Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
dajin muryar ta Sai hankalina ya tashi nara mezance ma dady Sai Nace mai Dady Batanan Sai yace man Ina tatafi? Sai Nace mai taje gidan kawarta Indo Sai ya fara man fada Dan ubanka neyasa zaka bar Sameera tafita cikin wannan daren ? Nayi Shuru Sai yaceman Ai gobe zamu dawo Idan wani Abu yasami Sameera to Ranka sayya 6ace bai bari nayi magana ba Sayya yanke wayar, WASHE GARI misalin karfe 11:46am Su dady suka shigo Zaria suna zuwa Zaria Sai Dady ya kirani awaya Ina dauka Sai yaceman My son Kamai su Sameera gida Mundawo yanzu Can Sai yakara Ceman Sikin Sanyin murya yace man My son Nakosa naga Sameera Bala'i Abunda Nace acikin zuciyata Sai na fata tunani wai mema zancecma dady ne Ina cikin wannan tunanin Ne yakara kira My son don Allah kayi Sauri kadawo dasu gida Da sauri na hada kayan Anwar dana Adnan Nasaka su a mota nuka tafi gidan Su dady Muna zuwa natarar da dady a harabar gidan a tsaye Muna fitowa ya kalleni jikina Sai rawa yake Buda bakin dady Sai yace man My son Ina Sameera? Nayi shuru Sai ya kara ceman Sameera ta byata ne? Nayi shuru Sai yace man cikin tsawa Bakajini Ina maka nagana Buda bakin Anwar Sai yace Dady Sameera ta byata Guduwa tai tabar gidan kuma tace har abada bazata dawo ba wai karma ayi wahalar nemanta dan baza aganta ba Sai naga dady ya fadi Ya suma da sauri na daukeshi nayi cikin gida dashi Bayan ya farfado Sai nabashi labarin abinda ya faru Komi na fada mai amma ban fada mai cewa kauraye sunyi zina da Sameera ba Haka mukaci gaba da Neman Sameera harna tsawon 4week amma bamu ganta ba bata ba a lamarta Har muka hakura Momy tayi kuka kamar ranta ya fita ni kaina nasan Suna Son Sameera sosai, Ashe Sameera bayan ta bar gida na Mota tahau Daniyyar zata Bauchi Gun wata kawarta wadda suka hadu tun a Secondary School Lokacin dataje bauchi Sai gidan kawar tata Mai suna Polina itama ba musulma bace dataje gidan Sai tatarar gidan Babu kowa Sai akayi ma Sameera kwatancen Gidan kawar Polina mai suna Manasa Bayan Sameera ta je gidan su Manasa Sai ta samu yaro daya kira mata Manasa a gidan Sameera na yatsaye Sai yaron yafito yace ance Manasa batanan Amma Idan zaki iya jiranta to Bazata dadeba zata dawo Sameera tun karfe 4:25pm take jiran manasa Amma Manasa bata dawo ba Sai bayan magriba Yunwa nadamun Sameera gashi kudin dake hannunta Saura naira 200 Tana tsaye Sai ga Wata Moha jeep Tatsaya agaban Sameera Sameera natsaye tana kallon Motar Sai taga Manasa ta fito Daga cikin motar Sai manasa ta zo inda Sameera take Sai take Cema Sameera anyi man Waya ne ance man Wata bakuwa tana kofar gidan mu tana jirana kece ? Sameera tace Eh nice Kece Manasa? Manasa tace Eh meke tafe dake? Sameera tace Nazo gidan Wata kawata mai suna Polina naga gidan a rufe Amma Ance nazo gunki kila kinsan Inda suka koma Ance man ke kawarta ce Manasa tace gaskiya Bansan inda polina suka koma ba Manasa ta juya zata tafi Sameera taduka tarike mata Riga tace Manasa kitai makene da gun kwana Kona bar nan bansan inda zanje na Kwanta ba Manasa ta Tambaye ta daga Ina kike? Kuma maye sunanki? Sameera ta Ce sunana Sameera Ina Zaune a katsina a wani kyauye mai suna Dandume. *** CIKIN DARE Part 8 ****** Nan dai sameera suka yi jinga zata rinqa yi ma su masana aiki. A wanchan bangaran kuma ina ta kiran sameera A waya taki dagawa da kyar na samu ta dauka. Sameera na daukar wayar tace Hello, Banji taba Tanata Hello bana jinta Sai na kashe wayar Saboda bana jinta Sameera ta ije wayar Inda taganta tatafi wajen aikinta. A wanchan bangaren kumah na shirye naje bauchi ziyara wajen abokina munnir. Muna tsaye da abokina Munir ya kira Yayan Manasa Mai suna Rahul Ya Ce mai Rahul Kazo Inda Muka Saba haduwa zakaganni nida Abokin nawa Rahul Cikin sauri yace Ganinan zuwa Ina tsaye Sai ga Yayan manasa Yana fitowa daga mota Muka hada Ido dashi Hankalina ya tashi Yana zuwa yace ma Munir wannan ne Wanda kukazo tare dashi? Munir yace Eh Shine Kasan shine? Rahul yace wannan Da kake gani Shine yayi wa Manasa Ciki Cikin sauri Munir ya kalleni yace Abdul Dama Kai Mazina cine? Nace mai A'A yace man Rufe man baki Rahul Kayi hakuri bansan hakan tafaru ba Dakar munir ya lallashi Rahul Har Rahul yaji yana son yayi Abota dani, Rahul shine ya kaimu gidan su Lokacin da muka kaje Sameera tana kasuwa Rahul shine yayi kokarin Hana mahaifiyarshi abunda tayi niyyar yimin Maman Manasa Wuka ta dakko da Niyyar zata kasheni Hankalin yayi matukar tashi Dakar Rahul Ya lallasheta Harta hakura Amma dai duk da haka taki Sakin jiki dani Munir Shikanshi Naga chanji atare dashi Saboda yaji Ance nayiwa Manasa Ciki, Muna zaune a falo Sai ga Manasa ta shigo gidan Tana zuwa falo ta kalleni Sai Murna da sauri ta kawo mana Abinci Mukaci muka koshi Manasa Ce ta kirani Izuwa dakinta don mu tattauna Gaskiya Manasa tana dakyau Amma Duk kyanta bata kai Sameera ba Manasa tace man Baffa banta6a haduwa da Namijin daya shiga rayuwa ta Lokaci guda ba Sai Saikai daga wannan lokacin na yadda da Soyayyar Manasa Kafin Sameera ta dawo Manasa ta shaida Ma iyayenta cewa Ni take so ta Aura Iyayenta Sunyi Farin ciki A daidai wannan Lokacin Mahaifin Manasa ya shigo yana masu Albishir dacewa Gobe Zasuje Gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi Zasu musulinta Matan gidan sunyi Farin ciki dama suna Sha'awar shiga musulinci Dadyn Manasa ne kawai baya so A wannan Lokacin Naji dadi Saboda nasan zan iya auranta tunda ta Musulinta Munir yana A falo ni kuma natashi na tafi dakin manasa Nabar Munir A falo Ina shiga dakin Manasa Dai dai lokacin da Sameera tashigo Gidan Su Manasa da Leda A hannunta Kayan miya ne tasiyo Tana shigowa Rahul yace to kaga yarinyar Bayan ta gaishi ta wuce ciki dan yin Aikin dake jiranta Munir yaji tausayinta Saboda ganin yadda take tafiya a Karkace jikinta duk ga Alamun Bulala nan, Kwance natarar da Manasa a dakinta tana tunanina Tana ganina a dakin Nayi Sauri Narun gomota.sai nayi tunanin kar abin ya faru baya ya kara faruwa.da sauri na saketa na fito dakin. Ina fitowa daga Dakin Manasa nayi sa'a ba Wanda ya ganni Ina zuwa Munir yace Abdul-rahman naga 'yar aikin gidan su rahul Wllh har tabani tausayi Abdul-rahman bara a kirata ku gaisa Sai Nada katar dashi Nace karabu da ita Watarana In na sake dawo zan ganta Munir kazo mutafi Yamma tayi Bayan munyi Sallama da Mutanen gidan Mun fito Sameera kau duk batasan abinda ke faruwa ba tana Kicin Sai aikinta take, Lokacin da zan shiga mota Manasa ta kalleni Cikin tausayi tace man Baffa yanzu Sai yaushe kenan? Sai Nace mata Sai munyi Waya Muna tsaye nida Manasa mahaifin ta ya fito daga cikin gida ya kallemu yace Baffa daga gani kai mutumin kirkine don haka idan har dagaske kake to katuro Iyayenka Ayi maganar aurenka kai da Manasa, Bayan muntafi Sameera ita batasan abinda ya faru ba Data gama aikin datake Shine taje daki ta zauna Ananne tayi tunanin dazu dazata shigo gida taga taga mota Irin ta yayanta Baffa A guje ta fito izuwa harabar gidan wai koda zataga motar Tana zuwa Sai taga babu motar Tana dawowa falo Sai taga Manasa Sai tace ma Manasa Don Allah suwaye sukazo gidannan dazu? Manasa tace Meya faru? Sameera tace naga motar da sukazo tayi man kama data Yaya na Manasa taja tsaki Mitswwewww Tare da fadin ke dai dabbace wllh dallah ga fara can wuce kibani gu wawuya kawai, Sameera ta shiga daki tana kuka Ananne tayi Data Sani bata Bar zaria ba Da tana da kudi da zaria zata koma rashin kudi ya hana Sameera yin kwalliya Ko kwalliya bata yi Saboda bata da kayan kwalliya Sameera Tayi kuka kamar ranta zai fita Rahul Yayi duk iya kokarinsa Wajen kawo mata Samiri Abokansa Amma ita takekashe Tana da Wanda zata aura Amma takasa Fada masu Sunan Wanda zata aura Rahul ya kawo mata Manyan mutane amma bata son kowa Sai ni Wannan dalilinne yasa take sanya likabi Idan aka Aiketa kasuwa Idan Sameera tazauna ita kadai tunanina Kawai takeyi, Rahul jiyayi Kamar kiyayyar Sameera takara dasuwa a cikin zuciyarshi Wata rana Sameera tana a kasuwa Rahul Zata siya naman miya Rahul Yazo inda take ya wanketa da Mari Saboda yasa ta gugar kaya Kafin ta fara Hajiya Wato Innar Rahul ta aiketa kaasuwa Amma tayima Rahul bayani amma duk da haka yaci gaba da dukanta A tsakiyar kasuwa Sameera dataji bugu batasan lokacin data zageshi ba Cemai tayi Allah ya isa banyafe maka ba mugu kawai. MU HADU A PART 9 DA SAFE, KUNA TARE **** CIKIN DARE Part 9 ****** Rahul yayi matukar mamaki da Sameera ta zageshi A guje ya Debi motarsa Izuwa gida Yana shiga gida Sai Hajiya tace Rahul Ya kashigo gidannan ranka A6ace meyasa meka? Rahul yayi shuru Hankalin Hajiya ya tashi Ta kara cewa Rahul Don Allah kafada man Waya 6ata maka rai? Rahul cikin fushi yake cewa Hajiya Wai Hajiya yanzu kamar Sameera Ita Ce zata zageni a tsakiyar Kasuwa Hajiya tace Sameeran Ce tazageka? Yace Eh Hajiya! Hajiya Tace kaje ka dakko wayar Redio Idan tadawo kai mata Kafirin duka Rahul yaje ya samu Wayar Redio Manasa ma Itama tasamo wayar Redio Wai harda ita za'a daka Sameera saboda tazagar mata Yayanta, A falo suke tsaye suna jiranta Manasa da tadawo gida tana zuwa harabar Gidan Taji gabanta yana fadi, Kamar tajuya ta fita gidan amma hakanan ta tashiga gidan Tana zuwa falo Manasa tayi saurin kulle kofar falon Sameera ta zaro Ido Tace Manasa Lafiya? Manasa ta wanketa da mari Rahul yacire hijabin dake jikin Sameera kukaci gaba da dukanta Sai da sukaimata ti6is Suka far fasa Mata jiki Ko ina ajikinta ya fashe Fuskarta Ce kawai batayi komai ba Saboda itama tana rife fuskar Sameera tayi kuka kamar ranta ya fita Bayan sun gama bugunta 3 Awos Bata iya tashi Sameera da rarrafe takai dakinta Jikinta gaba daya duk bakarfi Kankace haka ciwon kai mai karfi Ya kamata zazza6i Idonta biyu Ita kanta Tana tausaya wa kanta Gari nawayewa Rahul ya shigo yacewa Sameera Ke Ga kayana can dana Manasa Dana Hajiya Ki wanke Mana Kitabbatar da kin wanke su kafin Mu dawo daga Jos Cikin sauri Sameera ta Amsa Saboda gudun bugu, Yaja tsaki ya fita, CIKIN DAREN bacci yaki yuwuwa man Saboda tunanin Sameera Shin tunanin danakeyi Wane hali Sameera take ciki kuma Ina take Ammsar Dana kasa Samu kenan, Gari na wayewa nayi wanka Nadau Key din motata Naje gidan su Dady Ina zuwa nagaida momy na da Abba Sannan Nasanar dasu Yadda mukayi da Abban Manasa nacewa naturo Magabata na da ayi Maganar Aurena da manasa Dady yayi farin ciki Itama mahaifiya ta Buda bakin Momy Sai tace dannan Wlh harga Allah naso ka Auri Sameera Allah nedai bai nufaba yanzu nata Raye ko bata Raye Wallahu A alamu Sai dady yace man yaushe Iyayen Manasa sukace katuro mahaifan ka Sai nace mai Dady 2week suka Ce Dady yace Allah ubangiji ya kaimu lokacin Momy tace Ameen, Jingine nake ajikin motata a kofar super market din dake Tudun wada Zaria Tunanin Sameera ya hanani walwala da Kwanciyar hankali Ni Sai naga kamar 6atar Sameera batazana Ce ga Rayuwa ta Ina tsaye nayi tagumi Sai ga wata kyakykyawar Yarinya taci kwalliya Tazo tasameni tayi man Sallama, Salamu alaika? Na6ata rai nace mata Wa'alaiki salamu, Sai tace naga Malam naga kamar kana cikin damuwa kozan tayaka fira? Sai nasha kunu Na daure fuska Nace mata Dan Allah malama kirabu dani kona Ce maki Ina Son mutun yataya ni fira ne? 6ace man dagani ko kuma nayi maki wula kanci, Sai tayi murmushi tace Allah ya baka hakuri Sai munsake haduwa Natabbata idan kadaina fushi to zaka saurare ni Saboda ni kyakykyawa Ce, Sai nayi tsaki Naja motata izuwa gida, Ranar da Su Dady suka shirya zasu Bauchi zuwa kar6o aure na Sameera ji tayi gabanta nafadi kamar wani Abu zai sameta Su dady suka isa Bauchi Amma su Kansu sunji ajikinsu kamar zasu ga Sameera a bauchi Saboda suna isa Bauchi tunanin Sameera ne kawai ke yawo a zuciyar su, Ita kanta Sameera Baccin data danyi na mintoci Har mafalki tayi wai sun hadu dasu dady Da mom da kuma ni Lokacin Da muka isa harabar gidan su Manasa Kowanne Acikinmu gabanshi bugawa yake Muna Isa Falon Kawai Sai naga,,,,, Muna shiga falon gidan su Manasa Sai Mukaga Manasa Tafito ban daki Sai kunya ta kamata A guje tatafi dakinta Sai nacewa dady Wannan Wadda taruga Itace Manasa Sai dady yayi dariya Hajiya Ce taje tacewa Sameera Kada tasake Tafito Kicin din indai tasan bata gama Abincin ba Sameera ta Amsa dato Muna zaune Sai ga Abban Manasa ya shigo suka gaisa da Mahaifana ni kuma Natashi natafi dakin Manasa A wannan zuwan da mukai gidan su Su Manasa Shine Aka gama Komai har sukasa Ranar Aurena da Manasa Wata daya ne akasa Saboda Dady Yana so yatashi kasar England Har Muka gama komai Muka tafi Sameera batasan Abinda ya faru ba Sai bayan wuce Sameera ta gama girki Sannan tasamu damar fitowa Daga kicin tana zuwa falo Sai taji Ana Maganar Dame dame ya kamata ayi A daurin Auren Manasa Da Muhammad Abdulhadi Sai taji gabanta ya fadi har tanayiwa Manasa murnar Saranta da akayi Manasa Cikin Fushi ta iya Amsawa Saboda tatsani Manasa sosai Sameera ahankali cikin kasala ta tatafi Dakinta Tana zuwa dakinta tazauna tayi tagumi Sai Taji sallamar Wani yaro An aiko shi ya kirata, Yana shigowa Inda Manasa take Yace mata Sameera kizo ana kiranki Awaje Sai tasha kunu Tace wake kirana?.Sai yaron yace Wani mutimine Tana cikin fadin haka Sai Ga hajiya tashigo Dakin tana fadin Dan ubanki kitashi kije Abokin Rahul ne yake kiranki Idan baki jeba Rahul Zaici Ubanki kuwa, Sameera da sauri tatashi tatafi Saboda Tsoron Rahul datake yi, Tana zuwa gum matashin dake kiranta Mai suna Bala Sai tayi mai Sallama Sai ya amsa mata tare dayin murmushi Sai tace malam Don girman allah karabu dani wllh akwai Wanda make so Buda bakin Bala Sayyace Waye kike so Sai tace Inarunka dole Sai kaji sunansa? Sai yace a'a Amma don girman allah Kitai maka kifada Man Sai tace mai Sunansa Abdul-ahad Sai bala ya zaro ido yace Wanda zai auri Manasar Shine kike so? Sameera tace don Allah karufaman Asiri wlh bashi bane Wannan nanine daban kuma Ai anayin suna Iri daya Sai yace Hakane Amma wlh Koki bar garinnan konace wa Rahul Saurayin Manasa Shikike so, A guje Sameera ta shige gida Saboda taji bala yace zai gayawa Rahul shiyasa Sameera tayanke Shawar Barin gidan Sameera tana zuwa daret tana nufa Dakinta Ta Hado kayanta Duka Tasa acikin Leda Sai da ta fahimci falon Bakowa Sannan Tayo waje da gudu .Sai mai gadi ya tareta yace Mata Sameera Nasan kina Shan Wuya acikin gidannan Garama ki gudu Ni kuma zan taya ki da Addu'a Sameera a tsorace tace mai Nagode tafita da gudu Ashe Bala wasa yake mata Shikanshi baya jin dadin dukan da Rahul yake mata, Sameera Tana zuwa tasha Tasamu wani mai kudi Taroshi alfarma daya tai maka mata da kudin mota Zuwa Zaria city Mutiminnan Dubu 10,000 Ya bata Saboda tausaya mata da yayi Ganin yadda tazo A gigice, Ina zaune Dady Ya kirani Bayan mungaisa Sayyace man My son Yau wata daya kenan dagama gidajena na Kaduna Nawa da naka Don kada Gidan da kake ciki nasiyar dashi Da Wanda mu muke ciki don haka gobe kashirya da Sassafe Nasa azo man da Tirela ta kwashe kayanmu duka Sai naji dadi amma tsoran danayi Karmu bar gidan kuma yaza mana Sameera tadawo gidan nemanmu gashi dady yace kada Wanda ya fada makowa Inda zamu zauna A Kaduna Gari nawayewa Tirela Tazo ta kwashe kayanmu duka A wunin muka gama Kwashe kayanmu Muka koma Kaduna Su dady Suka zauna A Tudun wada ta Kaduna Ni kuma Nazauna a Kawo A gidan dazan zauna Nida Amaryata Sameera, Satinmu Daya da komawa Sameera Bayan tabar gidan su Rahul Gidan wata kawarta taje A jos mai suna Fadeela Isma'il Satin ta ukku A gun Fadeela dayake ta bata duk Labarin Abunda ya faru da ita Sameera tayi matukar Tausaya mata Sosai Shiyasa har bata so Sameera tatafi Watarana tace ma Sameera Ya kamata muje Zaria Kudaidai ta da Iyayenki da kuma Baffan Saboda kisamu kiyi Aure kinsan Yanzu zaman aure shiyafi komai Dadi Lokacin Da Sameera Sukazo Zaria sukatarar da muntashi Adaidai wannan Lokacin Ake Daura Aurena Da Manasa, Sameera tayi kuka sosai Hakanan ta hakura ta koma Jos sukaci gaba da zama da Fadeela, Bayan aurena abokai Kowa ya watse Aduniya banda iyayena Babu Wanda nake son gani Sai matata Manasa Manasa tana Mani son Da bata ta6a yiwa wani ba Shekararmu daya da wata biyu Manasa tasamu Ciki Wanda ya kai munzalin haihuwa Watarana zani office Manasa tarakoni Izuwa harabar gidana Sai nashafa mata cikin ta nace Insha allahu Kafin nadawo Sai dai naji Anyo man Waya ace kin haihu Sai tayi nurmushi tace Ameen Sai nasunbaceta na ja motata nayi gaba,saneera kuwa Sai Alokacin ta kara wayewa haduwarta da fadeela ta koya mata Kwalliya Da salon tafiya Kai idan baka san Sameera ba Sai karantse kace 'yar shugaban kasace Watarana Sameera taje Super market Sai ta hadu da Polina Polina tayi matukar far in ciki da taga Sameera Bayan rungume Polina tace Sameera wllh Kinyi kyau ko Gomna Ai yaganki dole ya kyasa Sai polina tace wa Sameera Kishirya kizo muje Kaduna gun Manasa Wata kawatace wadda muka hadu a bauchi Jikin Sameera yayi sanyi Sai taba Polina labarin Zawanta bauchi Polina tatausaya mata Sai tacewa Sameera karki damu ai yanzu kinfi karfin Manasa tata6aki barinma mujinta yaganki Ai kau Dole shima ya kyasa Sai sukai dariya Sukayan Ke shawarar Gobe da safe misalin karfe shida zasu wuce Kaduna Saboda basaso sukwana Sai Sameera tacewa polina kinsan Inda Manasan Tayi Aure? polina tace Naje gidansu aka bani Address Din gidan Ammace man Tana da ciki haihuwa yau ko gobe Ahaka suka rabu akan gobe zasu hadu Sai suwuce Kaduna, Gari nawayewa Sukakama hanyar zuwa Kaduna Misalin karfe Ukku suka Isa Kaduna Sai kai sa'a sukaga Gidan su manasan Ananne Sameera taji gabanta nafadi Suna zuwan falon Manasa Sai Sameera taci karo da Makeken hotona wanda muka Dauka Da Manasa Ahotan kamar zanyi magana Hankalin Sameera yayi muguntashi. MU HADU ANJIMA. ** CIKIN DARE Part 10 ****** Sameera tana tsaye tana kallon Hoton da mukayi da Manasa shiyasanya hankalinta yayi matukar tashi Wai Baffa na shine zai auri Makiya ta Lallai kam za'ayi ta Abinda keyawo cikin zuciyarta kenan Shigowar Manasa ne falon yayanke tunanin da Sameera take Ciki Manasa Tana Sakkowa kasa Sai suka hada Ido da Sameera shiyasa hankalin Manasa ya tashi Manasa na zuwa Tacewa Sameera meyasaka kika zo gida na? Sameera taja dogon tsaki Mitswww Tare fadin ai yanzu daidai nake dake wlh Saboda yanzu ba a karkashinku nake aiki ba Ehe, Manasa tayi mamakin jin abinda Sameera take fada mata Polina ce ta dunga ba Manasa hakuri Buda makin Manasa Sai tace wa Sameera Bara nakira mai gidana wlh Zakici Kutumar Ubanki Shegiya Kawai Sai ta hau sama kirana polina tacewa Sameera zomubar gidan nan Bansan haka zata faruba Sameera tacewa Polina barta ta kira Mijin nata shima daidai nake dashi yana bude man huta nima Zan bude masa Polina ta kalli Sameera tace lallai Sameera baki da hankali, Ina Kishingide A makeken dagon dake dake Dakina Manasa tashigo a firgice Tazo ta zauna kusa dani tana kuka, Sai na My dear Meya faru ne? waya ta6a manke ne? Sai tace man wannan shegiyar 'Yar aikin tamuce tazo gidannan Shine take zagina don Allah my dear kayi man wani Alkawari Sai nace mata Manasa kifada buka tarki Insha allahu zan Cika maki gurinki nayi maki alkawari, Sai tace Baffa don Allah ina so Ka dakko mata Police sutafi da ita Sai tayi 1week sannan Asake ta kaji my dear na Sai nace mata karki damu muje naga Shegiyar da tata6a manke, Da suri Manasa ta mike Ina biye da ita abaya A hankali na sakko Kasa Kujerar da Sameera ta zauna tana Facing Waje Ni kuma Banga Sameera ba bayan ta kawai nake nagani, Ina sakko wa Nace Ma Manasa acikinsu Wace shigiyarce ta zageki Nanasa tace man gatacan da Hannunta tayi man nuni, Buda bakina cikin fada Nace mata Ke dan ubanki kijuyo fuskarki jiki abinda zan fada maki Sameera taki joyowa Sai nace mata Nan gidan ubanki ne? Sameera tajuyo ahankali tare da fadin A'A bagidan ubana bane, Ta juyowa naga Sameera CE dama nayi ma wannan zagin Ashe Itace 'Yar aikin da take shan duka a gidan iyayen su Manasa abinda keyawo daga kwakwal wata kenan, Hankalina yayi matukar tashi danagan ta Sameera tayi matukar kyau Kyenta ya kara karuwa Gashi taci arniyar kwalliya kyenta ya fito Buda bakin Manasa Sai tace man Baffa na mekake kallo anan kaje ka dakko mata police mana, Cikin sauri da firgici nace TO To Nararimi Hula nadorata akai ta kalminma barau da bawa nasa Nafice a guje Ina zuwa kofar gida Nasamu wuri nazauna Ina jiran Sameera su fito, Manasa tayi jiran tayi jiran amma bandawo ba Taita kirana awaya naki dauka Tun karfe 1:30pm suke a gidana har zuwa karfe 6:00pm suna ciki Idan Sameera Zata fita gidan Manasa CE kerike ta tare da fadin dan ubanki kijira ya dawo mana, da Sameera taga banda woba nan tabar polina Tafito daga gidan lokacin data fito Manasa bata saniba tana Kicin amma nasan data ganta to bazata barta ta tatafiba har Sai na dawo, Ina zaune Sai ga Sameera tafito daga gidan Sai nayi sauri na mike duk jikina babu karfi Sameera tana gani na Sai tayi kamar bata ganni ba zata tafi na janyo mata gyale natace mata Ina kuma zaki batare da munyi magana ba? Sameera taja tsaki Mitsww Dalla gafara can kaban hanya nawuce Abun mamaki wai yau ni Sameera takewa tsaki Nadunga bata hakuri Sai nace mata Sameera bara na dakko mota na Muje gidan su Daddy Tunda nasan farin ciki zasuyi idan suka ganki Sai tace HMMMM Jeka dakko Motar A gigice na shiga gida natarar da Manasa da polina suna firar guduwar Sameera komagana ban masu ba na dau key Ina fitowa daga gida na tarar da Sameera bata gun Dana barta Muhadu gobe dan jin cigaban **** CIKIN DARE Part 11***** Bayan nafito daga gida na Sai natarar banga Sameera a inda nabarta ba, Duk nakewaye Unguwar nan ina ta tambayar Sameera Babu Wanda ya San Sameera ballanta idan nayi masa kwatan centa a ganeta Sai naja motata Sai da nayi Nisa da gida Sannan nanemi gu na parka Na kunna AC motata Amma duk da haka jikewa nake da zufa hankalina yayi mugun tashi Sai da nayi dana sanin Shiga gida nabar Sameera a waje, Dakyar na iya Jan mota izuwa gida Ina zuwa na zauna a falo Sai da nayi awa daya a falo Amma Manasa duk bata San nadawo ba, Can ta fito Sai ta tarar dani zaune Sai ta zauna kusa dani, Sai tace man Darling Meke faruwa ne? Naga jikinka yayi sanyi Nayi mata shuru Sai ta kara ceman Darling Meyasa dazu baka dakko ma waccan shegiyar sameerar Police ba? Sai na harareta Jinai kamar natatta kata Don da ta kara zagin Sameera a wannan lokacin to Sai nayi Kasa kasa da ita, Sai bata kara ba Sai tace man Darling ai Polina ta bani Address din gidan da Sameera take a garin Jos Wlh Kauraye zan tura mata har jos Naji dadi da maganar da tayi man nacewa an bata Address din gidan da Sameera take amma ban nuna mata cewa naji dadi ba Sai nace mata Ki bani address gidan ni dakai na zan dakko mata police Sai Manasa tayi tsalle tace yawwa mujina Goben kenan zaka jos din? Sai nace mata Eh Sai ta rungume ni muka Wuce daki, Ranar banyi Bacci Tun da sassafe nayi wanka nace ma Sameera In zan tafi jos don na daukar maki fansa, Bayan nayi Breakfas Na kama hanyar zuwa gun Sameera misalin karfe 12:30pm na isa Jos kuma nagane gidan da Sameera take Sai natura yaro nace Kira man Sameera Nan gidan Jim kadan yaron ya fito yace man ance gata nan zuwa Sai nayi masa godiya Ina tsaye Sameera ta Fito Muka hada Ido tajuya zata shiga cikin gidan nasha gabanta cikin zauren Sai tace man daga yau Sai yau bani baka, don idan kai ba maye ne .miyasa ka biyoni har jos.lalle yau na tabba kai babban sakarai ne.nache kabar wurin nan.bana son ganinka.sai taja wani gogon tsaki mtswwwwwww. Ji barka ko kunya baka da ita.wai kai ka biyo sameera. To bari kaji yanxuh ni dai dai dakai ce. Na bar gidanku zalinchi da kake man ya isa.hakanan.yanxuh kana so ka maidani gidan ku.kasa man hawan jini ko.to Allah ya fika. Nayi mamaki da sameera ke ta gayaman maganganu.ammankawai Sai nayi murmushi ni dai bakinta kawai nake kallo Sameera tana sona Jan ajine kawai. . sameera sai maganganu take gayama man da habaice habaice.naga abin yana niyyar wuche gona da irin.cikin katuwar murya na daka mata tsawa nace YA ISAH SAMEERA nasan nayi maki babban laifi amman ki sani bani nace ki gudu kibar gida ba. Nasan yanzuh zuciyar ki tsuma take ji kike kamar kisa bakin gatari ki sassareni ki huta. Ki sani nazo garin jos ne don na baki haquri akan abinda ya faru.na durkusa kasa ina cewa sameera don Allah kiyi hakuri ko Allah idan mukai mashi laifi idan muntuba yana yafe mana.sameera badan ni ba ko dan su mama da dady kiyi hakuri ki bini zariya mu koma gida. Na kaiki wajen su umma da dady ba karamin farinciki zasuyi ba. Idan suka ganki. Sameera ko kallo na bata yi ba ta juya fuskar daga gareni tai shuru sai da nace kinji sameera sannan tace man naji ka tafi zanyi tunani.sai ta shige gida ta barni nan tsaye. Lakaci da ta shiga gida daidai lokachin ne manasa matata ta kirani ta waya take ceman darling naji ka shuru har kasa ankama wannan shegiyar ko. Lokacin naji dama manasa na kusa dani da sai make ta.saboda zagin sameera da take. Kawai tsaki nayi na kashe wayar. Manasa tai ta kiran waya ta amman ban dauka.sai da naga 17 misscalls nata. Lokacin da nadawo zariya misalain karfe 9:12pm nazo gidana nayi sallama amman manasa tana jina taki amsaman sallamar naje na bude dakina na kwanta ina jiran manasa ta kawo man abinchi na domin na dawo da wata mahaukachiyar yunwa amman manasa shuru har kusan karfe 11:30pm manasa shuru. Na tashi na bude kofa naje kitchin naga ko zanga abinchi.ina budewa naga alamar andafa abinchi amman an cinye ni ba'a aje man ba. Lokaci ne naje dakin manasa naga ta kwanta amman itama ba barchi take ba.nace mata ina abinchi na. Manasa tace nayi baki sun cinye.nace abinchi na kika ba bakin. Manasa tace kwarai kuwa ai bakon ka annabinka. kaje kitchin ka sulala indomie kaci mana. Sai ta jawo bargo ta lullube duka jinkin da fuskar ta. Lokacin ji nayi kamar na kama manasa cikin daren nan nayi mata shegen duka

Chapter 3 of 4