Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
zan fada maka, ka dauke su da muhimmanci." Nuruddin ya wasici dansa da ya zamanto mutum mai yawan ibada da neman gafarar Allah madaukakin Sarki, ya kasance mai ladabi da girmama na gaba da shi, ya zama mai rikon alkawari da amana, ya kasance mai tausayi da adalci. Ya yi ta yi masa nasihohi a kan neman lahira, zaman finite da kuma sha'anin mulki. Daga nan sai ya tuna da dan uwansa Shamsuddin, da abin da ya faru tsakaninsu har ya bar gida. Hankalinsa ya tashi, ya yi kewar dan uwansa, da garinsu, ya fashe da kuka. Bayan ya gama kuka, ya dubi dansa ya ce, "Ka sani ya dana, ina da dan uwa mai suna Shamsuddin, shi ne Wazirin birnin Misira, bappanka ne. Na rabu da shi, na bar gida ba da yardarsa ba. Ina so ka dauko takarda da tawada in labarta maka abin da ya faru tsakaninmu duka, ka rubuta." Hassan ya tashi ya dauko takarda da tawada ya kawo. Waziri Nuruddin ya kwashe duka labarinsa da dan uwansa Shamsuddin, yadda suka tashi tun suna yara, da yadda mahaifinsu ya mutu suka gaji sarautarsa ta Wazirin Misira, da yadda suka rika raba karagar Wazirtaka tsakaninsu, da niyyarsu ta hada 'ya'yansu aure wdda ta jawo gardamar da har Shamsuddin ya yi masa gorin Wazirtaka wanda ya sa shi fushi ya bar garin, duk ya fada wa Hassan, shi kuma yana rubutawa. Sa'annan kuma ya fada masa yadda ya iso Basara, da yadda ya auri 'yar Wazirin Basara, da ranar da aka yi auren, ranar da ta yi daidai da ranar da aka nada shi Wazirin Basara, da ranar da aka haifi Hassan, duk ya fada wa Hassan, wanda shi kuma ya rubuce komai cikin takarda. Nuruddin ya ce da dansa, "Ka kiyaye wannan takarda, duk tarihinka da asalinka yana cikinta, ko bayan raina idan mutanen wannan birni sun juya maka baya, domin ni ina jin tsoron zamani, to ka nufi Misira ka nemi bappanka. Idan ka gaishe shi, ka sanar da shi ko kai wanene. Ka fada masa cewa na mutu bako a garin wasu ina mai tsananin begensa, ya gafarta mini laifin da na yi masa." Hassan ya nade takarda cikin wasu tsumma masu kyau, ya yi laya da ita, ya saka ta cikin damarun layunsa. Ya kasance yana kuka, domin yana ganin kamar ubansa ya kusa mutuwa ne, shi ya sa yake yi masa irin wadannan nasihohi. Ashe kuwa haka abin yake, Nuruddin bai gushe ba yana yi wa dansa wasiyya, tsawon 'yan watanni kadan, ya kwanta ciwon ajali, bayan jiyyar kwanaki kadan, sai ya ce ga garinku nan. Hassan da mahaifiyarsa suka yi bakin ciki mara misaltuwa. Ba Hassan da mahaifiyarsa kadai suka yi bakin cikin mutuwar Nuruddin ba, hatta Sarki da fadawansa da jama'ar birnin Misira sai da suka yi bakin ciki mai yawa. Aka rufe shi a makabartar da ke bayan gari, inda aka rufe surukinsa, tsohon Waziri. Aka yi zaman makoki na kwana uku. Tun bayan mutuwar mahaifinsa, sai ya kasance Hassan ya daina zuwa fada. Kullum yana cikin gida yana kuka har tsawon wata biyu. Da Sarki ya daina ganin Hassan fada, sai ya yi fushi da shi, ya ce a ransa, "Saboda mahaifinsa ya mutu, shi ya sa ya daina zuwa fada? Ashe ba mu da girman da wannan yaro zai rika zuwa yana gaishe mu? Da ma saboda mahaifinsa ne yake zuwa?" Nan take Sarki ya nada sabon Waziri, ya kuma ba shi umurni ya washe dukkan dukiyar da ke gidan Waziri Nuruddin, idan ma yana so yana iya hadawa har da dansa Hassan, ya zama bawansa. *** Lokacin da wannan al'amari ke faruwa a Basara, a Misira ma wata guguwar rikicin ce ke juyawa tsakanin 'yar Waziri Shamsuddin da Sarkin Misira. Ku biyo ni gobe hkr danifa sabida baku ganin comment dina ko like anaku comment. aikinne dayawa adan bani uzuri.. nagode masoya05. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Tun bayan mutuwar mahaifinsa, sai ya kasance Hassan ya daina zuwa fada. Kullum yana cikin http://fb.com/waziriaku gida yana kuka har tsawon wata biyu. Da Sarki ya daina ganin Hassan fada, sai ya yi fushi da shi, ya ce a ransa, "Don mahaifin wannan yaro ya mutu, shi ne ya daina zuwa http://fb.com/waziriaku fada? Ashe ba mu da girma da mutuncin da zai rika zuwa yana gaishe mu?" Nan take Sarki ya nada sabon Waziri, ya kuma ba shi umurni ya washe http://fb.com/waziriaku dukkan dukiyar da ke gidan Waziri Nuruddin, idan ma yana so yana iya hadawa har da dansa Hassan, ya zama bawansa. Nan take sabon Waziri ya aika da askar zuwa gidan Nuruddin, su rubuto dukkan dukiyar da ya mutu ya bari, sa'annan su dauro dansa Hassan, su zo masa da shi. Kafin askar su isa gidan Nuruddin, sai wani bafade, yaron Waziri Nuruddin, ya sukwani http://fb.com/waziriaku dokinsa a guje ya nufi gidan. Da isar bafade ya iske Hassan a zaune, kansa na sunkuye, yana zubar da hawaye saboda tunanin mahaifinsa. Bafade ya ce masa, "Ya shugabana, yi hanzari ka kama tafarkinka, Sarki ya nada sabon Waziri, kuma ya ba shi izinin ya kwace dukkan dukiyar mahaifinka, har kai kanka za ka zama bawansa. Askar na nan ya turo, domin su daure ka, su tafi da kai. Ni na ga babu adalci a cikin wannan hukunci na Sarki, shi ya sa na zaburo domin http://fb.com/waziriaku in sanar da kai. Yi sauri ka fice daga wannan birni ko ka tsira da 'yancinka." Hassan ya mike tsaye da sauri, ya ce, "Bari na shiga taska na debi wani abu domin guzuri." Bafade ya ce, "Ya shugabana, ba ka da lokacin da za ka dauki komai, ka yi hanzari ka fita, kada su same ka." Hassan ya nufi kofar gida, bai dauki komai ba sai mayafin da ke hannunsa. Da fitarsa waje, sai ya yi rawani da mayafin ya rufe fuskarsa, domin gudun kada a gane shi. Ya nufi bayan gari, yana mai bakin ciki bisa http://fb.com/waziriaku wannan fita ta gaggawa da ya yi wa birnin Basara, ko mahaifiyarsa bai sami yin sallama da ita ba, bai kuma san hanyar Misira ba, inda bappansa Shamsuddin yake Waziri, ballantana ya nufi can. Da fitarsa bayan gari, bayan ya tabbata ya yi nisa da mutane, sai ya cire mayafin da ya rufe fuskarsa da shi, sa'annan ya ce cikin ransa, bari ya tafi makabarta, ya kai wa kabarin mahaifinsa da na kakansa ziyara, ya yi ban kwana da http://fb.com/waziriaku su, sa'annan ya nemi hanyar zuwa Misira. Hassan ya nufi babbar makabartar garin. Yana cikin tafiya, zuciyarsa cike da tunani, bai yi aune ba, sai ya ga mutum http://fb.com/ waziriaku a gabansa, yana jaye da rakuma, kowane rakumi an labta masa kaya niki-niki. Hassan ya yi niyyar ya boye wa mutumin nan, amma ina ya makara, mutumin ya riga ya gan shi, har ma ya gane shi. Ashe wani bayahude ne, daya daga cikin mutanen da mahaifinsa http:// fb.com/waziriaku yake turawa zuwa fatauci, shi ne ya dawo daga fatauci, kuma an sami riba mai yawa. Da ya ga Hassan sai ya ja ya tsaya, ya lura da yanayinsa da kyau, ya ga alamun yana cikin tashin hankali da damuwa. Ya dube shi ya ce, "Ya shugabana, me yake damunka? Kuma ina za ka, http://fb.com/waziriaku kai kadai cikin daji, rana na shirin faduwa?" Hassan ya ce, "Ina cikin bacci da rana, na yi mafarki da mahaifina, yana zargina a kan na rabu da zuwa ziyarar kabarinsa, shi ne na fito yanzu, hankalina a tashe bisa http://fb.com/waziriaku wannan zargi da mahaifina ke yi mini. Ina so in tafi makabarta ne domin ziyartar kabarinsa tare da yi masa addu'ar neman gafara, kafin dare ya yi in koma gida." Bayahude ya rike baki cikin tausayi da mamaki, domin bai ji labarin mutuwar Maigidansa Nuruddin ba, ya bar Basara zuwa fatauci, tun wata biyar da suka wuce. Bayan ya yi wa Hassan gaisuwar mutuwar mahaifinsa, sai ya ce, "Ya shugabana, yanzu kai ne zan hannunta http://fb.com/waziriaku wa wadannan kaya na dukiya, duk mallakar mahaifinka ne." Hassan ya ce, "Ba ni da bukatar dukiya yanzu, idan akwai tsabar kudi a wurinka, na fi bukatarsu, sauran kayan na bar maka su kyauta." Bayahude ya zaro wata yar jaka ta kudi, ya mika wa Hassan, ya ce, "Akwai kudi a cikin wannan jaka, dinari dubu uku, amma ina so ka rubuta mini takarda, shaidar ka mallaka mini wannan dukiya." Hassan Badaruddin ya karbi kudi, bayahude ya dauko takarda da tawada daga cikin kayansa ya mika masa. Hassan ya rubuta takardar mallaka wa bayahude kaya, ya mika masa. Bayahude ya karbi takarda, ya yi wa Hassan godiya, ya juya da http://fb.com/waziriaku rakumansa, bai ko shiga Basara ba, ya nufi wani birnin inda ya san zai sayar da hajarsa da daraja. Hassan kuwa ya yi wa Allah godiya da ya sami kudin da zai yi guzuri da su har zuwa Misira. Ya kulle jaka a zariyar wandonsa, ya nufi makabarta, wajen kabarin mahaifinsa. Koda ya isa cikin makabartar yamma ta yi, ya nufi inda kabarin ubansa yake, ya zauna yana yi masa addu'a yana hawaye, yana tunanin juyin zamani a kansa. Da, yana zaman dan Waziri ne, cikin jin dadi da walwala, amma ga shi http:// fb.com/waziriaku yanzu bayan rasuwar mahaifinsa ya zama dan gudun hijira, wannan wane irin zamani ne? Wannan shi ake kira da 'mutuwa mai tonon asiri.' Bai gushe ba yana zaune wurin kabarin nan, yana tunani, har barci ya kwashe shi saboda gajiya, ya yi kwance fuskarsa tana kallon sama. Hassan Badaruddin ya tsunduma cikin barci mai nauyi har dare ya yi, farin wata ya fito ya haske fuskarsa, tana ta kyalli kamar mudubi. Allah da ikonsa, ya nufi wata aljana, musulma, ta shiga cikin makabartar. Ta ga Hassan kwance yana barci, ta kura masa ido, tana kallon irin baiwar kyau da http://fb.com/waziriaku cikar halitta wadanda Allah ya yi masa. Ta ce, "Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin Sarki, wanda ya halicci wannan yaro da dukkan siffa ta kyau. Hakika ko a cikin aljanu 'yan uwana, babu tamkar wannan yaro." Bayan ta dade tana kallon Hassan, ta tashi, ta kada zuwa ga sama, ta bar shi nan yana barci, ta tafi tana cike da tunaninsa a ranta. Aljana na fita daga makabarta, sai ta hadu da wani aljani, cikin yaran mahaifinta. Ya gaishe ta, ta gaishe shi, sa'annan ta tambaye shi daga inda ya fito. Ya ce mata ya fito ne daga birnin Misira. Ta ce masa, "Zo mu je, ka ga wani saurayi a http://fb.com/waziriaku cikin makabartar nan, wanda babu kamarsa a kyau, cikin wannan zamani." Ya ce da ita, "Na'am, ya shugabata." Suka koma cikin makabarta, wurin da Hassan yake kwance yana ta sharar barci. Da suka isa wurinsa, suka dade suna kallon shi, aljana ta dubi aljani, ta ce, "Duk tsawon rayuwarka, ka taba ganin mutum mai kyawun wannan saurayi?" Aljani ya ce, "Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan yaro, tabbas, da farko na dauka babu wanda ya kai 'yar Wazirin Misira kyau http://fb.com/waziriaku cikin bil'Adam, amma yanzu na ga wanda ya kusa cim mata da kyau, domin idan ba ta fi shi kyau ba, to sai dai su zo daidai. Sai dai kash! Waccan yarinyar tana cikin bakin ciki mara misaltuwa." Aljana ta ce, "Wane irin bakin ciki take ciki? Kuma menene sanadin bakin cikin nata?" *** Za mu ci gaba gobe insha allahu 06. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Da aljanun nan biyu suka isa inda Hassan yake kwance yana barci, bisa kabarin ubansa, suka dade suna kallon shi, aljana ta dubi aljani, ta ce, "Duk tsawon rayuwarka, ka taba ganin mutum mai http://fb.com/waziriaku kyawun wannan saurayi?" Aljani ya ce, "Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan yaro, tabbas, da farko na dauka babu wanda ya kai 'yar Wazirin Misira kyau cikin bil'Adam, amma yanzu na ga wanda ya kusa cim mata da kyau, domin idan ba ta fi shi kyau ba, to sai dai su zo daidai. Sai dai kash! Waccan yarinyar tana cikin bakin ciki mara misaltuwa." Aljana ta ce, "Wane irin bakin ciki take ciki? Kuma menene sanadin bakin cikin nata?" Aljani ya ce, "Ki sani ya shugabata, tsawon zamani a birin Misira ba a taba haihuwar yarinya kyakkyawa ba, kamar wannan yarinya 'yar Waziri Shamsuddin mai suna Sittul Hassanu. Yanzu da ta girma ta kuma isa aure , Sarkin Misira ya so ta, http://fb.com/waziriaku ya nemi aurenta ga mahaifinta, Waziri Shamsuddin. Amma sai Waziri ya ce da Sarki, "Ya shugabanmu Sarkin zamani, ka karbi hanzarina, ka share mini hawaye. Ka sani cewa ina da dan uwa mai suna Nuruddin, ya bar gida da dadewa ba mu san inda yake ba. Dalilin fitar sa daga gida kuwa, ya yi fushi ne a kan wani zance da muka taba yi da shi na hada 'ya'yanmu http:// fb.com/waziriaku aure, in har Allah ya arzutta mu da su. Na tsaurara masa zance a wancan lokacin wanda sanadiyyarsa ne ya yi fushi da ni. Bayan na raka ka zuwa wata tafiya da ka taba yi, da muka dawo sai ban iske shi gida ba. Har yanzu kuma maganar da ake yi ke nan." Waziri ya kwashe dukkan labarin da ya faru tsakaninsa da dan uwansa Nuruddin, ya fadawa Sarki. Sa'annan kuma ya ci gaba da cewa, "Ya shugabanmu, tun ranar da na haifi 'ya mace, na yi rantsuwa http://fb.com/waziriaku ba ni aurar da ita ga kowa sai ga dan dan uwana Nuruddin. Kuma Allah da ikonsa yanzu bai fi wata uku ba da na ji labari gun fatake, cewa dan uwana yana birnin Basara kuma har an nada shi Wazirin Basara. Karewa da karau ma an ce, ya haifi da namiji wanda yake kusan sa'ar 'yata ne. Ina cikin shirye-shiryen in aika wa dan uwana da sako, sai ga shi ka zo mini da wannan batu. Ya Sarki, Ina rokonka da ka janye wannan bukata ta auren 'yata domin girman Allah." Yayin da Sarki ya ji zancen Waziri, ya yi fushi, fushi mai tsanani, ya ce, "Yaya kamar ni zan zubar da girmana, in nemi bukata wurinka amma ka juya mini baya, ka kawo wani dalili mara kwari? Na rantse da raina, na fasa auren ta, kuma domin in hukunta ka, da kai da 'yar taka, zan http://fb.com/waziriaku aurar da ita ga wani bawana, ma fi muni daga cikin bayina." Daga nan Sarki ya kori Waziri daga wurinsa. Aljani ya ci gaba da ba aljana labari, ya ce "Sarki yana da wani bawa, wada mai kusumbi, gurgu mai hakora zago-zago. Wannan bawa yana da gajeren wuya, da doguwar keya, da shafaffen goshi. Kai wannan bawa da muni yake, ya shugabata, ban taba ganin mutum mummuna irin shi ba. Yanzu haka dai lokacin da na fito daga birnin Misira, Sarki ya sa an daura http:// fb.com/waziriaku wa 'yar Waziri aure da wannan mummunan bawa. Cikin wannan dare ango zai shiga dakin amaryarsa, wannan yarinya tana cikin bakin ciki ita da mahaifinta, bakin ciki mai yawa." Aljani ya ci gaba da ce ma aljana, "Wallahi yarinya 'yar Wazirin Misira ita ce ma fi kyawo daga wannan saurayi. Ina ma a ce wannan saurayi ne za a aura mata, da sun yi matukar dacewa da juna. Wadannan yara sai ka ce 'yan bappanni ne, ko kuma su 'yan uwan juna ne." Aljana ta ce da shi, "Ka yi karya! Kodayake ban ga waccan http://fb.com/waziriaku yarinyar ba, amma na tabbata babu wanda ya kai wannan yaro kyau a cikin wannan zamani." Aljani ya ce, "Ya shugabata, Wallahi ita ce ma fi kyawo daga wannan saurayi. Ni ina tausaya mata game da auren wannan wada, mai kusumbi." Aljanun nan suka ci gaba da gardama a tsakaninsu, aljani na cewa 'yar Waziri Shamsuddin ce ta fi kyau, ita kuma aljana tana cewa, Hassan Badaruddin ne ya fi kyau. Shi kuwa Hassan yana ta sharbar Barci abinsa, bai san wainar da ake toyawa ba. Daga nan sai aljana ta ce, "Ka dauki wannan saurayi mu tafi da shi Misira yanzun nan, mu gwada shi da yarinyar can, mu ga wanda ya fi wani kyau." Aljani ya ce, "Na ji, na dauka, ya shugabata. Hakika wannan shi zai warware mana gardama, domin an ce, gani ya kori ji." Nan take aljani ya sungumi Hassan yana barci, suka tashi da shi sama, http://fb.com/waziriaku kamar kyabtawar ido sai ga su a Misira. Suka sauka a kofar gidan da ake bukin auren 'yar Waziri Shamsuddin, mai suna Sittul Hassana, tare da mai kusumbi. Bayan sun sauka, sai aljani ya zunguri Hassan da ke barci. Hassan ya farka firgigi, ya duba ko'ina, ya rasa gane inda yake. Shi dai ya San yana cikin makabarta ne a gaban kabarin mahaifinsa, wurin da in banda kukan kwari babu abin da ake ji. To amma yanzu da farkawarsa, sai ya gan shi cikin wani birni tsundum, maimakon kukan kwari kuma, yanzu babu abin da yake ji sai kade-kaden ganguna da bushe-bushe. Hassan fa ya rikice gaba daya, ya yi niyyar ya kwala ihu domin ya gani shin mafarki ne yake yi ko a farke yake. Sai aljanin nan ya yi sauri ya rufe masa baki, sa'annan ya ce masa, "Kada ka ji tsoro, kuma ba mafarki kake yi ba. Ni ba mutum ba ne, aljani ne. Ni ne na zo da kai nan domin in http://fb.com/waziriaku aikata maka wani alheri." Aljani ya kunna fitila ya mika wa Hassan, ya ce, "Karbi wannan fitilar, ka shiga cikin taron jama'ar can, inda ake yin Kade-kade da bushe- bushe. Kada ka ji tsoron kome. Idan ka tafi, ka yi kokari ka zauna kusa da ango, har ya zama kamar kai ne babban abokinsa. Koyaushe mawaka da maroka suka zo wurinka, ka saka hannunka cikin aljihu, za ka ji shi cike da kudi, ka yi ta damka kana watsa musu. Wannan ba dabararka ba ce ko karfinka, iko ne na Allah madaukakin Sarki. Idan masu kawo http:// fb.com/waziriaku amarya sun kawo ta daki suka tafi, ka tashi ka shiga dakin, kada ka ji tsoron kome, ina tare da kai." Yayin da Hassan ya ji jawabin aljani, sai ya ce a cikin ransa, "Kaico ni! Wannan wane irin al'amari ne ke shirin faruwa gare ni. Anya akwai alheri a cikinsa?" Ya dai karbi fitila daga hannun aljani, ya tashi ya nufi wurin da ake shagalin buki. Yayin da ya isa cikin taron mutane, ya ga kowa rike da fitila, irin wadda aljani ya ba shi. Makada kuwa sun goce ganguna, 'yan mata sai rawa ake yi. Ya ga ango mai kusumbi a can gefe daya zaune, shi kadai kamar maye. Hassan ya kutsa kai cikin mutane, ya nufi inda ango yake zaune. Da mutane suka gan shi, saurayi http://fb.com/ waziriaku kyakkyawa, sanye da wata irin riga, wadda ta sha kwalliya da ruwan zinari, da hula bisa kansa zananniya da kumfar azurfa da lu'ulu'u, sai suka rika ba shi hanya yana wucewa. Su kuwa maroka da makada, suna ganinsa sai suka dafe gangunansu suka yiwo kansa da kida da bushe-bushe. Hassan ya sa hannunsa cikin aljihun rigarsa, ya ji shi cike da dinari. Ya rika damka yana watsa wa mawaka, da 'yam matan amarya da tsofaffi. Ya cika wuri da dinari. Mutane suka yi ta mamakin irin kyawunsa, da kuma wannan irin kyauta tasa, sai ka ce burgaggen famfo. Hassan ya isa inda ango mai kusumbi yake zaune, ya ci kwalliya http://fb.com/waziriaku kamar wani Sarki, amma babu kowa tare da shi, duk mutane sun tsane shi saboda muninsa, ga shi kuma kankamo, tunda aka fara bukin bai ba maroka ko dirhami ba. Hassan ya zauna kusa gare shi, kamar yadda aljani ya umurce shi. Aka ci gaba da buki, Hassan kuwa ya ci gaba da ruwan kudi. Can zuwa wani lokaci, sai ga tsofaffi masu kawo amarya sun iso da ita. Suka shige da ita cikin gidan da Sarki ya tanadar musu ita da angonta. Ango da sauran jama'a, ciki har da Hassan, suka tashi za su shiga cikin gida. A bakin kofar gidan akwai masu gadi, wadanda ba su barin kowa ya shiga gidan, daga ango sai tsofaffin mata da kawayen amarya http:// fb.com/waziriaku kawai ne za su shiga gidan. Tsofaffin matan nan suka ce, Allambaram su ba za su shiga gidan amarya ba face da Hassan, domin kuwa shi ne wanda ya raya wannan buki da ruwan kudi. Dole masu tsaron kofa suka bari Hassan ya wuce cikin gidan. A cikin gidan amarya kuwa, mata sun yi sahu biyu madaidaita, sun saki hanya a tsakanin sahun biyu, inda amarya za ta bi. Cikinsu kuwa daga matan Sarakuna, sai na Hakimai da Wazirai, da manyan attajirai. http://fb.com/ waziriaku Kowace mace da fitila a hannunta mai haske sosai. Matan nan sun ci ado, sun kure adaka. Da tsofaffi suka shigo tare da ango da kuma Hassan Badaruddin, matan nan suka ga irin kyawun Hassan, sai kowace ta rika yaye mayafin da ya rufe fuskarta, domin ta more wa idonta kallon kyakkyawar fuskar Hassan dan mutanen Basara. Suna cewa, aminci ya tabbata ga wannan saurayi. Sai kuma su rika yi wa mai kusumbi bakar addu'a, da duk wanda ke da hannu wajen http://fb.com/waziriaku aura masa kyakkyawar yarinya Sittul Hassana, wadda ba ta dace da kowa ba, face wannan saurayi. Hassan da ango suka zauna gefe daya, maroka suka buga tambura, tsofaffi suka fito da amarya suka biyo da ita ta tsakanin hanyar da mata suka yi sahu. Kai! Wannan amarya da kyawu take, kyawun da zai iya dimautar da duk wanda ya kalle ta. Ta ci ado da tufafi na sarauta, wadanda aka yi wa kwalliya da zinariya, da zane-zane masu kyau na tsuntsaye da namun daji. Ga wani http://fb.com/waziriaku dutsen wuya daure ga wuyanta, wanda babu irinsa duk kasar Misira. Amarya ta zama tamkar farin wata dan daren goma sha hudu, tsarki ya tabbata ga mahaliccinta. Ta biyo ta tsakanin matan nan, ka ce ita ce wata su kuma taurari, ta nufi inda angonta yake zaune tare da Hassan. *** Za mu ci gaba mai gobe zuwa daidai wannan lokaci insha allahu by YUSUF A JIBAGA07. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Hassan da ango suka zauna gefe daya, maroka suka buga tambura, tsofaffi suka fito da amarya suka biyo da ita ta tsakanin hanyar da mata suka yi sahu. Kai! Wannan amarya da kyawu take, kyawun da zai iya dimautar da duk wanda ya http://fb.com/waziriaku kalle ta. Ta ci ado da tufafi na sarauta, wadanda aka yi wa kwalliya da zinariya, da zane-zane masu kyau na tsuntsaye da namun daji. Ga wani dutsen wuya daure ga wuyanta, wanda babu irinsa duk kasar Misira. Amarya ta zama tamkar farin wata dan http:// fb.com/waziriaku daren goma sha hudu, tsarki ya tabbata ga mahaliccinta. Ta biyo ta tsakanin matan nan, ka ce ita ce wata su kuma taurari, ta nufi inda angonta yake zaune tare da Hassan. Da zuwanta wurinsu sai ango mai kusumbi ya tashi tsaye ya miko wa amaryarsa hannu domin ya zaunar da ita. Amma ina, hankalinta ba wurinsa yake ba, hankalinta ya karkata ga kallon Hassan, ta matsa kusa gare shi, ta durkusa ta kura masa ido tana kallon shi, ta bar mijinta http://fb.com/waziriaku mai kusumbi a tsaye kamar icce. Da mata suka ga amarya ta karkata ga Hassan, ta bar angonta, sai suka kwashe da dariya. Hassan ya saka hannunsa cikin aljihun rigarsa, ya damko dinari ya watsa musu. Nan take sai wuri ya kaure da guda, mata na cewa, "Mu, muna yi maka addu'a a kan wannan amarya ta zama taka, tir da wannan ango marowaci." Amarya kuwa da take durkushe http://fb.com/waziriaku a gaban Hassan tana kallonsa ba ko kyabtawa, ta daga hannuwanta sama tana cewa, "Ya Allah mai girma da daukaka, mai tsarawa da juyar da al'amurra yadda ya so, ka juyar da wannan aure nawa, ka sanya wannan saurayi ya zama shi ne mijina, ina neman tsari daga wannan wada mai kusumbi." Lokacin da dare ya fara yi sosai, sai aka umurci kowa ya fita daga cikin gidan. Tsofaffi suka shiga da amarya wani daki domin su yi mata nasiha ta karshe, kafin su kai ta ga dakinta. Duk sauran mata suka fita daga cikin gidan, babu wadanda suka yi saura sai ango da Hassan Badaruddin. Da ango ya ga Hassan bai fita daga http://fb.com/waziriaku cikin gidan ba sai ya ce masa, "Ya shugabana, hakika ka debe mana kewa a cikin wannan dare, ka jibince mu da alherinka, ba domin ka ba da wannan buki ya zama lami. Ga shi dare ya soma yi, ya kamata ka tashi ka tafi gida haka nan, amma fa kada ka ga kamar korar ka nake yi." Hassan Badaruddin ya tashi ya nufi kofar fita daga gidan, yana mai matukar bege da tausayin wannan amarya, wadda bai taba ganin kyakkyawar mace kamarta ba. Har ya zo bakin kofar fita, sai http:// fb.com/waziriaku aljani ya zungure shi, ya ce masa, "Ka tsaya kada ka fita, ya Badaruddin, idan ka ga mai kusumbi ya nufi cikin lambu, ka yi sauri ka shige wancan dakin, inda za a kai amarya. Idan aka kawo ta, ka ce da ita ni ne mijinki, da ma Sarki dabara ce ya yi na cewa ya aurar da ke ga mai kusumbi, domin kawai a kawar da idanun mutane, kuma a yi wa mai kusumbi dariya." Shi kuwa ango mai kusumbi, abin duniya duk ya dame shi, yana ta zagin Sarki a cikin ransa, ga shi ya daura masa aure da yarinyar da ba ta son shi, duk jama'a ma ba su son shi. Nan take ya ji duk duniyar ta yi masa baki, ya ce a cikin ransa, "Bari na shiga cikin lambun can ko na dan ji sanyi a raina, kafin tsofaffi masu yi wa amarya http://fb.com/waziriaku nasiha su gama yi mata nasihar. Na riga na sani dai duk nasihar da za su yi mata ba za ta yarda in kwanta kusa gare ta ba, ballantana har in kusance ta." Ya tashi ya nufi cikin lambu, aljani na biye da shi a baya. A cikin lambun an rataya fitilu, ko'ina ya haskake tamkar rana. Yayin da Hassan ya ga mai kusumbi ya shige cikin lambu, sai shi kuma ya yi sauri ya shiga dakin da za a kai amarya, ya yi zaune bisa gado. Akwai fitila a cikin dakin, tana haske tamkar rana, an kawata bangayen dakin da zane-zane masu kyau da ban sha'awa, an shimfide kasan dakin da shimfidu na alfarma, masu laushi. Hassan bai dade da zama ba, sai ga tsofaffin nan masu kawo amarya sun iso da ita. Suka tsaya daga bakin kofar dakin, wadda take rufe da labule http://fb.com/waziriaku . Daya daga cikinsu ta daga murya ta ce, "Ya Aba Shuhabi, zo ka karbi amaryarka. Mun bar ku da Allah da halinku. Allah ya sa ma wannan aure naku albarka." Suka tura keyar amarya cikin dakin, suka juya suka tafi. Amarya ta shiga dakin ranta a bace, tana sake- sake cikin zuciyarta, tana cewa, "Wallahi ba zai sami hadin kaina ba, ba zai taba kusantata ba har abada, sai dai ya kashe ni." Tana daga kanta sai ta yi tozali da Hassan, nan take ta tsaya cik, cikin kaduwa da mamaki. Bata san lokacin da ta ce da shi ba, "Ya masoyina, yaya aka yi ka shigo nan? Ina ce zan iske mijina ne, mai kusumbi." Hassan ya ce mata, "Don me mai kusumbi zai http://fb.com/waziriaku shigo nan, bayan an riga an biya shi jingar aikinsa ya tafi?" Sittul Hassana ta ce, "Shin ga wa aka aurar da ni? Gare ka, ko gare shi?" Hassan ya ce mata, "Haba masoyiyata, ai ko ba a gwada ba linzami ya fi karfin bakin zakara. Da yaya kamar

Chapter 2 of 4