Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
BAREWAR ta fuskanci bangaren sarki ta kalle shi ta zuramasa idanu, sai ta durqusa qasa ta tsunkuyar da kanta kamar tana gaisheda sarki tana bashi girma,, kawai atake sai tayi tsalle ta tsallaka wuyar sarki, ta arce a 100 ta gudu abunta ta shiga daji… to da sarki yaga haka sai yajuya wurin mutanen ( abokanen farautansa ) sai yaji suna qananan magan ganu a tsakaninsu game dashi, sai yacewa wazirinsa : ya kai waziri.. menene mutanen nan suke fada a kaina ?? sai wazirin yace masa : wai sukace" dazu kacemusu duk wanda BAREWA ta kubuce ta gudu ta bangarensa to babu shakka za’a kashe shi…. Da sarki yaji haka sai yace : wallahi na rantse da ALLAH sai nabi wannan BAREWAR na kamota na zo da ita… kawai sai ya shiga daji saboda ya kamo BAREWAR,, baigusheba yana tatafiya a cikin daji yana bin wannan BAREWA kuma TSUTSUN nasa yana bin BAREWAR yana caccakar idanunsa har sai da ta yamanto baya iya gani baya iya gudu… to sai sarkin yaciro kibiyarsa ya harbeta.. bayan tafadi sai yaciro WUQA ya yankata yafede ya ratayata a jikin dokinsa ya kama hanya zai koma… naga wasu sungaji da karatu. RANAR ASABAR ZAMU DAURA INSHA ALLAHU DAFATAN KUN WUNI LAFIYA03 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU Da sarki yaji haka sai yace : wallahi na rantse da ALLAH sai nabi wannan BAREWAR na kamota na zo da ita… kawai sai ya shiga daji saboda ya kamo BAREWAR,, baigusheba yana tatafiya a cikin daji yana bin wannan BAREWA kuma TSUTSUN nasa yana bin BAREWAR yana caccakar idanunsa har sai da ta yamanto baya iya gani baya iya gudu… to sai sarkin yaciro kibiyarsa ya harbeta.. bayan tafadi sai yaciro WUQA ya yankata yafede ya ratayata a jikin dokinsa ya kama hanya zai koma… To a a lokaci da sarkin yake kokarin komawa wurin abokanen farautarsa, ana zafin rana sosai.. to sai ishiruwa ta dameshi kuma yaga alamar dokinsa ma yana matuqar jin ishiruwa.. sai sarkin yajuya yaga wata bishiya mai inuwa sai ya zauna a qarqashinta,, kuma sai yaga ruwa yana tsiyaya daga saman wannan bishiya,, to sai ya dauko kwariya ya ajiye a inda ruwan yake tsiyaya saboda ya tari ruwan ya sha.. jim kadan sai kwariyar ta cika, sai sarkin ya dauki kwariyar ya ajiyeta a gabansa saboda ya sha,, kawai sai wannan TSUNTSU ya zo a guje ya buge kwariyar da qafarsa ya kifar da ita ruwan ya zube gabadaya a qasa.. To sai sarkin ya dauki kwariyar ya qara ajiyeta a inda ruwan yake tsiyaya,, jim kadan sai kwariyar ta cika, sai ya daukota ya ajiyeta a gaban wannan TSUNTSU saboda ya dauka TSUNTSUN yana jin ishiruwa ne, sai ya a jiye agabansa saboda ya soma sha tukuna , amma duk da hakan sai TSUNTSU ya qara buge kwariyar ya kifar da ita… To sai sarkin yaji haushin wannan TSUNTSU… sai ya dauki kwariyar a karo na uku ya qara a jiyeta har sai da tacika sannan sai ya dauketa ya ajiyeta a gaban dokinsa saboda dokin ya sha, sai ga wannan TSUTSU ya qara zuwa ya buge kwariyar yakifar da ita… sai sarkin yaji haushi yacewa TSUNTSUN : amma anyi la’anannen TSUNTSU anan.. ka hanani shan wannan ruwan, ka hana kanka sha, ka hanawa dokina sha… me kake nufi ne ? kawai sai ya zaro takobinsa ya buge TSUNTSUN ya cire mata fikafikinta ! sai TSUNTSUN ya fadi gefe ya numfashin fitan rai, jini na zuba daga jikinsa yana motsi kadan kadan !! To bayan haka sai TSUNTSUN ya soma daga kanasa sama yana kallon sarkin yana masa nuni (ishara) da idanunsa, yana gayamasa cewa : ka daga kanka sama ka kalli saman wannan bishiya, sai sarkin ya fahimci a bunda TSUNTSUN yake nufi,, sai ya daga kansa sama ya kalli wannan bishiya, kawai sai yaga wani katon maciji, wanda kuma wannan ruwa dake zubowa daga saman bishiyar ashe guban wannan macijinne ( wanda sarkin yake kokarin tara saboda ya sha amma TSUNTSUN ya hana shi ) da sarkin yaga haka sai yayi I’hu yayi kuka saboda matuqar nadamar abunda yayiwa wannan TSUNTSU na zalunci… bayan sarkin yagama kukarsa sai ya dauki TSUNTSUN ya hau dokinsa ya kama hanya ya koma wajen ‘yan uwansa… TSUNTSUN kuma yana hannunsa, rai a hannun ALLAH.. bayan ya isa wurin ‘yan uwansa sai yamiqa musu wannan BAREWA da ya kamo, yace musu : ku dauki wannan BAREWAR ku dafata.. sannan sai sarkin ya zauna a kan kujera a gefe yana riqe da TSUNTSUN … jim kadan sai TSUNTSUN yayi dogon nishi ya mutu !! sai sarkin yayi I’huu mai qarfin gaske saboda nadamar kashe wannan TSUNTSU da ya tsirar da shi daga halaka…. Wannan shine labarin abunda yafaru da sarki SINDI BADO.. To anan sai sarki YU’NAN yacewa wazrinnasa : To ka gani kar inkashe wannan mutumi – HAKIMU – inyi nadama kamar yadda sarki SINDI BADO yayi nadama… da waziri yaji abunda sarki YU’NAN ya fada sai yace : ya sarki mai martaba mai daraja.. wannan qoqari da kaga nakeyi saboda in rabaka da HAKIMU koda ya zamanto akoi laifi a ciki ko cutarwa ai saboda kai nakeyi !! kuma saboda ina tausaya makane kar ka hala… idan kaji shawarata to ka tsira, idan kuma kaqi zaka halaka kamar yadda wani waziri da ya yiwa dan sarki wayo da dabara saboda ya halakar da shi,, amma sai shi wazirin ya halaka… sai sarki YU’NAN yace menene labarin wazirin da kuma dan sarki ?? Sai waziri yacemasa : akoi wani sarki da ya kasance yana da wani dansa da yake matuqar son farauta a daji… to sai wannan sarki ya ‘umurci wazirinnasa da ya kasance tare da dan nasa duk inda zai je.. to anan sai wata rana dan sarkin ya fita zuwa daji, kuma wannan wazirin yana tare da shi.. To bayan sun shiga cikin daji" sai wazirin yaga wata dabba, sai yacewa dan sarki. kabi wannan dabbar ka kamota nasan kai jarumine .. shikuma dan sarkin da yaji haka sai yasoma bin wannan dabbar ,, bai gusheba yana ta binta ita kuma tana qara shiga cikin daji har sai da tajanyo shi cikin duhun daji sannan sai daga baya ya daina ganin wannan dabba atake ta bacemasa… sai dan sarkin ya tseya ya juya gaba da baya bai ga kowa, kuma bai san hanyar da zai bi ya koma ba.. ya bata a cikin wannan daji, sai ya rikice ya rude ya dimauce ya tsorata bai san ina zai nufa ba… jim kadan sai ga wata ‘yar buduruwa ta bullo a gabansa tana kuka.. sai ya tambayeta yacemata : daga ina kike ? sai tacemasa : Ni ‘yar wani sarkine daga cikin sarakunan qasar (INDIA) kuma nakasance inatafiya ne a kan dokina sai gyengedi (bacci) ya kamani sai na fado daga kan dokina, bayan na farka sai na nemi dokin na rasa, to sai narasa yadda zanyi, shine na kama hanya ina tafiya a qafa har na iso wannan wurin… da dan sarkin yaji haka sai ya tausaya mata ya dauketa a kan dokinsa ya daurata a baya shikuma yana gaba… sai suka cigaba da tafiya har sai da suka iso kusa da wani TAPKI ( qaramin kogi ) sai yarinyar tacemasa : ranka ya dade inaso ka sauqar dani anan saboda in biya buqatata (fitsari) sai dan sarkin ya sauqar da ita,, sai ta shiga.. bayan wani lungu ta yadda baza’a iya ganinta ba,, sai shikuma ya tseya yana jiranta.... kuma ta dau lokaci mai tsawo bata fito ba… To jim kadan sai yace bari ya bita ya duba ya gani me ya hana ta fitowa… ita kuma batasan cewa yana binta a baya ba… kawai da ya shiga wannan lungu sai leqa sai yaga wannan buduruwa ta zama ALJANA (a surar dabba) kuma yaji tanacewa : ‘ya‘yanta : ya ku ‘ya’yana kuna ina ne ? kufito yau na nazo muku da wani saurayi mai qwari mai nama.. sai yaran sukacewa uwartasu ALJANAN : yawwa mama, dan ALLAH ki kawo mana shi muci, dama yunwa mukeji, cikinmu babu komai, ke muke jira…. Da wannan dan sarkin yaji haka sai zuciyarsa ta buga, kuma ya tabbatar da cewa kwanarsa ta qare babu shakka zai zama nama ga wannan ALJANA.. bayan haka sai ya dawo baya hankalinsa atashe idanunsa sun yi hawaye yana karkarwa.. jim kadan sai ga wannan ALJANA ta dawo sai taga dan sarkin yana cikin wani hali na tsoro yana karkarwa… sai tace masa " me yasameka ne naga kamar kana cikin tsoro ? sai yacemata : akoi wani da nake tare dashi, kuma ya kasance maqiyina ne, kuma ina tsoron sa… sai ALJANAN tacemasa : shin dazu bakacemini kai dan sarki bane ? sai yacemata E’h tabbas ni dan sarki… sai tacemasa : me yasa bazaka bawa wannan maqiyin naka kudi ba saboda kasamu yardarsa ? sai yacemata : Ai wannan maqiyin nawa baya buqatan dukiya, ba’a samun yardarsa da kudi, shi raina kawai yakeso.. Nikuma tsoronsa nakeji sosai, kuma ni mutum ne wanda aka zalunta… sai tacemasa : idan ka kasance mutum ne wanda aka zalunta me yasa bazaka nemi taimakon ALLAH ka yi tawakkali ka dogara da shi zai iya kareka daga sharrin duk abunda kake tsoro…. Tosai dan sarki ya daga hannunsa sama yayi addu’a yace : ya wanda yake amsa addu’ar wanda yake cikin tsoro da matsi da fargaba idan ya roqesa kuma yake kawar da muunan abubuwa ya ALLAH ka bani nasara akan wannan maqiyi nawa kuma ka kawarmini da shi,, sadoba kaine mai iko akan duk abunda kakeso kayi… da wannan ALJANA taji wannan addu’ar kawai sai ta juya ta tafi abunta… sai shima dan sarkin ya kama hanya ya koma gida abunsa… bayan dan sarkin ya koma gida sai yasanar da mahaifinsa sarki abunda wannan wazirin yamasa.. (wato wazirin yamasa dabara ya turashi cikin daji idan yamutu, sannan idan sarkin ya mutu sai wazirin ya gaji sarauar sarkin) a daliln haka sai wazirin ya rasa ranasa…… To sai wzirin sarki YU’NAN yacewa sarki YU’NAN : ya mai martaba kaga kaima idan ka ciga da yiwa HAKIMU DAUYAN alheri to babu makawa zai kashe ka, saboda ya gaji sarautarka, kuma a duk lokacin da ka kyautata masa ka kusantar dashi ka sashi ajiki, to zai samu damar da zai halaka ka... shin bakaga yadda ya warkar dakai batare da ya baka magani ka sha kokuma ka shafa ba ? kawai wata ‘yar sanda ya baka ka riqeta ahannunka kawai sai ka warke ? To kar kayi mamaki a nan gaba ma zai iya baka wani abun kariqe da hannun kuma ka mutu ? …. To A nan sai sarki YU’NAN yacewa wazirin nasa" haqiqa kayi gaskiya.. wataqila abunda ka fada zai zama gaskiya… ya kai waziri wanda ya iya bada shawara da nasiha… wataqila wannan mutumin - HAKIMU – dan leqen asiri ne,, ya zo garinnan ne kawai saboda ya halakani.. kuma haqiqa idan wannan mutumi zai iya warkar dani daga cutar dake damuna da wani abu da zai bani in riqe da hannuna,, to babu makawa zai iya kasheni da wani abu da zai bani in shaqa ta hanci… To sai sarki YU’NAN yacewa wazirin : to yanzu menene abun yi ? wace hanya zanbi in kashe HAKIMU DAUYAN ? sai wazirin yacemasa : ka Aika a kirawoshi yanzu, idan ya zo sai ka kashe shi kawai ka huta da sharrinsa... ka kasheshi tun kafin shi ya kasheka… sai sarki YU’NAN yacewa wazirin nasa : kayi daidai ya waziri… To bayan haka sai sarki YU’NAN ya Aika aka qira HAKIMU… sai HAKIMU kuma yazo kamar yadda ya saba batare da bata lokaci… bayan ya shiga sai ya gaida sarki kuma ya yabeshi ya karanta masa baitoci da qasidu na yabo da godiya kamar yadda yasaba a kullum.. bayan gama sai sarki yacemasa : kasan meyasa nasa aka kiraka a wannan lokacin ? sai HAKIMU yace : babu wanda ya san GAIBU sai ALLAH.. sai sarkin yacemasa : na kirawokane saboda in kasheka in kawar dakai a bayan qasa !! sai HAKIMU yayi matuqar mamaki da jin wannan maganar kuma sai yacewa sarkin : ya mai martaba me yasa zaka kasheni ? wani laifi nayi da za’a kasheni ? sai sarkin yacemasa : Naji labarin cewa kai dan leqen asirine, ka zone saboda ka kasheni,, shiyasa nace bari in kashe kafin ka kasheni.. kawai atake sai sarki YU’NAN yayi I’hu ya kira mai pille kan mutane,, jim kadan sai ga wani gardi ya shigo da takobi a hannunsa,, sai sarki YU’NAN yacewa gardin : ka dauki wannan makirin ka sare kansa ka hutar dani daga sharrinsa.. sai HAKIMU ya zama abun tausayi ya rasa abunda zaiyyi.. sai ya durqusa ya soma roqon sarki YU’NAN ya cemasa : dan ALLAH kayi min rai ! kaima ALLAH zai rahamaceka !.. kar ka kasheni kaima ALLAH zai kashe ka… sannan sai HAKIMU yayi ta maimaita masa yana roqonsa kamar yadda nima nayi ta maimaita maka naroqe ya ALJANI ALMA’RIDU akan kar ka kasheni amma sai kaqi jin maganata… To sai sarki YU’NAN yacewa HAKIMU DAUYAN : NI hankalina bazai kwantaba sai na kasheka tukuna.. saboda ka warkar dani da wani abu da kabani na riqe a hannuna – sanda – To babu makawa zaka iya kasheni da wani abu da zaka bani in shaqa – in shishina- in mutu kokuma kayi wata dabarar daban dan ka kasheni… sai HAKIMU yace : ya mai martaba : yanzu wannan shine sakayyar da zaka saka mini da ita ?? nayi maka abu mai kyau kai kuma zaka sakamini da muumuna ? sai sarkin yacemasa : babu makawa sai na kasheka batareda bata lokaciba… To da HAKIMU ya tabba cewa sarki YU’NAN zai kasheshi babu makawa,, sai yayi ta kuka yana zubar da hawaye, kuma ya zargi kansa saboda irin abunda yayiwa sarkin amma sarkin kuma ya saka masa da wannan sakayar.. To bayan haka sai wannan gardin - mai pille kayin mutane – ya zaro takobinsa yacewa sarki : ya mai martaba ina jiran izininka ne… shikuma HAKIMU sai kuka yakeyi yana zubar da hawaye yanacewa sarki : kayi mini rai kaima ALLAH zai maka rahama, kar ka kasheni kaima ALLAH zai kasheka… sai HAKIMU ya soma karanta wasu baitici yace : Nayi nasiha ban bandace ba, su kuma sunyi zamba sai suka dace … to yau gashi nasihata ta shigar dani gidan wulaqanci Idan ALLAH ya rayar dani to bazan qara yin nasiha ba, idan kuma namutu to ku isar da saqona zuwa ga masu yin nasiha a bayana dukkan abuna nafada To sai. Bayan ya gama wakarsa sai" HAKIMU yacewa sarki YU’NAN : yanzu wannan shine sakamakona daga gareka ? zakayi mini sakayyay irin sakayyar da akayiwa wata KADA.. sai sarki YU’NAN yace : menene labarin wannan KADAR sai HAKIMU yace : Ai yanzu bazan iya baka wannan labari ba saboda irin halin da nake ciki... sai yace : dan ALLAH kayi mini rai, ALLAH zayyi maka rahama! Sai HAKIMU yayi tazubar da hawaye yana kuka.. sai wasu daga cikin muqarraban sarki YU’NAN suka tashi sukatashi sukacewa sarki YU’NAN : ya mai martaba ! ka yafe mana jinin wannan mutumi HAKIMU saboda bamu taba ganinsa yayi wani abu na laifi da zai sa a kashe shi ba, kuma mu dai bamu taba ganin yayi wani abu na laifi ba, saidai ma gashi yazo ya warkar da kai daga cutar da ta dukkan likitoci, babu wanda ya iya warkar da kai daga cikin likitacin qasanan gabadaya sai shi.. saboda haka bai kamata ka kasheshi ba, sai sarki YU’NAN yacemusu : bakusan dalilin da yasa nakeso na halaka HAKIMU ba… saboda idan na barshi ya rayu, to ni zan halaka babu makawa.. mutumin da ya warkar dani daga cutar dake damuna da wani abu da yabani na riqe da hannuna, ai babu shakka zai iya kashe da wani abu da zai bani da zan shaqa in mutu.. shi yasa yanzu nake tsoron kar ya halakani bari Ni insoma halakashi da HAKIMU ya tabbar da cewa sarki YU’NAN zai halakashi babu makawa, sai yacewa sarki YU’NAN : ya mai martaba ! idan har ya kasance babu nakawa sai ka kasheni, ina neman alfaram ka dan sauraramini ka bani dama inkoma gidana inbiya buqatuna kuma inyi WASIYYA ga iyalina da maqotana kuma in sanardasu warin da zasu bunne ni idan ka kasheni,... sannan kuma !! Akoi wani littafi na likitanci da nakeso inbaka wanda zai anfaneka bayan mutuwana, kuma Akoi wani littafin daban kebabbe wanda ba kowa nake bawa ba, inason inyi maka kyautar wannan littafi ka ajiye sa a wajenka saboda zai anfaneka sosai… sai sarki YU’NAN yace masa : wannan wani irin littafine kuma menene a ciki ?? sai HAKIMU yace : wannan littafi yana dauke da a bubuwa masu dimbin yawa sosai wanda baza’a iya irgawa ba,, kadan daga cikin abubuwan dake cikin wannan littafi na sirri shine kamr haka : bayan ka sare (pille) kaina sai ka bude wannan littafi kuma sai ka bude shafuka guda 3, sannan sai ka karanta layi 3 daga shafin farko daga hannunka na hagu, idan kayi haka to (KA'YIN NAWA) da ka sare zayyi maka magana, kuma duk tambayar da kamasa zai amsa maka… da sarki YU’NAN yaji wannan magana sai yayi mamaki matuqa.. ya girgiza kansa saboda mamaki.. yacewa HAKIMU : yanzu idan na sare kanka zayyi mini magana ?? sai HAKIMU yace : tabbas hakane.. sai sarkin yace : wannan abun mamakine ! sannan sai sarki YU’NAN ya amince masa da yaje gida ya biya buqa tunsa ya dawo kuma ya turashi tare da masu tsaronsa… bayan HAKIMU ya koma gida ya biya buqatunsa, a rana na 2 sai ya dawo wajen sarki YU’NAN… bayan ya shiga fadar sarki sai ya samu wazirai da hakimai da dukkan muqarraban sarki sun bayyana a fada… fada ta cika makil manyan gari kowa ya hallara… To sai HAKIMU ya tashi ya tseya a gaban sarki YU,NAN yana riqe da wani tsohon littafi, kuma a cikin wannan littafi akoi wani abu kamar kwalli (gaari-gaari) da wani sinadari da kuma abun rubutu (alqalami)… To jim kadan, sai HAKIMU ya zauna akan kujera yace "a kawomini faranti (plate) sai aka zo da faraniti,, sai yayi rubutu a cikin wannan farani .. sannan yacewa sarki YU,NAN : ya mai martaba ka dauki wannan littafin,, kuma kar kayi anfani da shi sai bayan ka sare kaina tukuna,, idan ka sare ka'yin nawa sai ka saka a cikin shi wanna farantin, sannan sai ka bada umurnin a danne kayin nawa ackin wannan faranti, bayan nan jinin dake tsiyaya zai yanke ya tsya.. sannan sai ka bude littafin… Da sarki YU’NAN yaji haka atake sai ya soma bude shafin littafi tun kafin ya aiwatar da abunda HAKIMU ya gayamasa, ya qosa yayi gaggawa saboda ya tabbatar da abunda HAKIMU ke fada gaskiyane ? …. Tosai sarki YU’NAN ya bude shafi (page) na farko sai yaga shafin ya mannu da shafi na biyu kuma ya yaqi buduwa, To sai ya saka ‘yar yatsarsa a cikin bakinsa saboda ya jiqata da nyawu saboda ya samu sauqin bude wannan shafi da yaqi buduwa .. bayan ya saka ‘yar yatsarsa a cikin bakinsa ya jiqata,, sai ya bude shafi na 1 da na 2 da na 3 kuma ko wanne shafi yana bashi wahala wajen budewa.. a haka har ya bude shafuka guda 6 amma bai ga rubutu a ciki ba, ko harafi daya babu…sai sarkin yace : ya HAKIMU : ni ban samu komai a cikin wannan littafi ba ?… sai HAKIMU yace : ya mai martaba ka cigaba da budewa zaka samu abun mamaki a ciki wannan littafi… sa sarki YU’NAN yacigaba da budewa… To ana cikin haka bayan wasu ‘yan mintuna.. sai guba ta shiga jikin sarki YU’NAN ta yadu a jikinsa (wato wannan abu mai kama da kwalii na cikin littafin gubane) To sai sarki ya soma juye juye yana kar karwa, kawai sai yayi I’hu yace : ya jama’a ! guba ta shiga jikina ! kawai sai ya fadi qasa ya mutu nan kwanarsa ta qare…. Sai mai kamun kifi yacewa ALMA’RIDU : ya ALMA’RIDU kasani cewa : da sarki YU’NAN bayyi qoqarin kashe HAKIMU ba, to da ALLAH ba zai halaka shi ba, amma sai sarki YU,NAN ya yarda da zugar wazirinsa yaso ya zalunci HAKIMU ba tare da wani haqqi ba (laifi) sai ALLAH ya kawar masa da basirarsa,, HAKIMU yayi nasara a kansa da hikimarsa da dabararsa… To kaga kaima da bakayi qoqrin halakani ba, da ALLAH ba zai mayarda kai haka ba.. yanzu gashi kana cikin qasqanci sai yadda nayi da kai.. kuma babu makawa sai na maka abun HAKIMU yayiwa sarki YU’NAN ….. RANAR LITININ ZAN DORA INSHA ALLAHU". By Yusuf abdullahi A jibaga What'sapp 0807105113804 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU Wannan bawan ALLAH mai kamun kifi yacewa ALJANI ALMA’RIDU : ya ALMA’RIDU... kaga yanzu daa sarki YU’NAN bayyi qoqarin kashe HAKIMU ba, to da ALLAH bai halaka shi ba.. to amma sai sarki YU,NAN ya amince da shawarar wazirinsa, yaso ya zalunci HAKIMU ba tare da wani haqqi ba (laifi).. sai ubangijin ALLAH ya kawar da basirarsar sarki YU’NAN… HAKIMU yayi nasara a kansa… To kaga kaima da bakayi qoqrin halakani ba, da ALLAH ba zai mayar da kai haka ba.. yanzu gashi kana cikin qasqanci sai yadda nayi da kai.. kuma babu makawa kaima sai na maka irin abun HAKIMU yayiwa sarki, zan rufeka a cikin wannan tulun sannan injefaka cikin wannan kogin har zuwa tashin Qiyamah … Da ALMA’RIDU yaji maganar da mai kamun kifi ya fada sai ya qolla I’hu yace : dan girman ALLAH kar kayi haka,, kayi mini halacci kar ka halakani.... kar ka dubi halina,, idan NI na kasance mai mugun haline, to kai kuma ka kasance mai kyautatawa,, saboda masu magana sukace : ( ya mai kyautatawa wanda yayi masa mugunta… kabar mugu da halinda ) kar irin abunda AMAMATU yayi wa A’TIQA… sai mai kamun kifi yace : menene ya faru tsakaninsu ? sai ALMARIDU yace : wannan lokacin ba lokacin bada labari bane,, yanzu ni inacikin kurkukune, bazan iya baka wannan labari ba, yanzu hankalina a tashe yake,, bazan iya yin komai ba har sai ka fitar dani daga cikin wannan tulu,, idan ka fitar da ni to zanbaka wannan labari… sai mai kamun kifi yace : Ai yanzu babu makawa sai na jefaka cikin wannan kogi, kuma babu wata hanya da zaka iya bi dan ka fita daga ciki…shin ka manta cewar dazu na rarrasheka na lallabeka na durqusa a gabanka saboda kar ka kasheni, amma kaqi, kace sai ka halakani babu makawa batareda wani laifi da na aikata ba ?, kuma babu abunda na maka sai alheri kasancewata na fitarda kai daga cikin kogi… Alokacin da kace sai ka kasheni sai na fahici cewar kai kana daga ciki asalin mugayen ALJANU la’anannu… kuma ka sani, zan jefaka cikin wannan kogi, duk wanda yazo saboda ya ceceka ciroka zan bashi labarin irin halayenka kuma in gargadeshi saboda koda ya ciroka a cikin rashin sani to zai mayar da kai kayi tazama a ciki har zuwa qarshen zamani, saboda kayi ta ganin azaba kala kala kafin tashin qiyamah…. Sai ALMA’RIDU yacemasa : dan ALLAH ka fitar dani kar ka halakani, saboda nalura naga kai mutumne mai mutunci mai halacci kuma yanzu lokacine na afuwa, namaka alqawari bazan cutar da kai ba idan ka fitar dani daga cikin wannan tulun, kuma zan baka wani abu da zai anfaneka ya arzuktaka har abada.. sai mai kamun kifi yaji haka sai ya tausayawa ALMARIDU. To Anan sai ALMA’RIDU da mai kamun kifi suka kulla yarjejeniya sukayi alqawari akan cewa idan ya yafitar da shi - ALMARIDU - ba zai cutar da shiba, kuma ALMA’RIDU zai kyautata masa har abada,, To sai ALMA’RIDU ya rantse da sunan ALLAH mai girma… sai mai kamun kifi ya bude tulun,, sai ga hayaqi ya fito daga cikin tulun, kuma ya nufi sama, sannan sai ya hadu a wuri daya, kawai sai ALMA’RIDU ya bayyana a cikin mumunan halitta.. bayan ya fito sai ya buge wannan tulun da kafarsa (yayi ball da ita ) sai ta fashe ta watse ta shiga cikin kogi… da mai kamun kifi yaga ALMA’RIDU ya buge wannan tulu ya fasata sai ya tsorata ya firgita zuciyar ta buga har sai da yayi fitsari a wandonsa, kuma ya tabbatar da cewa babu shakka kwanarsa ta kare, kuma yace - azuciyarsa - : wannan alamun ba na alkairi bane,, sannan sai ya nuna jarunta ya cire tsoro yacewa ALMA’RIDU : ya ALMA’RIDU ka sani cewa ALLAH yace : (KU CIKA ALQAWARI SABODA ALQAWARI ABUN TAMBAYA NE) kuma dazu kayi mini alqawari kayi rantsuwa akan ba zaka cutar da ni ba,, yanzu idan ka cutar da ni,, To ALLAH zai nuna maka, kuma dazu idan baka manta ba na baka labarin irin abunda ya faru tsakanin sarki YU’NAAN da HAKIMU DAUYAN da irin rokon da HAKIMU yayi wa sarki YU’NAN aka kar ya kashe shi… . Da (ALJANI ALMA’RIDU) yaji abunda mai kamun kifi ya fada sai ya kyal kyale da dariya saboda ganin yadda mai kamun kifi ya tsorata ya razana.. To bayan haka sai ALMARIDU ya soma taku yana tafiya har yawuce taga gaban mai kamun kifi,, sai yacewa mai kamun kifin : ya kai mai kamun kifi ! ka biyoni a baya,, sai mai kamun kifi ya bi ALMARIDU a baya yana cikin wani yanayi na tsoro da tashin hankali dakuma rashin yarda,, saboda yana ganin kamar ALMARIDU zai hallakashi…. Sai suka cigaba da afiya har sai da suka bar bayan gari,, bayan wani dan lokaci sai suka iso wurin wani babban dutse, sannan suka hau saman wannan dutse suka sauko,, sannan sai suka ga wani dan tapki (karamin kogi) mai fadi kuma a tsakiyansa akoi wani tapkin daban - dan qarami -,, To anan sai ALMARIDU ya tseya a wurin wannan kogi, sai ya ‘umurci mai kamun kifi da ya jefa shingensa saboda ya kama kifi,, sai mai kamun kifi ya qura idanunsa ya kalli wannan tapki (kogi) na ruwa sai yaga kifaye masu launi daban daban, - Akoi launi (kala) FARI akoi JAA akoi BLUE da kuma YELLO, To sai mai kamun kifi yayi mamaki matuqa… bayan haka sai ya jefa shingensa, bayan ya saurara zuwa wani dan lokaci, sai ya janyo shingen nasa,, sai ya samu kifaya guda 4 a ciki,... kowani daya daga cikin kifayen launinsa daban yake ( FARI - JAA - BLUE - YELLO )… . Da mai kamun kifi yaga haka sai yayi farin ciki sosai…To sai ALMARIDU yacemasa : ka dauki wadannan kifayen ka kaiwa sarki,, ka bashi kyauta,, shi kuma zai baka dukiya mai yawa wadda zata wadatar da kai… sannan sai ALMA’RIDU yacewa mai kamun kifi : dan ALLAH kayi mini uziri ! saboda ni na kasance cikin wannan kogi har tsawon shekara 1800 ban taba ganin dunuya ba sai yau, saboda haka zan tafi, zan barka anan,, kuma inaso inyi maka WASIYYAH dacewa : kar ka kama kifi a cikin wannan kogi a kowani rana,, a sati sau daya kawai zaka kama kifi,, sannan inamaka ban kwana… sai ALMA’RIDU ya bugi qasa da kafarsa sai qasar ta budu sai ALMA’RIDU ya lume ciki ya bace abunsa ya tafi… To sai shima mai kamun kifi ya kama hanya ya koma gida abunsa yana matuqar farin ciki da mamakin abunda ya faru da shi tare da ALMA’RIDU.. Bayan mai kamun kifi ya isa gida,,

Chapter 2 of 4