Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
tagaya mini sai nayi shiru na dan wani lokaci ban cemata komai ba, sannan daga baya sai nacemata : kiyi abunda kike ganin ya dace, ni bazan hanaki ba.. To tun daga wannan rana, matar tawa bata gushe ba tana cikin wani yanayi na bakin ciki da damuwa, tana kuka har tsawon shekara 1…. To ananan haka, Bayan ta cika shekara tana kuka, watara sai tacemini : ya dan uwana ! ina neman alfarma a wurinka, inaso ka bani dama in gina kabari ( gidan makoki ) a cikin fadarka saboda inkadaita a ciki da bakin cikina, kuma zan sanyawa wannan wuri suna : ( gidan bakin ciki ) ko gidan makoki.. sai nacemata : babu komai kiyi duk abunda kikaga yadace. To sai ta gina gidan makoki da kabari mai girma a cikin fadartawa, sannan sai ta kaurar da wannan BAWA ta kawoshi ta ajiyeshi cikin wannan makoki da ta gina. shikuma wannan BAWA – masoyinta matar tawa – tun daga wannan rana da naso na halakashi amma banyi nasara ba, ya kasance yana cikin tsananin rauni da rashin lafiya ko matsi baya iya yi, baya iya anfanar da ita da komai, shi dai kawai yana iya shan ruwa da sauransu.. tun daga wannan rana da na masa rauni baya iya magana shi dai kawai yana raye ne, saboda ajlinsa bai kareba. To Sai matar tawa ta kasance cikin kullum a cikin dawainiyar wannan BAWA, A kullum- safe da yamma - sai ta shiga wurinsa a daki ta zauna tayi ta kuka tana zubar da hawaye. Kuma tana bashi duk abunda yake bukata na abubuwan sha. bata gushe ba tana cikin wanna yanayi na dawainiyar wannan BAWA - safe da yamma - har A ka shiga shekara ta biyu. Nikuma na cigaba da hakuri da ita, na kai zuciyata nesa na zura mata ido ina kallon abunda takeyi.. Ananan Bamu gushe ba muna cikin wannan yanayi, har saida watarana na shiga wannan daki namakoki da ta gina ta ajiye BAWAN a ciki, - ba tare da saninta ba -.. Bayan na shiga cikin wannan daki sai na sameta a ciki ta daura hannunta akanata tana kuka saboda tsananin bakin ciki, tana raira wadannan baitoci kamar haka. ((Na kasa samun kaina a rayuwa bayan na rasaka)) ((Hakika zuciyata bata kaunar wani in ba kai ba)) ((Ka dauki gangar jikina nama kyauta duk inda zaka)) ((Duk inda ka mutu a ka bunneka abunneni kusa da kai)) ((Idan ka kira sunana a kusa da kabarina To )) (( Sautin motsin kasussuwata zasu amsa kiranka. Bayan ta gama raira wannan waka, nikuma in tseye a bayanta bata sani ba, sai na zaro takobina nacemata :Ai daama wannan shine irin zancen da mata mayaudara masu cin amana sukeyi, wadanda suka ki kusantar mazajensu, suka tauye hakkin Aure.. Bayan na fadamata wannan magana, sai ta fahimci cewa tabbas nine na raunata wannan BAWA da takeso. kafin ta juyo sai nayi yunkurin daga hannuna sama saboda in halakata da wukar dake hannuna.. kawai sai ta tashi ta tseya daram da kafafunta ta kalleni – cikin fishi da bacin rai – nikuma na daga hannuna sama ina rike da wuka, amma na kasa yin komai.. bayan ta tashi sai ta furuta wasu kalmomi (maganganu) da bana fahimta, bayan haka sai tace : Don darajan furucin da nayi ALLAH ya zamar da rabin jikinka dutse rabinka kuma DAN ADAM, Atake sai halittata ta canza na zama kamar yadda ka ganni, sai na kasance a cikin wannan yanayi bana iya tashi balle in zauna, nidai kawai ganinan ba macecce ba kuma ba rayayyeba. ( saurayin yake bawa wannan sarki labari ) To sai ya cigaba da cemasa : bayan na zama kamar yadda ka ganni, sai wannan matar tawa ta tsafe wannan gari nawa da kasuwanni da gonaki dake ciki gabadaya.. kuma daama a garin nawa Akoi al’umma – daban daban – har guda 4.. Akoi MUSULMAI, da NASARA (kirista) da YAHUDAWA da MAJUSAWA ( masu bautawa rana da wuta) duk a cikin wannan gari nawa.. to sai matar tawa ta sihirce (tsafe) su gabadaya ta zamar da su kifaye. fararen kifayen sune MUSULMAI, jajayen kuma sune MAJUSAWA, warawara (blue) sune NASARA, sudin kuma sune YAHUDAWA.. Bayan haka, sai ta sihirtar da sauran garurruwan baqaqen fata guda 4 da suke cikin masarutata ta zamar da su manyan duwatsu, sai ta zagaye wadannan duwatsu da wannan tapki da kagani.. sannan kuma kowane rana sai ta zo ta azabtar da ni tayi mini bulala 100, da bulalar irin ta fata, har sai jini ya koraro daga jikina.. sannan sai ta sakamini rigar da aka saaqa (dinka) da gashi ta lullubeni da shi saboda ya kara mini radadi… To a nan sai wannan surayi yayi ta kuka, hawaye suna korarawa daga idanunsa, ya raira wannan wakar kamar haka" (Ya ALLAH Nayi hakuri da qaddara da hukuncinka) (Ni mai ahkurine idan har Akoi yardanka a ciki) Hakika na ina cikin kunci na abunda ya sameni (Amma nayi ta wassuli da zuri’ar annabi yardajje. Da saurayin ya gama wannan waka, sai idanunsa suka koraro da hawaye ya fashe da kuka.. haka shima sarkin idanunsa suka koraro da hawaye saboda tausayawa halin da saurayin yake ciki.. sai wannan sarki ya daga kansa ya kalli saurayi yacemasa : ya kai samari ! hakika ka kara mini bakin ciki da damuwa a cikin zuciyata. Sannan sai ya tambayesa yacemasa : yanzu a ina wannan matar taka take ? sai saurayin yacemasa : tana tare da wannan BAWA (masoyinta) a cikin wannan gidana makoki da tagina, a kullum tana ziyartarsa sau daya a rana, kuma kafin taje wurinsa sai tazo wurina ta tube mini rigana tayi mini bulala 100, inyi ta I’hu ina kuka har ingaji, kuma gashi bana iya motsi balle inkare kaina daga radadin bulalarta,sannan bayan ta gama azabtar da ni, sai ta wuce ta tafi wurin wannan BAWA ta biyamasa bukatunsa tabashi abun sha ya sha, saboda baya iya cin abinci tun lokacin da na raunatashi. Da wannan sarki yaji wannan magana daga wurin saurayin sai yacemasa :wallahi na rantse da ALLAH sai na taimaka maka nayi maka irin alherin da za’a tuna da ni ko bayan raina, sai na maka abun alfahari wanda zai zama tarihi bayan raina. Sannan sai sarkin ya zauna tare da wannan saurayi yana hira tare da shi yana dauke masa kewa har zuwa dare.Sannan da dare yayi, al fijir ta kusa ketowa, sai sarkin ya tashi ya tube kayansa ya dauki takobinsa ya rataya a wuyarsa, ya nufi wurin da wannan BAWA yake kwance (makoki). Bayan ya shiga wannan wuri sai ya ga pitila da kendir a kunne. a wani gefen kuma, sai ya ga turaren wuta da magunguna da sauransu…. Sannan sai ya ga wannan BAWA a kwance . To da yaga haka, baiyyi wata wata ba, kawai sai ya zaroo takobinsa ya lumawa wannan BAWA ya karasashi ya kasheshi, sannan sai ya daukeshi yanufi rijiya da shi ya jefashi a ciki. bayan haka sai ya dawo ya dauki rigar wannan BAWA ya saka. sai ya koma ya shiga dakin BAWAN (makokin) da takobinsa a hannusa ya zauna cikin shiri.. Bai gushe ba yana zaune, bayan kamar Awa 1, sai ga matar ta shigo cikin fadar, isowarta ke dawuya sai ta shiga dakin da wannan saurayi (mijinta) yake, sai ta dauki bulala tayi ta zabga masa, shikuma sai I’hu yake yana – wayyo wayyo – yana I’hu yanacewa : dan ALLAH kibarni da abunda nake ji, kiyi min afuwa, ki rahamceni, sai tacemasa : shin kai ka rahamci masoyina ne ? sannan da ta gama sai ta sakamasa riga (wanda aka saqa da gashi ) ta yadda zai kara masa radadin ciwo. Sannan sai ta nufi dakin masoyinta BAWA da abinci a hannunta. To shikuma sarkin da yaga tanufi dakin da yake, sai ya kwanta akan gadon BAWAN ya lullube jikinsa yayi kamar yana bacci. sai matar ta shigo cikin dakin, da shigarta kawai sai ta zauna ta soma kuka tace : ya masoyina dan ALLAH kayi mini magana, dan ALLAH kayi min zance mana inji dadi a raina.. Sai ta cigaba da kuka tana cewa dan ALLAH kayi magana inji sanyi a raina. To sai sarkin ya kankatar da muriyarsa ya karkatar da hashensa yayi irin muriyar baqin fata (BAWA) yayi nishi irin ta marasa lafiya yace : AA’h, LA HAULA WA LA QUWWATA…. Da matar taji yayi magana sai tayi I’hu saboda tsananin murna har sai da tasuma dan farinciki.. bayan ta farka sai tace : - cikin murna - watakila masoyina ya samu lafiya ? . sai sarkin ya kankantar da muriyasa yace : ya ke fitsararriyar mata, baki cancanci inyi miki magana ba, sai tacemasa : menene dalilin haka ? me nayi maka ne ? sai yacemata : a kullum da rana kina azabtar da mijinki yana ta I’hu yana rokonki har yana hanani bacci da daddare, kuma bayan kin tafi sai mijin naki yayi ta qasqantar da kansa ga ubangiji yana ADDU’A yana kai kukarsa ga ALLAH yana kararki har sai da sautin muriyarsa ta hanani nitsuwa ta samini damuwa a cikin zuciyata, da ba don haka ba, da tuni na samu sauki na warke.. Shi yasa naki nayi miki mgagna dazu. To Sai tacemasa : ya masoyina idan ka amince zan warware masa wannan sihiri saboda kasamu kwanciyar hankali da nitsuwa da isheshen lafiya. Sai yacemata : kije ki warwaremasa wannan sihiri ki hutar damu mu samu nitsuwa a ranmu. sai tace : to ranka ya dade kamar yadda kakeso haka za’a yi. Sai ta tashi cikin sauri ta fita ta nufidakin da mijin nata yake (saurayi), shigarta dakin sai ta samesa a zaune yana kuka. sai ta dauko kwano ta cikashi da ruwa ta yi wasu maganganu (furuci)da ba fahimata, sai ta tofa a cikin wannan ruwa, sai ruwan ya soma tafasa, bayan haka sai ta yayyafawa mijin nata tece : don darajan furcin da nayi (tofi) ka fita daga wannan halittar ka koma halittarka ta farko, To sai saurayin ya kumbra ya canza kamanni ya koma halittarsa ta farko - cikekken DAN ADAM –To sai ya tashi ya tseya da kafafunsa yayi farin ciki sosai ya godewa ALLAH yayi salati ga ANNABI (S.A.W) sannna sai matar tasa tacemasa : ka fita daga wannan wurin ka bar garinnan kar ka kara dawowa, idan ka dawo zan kasheka, sai ta daka masa tsawa tace ya fita yabata wuri, shikuma bai ce komai ba, sai ya kama hanya ya fita abunsa. Bayan haka sai wannan mata to koma daki wajen wannan sarki, ta samesa yana kwance akan gado jikinsa a lullube. Da shigarta sai tacemasa" ranka ya dade na Aiwatar da abunda kakeso, dan ALLAH ka bude fuskarka inganga. Sai ya kankantar da muriyarsa yacemata : wani irin abu ne kike ganinizakiyi ki kwantar mini da hankalina ki cire mini damuwar da ke cikin zuciyata.?? Ai abunda kikayi bakiyi komai, saboda baki aiwatar da asalin abunda nakeso ba. Sai tace masa" menene asalin abunda kake so ya masoyina? sai yace : mutanen wannan garin da kuma garurruwa da suke hade da wannan garin da kika shiratar da su. kullm idan dare yayi sai wadannan kifayen su ke daga kawunanasu sama suna ADDU’A suna rokon ALLAH tare da tsinemana dani da ke. Kuma wannan shine dalilin rashin samun sauki da lafiya a gareni, saboda haka inaso ki je ki warware musu wannan sihiri sannan sai kizo ki kama hannuna ki tseyar da ni saboda yanzu na samu lafiya. Da wannan mata taji abunda sarkin ya fada, kuma ta dauka wannan BAWAN ne, sai tacemasa – a cikin farin ciki - : to ranka ya dade kamar yadda kake so haka za’a yi. Sai ta tashi ta mike cikin farin ciki ta fita a guje ta nufi inda wannan tapki yake. isowarta ke da wuya (wurin tapkin), sai ta dibi kadan daga cikin ruwan wannan tafki. Ranar lahadi zan daura wanda insha Allahu nake sa ran gama labarin duka Yusuf abdullahi A jibaga07 HIKAYAN MASUNCI DA IFRITU. KARSHE, wannan sarki dake kwance akan gadon ( BAWA ) – mara lafiya - ya umurci wannan fitsararriyar matar (matsafiya) SAI yacemata : yanzu inaso ki je ki warware wannan sihiri, sannan sai kizo ki kama hannuna ki tseyar da ni saboda na samu lafiya. To Da wannan mata taji abunda sarkin ya fada, kuma ta dauka wannan BAWAN ne, - masoyinta - sai tacemasa – cikin farin ciki - : to ranka ya dade kamar yadda kake so haka za’a yi. Sai ta tashi ta mike - cikin farin ciki - ta fita a guje ta nufi inda wannan tapki yake. Bayan ta iso wurin wannan tapki sai ta dibi kadan daga cikin ruwan tapkin, ta yi wani furuci (maganganu – ko lafuza) da baa’a fahimta, ta tofa a ciki, jim kadan sai wadannan kifaye suka motsa suka daga kawunansu, sannan atake sai halittarsu ta canza suka zama ‘yan ADAM – kamar yadda suke da farko – sihirn ya warware wa mutanenn wannan gari , sai garin ya koma kamar yadda yake da farko – agine – kasuwanni a bude, kowa yana harkarsa, ana ta hadahada, kamar babu a bunda yafaru, kuma wadannan duwatsu guda 4 suma suka koma kamar yadda suke ( daama sune qasashe baqaqen fata da ta tsafe su suka zama manyan duwatsu gudu 4 da suka zagaye tapkin ) to sai suma duwatsun suka koma kamar yadda suke da farko yan ADAM. To bayan haka, atake sai wannan mata – makira ma tsafiya – ta juya ta koma wurin wannan sarki, kuma ta dauka cewa wannan BAWAN ne wanda take so. Da isowarta wurinsa sai tacemasa : ya masoyina ! na aiwatar da abunda kakeso, ka miko mini hannunka mai al-barka in tsunbata inji dadi a raina. Sai sarkin ya kankantar da muriyarsa yace : to ki matso kusa dani, motsowarta ke da wuya kenan sai ya zaro takobinsa ya luma mata a kirji har sai da takobin ya fito ta bayanta sannan sai ya tsagata ya raba gangan jikinta biyu ya aikata lahira, a nan kwananta ya kare.. Sannan sai sarkin yafito waje ya sami wannan saurayi – mijin matar – yana tseye yana jiran fitowarsa, sai sarkin ya taya saurayin murnar kubuta daga halin da yake ciki - na wannan mata -, kuma sai saurayin ya rungumi wanna sarki ya gode masa, sai sarkin yacemasa : zaka zauna a wannan gari naka ko kuma zamu tafi tare zuwa masarutata (garisa) ? sai saurayin yacemasa : ranka ya dade sarki ! shin kasan tsawon tafiyar da ke tsakaninka da masarautarka kuwa ? sai sarkin yace : kwana biyu da rabi ne kawai.. . sai saurayin yayi dariya yacemasa : ya mai martaba ! idan bacci kake to ka farka, tafiyar da ke tsakaninka da masauratarka tafiyar shekara daya ne cib ga mai tafiya da sauri kenan,.. abunda yasa ka iso wannan gari nawa a cikin kwana biyu da rabi, saboda wannan fitsararriyar matar tawa ta tsafe garin ne shi ya sa. Amma yanzu dunda komai ya koma daidaita, to babu makawa zakayi tafiyar shekara daya cib kafin ka iso masarautar ka, sai wannan sarki yayi mamaki matuqa da jin wanna maga. Sannan bayan haka sai saurayin yacemasa : ya mai martaba wallahi ina qaunarka bazan taba rabuwa da kai ba, saboda kayimini abunda bazan taba mantawaba. Sannan sai suka rungumi juna suka yi farin ciki matuqa.. sannan sai sarkin yace : godiya ta tabbata ga ALLAH wanda yayi mini Ni’ima ya hadani da kai, yanzu ka zama 'dana, saboda ALLAH bai arzuqtani da (‘DA ) ba duk tsawon rayuwata, sannan sai suka kara runguman juna sukayi farin ciki, sai suka nufi cikin fadar masarautar wannan saurayi, sai saurayin ya tara muqarrabansa da fadwansa ya gabatar musu da wannansarki. Washe gari sai saurayin ya sanar da jama’ar garinsa cewar yana so ya yi tafiaya zuwa qasa mai tsarki saboda yiyi aikin HAJJI, sai aka shiryama abunda yake bukata gabadaya. Sannan suka kama hanaya da shi da wannan sarki,.. a wannan lokaci. shikuma sarkin zuciyarsa tana cike da begen masarautarsa, saboda yayi shekara cib da barin gari nasa. To basu gusheba suna ta tafiya dare da rana kwana da kwanaki har sai da sukayi shekara 1 cur suna tafiya, tare da askarawa, har sai da watara suka iso kofar shiga wannan masarauta ta wannan sarki. Sannan sai wazirin wannan sarki ya fito tare da askarawa saboda tarbar sarki bayan sun cire tsamanin dawowarsa, sai fadawa da askarawa suka zo sukayiwa sarki marhaba suka girmamashi. Da komai ya daidaita, sai sarki ya shiga fadarsa, jama’a da mukarraban sarki da fadawa suka taru, sannan sai sarkin ya gabatar da wannan saurayi, yayi musu bayanin a bunda yafaru gabadaya daga farko zuwa karshe. Sannan bayan haka, sai sarki ya ‘umurci waziri da ya kirawo masa (masunci) mai kamun kifi, wanda shine dalilin kubutar da wannan saurayi da mutanen masarautarsa gabadaya. To atake sai waziri ya zo da mai kamun kifi, sai sarki yayi masa gagarumin kyauta, kuma ya tambayeshi irin rayuwar da yake ciki, ya tambayeshi shin yana da yara ne ? sai mai kamun kifi ya gayamasa cewar yana da yara uku, daya na miji biyu kuma mata. To sai sarkin ya Auri daya daga cikin ‘ya yan mai kamun kifi, sannan sai shi kuma wannan saurayi ya auri dayar, sai sarkin ya dauki dan mai kamun kifi na mijin ya bashi mukami mai girma (mai lura da baitul mali) a masarautarsa. Sannan sai sarkin ya aika wazirin nasa zuwa masarautar wannan saurayi, ya nada shi a matsayin sarkin wannan gari. To daga wannan lokacin ne rayuwa ta kasance madaidaiciya ga wannan sarki da kuma saurayin.. suka rayu cikin wadata da annashwa, shima mai kamun kifi ya wayi gari yana daga cikin mafiya arzikin wannan zamani gabadaya, ‘ya yan sa kuma sune matan sarakuna.... Basu gusheba suna cikin wadatacciyar rayuwa har sai da mai raba tsakanin ‘yan uwa da masoya ya zo ya daukesu ( mutuwa).. A NAN LABARIN MAI KAMUN KIFI ( MASUNCI) YA KARE. Wanda ni yusuf abdullahi A jibaga' na jagoranci kawo muku. Sai bayan kwana biyu idan munsake haduwa awani labari, This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4