Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
zaune tsakanin wasu kaburbura guda biyu, yana kuka yana gunji. Bulukiya ya yi masa sallama, saurayi ya dakata da kuka ya mayar masa da sallama. Bulukiya ya tambaye shi, "wanene kai? Wadannan kaburburan fa? Su waye a cikinsu?" Saurayi ya dube shi ya kara fashewa da kuka. Ya yi kuka har sai da hawaye suka jike masa gaban riga. Sa'annan ya ce, "ka sani ya kai dan uwana, labarina abin mamaki ne da ban tausayi. Amma ba zan gaya maka shi ba har sai ka zauna tare da ni ka gaya mini labarinka da kuma inda ka nufa." Bulukiya ya sami wuri kusa ga saurayi ya zauna. Ya kwashe labarinsa duka, tun daga mutuwar mahaifinsa da yadda ya fito gida da dalilin fitowarsa da abubuwan mamaki da ya gamu da su, ya gaya wa saurayi. Ya kara da cewa, "yanzu Allah kadai ya san abin da zai faru gare ni bayan wannan." Saurayi ya yi ajiyar zuciya, bayan ya ji labarin Bulukiya. Ya ce, "ya dan uwana, Wallahi ba ka ga kome na mamaki ba a kan abin da na gani. Ka sani ya kai Bulukiya, ni na gamu da wakilan Shugabanmu Annabi Sulaimanu wato wadanda ya dora kan wakilci tun a lokacin rayuwarsa. Na gamu da abubuwan mamaki barkatai. Hakika labarina bako ne, ina so ka zauna nan wurina har in gaya maka dukkan labarina. Za ka ji sababin zamana a wannan wuri, da labarin wadannan kaburbura da kake gani." Lokacin da Sarauniyar Macizai ta kawo nan da labarinta sai Hasibu ya katse ta ya ce, "Allah ya ba ki nasara ya Sarauniya, ki bar ni in tafi gida. Ki hada ni da bayinki su fitar da ni daga wannan rami su kai ni bisa ga bayan kasa. Na rantse miki da Allah idan na koma gida ba zan kara yin wanka a gidan wanka ba sai a gidana duk tsawon rayuwata." Ta ce, "ba zan bari ka fita daga wannan rami ba, domin ban yarda da rantsuwarka ba." Da ya ji haka sai ya fashe da kuka, macizai suka yi kuka don tausayinsa. Suka shiga ba Sarauniya hakuri suna cewa, "muna rokonki ki hada shi da daya daga cikinmu ya fitar da shi daga wannan rami. Ya ranste miki ba zai kara shiga gidan wanka ba tsawon rayuwarsa." Yayin da Sauraniyar Macizai, mai suna Yamlaika, ta ji macizai sun matsa mata da roko, sai ta juya wurin Hasib ta sa ya rantse har cikin zuciyarsa cewa bayan ya fita daga wurinta ba zai kara shiga gidan wanka ba. Bayan ya rantse sai ta umurci wani katon maciji, wanda ya fi jaki girma, ya dauke shi ya fitar da shi waje. Maciji ya duka zai dauke shi, sai ya juya wurin Sarauniya Yamlaika ya ce, "ba zan tafi ba sai na ji labarin saurayin nan da Bulukiya ya iske yana kuka a cikin tsibiri da kaburbura a gabansa." ZANCI GABA INSHA ALLAH09 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI bayan Bulukiya ya gama labarinsa, sai saurayi ya ce, "ya dan uwana, me ka gani na mamaki? Ai ba ka ga kome ba a kan abin da na gani. Ni na ga Shugaba Sulaimanu a lokacin rayuwarsa. Na hadu da abubuwan mamaki iri-iri wadanda wani na bai taba gani ba. Sai ya fara labarinsa kamar haka: LABARIN JANSHAHU DAN SARKIN KABILA Ka sani cewa ya kai Bulukiya, mahaifina Sarki ne, sunansa Daigamusu. Yana mulkin daular Kabila (Kabul) da ta Banu Shahalan. A karkashin mulkinsa akwai daulolin sarakuna dubu goma, kowane sarki yana mulki da birane dari, kowane birni yana da kauyuka dari a karkashinsa. A cikin kowane kauye akwai akalla gidaje dari. Duka wadannan dauloli sukan kawo masa haraji a kowace shekara. Saboda haka a tsaya kwatanta yawan arzikinsa da yawan askarawansa bata lokaci ne kawai. Ya kasance Sarki mai adalci, yana kuma mulkin jama'arsa da gaskiya. Sai dai duk da wannan ni'ima da yake ciki, Allah bai nufe shi da samun da ba, wanda zai gaje shi bayan ransa. Kullum da wannan tunani mahaifina ke kwana, da shi yake tashi. Rannan dai sai ya sa aka tara masa dukan Malaman kasar, da masu bugun taurari da masu hisabi. Ya ce musu, "ina so ku duba mini taurari ku gani, shin zan sami dan da zai gaje ni kafin mutuwata?" Kowanen su ya dukufa ga aikinsa. Masu bugun taurari suka shiga zane bisa kasa suna sharewa, masu hisabi suka shiga lissafi, Malamai suka dauko takardu suka shiga nazari. Zuwa can suka ce masa, "ya Sarki, hakika Allah zai arzuta ka da haihuwar da namiji. Amma ba za ka sami wannan da ba sai tare da 'yar Sarkin Hurassana." Sarki ya yi farin ciki da wannan albishir na Malamai. Ya yi musu kyauta mai tarin yawa, ya sallame su. Ya kira babban Wazirinsa mai suna Ainazari, shi kuma wani shahararren jarumi ne wanda shi kadai yakan fatattaki rundunar mutum dubu. Duk fadin daular Kabila da kewayenta sun san shi, sun san tsananin jaruntaka tasa. Da ya zo Sarki ya gaya masa abin da Malamai suka gani a cikin taurari. Ya kara da cewa, "yanzu sai ka shirya maza ka tafi zuwa Hurassana, ka nemo mini auren 'yar Sarki Baharwanu." Waziri Ainazari ya tafi ya hada tawagar da zai tafi da ita, suka kafa tantuna bayan gari suna jira Sarki ya sallame su. Sarki Daigamusu ya kawo dukiya mai yawa ciki har da kyankyandi na alharini alfan da dari biyar da zinariya da azurfa da yakutu da sauran duwatsu masu daraja, ya ce a kai wa Sarki Baharwanu. Ya kuma kawo kaya irin wadanda amarya za ta bukata wajen yin ado ya bayar. Aka labta wa rakuma da alfadarai kaya. Kafin su tafi Sarki ya dauko takarda da alkalami ya rubuta wa Sarki Baharwanu wasika. A cikin takardar ya rubuta: Bayan gaisuwa da fatar alheri, daga Sarki Daigamusu zuwa ga Sarki Baharwanu. Ka sani cewa mun tara masana ilimin taurari da hisabi sun gaya mana cewa za mu samu haihuwar da namiji, amma wannan da ba zai samu ba face tare da 'yarka. Saboda haka ne na turo Wazirina Ainazari tare da gaisuwa zuwa gare ka da kuma dukiyar neman aure. Na umurce shi, idan ka yarda, ya zama wakilina a wurin auren da duk wata hidima da za a yi. Idan an kammala kome ya zo mini da amarya. Kamar yadda na san ka mutum mai saukin kai da saurin fahimtar al'amurra na san ba za ka juya wa wannan muhimmiyar bukata tawa baya ba. Kada ka manta ya Sarki Baharwanu, ni ke mulki da daular Kabila da ta Banu Shahalan, a karkashina ina da dauloli masu karfi. Idan na auri 'yarka za mu yi tarayya a cikin mulkin wadannan dauloli, na kuma yi alkawari zan rika turo maka da wani yanki na harajin da nake karba duk shekara. Ko ba kome ma, ai dan da za mu haifa shi zai gaje ni, kuma jikanka ne. Wannan ita ce bukatata zuwa gare ka. Sarki ya like bakin takarda, ya manna mata wata alama shaidar daga gare shi take, ya ba Wazirinsa. Waziri ya tafi tare da tawagarsa zuwa birnin Hurassana. Kwanci tashi har suka isa bayan birni, suka kafa tantunansu. Yayin da labarin zuwan su ya iske Sarki Baharwanu sai ya tada manyan fadawansa domin su tarye su. Aka aza wa dabbobi abinci da abin sha da kuma harawa saboda dabbobi, suka nufi wurin tawagar Waziri Ainazari da ke bayan gari. Da suka isa suka sauka daga kan dabbobinsu, suka gaggaisa da juna, aka shirya abinci da abin sha. Suka zauna suka ci suka sha har suka tumbatsa, daga nan sai suka shiga hira. Haka suka kasance a bayan gari tsawon kwana goma, sa'annan suka shirya kayansu duka, suka hau dabbobi suka dunguma sai cikin gari. Sarki Baharwanu ya taryi Waziri Ainazari a bakin fadarsa cikin murna da farin ciki, suka rungumi juna, Sarki ya ja shi zuwa cikin fadarsa. Ainazari ya kawo dukan dukiyar da ya zo da ita daga Sarki Daigamusu ya ba Sarki Baharwanu, ya zaro wasika ya ba shi. Bayan Sarki ya karanta wasika ya fahimci sakon da ke cikinta, sai murna ta kashe shi. Ya juya wurin Waziri fuskarsa cike da fara'a ya ce, "ka yi murna ya kai Waziri, wallahi da Sarki Daigamusu zai bukaci rayuwata da sai in ba shi balle 'yata." Ya tashi ya shiga cikin gida, ya tarar da diyarsa da mahaifiyarta, ya kwashe labarin abin da ke tafe da Wazirin Sarki Daigamusu ya shaida musu. Ya tambayi ra'ayinsu, suka ce ya yi abin da duka ya ga ya dace. Ya kuma tara fadawansa ya gaya musu dalilin zuwan Ainazari, ya nemi shawararsu. Su ma suka ce masa ya yi abin da duk ya ga ya dace. Sai ya tafi wurin Waziri Ainazari ya shaida masa cewa ya amince da bukatar Sarki Daigamusu ta auren 'yarsa. Waziri ya zauna a wannan birni tsawon wata biyu, daga nan sai ya ce wa Sarki, ya kamata a yi haramar daurin aure domin yana so ya koma kasarsu. Sarki ya ce, wannan shi ne zancen hankali. Aka shirya dukkan abin da ake bukata na daurin aure. Sarki ya tara waziransa da hakimai da fadawa da malamai, kai har da talakawan gari sai da aka gayyato. Aka taru tinjim a kofar fada. Sarki ya umurci malamai su daura auren Sarki Daigamusu da 'yarsa karkashin wakilcin Waziri Ainazari. Bayan an daura aure, Sarki ya sa aka kawata birni da kwalliya, aka shimfide dukkan hanyoyi da shimfidu na alfarma. Aka shirya amarya da kayan ado iri-iri ta fito kamar 'yar tsana. ZANCI GABA INSHA ALLAH matsalar dayace gaskiya comment da like suna kasawa dole mutum yaji sanyin jiki wannan fa anayi ne kawai dan sha'awa bawai kudiba' anma in zaku karanta kuwuce shuru to tayaya zangane cewa bani daya nake rawa na ina kida ba. WhatsApp only 08032767547 This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4