Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
É—aukar ido,ba komai bane cikin akwatin sai sarÆ™oÆ™inta na gwal kala -kala. Wata yar Æ™aramar akwatin ce ahannunta tana mai kallon sarkar fattu data adana aciki. Murmushi tayi tare da faÉ—in"nayi alÆ™awarin keda haÉ—uwa da ahalinki saidai alahira,zanyi Æ™oÆ™arin toshe duk wata hanya da zata sadaki dasu,domin cike burina" ammi ta faÉ—a cikin zuciyarta tana mai murmushi da Æ™arewa kyakyakywar sarÆ™ar kallo. Kamar daga sama ta tsinkayo sallar Adeeb .dan haka cikin azama ta maida sarÆ™ar cikin dan akwatin tare da rufe babban ta maida shi ajiyarsa. Zama Adeeb yayi kusa da ita ,ba tare da yaga abinda tayi ba.cikin zafin zuciya yake magana da harshen larabci" ammi zan É—auki mataki mai tsanani akan Rashad da mahaifiyarsa ,Dan kuwa sun Æ™etare iyakarsu" Adeeb ya faÉ—a yana huci cikin É“aci rai. Wani daÉ—ine ya mamaye zuciyar ammi ,amma a zahiri da sauri ta kamo hannun Adeeb tana mai marairaice fuska tace " haba habeebee ,me yayi zafi ?me sukayi maka?Indai akan wannan maganar ce ,to kabar komai ahannuna zanyi wa tubkar hanci,bazai kara zuwa gurin ta ba"Ammi ta faÉ—a tana mai shafa bayan hannun Adeeb É—in. Girgiza kai yayi cike da jin tsanar Rashad da Amma,kafin yace " ba wannan maganar bace,ammi Rashad ya É—auke sarÆ™ar da zata zama makamin da zai sada yarinyar da mahifanta,kuma nasan wannan tabbas shirin Amma ne, Ammi na rasa me kika tsarewa matar nan ta Tsaneki da ahalinki baki É—aya,kullum burinta ta ganmu cikin tashin hankali ,why Ammi ?" Adeeb ya faÉ—a cikin mugun damuwa da tausayin Ammin nashi. Sosai Ammi ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ,kafin ta fara magana" habeebee nima bansani ba ,duk yadda nake Æ™aunarta da iyalinta,amma sam bata gani tun kana yaro take Æ™oÆ™arin saita ga bayanka ,amma Allah bai bata Sa'a ba, kai dai karvi gaba da haÆ™uri, sannan kabi komai cikin lumana.kuma awannan karon na goyi bayan ka É—auki mataki akansu har sai sun bayyana sarÆ™ar nan" Ammi ta faÉ—a cikin Æ™arfafa gwuiwa ga Adeeb . Jinjina kai yayi cike da gamsu da shawarar ammin nashi.sun jima suna tattaunawa akan al'amarin ,ba abinda ammi ke yi sai tunzura Adeeb cikin cikima da basira. Amma kuwa tana zaune abakin dagon Rashad,yayin da take shafa masa maganin zafi aciwonsa bayan yayi wanka da ruwan dumi.sosai take jin zafin abinda Adeeb yayiwa Rashad,kalli yadda yaji masa ciwo kamar wani marar gata?lallai saita É—auki mataki,dan bazata yarda da wannan cin mutuncin ba. Kallon Rashad tayi wanda yake É—an runtse ido idan ta shafa masa maganin zafin. "HaÆ™iÆ™a Adeeb yana wuri gona da iri masarautar nan,kaima fa É—ane ba bawa ba,dan me zaiyi maka irin wannan dukan?saikace ya sami yaronsa, haÆ™iÆ™a bazan amince ba ,dole mai martaba ya shiga maganar nan,kuma wllh nayi alÆ™awarin sainaga bayan Ammi ,dan kuwa ita ke daure masa....yake abinda yaga dama.haka kawai an maidamu kamar wasu matasa iko agida,bazai yiwuba ,sam bazan laminci wannan abun ba" Amma ta kai Æ™arshen zancen ta cikin fushi sosai da bacin rai. Kallonta Rashad yayi shima cikin É“aci rai,yana mai faÉ—in "amma kibar wannan maganar atsakanin mu ,kar ki bari mai martaba yaji,dan kuwa da kaina zan É—auki mataki,wllh saina yi masa abinda sai yayi dana sanin aikata min wannan abun akan wata bare,ke dai kawai ki zubamin ido" Rashad ya faÉ—a yana mai kitsa abubuwa cikin ransa. Wannan kenan. BaÆ™i sun fara zuwa ta ko ina ,manyan sarakai da yan siyasa na Æ™asar Misra, ko ina acikin gidan jama'ane keta kaiwa da kawowa,dan kuwa yau ne za'a gudanar da Æ™ayatacciyar walimar murnar dawowar prince Adeeb gida,daga É“angaren Amma baÆ™i sunzo sosai,matan sarakuna na Æ™asashe da dama,da matan manyan masu kudi da yan siyasa.dan haka hadimai sai kaiwa da kawowa suke dan kula da baki. Yayin da bangaren Ammi kuwa ,ba magana ,dan kuwa itace uwar taro ,mai gayya mai aiki kenan,sosai ta tara manyan matan sarakuna dana yan siyasa ,da matan manyan attajiran larabawa,kai harda na Æ™asashen Afrika . Ammi taci uwar kwalliya cikin kaya na alfarma ,tayi ado da gwala-gwalai sai Æ™amari take bugawa tana cikin matan data gayyata suna ta hira kafin a fara gudanar da taro. Busar sarewace ta karfe fadar ,alamun da ke nuna wasu baÆ™in sarakan sun sami hallara,murmushi Ammi tayi dan kuwa ta gane busar ko ta wace Æ™asace, ba kowa bace bace Æ´ar uwarta gimbiya Zulaihat ,wacce ke auren Sarkin gana.dan haka cikin farin ciki ta mike tare da cewa matan tana zuwa.kafin ta fice zuwa farfajiyar da aka ware musamman dan tarbar baÆ™in ta ,gurine Æ™ayatacce wanda yasha ado ,aka wadatashi da komai na jin dadi. Tana tafe haÉ—imanta na biye da ita ,murmushine É—auke akan fuskarta wanda ya Æ™ara Æ™asa ta fuskar tata. Wata farar mace ce kyakyakywar gaske ta fito daga cikin lafiyayyar motar da aka bude,masha Allah matar ta ko ina ta hadu ,fuskarta É—auke da murmushi mai Æ™ayatarwa,idanunta na kan Ammi rungume juna sukayi cikin farin ciki,ammi keyiwa matar Barka da zuwa. Wasu kyawawan yara ne su biyu suka fito daga É—aya gefen,da ala'ma yaran tagwayene duba da yadda suke tsananin kama da juna.yaran zasu kai shekara goma ,saidai yanayin jin dadi da hutu,yasa zaka yi tunanin sun wuce hakan,suna sanye da kaya iri É—aya ,cikin shiga ta ya'yan sarakai. Gurinsu ammi suna nufo cike da murna suka rungume Ammi,ita cikin jin daÉ—i ta rungumesu tare da sunbatar gishinsu,tana mai faÉ—in," yazeed and zayyad my children" ammi ta faÉ—a tana shafa kansu. Part É—in ammi suka nufa gaba É—ayansu,cike da murna. Adeeb ne zaune bakin gado yayin da tareeÆ™ ke gefensa ,yana tashi shiryawa,shi dama Adeeb baida aboki ,tareeÆ™ kaÉ—ai ne abokinsa kuma yaronsa,dashi yake ko wace irin shawara ,dan haka ya zuma suna zaune suna shiryawa,dan Adeeb baya barin kowa ya shigo masa part É—insa, shi fa akan dole yake abubuwan masarauta, dan sam sarauta bata burgeshi, yafi son kasuwancinsa. Kallon tareeÆ™ yayi yana mai faÉ—in,"tareeÆ™ nufa na gaji da wannan shirin Please ya isa haka" ya faÉ—a yana É—an kwaÉ“e fuska cikin salon shagwaba. Murmushi tareeÆ™ yayi yana mai É—aurawa Adeeb wani agogon azurfa ahannunsa kafin yace " yallaÉ“ai yaufa dole kayi haÆ™uri ,dan kuwa saikayi shiga irin ta yarima sosai " tareeÆ™ ya faÉ—a yana É—an danne dariyarsa ganin yadda Adeeb ya wani marairaice kamar zaiyi kuka.harararsa Adeeb yayi yana mai faÉ—in" dariya ma zakayimin ko?ai kaima mugune nasani ,shiyasa kake ta lodamin kaya haka kamar wani dan dako" Dariya sosai tareeÆ™ ya sanya yana mai faÉ—in" yallabai kasan fa yau sauka gaji da ganin yan mata ,dan zasu yi ta kawo maka hari ne,Suda iyayensu,dan haka dole kayi adon da zaka rikitasu" tare ya faÉ—a yana kallon yanayin Adeeb É—in. HaÉ—e rai Adeeb yayi yana mai gwabe baki yace " aikuwa zasu wahalar da kansu ne kawai,dan duk ba wacce zata burgeni acikinsu" ya faÉ—a yana mai mikewa tare da gyara kwalar rigarsa. Murmushi tareeÆ™ yayi kafin yace "amma yallaÉ“ai yau idan Madam ta ganka zaiyi wahala ta gane ka ,dan kuwa kayi matuÆ™ar kyau Masha Allah,yau lafiya ayarimanka sai" tareeÆ™ ya faÉ—a yana mikawa Adeeb wani takobi ,wanda ke matukar gyalli da É—aukar ido. Murmushi ne yakub cewa adeeb,jin tareeÆ™ ya ambaci Madam,kallon kansa ya karayi cikin madubi,masha Allah,ko aljanu ya kalli Adeeb to tabbas dole saiya yaba kyau da Allah yayiwa adeeb. " Kasan bata da lafiya ma,kuma bazata je gurin taron nan ba,zata zauna tare da nanny ,acikin gida,dan haka muyi sauri muje In dubawa sai mu wuce " Adeeb ya faÉ—a yana mai rataya takobin. Murmushi tareeÆ™ yayi yana mai jin dadi cikin zuciyarsa,tabbas hasashensa yana neman zama gaskiya,dan kuwa ya kula Adeeb ya faÉ—a kogin SOYAYYA ,wanda hakan yayi masa daÉ—i,fattu itace daidai da Adeeb." YallaÉ“ai kayi kama da mai son zuwa ganin budurwarsa fa" tareeÆ™ ya faÉ—a yana É—an sosa kansa. Ƙeyarsa adeeb ya É—an buga kafin yace " ka manta dai ba budurwa ba ,mata zakace ,kuma kasan hakkin ta ne induba lafiyarta ,kafin na sawwaÆ™e mata,iya muje" Adeeb ya faÉ—a yana mai kamo hannun tareeÆ™. Murmushi tareeÆ™ yayi yana mai cewa " zaka dawo hanya ma yallaÉ“ai" ya faÉ—a cikin zuciyarsa. Suna fitowa kuwa hadiman da suke Æ™ofar part É—in suka É—auka kirari da bushe bushe irin na larabawa,runtse ido Adeeb yayi cike da damuwa,dan shikam wannan bushe bushe baya so ,dan dai ba yadda zaiyine. Cikin takun izza da isa yake takawa ,tareeÆ™ yan gefensa sai hadiman dake binsa baya suna busa. Kai tsaye ya wuce part É—in ammi,da gudu su zayyad suka taho suka rungume ,Adeeb cike da murna ,dan kuwa sun saba dashi sosai.dagsu yayi daya bayan É—aya yana dariya , Gimbiya suhaimat ma cike da murmushi take kallon Adeeb,yaron yana burgeni sosai,yana da nutsuwa ga don yara,har Æ™asa ya durÆ™usa ya gaida gimbiya suhaimat,da amminsa, sosai ammi ke yaba kyan da Adeeb É—in yayi,wani lambu ta É—auko na na zinare ta sanya masa hannunsa ,tare da wani turare mai kanshi daÉ—i. Murmushi yayi tare da mata godiya sosai,kafin ya É—an juyo yana kallon gimbiya suhaimat,haka kawai yaji gabansa ya fadi sosai ,wani tunanine ya É—arsu cikin zuciyarsa ,saidai da sauri ya kawar da batun daga ransa,ya yayi waje .yana gab da ficewa saiga gimbiya Zulaihat ta shigo part É—in ,taci uban ado kamar wacce zata gasar sarautar kyau. Kallo daya Adeeb yayi mata ya kauda kansa tare da haÉ—e fuska. Ita kuwa neman gigicewa tayi da yadda taga Adeeb yayi kyau,cikin hanzari ta tari gabansa tare da kamo hannunsa tana mai jin kamar ta rungume shi. Wani shegen kallo da Adeeb ya watsa mata ,bata san lokacin datayi saurin sakin hannunsa ba ," kayi kyau my prince"ta faÉ—a tana wani narkar da fuska cike da tsantsar Æ™aunar Adeeb É—in. Harara ya watsa mata tare da tsaki kafin ya bar gurin cikin sauri. Kai tsaye part É—in nanny suka shige ,tana zaune afalo ,gefen ta kuma ,wani É—an karamin akwatine mai kyau da É—aukar ido. Zama sukayi shida tareeÆ™ suka sata atsakiya, gaida ta sukayi,ta amsa cikin farin ciki tana mai shafa kan Adeeb,akwatin nan ta buÉ—e tare da É—auko wani zobe mai kyau sosai ta zira masa ayatsansa na dama. Murmushi yayi tare da sumbatar zoben kafin yace " tana ina " ya faÉ—a cikin salonsa yana É—an yamutse fuska. "Tana ciki magajin faÉ—a " nanny ta faÉ—a . Tashi yayi cikin nutsuwa ya nufi dakin da fattu ke zaune..... Masu karatu ina barar addu'ar ku,iftila'in rusau ne ya faru agarinmu,wllh gidaje sai rushewa suke,,dan Allah ku samu cikin addu'a bayin Allah suna cikin damuwa sosai ,shiyasa kukajini shiru kwana biyu,abin ya taÉ“a har anguwar da mahaifiyata take Muna buÆ™atar addu'ar ku. Na gode Mrs babi ce💘💘 29/08/2022, 10:59 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄 MACIJI NE🪱🪱🪱 Na mammy kabeer (Anty mammy) Elegant online writers📚📚 Free book Page 49/50 _______________Tashi Adeeb yayi cikin nutsuwa, da takunsa irin na jaruman maza ,ya nufi É—akin da fattu ke ciki. Fattu na zaune abakin gado, tayi shiru kamar mai tunanin wani abu,Adeeb ya turo Æ™ofar da sallama É—auke abakinsa,saidai idan ba ka kasa kunne ba ,to bazakaji me yake faÉ—i ba. Dago Kai fattu tayi jin muryar Adeeb datayi,baki buÉ—e take kallon Adeeb ,tunda take arayuwarta,zata iya cewa bata taÉ“a ganin mutum mai kyau irin na Adeeb ba ."masha Allah"fattu ta faÉ—a tana mai mikewa tsaye fuskarta É—auke da murmushi,ta Æ™ure Adeeb da ido kamar yau ta taÉ“a ganinsa. Ƙarasowa Adeeb yayi cikin É—akin,shima idonsa na kanta ,dan haka kawai yaga tayi masa kyau shima . ÆŠan harararta yayi kafin yace " Please karki cinyeni da kallo mana"ya faÉ—a yana É—an wani gwabe fuska cikin shagwabar da baisan yayi ba. Da sauri fattu ta sanya hannu tare da rufe fuskarta tana É—an dariya ,dan kunya taji da yadda yayi salon maganar tasa. "Hamma kayi kyau sosai ,kai mai kyaune" fattu ta faÉ—a kanta a Æ™asa tana É—an mirza hannunta. Wani irin sanyi ne yake ratsa zuciyar Adeeb, sosai yaji daÉ—in maganar fattu ,dan haka cikin wani irin shauÆ™i ya mika hannunsa tare da dago habarta .kallon juna suke ido cikin ido,murmushi Adeeb yayi kafin yace "kin tabbata nayi kyau a idonki?wankana yayi miki kyau?" Ya faÉ—a yana mai kallon lips É—in fattu ,wanda yake ji kamar ya cinyesu. Lumshe ido fattu tayi tare da jinjina kai tace " Hamma bantaÉ“a ganin mutum mai kyan ka ba,kuma Ni kullum ma kyau kakemin" ta faÉ—a tana É—an riÆ™e lips É—in ta na Æ™asa da haÆ™oranta. Wani irin abu Adeeb yaji yana masa yawo ajikinsa,sosai yake jin yana son rungumar fattu ajikinsa ,duk lokacin da yake tare da ita yakan tsinci kansa cikin wani irin shauÆ™in son kasancewa da ita . Murmushi yayi tare da shafa gefen fuskarta yace " to me zaki bani matsayin kyautar dazan fita gurin taro da ita?" Ya faÉ—a idanunsa akan lips É—in ta. Shiru fattu tayi tana É—an rarraba ido,to ita me take dashi ma ?dazata ba Hamma? "Hamma Ni bani da komai fa ,bansan me zan baka ba. Kallonta yake baya ko Æ™iftawa ,ajiyar zuciya ya sauke yana faÉ—in " shikenan tunda ba abinda zaki bani,zan tafi,amma karki fito ko ina kinji?ki kwanta kiyi barci da zaran mun tashi daga gurin taro zanzo in ganki "Adeeb ya faÉ—a yana mai kallon fuskarta. Jinjina kai fattu tayi tana mai kallon Adeeb É—in,sai taji bataji daÉ—i ba ,ace ya tambaye ta wani abu ita kuma bata bashi ba,kuma duk abinda take dashi ma ai shine ya siya mata,to mezata bashi?fattu ta faÉ—a cikin zuciyarta ,fuskarta É—auke da yanayin damuwa. Ahankali Adeeb ya fara takawa zuwa bakin Æ™ofar fita daga É—akin haka kawai yake jinsa wani iri, sam baya don rabuwa da fattu yau É—in nan.ganin yana neman fita yasa Fattu ta tako da sauri tare da rungumeshi ta baya. Dammm!dammmmm!!dammmm!!!gaban Adeeb ya bada wani sauti na bugawa. Cikin hanzari ya runtse idanunsa,dan yadda yaji fattun ajikinsa ,abin yazo masa cikin bazata. "Hamma kayi haÆ™uri wllh bani da abinda zan baka ,amma indai na tara kuÉ—ina zan siya maka cin-cin burodi,nima baffa ke siyomin idan yaje gari, ka fadi abinda kake so nayi maka yanzun" ta faÉ—a tana mai gyara kanta dake kwance tsakiyar bayan Adeeb. Cikin dauriya da jarumta Adeeb ya sanya hannunsa ya jawo fattu zuwa gabansa.bude idanunsa yayi dasuka fara rinewa sai wani lumshewa da budewa yake . Ido ya Æ™ura mata na wani lokaci,kafin ya matso da fuskarsa zuwa gareta,ta yadda numfashinsa ke sauka akan Tata fuskar. "Kin amince Ni na É—auki Abinda nake ganin yayi amatsayin kyauta ta " Adeeb ya faÉ—a cikin voice É—insa mai kama da yana mata raÉ—a. Da sauri fattu ta gyada kanta ,dan yadda yayi maganar saiya sata jin wani iri atare da ita. Lips É—inta Adeeb ya kalla cike da tsantsar son jinsu cikin bakinsa.bai jira komai ba ya É—ora nasa lips É—in nata. Gaba É—ayansu sun shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa ,cikin salo da narkar da zuciyar mace Adeeb ke kissing fattu ,yayi da ita kuma take jin abin da yake mata har cikin ranta.idonsu alumshe yake sun lula wata duniyar ,dan tuni Adeeb ya mance da batun taro ,ya sami lips É—in fattu kamar ya sami lollipop. Bugun da akeyiwa Æ™ofar ne yasa Adeeb saurin dawowa cikin hayyacinsa,ahankali ya zare lips É—in sa daga bakin fattu yana kallonta .har lokacin idanunta alumshe suke ,sai sauke numfashi take cikin sauri,jikinta yana bari. Bakin gado Adeeb ya zaunar da ita,tare da shafa gefen fuskarta yace " wannan ma ya isheni nishaÉ—i har agama taron ,antee sururi Hulwa" Adeeb ya faÉ—a yana mai juyawa ya bar É—akin. SaÆ™are fattu ta zauna abakin gadon kamar wata butumbutumi,haÆ™iÆ™a tana jin Hamma har cikin ranta,wani irin shauÆ™i takeji game dashi,sannan ko kaÉ—an bata jin damuwa idan tana tare dashi,lallai Hammanta shine farin cikinta,ga shi aduk lokacin da Hamman nata ke sha mata baki tanajin wani irin nishaÉ—i sosai,ko me yasa ma yake sha mata bakin oho? Murmushi tayi tare da shafa lips É—in ta ,tanaji kamar har yanzu hamman na shan lips É—in nata. Taro yayi taro ta ko ina ka Æ™alla jama'ane Malik a haÉ—aÉ—den dakin taron dake cikin masarautar,abie na zaune kan wata kyakykyawar kujera ta zinare, yayinda Adeeb ke gefensa shima zaune kan wata kujera mai shegen kyau da É—aukar hankali. Gaba É—aya yan gidansu Adeeb suna zaune kan kujeru masu kyau,sai baki sarakuna da matayensu,kowa kagani yayi ado na kece raini, Yan mata sai kaiwa Adeeb hari suke da idanuwansu da jikinsu, amma ba wacce ta ishe shi kallo acikinsu. Anata jawabai da taya abie murnar dawowar É—ansa bayan tsawon lokaci da aka dauka ana nemansa. Ammi na zaune ita da tawagarta,yayinda gimbiya suhaimat ke kusa da ita ,sai sauran baÆ™inta, hakama amma na zaune tare da Tata tawagar cikin ado mai kyau.wata matace zaune agefenta tana É—an kallon ammi,kafin ta juyo da kallonta ga amma tace " Dole saikinyi da gaske kafin ki gama da matar can,makircin ta yayi yawa,ina tsoron kaidinta" Kallon ammi itama amma keyi kafin ta sauke ajiyar zuciya tace " karki damu Maryam,ninasan ta inda zan bullowa al'amarin nan,akwai Abinda ke É—auremin kai sosai,game da gimbiya suhaimat, ina don gano asalin gaskiyar abin kafin nayiwa ammi kwaf É—aya,amma zanyi bincike sosai akan lamarin. "Shikenan zan ci gaba da baki goyon baya ,Abdul lokacin da kike buÆ™atar taimakona Æ™ofa abude take" cewar matar. Godiya amma tayi mata cikin murmushi, Nan dai suka ci gaba da tattauna akan yadda zasu ga bayan ammi. Rashad na hango zaune cikin wani kaya masu kyau irin na sarauta,fuskarsa É—auke da murmushi,ya kafe Adeeb da ido baya ko kiftawa.wayarsace tayi Æ™ara dan haka ya É—auka tare da karawa akunnensa, har lokacin idonsa na kan Adeeb,wanda shima hankalinsa yayo kan Rashad É—in,kallonsa yake cike da tsana, tun lokacin da ya zaune yake kallon Rashad É—in yana kula da duk wani motsinsa. Dan kwata-kwata zuciyarsa bata yarda da Rashad É—in ba,gani yake kamar akwai wani makircin da yake Æ™ullawa. Dan haka ya sa tareeÆ™ ya kula da Rashad sosai. "Ya kamata fa kaje ka aiwatar da abinda zakayi, kafin lokaci ya Æ™ure " ammi ta faÉ—a tana É—an kallon gefen da Rashad ke zaune,waya kange akunnenta,da alam ita ta kira Rashad É—in. Wata dariya Rashad yayi kafin yace " ammina ta kaina ,ina sane da lokaci,yanzu zan tashi domin cike burina, yau saina hana Adeeb barci da irin aika -aikar da zanyi masa" Rashad ya faÉ—a idanunsa Æ™ur akan Adeeb, wanda ya Dan rangwafo kusa da mai martaba ,da alama suna magana ne. Kashe wayar ammi tayi tare da sauke wata ajiyar zuciya mai Æ™arfi,kafin ta kalli gimbiya suhaimat tace " Ni kuwa suhaimat ina wannan sarÆ™ar taku ta ahali, bana gajiya da kallonta ko kaÉ—an ,naga banganta atare da ke ba" ammi ta faÉ—a tana mai kallon gimbiya suhaimat. Murmushi matar tayi kafin tace " har abada bazan taÉ“a rabuwa da wannan sarÆ™ar ba,dan kuwa itace shaidar dazata sadani da Æ´ata, Aduk inda take,ina ji ajikina mun kusa haduwa da juna kuma nayi alÆ™awarin saina É—auki fansar rabani da ita da akayi na tsawon shekaru,akan koma waye keda hannu cikin al'amarin " ta faÉ—a idanunta cike da kwallah.kafin ta É—an daga mayafin jikinta ,saiga sarÆ™ar ta bayyana ,Æ™urawa sarÆ™ar idanu ammi tayi,tabbas wannan irin sarÆ™ar wuyan yarinyar can ce ,hakan na nufin fattu itace É—iyar suhaimat da suka rasa shekarun baya?innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.banga ta zama ba. Cewar ammi cikin zuciyarta. Da sauri ta miÆ™e tana mai faÉ—in "suhaimat ina zuwa "bata jira amsar taba tayi gaba. Rashad ma ganin ammi ta mike yayi saurin bin bayanta dan zuwa ga fattu,yau kam za'ayi ta ta Æ™are. Zulaihat dake zaune cikin Æ™awayenta tana ta zuba izza da iyawa ,ganin su duka biyun sunyi waje hakan yasa itama ta mike cikin sauri ta rufa musu baya, dan kuwa tare zasu aikata mugun nufin nasu akan fattu, tana son ganin komai ya wakana akan idonta , Ko ina zasu kuma oho? Muje zuwa masu karatu, Manage please har yanzu muna cike da alhini. Na gode sosai da addu'ar ku garemu,waÉ—anda suka kirani,da waÉ—anda sukayi min ta waya. ðŸ™ðŸ™ Anty mammy ce Mrs babi💘💘 Share and comment fisabilillah. 29/08/2022, 11:00 am - Khadijah Salisu Fari: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄 MACIJI NE🪱🪱🪱 Na mammy kabeer (Anty mammy) Elegant online writers📚📚 Free book Page 51/53 _________________Abakin Æ™ofar hall É—in Zulaihat ta tarar da Rashad ,yana tsaye da waya ahannunsa ,da alama kira yake Æ™oÆ™arin yi,saidai yana ganinta ya maida wayar cikin aljihunsa yana mai faÉ—in,"yawwa dama ke nake Æ™oÆ™arin kira,sai gaki kin fito. Ƙarasowa Zulaihat tayi kusa dashi ta tsaya" ya ake ciki ne ?" Ta faÉ—a tana É—an waigen bayanta. "Yau burina zai cika ,zan sami abinda ke hanani barci,kuma zanyiwa Adeeb illah,saina rama dukan da yayi min akan yarinyar da yake iÆ™irarin yar amanar da ce,bayan kuma Ni nasan dadironsa ce ,kawai kishine da mugunta sukayi masa yawa,shine ya hanani Nima in É—ana"cewar Rashad yana mai kallon Zulaihat. "Kaga Rashad karka Æ™ara cewa dadiron my Prince ce,karkayi masa sharri,dan kuwa nasan halinsa nasan koshi waye,wllh bazai taba ajiye yarinyar nan dan biyan buÆ™atarsa ba,mutumin da har maganin sha'awa nake saka masa alemo,dan kawai yayi tarayya dani,amma duk yadda ya galabaita bazai koda rungumeni ba. Dama dai kaine akace ka ajiye ta dan biyan buÆ™atarka,to wannan kam na yarda dan nasan kai din namamajo ne " Zulaihat ta faÉ—a tana mai galla masa harara,dan taji haushin sharrin da yayiwa adeeb,ita da take burin ace itace zata fara bude Adeeb aledarsa ina zataso jin wannan batu. Wani shegen kallo Rashad ya watsa mata kafin yace " banza yar tasha ,ke har Ni zaki cewa na mamajo? Ai duk iskancina ban kaki ba,kefa Æ´ar maye ce sannan jarababbiya, Ni kaina sau nawa ina taimaka miki ?ina ce wataran har guduwa nake saboda jarabarki ?zaki raina min hankali wawiya kawai" Rashad ya faÉ—a cikin faÉ—a. Haushi sosai ya kama Zulaihat ,ranta ya É“aci da kalaman Rashad gareta ,wato har gori zaiyi mata ,dan ta neme shi kusan sau uku ?ba komai zai gane kurensa wllh. "Ni kakeyiwa gori Rashad ?to wllh kasani bazan taimaka maka akan Æ™udirinka na yauba ,saidai kayi kai kadai ,banza marar mutunci" Zulaihat ta faÉ—a cikin É“aci rai tana mai barin gurin cikin sauri. Tsaki Rashad yayi yana mai faÉ—in"aikin banza ,da me zaki iyamin agurin banda kema kice kina so intaimaka miki ,Ni kuwa ranata ta yau duka ta fine baby ce,yar Æ™waya kawai " ya faÉ—a yana mai nufar part É—in ammi. Ammi kuwa tana zuwa part É—inta cikin É—akinta ta nufa ,Æ™ullewa tayi tare da zama bakin gado,tana tunani iri iri cikin ranta, wata akwati ta É—auko dake can Æ™asan gadon ta tare da budewa, Tana buÉ—ewa wani hayaÆ™i yayo sama baÆ™iÆ™irin dashi,banda wari ba abinda ke tashi cikin hayaÆ™in nan,da sauri ammi ta toshe hancinta, tana mai zaro ido waje,abayyane ta furta " na shiga ukuna ba dai kwalbar nan ta fashe ba? Shikenan ta faru ta Æ™are ,dama nasan hakan zata faru wayyo Allah na" ammi ta faÉ—a tana mai bin wata kwalba yar gajeriya da ta tarwatseda ido,wani farin abu mai kauri yana ta motsi kamar tsutsa. Bugun Æ™ofar da ammi tajine yasata saurin rufe akwatin ta tura can kasan gado,saita kanta tayi cikin É—auriya ta nufi Æ™ofar . Rashad ta gani tsaye abakin Æ™ofar ,"ammi ya ake ciki ne ?ta yaya zan É—auki yarinyar ne ?kinsan ba aÉ—akin ta zan aiwatar da Æ™udirina ba,dan wancan mayen zai iya zuwa ya cin mini" ya faÉ—a yana kallon fuskar ammi . "Ka tafi can É—ayan part É—ina ka jira zan kawo maka ita da kaina ,ina son kayi mata abinda nan da wata guda ma bazata san inda kanta yake ba,bana son ka tausaya mata ko kaÉ—an"ammi ta fada fuskarta ahaÉ—e. "Kada ku damu ammi bazan taÉ“a baki kunya ba,nayi alÆ™awarin saina yi mata abinda Bama ki tsammata ba"Rashad ya faÉ—a yana wani irin killer smile. Ficewa ammi tayi tare da nufar part É—in su fattu.ba kowa afalon,dan kuwa nanny ta É—an leÆ™e gurin taron ,ganin fattu kwance tana barci. Cikin É—akin ammi ta shiga ,tsaye tayi agaban gadon da fattu ke kwance ,idanunta arufe kamar mai barci,amma idanunta biyu,hammanta kawai take tunani. Kusan minti uku ammi tayi tana kallon fattu dake kwance ,tabbas ko tantama batayi ,wannan yarinyar gimbiya suhaimat ce ,dan kuwa sai yanzu take ganin tsantsar kamannin dake tsakaninsu,amma ta yaya suka haÉ—u da Adeeb?har ya taho da ita nan?wannan shine abinda take son sani. Ganin fattu ta É—an motsa ne yasa ammi ta É—an kira sunanta " fateema tashi" Ammi ta faÉ—a tana É—an shafa kan fattu. Ahankali cikin nutsuwa fattu ta tashi zaune tana É—an mika ,dan ta jima akwance. Murmushi tayiwa ammi tare da sunkuyar da kanta Æ™asa cikin kunya . "Fateema Sarkin kunya,ke kadaice aÉ—akin ne"ammi ta faÉ—a cikin Hausa ,dan kuwa ta iya Hausa sosai itama. Jinjina kai fattu tayi tana wasa da Æ´an yatsunta. Murmushi ammi tayi tana shafa kan fattu kafin tace " to ya jikin

Chapter 12 of 23