Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
yadda ta yi masa aure har zuwa lokacin da ta saya masa jaki ya rik'a bin masu saran itace. Sannan ya ba ta labarin yadda saukar ruwa ya tilasta musu shiga kogo domin su fake, a nan kuma ya rik'a buga gatarinsa har ya ci karo da rijiyar zuma. Da yadda 'yan uwansa suka tafi suka bar shi da yadda kunama ta fad'o masa ya gane wurin da ta fito har ya yi babban rami ya fita zuwa inda ya ga k'ofa ya shiga zuwa wannan fadar. Har zuwa inda ya gamu da sarauniyar macizai. Daga nan ya ce mata, "wannan shi ne labarina daga farko har zuwa yanzun nan da nake magana da ke, Allah shi ne kuma ya san abin da zai faru da ni nan gaba." Sarauniyar macizai ta ce, "kwantar da hankalinka, babu abin da zai same ka sai alheri." ZAMUCI GABA03 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI bayan Hasib ya gama ba wa sarauniyar macizai labarinsa sai ta ce da shi, "babu abin da zai same ka sai alheri, amma ina so ya zauna nan na ba ka tarihina gami da labarai masu ban al'ajabi wad'anda suka faru da ni." Hasib ya ce, "na ji na amince." Sarauniyar macizai ta soma ba shi labari kamar haka: LABARIN BULUKIYA Ka sani ya Hasib akwai wani Sarki a birnin Misra cikin Bani Isra'ila, ya kasance malami ne mai tsoron Allah da gudun duniya wanda ya karanta littattafai ma su yawa, yana d'a namiji ana kiransa Bulukiya. Yayin da tsufa ya zo masa ya raunana, jikinsa ya mik'a wuya zuwa ga mutuwa sai ya tattara manyan fadarsa gaba d'aya, suka gaishe shi alhali yana kan gado yana jinya. Ya ce da su, "babu wata wasiyyar da zan muku face a kan d'ana Bulukiya, ku kula da shi bayan na mutu. " Daga nan ya yi kalmar shahada ya mutu. Allah ya ji k'an sa da rahma. Bayan mutuwarsa aka yi ta koke - koken al'ada sannan aka shirya shi aka bisne. Daga nan aka zab'i Bulukiya ya zama magajinsa. Ya rik'a mulkin mutane da adalci da mutuntawa ya zamana kowa yana son sa. Wata rana sai ya shiga taskar mahaifinsa domin ya ga abin da ta k'unsa ya ci karo da wata k'aramar k'ofa ya shiga sai ya ga wani d'an d'aki ya bud'e sai ya ga ashe k'aramar taska ce da ginshik'i a cikin na farin ruhham. A k'asa kuma akwai wani akwati na zinariya. Bulukiya ya d'auko akwatin ya bud'e shi sai ya tarar da takardu a ciki masu yawa tamkar girman littafi. Ya bud'e su ya shiga karantawa, ya ga a ciki an yi bayani siffofi da halaye da d'abi'un Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ya ga an rubuta cewa za a aiko shi a k'arshen zamani, amma shi ne shugaban farko da na k'arshe ga dukkan annabawa da manzanni. Yayin da Bulukiya ya k'are karatun takardun, ya fahimci siffofin Annabinmu Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ya ji k'aunarsa ta shiga ransa, ya tara manyan fadarsa da sauran masu fad'a a ji cikin Bani Isra'ila da malamansu da Ruhubaniyawa da bokayensu duka ya nuna musu wannan littafi, ya bayyana musu abin da ya k'unsa. Ya karanto musu wani b'angare daga cikinsa sannan ya ce, "ya ku jama'ata, ni ina nufin zan fito da ubana daga kabari na k'one gawarsa." Suka ce, "don me za ka aikata haka?" Ya ce, "saboda ya samu wannan littafi da jimawa amma ya b'oye mana shi bai bayyana mana ba. Ya samo shi daga littattafan da aka saukar wa Annabi Ibrahima da wasu bayanan daga Attaura, amma ya saka shi cikin taska ya b'oye bai nunawa kowa ba." Suka ce, "ya Sarki, ka sani mahaifinka ya riga ya bar duniya, gawarsa na cikin rami kuma da sannu za ta zama k'ura lamarinsa na wurin Ubangijinsa. Kada ka fito da shi daga kabarinsa." Da ya ji haka sai ya k'yale maganar fito da gawar mahaifinsa ya tafi wurin mahaifiyarsa ya ce, "uwata kin ga abin da na samu a taskar mahaifina, littafin da ke bayani kan siffofi da halayyar Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda zai zo a k'arshen zamani, na ji zuciyata ta tafi ga begensa. Na k'udurce a raina zan tafi yawo a doron k'asa ko Allah zai sa na sadu da shi, idan ba haka ba kuwa zan iya mutuwa saboda k'aunarsa da nake yi." Ya cire tufafin sarautarsa ya saka rigar fatar akuya da takalman fata ya ce da mahaifiyarsa, "ya uwata kada ki manta da ni a addu'oinki." Ta yi kuka mai yawa ta ce da shi, "me zai same mu bayan baka nan?" Bulukiya ya ce, "ba zan iya hak'uri ba sai na tafi, na mik'a al'amarina da naku ga Allah mad'aukakin Sarki." Daga nan ya fita a k'asa zuwa yankin Sham ba tare da sanin mutanensa ba. Ya tafi har zuwa gab'ar kogi ya shiga suka tafi zuwa wani tsibiri suka sauka gaba d'ayansu domin su huta. Bulukiya ya tafi k'ark'ashin wata bishiya ya d'an kishingid'a, babu jimawa barci ya kwashe shi saboda gajiya da ya yi. Yayin da ya farka ya tashi zuwa inda jirgin yake sai bai ga komai ba, jirgin ya tafi. Yana tsaye yana jimamin abin da ya same shi sai ya rik'a ganin macizai manya - manya, wasu girmansu kamar na rak'umi wasu suna da tsawo kamar bishiyar dabino, ya yi ta maimaita ambaton sunayen Allah yana neman tsari. Sai ya ji su ma suna hailala da tasbihi gami da salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhamamdu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ya ji suna ambaton sunayen Allah mad'aukakin Sarki. Bulukiya ya cika da mamaki bisa ga wannan. Yayin da suka gan shi sai suka kewaye shi suka ce da shi, "kai wanene? Daga ina kake, kuma ina za ka je?" Ya ce musu, "ni sunana Bulukiya daga Bani Isra'ila nake, na fito domin k'aunar saduwa da fiyayyen halitta Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata gare shi. Amma ku su waye, ya kuka kasance halitta mai ban mamaki haka?" Suka ce, "muna daga halitttun cikin wutar jahannama, Allah ya halicce mu domin mu rik'a d'and'anawa kafirai azaba." "Ta yaya kuka zo wannan wuri?" Suka ce, "ka sani ya Bulukiya cewa wuta ta tafarfasa, tafasa mai yawa, saboda tsananin zafin da ta yi sai ta rok'i Allah da samun sassauci. Allah ya nufe ta da yin numfashi sau biyu a shekara. Takan shak'i iska a lokacin hunturu ta fesar a lokacin bazara, wannan dalilin ne ya sa ake samun hunturu yake da sanyi, bazara kuma zafi. To duk lokacin da ta saki numfashinta sai ta watso irinmu waje. Yayin da ta natsu kuma za ta shak'i iska sai ta ja mu zuwa cikinta." Bulukiya ya ce da su, "shin akwai macizan da suke fi ku girma kuwa a jahannama kuwa?" Suka ce, "ka sani mu ba ta fito da mu nan ba face saboda k'ank'antar mu, akwai a cikinta macijiyar da idan babbar mu a nan za ta yi tafiya ta kafar hancinta ba za ta sani ba." Bulukiya ya ce da su, "na ji kuna ambaton Allah tare da ambaton sunan Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Ta yaya kuka samu labarinsa?" Suka ce, "ka sani ya Bulukiya, cewa wannan suna an rubuta shi a k'ofofin aljanna. Allah bai halicci duniya ba wala wuta, wala aljanna sai domin darajarsa. Haka nan sama da k'asa da abin da ke tsakaninsu duka domin alfarmarsa aka samar da su. Sannan Allah ya had'a sunansa da nasa a wurare da dama, don haka muke son Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi." Da Bulukiya ya ji sai begensa ga Annabi Muhammadu ya k'aru, ransa ya ratayu ga son saduwa da shi. Daga nan ya yi bankwana da wad'annan macizai ya tafi zuwa gab'ar kogi ya samu jirgi ya shiga. Suka yi ta tafiya har suka isa wani tsibiri suka sauka suka shiga ciki. A nan suka ga macizai manya da k'anana, babu wanda ya san adadin yawansu sai Allah. Daga cikinsu akwai wata macijiya fara mai hasken jiki fiye da buluri, tana zaune a kan wani faifan zinariya wanda yake bayan wani maciji babba kamar giwa. To ita wannan macijiyar ya Hasib ita ce sarauniyar macizai watau ni da nake magana da kai a yanzu." Hasib ya ce, "fad'a min yaya kuka yi da Bulukiya." Sarauniyar macizai ta ce, "ka sani ya Hasib, yayin da na gan shi sai na yi masa sallama ya amsa min, na ce da shi, "fad'a min wanene kai, me ya kawo ka nan wurin kuma ina ka nufa?" Ya ce, "sunana Bulukiya, ina daga Bani Isra'ila kuma na fito domin mararin saduwa da Annabi Muhammadu wanda aka siffanta kamanninsa a littattafai, shi na fito ina nema. Ke kuma wacece, me wad'annan macizan suke miki?" Na ce, "ya Bulukiya ni ce sarauniyar macizai , idan ka sadu da Annabi Muhammadu ka isar min da gaisuwa gare shi." Daga nan Bulukiya ya yi min bankwana ya tafi har ya isa ga birnin Baital Muk'addis. To a cikin birnin nan akwai wani masani wanda ya karanta littattafai da yawa, yana da d'imbin sani na daga lissafi da magani da sauran fannoni na daga ilmin taurari da hirji. Haka nan ya karanta attaura da zabura da littattafan da aka saukar wa Annabi Ibrahim. Ana kiransa Affanu. A cikin karance - karancensa ya karanta a wani littafi cewa duk wanda ya sanya zoben Annabi Sulaimanu, to dukkan mutane da aljanu da tsuntsaye da dabbobin gida da na daji da dukkan abin halitta za su yi masa biyayya. Haka nan ya gano cewa an binne Sulaimanu a cikin wani akwati wanda aka d'auke shi zuwa wani gida a can bayan koguna bakwai aka binne a can. Zoben kuma na hannunsa babu mai ikon cire shi daga gare shi, walau mutum ko aljani, domin kuma jirgin da zai iya ratsa koguna bakwai shi kad'ai ko gayya ne. Affanu ya karanta a littattatafai cewa mutum ko aljan babu mai ikon cire zoben nan daga hannun Sulaimanu, sannan babu jirgin da zai iya ratsa kogunan nan ya je wurin da aka binne shi. Haka kuma ya karanta cewa akwai wata itaciya daga itatuwa idan mutum ya samu wani abu daga jikinta ya nannaga ya matse ruwan sannan ya matsi man da ke jikinta ya gama ya shafa a k'afafunsa, to zai iya ratsa dukkan kogunan da Allah ya halitta a duniya tamkar yadda yake tafiya a k'asa ba tare da ya jik'e ba. Sai dai ita wannan bishiyar ba a iya sanin ta sai mutum na tare da sarauniyar macizai. Yayin da Bulukiya ya isa Baitil Muk'addis ya samu wani waje ya zauna yana ibada. Sai Affan ya zo gare shi ya yi masa sallama suka gaisa. Affanu ya ga Bulukiya yana karanta wani abu daga Attaura yana addu'a sai ya ce masa, "ka fad'a min kai daga ina kake kuma ina za ka? Ya ce, 'Ni sunana Bulukiya, kuma na fito daga Misra za ni neman Muhammadu mai tsira da abincin Allah su tabbata a gare shi." Affan ya ce, "ka zo mu je gidana domin na sauke ka ka zama bak'ona." Bulukiya ya ce, "na ji na amince." Suka tafi zuwa gidansa suka ci abinci sannan suka shiga tattaunawa. Affanu ya ce, "ka ba ni labarin inda ka samu labarin Ma'aikin Allah Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi." Bulukiya ya kwashe labarinsa kaf daga farko har karshe har gamuwarsa macizai duk ya fad'a masa. Affan ya ji kamar hankalinsa ya fita daga jikinsa don murna da ganin wanda ya san inda sarauniyar macizai take. Ya ce da shi ka kai ni inda sarauniyar macizai take ni kuwa na yi maka yadda za ka sadu da Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ka sani bayyanarsa lokaci ne mai nisa daga yanzu. Amma idan muka yi sa'ar kama sarauniyar macizai muka sa ta a tarko za mu zagaya da ita tsakanin itatuwan da suke cikin duwatsu. To matuk'ar tana tare da mu duk bishiyar da muka wuce ta gabanta za ta fad'a mana irin amfanin da ake yi da ita na daga magani cikin ikon Allah. Idan muka samu bishiyar da ke da wannan amfani sai mu matse ruwan jijiyar ta mu shafa a k'afafunmu za mu iya tafiya bisa doron kogunan da Allah ya halitta ba tare da mun jik'e ba. Idan mun samu bishiyar sai mu dawo da ita inda muka d'auke ta, mu kuma mu shafa ruwan a k'afafunmu mu ratsa koguna bakwai har mu isa inda aka binne shugabanmu Sulaimanu d'an Dawuda. Daga nan sai mu cire zoben daga hannunsa mu mallaki duniya gaba d'aya kamar yadda Sulaimanu ya yi, mu samu cimma burinmu. Bayan haka sai mu ratsa kogin duhu mu sha ruwan rayuwa, ka ga sai mu yi tsawon rai har zuwa bayyanar Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi." Da Bulukiya ya ji haka sai ya ce, "ya Affanu zan kai ka inda sarauniyar macizai take." Affanu ya shirya tarkon bak'in k'arfe ya sa kasake biyu a ciki. D'aya ya cika shi da madara d'ayan kuma ya cika shi da giya, suka d'auka suka tafi kwana da kwanaki, ranaku da darare har suka zo tsibirin da Sarauniyar macizai take ciki suka ajiye tarkon bakinsa a bud'e ya saka abin rud'i na daga madara da na giya, suka b'uya. Bayan wani lokaci sai ga sarauniyar macizai ta ji k'amshin madara, sai ta sauko daga kan faifanta ta shiga ta sha madara ta ishe ta, sannan ta juya giya ita ma ta sha ta k'oshi. Daga nan sai kanta ya juye ta kwanta barci a nan. Su Affan na ganin haka suka yi hanzari suka d'auke ta. Yayin da ta farka sai ta ganta a cikin d'akin bak'in k'arfe bisa kan wani mutum, gefensa kuma Bulukiya ne suna tafiya. Ta ce da Bulukiya, "yanzu wannan shi ne sakamakon wanda ba ya cutar da bil adama?" ZAMUCI GABA GOBE INSHA ALLAH04 HIKAYAR SARAUNIYA MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI Bulukiya ya ce, "ka da ki ji tsoron komai daga gare mu, mun d'auko ki ne domin mu wuce da ke ta gaban itatuwa za su rik'a fad'in amfaninsu da kansu. Muna son sanin bishiyar da ake shafa ruwanta a k'afafu a shiga kogi a yi tafiya ba tare an jik'e ba. Idan mun samu wannan za mu dawo da ke wurinki ba tare da cutarwa ba." Affanu da Bulukiya suka hau bisa duwatsu suka yi ta ratsa tsakanin itatuwa suna yin magana suna furta irin amfaninsu cikin ikon Allah. Bayan sun wuce itatuwa da yawa suna ta fad'in amfaninsu a hagu da dama can sai wata itaciya ta ce, "ni ce itaciyar da duk wanda ya rik'e ni ya dandak'a ya matse ruwan ya shafa a k'afafunsa, to zai tsallake duk wani kogi da Allah ya halitta ba tare da ya jik'e ba." Da Affanu ya ji haka sai ya sauke sarauniyar macizai ya rik'i abin da zai ishe su daga itaciyar ya nannaga ya d'ebe ruwan cikin battoci biyu saboda gaba. Daga nan suka juyo suka mayar da sarauniyar macizai inda suka d'auke ta. Bayan ta samu kanta sai ta ce da su, "me za ku yi da wannan ruwan haka?" Suka fad'a mata aniyar su. Da ta ji daga bakinsu sai ta ce, "ni sarauniyar macizai ina sanar da ku cewa ba za ku tab'a samun cire zoben nan ba har abada!" Suka ce, "don me kika ce haka?" Ta ce, "Allah mad'aukakin Sarki ya ba wa Annabi Sulaimanu zoben nan bisa baiwar da ya yi masa albarkacin addu'ar da ya yi cewa 'Ubangijina, ka ba ni mulki da sarauta wadda ba kamar ta ga wani bayan ni. Hak'ik'a kai ne mai baiwa.' Don haka wannan zoben ya fi k'arfinku, ba naku ba ne." Sannan ta k'ara da cewa, "ina ma a ce ku biyun nan itaciyar da idan aka ci ta ba a mutuwa kuka ci ai da ba haka ba. Idan mutum ya ci itaciyar to ba zai mutu ba har san an busa k'ahon farko. Kuma ita wannan itaciyar tana nan wurin da kuka je." Da suka ji haka sai suka yi bak'in ciki da nadama mai yawa. Daga nan babu yadda za su yi suka wuce zuwa aiwatar da aikinsu. yayin da Affanu da Bulukiya suka ji zancen sarauniyar macizai, sai suka yi bak'in ciki da nadama mai yawa. Daga nan babu yadda za su yi suka wuce zuwa aiwatar da aikinsu. Wannan kenan game da lamarinsu. Ni kuwa da na samu kaina sai na tafi wajen mutanena, na same su sun raunana suna halin jimami da firgici. Masu k'arfinsu sun zama raunana, raunanansu sun mutu, wasu sun jikkata, sun kasa motsi. Yayin da suka gan ni sai suka taso gaba d'aya suka yo kaina cikin farin ciki suka ce da ni, "me ya same ki?" Na fad'a musu abin da ya faru, daga nan na had'a kan rundunata na jagorance su zuwa dutsen kaf inda nake zama a lokacin d'ari, da bazara kuma ina hutawa a wannan wurin da ka gan ni. Ta dube shi ta ce da to Hasib Karimuddini wannan shi ne labarina da abin da ya auku gare ni." Hasib ya cika da mamaki mai yawa sannan ya ce da ita, "ni dai ina rok'on alfarmarki da ki sa d'aya daga hadimanki ya fitar da ni zuwa doron k'asa domin na koma wajen mutanena." Ta ce, "ya Hasib ba za ka bar mu ba sai lokacin d'ari za mu tafi da kai zuwa dutsen Kaf ka yi kallo a can ka shak'i iska mai dad'i, ka ga tuddai da rairayi da itatuwa da tsuntsaye manya - manya suna tsarkake sunan Allah mai girma. Kuma ka ga Maridai da Ifritai da Aljannu wad'anda babu wanda ya san adadin yawansu sai Allah." Yayin da Hasib ya ji haka sai ya fashe da kuka mai tsanani. Bayan ya natsu ya ce da ita, "fad'a min game da Affan da Bulukiya yayin da suka bar ki suka tafi, yalla sun samu tsallake koguna bakwan, sun isa inda suke son zuwa, sun yi nasarar d'auko zoben?" Ta ce, "yayin da suka bar ni, suka shafe k'afafunsu da ruwan nan suka shiga kogi suna tafiya da k'afafunsu kuma ba su nutse ba, ba su jik'e ba. Abin gwanin ban sha'awa da mamaki. Suna ta kallon ikon Allah na game da girman kogunan da zurfinsu har suka kai kogi na bakwai sai suka hangi wani tsauni mai girma wanda ya tokare sararin sama, duwatsunsa na zubarjadi ne, k'asar wurin ta miski ce, daga k'ark'ashinsa ruwa ne ke gudana. Yayin da suka ga wurin sai suka cika da farin ciki suna cewa, "mun samu cikar burinmu." Suka kama hawan tsauni har suka ga wani kwararo a ciki suka shiga cikin tsaunin suka yi ta tafiya har suka ga wani haske na fitowa daga wata k'ubba. Suka shiga cikin k'ubbar a nan suka ga wani gadon zinariya an yi masa ado daga dukkan nau'in jauhari, a gaba gare ta kuma kujeri ne reras bilahaddin. Suka ga Annabi Sulaimanu kwance a bisa gadon tamkar yana barci. Yana sanye da riga ta d'anyen alharini, an yi masa zane da zinariya sannan an daje shi da zab'ab'b'en lu'ulu'u da jauhari. Ya d'ora hannunsa na dama akan k'irjinsa, zoben na cikin yatsansa. Hasken zoben ya rinjayi dukkan hasken abubuwan da ke wajen. Affanu ya koya wa Bulukiya wasu addu'o'i da d'alamisai ya ce ya yi ta karantawa kada ya daina har sai ya d'auko zoben. Bulukiya ya yi ta maimaita kalmomin yayin da Affanu ya matsa kusa da gadon yana karanta addu'oi. Ya taka matakala kenan sai wata babbar macijiya ta bayyana gabansa, ta yi gunji gami da kururuwa har sai da wajen ya rik'a raurawa. Tartsatsin wuta ya rik'a fita daga bakinta ta ce, "koma da baya ko ka mutu!" Bai saurare ta ba ya ci gaba da karance - karancensa yana matsawa zuwa ga zoben. Ta huro masa wata dunk'ulalliyar wuta gabansa ta ce, "kaitonka! Koma da baya ko na k'one ka!" Da Bulukiya ya ji haka sai ya razana ya fita daga wajen, shi kuwa Affanu ya ci gaba da matsawa gaba yana addu'a. Ya matsa kusa da shugaba Sulaimanu ya sa hannunsa kan zoben, sai dabbar da ke kusa da gadon ta yi kuka, macijiyar nan ta feso masa wuta ta k'one shi nan take ya zama toka. Wannan kenan game da Affanu. Amma Bulukiya kuwa da ya ga haka sai ya gigice ya fad'i k'asa sumamme. ZAMU CI GABA05 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI sarauniyar macizai ta ci gaba da ba wa Hasib labari, "yayin da Bulukiya ya ga wutar da ta k'one Affa nu ya zama toka sai ya gigice ya fad'i k'asa sumamme. Macijiyar kuma ta haw o zuwa inda yake domin shi ma ta gama da shi. Allah ya aiko wani mala'ika y a d'auke shi, ya kub'utar da shi sannan ya tashe shi ya yi masa sallama ya ce, "ta yaya ka zo wannan wurin?" Bulukiya wanda a tsammaninsa da d'an Adam yake magana ya ba shi labarinsa, sannan ya k'ara da cewa, "na zo nan a bur ina na saduwa da Annabi Muhammadu mai tsira da amincin Allah su tabbata gar e shi, Affanu ya shaida min cewa sai a k'arshen duniya zai bayyana don haka muka zo da nufin samun yadda za mu sha ruwan rayuwa ta zoben shugaba Sulai manu, hakan zai sa mu tabbata a k'arshen zamani lokacin da zai bayyana." Ya ci gaba da cewa, "ga shi yanzu mun zo wajen shi kuma Affanu ya rasa ransa. Ni kam yanzu burina shi ne ka fad'a min ta yaya zan sadu da manzon tsira M uhammadu?" Mala'ikan ya ce masa, "ka dangana ka koma gida, cewa ba zai bayy ana ba sai a k'arshen zamani." Daga nan ya bar shi ya koma zuwa sama. Bulukiya ya zauna yana kuka mai tsanani yana tuba bisa ga zunubansa yana na dama. Daga nan ya tuna gargad'in da na yi musu na cewa d'an Adam bai isa ma llakar zoben nan ba har abada. Ya gangaro da tsaunin cikin damuwa ya tafa g ab'ar kogi ya kwanta yana ta mamakin tsaunuka da tsibirin da ke kewaye da s hi. Da gari ya waye ya shafa ruwan bishiyar nan ya shiga cikin kogin yana t a tafiya dare da rana har ya zo wani tsibiri mai cike da 'ya'yan itatuwa ta mkar aljanna domin kyawo. Ya sauka a cikinta ya ga tana k'unshe da abubuwan al'ajabi da yawa. K'asar wajen ta yak'utu ce, duwatsun na zubarjadi sannan akwai wad'anda suke dangin murjani da ambar, rairayinta na k'amshin yasimi , ganyayenta na haske da k'amshi, bishiyoyinta na turaren wuta ne sandal ma i haske. 'Ya'yan bishiyun gwanin zak'i kowannen su tamkar ya fi d'an uwansa zak'ak'awa. Akwai furanni bilahaddin masu mabambamtan launi da k'amshi.. Is kar wajen na bugawa gwanin sanyi mai sanyaya zuciya. A tak'aice dai wannan tsibiri ya had'a dukkan abin da ake buk'ata na kyawo da ban sha'awa. Ga kum a tsuntsaye suna wak'ok'i da murya gwanin dad'i wadda za ta sa mutum ya dul miya duniyar bege da nishad'i. Gefe d'aya kuma bareyi na tsalle - tsalle su na kiwo, ga dabbobin daji dangin su b'auna da gada suna kai wa da komowa a sararinta. Bishiyoyinta dogaye ne, daga can jikin wani tsauni kuma ruwa ne ke gangarowa zuwa wata k'orama mai haske da dad'in sha da dad'in gani. Bulu kiya ya tsaya yana mamakin wannan tsibiri da bai ga tamkarsa ba tun da ya f ito. A nan ya fahimci ya kuskure hanyar da suka biyo shi da Affanu. Ya zaga ya cikin tsibirin ya yi kallo ya kashe kwarkwatar idanunsa har zuwa dare sa nnan ya hau wata bishiya ya kwanta barci. Tun barcin bai yi nisa ba ya ji w ata k'ara mai ban firgici da wani irin motsi daga cikin kogin. Can jimawa s ai wata babbar halitta ta fito daga ciki tana gurnani da huci. Bulukiya ya tsorata da ganin ta har ya kusa fad'owa daga kan bishiyar. Ya rik'a mamaki n irin girmanta. Babu jimawa sai ga wasu halittun suna fitowa daga cikin ruwan, kowanne na d 'auke da jauhari yana haske, har sai da tsibirin ya haskake saboda yawan ja uharin. Bayan haka sai ga dabbobin daji suna tattaruwa a wajen, sun had'a d a dukkan namun daji na daga zaki da damisa da kura da giwaye babu wanda ya sa adadinsu sai Allah. Suka yi ta hira da junansu har zuwa asuba sannan kow anne ya kama hanya zuwa ga halin tafarkinsa. Da Bulukiya ya ga haka sai ya tsorata ya shafawa k'afarsa ruwan nan ya shiga kogi na biyu. Ya yi ta tafi ya dare da rana har ya isa k'arshen kogin zuwa wani tsibiri inda ya shiga y a sadu da wani dutse mai girma da wani kwari a cikin dutsen wanda ba shi da iyaka duka duwatsunsa maganisu ne kuma dabbobinsa duka zakoki ne da zomaye da damisu. Bulukiya ya hau bisa ga wannan dutsen ya yi ta tafiya har zuwa maraice ya zauna k'ark'ashin wani kogon dutse a gefen kogi ya rik'a tsintar busassun kifaye da ruwa ya turo gefe yana ci. Yana cikin wannan halin ya w aiwaya kenan sai ya ga wata babbar damisa mai girman gaske tana sand'a domi n ta taushe shi. Ya firgita da ganin haka, cikin hanzari ya shafawa k'afars a ruwa ya fad'a kogi na uku ya tafi cikin dare. Daren kuwa ya kasance mai d uhu iska na kad'awa, igiyar ruwa na murd'awa. A haka har ya isa wani tsibir in ya sauka ya ga 'ya'yan itace na daga kayan marmari d'anyu da nunannu da busassu. Ya d'ebi daidai gwargwadon da yake buk'ata ya ci ya k'oshi ya gode wa Allah. Ya zagaya cikin ta yana yawo, ya yi ta zagayawa har dare ya yi. Bulukiya ya yi ta yawo cikin tsibirin nan har dare ya yi sannan ya samu wuri ya kwanta.. Da gari ya waye ya ci gaba da zagaya tsibirin yana kallo idan ya gaji ya zaun a ya huta har kwanaki goma. Daga nan ya shafa ruwa a k'afarsa ya shiga kogi na hud'u. Yayi ta tafiya a cikinsa dare da rana har ya iso wani tsibirin, ya ga k'asar wurin tattausa ce fara, babu komai a cikinta na daga itace ba llantana shuka ko tsuntsaye. Ya huta a cikinta sa'a guda sannan ya tashi y a shiga kogi na biyar ya yi ta tafiya ba dare ba rana har ya isa wani tsibi rin mai k'unshe da duwatsu masu haske kamar k'ank'ara. Daga duwatsun akwai irin wad'anda ake samun zinariya a ciki da wad'anda ake gyara su a yi zinariya da su. Ya ga a ciki wasu irin itatuwa masu ban mam aki wad'anda bai tab'a ganin tamkarsu ba a baya, furensu tamkar zinariya, ' ya'yansu tamkar lu'ulu'u. Ya shiga cikin tsibirin ya zagaya yawo har lokaci n da dare ya yi, sai ya ga furannin nan na haskakawa kamar taurari. Ganin h aka ya yi mamaki sosai ya ce a ransa, 'ko furannin nan suna daga wad'anda k e fad'owa daga rana zuwa duniya sai iska ta kad'a su zuwa

Chapter 2 of 4