Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
k'ark'ashin duwat su idan an fasa dutsen a fito da su ana aikata zinariya da su?' ZANCI GABA INSHA ALLAH 06 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI Ya yi barci a nan har zuwa wayewar gari sannan ya shafa ruwa a k'afarsa ya shiga kogi na shida, ya yi ta tafiya dare da rana har ya isa wani tsibiri. Ya sauka a ciki yana tafiya kimanin sa'a guda sai ya ga wasu duwatsu manya guda biyu itatuwa sun mamaye su wad'anda 'ya'yansu tamkar fuskar mutum suke, akwai gashi da hanci da ido da baki da kunne a jikinsu. Wasu kuma 'ya'yansu tamkar tsuntsaye suke suna mak'ale da k'afafunsu a jikin bishiyar. Wata bishiyar kuma 'ya'yanta tamkar k'wai da nama suke suna fad'owa. Ta kasance tana cin wuta a bisanta duk wanda ya je kusa da ita zai iya k'onewa. Wasu kuma 'ya'yan itaciyar tamkar mutane na dariya, wasu kamar suna kuka. Ya ga dai abubuwan al'ajabi da yawa a wannan tsibirin. Da gari ya waye ya tafi gab'ar kogi sai ya ga wata doguwar bishiya ya zauna k'ark'ashinta har lokacin da dare ya yi sannan ya hau kan ta ya yi barci. Ya zamana yana tunanin ayyuka da hikimomin ubangiji mad'aukakin Sarki, yana wannan tunanin sai ya ga ruwa ya yi k'asa, 'ya'yan ruwa suka fito daga ciki kowanne na d'auke da jauhari yana haske. Suka tattaru a k'ark'ashin bishiyar nan da yake kai suna wasanni suna rawa, suna wak'a, shi kuwa yana daga sama yana kallon su yana nishad'i, yana mamakin haka. Ba su gushe ba suna haka har gari ya waye sannan suka koma cikin ruwa suka b'ace. Ya sauko k'asa ya shiga kogi na bakwai bayan ya shafe k'afarsa da ruwan nan. Yayi ta tafiya ba dare ba rana bai ga wani tsibiri ba ko gab'a ko itace ko fili ko kwari har wata biyu cikakku sannan ya kawo k'arshen sa. Ya wahala sosai saboda yunwa har sai da ya kai yana farautar kifi da hannunsa kuma yana cinsa haka d'anye saboda yunwa. Ya sauka daidai lokacin walaha cikin wani tsibiri mai yawan itatuwa dogaye. Ya rik'a dubawa dama da hagu yana tafiya ciki har ya ga itaciya tuffaha mai 'ya'ya a jikinta, ya sa hannu zai tsinko, sai ya ji an daka masa tsawa daga saman bishiyar ana cewa, "kul ka kuskura ka matso kusa da wannan bishiyar, zan raba jikinka biyu!" Ya d'aga kai cikin firgici ya ga wani jiki ya kai zira'i arba'in na mutanen wannan zamani. Tsoronsa ya k'aru ya yi hanzarin barin wannan bishiyar. Sannan ya ce da jikin, "me ya sa ka hana ni ci daga wannan bishiyar?" Jikin ya ce, "saboda kai d'an Adam ne ubanka Adamu ya manta da alk'awarin Allah ya ci daga bishiyar da aka hana shi ya aikata zunubi. "To kai menene, kuma wannan tsibirin na wanene, kuma yaya sunanka?" Bulukiya ya tambayi jikin. "Ni sunana Sharahiyu kuma tsibirin nan mallakin sarki Saharu ne, ni bawansa ne wanda ke kula da nan." Daga nan ya ce da Bulukiya, "kai kuma wanene, ta yaya ka zo nan?" Ya fad'a masa labarinsa kaf, daga nan ya ce, "kada ka ji tsoro, babu abin da zai same ka." Ya kawo masa abin da zai ci na daga abinci, ya ci har ya ishe shi sannan ya yi sallama da jikin nan ya tafi. Yayi ta tafiya tsakanin duwatsu da hamada da rairayi har kwana goma. Daga nan ya tsinkayi k'ura na murtukewa daga nesa kamar rumfa. Da ya sake matsawa sai ya ji ana kururuwa da nishi da tankiya. Ya ga jama'a bisa dawaki suna ta yak'i da junansu jini na zuba har ya zama tamkar k'orama na gudana. Muryoyinsu na rugugi tamkar aradu, suna rik'e da takubba da masu da gatura da majaujawa da kibiya da sulke da buke da duk wasu nau'in kayan fad'a abin k'erawa da bak'in k'arfe. Da ya ga haka sai ya firgita tsoro mai tsanani ya kama shi. yayin da Bulukiya ya ga irin wannan yak'i sai ya firgita ya razana da tsoro mai tsanani. Yayin nan ya toge bai iya k'arasawa gare su ba, can sai suka hange shi, suka rirrik'e hannayen junansu suka bar yak'in suka taho zuwa gare shi. Suka kewaye shi suna mamakinsa, d'aya daga cikinsu ya ce, "wanene kai, ta yaya ka zo nan kuma ina za ka je, sannan wanene ya nuna maka wannan gari namu?" Ya ce musu, "ni d'an Adam ne daga cikin Bani Isra'ila, na fito cikin begen saduwa da annabin k'arshen zamani Muhammadu mai tsira da aminci su tabbata a gare shi, amma na b'ace hanya ne na biyo nan." Mahayin dokin ya ce, "ba mu tab'a ganin d'an Adama ya zo nan ba sai kai a yau d'in nan." Suka yi ta mamakinsa da iya maganarsa. Ya ce musu, "ku wace irin halitta ce?" Suka ce "muna daga k'abilun aljanu ne." "Menene musabbabin wannan yak'in naku, yaya sunan wannan bigire kuma daga ina kuke?" Suka ce, "daga farar k'asa muke, duk shekara Allah kan umarce mu da mu zo wannan wuri mu yak'i kafiran aljannu." Bulukiya ya ce, "ina farar k'asa take?" "Can ne bayan dutsen K'af daga nan tafiyar shekara saba'in da biyar ne, nan kuma tana cikin k'asashen Shaddadu d'an Adu, mu aikinmu kenan yak'i da kuma tasbihi da hailala ga Ubangiji. Kuma muna da sarki sunansa Saharu, babu komai a kan ka za mu je tare da kai wajensa domin ya gan ka ya ji dad'i." Suka tafi tare da shi har suka isa masaukinsu inda ya ga wasu manya - manya shigifu na koren alharini babu wanda ya san adadinsu sai Allah mad'aukakin Sarki. Daga tsakiyarsu kuma wani d’aki ne ma fi girma an yi masa ado da jan alharini fad'insa ya kai murabba'in zira'i dubu, gefensa an d'aura shudin alharini, sannan itatuwan da aka kafa shi an d'ad'd'aura zinariya da azurfa. Bulukiya ya yi mamaki mai yawa da ganin wannan wuri ya tafi tare da su zuwa babban d’akin, wanda shi ne na sarkinsu. Suka shigar da shi gaban sarki Saharu wanda ke zaune akan k'asaitacciyar kujera ta azurfa kansa na d'auke da kambi na jan zinariya, an mata ado da lu'ulu'u. Daga damansa sarakunan aljanu ne hagunsa kuma malamai da mahukunta da sauran ma'abuta daula da wasun su. Da sarki ya gan shi sai ya buk'aci a shigo da shi gabansa. Bulukiya ya sunkuya ya sumbaci k'asa a gaban sarki. Sarki Sahara ya ce, "matso nan kusa da ni ya kai namiji." Ya matsa kusa da shi, Sarki ya yi umarnin a kafa masa kujera ya zauna sannan ya ce masa, "kai wace halitta ce? Bulukiya ya ce, "ni bil adam ne daga cikin Bani Isra'ila." "Fad'a min labarinka da yadda ka zo wannan wurin namu." Bulukiya ya kwashe labarinsa ya fad'a wa sarki Saharu. Sarki ya cika da mamaki da jin wannan labari. Zanci gaba insha Allah07 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI bayan Bulukiya ya k'are bai wa Sarki labarinsa, Sarki ya yi ta mamaki da haka. Sannan ya yi umarnin a shigo da abinci, suka kafa manyan shimfid'u aka shigo da kabuka guda dubu d'aya da d'ari na jan zinariya da azurfa da tagulla, wasu kabuka na d'auke da dafaffun rak'uma ashirin, wasu hamsin, wasu kuma na d'auke da tumaki hamsin wasu d'ari. Bulukiya ya cika da mamaki mai yawa. Suka wanke hannu gaba d'aya fada aka shiga cin abinci har da Bulukiya. Suka ci suka tumbatsa sannan aka kawar da kabuka aka shigo da kayan marmari da ruwan sha. Suka ci suka sha suka gode wa Allah mad'aukakin Sarki sannan suka shiga zikiri da salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Da Bulukiya ya ji suna ambaton sunan Annabi Muhammadu sai ya yi mamaki mai yawa ya ce da Sarki, "ina so na yi maka wata 'yar tambaya." Sarki ya ce, "yi tambayar ka ko wace iri ce." "Ya sarki, ku wacce irin halitta ce, menene asalinku, ta yaya kuka san sunan Annabi Muhammadu har kuke k'aunar sa?" Sarki Saharu ya ce, "ka sani ya Bulukiya, Allah halicci wuta bisa rufi bakwai, tsakanin kowane rufi da wani rufin nisan tafiyar shekara dubu ce. Ya ambaci rufi na farko da Jahannama domin hukunta musulmi masu sab'o da suka mutu ba su tuba ba. Rufi na biyu ya ambace shi da Laza, an tanade ta domin kafirai. Rufi na uku mai suna Jahimu domin a jefa Yajuju da Majuju ne. Rufi na hud'u kuwa sunansa Sa'ir domin Iblis da rundunarsa. Na biyar kuwa sunansa Sak'ara an tanadi wannan domin masu wasa da sallah. Na shida sunansa Hud'ama domin yahudu da nasara, sai na bakwai kuwa Hawiya an tanade shi domin munafukai. Wad'annan su ne rufin da aka yi wa wuta." Bulukiya ya ce, "kenan Jahannama ta fi kowacce sauk'in azaba kasancewar ta a rufi na farko." Sarki Saharu ya ce, "na'am domin ita ce mafi sauk'in azaba duka, amma duk da haka a cikinta akwai duwatsu dubu na wuta a ciki, a bisa kowanne dutse akwai jeji dubu saba'in, a kowanne jeji akwai birane dubu saba'in na azaba a cikin kowanne birni akwai gidaje dubu saba'in na azaba, a kowanne gida akwai, d'akuna dubu saba'in, a kowanne d'aki akwai gado dubu saba'in na wuta. A kowanne gado akwai dangin azaba dubu saba'in. Amma ragowar rufin wutar kuwa babu wanda ya san k'iyasin tsananin azabar da ke ciki sai Allah." Yayin da Bulukiya ya ji haka sai ya fad'i sumamme saboda tsoro, yayin da ya farfad'o ya yi kuka mai yawa sannan ya ce, "ya Sarki yaya halinmu zai kasance?" Sarki ya ce, "kada ka ji tsoro, na sani cewa duk wanda ke k'aunar Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi to wuta ba za ta shafe shi ba. Domin kuwa duk wanda ya kasance bisa tafarkinsa to wuta gudunsa take. Game da mu kuwa Allah ya halicce mu daga wuta, farkon abin da Allah ya halitta da jahannama su ne wasu jiki guda biyu ana kiransu Halitu da Malitu. Shi Halitu an yi masa fasali kamar zaki, wutsiyarsa kamar ta kunama. Tsawonsa ya kai tafiyar shekara ashirin, an yi masa azzakari irin na namiji. Malitu kuwa an yi masa siffar kura, yana da wutsiya irin ta maciji, gabansa kamar farjin mace. Sai Allah ya nufi wad'annan wutsiyoyin su had'u su yi aure inda suka hayayyafa daga macizai da kunamun cikin wuta wad'anda Allah zai azabtar da wad'anda aka jefa a ciki. A kullum suna k'ara yawa suna rub'anya yawan su. Daga nan Allah ya umarci wutsiyoyin Halitu da Malitu su sake aure a karo na biyu, suka haifi 'ya'ya goma sha hud'u, bakwai maza, bakwai mata. Su kuma suka yi aure a junan su suka. Dukkansu suna biyayya ga iyayensu sai guda d'aya da ya fand'are sai ya zama tsutsa wadda ita ce asalin Iblis, la'ananne. Iblis ya kasance daga makusantan Allah yana bauta gare shi har ya zama an d'auke masa sama ya zama cikin mala'iku yana bauta tare da su. Iblis ya ci gaba da bautawa Allah cikin mala'iku har ya zuwa lokacin da Allah ya halicci Adamu, amincin Allah ya tabbata a gare shi, sai ya yi umarnin mala'iku su yi masa sujjada, Iblis ya k'i bin umarnin. Don haka Allah ya kore shi daga sama Allah ya la'ance shi. Shi Iblis yana da zuri'a wad'anda su ne shaid'anu, amma ragowar mazaje shidan nan da ba su fand'are su ne rundunar aljanu nagari. Mu kuma muna daga zuri'arsu. To ka ji Bulukiya wannan shi ne asalinmu." Bulukiya ya yi mamaki mai yawa dangane da wannan labari. Daga nan ya ce da Sarki, "ina rok'on ka sa wani hadiminka ya d'auke ni zuwa garinmu." Sarki ya ce, "mu ba mu da ikon aikata komi dai da iznin Allah, amma idan kana da muradin tafiya daga gare mu, to zan d'ora ka bisa wata god'iyata na sa ta kai ka can iyakar mulkin k'asata inda za ka sadu da wani Sarki mai suna Barahiya. Idan ya ga god'iyar zai shaida ta, ya karb'e ka sannan ya dawo mana da ita. Wannan ne iyakar abin da za mu iya maka, babu k'ari." Da Bulukiya ya ji haka sai ya yi kuka sannan ya ce, "aikata hakan gare ni ya Sarki." Daga nan sarki Saharu ya d'ibiya shi akan god'iya ya ce masa, "ka yi hankali kada ka zungure ta ko ka yi mata kururuwa za ta kashe ka. Kai dai ka zauna kurum a bayanta cikin natsuwa za ta kai ka inda aka umarce ta." Bulukiya ya ce, "na ji na d'auka." Ya hau ya zauna, god'iya ta soma tafiya ta wuce da shi ta gaban d’akuna zuwa inda ake girki da dafe - dafe. A nan ya ga manyan tukwane an hura wuta k'ark'ashinsu, kowace tukunya akwai rak'uma hamsin a cikinta. Wasu rak'uman kuma an rataye su wuta na ci a k'asan su suna gasuwa a haka. A nan ya tsaya yana kallo cike da mamaki har Sarki Saharu ya yi tsammanin yunwa yake ji. Ya yi umarnin a k'unsa masa rak'umi biyu gasassu. Aka sassara masa naman aka cusa a kwacciyar god'iya sannan ya yi bankwana da su ya yi gaba. God'iya ta yi ta tafiya da shi har zuwa k'arshen iyakar ikon sarki Saharu sai ta tsaya cif, shi kuma ya sauka ya shiga karkad'e k'urar da ta mak'ale a tufafinsa. Yana cikin haka sai ga wasu jama'a sun zo gare su, suka shaida god'iyar suka tafi da ita tare da shi zuwa ga sarki Barahiya. Bulukiya ya gaishe da shi yana mai yi masa sallama. Sarki ya amsa gaisuwar da sallama, sannan ya zaunar da shi a kujerar alfarma a kusa da shi kewaye da rundunar jarumawansa da zab'ab'b'unsa da sarakunan aljannu sun jeru hagu da dama. Bayan sun d'an tattauana aka shigo da abinci suka ci suka k'oshi suka tumbatsa suka gode wa Allah. Sannan aka hallaro da kayan marmari suka sha. Sarki Barahiya wanda fadarsa take tamkar ta sarki Saharu ya ce da Bulukiya, "yaushe ka baro sarki Saharu?" Bulukiya ya ce, "kwana biyu da suka wuce." Sarki Barahiya ya ce, "ka kuwa san nisan tafiyar da ka yi a wad'annan kwana biyun?" Ya ce, "A'a." "Ka sani kai ka yi tafiyar shekara biyar da wata goma ne a wannan tsakanin." Barahiya ya ce da Bulukiya, "tafiyar nan da kake gani tamkar ta kwana biyu, to tafiyar shekara biyar da wata goma ce ka yi. Don ma god'iyar da ta d'auko ka ta razana da kai ne, domin ta ga kai d'an Adama ne ta yi nufin ta jefar da kai ka halaka, to amma nauyin rak'uman nan biyu da aka d'aura mata ya sa ta ji nauyi ba ta iya jefar da kai d'in ba." Bulukiya ya gode wa Allah da ya tserar da shi sannan Sarki ya ce da shi, "fad'a min labarinka da sanadin zuwanka k'asashenmu." Bulukiya ya zanta masa labarinsa gaba d'aya da yadda ya zo har nan wurinsa. Sarki ya yi mamaki da jin wannan labarin, ya zaunar da shi a wajensa har wata biyu." A nan sarauniyar macizai ta tsahirta da bai wa Hasib labarin Bulukiya. Hasib ya yi mamaki mai yawa, sannan ya ce da ita. "Ni dai ina rok'o cikin alfarmar ki da kyautatawarki ki umarci wani daga sarakunanki ya kai ni bayan k'asa na sadu da mutanena." Ta ce, "kai Hasib Karimuddini idan ka fita wajen iyalinka za ka shiga gidan wanka, idan ka k'are wankan ni kuma hakan zai yi sanadin mutuwa ta." Hasib ya shiga rantsuwar cewa ba zai sake shiga gidan wanka ba har abada. Ya k'ara da cewa, "idan wanka ya kama ni zan rik'a yi a gidana." Sarauniya ta ce, "ai fa da za ka rantse min sau d'ari ba zan yarda da kai ba, ku 'yan Adam ba ku d'auki alk'awari a bakin komai ba. Hatta babanku Adamu da ya yi alk'awari da Allah wanda ya halicce shi daga tab'o ya rik'a cud'a yumb'unsa safiya arba'in sannan ya umarci mala'iku su yi masa sujjada, amma daga k'arshe sai da ya manta ya sab'a umarnin da Allah ya yi masa." Da ya ji haka sai ya yi shiru, ya yi ta kuka, bai daina kuka ba har kwana goma sannan ya dangana. Ya ce da sarauniyar macizai, "to ba ni labarin k'arashen hik'ayar Bulukiya." Sarauniya ta ce, "ka sani ya Hasib bayan Bulukiya ya kwashe watan biyu a wajen sarki Barahiya sai ya yi masa bankwana ya tafi cikin daji dare da rana har ya sadu da wani babban tsauni mai girma. Ya kama ya hau. A nan ya samu wani mutum zaune a saman yana tasbihi da hailala da salati ga Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ya yi masa sallama ya amsa masa, sannan ya tambaye shi daga inda ya fito da inda ya nufa. Bulukiya ya fad'a masa sannan ya ba shi labarinsa daga farko har k'arshe. Mutumin ya yi mamaki mai yawa, sannan ya yi addu'a da fatar alheri suka yi bankwana. Ya ci gaba da tafiya ba dare ba rana har ya sadu da wani kwari mai girma, ya gangara zuwa cikinsa inda ya ga k'orammu bakwai masu girma da bishiyoyi gewaye da wajen. Ya tsaya yana kallon kyawon wajen yana k'ayatar da shi. Daga wata kusurwa kuma ya hangi wata babbar bishiya k'ark'ashinta wasu halittu ne guda hud'u. Ya sake matsawa kusa domin ya k'are musu kallo, ya ga na farko yana kama da mutane, na biyu yana kama da dabbobi na uku yana kama da tsuntsaye na hud'u kuma yana kama da bajimi. Ya ji suna tasbihi suna tsarkake sunan Allah Mad'aukakin Sarki suna salati ga fiyayyen halitta. Bulukiya ya yi mamaki sannan ya yi gaba yana tafiya har ya sadu wani babban dutse a samansa wani mutum na ta sallah. Ya isa gare shi ya yi masa sallama. Mutumin ya amsa masa sannan ya nemi sanin daga inda yake da inda ya nufa, ya fad'a masa. Sannan Bulukiya ya tambaye shi sunan wurin da abin da yake yi a nan. Ya amsa masa ya ce, "wannan shi ne Jabala K'af babban dutsen da ya kewaye duniya duka. Ni kuma Allah ya sallad'a min dukkan duniya da abin da ke cikinta a tafin hannuna. Idan Allah ya so wuri da azaba na daga girgizar k'asa ko yunwa ko fari ko yak'i ko ni'ima yakan umarce ni da na aiwatar gwargwadon yadda ya so ba tare da na bar wurin nan da nake ba. ZANCI GABA INSHA ALLAH08 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI waliyin nan ya fad'a wa Bulukiya game da zaman da yake a dutsen Kaf. Bulukiya ya ce, "yalla bayan dutsen nan akwai wani abu da Allah ya halitta?" "Allah ya halicci wata duniya wadda take fara tamkar azurfa, babu wanda ya san girmanta sai shi. Tana cike da mala'iku wad'anda abincinsu da abinshansu zikiri da tasbihi gare shi. Duk daren Juma'a suna tattaruwa a kan dutsen nan suna bauta wa Allah. Idan gari ya waye sai su nemi gafara ga al'ummar fiyayyen halitta mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma dukkan mai wankan Juma'a. Aikinsu kenan har ya zuwa ranar alk'iyama." Bulukiya ya ce, "yalla bayan wannan dutse akwai wani babban dutsen a gabansa?" Waliyi ya amsa ya ce, "kimanin tafiyar shekara d'ari biyar akwai wani dutse na rab'a da k'ank'ara ne. Shi yake hana zafin jahannama shigo wa duniya, ba domin shi ba da ta k'one duniya duka. Sannan a bayan wannan dutse akwai duniyoyi guda arba'in kowace duniya ta ninka duniyarmu sau arba'in. A cikinsu gaba d'aya mala'iku ne ke tasbihi. Su kuwa sun kasance kowace da irin launinta, wata ta zinariya, wata ta azurfa, wata ta tagulla da yak'utu. Mala'ikun da ke ciki babu wanda ya san adadinsu sai Allah, ba su san Hauwa'u ba ballantana Adamu, ba su san dare, balle rana. Aikinsu kawai tasbihi da tahmidi. Ka sani ya Bulukiya yadda sama take bakwai haka k'asa take bakwai. Allah ya halicci wani mala'ika mai girman halitta, babu wanda ya san girmansa sai wanda ya halicce shi. To shi yake d'auke da dukkan k'assan. A k'asa da shi kuma wani babban dutse ne, a k'asan dutsen bajimin sa ne ke d'auke da shi. A k'asan sa d'in kuma wani babban kifi ne, a k'asan kifin wani makeken teku ne. Allah mad'aukakin sarki ya tab'a fad'a wa Annabi Isa, amincin Allah ya tabbata a gare shi game da wannan kifi. Sai Annabi Isa ya ce, "ya ubangiji ka nuna min wannan kifin na gan shi. Sai Allah ya umarci mala'ika da ya kai Isa zuwa inda kifin ya ke. Ya ce da shi, "duba izuwa ga kifin ya Isa." Isa ya duba bai ga komai ba sai wani haske da ya wuce ta gabansa tamkar walk'iya. Ganin hasken sai Isa ya fad'i sumamme. Yayin da ya farfad'o sai Ubangiji ya ce masa, "ya Isa ka ga kifin?" Isa ya ce, "da girman buwayarka da d'aukakar ni ban ga kifin ba, amma na ga wani haske ya wuce ta gabana gwargwadon nisan tafiyar kwana uku." Ubangiji ya ce, "wannan hasken da ka gani gwargwadon tafiyar kwana uku kan kifin ne ya wuce ta gabanka. Ka sani a kullum ina halittar kamar wannan guda arba'in." Bulukiya ya yi mamaki gaya da jin wannan labarin, sannan ya ce, "yalla ko a bayan tekun nan da kifin ke ciki akwai wani abu da Allah ya halitta?" "A bayan tekun Allah ya halicci iska mai yawa, a k'asan iskar akwai wuta, a k'asan wutar wata macijiya ce mai girman halitta ana kiranta Falaki, ita ta kasance ba domin tsoron Allah ba za ta iya lank'wame duniya da abin da ke cikinta da dukkan abubuwan da ke bisanta na daga mala'ika da sa da kifi da ruwa da wuta duka, cikin abin da bai fi k'iftawar ido ba. , Waliyyi ya ci gaba da ba Bulukiya labari ya ce, "ba don da wannan macijiya take jin tsoron Ubangiji Mai Girma da d’aukaka ba, da tuni ta had’iye dukan abin da ke bayanta na iska da wuta da Mala'ikan da ke tare da su. Ba tare da ta ji kome ba a cikin cikinta. Lokacin da Allah ya halicci wannan macijiya sai ya umurce ta da kudurarsa, "bude bakinki zan yi ajiya a cikinsa." Macijiya ta amsa, "na ji na yarda, ya Ubangijina." Sai ta bude bakinta. Allah Madaukin Sarki ya saka wuta a cikin bakin macijiyar ya ce, "ajiye mini wannan har zuwa ranar tashin kiyama." Idan ranar ta zo, Allah zai aika Mala'iku da sarkoki, ya umurce su su kawo masa wutar a daure. Sai su zo da ita a gabansa daure cikin sarkoki tana toroko, tana tirjiya, tana neman abin da za ta lasa. Idan aka tara mutane sai Allah ya umurci wuta da ta bude kofofinta. Idan kofofin sun bude za su rika fitar da wadansu irin tartsatsi na wuta, girman kowane tartsatsi ya fi duk wani babban tsauni da ke cikin duniya." Yayin da Bulukiya ya ji zancen Waliyyi sai ya fashe da kuka don tsananin tsoro. Ya yi kuka kuka mai tsananin, ya wuce gaba yana zubar da hawaye ya nufi Yamma. Bayan ya yi tafiya mai tsawo sai ya hangi wadansu halittu guda biyu, manya-manya kowanensu ya fi giwa girma, suna zaune a gaban wata kofa da take rufe, suna tsaron ta. Yayin da ya yi kusa ga wadannan halittu sai ya ga daya na da siffar zaki, daya kuma siffarsa irin ta bajimin sa ce. Ya yi sallama gare su, suka mayar masa da sallama. Suka tambayi labarinsa da inda yake nufin zuwa. Bulukiya ya ce, "Ni dan Adamu ne, na fito yawon neman shugabanmu Annabi Muhammadu, mai tsira da amincin Allah, hanya ta biyo da ni ta wannan tsibiri." Sa'annan ya tambaye su labarinsu da kuma dalilin zaman su a gindin wannan kofa kublalliya. Suka amsa masa, "mun kasance masu tsaron wannan kofa tun lokacin da aka halicce ta. Bayan wannan kuma ba mu da wani aiki sai na zikirin Allah da yi wa Annabi Muhammadu salati. A haka za mu dawwama har zuwa ranar tashin kiyama." Bulukiya ya yi mamaki, ya tambaye su menene a cikin kofar? Suka amsa masa da cewa, "ba mu san abin da ke cikin ta ba." Ya ce, "na gama ku da Allah ku bude mini ita in shiga domin ganin abin da ke ciki." Suka ce, "ba mu da ikon bude maka ita. Duk duniya babu mai iya bude ta sai fa Ubangijin da ya halicce ta." Da Bulukiya ya ji haka sai ya daga hannayensa sama yana addu'a, "ya Ubangiji, ka bude mini wannan kofa in ga abin da ke cikinta." Allah kuwa ya karbi rokonsa, ya umurci kofa ta bude, nan take sai ta bude a gabansa. Bulukiya ya shiga cikinta, ta koma ta rufe kamar yadda take da farko. Bulukiya ya yi duba a gabansa sai ya ga wani babban teku yana gudana, rabin ruwansa na gishiri rabi kuma mai dadi. A kowane gefe na tekun a kawai manyan duwatsu na jan yakutu. Ga kuma wasu irin halittu ko'ina suna ta ambaton sunan Ubangiji tare da yi wa Annabi Muhammadu salati. Bulukiya ya tafi gare su ya yi musu sallama. Bayan sun amsa masa sallamarsa, ya tambaye su labarin wannan teku da duwatsunsa. Suka ce masa, "wannan teku da kake gani ya kasance asalin dukkan ruwan da ke bayan kasa. Ruwan gishiri ya tafi zuwa ga tekunan da ke bayan kasa. Ruwa mai dadi kuma ya tafi ga gulabe da koramu da tafukka. Haka wannan teku za ta dawwama cikin kudurar Ubangiji, buwayi gagara misali, har zuwa ranar tashin kiyama. Duwatsun nan suke tare ruwan idan ya yi yawa." Su kuma suka tambaye shi labarinsa da inda ya nufa. Ya kwashe labarinsa duka ya gaya musu, ya tambaye su tafarkin da zai bi, suka ce masa ya ketare tekun da ke gabansa. Ya shafa ruwan ciyawar nan da ke tare da shi ga tafin kafafunsa, ya yi sallama da su, ya taka ruwan teku ya ci gaba da tafiya. Bayan ya yi tafiyar kwanaki da yawa a bisa teku rannan sai ya hadu da wani kyakkyawan saurayi yana taka ruwa yana tafiya, kamar yadda shi ma yake takawa. Da suka hadu da juna suka gaisa, amma babu wanda ya tsaya jin labarin dan uwansa sai kowa ya kama gabansa. Bayan Bulukiya ya rabu da saurayin nan sai ya hangi wasu halittu guda hudu manya-manya, kowane daya ya fi giwa girma, daga nesa, sun tinkaro inda yake suna tafiya kamar walkiya. Da suka zo kusa gare shi sai suka tsaya. Ya yi gaisuwa gare su, sa'annan ya ce, "ina gama ku da Allah Mai Girma da daukaka, ku gaya mini labarinku, ina kuka nufa cikin hanzari haka? Suka ce masa mu bayin Ubangiji ne, Allah ya umurce mu da mu tafi zuwa ga Gabas domin kamo wani babban maciji wanda ya rushe birane ya darkake mutanen da ke cikinsu. Allah ya umurce mu da mu kashe wannan majici domin mutane su huta da zaluncinsa." Bulukiya ya yi mamaki da irin girman siffarsu, ya ci gaba da tafiya ba dare ba rana har ya iso ga wani tsibiri. Ya shiga tsibirin yana yawo a cikinsa. Bulukiya ya shiga cikin tsibiri yana yawo, sai ya tarar da wani saurayi kyakkyawa, fuskarsa tana sheki, hawaye na tarara daga idanunsa. Yana

Chapter 3 of 4