Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 01 HIK’AYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI A zamani mai tsawo da ya shud’e, an yi wani malami mai hukunci daga cikin mahukuntan Yunana ana kiransa Daniyala. Ya kasance a k’ark’ashinsa akwai d’alibai da mabiya wad’anda ke masa biyayya ga umarninsa suna hanuwa da haninsa, sun dogara gaba d’aya a kan ilminsa da fatawarsa. To amma duk da d’imbi ilmin wannan malami ya kasance bai tab’a haihuwa ba. A wani dare ya kwanta yana tunanin halin da yake ciki na rashin magaji, hankalinsa ya tashi ya rasa inda zai sa kan sa. Sai ya tuna Ubangiji mad’aukakin Sarki yana amsa addu’ar bayinsa ba tare da shamaki ba. Yana azurta wanda ya so a lokacin da ya so da abin da ya so. Ba ya maida wanda ya koma gare shi mawofinci ga biyan buk’ata. Yana alheri ga mai biyayya gare shi, yana yin baiwa ga wanda ya so. Ya mik’e tsaye ya yi sallah sannan ya yi addu’a. Bayan ya shafa ya kama hannun matarsa ya sadu da ita, a wannan daren kuwa ta samu ciki. A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse zancenta mai dad'in saurare. DARE NA 483 A dare na d'ari hud’u da tamanin da uku, Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai wannan hamshak’in Sarki, malamin nan ya sadu da matarsa, a wannan daren ta samu ciki. Bayan wasu kwanaki sai tafiya ta kama shi cikin jirgin ruwa. A tsakiyar ruwa jirgin ya wargaje dukkan littattafansa suka dulmuye cikinsa, ya tsira da kyar ta hanyar kama wani allon jirgin. Ya zamana babu abin da ya saura gare shi na daga littattafai sai ‘yan takardu guda biyar. Yayin da ya dawo gida sai ya zuba takardun a cikin wani akwati ya kulle ya dank’a wa matarsa mukullan wadda cikinta ya soma girma ya ce da ita, “ki sani mutuwata ta kusa domin ciwon da ke jikina yana yawaita. Na kusata da barin wannan rayuwar zuwa gidan tabbata. Watak’ila ki haifi namiji daga cikin nan naki. Idan kin haife shi ki rad’a masa suna Hasib Karimuddini, ki raine shi da mafi kyawun raino. Idan yaron ya girma ya tambaye ki gadon da mahaifinsa ya bar masa ki nuna masa wad’annan takardu guda biyar. Idan ya karanta zai fahimci abin da suka k’unsa zai zama babban malamin zamaninsa.” Daga nan ya yi mata bankwana ya ja dogon numfashi ransa ya fita. Allah ya jik’ansa. Iyalinsa da danginsa da dukkan mutanensa suka yi ta kuka sannan suka yi masa wanka suka shigar da gawar cikin likkafani sannan suka yi masa sallah suka bisne shi. Bayan sun yi addu’oi kamar yadda aka saba sai kowa ya tafi ya zuwa sha’anin gabansa. Bayan kwanaki kad’an da mutuwarsa sai matarsa ta haifi wani yaro namiji kyakkyawa aka rad’a masa suna Hasib Karimuddini kamar yadda mahaifinsa ya ba da wasiyya. Bayan suna suka kirawo malamai masana ilmin taurari domin su duba game da sha’anin wannan yaro. Da suka k’are bincikensu sai suka ce da ita, “ki sani ya wannan matar, cewa d’anki zai yi rayu shekaru masu yawa amma wani al’amari zai faru gare shi a farkon rayuwarsa, zai sha wahala kuma zai ga abin mamaki. Amma idan ya kub’uta daga nan zai zama mai yawan ilmi na daga sha’anin duniya da na lahira.” Ta ci gaba da shayar da shi har ya shekara biyu sannan ta yaye shi. Yayin da ya shekara biyar ta shigar da shi makaranta ya soma koyon karatu da rubutu, amma sai ya kasance bai iya karatun komai ba, kuma bai koyi rubutu ba. Da ta ga haka sai ta cire shi daga makarantar ta kai shi wajen koyon sana’a, nan ma ya kasa koyon komai na daga aikin hannu. Uwar sai ta shiga halin damuwa da bak’in ciki, mutane suka ce da ita, “ki yi masa aure, watak’ila zai natsu ya aikata abin da ake so da shi na daga sana’a.” Ta tafi ta nemo masa auren wata yarinya a nan unguwarsu. Duk da an yi masa auren amma bai mai da hankali ga aikin komai ba, ga shi ya soma datawa domin ya kai shekara goma sha tara bai iya komai ba na daga karatu ko aiki. Uwar ce ke d’awainiyar ciyar da shi tare da matarsa. Wata rana wasu mak’wabtanta masu saro itace suka ce da ita, “ki sayo wa d’anki jaki da igiya da gatari ki had’a shi da mu mu rik’a zuwa daji muna saro itacen wuta muna sayarwa. Duk abin da muka samu sai mu rik’a rabawa tsakaninmu. Kin ga sai ku samu abin da za ku rik’a taimakon kanku.” Da ta ji haka sai ta cika da farin ciki ta gode musu sannan ta tafi ta sayo jaki da igiya da gatari ta had’a Hasib da su bisa amanar su kula da shi a dukkan inda suka shiga. Suka ce, “kada ki damu, Allah zai kiyaye shi da mu baki d’aya. Ko ba komai ai d’an malaminmu ne dole mu kula da shi.” Suka tafi da shi cikin daji bisa duwatsu inda itatuwa suka fi girma, suka sari daidai yadda za su iya, suka lafta wa jakunansu zuwa cikin gari suka sayar suka yi wa iyalinsu sayayyar kayan abinci. Washegari ma suka fita, a rana ta uku ma suka. Haka suka ta yi kullum suna zuwa suna sayarwa har wata rana bayan sun shiga dajin sai gari ya murtuke bak’ik’k’irin hadari ya gangamo ana cida da walk’iya da iska mai cike da k’ura. Bayan wani lokaci ruwa suka sauko mai k’arfi da guguwa. Nan da nan suka ruga wani kogo suka fake kafin ruwan ya k’are sauka. Hasib sai ya matsa daga ragowar abokan tafiya ya matsa can k’urya da gatarinsa yana bubbuga shi a k’asa. Sai ya ji k’asan yana amsawa kamar ana buga ganga, tamkar k’asan wajen akwai wani abu a ciki. Bai jima da fahimtar haka ba sai ya ji gatarinsa ya b’urma wajen. Ya sa hannu ya kwashe k’asar sai ya ga wani dutse ya d’auke shi sai ga wata k’ofa kamar an danne ta da wani zagayayyen bak’in k’arfe. Da ya ga haka sai ya cika da farin ciki, ya kirawo abokan aikinsa ya nuna musu. Zamuci gaba gobe insha Allah02 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI Yayin da Hasib ya d’auke dutsen sai ga wata k’ofa kamar an danne ta da wani zagayayyen bak’in k’arfe. Da ya ga haka sai ya cika da farin ciki, ya kirawo abokan aikinsa ya nuna musu, suka cire bak’in k’arfen sai suka ga wani d’an kururrumin rami cike da ruwan zuma. Da suka ga haka sai suka ce, “wannan zumar tana da yawan gaske, babu abin da ya fi sai mu koma cikin gari mu samo salkuna da tukwane mu kwashe ta gaba d’aya mu je mu sayar mu raba kud’in tsakaninmu. Amma d’aya daga cikinmu ya tsaya kula da wajen kada wasu su zo su kwashe mana alhali ba ma nan.” Hasib ya ce, “ni zan zauna kula da wurin har ku je ku dawo.” Suka tafi suka bar shi yana kula da wajen, bayan wasu lokuta suka dawo d’auke da salkuna da tukwane da mazubai masu yawa. Suka yi ta cika su suna laftawa jakunansu zuwa kasuwa. Washegari ma suka dawo suka d’iba, suka sake dawowa a karo na uku. Ba su gushe suna kai wa da komowa ba kwanaki masu yawa har sai da ya kasance sun kusan kwashe zumar nan, saura kad’an. Duk wad’annan kwanaki Hasib ne ke zama a wurin yana kula da shi dare da rana. A cikin gari kuwa sai suka rik’a magana da junansu suna cewa, “kun ga Hasib ne ya gano wannan zumar kuma shi ne yake kula da ita har ga shi yau za mu k’arasa kwashe ta zai dawo cikin gari tare da mu. Zai yi mana k’orafin tasa ce, mu kenan za mu tashi ba mu da komai ko kuwa rabonsa ya ninka namu.” Sai wani daga cikinsu ya ce, “idan kuwa haka ne babu makawa mu shirya masa kaidi yadda za mu bar shi a cikin ramin zumar. Yunwa da k’ishirwa ma sa kashe shi daga baya. Kun ga mun magance wannan matsalar kenan.” Suka amince da wannan shawara, suka tafi daji a kan haka. Da suka isa sai suka ce da shi, “shiga cikin rijiyar ka d’ebo mana abin da ya saura a ciki na daga zuma.” Ya shiga ya rik’a d’ebo musu zumar suna tarawa har sai da komai na ciki ya k’are. Ya ce musu, “ku fito da ni babu abin da ya rage yanzu.” Ba su kula da shi ba suka lafta wa jakunansu kaya suka tafi suka bar shi a ciki shi kad’ai. Ya zama yana neman taimako yana kuka babu wanda ya ji shi yana cewa, “lahaula wala k’uwwata illa billahi. Yau na gamu da wahala. Ya Allah ka fitar da ni!” Wannan kenan game da al’amarinsa. Amma game da abokan aikinsa kuwa, yayin da suka isa cikin gari suka sayar da zumar nan sannan suka tafi wajen mahaifiyar Hasib suna kuka suka ce da ita, “kaiton d’anki Hasib!” Ta ce, “me ya same shi?” Suka ce, “Allah ya yi masa cikawa, ya mutu a daji!” “Me ya kashe shi?” “Muna cikin saran itace a can saman tsauni sai iska ta taso ruwa mai k’arfi ya sauko muka shiga wani kogo domin mu fake. To ana cikin ruwan sai jakinsa ya kwance ya gudu cikin daji. Ya tashi ya bi shi domin ya dawo da shi, a dajin sai wani babban kerkeci ya taso ya buge shi ya kashe shi nan take. Kuma ya kashe jakin ya cinye shi.” Yayin da uwar ta ji zancen masu itace sai ta rik’a marin fuskarta tana kuka da jimami tana tula k’asa a kan ta. Ta tabbata cikin bak’in cikin rashinsa. Masu itace suka zama suna kawo mata abinci da abinsha da sutura. Wannan kenan game da al’amarin uwar Hasib. Masu itace kuwa suka sayar da zumar nan suka sayi rumfuna da jari suka zama attajirai suna saye da sayarwa, suka zama cikin farin ciki da nishad’i. Hasib kuwa ya zauna a rijiyar nan yana ta kuka gami da kiran neman taimako har ya gaji ya daina. Ya zauna a ciki ya rasa abin da ke masa dad'i. Can an jima sai wata kunama ta fad'o masa, ya mik'e da hanzari ya kashe ta. Sannan ya d'auke ta yana jujjuya ta yana mamaki, ya ce, "rijiyar nan na cike da zuma a baya, ta ina aka samu wannan kunamar?" Ya mik'e yana duba jikin garun rijiyar hagu da dama, kudu da arewa ya ga wani rami inda kunamar ta fito haske na fitowa daga gare shi. Ya fito da wuk'a da ke k'ugunsa ya rik'a rarake wurin har ya ga tamkar taga, ya cusa kansa ciki sai ya gan shi a wani sarari. Ya rik'a tafiya bai san inda ya nufa har ya zo wata farfajiya mai girma, ya shiga sai ya gan shi a wani babban zaure. Ya tafi zuwa ga wata k'ofa ta bak'in k'arfe tana da makulli na azurfa. Wannan mukullin ya kasance a jikinta mak'ale yana haske da kwad'on zinariya. Ya sa hannu ya bud'e ya shiga, ya yi ta tafiya sa'a guda sannan ya sadu da wani k'aramin tafki da aka gina domin ado. A nan ne ya ga wani abu na haskakawa tamkar ruwa. Bai gushe yana tafiya ba har ya sadu da wani tudu mai girma na d'anyen zubarjadi da wani dunk'ulen zinariya an masa tulluwa da kuma wani babban gado na zinariya an shafe shi daga dangin yak'utu da zubarjadi. da wani dunk'ulen zinariya an masa tulluwa da kuma wani babban gado na zinariya an shafe shi daga dangin yak'utu da zubarjadi, a gewaye da shi kujeru ne masu yawa, wasu na zinariya, wasu na azurfa, wasu na yak'utu, wad'ansu na d'anyen zubarjadi. Ya tsaya yana k'idaya su ya ga guda goma dubu sha biyu ne, ya ga wata babbar kujera a tsakiyarsu babu kowa, ya zauna a kai. Ya zama cikin mamaki da wad'annan gadaje da wannan tafkin da irin adon da aka yi musu. Bai gushe ba bisa haka har barci ya kwashe shi. Ya farka a firgice sakamakon wata k'ara da huci da wani irin motsi da ya ji na nufo shi, ya bud'e idanu ya zauna ya ga dukkan kujerun nan wasu manya - manyan macizai na zaune a kan su, girmansu ya kai k'afa d'ari. Tsoro ya kama shi da ganin wannan abin tsoro, yawun bakinsa ya bushe don tsananin tsoro. Ya d'ebe tsammanin rayuwa don tsoro, ya ga idon kowacce macijiya jajawur kamar garwashin wuta. Ya duba wannan k'aramin tafkin nan ya ga macizai k'anana babu wanda ya san adadinsu sai Allah, suna ta kai wa da komowa a ciki. Bayan jimawa wata macijiya kamar alfadara ta gabato zuwa gare shi, bisa bayan wannan macijiya akwai wani faifan zinariya. A cikin wannan faifan akwai wata 'yar k'aramar macijiya tana haske kamar lu'ulu'u. Fuskarta irin ta mutane ce, tana zance da fasaha da harshe mai dad'i. Yayin da ta gabato wurin Hasib Karimuddini ta yi masa sallama, ya mayar mata da sallamar. Daga nan d'aya daga macizan nan ya sauko daga kujerarsa ya kama faifan ya saukar da ita zuwa wata kujera da ta fi ragowar kyau. Ta yi kururuwa gaba d'aya macizan suka fad'i suna masu gaisuwa da irin yarensu. Macijiya ta yi musu alamar su zauna, suka koma suka zauna. Ta juya ga Hasib ta ce, "kada ka ji tsoronmu ya kai saurayi, ni ce sarauniyar macizai, kuma jagorarsu." Da Hasib ya ji haka sai zuciyarsa ta natsu ya zauna. Ta sa macizai su kawo masa wani abu da zai ci. Suka kawo masa tuffa da inibi da rumman da gyad'a da kuma ayaba suka ajiye a gabansa. Sarauniyar macizai ta ce da Hasib, "barka da zuwa ya saurayi, yaya sunanka?" Ya ce, "sunana Hasib Karimuddini." Ta ce, "ya Hasib zauna ka natsu ka ci wad'annan 'ya'yan itatuwa, domin ba mu da nama ko wani abu daban. Ci sosai kada ka ji tsoronmu." Da ya ji haka sai ya natsu sosai ya ci kayan marmarin nan har ya tumbatsa ya gode wa Allah. Daga nan aka d'auke farantan abincin daga gabansa. Sarauniya ta ce masa, "Hasib fad'a min yadda ka zo wurin nan da abin da ya faru gare ka ya yi sanadin zuwanka." Hasib ya gyara zama ya ba ta labarinsa tun daga kan mahaifinsa da yadda ya rasu kamar yadda mahaifiyarsa ta fad'a masa, da yadda aka sa shi makaranta yana shekara biyar ya zamana bai iya karatu da rubutun komai ba, da yadda ta kai shi wurin koyon sana'a bai iya ba, da yadda ta yi masa aure har zuwa lokacin da ta saya masa jaki ya rik'a bin masu saran itace. Sannan ya ba ta labarin yadda saukar ruwa ya tilasta musu shiga kogo domin su fake, a nan kuma ya rik'a buga gatarinsa har ya ci karo da rijiyar zuma. Da yadda 'yan uwansa suka tafi suka bar shi da yadda kunama ta fad'o masa ya gane wurin da ta fito har ya yi babban rami ya fita zuwa inda ya ga k'ofa ya shiga zuwa wannan fadar. Har zuwa inda ya gamu da sarauniyar macizai. Daga nan ya ce mata, "wannan shi ne labarina daga farko har zuwa yanzun nan da nake magana da ke, Allah shi ne kuma ya san abin da zai faru da ni nan gaba." Sarauniyar macizai ta ce, "kwantar da hankalinka, babu abin da zai same ka sai alheri." A nan sai Shaharzad, ta katse zancenta mai dad'in saurare.DARE DUBU DA DAYA (242) A nan asuba ta riski Shaharzad, ta katse zancenta mai dad'in saurare. DARE NA 484 A dare na d'ari hud’u da tamanin da hud’u, Shaharzad ta ce, na samu labari ya kai wannan hamshak’in Sarki, Yayin da Hasib ya d’auke dutsen sai ga wata k’ofa kamar an danne ta da wani zagayayyen bak’in k’arfe. Da ya ga haka sai ya cika da farin ciki, ya kirawo abokan aikinsa ya nuna musu, suka cire bak’in k’arfen sai suka ga wani d’an kururrumin rami cike da ruwan zuma. Da suka ga haka sai suka ce, “wannan zumar tana da yawan gaske, babu abin da ya fi sai mu koma cikin gari mu samo salkuna da tukwane mu kwashe ta gaba d’aya mu je mu sayar mu raba kud’in tsakaninmu. Amma d’aya daga cikinmu ya tsaya kula da wajen kada wasu su zo su kwashe mana alhali ba ma nan.” Hasib ya ce, “ni zan zauna kula da wurin har ku je ku dawo.” Suka tafi suka bar shi yana kula da wajen, bayan wasu lokuta suka dawo d’auke da salkuna da tukwane da mazubai masu yawa. Suka yi ta cika su suna laftawa jakunansu zuwa kasuwa. Washegari ma suka dawo suka d’iba, suka sake dawowa a karo na uku. Ba su gushe suna kai wa da komowa ba kwanaki masu yawa har sai da ya kasance sun kusan kwashe zumar nan, saura kad’an. Duk wad’annan kwanaki Hasib ne ke zama a wurin yana kula da shi dare da rana. A cikin gari kuwa sai suka rik’a magana da junansu suna cewa, “kun ga Hasib ne ya gano wannan zumar kuma shi ne yake kula da ita har ga shi yau za mu k’arasa kwashe ta zai dawo cikin gari tare da mu. Zai yi mana k’orafin tasa ce, mu kenan za mu tashi ba mu da komai ko kuwa rabonsa ya ninka namu.” Sai wani daga cikinsu ya ce, “idan kuwa haka ne babu makawa mu shirya masa kaidi yadda za mu bar shi a cikin ramin zumar. Yunwa da k’ishirwa ma sa kashe shi daga baya. Kun ga mun magance wannan matsalar kenan.” Suka amince da wannan shawara, suka tafi daji a kan haka. Da suka isa sai suka ce da shi, “shiga cikin rijiyar ka d’ebo mana abin da ya saura a ciki na daga zuma.” Ya shiga ya rik’a d’ebo musu zumar suna tarawa har sai da komai na ciki ya k’are. Ya ce musu, “ku fito da ni babu abin da ya rage yanzu.” Ba su kula da shi ba suka lafta wa jakunansu kaya suka tafi suka bar shi a ciki shi kad’ai. Ya zama yana neman taimako yana kuka babu wanda ya ji shi yana cewa, “lahaula wala k’uwwata illa billahi. Yau na gamu da wahala. Ya Allah ka fitar da ni!” Wannan kenan game da al’amarinsa. Amma game da abokan aikinsa kuwa, yayin da suka isa cikin gari suka sayar da zumar nan sannan suka tafi wajen mahaifiyar Hasib suna kuka suka ce da ita, “kaiton d’anki Hasib!” Ta ce, “me ya same shi?” Suka ce, “Allah ya yi masa cikawa, ya mutu a daji!” “Me ya kashe shi?” “Muna cikin saran itace a can saman tsauni sai iska ta taso ruwa mai k’arfi ya sauko muka shiga wani kogo domin mu fake. To ana cikin ruwan sai jakinsa ya kwance ya gudu cikin daji. Ya tashi ya bi shi domin ya dawo da shi, a dajin sai wani babban kerkeci ya taso ya buge shi ya kashe shi nan take. Kuma ya kashe jakin ya cinye shi.” Yayin da uwar ta ji zancen masu itace sai ta rik’a marin fuskarta tana kuka da jimami tana tula k’asa a kan ta. Ta tabbata cikin bak’in cikin rashinsa. Masu itace suka zama suna kawo mata abinci da abinsha da sutura. Wannan kenan game da al’amarin uwar Hasib. Masu itace kuwa suka sayar da zumar nan suka sayi rumfuna da jari suka zama attajirai suna saye da sayarwa, suka zama cikin farin ciki da nishad’i. Hasib kuwa ya zauna a rijiyar nan yana ta kuka gami da kiran neman taimako har ya gaji ya daina. Ya zauna a ciki ya rasa abin da ke masa dad'i. Can an jima sai wata kunama ta fad'o masa, ya mik'e da hanzari ya kashe ta. Sannan ya d'auke ta yana jujjuya ta yana mamaki, ya ce, "rijiyar nan na cike da zuma a baya, ta ina aka samu wannan kunamar?" Ya mik'e yana duba jikin garun rijiyar hagu da dama, kudu da arewa ya ga wani rami inda kunamar ta fito haske na fitowa daga gare shi. Ya fito da wuk'a da ke k'ugunsa ya rik'a rarake wurin har ya ga tamkar taga, ya cusa kansa ciki sai ya gan shi a wani sarari. Ya rik'a tafiya bai san inda ya nufa har ya zo wata farfajiya mai girma, ya shiga sai ya gan shi a wani babban zaure. Ya tafi zuwa ga wata k'ofa ta bak'in k'arfe tana da makulli na azurfa. Wannan mukullin ya kasance a jikinta mak'ale yana haske da kwad'on zinariya. Ya sa hannu ya bud'e ya shiga, ya yi ta tafiya sa'a guda sannan ya sadu da wani k'aramin tafki da aka gina domin ado. A nan ne ya ga wani abu na haskakawa tamkar ruwa. Bai gushe yana tafiya ba har ya sadu da wani tudu mai girma na d'anyen zubarjadi da wani dunk'ulen zinariya an masa tulluwa da kuma wani babban gado na zinariya an shafe shi daga dangin yak'utu da zubarjadi. da wani dunk'ulen zinariya an masa tulluwa da kuma wani babban gado na zinariya an shafe shi daga dangin yak'utu da zubarjadi, a gewaye da shi kujeru ne masu yawa, wasu na zinariya, wasu na azurfa, wasu na yak'utu, wad'ansu na d'anyen zubarjadi. Ya tsaya yana k'idaya su ya ga guda goma dubu sha biyu ne, ya ga wata babbar kujera a tsakiyarsu babu kowa, ya zauna a kai. Ya zama cikin mamaki da wad'annan gadaje da wannan tafkin da irin adon da aka yi musu. Bai gushe ba bisa haka har barci ya kwashe shi. Ya farka a firgice sakamakon wata k'ara da huci da wani irin motsi da ya ji na nufo shi, ya bud'e idanu ya zauna ya ga dukkan kujerun nan wasu manya - manyan macizai na zaune a kan su, girmansu ya kai k'afa d'ari. Tsoro ya kama shi da ganin wannan abin tsoro, yawun bakinsa ya bushe don tsananin tsoro. Ya d'ebe tsammanin rayuwa don tsoro, ya ga idon kowacce macijiya jajawur kamar garwashin wuta. Ya duba wannan k'aramin tafkin nan ya ga macizai k'anana babu wanda ya san adadinsu sai Allah, suna ta kai wa da komowa a ciki. Bayan jimawa wata macijiya kamar alfadara ta gabato zuwa gare shi, bisa bayan wannan macijiya akwai wani faifan zinariya. A cikin wannan faifan akwai wata 'yar k'aramar macijiya tana haske kamar lu'ulu'u. Fuskarta irin ta mutane ce, tana zance da fasaha da harshe mai dad'i. Yayin da ta gabato wurin Hasib Karimuddini ta yi masa sallama, ya mayar mata da sallamar. Daga nan d'aya daga macizan nan ya sauko daga kujerarsa ya kama faifan ya saukar da ita zuwa wata kujera da ta fi ragowar kyau. Ta yi kururuwa gaba d'aya macizan suka fad'i suna masu gaisuwa da irin yarensu. Macijiya ta yi musu alamar su zauna, suka koma suka zauna. Ta juya ga Hasib ta ce, "kada ka ji tsoronmu ya kai saurayi, ni ce sarauniyar macizai, kuma jagorarsu." Da Hasib ya ji haka sai zuciyarsa ta natsu ya zauna. Ta sa macizai su kawo masa wani abu da zai ci. Suka kawo masa tuffa da inibi da rumman da gyad'a da kuma ayaba suka ajiye a gabansa. Sarauniyar macizai ta ce da Hasib, "barka da zuwa ya saurayi, yaya sunanka?" Ya ce, "sunana Hasib Karimuddini." Ta ce, "ya Hasib zauna ka natsu ka ci wad'annan 'ya'yan itatuwa, domin ba mu da nama ko wani abu daban. Ci sosai kada ka ji tsoronmu." Da ya ji haka sai ya natsu sosai ya ci kayan marmarin nan har ya tumbatsa ya gode wa Allah. Daga nan aka d'auke farantan abincin daga gabansa. Sarauniya ta ce masa, "Hasib fad'a min yadda ka zo wurin nan da abin da ya faru gare ka ya yi sanadin zuwanka." Hasib ya gyara zama ya ba ta labarinsa tun daga kan mahaifinsa da yadda ya rasu kamar yadda mahaifiyarsa ta fad'a masa, da yadda aka sa shi makaranta yana shekara biyar ya zamana bai iya karatu da rubutun komai ba, da yadda ta kai shi wurin koyon sana'a bai iya ba, da

Chapter 1 of 4