Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 01 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan sarakuna. Shi ne mafi tsarki daga dukkan abubuwa. Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa kuma Annabinsa, Muhammadu dan Amina (SAW). : Akwai wani mutum tsoho masunci, yana da mata d'aya da 'ya'ya uku, ya kasance talaka ne, bai ajiye abincin yau ba ballantana na gobe. Kullum yakan je kogi ya kamo kifi ya kai kasuwa ya sayar ya sayo abin da za su ci. Yana da wata al'ada mai ban mamaki, duk lokacin da ya tafi su, yakan jefa komarsa sau hud'u ne kawai, daga nan sai ya nad'e ta ya tafi da kifin da ya kama ya sayar, idan ma bai kama komai ba a jefawa hud'un nan, to ba zai yi ta biyar ba, sai dai ya koma gida haka nan, ranar su kwana da yunwa. Wata rana ya fita da Azuhur zuwa ga yankin bahar domin yin su, da ya isa ya shiga cikin ruwa daga bakin gaba, ya jefa komarsa ciki, ya juya ta, ya kuma juyawa, sa'annan ya jawo ta, ya ji ta da nauyi, ya fitar da ita daga cikin ruwa. Ya juye abin da ke ciki, bai ga komai ba face ciyawa. Ya kakkab'e ta ya sake jefawa karo na biyu cikin ruwa, jim kad'an ya jawo ta da kyar saboda nauyi, har rigarsa ta bi ruwa. Koda ya juye abin da komarsa ta d'ebo, bai ga komai na daga kifi ba face mataccen jaki. Da ya ga haka ya yi bak'in ciki, ya ce a ransa babu tsimi babu dabara face daga Allah mai girma da d'aukaka, neman wannan abinci nawa da ban al'ajabi yake, yayin nan ya waka wad'annan baitoci: "Ya mai bayarwa a cikin duhun dare, Ba da dabara ko wayo ba, Na dogara gare ka ya Razzak'u, Kai ke azurta mu ba don k'ok'arinmu ba." Bayan ya gama rera wannan wak'a, ya jefar da mataccen jakin, ya wanke komarsa ya shanya ta, ta sha iska, ya d'auke ta ya shiga cikin ruwa sosai sannan ya jefa ta kashi na uku yana mai cewa Bismillahi. Koma ta nutse cikin ruwa, ya hak'ura har ta nutse sosai. Ya jirkita ta, sannan ya fara jawo ta zuwa tudu, ya ji ta nannauya fiye da jefawar farko da ta biyu, ya yi farin ciki domin ya zaci kifi ne. Koda ya juye abin da ke cikin koma, sai ya tarar da karafuna da matattun tangaram da duwatsu da yashi da laka, babu komai na daga kifi. Yayin da ya ga haka ya yi bak'in ciki mai yawa, ya rera wannan wak'ar: "Ya rayuwar zamanina ki fahimta, Idan ba ki fahimta ba ki yafe ni, Har yanzu ba a ba ni rabona ba, Har yanzu ba a yi hukunci a kaina ba, Na fita bid'ar arzikina na ishe ya k'are, Sau da yawa jahili yakan ga abin b'oye, Sau da yawa ilimi kan b'ace wa Malami." Masunci ya zubar da tarkacen da komarsa ta kwaso, ya wanke ta, ya nemi gafara ga Allah bisa wannan wak'a da ya yi. Da komar ta sha iska ya d'auke ta ya shiga cikin ruwa, wannan karon ya kutsa nesa cikin ruwa, ya d'aga kansa sama ya ce, ya Ubangiji ka sani cewa ba ni jefa komata fiye da sau hud'u a rana, na jefa sau uku ban sami komai ba, Allah ga ta hud'u kuma ta k'arshe zan jefa, ka nufe ni da samun abin da zan ci, ni da iyalina. Ya ambaci sunan Allah, ya jefa komarsa karo na hud'u. Bayan ya dad'e yana juya ta, sai ya jawo ta zuwa tudu, wannan karon ta fi koyaushe nauyi. Da ya fito da ita da kyar, ya juye abin da ke ciki, babu komai face yashi da wata yar batta (kwalba) k'arama, ta farin k'arfe, girmanta bai wuce a saka ta a cikin aljihu ba, an lik'e bakinta da darma, an buga hatimin Annabi Sulaimanu a saman murfin. Yayin da masunci ya ga wannan batta, ya yi farin ciki ya ce wannan na sayar da ita a kasuwar farin karfe dinari goma, in sayi abin da za mu ci. Ya sa hannu d'aya zai d'auki batta, ya ji ta da nauyi, hannunsa d'aya ya kasa d'aukar ta. Ya yi mamaki da wannan abu, ya ce babu makawa in bude ta in ga abin da ke ciki, in zazzage shi cikin jaka, sannan in sayar da battar a kasuwa. ya zare wuk'a, ya b'amb'are murfin darma daga batta, ya ajiye shi gefe a kan k'asa. Ya girgiza batta domin ya ji abin da ke ciki ko yana motsi, sai ya ga hayak'i na fitowa yana yin sama. Masunci ya cika da mamaki, ya yi tsaye yana kallon ikon Allah. Da hayak'i ya gama fita, ya tattaru wuri d'aya a sama, sai ya juye ya zama Ifiritu, kansa yana cikin gajimare, k'afafunsa cikin k'asa. Girman kansa kamar d'aki, bakinsa tamkar kogo, hak'oransa kamar duwatsu, k'ofofin hancinsa tamkar ibirik', idanunsa ja wur kamar garwashin wuta, damuttsan hannuwansa kamar ginshik'i, k'afafunsa kuwa tamkar bishiyoyin kuka. Wannan Ifiritu ya kasance mafi daud'a da k'ura cikin halittu. Yayin da masunci ya ga wannan irin halitta, gab'ob'insa suka yi sanyi, yawun bakinsa ya k'afe, ya kasa motsawa daga inda yake. Da Ifiritu ya ga masunci sai ya ce, babu Sarki madawwami sai Allah, na shaida Sulaimanu Annabin Allah ne kuma Manzonsa. Ya Annabin Allah kada ka kashe ni, na rantse da Allah ba ni koma sab'a wa umurninka. Muryar masunci na rawa don tsoro ya ce, "Ya kai wannan maridi, kana tsammanin a gaban Annabi Sulaimanu kake? Bayan ya rasu da shekara dubu d'aya da d'ari takwas, ka sani yanzu muna k'arshen zamani ne. Ka labarta mini wanene kai? Menene sanadiyyar shigarka wannan batta?" Koda Ifiritu ya ji zance masunci sai ya ce, "Babu Sarki sai Allah, hak'ik'a ka faranta mini ciki ya kai wannan dan Adam, da sannu zan saka maka da abin da ka yi mini." Masunci ya fara murna ya ce, "Da me za ka saka mini?" Aljani ya ce "Da kashe ka a cikin wannan sa'a, muguwar kisa." muyutumin yace " yanzu wannan shine abunda zakamini albishir dashi, kuma menene nayi dazan chanchanci kisa ? me nayi dazaka kasheni ? NI da nataimaka maka nafito dakai daga cikin wannan kogi, kuma naciroka daga cikin wannan tulu natsirar dakai daga halaka wannan shine sakamakona ?... sai aljani (almaridu) yacemasa : kazabi kalar kisanda zanma saboda kana batamini lokaci… sai mutumin yace : wani zunubine na aikata da zaka sakamini da wannan mumunan sakayya ? sai (Almaridu) yacemasa : kafin inkasheka bari inbaka labarina tukuna… sai maikamun kifin yacemasa : inasauraranka kuma kataqai labarinnaka saboda yanzu zuciyata tabuga… sai aljani (almaridu) yace : kasani cewa : ni nakasance dagacikin aljanu (ma’riqai) wato - masu taurin kai - wadanda sukabijirewa umurnin ALLAH da manzonsa kuma suka kafircewa ALLAH.. kuma nasabawa annabi (sulaimana) dan annabi (da’wuda) dani da aljani maisuna (sakhru) To sai annabi (sulaimana) ya aikamini wazirinsa maisuna (a’sifu dan barkhiya) yakamani adole yakawoni wajan (annabi sulaimana) ya tsayardani agabansa aqasqance.. da (annabi sulaimana) yaganni sai yarazana yace : (A uzu billahi) saboda munin halittata.. daganan sai (annabi sulaimana) umurceni da inyi I’MANI da ALLAH kuma inshiga qarqashin ikonsa, (wato – inyiwa annabi sulaimana DA’A) To nikuma sai nayi taurin kai naqi amincewa… To sai (annabi sulaimana) yasa aka kawomasa wannan tulun yasakani aciki yamanne bakin tulun, yabuga tambarinsa da suna maigirma, sannan sai yasa akajefani cikin (teku) kogi, nikuma sai nakasance acikin kogin har tsawon shekara 100, sai nace - acikin zuciyata - : duk wanda yazo yafitardani daga cikin wannan kogin acikin shekaru 100 to zan arzuqtashi har abada.. amma babu wanda yazo yafitardani dagacikin wannan kogi, sai nacigaba da zama aciki har nakai shekaru 200 bangusheba inaciki, to anan sai nace : duk wanda yazo ya fitardani zan budemasa taskokin duniya gabadaya.. amma babu wanda yafitar dani, sai nacigaba dazama aciki har shekaru 400 suka shude bangusheba inaciki.. bayan haka sai wasu shekaru 400 daban sukazo sukashude sai nace : duk wanda ya fitardani a wannan lokacin to zan biyamasa buqatu guda 3… amma babu wanda yafitar dani daga cikin wannan teku.. To daganan kawai sai nayi fishi mai tsanani nace : - acikin zuciyata - duk wanda yazo a wannan lokacin to zan yimasa mumunan kisa, kuma zan bashi dama yazabi kalar kisanda zanmasa.. To yau gashi kazo kafitar dani saboda haka zan kasheka kamar yadda nayi alqawari.. da wannan maikamun kifin yaji wannan labari sai yacemasa : to ai ni ALLAH baibani damarda zan fitardakai daga wannan kogi ba sai a wannan lokacin… saboda haka kayi hakuri kar kasheni ALLAH zaimaka afuwa, idankuma ka kasheni to ALLAH zaikawo wanda zai halakaka kaima.. amma sai (almaridu) yace karka batamini lokaci kasheka babu makawa.. kawai kazabi kalar kisanda zanmaka… Da maikamun kifin yatabbatar cewa (almaridu) zai halakashi, sai yaqara durqusawa yaroqeshi yacemasa : kayimini afuwa saboda karamcin tsirar dakai danayi.. sai (almaridu) yace : To ai nima zan kashekane saboda tsirardani da kayine… sai mutumin yacewa (almaridu) ya dattijon aljanu shin zan maka alheri kaikuma kasakamini da sharri ? sai (almaridu) yacemasa : karkasa tsammanin zaka rayu inajiranka kazabi kalar kinsanda zan maka .. To anan sai mai kamun kafin yatseya yaiy tunani - acikin zuciyarsa – yace : wannan aljanine, niku DAN ADAM ne, kuma ALLAH yabani hankali cikekke, saboda haka zanshirya wata dabara saboda inhalaka wannan aljanin kafin ya halakani.. bayan yagama tunaninsa sai yacewa (almaridu) : shin bakagusheba har yanzu kanada ra’ayin kasheni ? sai (almaridu) yace : e’h inakan ra’ayina.. sai mutumin yace : dan darajar suna maigirma wanda aka rubuta akan zoben (annabi sulaimana) inason inyimaka wata tambaya kuma inafata zakabani amsa daidai.. da (almaridu) yaji an ambaci ( suna mai daraja ) sai yaji dadi ya girgiza kanshi yace : kayi tambayarka kuma kataqaita zan amsamaka.. sai mutumin yace : taya ka kasance cikin wannan dan karamin tulu, bayan kuma ko hannunkama bazai iya shiga cikin wannan tulu ba ballema kafafunka ?.. yaya akayi tulun ya daukeka ?... sai (aljani almaridu) yace : shin baka yardabane daga cikin wannan tulu nafito ? sai mutumin yace : bazan taba yardaba sai nagani da idona quru quru.. MUHADU RANAR LARABA MISALIN 9 PM DONCI GABA INSHA ALLAHU02 HIKAYAR MASUNCI DA IFRITU wannan mai kamun kifi (masunci) yacewa ALJANI ALMA'RIDU : ba zan taba yarda da maganarka ba, har sai nagani - quru quru – da idanuna ka koma cikin wannan tulu kamar yadda ka kasance a ciki da farko... Atake sai (alma'ridu) ya kumbura ya cika, sai yazama hayaqi, kuma hayaqin yanufi sararin samaniya, sannan sai ya shiga cikin tulun kamar yadda ya kasance a ciki dafarko. . To da mai kamun kifi yaga haka sai yayi sauri ya daukko murfin wannan tulu – wanda aka manna tambarin (annabi sulaimana) ajiki - sai yarufeta (kirip).. sai yaqira sunana aljani (alma’ridu) yacemasa : ya kai matsiyaci la’nanne kazabi kalar kisan da zan maka… zan jefaka cikin wannan kogin..., kuma daga yau dinnan zan gina gidana anan wurin, duk wanda yazo wannan kogin zai kama kifi zan hanashi, kuma zan sanar dashi cewa : acikin wannan kogin akoi wani aljani la’nanne (ALMA'RIDU) duk wanda ya fitar dashi daga cikin wannan kogin sakamakonsa shine : zai bashi zabi ya fadi kalar kisan da zai masa.. -inji mai kamun kifi yake gayawa ALJANI ALMA’RIDU.. Da ALMARIDU yaji abunda mai kamun kifi yafadamasa, sai yayi qoqarin fitowa daga cikin tulun, amma sai yaji – inaa – bazai iyaba, saboda an rufeta da murfi mai tambarin zoben (annabi sulaimana).. Anan sai ya tabbatar da cewa wannan mai kamun kifin ya shiryamasa tarkon da bazai iya kubuta daga cikintaba.. shikuma mai kamun kifi sai ya dauki wannan tulu ya nufi kogi da ita, daniyyar zai jefata a ciki.. sai ALMARIDU yayi I’hu yace : A’A dan ALLAH kar ka aikata haka !! .. sai mai kamun kifi yace : ai babu makawa sai na maidaka inda kafito da farko… da ALMARIDU yaji haka sai ya yafirgita ya zama abun tausayi, ya qasqantar da kansa, ya soma lallabar mai kamun kifi.. sai mai kamun kifin yacemasa : zan jefaka cikin wannan kogi.. idan har kakasance ka zauna a ciki har tsawon shekaru 1800 To yanzu zan mayar da kai ka cigaba da zama a ciki har zuwa ranar da za’a buusa qaho - tashin qiyama -.. kuma koda na mutu zanbar wasiya ga mutanen da zasu zo nangaba.. Mai kamun kifin yacigaba da cewa : kuma shin dazu ban rokekaba nacemaka : kayimini afuwa kar ka kasheni kaima ALLAH zai maka rahama ?, amma sai kaqi saurarata, kayi kunnene uwar shegu kaso ka ha’inceni ? sai gashi ALLAH yasa yanzu ka fada a hannuna…? sai ALMARIDU yace : dan ALLAH ka yimin rai, ka fitar dani, wallahi idan ka fitar dani to zan kyautata maka.. sai mai kamun kifi yacemasa : karya kake tsinanne… Ai irin abunda yafaru tsakanina da kai, kamar irin abunda yafaru da wazirin wani sarki da ake kira (SARKI YUUNA’N) da kuma wani mutum da ake kira (HAKIM DAUYAN) sai ALMARIDU yace : manene yafaru tsakanin wazirin sarki da HAKIM DAUYAN ? sai mai kamun kifi yacemasa : kasani cewa : a zamanin da yagabata, antaba samun wani sarki a qasashen FARISAWA (iran) da ROMAWA (italy) mai suna sarki (YUUNA’N).. kuma wannan sarki yakasance yanada dukiya mai dunbin yawa, dakuma rundunoni na soji masu yawan gaske.. kuma masarautarsa tana da fadin gaske, kuma yanada muqarrabai da sauransu… A wani bangaren kuma.. wannan sarki ALLAH ya jarrabeshi da cutar BARAS (zabya) wanda likitoci da masu hikma suka kasa warkardashi… dukiyar da sarautarsa basu iya sun anafanar dashi ba… haka kuma magunguna da yaka anfani dasu basu tsinana masa komaiba aka… babu wani daga cikin lilitocin wannan gari dama wasu qasashen daban da ya iya warkar dashi.. To ananan.. wata rana sai wani mutum – tsoho – da ake kira (HAKIM DAUYA’N) ya shigo wannan gari – wato garin sarki yuunan – kuma wannan mutumi ya kasance yanada ilimi sosai.. ya karanta litatafai na al’ummomi da dama, ya karanta littatafan mutanen YUUNAN (girka) da FARISA (iran) da RUUM (italy) da LARABAWA da sauransu.. kuma yayi fice afannin likitanci da ilimin taurari da abinda yashafi ‘ya’yan itatu masu anfani da masu cutarwa, kuma shehun malamine abangaren falsafa, (philosophy).. a taqaice dai, babu wani bangare na ilimi da bayyi fice aciki ba.. To bayan wannan mutumi ya shigo wannan gari, sai yaji labarin wannan sarki, da kuma irin matsalarr dake damunsa - na cutar BARASI - ( zabiya ) kuma babu wani daga cikin likitaci da ya iya warkar da shi.. Da wannan mutumi yaji wannan labari, sai ya soma lissafi da tunanin yadda zai samu damar isa wurin wannan sarki saboda ya jarraba iliminsa da qorewarsa ta likitanci kuma ya samu karbuwa a wurin wannan sarki.. Wayewar gari kedawuya, sai HAKIMU ya sanya kayansa, ya kama hanya yanufi gidan sarki, kuma ya samu damar shiga cikin fada.. bayan ya shiga sai ya gaishe da sarki ya girmama shi, yayi masa ADDU’A da fasahar harshe, sannan sai ya gabatar da kansa yace : ya mai martaba naji labarin irin abunda ke damunka - na cutar BARASI - (zabiya), kuma naji labari cewa likitoci sun kasa warkar da kai, basu san yadda zasu rabaka wannan cutarba, shiyasa yau nazo saboda in warkar da kai, ba tareda na baka magani kasha ba, ko ka shafa ba… Da sarki YUUNA’N yaji abunda wannan mutumi yafada, sai yayi mamaki matuqa kuma yacemasa : ta yaya zaka iya warkar dani.. ?? wallahi idan ka warkar dani zan baka dukiyar da zaka anfana da ita dakai da jikokinka.. kuma zan yimaka ni’ima, kuma duk abunda kakeso zan baka shi, kuma zaka kasance daga cikin mafi kusa dani, masu cin abinci tare dani, zan nunamaka so da qauna… Daganan sai sarkin ya dauko wata kyauta ya miqawa HAKIMU saboda jindadin abunda ya zo dashi.. kuma sai sarkin ya qara tambayarsa yacemasa : shin zaka iya warkar dani daga wannan cutar ba tareda na sha magani ko na shafa ba… ?? sai HAKIMU yace : tabbas babu shakka zan iya warkar da kai, batare da wata wahala ba… sai sarki yayi mamaki matuqa, kuma yacemasa : To yanzu da yaushe zaka soma wannan aiki.. ? sai HAKIMU yacemasa : gobe zan soma aiki ya mai martaba… Daganan sai HAKIMU yafice daga fadar sarki, yaje yakama gidan haya, yazuba littatafansa da kayan aikinsa da sauransu... sannan sai yaciro kayan aikinnasa da magungunasa.. bayan haka sai yaqera wata sanda ‘yar karama irin ta sarakuna, yayi mata mariqi… sannan a wani bangaren kuma yaqera qollo - kamar qollon (ball) - … bayan ya gama, washe gari sai yanufi gidan sarki, yaje ya masa bayanin yadda zayyi… ya ‘umurceshi da yashiga babban fili, wanda dawakai suke tsukuwa a ciki, sannan sai ya soma wasa da wannan qollo, yana bin qollon yana dukansa yana gudu batareda ya tseyaba… A lokacin da HAKIMU yashigo fadar sarki, ya sameshi tare da waziriransa da manyan gari gabadaya suna shawarwari gameda al’amura da suka shafi masarauta.. amma duk da haka, da sarki YUUNA’N yaga HAKIMU yashigo ya miqa masa sanda da qollo, sai yatashi yabar abunda yakeyi.. To sai HAKIMU yacemasa : kashiga babban fili, sannan sai ka wurga wannan qollon, kayita tabinsa kana duukansa da sandar daqarfi, kuma koda kagaji kar ka tsaya har sai kayi gumi, tafin hannunka ya jiqe da gumi, idan kayi haka to maginin da yake jikin sandar zai shiga cikin jikinka ya soma aiki.. bayan haka sai ka koma gida kayi wanka, ka kwanta kayi bacci, daganan zaka warke.. Sai sarki yayi dukkan abinda HAKIMU ya gayamasa… bayan yagama sai ya sanar da HAKIMU, sai HAKIMU ya ‘umurceshi da ya koma fadarsa yayi wanka batareda bata lokaciba.. To sai sarki ya koma yayi wanka ya chanza tufafinsa… wannan shine halin da sarki YUUNA’N ya kasance a ciki… Amma shikuma HAKIMU DAUYA”N bayan yakoma gida ya kwanta, washegari sai ya nufi gidan sarki, da isarsa sai yanemi izinin shiga fada, bayan yashiga sai ya tsunkuyar da kansa yayi gaisuwa, kuma ya yabi sarki YUUNA’N da baitoci.. bayan yagama yabon sarkin, sai shikuma sarkin yatashi ya tseya da kafafunsa ya rungumi HAKIMU kuma ya zaunardashi akusa da kujerarsa ta sarauta, kuma yayi masa kyautar alkebba da wasu keututtukan daban.. Bayan sarki yafito daga wanka, kawai sai yaga fatar jikinsa takoma kamar ta kowa, babu sauran BARASI (zabya) ajikinsa,, yayi matuqar farin ciki da haka, hankalinsa yakwanta… Da gari ya waye, sai sarki YUUNA’N yashiga fadarsa yazauna, waziransa da muqarrabansa sun bayyana a fada, sai ga HAKIMU ya shigo, da sarki ya gansa sai ya tashi cikin sauri yarungumeshi ya zaunardashi agefensa,, sannan sai ya bada ‘umurni aka kawo abinci sukaci tare.. shikuma HAKIMU yana cike da farin ciki saboda yadda sarki yake karramashi fiye da kowa acikin fadar.. HAKIMU baigusheba yana tare da sarki har zuwa faduwar rana… sannan sai sarki yabashi DINARI 2000 da wasu keututtuka daban, sannan da HAKIMU ya tashi tafiya sarki ya rakashi ya daurashi kan dokinsa,, sannan sai sarki ya dawo gida yana matuqar mamakin irirn yadda HAKIMU ya warkar dashi,, kuma yace : (acikin zuciyarsa) wannan mutumin ya warkar dani daga cutar dake damuna batareda ya shafamini magani ba, wallahi wannan ba karamin baiwa bace, kuma ya zama wajibi akaina in keutatawa wannan mutumin in daukeshi in kusato dashi, in daukeshi abokin hirana har tsawon rawuta.. sannan sai sarki ya kwana cikin farin ciki .. Da gari ya wa’ye… sarki yafito fada, wazirai da hakimai dakuma manayn gari kowa yabayyana a fada.. sai sarki yasa aka kirawo HAKIMU.. To bayan HAKIMU ya shigo, sai ya gaida sarki,, shima sarkiN ya tashi saboda girmama HAKIMU.. ya zaunar da shi yasa aka kawo abinci sukaci tare kuma sarkin ya keutatata masa.. sannan da yamma tayi sai yabashi keututtuka daban daban har guda 5 ya hadamasa da DINARI 5000 sai HAKIMU yakoma gida abunsa yana mai farin ciki da godiya.. Washegari sarki ya taho fadarsa.. wazirai da ha’kimai da manyangari sun kewayeshi.. To daga cikin waziran sarki YU’NAN akoi wani waziri da ya kasance bashida hali mai kyau, yanada matuqar muuni, bashida kyan gani, mai yawan tsangoma da zargi, kuma mai hassada, marowaci, annamimi, dasauransu…. Da wannan waziri yaga cewa sarki yana kyautatawa HAKIMU, kuma ya kusantar dashi ya daukeshi tamkar aboki fiye dasu, sai yasoma HASADA, ya shirya masa makirci da mugunta.. To anan sai wata rana wannan waziri ya gabato ya matso kusa da sarki YUUNA’N ya yayi gaisuwa ya yabi sarki, sannan sai yace : ya mai martaba idan ka amince inada NASIHA da nakeso inyi maka, saboda idan nayi shiru ban gayamaka wannan nasihar ba, to babu shakka zan kasance munafiki, kuma kamar (‘DAN) da aka haifa daga zina… idan ka amince inbayyana maka nasihar to zan bayyana… sai sarki yacemasa ( tareda mamakin irirn kalaman da suke fita daga bakin wannan waziri ) : menene nasihar da kakeso kayi ? kafada inasauraronka ? sai wazirin yace : ya mai martaba : masu magana sukace : duk wanda bayyi nazari yayi tunani ya hankalta acini duk abunda yakeyiba, to duniya ba abokiyarsa bace… saboda nalura naga sarki yana kan kuskure, saboda irin kyautatawa da yakewa dan adawarsa, kuma wanda yake qoqarin qwace masa sarautarsa… hakika ka kyautatamasa sosai har ya wuce iyaka.. kuma ka kusantar da shi sosai ya wuce misali.. Ni ina fargabar kar yayi maka juyin mulki… Da sarki yaji wannan maganar daga wajen wannan waziri, atake sai yafirgita launinsa ya chanza yamike tseye yace". wacce irin magana kake fada ne ? wanene kake ganin zai zama abokin adawata? kuma na kyautatamasa har na wuce gona da iri ? sai wazirin yacemasa : ya mai martaba idan bacci kake to ka farka.. ba kowa nake zargi ba sai HAKIMU DAUYAN… sai sarki yace : A’A wannan abokina ne, kuma yafi kowa mutunci a idona… sabodamutum ne mai ilimi da hikma sosai, kuma ya warkar dani daga cutar da babu wani likitan da ya iya warkar dani, ba tareda ya bani magani na sha ko shafa ba, babu mutum kamarsa a wannan zamani – gabar da yamma – saboda haka banga dalilin da yasa kake fadin wannan magana gameda wannan bawan ALLAH, kuma - bugu daqari ma – daga yau dinnan na yanke shawar sanyamasa albashi, a qarshen kowani wata yanada DINARI 1000… kuma abunda wannan bawan ALLAH yamini koda ace na raba masarautata kashi biyu na basa kashi daya, to ban biyashi ba, abunda nabashi yayi kadan… Ni dai kawai inganin HASADA kake masa,, kamar yadda labarin wani sarki mai suna ( sindi bado ) ya iso mini… sai waziri yace : wanene kuma sarki ( sindi bado ) kuma menene labarinsa ?? sai sarki yace : an rawaito wani labari cewa…….. Akoi wani sarki daga cikin sarakunan FARISAWA (iran) wanda ya kasance yana matuqar son shaqatawa da yin farauta adaji, kuma wannan sarki yakasance yanada wani TSUNTSU da ya horarar dashi kan al’amuran farauta kuma baya rabuwa da wannan TSUTSU dare da rana ya saba da shi, kuma koda zai kwanta bacci ma tare suke suke kwana, da rana kuma yana yawo dashi a hannunsa duk inda zai je, yasaba dashi kamar dan uwansa, kuma ya ratayamasa wani dan qarmin qorya na goal a wuyarsa, kuma wannan TSUNTSU yana taimaka masa sosai wajen farautar namun daji.. Toh ananan watara sai lokacin tafiya farauta yayi, sai sarikin ya shirya ya dauki wannan TSUNTSU a hannunsa suka fita suka nufi daji, da shi da muqarrabansa masu tayashi farauta, to bayan sun isa.. sai suka dana (suka shirya) tarkonsu na farautar namun daji… (kuma tarkon nasu ya kasance kamar wata igiyace aka daura a jikin sanduna,, sai aka zagaya ta yadda idan dabba ta shiga ciki ba zata iya fita ba,, sai dai idan tayi tsalle ta tsallaka wannan igiya to sai tasumu kubuta,, kuma duk da haka mutane zasu kewaye wannan wuri da aka sa igiya aka killace ) to jim kadan sai ga wata BAREWA ta danno kai, sai ta fada cikin wannan tarko,, sai suka tashi suka kewaye ta,, sai sarkin yacewa wadanda suke tare dashi suke tayashi farauta : duk wanda wannan BAREWAR ta gudu ta bangarensa to za’a kashe shi, har ma dani sarki.. sai suka amince da haka.. to sai kowa ya dau damara saboda kar BAREWAR ta gudu ta bangarens a kashe shi… to sai

Chapter 1 of 4