Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
wannan bawa mummuna zai zama mijinki? Sarki ya yi jinga da shi ne dinari goma, ya zama kamar shi ne mijinki, domin kawar da hankulan jama'a, kuma a yi dariya. Da ni aka daura miki aure ba da shi ba. Tuni ma har an biya shi kudin jingarsa, ya tafi gida." Koda Sittul Hassana ta ji wannan zance, sai ta lumshe idonta don farin ciki, ta ce, "Ya masoyina, abin begena, ka taso ka kusance ni, ni taka ce, na mallaka maka dukkan kaina. Nan take Hassan http://fb.com/waziriaku ya tashi, ya riki hannunta ya ja ta kan gado, ya kashe fitila, duhu ya mamaye dakin. Suka yi kwance bisa gado suna masu rungumar junansu. Hassan ya same ta cikakkiyar budurwa, wadda ta tsare kanta da mutuncinta, waninsa bai taba kusantar ta ba. Suka kasance cikin wannan yanayi na soyayya, har barci ya dauke su. Shi kuwa ango mai kusumbi, yayin da ya shiga cikin lambu domin ya ji sanyi a ransa, sai ya sami wuri ya zauna yana tunani. Can sai ya ga wani dan bera ya fito daga cikin rami. Sai ya ji beran nan ya buda baki ya ce, "Zayyik!" Mai kusumbi ya tsorata, ya ce, "Me ya kawo wannan bera cikin lambu?" Daga nan sai bera ya kara girma ya http://fb.com/waziriaku zama kyanwa. Sai kuma ya kara girma ya zama kare, ya dubi mai kusumbi ya yi masa haushi, "Uh! Uh! Uh!...." *** Za mu ci gaba gobe insha allahu08. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Ango mai kusumbi kuwa, yayin da ya shiga cikin lambu domin ya ji sanyi a ransa, sai ya sami wuri ya zauna yana tunani. Can sai ya ga wani dan http://fb.com/waziriaku bera ya fito daga cikin rami. Sai ya ji beran nan ya buda baki ya ce, "Zayyik!" Mai kusumbi ya tsorata, ya ce, "Me ya kawo wannan bera cikin lambu?" Daga nan sai bera ya kara girma ya zama kyanwa. Sai kuma ya kara girma ya zama kare, ya dubi mai kusumbi ya yi masa haushi, "Uh! Uh! Uh!...." Nan take mai kusumbi ya firgice, yana cewa, "Yau na hadu da http://fb.com/waziriaku shu'umi." Kare ya kumbura ya kara girma, ya zama jaki. Mai kusumbi ya fara kururuwa yana cewa, "Ina mutanen gidan nan, ku kawo mini agaji." Ya zabura sai sheka da gudu, sai jaki ya juye ya zama bauna, ya tare masa hanya. Bauna ta yi magana da harshen 'yan Adam, ta ce, "Kaicon ka ya kai wannan wada! Don me ka auri abar sonmu? Da sannu za mu kuntata maka, mu mayar da kai kasa!" Mai kusumbi ya fadi bisa ga gwiwowinsa, bakinsa na rawa, yana cewa, "Wallahi ba ni da laifi, tilasta ni aka yi, ba cikin son http://fb.com/waziriaku raina ba. Ni ban san tana da masoya ba a cikin namun daji, na tubar wa Allah, na tubar muku. Wallahi ba ni koma kula ta, Allah ya la'anci duk wanda ya yi sanadiyyar aura mini ita." Daga nan sai mai kusumbi ya ji an suri duga- dugansa, an juyar da shi, kansa a kasa kafafunsa a sama, aka rataye shi ga reshen bishiya. Sa'annan ya ji an ce masa, cikin wata kakkausar murya, "Ka tsaya kamar haka, ina nan ina gadin ka har zuwa fitowar rana. Da zarar na ji ka furta http://fb.com/waziriaku wata kalma guda, zan kashe ka. Idan ka ga rana ta fito, ka sauka daga wannan bishiya, ka kama gabanka. Kuma idan na ga ka kalli kofar dakin amarya, yayin da za ka fita, zan yi maka azaba mai tsanani." Aljani ya bar shi nan ya fita. Yayin da aljani ya fito daga cikin lambu, sai ya hadu da aljana, suka tafi tare, suka shiga dakin da Hassan da Sittul Hassana suke kwance a ciki. Da shigarsu, sai suka kunna fitilar dakin, suka iske su kwance suna barci, fuskokinsu suna http://fb.com/waziriaku kallon sama. Hassan ya cire rigarsa da wando da hularsa, ya ajiye su can gefen gado, daga shi sai wata riga 'yar ciki. Ita kuwa Sittul Hassana in ban da wani dan mayafi babu komai a jikinta. Aljanun nan suka kura musu ido suna kallon su. Aljani ya ce, "Ya shugabata, yanzu kin gani da idonki cewa wannan yarinya ta fi http://fb.com/waziriaku wannan saurayi kyau ko?" Aljana ta ce ita faufau bata yarda ba, saurayin shi ne ya fi kyau. Suka yi ta gardama a tsakaninsu, kowa yana nuna wa dan uwansa abin da yake gani mai kyau a jikin Hassan da Hassana har alfijiri ya fara ketowa. Daga nan sai aljana ta ce,"Mu yi sauri mu http://fb.com/waziriaku dauki wannan saurayi mu mayar da shi inda muka dauko shi kafin gari ya waye." Nan take aljana ta dauki Hassan yana barci suka tashi sama da shi, suka bar yarinya Sittul Hassana tana barci. Aljanu suna cikin tashi da Hassan, kafin su kai birnin Basara, sai Allah ya kaddari aka jefi aljani da tauraro na wuta, ya kone nan take. Aljana na ganin haka, sai ta yi http://fb.com/waziriaku kasa ta sauke Hassan daga wajen kofar wani birni, ta kada cikin iska ta yi tafiyarta. Wannan birni ya kasance birnin Damashka ne, na kasar Sham. Hassan yana nan kwance a bakin kofar shiga birni, yana barci, har gari ya waye, rana ta fito, aka bude kofofin birni. Mata suka fito daga cikin birni za su tafi rafi dibar http://fb.com/ waziriaku ruwa, sai suka ga Hassan kwance a bakin kofa yana barci. Koda suka gan shi, suka lura da irin kyawunsa, da kuma irin yanayin da yake ciki, na rashin isassun tufafi a jikinsa, sai wasu daga cikinsu suka ce, "Kai amma duk macen da wannan kyakkyawan saurayi http://fb.com/waziriaku ya kwana wurinta, cikin daren da ya gabata, lalle ta more. Kaiconsa da bai tsaya sanya tufafinsa ba." Wasu kuma suka ce, "Da ganinsa irin 'ya'yan masu mulki ne, wadanda ke aikata http://fb.com/waziriaku yadda ransu yake so ga talakawa. Watakila daga mashaya ya fito, giya ta buge shi ya fadi nan har bacci ya dauke shi. Watakila ma wajen caca ya salwantar da tufafinsa. Amma an yi hasarar kyau wannan wuri, tunda babu hali na gari." Haka dai matan nan suka yi ta zancensu na son zuciya a kan halin da suka tarar da Hassan Badaruddin a ciki. Can sai iska ta kada, 'yar rigar da ke jikin Hassan http://fb.com/waziriaku ta yaye, tun daga cinyoyinsa har zuwa saman cibiyarsa suka bayyana. Nan fa hankulan matan nan ya tashi a kan kyawun Hassan da ya kara bayyana. Kadawar wannan iska shi ya tayar da Hassan daga barcin da yake yi, ya ga mata sun kewaye shi suna kallo, kamar http://fb.com/ waziriaku masu kallon wata halitta ta daban. Ya yi sauri ya gyara rigarsa da iska ya kwashe, ya dube su ya ce, "Don Allah a ina nake nan? Me ya sa kuka taru nan kuna kallo na? Shin me ya faru gare ni?" Suka ce masa, "Mu, mun fito daga cikin birni muka gan ka yashe a nan kana barci, bayan wannan ba mu san kome ba game da kai. Ina ka tafi cikin daren jiya, http://fb.com/ waziriaku har aka rufe kofa kana wajen birni?" Hassan ya sake duba wurin da yake, da mutanen da suka kewaye shi, ya cika da mamaki, yana tunanin shin me yake faruwa ne? Ya dube su ya ce, "Ku sani, ni na kwana a birnin Misira cikin daren da ya gabata." Koda matan nan http://fb.com/waziriaku suka ji haka sai suka fashe da dariya gaba daya, wata daga cikinsu ta ce, "Ko dai ka kwana cikin ciyawa?" Wata kuma ta ce, "A'a, a birnin Sin ya kwana fa." Suka sake fashewa da dariya, su a ganinsu, Hassan mahaukaci ne. Daga nan sai wata daga http://fb.com/waziriaku cikinsu ta ce, "Ga alama dai kai mahaukaci ne, duk da muna ganin ka kyakkyawa. Da kaka mutum zai kwana Misira sa'annan ya wayi gari yana Damashka, in ba zancen hauka ba?" Hassan ya ce, "Ni ba zan yi muku karya ba har abada, shekaranjiya na http://fb.com/waziriaku kwana a birnin Basara, jiya kuwa na kwana tare da amaryata a birnin Misira." Da jin haka sai wannan ta kalli waccan, waccan ta kalli wannan, suna taba hannu suna rike baki, wata daga cikinsu ta ce, "Oh, kun ji abun mamaki, ba makawa wannan saurayi mahaukaci ne, ko kuwa shaye-shayen da ya yi ne bai sake http:// fb.com/waziriaku shi ba har yanzu?" Wasu kuma suka rika tausaya masa suna cewa, "Ya hasarar kyawunsa, wallahi babu makawa ga haukansa." gobe zamu daura insha allahu 9pm. bar kanku da juma,a via ajibaga09. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Da mata suka ji zancen Hassan na cewa jiya ya kwana a Misira kuma shekaranjiya yana Basara, sai wannan http://fb.com/waziriaku ta kalli waccan, waccan ta kalli wannan, suna taba hannu suna rike baki. Wata daga cikinsu ta ce, "Oh, kun ji abin mamaki, ba makawa wannan saurayi mahaukaci ne, ko kuwa shaye-shayen da ya yi ne bai sake shi ba har yanzu?" Wasu kuma suka http://fb.com/waziriaku rika tausaya masa suna cewa, "Ya hasarar kyawunsa, wallahi babu makawa ga haukansa." Da hassan ya ji haka, sai ya ce, "Ni, Hassan Badaruddin wallahi na kasance ango a daren jiya cikin birnin Misira." Da matan nan suka ga Hassan dai ya nace da zancensa, kuma suka http://fb.com/waziriaku lura da cewa ga dukkan alamu ba mahaukaci ba ne, sai suka ce masa, "To watakila dai abin da kake fadi cewa ka kwana Basara shekaranjiya, jiya kuma ka kwana Misira kana ango, duk mafarki ne." Hassan ya ce, "Wallahi ba mafarki ba ne, idan mafarki ne ina wando na da http:// fb.com/waziriaku rigata da hulata? Ina jakar kudin da na karba daga hannun Bayahude? Kuma ina mai kusumbi?" Da Hassan dai ya ga alamar har yanzu ba su yarda da shi ba, sai ya tashi ya shiga cikin gari. Ya bi wani kwararo yana tafiya, da yara suka gan shi haka, rabi http://fb.com/waziriaku tsirara, sai suka dafo masa baya, sun ga wani sabon mahaukaci. Hassan ya ci gaba da tafiya cikin wannan kwararo har ya iso rumfar wani namiji mai sayar da abinci. Da yaran nan suka ga Hassan ya tsaya wurin rumfar mai sayar da abinci sai duk suka watse, kowa ya kama gabansa. Mai http:// fb.com/waziriaku wannan rumfa ya kasance tsohon soja ne, duk garin manya da yara, kowa tsoransa yake ji saboda fadansa. Bayan ya yi ritaya daga aikin soja ne ya bude rumfar sayar da abinci a cikin birnin Damashka. Ya kasance babu wani abinci daga cikin rumfunan sayar da abinci da ke birnin Damashka da ya kai na rumfarsa gyaruwa da dadi. http://fb.com/ waziriaku Lokacin da Hassan ya shiga cikin rumfa, mai abinci ya dube shi, nan take kwarjininsa da kyawonsa suka dimautar da shi, son Hassan ya darsu a cikin zuciyarsa, ya ce, "Daga ina ka fito ya kai wannan saurayi? Fada mini labarinka, domin ni ban taba ganin mutumin da ya yi mini kwarjini ba kamar ka." Hassan http://fb.com/ waziriaku ya zauna ya labarta wa mai abinci labarinsa, tun daga farko har karshe. Mai sayar da abinci ya yi mamaki da jin wannan labari, matukar mamaki, sa'annan ya ce, "Ya dana, hakika wannan labari naka abin al'ajabi ne, zancenka bakon ji ne. Ka boye wannan labari naka ga kowa har Allah ya biya maka bukatar zuciyarka. Ka zauna nan tare da ni http:// fb.com/waziriaku , tunda Allah bai nufe ni da samun haihuwa ba, zan rike ka tamkar dana, amma fa sai idan ka yarda." Hassan ya ce da shi, "ka aikata tamkar yadda kake so, za ka same ni mai biyayya a gare ka." Mai sayar da abinci ya yi farin ciki da jin haka, nan take ya fita zuwa kasuwa. Ya sayo wa Hassan sababbin tufafi masu kyau da tsada. http://fb.com/waziriaku Bayan Hassan ya yi wanka, ya saka tufafi, sai mai sayar da abinci ya riki hannunsa suka tafi wurin alkali. Bayan ya fada wa alkali abin da ya faru tsakaninsa da Hassan, ya nemi da a rubuta masa takardar shaidar cewa Hassan ya yarda da zama tamkar dansa. Alkali ya tambayi Hassan idan ya amince da haka, Hassan ya ce ya amince http://fb.com/ waziriaku . Alkali ya rubuta takarda ya ba mai sayar da abinci. Tun daga ranar kowane mutum da ke cikin birnin Damashka ya san cewa Hassan yana zaman tamkar dan mai sayar da abinci ne. Hassan ya zauna rumfar mai sayar da abinci yana taimakonsa wurin karbar kudi, wani lokaci har ma da dafa abinci. Amma abin http://fb.com/waziriaku da ya faru ga amarya Sittul Hassana shi ne, bayan ta farka daga barci, lokacin da gari ya waye, ta duba ba ta ga angonta ba, sai ta yi zaton ya shiga makewayi ne domin yin wanka, don haka sai ta suturta jikinta, ta zauna zuwa wani lokaci tana jiransa. Tana nan zaune fuskarta cike da annurin farin cikin amarcinta, sai http://fb.com/ waziriaku ga mahaifinta, Waziri Shamsuddin, ya fado cikin gidan babu ko sallama. Yana cike da bakin cikin abin da Sarki ya yi masa, yana cewa a cikin ransa, "Wallahi idan har wannan yarinya ta yarda ta ba da kanta ga wannan mummunan bawa, mai kusumbi kuma wada, babu makawa sai na kashe ta." Ya iso gaban kofar http:// fb.com/waziriaku dakinta ya kwankwasa, ya ce, "Ya Sittul Hassanu." Ta amsa masa, bayan ta gane muryarsa. Ta tashi ta nufi kofar daki, fuskarta cike da farin ciki. Bayan ta bude kofa, sai ta durkusa har kasa ta gaishe da mahaifinta, tana murmushi, fuskarta na haske. Da Waziri ya gan ta cikin wannan hali sai fushinsa ya karu a kan fushi, ya daka mata tsawa yana cewa, "Kaiconki ya daddauda! Ashe har za ki yi farin ciki http://fb.com/waziriaku bisa ga auren wannan mai kusumbi?" Da Sittul Hassana ta ji haka, sai ta sunkuyar da kanta kasa ta yi murmushi, sannan ta ce, "Bayan mutane sun gama yi mini dariya a kan auren mai kusumbi, wanda bai ko yi tsawon yatsan hannun mijina ba, Wallahi a cikin raina http://fb.com/ waziriaku ban kwana a wani dare mafi kyawo daga daren da na kwana jiya ba. Kada ka ba ni tsoro da mutumin da kuka hada ni da shi domin a yi dariya. Ba ni so kana ambata mini wannan mai kusumbi, ya mahaifina." Yayin da Waziri ya ji wannan zance daga 'yarsa, sai fushinsa ya karu, idanunsa suka kada suka yi jawur, ya ce mata cikin tsawa, "Wannan wane irin zance ne kike fada mini? Cewa http://fb.com/ waziriaku mai kusumbi ya kwana tare da ke shi ne mafi kyawun dare a gare ki? Kaiconki!" Da Sittul Hassana ta ji abin da mahaifinta ya fada, sai ranta ya fara baci, ta ce da shi, "Don Allah ka daina ambaton wannan mai kusumbi gare ni. Allah ya la'ance shi! Allah ya la'anci ubansa! Ba na so ko sunansa in ji ana http://fb.com/ waziriaku ambata a gabana. Kun dai dauko shi haya ne domin a yi dariya, a kan kudi dinari goma, an kuma biya shi ya kama gabansa. Ina shiga daki na tarar da mijina ya na jira na. Shi ne wanda ya raya buki, ya wadata mahalarta da jan dinari. Ni na kwana a http://fb.com/waziriaku cikin kirjin mijina, mai tattausar fata, mai fararen idanu, mai jajayen kundukuki." Da Waziri ya ji haka sai fuskarsa ta yi duhu, zuciyarsa ta yi zafi tana tafarfasa, ya ji kamar ya kashe ta. Ya ce mata, "Wai ina hankalinki ya tafi ne? Ko kina cikin maye ne? Tun wuri ki koma cikin hankalinki, babu wanda kika kwana da shi sai mai kusumbi!" Sittul Hassana ta fara magana cikin bacin rai, ta ce, "Wallahi da hankalina ras! Ya mahaifina, ka fara ba ni tsoro, ko wani abu ne ya same ka http://fb.com/waziriaku har ka manta da wannan shiri da kuka yi da Sarki? Tun da aka biya mai kusumbi ya tafi, bai komo ba. Ka jira yanzu mijina zai fito daga makewayi, sai ka tabbatar da abin da nake fada maka." Waziri ya dubi 'yarsa ya ga dai da hankalinta, kuma bai ga alamun maye tare da ita ba, kuma ya san ba ta taba fada masa karya ba. Saboda haka sai http://fb.com/waziriaku fushinsa ya ragu, ya yanke shawarar ya jira har wanda 'yar tasa take kira da mijinta ya fito, ya gan shi. Sai ya nufi lambu domin ya jira fitowarsa daga makewayi. Waziri na shiga cikin lambu, sai ya hangi mutum yana reto bisa reshen bishiya, kafafunsa a sama, kansa a kasa. Da ya matsa kusa da mutumin sai ya ga mai kusumbi ne. Waziri ya dimauta da ganin haka, ya yi magana yana cewa, "Shin wannan ba http://fb.com/waziriaku shi ne mai kusumbin da Sarki ya aurar da 'yata gare shi ba?" Mai kusumbi bai mayar da jawabi ba domin yana zaton aljani na nan kusa yana kallon shi. gobe zamu daura insha allahu10. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Lokacin da Waziri ya yi wa mai kusumbi magana, sai http://fb.com/waziriaku mai kusumbi ya yi kurum, bai mayar da jawabi ba, domin yana jin tsoron watakila alajani na nan na kallonsa. Waziri ya yi masa tsawa, ya ce, "yi magana, idan kuwa ka ki, yanzu in yanke kanka da wannan takobi." Mai kusumbi ya ce, "ya shugaban aljanu, Wallahi tun da ka ajiye ni nan, ko kaina ban motsa ba balle in yi magana. http://fb.com/waziriaku Na roke ka don Allah ka ji tausayina." Yayin da Waziri ya ji zancensa sai ya ce, "Me kake fada ne? Ni ne mahaifin amaryarka da aka daura maka aure da ita jiya. Ni ba aljani ba ne, fada mini menene yake faruwa? Sa'annan ka kama tafarkinka." Mai kusumbi ya ce, "ina ba ka shawara da ka bar wurin nan tunda wuri, kafin wanda ya ajiye ni nan ya dawo. Ashe kun san cewa 'yarku tana da masoya cikin aljanu kuka aurar http://fb.com/ waziriaku mini da ita? Ina rokon Allah ya la'ani wanda ya aura mini ita." Da Waziri ya ji zancen mai kusumbi sai mamaki ya kara rufe shi, al'amarin duk ya daure masa kai. Ya dubi mai kusumbi da ke reto, ya ce masa, "sauko ka fita daga wannan wuri." Mai kusumbi ya ce, "ni mahaukaci ne da zan bi umurninka ba tare da wanda ya ajiye ni nan ya ce in tafi ba. Ba zan http://fb.com/waziriaku fita daga nan ba sai rana ta fito, kamar yadda ya ba ni umurni. Duba mini ma ka gani shin rana ta fito? Kai ko ma ta fito ba zan tafi ba sai na gan ta nan da idona." Waziri ya tambaye shi, "shin wa ya kawo ka wannan wuri?" Mai kusumbi ya ce, "ni na shigo da kaina domin in ji sanyi a cikin raina, daga nan sai na ga bera ya fito mini. Beran ya girma ya zama kyanwa. Kyanwa ta girma ta zama kare, yana yi mini haushi. Kare kuma ya zama jaki. Jaki ya zama http://fb.com/ waziriaku bauna. Shi ne ya rataye ni a wannan wuri, ya ce kada in fita daga nan sai rana ta fito. Kai ma ina ba ka shawara da ka tafi kafin ya dawo ya same ka. Allah ya la'anci wannan amarya da wanda ya yi sanadin aura mini ita." Waziri ya matsa kusa gare shi, ya sa hannu ya taba shi. Mai kusumbi ya fado, kansa ya bugi kasa. Ya tashi ya zura a guje yana waige-waige har ya fita daga gidan, ya nufi gidan Sarki. Yayin da Waziri ya ga mai kusumbi ya zura a guje, ko http://fb.com/waziriaku waiwaye ba ya yi, sai ya koma wurin 'yarsa yana madimauci bisa wannan abu da ya gani. Waziri ya ce da ita, "ya 'yata, na gama ki da Allah ki yaye mini wannan bakon al'amari da na gani. Ina wannan saurayi da kika ce kin kwana http://fb.com/ waziriaku da shi?" Sittul Hassana ta ce, "hakika saurayin da na kwana tare da shi a cikin wannan dare, zuciyata ta kamu da son shi, so mai tsanani. Ka sani cewa bayan fitarka daga wannan daki, na leka makewayi amma ban ga wannan saurayi ba. Amma ga wandonsa, da rigarsa, da hularsa can bisa gado, idan har ba ka yarda da zancena ba." Lokacin da Waziri ya ji zancen 'yarsa, sai ya wuce cikin dakin ya nufi wurin gado inda Hassan ya bar kayansa. Waziri ya dauki hular ya juya ta, ya sake juya ta a hannunsa, ya dubi 'yarsa ya ce, "wannan ai irin hular Wazirai ce." Ya sa hannu ya dauko wandon Hassan, sai ya ji wani http://fb.com/waziriaku abu mai dan nauyi- nauyi kunshe a cikin wandon. Ya fitar da abin da ke da nauyin, sai ya ga jaka ce ta kudi. Ya zazzage kudin ya kirga, ya ga dinari dubu uku ne cif-cif. Tare da kudin kuma ya ga takarda, ya warware takardar sai ya ga an rubuta: Ni Hassan Badaruddin dan Waziri Nuruddin na mallaka wa Wannan Bayahude dukiyar mahaifina da ya tafi fatauci da ita dukkanta, a matsayin ladar fataucin da ya dade yana http://fb.com/ waziriaku yi wa mahaifina shekara da shekaru. Da waziri ya karanta wannan takarda, sai ya yi kururuwa da karfi, daga nan sai ya fadi kasa sumamme. Bayan Waziri Shamsuddin ya farfado daga suman da ya yi, ya kara karanta takarda, ya yi al'ajabi ya ce, "babu Sarki sai Allah mai iko bisa ga kome, mai aikata yadda ya so." Sa'annan ya dubi 'yarsa ya ce, "Shin kin kuwa san wanda ya kwana tare http://fb.com/waziriaku da ke a daren jiya?" Yarinya ta ce, "a'a." Waziri ya ce, "shi dan dan uwana ne, Nuruddin. Ke da shi 'yan baffanni kuke. Shi ne wanda na riga na yi alkawarin aura masa ke, amma sai Sarki ya nuna mana karfin iko ya ba da ke ga mai kusumbi ba tare da yardata http://fb.com/ waziriaku ba, kuma ba tare da ya bayar da sadaki ba. Amma kin ga wannan jakar kudin, ita ce sadakinki ta daga dan dan uwana, Allah ya kaddara ya turo shi wurinki da ita domin halasta saduwarku. Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Kaiton sanina, da kaka na yi muwafaka da wannan hukunci." Yayin nan Waziri ya dauko ratayen layun Hassan yana dubawa, sai ya lura da wata laya daya wadda ta sha banban da sauran. To da ma ya san al'adar kasarsu ta boye sako a cikin laya. Da ganin wannan layar ta sha banban http:// fb.com/waziriaku da saura, sai ya sa hannu ya farke ta, sai ya ga takarda nannade da tsumma. Ya warware takarda ya karanta. A ciki ya ga labarin da dan uwansa ya ba Hassan tun daga haihuwarsu, da kuruciyarsu, da sanadiyyar fitowarsa daga gida har ya isa Basara. Da yadda ya zama Wazirin Basara, da ranar da ya yi aure da ranar da http://fb.com/waziriaku aka haifi Hassan, duk suna rubuce a cikin takarda. Waziri Shamsuddin ya yi lissafi ya ga ranar da ya yi aure ta yi daidai da ranar da dan uwansa ya auri 'yar Wazirin Basara, ranar kuma da aka nada shi Wazirin Basara. Ya yi lissafin ranar da aka haifi Hassan ya ga ta yi daidai da ranar da aka haifi Sittul Hassana. Waziri ya http://fb.com/waziriaku cika da farin ciki, ya kwashe dukkan labari ya fada wa 'yarsa, sa'annan ya kwashi takardu ya nufi fada, domin ya sanar da Sarki wannan labari mai ban al'ajabi. Da zuwansa fada, bayan ya yi gaisuwa ga Sarki, ya duka ya fede wa Sarki biri har wutsiya, sa'annan ya ba shi takardu ya karanta. Sarki ya yi matukar mamaki a kan wannan al'amari, wanda Allah ya kaddara burin wadannan 'yan uwa http://fb.com/waziriaku a kan 'ya'yansu ya tabbata. Ya roki Waziri gafara bisa ikon da ya nuna masa a kan 'yarsa. Waziri ya gafarta masa, Sarki ya sa aka rubuta wannan labari da ruwan zinariya bisa ga takarda, aka ajiye shi domin na baya su karanta ko za su karu da darasin da ke ciki. Ita kuwa 'yar Waziri, Sittul Hassana, sai ya kasance ta dauki ciki a wannan http://fb.com/ waziriaku dare da Hassan ya kwana da ita. Waziri da 'yarsa suka zauna zaman jiran dawowar Hassan. Da Waziri ya ga kwanaki na ta http://fb.com/waziriaku shudewa Hassan bai komo ba, sai ya ce a ransa, "Wallahi sai na aikata wani abu wanda wanina bai taba aikata irinsa ba." gobe zamu daura 11. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Waziri Shamsuddin ya ce a ransa, Wallahi sai na aikata wani abu, wanda wanina bai taba aikata irinsa ba. Yayin nan ya dauko takarda da tawada, ya rubuta dukkan yadda tsarin gidan da Hassan ya kwana da 'yarsa Sittul Hassana yake. Hatta rigar Hassan da hularsa da wandonsa, duk sai da Waziri ya rubuta su yadda Hassan ya bar su a gidan. Ita kuwa 'yar Waziri, ta ci gaba da renon cikinta har ya kai wata tara. Da lokacin haihuwa ya yi, ta hai fi danta namiji, kyakkyawa mai kwarjini da farin jini kamar ubansa. Aka yanke masa cibiya, aka yi masa wanka, aka shafa masa kwalli ga makyabtansa. Da ranar suna ta zagayo aka rada masa suna Ajibu. Aka bayar da shi ga mai shayarwa. Tun ranaku na shudewa zuwa makonni, makonni na komawa watanni, watanni na rikide zuwa shekaru, a hankali har yaro ya shekara bakwai. Lokacin da Ajibu ya shekara bakwai, sai kakansa, Waziri Shamsuddin, ya damka shi a hannun wani Malami, domin ya koyi karatun Alkur'ani mai girma da kuma hukunce-hukuncen addinin musulunci. Ajibu ya ci gaba da karatu a hannun Malami, tsawon shekara hudu, sai dai ya tashi a matsayin yaro mai girman kai. Kodayaushe ya kan riki bulala yana bugun yara 'yan uwansa yana zaginsu, yana cewa, "Duk a cikin ku, wa ya kai tamkar ni? Ni ne dan Wazirin Misira gaba dayanta." Da yara suka ga Ajibu ya matsa musu da bugu da zagi, sai suka kai kararsa wurin Malaminsu. Yayin da Malami ya ji karar yara zuwa gare shi, sai ya ce, "bari in sanar da ku abin da za ku rika ce masa ku yi maganinsa, ai wata magana ta fi bugun bulala zafi. Duk lokacin da ya kara yi muku alfahari da sarauta, kuma ya nemi ya yi wasa tare da ku, ku ce ba za ku kara yin wasa da kowa ba sai wanda ya fadi sunan mahaifiyarsa da mahaifinsa." Yara suka shirya bisa ga maganar Malaminsu. Washe gari da yara suka hadu wurin karatu, kafin Malaminsu ya fito, sai Ajibu ya fara zagin su yana yi musu alfahari da cewa shi dan Wazirin Misira ne. Daga nan wani yaro daga cikin yaran ya ce, "idan an gama karatu yau, ba za mu yi wasa da kowa ba, sai wanda ya fadi sunan mahaifiyarsa da mahaifinsa." Can sai wani yaro ya mike tsaye ya ce, "sunana Majidu, sunan uwata Ulwiya, sunan ubana Izzuddin." Wani ma ya tashi ya fadi sunansa da na uwarsa da na mahaifinsa. Wani ma ya yi haka. Daga nan sai Ajibu ya ce, "sunana Ajibu, sunan uwata Sittul Hassana, sunan ubana Shamsuddin, Wazirin Misira." Sai yara suka dauka gaba daya, Waziri ba mahaifinka ba ne, shi mahaifin mahaifiyarka ne, lalle mu ba za mu yi wasa da kai ba yau, sai ka fada mana sunan mahaifinka. Ran Ajibu ya baci, ya fasa kuka. Yara kuwa suka yi ta yi masa dariya da shegantaka, suna cewa, "eho! wani bai san ubansa ba sai kakansa." Suna cikin wannan hayaniya sai ga Malaminsu ya shigo. Ajibu ya kai karar yara gaban Malaminsu, ya kwashe duk yadda aka yi ya shaida wa Malam. Malamin ya ce masa, "gaskiya ne, ka sani cewa ko mu da

Chapter 3 of 4