya isa yasaka ta kuka har da su majina ta bangare Habeeb kuwa yana gani tafice ya ja tsoki ya Ciro phone ya yi dialling number Bala P.A kai! In ka ga dama ka zo mu ci abinci bai jira amsar da Bala zai bashi ya yi "hanging up after 4-6 minutes sai ga Bala yashigo direct yanufi "dining area cikin zolaya yace "Boss na yi zato Amarya ta ture gwanati na kadaina cin abinci da ni ashe har yanzu matsayina na nan bai sauya ba yak'arasa magana yana dariya shak'iyanci Habeeb ya wani dage gira sama ya cize lips in shi yana yi wa Bala kallon k'asa ido daga bisani yace wallahi Bala ka kiyaye ni karka ga kamar bara iya firing naka kanemi ka raina mini hankali Bala yadafe baki yana dariya k'asa-kasa ya bud'e warmer ya yi musu "serving Habeeb yad'an tsakare abinci ya mik'e batare da ya dube Bala ba yace bacci nakeji zan kwanta inda ka gama ka rufe mana k'ofa "Bala yacika baki da katuwar loma pounded yam don tsabar k'arfi hali irin na shi saida ya furta abunda ke ranshi "Boss bacci tun yanzu kwata-kwata 10:08pm sai naga kamar ka yi sauri kwanciya yak'arasa magana had'e da tand'e yatsunshi wani mugun haushi yak'ara turnuk'e Habeeb rasa abunda zai ce da Bala ya ja tsoki yajuya kawai yanufi bedroom d'inshi ya gyarawa Imaan kwanciya ta ya yi pecking nata a goshi yanufi doguwar kujera kwara d'aya chal da ke cikin room d'in da alama had'e take da bed yaciro System d'inshi da ke soke a socket tana charging ya zauna a tsakiyar kujera ya langwashe k'afafu shi yasoma kallon pic's d'in motoci a wani Company motoci da ke Japan suna turo masa simple na new models na car's har 2:00 o'clock ta buga yana zaune sai fama zabga hamma yake bacci yakeji sosai ya mik'e tsaye da kyar ko rufe laptop d'insa bai yi ba yafad'a kan bed ya karato addu'a kwanciya bacci ya tofe Imaan ya dauki remote yak'ara gudun Ac al'ada Habeeb ce Sam baya iya kwanciya sai yaji sanyi Ac na ratsa k'assa jikinshi sosai, ya jawo blacket ya lullu6e su ya lumshe sexy eye's d'inshi bai d'auki "long time bacci ya yi nassara kwashe shi ta 6angare Haleesa kuma ta ci kuka ta ita kadai ba mai rarrashinta gani kuka ba zai amfane ta da komai ba ta mik'e tashiga bathroom ta daura alwala tasoma Nafilla saida ta yi raka'a 11 ta d'aga hannaye ta sama hawaye na zuba akan fuskarta tasoma kai kukanta wurin Ubangiji da baya bacci _ya Allah ina tawasali da kyawawa sunaye ka masu girma da d'aukaka Allah Kaine_ _masani sirri da ke boye da sirri da ke baiyane ya Allah ina rok'o ka idan har aure na da Habeeb Lamido akwai alkhairi a cikin sa Ya Allah kabani_ _hankuri da juriya cinye wannan jarabawa ya Allah ka tausaya mini ka cire min son marigayi yaya Habeeb a zuciyata, ka maye mini zuciyata ka mini zuciyata da son mijina_
_Ya Allah kabani iko yi biyayya a gareshi Ameen_ ta Shafa addu'ar ta mik'e had'e da linke pray mat tanufi bed ta kwanta sai kawai ta ji duk wani b'aci rai da takeji yafita bacci mai dad'i gaske ya yi awo gaba da ita.

```HABEEB```
Zaune yake akan resting chair yana shan ice cream yashak'i k'amshin turare "musk Al-ghazal, bai Sam lokacin da ya lumshe idanushi daga bisani ya bud'e su yasauke ganinshi akan pretty face d'inta sai fama zuba masa murmushi take cikin tafiya kassaita tanufi wurinshi tashige jikinshi ta lafe kamar magge Habeeb yasaki sanyayar ajiyar zuciya, chan k'asan mak'oshi sa ya kira sunanta _leesa_ shiru ta yi bata amsa ba ya daura bakinshi akan kunneta ya maimaita sunan nata ta sigar Jan suna iska bakinshi ya ratsa dodo kunnenta ba bu shiri tad'ago dara-dara idanuta ta dube shi kallon-kallon mai cike da tsan-tsan so suke yi wa junansu daga bisani leesa ta d'auke kanta had'e da kar6e roba ice cream d'in hannunshi ta ciko spoon tasaka masa a baki bai ankara ba yaji bakinta akan nashi a hankali take shan ice cream d'in da tasaka masa a baki saida tashanye shi tass sannan ta debo tasaka a nata baki ta turawa Habeeb bakinta ta lumshe idanuta ga bakinta a bud'e Habeeb ya dube ice cream d'in da ke shinfide akan halshenta ya matsa face d'inshi daf da nata ya zura bakinshi cikin nata firgigit Habeeb ya zabura ya mik'e zaune daga mafalki da yakeyi yadafe goshi zufa ya tsatsafo masa yajuya ya dube Imaan da ke ta fama sharar baccinta
"Ya sauke ajiyar zuciya yafi a kirga yasoma aikawa brain d'inshi zafafa tambayoyi _meke faruwa da ni"?_
_miyasa nake yawan mafalki yarinya nan"?_
_iya sanina bana sonta batada muhalli a zuciyata amma a duk lokacin da na kwanta bacci sai nayi mafalkinta to me hakan yake nufi"?_
Ya ja iska mai zafin gaske ya furza Haleesa tanaso ta zamewa rayuwata karan tsaye ya lumshe idanushi mafalki da ya yi yasoma yi masa shawagi sai kawai ya tsince kanshi da sakin dogon tsoki, ya shafi sumar kanshi had'e da lashe lips d'inshi wani irin haushi da tsanar Haleesa suka mamaye masa zuciya cike da takaici ya gyara zaman pillow ya kwanta.

```WASHE GARI ```

_10:00am_

Haleesa na zaune a gaban dressing mirror tana Shafa lotion, ta d'a Shafa powder had'e da kwalli ta mik'e tanufi tarin trolley's d'in da ke jere tasauke guda d'aya tasoma kallon kayan da ke ciki duk tari kayan da ke ciki rasa na sakawa ta yi domin ganin take yi, matsayinta bai kai na saka wad'annan tsadadu kaya tsohuwar trolley d'inta tadauko ta zuge zip karaf idanuta suka sauko bisa wata fitted gown na shacking material a sanyaya tadauki rigar nan take kwakwalwa ta tasoma tuno mata da abunda yawuce ba za ta6a manta ranarda marigayi yaya Habeeb ya kawo mata d'inki rigar nan daga d'akinta tafito sanye da rigar zip yak'i rufewa sai fama gunguni take yayin da yaya Habeeb ke tsaye a k'ofar kitchen suna fira shi da Ammi tun kafin tafito daga d'aki take kwada masa kira yaya Habeeb! Wannan wane irin d'iki ne ka yi min zip yak'i rufewa"?
"Yaya Habeeb yadafe bakinshi yana dariya tak'araso daf da shi yaya Habeeb ina magana ka kyalle ni tafad'a cikin shagwa6a ya sauke hannunshi daga dafe bakinshi da ya yi ya k'ura mata ido ba ko kiftawa a shagwa6e tace me ye haka yaya Habeeb ya ina maka k'orafi akan zip d'in riga na yak'i rufewa kai kuma kana aikin kallona"?
Ya yi murmushi had'e da cewa babylove rigar nan ta yi masifar yi miki kyau, muddin nayi sake kika fita da ita ba k'aramin "accident za ki had'a dad'i ya lullu6e Haleesa ta kada kwayar ido ta kyalkyale da dariya Ammi da ke kitchen tace Allah yaraba mu da masifa duk abunda kyau shi ya zama masifa abun gudu ne yaya Habeeb ya dube Haleesa suka kyalkyale da dariya Ammi tace au ni ku ke yiwa dariya to maza ko bace min da gani gaba d'aya kun toshe k'ofar kitchen kun hanawa iska shigowa sai fama shak'ar hayaki nake Yaya Habeeb yarik'o hannunta zo mu je d'aki mu yi sirri banaso Ammi ta ji abunda za mu fad'a a bakin k'ofar d'akin Haleesa ya ja birki ya yi k'asa da murya kada Ammi ta ji abunda yakeso fad'a babylove ina matuk'ar sonki shiyasa nake kishinki wallahi banaso kowane d'a namiji ya kalli kyakyawa surarki na rok'e kada ki saka rigar nan ki barta sai mu yi aure ki yi min kwalliya na dinga gani ni kadai kinji babylove"?
Murmushi Haleesa ta yi tace yaya Habeeb rigima ina lissafi kusan kala 4 ka yi min d'iki kana hanani sakawa kace na ajiye sai mu yi aure ni fa hijab nake sakawa ba haka zan fita ba tak'arasa magana had'e da turo baki yaya Habeeb yak'ara narkewa sai kace manshanu na amince ki sakawa wad'anchan amma wannan ki ajiye ki yi min kwalliya amarci dariya sosai Haleesa ta yi daga bisani tace shikenan amma bana iya rufe zip din rigar da kaina cikin sigar jin dad'i yace wannan ba matsala bane ranarda da duk kika saka rigar ni da kaina zan k'arasa rufe miki zip da sauri Haleesa tarufe fuskarta da tafin hannunta yaya Habeeb yayi dariya yace bara na koma shago salman yana jira na in nadawo da dare zan ji dalilin wannan rufe fuska yajuya yafice Haleesa tadawo daga dogon tunani da ta afka tafashe da matsananci kuka "Allah sarki yaya Habeeb Allah ya yi nufi bara maka kwalliya da wannan rigar wance na d'auki tsawon lokacin ina adana ta kuka sosai Haleesa ta yi mutuwar yaya Habeeb tadawo mata sabuwa

Please Login or Register in order to submit comment