Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
sai nayi tunanin ai ciki ne gareta bai kamata na dake taba. Nayi tsaki mtsww na fito daga dakinta naje kichin na dafa indomie fara tas ko yaji babu haka na cinye ta saboda masifar yunwar da nake ji.na chinye na koma daki na kwanta ina tunane tunane har barchi ya daukeni.da asubah na tashi naje nayi alwala na tafi massalaci. Aka gama sallah na taso na taho gida.in shiga gida na tarar da manasa tana hada kayanta A akwati. Da nace bazan mata magana ba bari na kyaleta naga mi take nufi.sai wata zuchiya tace may be gidan su zata tafi.kawai sai na yanke shawara naje na sameta.ina zuwa nace ma manasa INA ZAKI? Budar bakin gidan mu zan tafi. Na kara tambayar ta Nace mata mi zaki yo? Tace man ta gaji da zama dani.nache amman baki da hankali haka da tsofan ciki zaki kama hanya ki tafi bauchi.kumah A motar haya.sannan tun da safe haka ko gari bai gama waye wa ba. Nace mata babu inda zaki idan ko kika tafi duk hukuncin dana yanke maki ke kika jawo. Naje nayi wanka na shirya na tafi gidan su dady na gaishe su san nan na fada masu cewa naga sameera.ina fadi naga momi tayi sujada ta godewa Allah. Na kwashe labarin zuwa na jos duk na fada masu.sai dady yace basu ga ta zama ba. Injira su.suyi break pass. Mu tafi jos. Mu taho da sameera. Nima lokacin ko karyawa banyi ba amman ban fada masu ba.kada suyi tunanin akwai wani abu tsakanin mu da manasa.suna gamawa muka dauki hanya sai garin jos. Misalin karfe 8:30am na safe muka isa garin jos.muna zuwa kofar gidan da sameera take.muka chi karo da sameera ta dauko akwatinta da niyyar zata bar garin jos.tasan daman sai nazo da umma da dady.sameera tana ganin su ta yarda akwatin ta ruga ta shige cikin gidan da gudu. kawar ta fadeela ta leko taga mike faruwa.ita ce ta bamu izinin mu shigo gidan.muna shiga sameera tazo da gaida su dady.nan su umma sukai ta bata haquri akan ta dawo gida.fadeela ce mai cewa sameera kiyi haquri ki koma.duk abinda ya faru ga bawa Allah ya riga ya kaddara zai faru dashi. Sameera ta yarda ta biyo mu misalin karfe 3:20pm muka iso zariya.kannai su adnan suma sun nuna farin cikin su sosai da suka ga sameera.washe gari kamar yadda na saba zuwa gaida ummana da dady na naga sameera.tachi wata uwar kwalliya tsayawa kawai nayi ina kallon ta.data fahimchi ina kallo sannan tazo ta duqa ta gaidani sannan ta rokeni gafara na yafe mata akan maganganun data fadi man.na che mata ai babu komai. Allah ya yafe mana baki daya.nan har nake to nan ta nace saura yanzuh ma ki gudu.sai tayi wani murmushi tace kaji yayana da wata magana..mukai wasa da dariya na shiga falo na gaida su dady. Bayan na gaisa dasu. sai dady yake ceman my son inaso zanyi wata magana da kai.bai gama rufe bakin saba sai naji wayata na kururuwa. Da alama wani ne ke kirana.ina dubawa naga polina ce kawar manasa.ke kirana.ina amsa kiran akace munan asibiti manasa ta haihuwa ta sami budurwa.kayi sauri kazo ka biya kudi za'a salla Alhamdulillah nace.to ganin tafe.na fada masu dady cewa manasa ta haihu suma sunyi farin ciki ummace tace bari na dauko hijabi na mu tafi tare. Ina zuwa falo na fadi ma sameera cewa manasa ta haihu tayi man murna dayi ma jaririyayar addua Allah rayata.amman naga alama sameera na cikin damuwa amman bata nuna man ba.muna zuwa asibiti na biya kudi muka dawo gida nayi ma jaririya huduba. Na sa mata suna sameeeeera. Nayi dana sanin fadi ma manasa sunan jaririyaR bayan nayi ma ta huduba.nace ma. manasa sameera na sa ma ta suna.tace baka isa ba wallahy dole ka chanza mata huduba.wallahy da kasa ma yar"ta sunan wannan jakar yarinyar gwanda ta mutu na huta. lokacin ne na tsinke manasa da mari ina ce mata na lura ke mahaukaciya ce to bari kije wannan sunan shi nayi niyyar sama yar"ta yanzuh tunda kin haihu ni daidai dake ne.na fice daga dakinta na barta tana sharar kuka. Lokacin da naje daki na naji jaririyar tana ta kuka.amman manasa taki daukar ta sai uban kuka take. Na leko nace mata manasa kiji tsoron Allah wannan jaririyar bata son komai ba amman kina zalintarta.lokachin ne ta dauke ta ba bata mama. Sannan nace mata idan ta gama da ita zamuyi wata magana da ita. Tana gama bata mama jaririyar tayi barchi sai tazo daki na ta sameni.na fara bata labarin sameeera tunda farko har karshe. Da Alama manasa taji tausayin sameera lokacin da na gama bata labarin naga manasa tana share hawaye ta rokeni gafara na yafe mata laifunkan data yiman. sannan tace tanason taga sameera.na kira sameera tazo gidana tayi ma manasa barka.zata tafi manasa tace ta tsaya. manasa taba sameera haquri akan abinda ya faru.suka yafe ma juna.da daddare ina kwance manasa tazo dakina taceman mijina inaso na rokeka wata Alfarma don Allah ka auri sameera. Wallahy nayi ma alkawarin zamu zaune lafiya da ita. Nayi farin ciki kwarai da manasa tace na auri.sameera safiya nayi naje gaida su dady kamar yadda na saba. sannan na fadi mai abinda manasa tace.shima yayi farin ciki sosai.yace daman ranar da matar ka ta haihu maganar da nake so nayi ma kenan.sai aka kiraka. Amman yanxuh bazan yanke hukunchi ba sai naji daga sameera idan zata aureka. Dady ne yasa umma ta tambayi sameera idan tana sona.tana tambayar tache eh tana sona kumah zata aure ni.bayan sati 1 da haihuwar manasa Akayi suna.aka sa ma yarinyar sameera......... Sameera tayi farin ciki da taji sunan ta nasa ma yar"ta.sameera ta suwo kaya masu yawa ta kawo ma takwararta. Bayan anyi suna kowa ya watse. Aka sa mana ranar aure nida sameera.lokachin da akasa yayi akashe shagali aka kawo sameera gida.na tara su nayi masu nasiha akan su zauna lafiya.nace ke sameera kece karama kiyi ma manasa biyayya.ke kuma manasa ki wa Allah ku zauna lafiya kada wani ya zalinchin wani. Haka suka zaune lafiya. sameera aunty take ce ma manasa.bayan shekara 1 da "yan watanni sameera ta haifa man yaro namiji.na saka masa sunan dady na SULAIMAN amman Abba ake kiransa.gaskiyaba karamin farinci nayi ba da naga mata na suna zaune lafiya babu rigima babu tashin hankali. Muka chi gaba da rayuwa mai inganci muka manta da abun ya faru A baya. KARSHEN LABARIN KENAN WANI DARASI KUKA SAMA GAME DA WANNAN LABARIN? Kuma wani korafi zakuyi game da wannan labarin domin mu gyara, zaku iya fata tanan ko kuma ku turo mun da sakon ku ta nomber ta 07033020404 Admin ..........CIKIN DARE { Part 12 }........... Rahul yayi matukar mamaki da Sameera ta zageshi A guje ya Debi motarsa Izuwa gida Yana shiga gida Sai Hajiya tace Rahul Ya kashigo gidannan ranka A6ace meyasa meka? Rahul yayi shuru Hankalin Hajiya ya tashi Ta kara cewa Rahul Don Allah kafada man Waya 6ata maka rai? Rahul cikin fushi yake cewa Hajiya Wai Hajiya yanzu kamar Sameera Ita Ce zata zageni a tsakiyar Kasuwa Hajiya tace Sameeran Ce tazageka? Yace Eh Hajiya! Hajiya Tace kaje ka dakko wayar Redio Idan tadawo kai mata Kafirin duka Rahul yaje ya samu Wayar Redio Manasa ma Itama tasamo wayar Redio Wai harda ita za'a daka Sameera saboda tazagar mata Yayanta, A falo suke tsaye suna jiranta Manasa da tadawo gida tana zuwa harabar Gidan Taji gabanta yana fadi, Kamar tajuya ta fita gidan amma hakanan ta tashiga gidan Tana zuwa falo Manasa tayi saurin kulle kofar falon Sameera ta zaro Ido Tace Manasa Lafiya? Manasa ta wanketa da mari Rahul yacire hijabin dake jikin Sameera kukaci gaba da dukanta Sai da sukaimata ti6is Suka far fasa Mata jiki Ko ina ajikinta ya fashe Fuskarta Ce kawai batayi komai ba Saboda itama tana rife fuskar Sameera tayi kuka kamar ranta ya fita Bayan sun gama bugunta 3 Awos Bata iya tashi Sameera da rarrafe takai dakinta Jikinta gaba daya duk bakarfi Kankace haka ciwon kai mai karfi Ya kamata zazza6i Idonta biyu Ita kanta Tana tausaya wa kanta Gari nawayewa Rahul ya shigo yacewa Sameera Ke Ga kayana can dana Manasa Dana Hajiya Ki wanke Mana Kitabbatar da kin wanke su kafin Mu dawo daga Jos Cikin sauri Sameera ta Amsa Saboda gudun bugu, Yaja tsaki ya fita, CIKIN DAREN bacci yaki yuwuwa man Saboda tunanin Sameera Shin tunanin danakeyi Wane hali Sameera take ciki kuma Ina take Ammsar Dana kasa Samu kenan, Gari na wayewa nayi wanka Nadau Key din motata Naje gidan su Dady Ina zuwa nagaida momy na da Abba Sannan Nasanar dasu Yadda mukayi da Abban Manasa nacewa naturo Magabata na da ayi Maganar Aurena da manasa Dady yayi farin ciki Itama mahaifiya ta Buda bakin Momy Sai tace dannan Wlh harga Allah naso ka Auri Sameera Allah nedai bai nufaba yanzu nata Raye ko bata Raye Wallahu A alamu Sai dady yace man yaushe Iyayen Manasa sukace katuro mahaifan ka Sai nace mai Dady 2week suka Ce Dady yace Allah ubangiji ya kaimu lokacin Momy tace Ameen, Jingine nake ajikin motata a kofar super market din dake Tudun wada Zaria Tunanin Sameera ya hanani walwala da Kwanciyar hankali Ni Sai naga kamar 6atar Sameera batazana Ce ga Rayuwa ta Ina tsaye nayi tagumi Sai ga wata kyakykyawar Yarinya taci kwalliya Tazo tasameni tayi man Sallama, Salamu alaika? Na6ata rai nace mata Wa'alaiki salamu, Sai tace naga Malam naga kamar kana cikin damuwa kozan tayaka fira? Sai nasha kunu Na daure fuska Nace mata Dan Allah malama kirabu dani kona Ce maki Ina Son mutun yataya ni fira ne? 6ace man dagani ko kuma nayi maki wula kanci, Sai tayi murmushi tace Allah ya baka hakuri Sai munsake haduwa Natabbata idan kadaina fushi to zaka saurare ni Saboda ni kyakykyawa Ce, Sai nayi tsaki Naja motata izuwa gida, Ranar da Su Dady suka shirya zasu Bauchi zuwa kar6o aure na Sameera ji tayi gabanta nafadi kamar wani Abu zai sameta Su dady suka isa Bauchi Amma su Kansu sunji ajikinsu kamar zasu ga Sameera a bauchi Saboda suna isa Bauchi tunanin Sameera ne kawai ke yawo a zuciyar su, Ita kanta Sameera Baccin data danyi na mintoci Har mafalki tayi wai sun hadu dasu dady Da mom da kuma ni Lokacin Da muka isa harabar gidan su Manasa Kowanne Acikinmu gabanshi bugawa yake Muna Isa Falon Kawai Sai naga,,,,,, mu hadu a part 13 anjima n gidan su Manasa Sai Mukaga Manasa Tafito ban daki Sai kunya ta kamata A guje tatafi dakinta Sai nacewa dady Wannan Wadda taruga Itace Manasa Sai dady yayi dariya Hajiya Ce taje tacewa Sameera Kada tasake Tafito Kicin din indai tasan bata gama Abincin ba Sameera ta Amsa dato Muna zaune Sai ga Abban Manasa ya shigo suka gaisa da Mahaifana ni kuma Natashi natafi dakin Manasa A wannan zuwan da mukai gidan su Su Manasa Shine Aka gama Komai har sukasa Ranar Aurena da Manasa Wata daya ne akasa Saboda Dady Yana so yatashi kasar England Har Muka gama komai Muka tafi Sameera batasan Abinda ya faru ba Sai bayan wuce Sameera ta gama girki Sannan tasamu damar fitowa Daga kicin tana zuwa falo Sai taji Ana Maganar Dame dame ya kamata ayi A daurin Auren Manasa Da Muhammad Abdulhadi Sai taji gabanta ya fadi har tanayiwa Manasa murnar Saranta da akayi Manasa Cikin Fushi ta iya Amsawa Saboda tatsani Manasa sosai Sameera ahankali cikin kasala ta tatafi Dakinta Tana zuwa dakinta tazauna tayi tagumi Sai Taji sallamar Wani yaro An aiko shi ya kirata, Yana shigowa Inda Manasa take Yace mata Sameera kizo ana kiranki Awaje Sai tasha kunu Tace wake kirana?.Sai yaron yace Wani mutimine Tana cikin fadin haka Sai Ga hajiya tashigo Dakin tana fadin Dan ubanki kitashi kije Abokin Rahul ne yake kiranki Idan baki jeba Rahul Zaici Ubanki kuwa, Sameera da sauri tatashi tatafi Saboda Tsoron Rahul datake yi, Tana zuwa gum matashin dake kiranta Mai suna Bala Sai tayi mai Sallama Sai ya amsa mata tare dayin murmushi Sai tace malam Don girman allah karabu dani wllh akwai Wanda make so Buda bakin Bala Sayyace Waye kike so Sai tace Inarunka dole Sai kaji sunansa? Sai yace a'a Amma don girman allah Kitai maka kifada Man Sai tace mai Sunansa Abdul-ahad Sai bala ya zaro ido yace Wanda zai auri Manasar Shine kike so? Sameera tace don Allah karufaman Asiri wlh bashi bane Wannan nanine daban kuma Ai anayin suna Iri daya Sai yace Hakane Amma wlh Koki bar garinnan konace wa Rahul Saurayin Manasa Shikike so, A guje Sameera ta shige gida Saboda taji bala yace zai gayawa Rahul shiyasa Sameera tayanke Shawar Barin gidan Sameera tana zuwa daret tana nufa Dakinta Ta Hado kayanta Duka Tasa acikin Leda Sai da ta fahimci falon Bakowa Sannan Tayo waje da gudu .Sai mai gadi ya tareta yace Mata Sameera Nasan kina Shan Wuya acikin gidannan Garama ki gudu Ni kuma zan taya ki da Addu'a Sameera a tsorace tace mai Nagode tafita da gudu Ashe Bala wasa yake mata Shikanshi baya jin dadin dukan da Rahul yake mata, Sameera Tana zuwa tasha Tasamu wani mai kudi Taroshi alfarma daya tai maka mata da kudin mota Zuwa Zaria city Mutiminnan Dubu 10,000 Ya bata Saboda tausaya mata da yayi Ganin yadda tazo A gigice, Ina zaune Dady Ya kirani Bayan mungaisa Sayyace man My son Yau wata daya kenan dagama gidajena na Kaduna Nawa da naka Don kada Gidan da kake ciki nasiyar dashi Da Wanda mu muke ciki don haka gobe kashirya da Sassafe Nasa azo man da Tirela ta kwashe kayanmu duka Sai naji dadi amma tsoran danayi Karmu bar gidan kuma yaza mana Sameera tadawo gidan nemanmu gashi dady yace kada Wanda ya fada makowa Inda zamu zauna A Kaduna Gari nawayewa Tirela Tazo ta kwashe kayanmu duka A wunin muka gama Kwashe kayanmu Muka koma Kaduna Su dady Suka zauna A Tudun wada ta Kaduna Ni kuma Nazauna a Kawo A gidan dazan zauna Nida Amaryata Sameera, Satinmu Daya da komawa Sameera Bayan tabar gidan su Rahul Gidan wata kawarta taje A jos mai suna Fadeela Isma'il Satin ta ukku A gun Fadeela dayake ta bata duk Labarin Abunda ya faru da ita Sameera tayi matukar Tausaya mata Sosai Shiyasa har bata so Sameera tatafi Watarana tace ma Sameera Ya kamata muje Zaria Kudaidai ta da Iyayenki da kuma Baffan Saboda kisamu kiyi Aure kinsan Yanzu zaman aure shiyafi komai Dadi Lokacin Da Sameera Sukazo Zaria sukatarar da muntashi Adaidai wannan Lokacin Ake Daura Aurena Da Manasa, Sameera tayi kuka sosai Hakanan ta hakura ta koma Jos sukaci gaba da zama da Fadeela, Bayan aurena abokai Kowa ya watse Aduniya banda iyayena Babu Wanda nake son gani Sai matata Manasa Manasa tana Mani son Da bata ta6a yiwa wani ba Shekararmu daya da wata biyu Manasa tasamu Ciki Wanda ya kai munzalin haihuwa Watarana zani office Manasa tarakoni Izuwa harabar gidana Sai nashafa mata cikin ta nace Insha allahu Kafin nadawo Sai dai naji Anyo man Waya ace kin haihu Sai tayi nurmushi tace Ameen Sai nasunbaceta na ja motata nayi gaba,saneera kuwa Sai Alokacin ta kara wayewa haduwarta da fadeela ta koya mata Kwalliya Da salon tafiya Kai idan baka san Sameera ba Sai karantse kace 'yar shugaban kasace Watarana Sameera taje Super market Sai ta hadu da Polina Polina tayi matukar far in ciki da taga Sameera Bayan rungume Polina tace Sameera wllh Kinyi kyau ko Gomna Ai yaganki dole ya kyasa Sai polina tace wa Sameera Kishirya kizo muje Kaduna gun Manasa Wata kawatace wadda muka hadu a bauchi Jikin Sameera yayi sanyi Sai taba Polina labarin Zawanta bauchi Polina tatausaya mata Sai tacewa Sameera karki damu ai yanzu kinfi karfin Manasa tata6aki barinma mujinta yaganki Ai kau Dole shima ya kyasa Sai sukai dariya Sukayan Ke shawarar Gobe da safe misalin karfe shida zasu wuce Kaduna Saboda basaso sukwana Sai Sameera tacewa polina kinsan Inda Manasan Tayi Aure? polina tace Naje gidansu aka bani Address Din gidan Ammace man Tana da ciki haihuwa yau ko gobe Ahaka suka rabu akan gobe zasu hadu Sai suwuce Kaduna, Gari nawayewa Sukakama hanyar zuwa Kaduna Misalin karfe Ukku suka Isa Kaduna Sai kai sa'a sukaga Gidan su manasan Ananne Sameera taji gabanta nafadi Suna zuwan falon Manasa Sai Sameera taci karo da Makeken hotona wanda muka Dauka Da Manasa Ahotan kamar zanyi magana Hankalin Sameera yayi muguntashi, Muhadu a part 14 gobe yi comment domin shine yake karamin kwarin guiwa NAKU> Mahmud A Yusuf CIKIN DARE { Part 14 } Sameera tana tsaye tana kallon Hoton da mukayi da Manasa shiyasanya hankalinta yayi matukar tashi Wai Baffa na shine zai auri Makiya ta Lallai kam za'ayi ta Abinda keyawo cikin zuciyarta kenan Shigowar Manasa ne falon yayanke tunanin da Sameera take Ciki Manasa Tana Sakkowa kasa Sai suka hada Ido da Sameera shiyasa hankalin Manasa ya tashi Manasa na zuwa Tacewa Sameera meyasaka kika zo gida na? Sameera taja dogon tsaki Mitswww Tare fadin ai yanzu daidai nake dake wlh Saboda yanzu ba a karkashinku nake aiki ba Ehe, Manasa tayi mamakin jin abinda Sameera take fada mata Polina ce ta dunga ba Manasa hakuri Budan bakin Manasa Sai tace wa Sameera Bara nakira mai gidana wlh Zakici Kutumar Ubanki Shegiya Kawai Sai ta hau sama kirana Polina tacewa Sameera zomubar gidan nan Bansan haka zata faruba Sameera tacewa Polina barta ta kira Mijin nata shima daidai nake dashi yana bude man huta nima Zan bude masa Polina ta kalli Sameera tace lallai Sameera baki da hankali, Ina Kishingide A makeken gadon dake Dakina Manasa tashigo a firgice Tazo ta zauna kusa dani tana kuka, Sai nace My dear Meya faru ne? waya ta6a manke ne? Sai tace man wannan shegiyar 'Yar aikin tamuce tazo gidannan Shine take zagina don Allah my dear kayi man wani Alkawari Sai nace mata Manasa kifada buka tarki Insha allahu zan Cika maki gurinki nayi maki alkawari, Sai tace Baffa don Allah ina so Ka dakko mata Police sutafi da ita Sai tayi 1week sannan Asake ta kaji my dear na Sai nace mata karki damu muje naga Shegiyar da tata6a manke, Da suri Manasa ta mike Ina biye da ita abaya A hankali na sakko Kasa Kujerar da Sameera ta zauna tana Facing Waje Ni kuma Banga Sameera ba bayan ta kawai nake nagani, Ina sakko wa Nace Ma Manasa acikinsu Wace shigiyarce ta zageki manasa tace man gatacan da Hannunta tayi man nuni, Buda bakina cikin fada Nace mata Ke dan ubanki kijuyo fuskarki jiki abinda zan fada maki Sameera taki joyowa Sai nace mata Nan gidan ubanki ne? Sameera tajuyo ahankali tare da fadin A'A bagidan ubana bane, Ta juyowa naga Sameera CE dama nayi ma wannan zagin Ashe Itace 'Yar aikin da take shan duka a gidan iyayen su Manasa abinda keyawo daga kwakwal wata kenan, Hankalina yayi matukar tashi danagan ta Sameera tayi matukar kyau Kyenta ya kara karuwa Gashi taci arniyar kwalliya kyenta ya fito Buda bakin Manasa Sai tace man Baffa na mekake kallo anan kaje ka dakko mata police mana, Cikin sauri da firgici nace TO Nararimi Hula nadorata akai ta kalminma barau da bawa nasa Nafice a guje Ina zuwa kofar gida Nasamu wuri nazauna Ina jiran Sameera su fito, Manasa tayi jiran tayi jiran amma bandawo ba Taita kirana awaya naki dauka Tun karfe 1:30pm suke a gidana har zuwa karfe 6:00pm suna ciki Idan Sameera Zata fita gidan Manasa CE kerike ta tare da fadin dan ubanki kijira ya dawo mana, da Sameera taga banda woba nan tabar polina Tafito daga gidan lokacin data fito Manasa bata saniba tana Kicin amma nasan data ganta to bazata barta ta tatafiba har Sai na dawo, Ina zaune Sai ga Sameera tafito daga gidan Sai nayi sauri na mike duk jikina babu karfi Sameera tana gani na Sai tayi kamar bata ganni ba zata tafi na janyo mata gyale natace mata Ina kuma zaki batare da munyi magana ba? Sameera taja tsaki Mitsww Dalla gafara can kaban hanya nawuce Abun mamaki wai yau ni Sameera takewa tsaki Nadunga bata hakuri Sai nace mata Sameera bara na dakko mota na Muje gidan su Daddy Tunda nasan farin ciki zasuyi idan suka ganki Sai tace HMMMM Jeka dakko Motar A gigice na shiga gida natarar da Manasa da polina suna firar guduwar Sameera komagana ban masu ba na dau key Ina fitowa daga gida na tarar da Sameera bata gun Dana barta......... Muhadu a Part 15.. yi comment domin nuna kosawarka... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4