Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
muke manya ba mu san mahaifinka ba. Mun dai san cewa Sarki ya aurar da mahaifiyarka ga wani wada mai kusumbi, ranar tarewar mahaifiyarka, aljanu suka daure mai kusumbi a cikin lambu, wani daga cikin aljanun ya auri mahaifiyarka har aka sami cikinka. Duk fadin Misira babu wanda ya san mahaifinka, babu kuma wanda ya taba ganinsa. Lalle idan ba ka sanar da su ko wane ne ubanka ba, ba su kara wasa da kai." Ko da Ajibu ya ji zancen Malaminsu sai ya nufi gida yana kuka, ranar ko karatun bai tsaya yi ba. Ajibu ya isa gida wurin mahaifiyarsa yana kuka, ta yi lallashin duniyar nan amma ya ki yin shiru. Ta tambaye shi dalilin kukansa, ya kwashe dukkan abin da ya faru tsakaninsa da yara ya fada mata. Ya kuma fada mata abin da Malaminsu ya fada masa, sa'annan ya dube ta ya ce, "ya mahaifiyata, ki fada mini wanene mahaifina?" Ta ce da shi, "Waziri shi ne mahaifinka." Ya ce da ita, "kada ki yi mini karya, ya mahaifiyata. Waziri mahaifinki ne, ni kuma kakana ne. Wallahi idan ba ki fada mini ko wanene mahaifina ba, to zan kashe kaina da wannan dutsen!" Ya dauki wani babban dutse ya rike ga hannunsa. Yayin da Sittul Hassana ta ji ambaton Hassan Badaruddin, uban Ajibu. Ta tuna da kyawunsa, da abin da ya faru tsakaninsu a daren amrcinta. Soyayyarsa ta motsa a cikin zuciyarta, ta waka wadannan baitoci: "Kun motsa mini so kwantacce cikin zuciyata. Kun taso shi amma kuma gida ya nesanta gare shi. Hankalina ya jirkita domin nesanta tasa daga gare ni. Da, na hakura da rashin ganinsa amma yanzu kun tashe ni. Kun raba ni da farin ciki yanzu babu zama a gare ni. Hawayen idona sun gudana domin tuna rabuwa tamu. Hawayena sun zama tamkar kogi domin bege a gare shi. Na yi begen in gane shi begensa yakan dadu hakuri yakan takaita. Na misalta ganinsa a cikin zuciyata ina bege irin na so da zumunci. Ya wanda ambatonsa shi ne wakata ya wanda nake jin dadi idan na tuna shi. Yaushe za ka dawo gare ni yaushe ne wannan jinkiri zai yanke." Da ta gama rera wannan waka, sai ta fashe da kuka. Danta Ajibu ma ya yi kuka tare da ita. Suna cikin wannan hali sai ga Waziri ya shigo gidan. Yayin da ya tarar da su suna kuka, sai ransa ya baci, zuciyarsa ta sosu, ya tambaye su dalilin kukansu. Sittul Hassana ta labarta masa abin da ya sami danta a makaranta duka. Waziri ya yi shiru yana tunani, ya tuna da dan uwansa Nuruddin, ya tuna abin da ya faru a tsakaninsu. Ransa ya baci, zuciyarsa ta motsa, nan take ya yi kudirin zuwa birnin Basara wurin dan uwansa Nuruddin da kuma neman mijin 'yarsa kuma uban Ajibu, watau Hassan Badaruddin. Nan take Waziri ya fita daga gidansa ya nufi fada wurin Sarki. Ya fada wa Sarki cewa ya yi niyyar fita zuwa Basara neman dan uwansa da kuma mijin 'yarsa. Ya nemi Sarki da ya rubuta masa takarda zuwa ga Sarkunan da zai keta ta cikin biranensu domin su tare shi da girmamawa idan ya shiga biranen nasu. Sarki ya rubuta masa takardu kamar yadda ya bukata, suka yi ban kwana da juna. Waziri ya koma gida domin fara shirye-shiryen tafiya. Waziri ya hada dukkan abin da za su bukata a wurin wannan tafiya, ya debi bayi da kuyangi, sa'annan ya tafi tare da 'yarsa, Sittul Hassana, da jikansa Ajibu. Suka kama hanya suka nufi Basara. Kwanci tashi, bayan sun yi tafiyar kwana uku, sai suka isa birnin Damashka. Suka gan shi birni ne ma'abocin koramu da itatuwa. Waziri ya yi umurni da a sauka a huta kwana biyu kafin a ci gaba da tafiya. Suka sauka a bayan gari, a wuri mayalwaci, suka kafa tantina, suka sauke kayansu. Waziri ya ba bayi da kuyangi dama, duk mai so yana iya shiga cikin gari domin bude idonsa, ko sayen wani abu da yake bukata. Bayi suka warwatsu cikin birni domin kashe kwarkwatar idanunsu. Wasu suka nufi dakin baki, wasu suka nufi kasuwa, wasu suka nufi masallacin Juma'ar Banu Umayyata, wannan wanda babu tamkarsa a cikin duniya. Ajibu kuwa sai ya shiga gari tare da wata kuyanga, suka yi ta yawo cikin gari kwararo-kwararo, sako-sako, yana rike da wata bulala ta bugun rakumi, yana wasa da ita ga hannunsa. Yayin da mutane suka ga Ajibu, da irin kyawun da Allah ya yi masa, da cikar halittarsa, da daidaito, da kwarjini, da haiba. Sai suka rika bin su a baya, suna kallon Ajibu. Ajibu da kuyanga suka ci gaba da zagaya gari har kaddara ta sa suka iso wurin rumfar mai sayar da abinci, wanda ya riki Hassan Badaruddin a matsayin dansa. Yanzu da ya fara tsufa, sai ya daina fitowa rumfar, ya sakarwa Hassan ragamar tafiyar da kasuwancin abinci. Aka kuwa yi gamo da katar, lokacin da su Ajibu suka iso daidai wurin rumfar, lokacin kuma Hassan ya fito daga cikin rumfar. Hassan ya dubi Ajibu, Ajibu ma ya dubi Hassan. Nan take sai soyayyar juna ta shige su, suka yi tsaye suna kallon juna. Hassan ya yi al'ajabi da kyawun Ajibu, ya fada a cikin ransa, "ya kaiton kaina! Wa zai mallaka mini wannan yaro a matsayin dana? Wallahi zuciyata ta so shi, raina na begen shi." Nan take hawaye suka karyo masa ba tare da ya sani ba. Sa'annan ya ce da Ajibu, "ya shugabana, ina rokonka da ka faranta mini rai, ka shiga wannan rumfa tawa ka ci daga wainar da na toya ta kwayar ruman." Yayin da Ajibu ya ji zancen Hassan, ya juya zuwa ga kuyangarsa ya ce, "wannan mai sayar da abinci, zuciyata ta so shi. Kuma ga alama yana cikin damuwa na wani abu mai muhimmanci da ya rasa. Mu shiga rumfarsa, mu ci abincinsa, mu faranta masa rai, watakila sanadiyyar haka Allah ya sa mu hadu da abin da muka fito nema." Kuyanga ta ce, "ya shugabana, wannan abu bai kamata ba. Kaka dan Waziri kamarka zai ci abinci a cikin rumfar sayar da abinci, wannan ba girmanka ba ne. Ka sani cewa an hada ni da kai ne domin in tsare ka daga aikata abin da bai kamata ba." Da Hassan ya ji zancen kuyanga, ya waiwaya wurinta, idanunsa na zubar da hawaye, ya ce mata, "zuciyata ta so shi, ku yi hakuri ku faranta mini ciki da cin abincina." Kuyanga ta ce, "ka bar wannan zance, domin ba mai yiwuwa ba ne." Hassan ya yi ta rarrashin kuyanga, har ta ji tausayinsa. Ta riki hannun Ajibu, suka shiga cikin rumfa. Hassan ya yi musu shimfida mai kyau, ya dauki kwanuka ya zuba musu waina ta 'ya'yan ruman hade da wake. Ya zuba musu mai a wani wuri daban, ya kuma zuba zuma a wani wurin na daban, a wani wurin kuma ya zuba musu miya cike da nama. Hassan ya ce musu, "kada ku yi gaggawa, ku ci a cikin nutsuwa da tsanaki. Cewa gaggawa tana daga cikin aikin Shaidan." Ajibu ya ce, "ai sai ka zauna mu ci tare da kai, mai yiwuwa Allah ya hada mu da wanda muka fito nema albarkacin wannan haduwa tamu." Hassan ya ce masa, "ya shugabana, shin kai ma ka hadu da bakin cikin rabuwa da masoya ne, duk da karancin shekarunka?" Ajibu ya ce, "na'am ya baffana. Raina na cike da bakin cikin rabuwa da mahaifina, wanda tunda aka haife ni ban san shi ba. Shi ne muka fito nema, ni da kakana da mahaifiyata, har yanzu Allah bai nufe mu da saduwa da shi ba. Ka yi mana addu'a bisa ga wannan bukata tamu." Yana gama fadin haka sai hawaye suka zubo daga idanunsa. Hassan ya tausaya masa, ya yi musu addu'a Allah ya sa su hadu da wannan mutum da suka fito nema. Suka ci abinci tare, har ya ishe su. Daga nan sai suka fita daga rumfar Hassan, suka nufi bayan gari inda masukinsu yake. Ko da suka fita daga cikin rumfar, sai Hassan ya ji kamar ransa ne yake fita daga jikinsa. Ya ji wani sabon bakin ciki ya lullube shi. Ya ji cewa sam ba zai iya jimirin ganin wannann kyakkyawan yaro ya tafi ya bar shi ba. Nan take ya rufe rumfar abinci, ya bi bayansu, bai san cewa wannan yaro dansa ne ba. Ajibu da kuyanga suka nufi masaukinsu, Hassan na biye da su a baya. Kafin su fita daga kofar birni, sai kuyanga ta waiwaya baya ta ga Hassan na biye da su. Suka tsaya har ya iso wurinsu. Kuyanga ta ce, "me ya same ka, ya kai mai waina?" Hassan ya ce, "Wallahi lokacin da kuka fita daga cikin rumfata, sai na ji kamar raina ne ya fita. Shi ya sa na rufe rumfar. Ina so in tafi tare da ku bayan gari in sha iska ko na ji sauki a cikin raina." Kuyanga ta ce, "wannan abinci naka ya zama shu'umi, daga mun shiga rumfarka mun ci abinci sai ka rika bin mu a baya? Wannan ai fallasa ne, wanda zai sa duk mutane su gane cewa mun ci abinci a rumfarka." Ajibu ya yi fushi da Hassan, ya ce masa, "ka tafi zuwa ga bigirenka, ka daina bin mu." Suka juya suka tafi, suka bar Hassan nan a tsaye. Bayan sun fita daga kofar gari, Hassan ya ci gaba da bin su. Da Ajibu ya waiwaya ya gan shi, sai ransa ya baci sosai. Ya duka ya dauki dutse ya jefi Hassan da shi. Dutse ya sauka bisa goshin Hassan, ya ji masa ciwo har jini ya fito. Ajibu da kuyanga suka bar Hassan nan tsaye dafe da goshi, suka tafi da sauri har suka isa inda tantinansu. Shi kuwa Hassan ya juya ya koma zuwa ga rumfarsa. Ya yanki kyalle daga rawaninsa, ya daure wurin da Ajibu ya jefe shi. Ya zargi kansa da kansa, ya ce a ransa, "ni na zalunci kaina, yayin da na fita daga cikin rumfata na bi su, har suka yi mini mummunan zato." Ya zauna yana mai tunanin halin da mahaifiyarsa take ciki a birnin Basara. SANARWA. Zamu dan dakata dawannan hikya zuwa ranar alhamis me zuwa saboda dalilin dan gajiya dakuma yawan aiki dayawa takuramun a wannan satin afuwan ,yan.uwa daga naku yusuf a jibaga This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4