Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
sai ya dauki wannan kifi ya nufi gidan sarki kamar yadda ALMA’RIDU ya ‘umurceshi,,, isowarsa gidan sarki keda wuya sai ya samu damar shiga fada ya isa wajen sarki yayi gaisu sai ya gabatarwa sarki kifin nasa ya bashi kyauta, sai sarkin yayi farin ciki,, kuma yayi mamaki sosai saboda a rayuwarsa bai taba ganin kifi mai launi - kala kala - daban daban ba,, sai sarkni yayi ‘umurni da a mikawa mai girki wannan kifi ta dafamasa… sai wazirin sarki ya kira buduruwa (kuyanga) mai giri ya ‘umurceta da ta dafa wa sarki wannan kifi… Kuma dama wannan ‘yar buduruwa ta kasance kuyangace wanda sarkin RUM (italy) ya aikawa wannan sarki HADAYA tun shekaru 3 da suka wuce, to sai a wannan rana sarkin yabada ‘umurni a bawa wannan budurur kifin ta dafa shi saboda ya jarraba korewaeta a girki … To bayan waziri ya ‘umurci mai girki da ta dafa kifi, sai yacemata : ya ke ‘yan mata : mai martaba yace : ba’a yin tanadi sai don gaba, saboda haka yau sarki ya tanadeki don wannan rana irin ta yau,, kuma yanaso ya jarraba korewarki ne a girki yanaso ki girkashi yayi dadi sosai…sai wazirin yacigaba da gayamata : wannan kifi wani bawan ALLAH ne ya kawawo sarki … bayan haka sai waziri ya koma cikin fada abunsa. Bayan waziri ya koma cikin fadar sarki, sai sarki ya ‘ umurcesa da ya bawa mai kamun kifi DINARI 400… sai waziri ya aiwatar da umurnin sarki…. Da mai kamun kifi ya karbi DINARI 400 sai yayi farin ciki sosai saboda bai taba riqe irin wannan kudi ba,, sai ya wuce kasuwa ya sayi duk abunda yake buqata da shi da iyalinsa.. wannan shine halin da mai lamun kifi ke ciki… Amma ita kuma mai girki,, bayan ta karbi kifin daga waje waziri sai ta wanke ta tsabtace shi ta gyara ta saka a cikin tukunya ta soma dafawa,, jim kadan kifin ya soma dafuwa, yana tafasa sai ta juya daya bagaren saboda ya nuna.. To juya kifin ke da wuya.. kawai sai ga bangon kicin din ya tsage, sai ga wata BUDURUWA kyakkyawa sosai ta bullo daga jikin wannan bango tana riqe da sanda a hannunta,, sai ta saka sandar a cikin tukunyar da kifin yaka ciki sai tace : ya ku wadannan kifaye, !! ya ku wadannan kifaye !! shin har yanzu baku gushe ba kuna kan bakar ku ??...wato (kuna kan ra’ayinku) … da mai girkin taga abunda ya faru atake kawai sai ta suma… To sai wannan BUDURUWA da ta bulla ajikin bango ta kara maimaita abunda ta fa darko har sau 3 .. To sai kifayen suka daga kansu daga cikin tukunyan sukace : E’h, E’h, E’h muna kan bakrmu.. to sai BUDURUWAR ta kifar da tukunyar kuma sai ta koma jikin bangon ta shiga wurin da ta bullo da farko sai ta bace… jim kadan sai mai girki ta farfado daga sumar da tayi,, sai taga wannan kifi ya zama toka baqi kamar gawayi…. To Tana cikin wannan hali sai ga waziri ya shigo ya tseya akanta yacemata : ya ke ‘yan mata ki kawo kifin da kika dafa sarki yana jira tun dazu…. Sai mai girki tayi kuka ta bawa waziri labarin abunda ya faru gabadaya… da waziri ya ji wannan labari sai yayi mamaki qorai da gaske yace : kai wannan al amrine mai ban mamaki sosai…. To bayan haka sai waziri ya aika a kirawo mai kamun kifi,, da mai kamun kifi yazo sai waziri yacemasa : ya kai wane, munaso ka qara kawo mana irin wadannan kifaye guda 4 da ka kawo wa sarki rannan muna bukata… sai mai kamun kifi ya kama hanya ya nufi wurin da ALMARIDU ya kaisa sai jefa shingensa ya kamo kifi 4 kamar irin na farko ya kawo wa waziri aka bashi DINARI 400 ya juya ya tafi abunasa To bayan haka, sai waziri ya dauki kifin ya baiwa mai girki yacemata : yau ki dafa wannan kifin a gabana saboda inaso in gani da idona abunda zai faru.. sai mai girki ta karbi kifi ta wanke ta tsabtace ta saka a cikin tukunya… jim kadan da kifi ya soma dafuwa yana tafasa , kawai sai ga bangon kicin din ya tsage sai ga kyakkyawar BUDURUWA ta fito daga ciki, da sanda a hannunta sai ta taba kifin da sandar tace : ya ku kifaye shin baku gusheba har yanzu kuna kan bakarku ne ?... sai kifayen suka daga kansu sama sukace : (( ﺇﻥ ﻋﺪﺕ ﻋﺪﻧﺎ ﻭﺇﻥ ﻭﺍﻓﻴﺖ ﻭﺍﻓﻴﻨﺎ = ﻭﺇﻥ ﻫﺠﺮﺕ ﻓﺈﻧﺎ ﻗﺪ ﺗﻜﺎﻓﻴﻨﺎ )) Idan kika maimaita muma zamu maimaita (wato iadan kika kara tambayarmu muma zamu baki amsa irin ta farko) idan kuma kika cika alkawari muma zamu cika, idan kuma kika kaurace to muma mun isa komai A lokacin da wadannan kifaye suka daga kawunansu sama suka mayar wa wannan ‘yar BUDURUWA amsa cewar suna kan bakarsu, ita kuma BUDURUWAR sai ta kifar da wannan tukunya da sandar da ke hannunta, bayan haka,, sai bangon kicin din ya budu – ya tsage - sai ta koma ta shiga jikin bangon kamar yadda ta fito, sai bangon ya kara rufuwa ya hade. To da wazirin yaga abunda ya faru a idonsa – quru quru – sai ya tashi tseye yace : wannan al’amri ne mai ban mamaki, kuma ya zama dole in sanar da sarki abunda ake ciki… sannan sai ya shiga wurin sarki ya sanar da shi abunda ya faru a idonsa… sai sarki yace bazan yarda ba sai na gani da idona – quru quru. To sai sarki ya bada umurni aka akirawo mai kamun kifi,, RANAR LARABA ZAN DAURA INSHA ALLAHU. Wannan labari na zuwa Muku ne daga ==>Yusuf Addullahi A jibaga05 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU quru quru – sai ya tashi tseye yace : wannan al’amri ne mai ban mamaki, kuma ya zama dole in sanar da sarki abunda ake ciki… sannan sai ya shiga wurin sarki ya sanar da shi abunda ya faru a idonsa… sai sarki yace bazan yarda ba sai na gani da idona – quru quru – To sai sarki ya bada umurni aka akirawo mai kamun kifi,, bayan mai kamun kifi ya iso fadar sarki, sai sarkin ya umurceshi da ya kawo masa kifaye guda 4 kamar yadda ya saba,, atake ba tare da wata wata ba,, sai mai kamun ya kama hanya ya nufi wannan tapki dake bayan gari yaje kamo kifaye guda 4 masu launi daban daban ya kawo wa sarki, sai sarki ya bada umurnin a baiwa mai kamun kifi DINARI 400. To Bayan haka sai sarki ya dauki kifin ya mikawa waziri yace masa : ka dauki wannan kifin ka wanke ka gyara ka dafashi a anan a gabana saboda ingani da idanuna – quru quru – sai waziri yace : ranka ya dade ! kamar yadda kaso haka za’ayi… atake sai waziri yaje ya kawo murhu da tukunya ya hura wuta, ya hada komai da komai, ya wanke kifi ya gyara, sannan sai ya zubashi a cikin tukunyar sai ya dan saurara, jim kadan bayan tukunyar ta soma tafasa kawai sai ga bangon fadar sarki ta ya tsage kuma sai ga wani baqin BAWA mai muumunar halitta mai tsoratarwa ya bayyana a gabansu da ganye a hannunsa, sai ya daga muriyarsa da karfi yace : ya ku wadannan kifaye ! shin har yanzu baku gushe ba kuna kan bakarku ?.. wato (kuna kan ra’ayinku ?.) sai kifayen suka daga kansu daga cikin tukunyar sukace : E’h, Eh, Eh, bamu gushe ba muna kan bakarmu, sannan sai suka rai raya wannan baiti" idan ka kara tambayarmu zamu ba amsa irin ta farko, idan kuma ka cika alkawari muma zamu cika, idan kuma ka kaurace to muma mun isa komai - bama bukatar wani . (sai labarin ya qare za’a fahimci wannan maganr) Sannan bayan haka sai wannan baqin BAWA ya kifar da tukunyar a cikin murhun, kifayen suka qone kurmus suka zama toka baqi, sannan sai wannan BAWA ya juya ya koma daga inda yafito ya bace.. To a nan sai sarkin yayi mamaki matuqa yace" kaai ! wannan Al amarine mai ban al’ajabi, babu shakka akoi wani sirri boyeyye game da wannan kifi, kuma ba’zaiyyu muyi shiru a kai ba, dole muyi bincike akai musan me ke faruwa.. To sai sarki ya bada umurni da aje akawo masa mai kamun kifi, atake akaje aka cincimo mai kamun kifi aka kawo gaban sarki, shikuma mai kamun kifi yana cikin wani hali na tsoro da firgita saboda bai san me ke faruwa ba… To bayan mai kamun kifi ya bayyana a gaban sarki, sai sarkin yacemasa : ya kai mai kamun kifi ! A wani wuri ne kake kawo wannan kifi ??.. sai mai kamun kifi yace : ya mai martaba ina kawo wannan kifin ne daga wani dan karamin tapki ( kogi) da yake tsakanin wasu duwatsu guda 4 da suke bayan wani babban dutse a bayan wannan gari naka, To sai sarkin ya matso kusa da mai kamun kifin yacemasa : tafiyan miniti nawa ne za’a yi kafin a iso wannan tapki – kogi- . .? sai mai kamun kifi yace : tafiyar minti 30 ne kawai ya mai martaba.. Da sarki yaji wannan magana daga wurin mai kamun kifi sai ya kara mamaki matuqa, kuma atake ya bada umurnin a fitar da rundunar sojoji ( askarawa) a shiryasu kuma a dauki mai kamun kifi a saka shi a gaba yaje ya nuna inda yake kamo wadannan kifaye masu launi daban daban,, da mai kamun kifi yaga kansa a gaban rundunar soja ana tafiya dashi sai ya tsorata yana kuka yana La’antar ALMA’RIDU yana tsine masa yace : daa ma ya barni a cikin talaucina… To sai sarkin wannan gari da rundunarsa ta soji sukayi ta tafiya a cikin daji, mai kamun kifi yana gaba yana nuna musu hanya har sai da suka iso wurin wannan dutse suka hau kansa suka sauqa, sannan sai suka tarar da wani daji mai fadin gaske wanda basu taba ganisaba, basu sanda zaman wannan wuri ba duk tsawon rawuwarsu a wannan gari da su da kakanninsu,, sai sarkin yayi matuqar mamaki, haka ma sauran jama’a da askarawa da suke tare da sarki sukayi mamakin ganin wannan daji da basu taba ganinsa a baya ba, basu taba jin labarinsa ba.. To Bayan haka, sai suka cigaba da tafiya, jim kadan sai suka ga wasu duwatsu guda 4, kuma a tsakiyan wadannan duwatsun akoi wani dan karamin tapki – kogi - wanda a ciki akoi kefaye masu (nau’i) da launi - daban daban – har kala hudu.. akoi : FARI JAA SHUDI da kuma KORE duk acikin wannan dan karamin tapki da yake tsakanin duwatsu guda 4.. da sarki yaga haka sai ya qara matuqar mamaki da ganin irin wannan abun al ajabi da bai taba gani ba a rawuwarsa.. To sai sarki ya juya ya kalii ASKARAWANSA da sauran jama’a dake tare da shi, tare da mamaki ya tabayesu yace : shin a cikinku akoi wanda ya taba ganin wannan wuri ko yaji labarinsa ?? gabadayansu suka hada baki sukace : A’ A’ ko kadan.. sai sarkin yace : To wallahi na rantse bazan koma masarauta ta ba har sai nasan hakikanin abunda yake faruwa game da wannan dan qaramin tapi (kogi) da kuma kifayen da suke ciki.. sannan sai sarkin ya umurci jama’a da su koma gefe suyi nesa da dutsen.. To Bayan haka, sai sarkin ya kira wazirinsa suka koma gefe, sai yacewa wazirin nasa : Akoi wani Abu da nakeso inyi shiyasa nakira ingayamaka… sai sarkin yacigaba da gayawa wazirin nasa yace : nayi tunani naga cewa yakamata in zauna anan wurin har zuwa dare – inkwana annan - saboda inaso in gudanar da bincike gameda wannan dan karamin tapki da kifayan da ke ciki, saboda haka ka kawomini KHAIMATA ( kamar daki ko rumfa ) ka kafa mini ita anan, kuma kasanar da dukkan faadawa da hakimai da sauran wazirai cewa sarki yana cikin wani yanayi na damuwa bayaso kowa ya shiga wurinsa, kuma ya umurceni da kar inbar kowa ya shiga wurinsa kuma kar ka sanar da kowa abunda nayi niyyar aiwatarwa…( abunda sarkin ya gawa waziri kenan ) Da waziri yaji wannan magana daga wajen sarki bai iya ya saba umurnin sarki ba, sai ya aiwatar da dukkan abunda sarkin ya bukata… sannan bayan haka sai sarkin ya canza tufafinsa ya badda kamaninsa ya dauki takobinsa ya rataya a kafadarsa ya sulale a tsakanin jama’arsa ya fita batare da kowa daga cikinsu ya sani ba, sai ya kutsa ya shiga daji abunsa … To sai sarkin ya cigaba da tafiya a cikin dajin ALLAH har sai da dare yayi sarki baigusheba yana tafiya har gari ya waye aka shiga dare na 2 gari ya waye sarki baigushe ba yana ta tafiya acikin dajin ALLAH batare da ya hadu da wani mahluuqi ba – ko dabba ko mutum – a cikin kwana na 3 bayan gari ya soma haske sarki bai gusheba yana ta tafiya a cikin daji… jim kadan sai sarki ya hango wani baqin abu daga nesa, sai yayi farin ciki da ganin wannan abun duk da cewa baaisan ko menene ba, To sai yace – a zuciyarsa - : yawwa ! yanzu wataqila ko zan samu wanda zai bani labarin wannan dan karamin tapki (kogi) da kifaye masu launi daban daban da ke ciki !!! to bayan haka, sai ya matso kusa wannan baqin abu da ya gani daga nesa,, bayan ya matso kawai sai ya tarar da wani baban masaurata da aka gina da baqaqen duwatsu da karafuna,, kuma sai yaga kofar wannan masarasuta a bude yake, sai yayi matuqar farin ciki da ganin haka, sannan sai ya matso kusa da kofar ya tseya ya konkosa a hankali, amma babu wanda ya amsa masa, sannan sai ya qara konkosawa karo na 2 da na 3, duk da haka dai bai ji alamun amsa ba, to anan sai ya qara konkosawa da karfi a karo na 4 amma duk da haka bai ji alamun akoi wani aciki ba, babu motsin komai… To sai yace : babu shakka wannan gida babu kowa a ciki, to kawai sai ya kutsa ya shiga ciki yayi ta tafiya har ya iso cikin zaure, sannan sai ya kolla I’hu yace : ya ku masu wannan masarauta ni mutum ne, kuma matafiyi, ina neman taimako, shin za’a samu abinci a wurinku ne ?? ya maimaita wannan magana har sau 3 amma baiji motsin kowa ba.. to sai ya kutsa ya shiga can ciki har sai da ya isa tsakiyar wannan fadar amma baiga kowa ba, amma kuma sai yaga wurin gabadaya anyi shimfida mai kyau, kuma gashi aniyiwa wurin ado da gwalagolai da wasu abubuwan daban na ado.. sai yayi mamaki kuma yaji takaicin rashi samun kowa a ciki wannan fada da zai bashi labarin wancan tapki da kifayen da ke ciki da kuma duwatsun da suka zagaye tapkin,, to kawai sai ya zauna ya rasa abun yi yana tunani, kawai can sai yaji karar nishin mutum daga nesa, kuma a bisa dukkan alamu mai wannan nishi yana ciki wani yanayi na bakin ciki da muwa,, to da yasa hankali ya saurara sai yaji mai wannan nishi ya rairai wannan waka kamar haka. ((Na boye halin da nake ciki na wahala amma ya bayyana)) ((bacci a idona ya juya ya zama rashi bacci)) ((Nayi I’hu na kira bakin cikin da yake ta karuwa da tunani)) (( nace : ya bakin ciki na rokeka kar ka kasance a tareda ni)) ((Yau ga rayuwata tana tsakanin wahala da kuma hadari)) Da sarkin yaji wannan waka atake ya mike tseye ya nufi inda wannan mai waka yake… bayan ya iso wannan wuri sai yaga wata kofa anyi mata sutura da labule, sai ya bude wannan labule, budewarsa ke dawuya sai yaga wani saurayi mai matukar kyawun sura da kamala da jamala yana zaune akan wani gado kuma yana sanye da hula irin ta sarauta yana kuka yana zubar da qolla, kuma akoi alamun damuwa da bakin ciki atare da wannan saurayii. To sai sarkin yayi farin cikin samun wannan saurayi, sai yayi sallama, sai saurayin ya amsa kuma yacewa sarikin : kayi mini uzuri saboda ban tashi na tseya dan girmamaka ba !.. amma sai sarkin ya nuna rashi damuwa. sai sarkin ya tambayi saurayin yacemasa : ya kai saurayi ! kabani labarin wannan dan karamin tapki (kogi) da kifaye masu launi – daban daban - da ke ciki da kuma wannan masarauta mai girma da nasameka a ciki da kuma dalilin da yasa na sameka kai kadai kuma me yasa naga kana kuka kana zubar da hawaye. Da wannan saurayi yaji wannan magana daga wurin wannan sarki sai hawaye suka zubo daga idanunsa suka cika kumatunsa kuma yayi ta yin kuka sosai har saida wannan saki yaji tausayinsa kuma yayi mamaki sosai, to bayan haka sai sarkin ya tambayesa yace : ya kai saurayi me yasa kake kuka ? sai saurayin yace : me yasa bazanyi kukaba ? irin wannan hali da nake ciki ?.. sai saurayin ya mika hannunsa ya daga rigarsa, kawai sai sarkin yaga rabin jikin wannan saurayi gabadaya dutse ne ( daga konkoso zuwa kafarsa ) abunda ya kama daga cibiyarsa zuwa kansa kuma siffar (DAN ADAM) ne. To sai saurayin yacemasa : kasani cewa wannan tapki da kagani yana da labari mai ban al ajabi sosai, kuma akoi darasi ga wanda ya lura. Kuma sai yace : kasani cewa mahaifina shine sarkin wannan babban masarauta da ka gani, kuma sunansa MAHMUD wanda yake mulkar wasu kasashen baqin fata, kuma wannan tapki mai kifaye da duwatsu guda 4 suna cikin masarautarsa ne. kumu yayi mulkain wannan masarauta kimanin shekara 70 sannan sai ya rasu. sai nikuma na gaaji sarautar mahaifina bayan rasuwarsa, sai na auri ‘yar bappa na (kanin baba) kuma takasance tana matuqar sona sosai ta yadda idan na tafi nabarta ita kadai bata iya cin abinci har sai ta ganni, To sai nakasance tare da ita har tsawon shekaru 5, to ananan watarana sai wannan matar tawa – kuma ‘yar bappana – ta fita ta tafi zuwa shagon da ake yin kwalliya (saloon) ta barni a gida, kuma ta umurci mai girki da ya shirya mana abincin dare, to nikuma sai na shigo ciki na kwanta akan wannan gado da ka ganni akai yanzu na yi bacci. To daama matar tawa ta umurci ‘yan mata (kuyangu) guda 2 da suzo wajene suyi mini tausar jiki suke shafar fuskata kafin ta dawo. To sai daya daga cikin yan matan ta zauna akusa da kafafuna, dayar kuma ta zauna kusa da kaina, nikuma a wannan lokaci inacikin matuqar damuwa saboda kasancewar matata batanan ta fita waje, a dalilin haka sai na kasa yin bacci, amma kuma idanuna a rufe suke nayi kamar nayi bacci zuciyata a farke take, wadannan ‘yan mata suna mini tausar jiki sun dauka nayi zurfi a bacci.. To sai naji daya daga cikin ‘yan matan – wanda take zaune a kusa da kaina – tana gayawa ‘yar uwarta – wanda take zaune akusa da kafafuna – cikin kakkausar muriya : ya ke MAS’U’DATU : sai dayar ta juya ta kalli wanda ta kira sunan nata. sai wanda tayi kiran tace : umh mai martaba (sarkin da yake bacci kenan) abun tausayi ne, kuma asararre ne, saboda bai san abunda wannan fitsararriyar matar tashi takeyi ba idan tafita, sai dayar tace : ALLAH ya tsinewa matan aure mazinata, kuma mutum mai daraja da halaye masu kyau kamar mai martaba baidace da wannan mata fitsararriya mazinaciya ba, wanda kullum take zuwa ta kwana da wani kato a waje amma shikuma mai martaba baisani ba, sai wanda take kusa da kansa tace : ai mai martaba baya cikin hankalinsa saboda kinga baya tambayar ina take zuwa.. sai dayar tace : to ai shi baisan abunda yake faruwa ba kuma baisan halinta ba, saboda wannan tsinanniyar matar tashi a kullum da daddare tana saka masa magani a cikin ruwan da yake sha kullum kafin yayi bacci, da zarar ya sha wannan ruwa baya iya sanin abunda yake faruwa, koda yanke naman jikinsa akayi bazai iya saniba, shi yasa bazai san ina take zuwa da daddare ba kuma me takeyi, saboda bayan ta bashi wannan magani yayi bacci sai tayi kwalliya abunta tasaka kaya mai kyau ta fita ta tafi abunta ta je ta kwana da wani kato bazata dawo ba sai bayan sallar asubahi, idan ta dawo saita hada masa wani turaren wuta mai karfi sosai wanda idan hayakin ya shiga hancinsa to sai ya farka, baisan wainar da aka tauna a wannan dare ba, saboda karfin wannan magani da ta bashi ya sha a ruwa. Sai saurayin ya cigaba da bawa wannan sarki labari yace : To bayan na saurari abunda wadannan ‘yan mata suak fada, kawai sai naji duniyar gabadayanta tayi mini matsi, haske ya zama duhu a idanuna saboda tsananin bakin ciki, bansan lokacin da dare yayi ba, kawai sai ga matartawa ta dawo daga shagon da ake yin kwalliya ( beauty saloon). To bayan ta dawo, sai aka kawo mana abincin dare mukaci dani da ita, sai muka zauna muna hira, jim kadan sai aka kawo ruwan da nake sha kafin inyi bacci, kuma daama tariga ta saka magani a ciki kamar yadda ta saba, sai ta dauki wannan ruwa ta mika mini, nikuma sai na karba na dan juya gefe nayi kamar inasha amma bansha ba, jim kadan sai na kwanta nayi kamar nayi bacci mai nauyi, itama ta dauka nayi bacci, sai naji tace : umh kayi bacci sosai kuma wallahi bazaka farka ba har sai gari ya waye, wallahi na tsaneka na tsani mai sonka na tsani ganin siffarka, kuma na tsani kusantarka. To Bayan haka, sai ta dauki rigarta ta saka, ta fesa turare ta dauki takobinta ta rataya a wuyanta ta bude kofar fada ta fita. To niku sai na tashi na bita a baya bata saniba, bata gusheba tana tafiya nikuma ina binta a baya har sai da tashige ta cikin kasuwa ta fita nima ina binta duk inda ta shiga tana ta tafiya har saida ta iso kofar fita daga gari. Bayan ta iso wannan kofa sai tayi wasu maganganu da bana fahimtarsu, sai kofar ta budu, nikuma ina bayanta bata sani ba har sai da ta iso wani gini mai tsawo sannan sai ta shige ta wannan gini, nikuma sai na hau saman ginin ina kallonta daga nesa, kawai sai naga taje tasamu wani (bakin bawa) mai muumunar halitta, bakinsa kamar murfin kwano, duk jikinsa a jike yake, yana kwance akan wasu itatuwa da ciyayi. To Bayan ta iso gabansa sai ta tsunkuyar da kanta ta durkusa ta gaisheshi ta gimamashi, sai shi kuma ya bata rai, ya daka mata tsawa yacemata - cikin fishi da bacin rai - : kaiton ki !.. me yasa kika bata lokaci baki fito da wuriba ? gashi duk abokanaina gabadaya sun hallara a wannan wuri, kowa yana tare da masoyiyarsa amma ni inzaune ni kadai naki naci komai. sai tacemasa : ranka ya dade mosiyana rabin raina, shin bakasan cewa ni matar Aurebane ? kuma dan bappana nake Aure (sarki) ? kuma kaima kasan cewa babu wanda na tsana kamar wannan mijin nawa, ina kyamar ganin mai kama da surarsa, ina nisantar da kai a gareshi, da ba don ina tsoron fishinka ba da na tsafe wannan garin gabadaya, na tarwatsasa, ta yadda zai zamanto babu komai a ciki sai hankaki da tsuntsaye, kuma in kaurar da duwatsun dake cikin wannan gari in kaisu bangon duniya. Sai masoyin nata (wannan bakin bawan.) yacemata -cikin fishi - : ke fitsararriya kariya kike mini, wallahi na rantse daga yau idan kika kara yin jinkiri baki fita da wuri, to ba zan kara abokanta da ke ba, bazan kara hada jikin da jikinki ba, mayaudariyar mace kawai. Sai saurayin (sarkin) ya cigaba da bawa dayan sarkin labari yacemasa : wallahi da naji maganr da matata tayi da wannan bakin bawa kuma ina kallo da idanuna – quru quru – kawai gabadaya sai naga duniyar tazama duhu a idanuna, bansan inda ruhina yake ba. Kuma bayan haka sai naga matar tawa ta tsunkuya tana kuka ta qasqantar da kanta tana rokon wannan baqin bawa tana rarrashinsa akan ya yafemata tana cemasa : ya masoyina rabin raina kayi hakuri, saboda banida wani inba kai ba idan narasaka zan mutu, idan ka koreni to ina zan je ? ya hasken idona dan ALLAH kayi hakuri ! . bata gusheba tana ta kuka tana kasqantar da kanta tana rokonsa har saida ya yarda ya yafemata sannan sai tayi farin ciki ta ji dadi. To bayan haka, sai matar tawa ta tashi tseye ta tube kayanta, tacewa wannan baqin bawa (masoyinta) : ranka ya dade mosoyina ! shin akoi abinci a wurinka ne wanda masoyiyarka zata ci ? sai ya nunamata wani wuri yacemata taje akoi dafaffen qasussuwan beraye ta dauka taci. Bayan ta gama cin abici ta wanke hannu, sai tazo ta kwanta tare da masoyin nata – baqin bawa - a wani lungu, nikuma da naga abunda ‘yar uwata kuma mata takeyi na cin amana a gabana sai nakasa hakuri nayi yunkurin kashesu, su biyu gabadaya. Sai na zaro takobina na soma da wannan bawa da farko, na doke wuyarsa da takobi. To Alokacin da na bugeshi da takobina, sai nayi tsammanin cewar ya mutu….. Naga kamar wasu sungaji da karatu" sai ran juma,a idan Allah yakaimu. Yusuf abdullahi A jibaga. Shike kawo muku wannan lbr dafatan mu kwana lafiya. 06 HIKAYAN MASUNCI DA IFRITU wannan saurayi da aka tsafe – wanda kuma shima sarki ne – ya cigaba da bawa dayan sarkin labari, sai yace masa" A lokacin da na zaro takobi na doke wuyar wannan lalataccen BAWAN saboda in pille masa kayi.sai na yanke fatar wuyarsa da makokoronsa, amma ban raba kayinsa da gangar jikinsa ba, sai yayi gurnani ya numfasa yayi nishi irin ta fitar rai, ya daina motsi, to nikuma sai na zaci cewar ya mutu.. To sai matarwa – ‘yar uwata – tafarka daga bacci, - bayan ni nagudu na barwajaen – kawai sai taga an sare wuyar BAWAN, sai ta dauki wannan takobi da na pille wuyar BAWAN dashi ta boyashi, bayan haka sai ta kama hanya ta shigo gari ta dawo gida a cikin wani yanayi. To Bayan matar tawa ta dawo ta shigo fada jikinta amace, kawai sai ta kwanta akan gadona har zuwa wayewar gari. Daga wannan rana, sai matar tawa ta aske gashin kanta gabadaya tasanya tufafin bakin ciki ( bakin tufafi ) ta soma zaman makokin rashin wannan BAWA da takeso. To bayan haka Sai matar tawa tacemini : ya ‘dan uwana ! kar ka zargeni a bisa abunda kaga nakeyi na zaman makoki, saboda labari ya iso mini cewar mahaifiyata ta rasu, mahaifina ma an kashe shi a wurin JIHADI ( yaki ) haka kuma ‘yan uwana guda 2 daya anyi masa rauni a kayi, dayan kuma gini ya ruso a kansa. saboda haka na cancanci inshga wannan yanayi insanya tufafin bakin ciki, kuma naga ya kamata inyi zaman makoki inyi ta kuka in sanarwa duniya bakin cikin da nake ciki. Da naji abunda matar tawa

Chapter 3 of 4