Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng 01. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN'UWANSA SHAMSUDDIN. Allah shi ne Sarki ma fi daukaka daga dukkan Sarakuna, shi ne ma fi tsarki daga dukkan abubuwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonsa, Annabi Muhammadu (S.A.W). Ka sani, ya Sarkin Musulmi, a kasar Misira an yi wani Sarki, ma'abucin adalci da kyautatawa. Yana da Waziri mai hankali, mai rarrabe abubuwa da dabaru, mai tarin ilimi da fasaha, sai dai ya kasance tsoho ne, shekaru sun yawaita a kansa. Wazirin nan yana da 'ya'ya biyu maza, kai ka ce 'yan tawaye ne. Ga su kyawawan gaske, babu kamar su a duk fadin kasar. Sunan babban Shamsuddin, sunan karamin kuwa Nuruddin. Karamin, watau Nuruddin, ya zarce wansa ga kyawo da cikkar halitta. Ya kasance a cikin wancan zamanin babu tamkarsa ga kyawo. Labarin kyawonsa ya watsu cikin manyan birane da kauyuka. Mutane da dama sukan tafi tun daga garinsu har zuwa Misira, domin ganin kyawo irin na Nuruddin. Kwanci tashi, ran nan sai Wazirin Misira ya kwanta ya mutu. Sarki ya yi matukar bakin ciki a kan mutuwar Wazirinsa. Sarki ya rungumi 'ya'yan Waziri a jikinsa, ya ce, "Ku ne a matsayin ubanku a wurina." Yara suka yi farin ciki. Aka yi zaman makokin mahaifinsu aka gama. Shamsuddin da kanensa Nuruddin suka zama su ne a matsayin Waziri ga Sarkin Misira. Idan wannan ya hau karagar mulki, bayan sati guda sai ya sauka dan'uwansa ya hau. Sukan yi canji duk ranar Jumu'a, idan kuma Sarki zai yi tafiya, sai ya tafi da daya, ya bar daya yana mulkin gari. Wata rana daga cikin ranaku, Sarki ya yi niyyar tafiya wata kasa, aka yi gamo da katar, hukunci ya fada za a tafi da babban ne, watau Shamsuddin. Daren da za su tafi, Shamsuddin ya kira dan uwansa suka zauna suna hira. A cikin hirar tasu Shamsuddin ya ce da dan'uwansa, "Na yi nufin idan Allah ya maido mu gida lafiya daga tafiyar da za mu yi gobe da Sarki, mu yi aure lokaci guda, a cikin rana guda." Nuruddin ya ce, "Kai ne babba, kuma kai ne a matsayin ubana a halin yanzu. Ka aikata duk yadda ka so, za ka same ni mai biyayya a gare ka." Shamsuddin ya ce, "Insha Allahu da zarar na dawo, zan nema mana 'yan mata biyu, mu aure su rana daya, mu shiga dakinsu dare daya, su sami ciki lokaci daya, su haihu rana daya. Matarka ta haifi da namiji, matata ta haifi 'ya mace. Su tashi tare, su yi wasa tare, idan suka isa aure mu aurar da su ga junansu, su zama 'yan bappanni." Nuruddin ya ce, "Allah ya sa haka. To amma idan haka ta tabbata, me za ka karba gun dana a matsayin sadakin 'yarka?" Shamsuddin ya ce, "A matsayin sadakin 'yata, zan karba gun danka, dinari dubu uku, da gona talatin, da gidaje uku." Yayin da Nuruddin ya ji haka sai ya ce, "Haba! Wane irin sadaki ne mai tsanani za ka dora wa dana haka, ko ka manta cewa mu 'yan'uwan juna ne, kuma Wazirai muke, matsayinmu daya. Ya zamanto wajibinka ne ka aurar da 'yarka ga dana kyauta, ba tare da karbar ko dirhami daga gare shi ba. Ko ba ka san namiji ya fi mace daraja ba?" Shamsuddin ya harzuka da wannan zance na kanensa, ya ce, "Babu shakka kai ba ka da hankali, tun da ka ambata tarayyar Wazirtaka tare da ni, kuma kana nufin danka ya fi 'yata daraja ne? Ni fa na roki Sarki ya sa ka Waziri tare da ni saboda tausayinka da nake ji, shi ne yanzu har kake hada kanka da ni. Tun da har ka fadi haka, to Wallahi ba ni aurar da 'yata ga danka, ko da zai biya zinariyar da ta kai nauyin 'yar tawa a matsayin sadaki." Yayin da Nuruddin ya ji zancen dan'uwansa, ya yi fushi, ya ce, "Ni ma dana ba zai auri 'yarka ba, ko da babu sauran mata a duniya sai ita kadai." Shamsuddin ya ce, "Ni ma ban yarda 'yata ta auri danka ba, ko da babu sauran maza a duniya sai shi kadai. Amma yanzu na yi nufin tafiya, waccan niyyar ta aurenmu lokaci daya na fasa yin ta, Allah ya aikata yadda ya so." A cikin wannan dare, Nuruddin da Shamsuddin ba su kwana wuri daya ba kamar yadda suka saba, kowa ya kwana daki dabam saboda bacin rai. Da gari ya waye, Shamsuddin ya shirya domin tafiya da Sarki, ya nemi dan'uwansa domin su yi sallama amma bai gan shi ba. Don haka sai ya bi Sarki suka tafi. Ashe kuma tun da asuba Nuruddin ya riga Shamsuddin tashi daga barci, ya shiga taska, ya dauki jaka karama ya cika ta da dinari. Ya tuna maganganun da dan'uwansa ya yi masa a daren jiya, da kuma gorin Wazirantaka da ya yi masa. Ya tuna wakar wani mawaki, in da yake cewa: "Ka yi tafiya cikin duniya, za ka sami musayar abin da ka rasa. Ka kafu da kafafunka, farin ciki na ga wanda ya dogara da kansa. Ni na ga tsayuwar ruwa wuri daya tana gurbata shi, ruwan da yake gudu shi yake tsarkaka. Ba don farin wata yana fakuwa ba, da ba a dube shi ba ranar tsayuwarsa. Ba don zaki yakan rabu da surkuki ba, da bai sami abin farauta ba. Ba don kibiya takan rabu da baka ba, da ba ta zama abin tsoro ba. Komai kyawon sanda, idan tana jikin icce ba a ganin kyawonta. Zinariya tamkar kasa take, ba a ganin kyawonta sai ta rabu da kasa. Wanda ya zauna gida, ba ya daukaka har duniya ta san da shi." Bayan ya dauki abin da yake so ya dauka daga cikin taska, ya umurci wani bawansa ya daura masa sirdi ga wani farin dokinsa mai kiba, mai gaggawar tafiya. Bawa ya daura wa doki sirdi da likkafu kirar kasar Hindu. Ya shimfida shimfidar Asbihaniya a kan sirdin. Bawa dai ya shirya doki da kayan kawa masu tsadar gaske wadanda sai sarakuna da attajirai ke yin amfani da su. Da Nuruddin zai fita, ya ce wa bawan nan nasa, "Ina so in fita zuwa bayan gari, zan tafi unguwar Kalyubati in kwana uku. Kada kowa ya bi bayana, ina da bacin rai tattare da ni, idan na sami nutsuwa zan dawo." Yayin nan ya yi gaggawa ya hau dokinsa, ya rike wani abu kadan na guzuri a hannunsa, ya fita daga Misira ba tare da ya san inda zai tafi ba. Burinsa kawai ya yi nisa da kasarsu da kuma dan'uwansa Shamsuddin, ya shiga duniya, duniya ta gan shi, shi ma ya ga duniya. *** Wannan shi ne farkon labarin mai cike da tu'ajibi da mamaki da ban tausayi. Za mu ci gaba gobe daidai wannan lokaci (karfe 8 - 9 PM), Insha Allah. A jibaga√002. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Nuruddin ya yi gaggawa ya hau dokinsa, ya rike wani abu kadan na guzuri a hannunsa, ya fita daga Misira ba tare da ya san inda zai tafi ba. Burinsa kawai ya yi nisa da kasarsu da kuma dan'uwansa Shamsuddin, ya shiga duniya, duniya ta gan shi, shi ma ya ga duniya. Ya fita daga Misira ya shiga daji, Azuhur ba ta yi masa ba sai da ya shiga birnin Bilbis. Ya sauka ya huta, dokinsa ma ya huta. Bayan ya ci abinci ya kuma ciyar da dokinsa, ya sayi duk wani abu da ya san zai bukata a kan hanya. Ya hau dokinsa ya fita daga wannan birni ya kutsa kai cikin daji. Bayan tafiyar dare daya da yini, ya isa birnin Kudus. Ya sauka ya huta, dokinsa ma ya huta ya ci abinci ya ciyar da dokinsa. Ya yi shimfida ya kwanta domin ya rama baccin da bai yi ba, zuciyarsa na cike da fushin dan uwansa har bacci ya dauke shi. Ya kwana a wannan wuri. Da gari ya waye ya kama dokinsa ya hau ya ci gaba da tafiya har ya isa birnin Halbi. A birnin Halbi ya sauka a gidan baki, ya huta sosai, ya sha iska tsawon kwana uku, bakin cikinsa ya fara yayewa. Daga nan ya hau dokinsa ya ci gaba da tafiya, ba tare da ya san inda za shi ba. Bai gushe ba yana tafiya har ya iso birnin Basara cikin dare, ba tare da ya san ko wane gari ne ba. Ya nemi gidan baki ya kwana. Da gari ya waye Nuruddin ya ce da mai kula da kofar gidan baki yana so ya tafi da dokinsa rafi ya yi masa wanka ya shafe shi da mai. Mai kula da kofa ya kama ragamar doki ya ja ya nufi rafi, aka yi gamo da katar hanya ta bi da shi ta gaban gidan Wazirin Basara, yana kuwa zaune a cikin soronsa. Da Wazirin Basara ya kyalla ido ya ga dokin Nuruddin da irin kayan kwalliyar da aka kawata dokin da su, sai ya ce a cikin ransa, lalle wancan dokin na wani babban Sarki ne ko Waziri, ko kuma na wani babban attajiri ne. Ya dubi wani yaronsa ya ce, ka zo mini da dokin can tare da wanda ke jaye da shi. Yaro ya tafi nan take ya zo da mai kula da kofar gidan baki tare da doki. Da suka zo mai kula da kofa ya durkusa ya yi gaisuwa ga Waziri. Wazirin Basara ya kasance tsoho ne sosai, shekaru sun yawaita a kansa. Ya ce da mai kula da kofa, wane ne mai wannan doki? Mai kula da kofa ya ce, "Ya shugabana, mai wannan doki saurayi ne karami, mai karancin shekaru, mai kyakkyawan hali na daga 'ya'yan tajirai, yana da kwarjini da nutsuwa. Jiya ya sauka a gidan baki, amma na yaba da kyawawan halayensa, ya shugabana." Yayin da Waziri ya ji wannan zance ya tashi tsaye a kan duga-dugansa, ya ce da mai kula da kofa, "Kai ni inda yake in gan shi." Waziri ya hau dokinsa suka tafi zuwa ga gidan baki. Da suka isa gidan baki, suka zarce dakin Nuruddin, suka yi masa sallama, Nuruddin ya leko da kansa waje, Waziri ya ga Nuruddin. Da Nuruddin ya ga Waziri, duk da bai san ko wanene shi ba, ya fito daga cikin dakin, ya durkusa a gabansa, ya gaishe shi da lafazi mai dadi cikin ladabi da biyayya. Waziri ya sauko daga kan dokinsa, ya rungumi Nuruddin, ya ce da shi, "Ya dana, daga wane birni ka zo wannan birni namu? Kuma ina kake nufin tafiya daga nan?" Nuruddin ya ce, "Ya shugabana, na fito ne daga birnin Misira, mahaifina shi ne Wazirin Misira amma Allah ya yi masa rasuwa." Nuruddin ya labarta wa Waziri duk abin da ya gudana tsakaninsa da dan uwansa Shamsuddin, da yadda ya yi masa gorin wazirtaka, har ya yi fushi ya baro garinsu, har Allah ya kawo shi wannan birni. Waziri ya ce da Nuruddin, "Yanzu mene ne burinka a rayuwa?" Nuruddin ya ce, "Buri na yanzu shi ne in ci gaba da zagaya duniya, ba zan koma gida ba har sai na ga manya-manyan birane da garuruka na duniya gaba dayansu." Yayin da Waziri ya ji haka ya yi murmushi, ya ce da Nuruddin, "Ya dana, kada ka biye wa bacin zuciya ta jefa ka ga halaka, sai ka mutu ba ka ko ji labarin wani birni na duniya ba, ballantana ka gan shi. Ina rokon ka, ka tashi daga wannan gidan baki, ka koma gidana da zama." Nuruddin ya amince da bukatar Waziri, ya hau dokinsa ya bi shi har suka isa gidan. Waziri ya sa aka kawo wa Nuruddin abinci da abin sha masu daraja. Da Waziri ya ga hankalin Nuruddin ya fara kwanciya, sai ya ce da shi, "Ya dana ka ga ni tsoho ne mai yawan shekaru, Allah bai arzuta ni da da namiji ba sai mace, ita kenan na haifa. 'Yar nan tawa kuwa idan ba ta zarta ka a kyau ba, to kuwa za ku zo daidai da ita, kuma ga shi sa'o'in juna kuke. 'Ya'yan sarakuna da 'ya'yan attajirai sun nemi aurenta amma duk na hana su, domin duk cikinsu ban ga wanda hankalinsa da halayensa suka dace da 'yata ba. Tun lokacin da na dora ido a kanka, na san cewa duk duniya babu wanda ya dace da ya auri 'yata sai kai. Shin ko za ka amince da wannan tayin na auren wannan 'ya tawa?" Yayin da Nuruddin ya ji wannan zance na Wazirin Basara, ya sunkuyar da kansa cikin jin kunya ya ce, "Na ji na kuma amince da wannan babbar kyauta taka." Waziri ya yi farin ciki da haka ya ce, "Tunda na sami suruki, ni zan yi murabus daga karagar mulki, a nada ka a matsayin Wazirin Basara, ni kuwa in koma gefe in ci gaba da bautar Ubangiji a cikin 'yan sauran kwanakin da suka rage mini a duniya. Gobe za mu je in gabatar da kai a gaban Sarki." Waziri ya tara abokansa, ya yi kiran manyan attajirai da alkalai na birnin Basara ya ce da su, "Ku sani cewa ina da dan uwa a birnin Misira wanda ya kasance shi ma Waziri ne a can. Wannan dan uwa nawa yana da 'ya'ya biyu maza, ni kuwa Allah ya arzutta ni da 'ya daya, kamar yadda kuka sani. Kafin dan uwana ya rasu ya yi mini wasicci da in aura wa daya daga cikin 'ya'yansa 'yata, ni kuwa na amsa masa da haka. Yanzu da na ga ta isa aure, na aika Misira wannan dan dan uwan nawa ya zo domin cika alkawarin da na daukar wa dan uwana. Ina so in rubuta takarda a kan aurensu, ku kuma ku zama shaida." Mutane suka ce, madalla da wannan karimci da cika alkawari naka ya Waziri. Yayin nan jama'suka sha madara da zuma, aka yayyafa musu wardi, suka watse suna sa wa Waziri albarka. Waziri ya sa aka gyara wa Nuruddin wani daki nan cikin gidan, aka zuba masa kayan kawa da na ado masu kyau da tsadar gaske, sannan ya sa aka fara gyaran wani gida daban wanda Nuruddin zai zauna idan an daura musu aure da matarsa 'yar Waziri. Al'amarin Shamsuddin kuwa.... gobe zàmuci gaba Insha allahu ayi hakuri kwana biyu anjini shuru hakan yafarune. sakßmakon. tàfiya danayi amma yanzu nadawo komai yayi dàidai03. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Waziri ya sa aka gyara wa Nuruddin wani daki nan cikin gidansa, aka zuba masa kayan kawa da na ado masu kyau da tsadar gaske, sannan ya sa aka fara gyaran wani gida daban, wanda Nuruddin zai zauna idan an daura musu aure da matarsa 'yar Waziri. Kashe gari, Wazirin Basara ya riki Nurddin ya tafi da shi gaban Sarkin Basara. Da suka isa, suka fadi suka yi gaisuwa gun Sarki. Nuruddin ya kasance mai fasahar magana, mai natsattsiyar zuciya da kyan hali, sai ya rera wa Sarki wadannan baitoci: "Wannan shi ne Sarkin da ya game jama'arsa da adalci, Idan ya yi fushi yakan kori rundunar mayaka dukkanta, Ba ya so a yabe shi domin aikinsa gun talaka, Ya sani aikinsa gun talaka hakkinsa ne a gare shi, Ku zo mu sumbanci yatsunsa, domin mabudan arzukka ne." Sarki ya yi mamaki a kan fasaha da iya kalamai na Nuruddin, ya dubi Waziri ya ce, "Wannan wane saurayi ne, daga ina ya zo wannan birni namu?" Waziri ya ce, "Wannan yaro dan dan uwana ne." Sarki ya ce, "Ashe kana da dan uwa wanda ba mu san da labarinsa ba?" Waziri ya ce, "Ya shugabammu, dan uwa ya kasance a gare ni, shi ne Wazirin Misira, ya mutu ya bar 'ya'ya biyu. Babban dansa ya gadi matsayin ubansa na Wazirin Misira, shi kuma wannan karamin ya zo gare ni. Kafin dan uwana ya mutu, ya yi mini wasici da in karfafa zumuncinmu ta hanyar aurar da 'yata ga daya daga cikin 'ya'yansa, na kuma yi masa alkawarin yin haka. Yanzu da na ga 'yata ta isa aure, na aika ga wannan yaro ya zo wurina domin cika wannan alkawari da na yi wa dan uwana, ya Sarki. Ni ina nufin aurar da 'yata ga wannan saurayi, ina kuma rokon Sarki ya nada shi a matsayina, yaro ne mai hankali da dabara wanda ya gaji sarautar Wazirtaka. A halin yanzu tsufa ya zo mini, karfina ya kare, ina so in koma gefe guda in huta kafin zuwan ajalina." Sarki ya dubi Nuruddin, ya gan shi yaro ne natattse mai hankali da kuma iya zance na hikima. Kodayake dai a cikin ransa, Sarki bai yarda da labarin Wazirinsa ba cewa Nuruddin dan dan uwansa ne, domin ya san Waziri ba ya da wani dan uwa a Misira, duk da haka ya amince da wannan bukata ta Waziri, saboda girmama shi da yake yi. Aka sa ranar da za a nada Nuruddin a matsayin Wazirin Basara, aka kuma sa ranar ta yi daidai da ranar da zai auri 'yar Waziri. Amma abin da ya kasance ga dan uwansa Shamsuddin kuwa shi ne, bayan tafiyarsu tare da Sarki, suka dauki tsawon lokaci kafin su dawo gida. Bayan sun dawo, Shamsuddin ya huta, dukkan mutanen gidansa suka zo suka gaishe shi suka yi masa sannu da zuwa amma bai ga dan uwansa Nuruddin ba. Ya tambayi bayi, ina Nuruddin? Bayi suka ce masa, tun ranar da ya fita tare da Sarki, Nuruddin ya daura wa dokinsa sirdi, ya ce zai tafi unguwar Kalyubati domin yana tare da bacin rai, ya ce kuma ba ya so kowa ya bi bayansa. Tun lokacin har yanzu ba mu kara jin labarinsa ba. Yayin da Shamsuddin ya ji wannan labari, zuciyarsa ta yi baki, ransa ya baci, ya tuna maganganun da suka yi da dan uwansa daren da zai yi tafiya da Sarki. Ya ce a cikin ransa, wannan duk laifina ne, ba shakka dan uwana ya yi fushi ne sakamakon tsaurara masa zance da na yi, daren da zan yi tafiya, ya zamar mini dole in sa a nemo shi, a lallashe shi, a ba shi hakuri ya dawo gida. Shamsuddin ya fada wa Sarki abin da ya faru tsakaninsa da dan uwansa. Nan take Sarki ya aika da manzanni cikin kasarsa, kudu da arewa, gabas da yamma, domin su nemo labarin Nuruddin. Manzanni suka tafi, bayan kwanaki masu yawa, suka dawo gun Sarki, ba tare da sun ji ko da labarin hanyar da Nuruddin ya bi ba. Shamsuddin ya yi bakin ciki kwarai da gaske, ya debe tsammanin sake ganin dan uwansa, ya ce a cikin ransa, "Kaito! Wallahi ni na tsaurara masa zance a kan auren 'ya'yanmu, wannan yana daga cikin karancin hankalina da kuma shairin shaidan. Ina rokon Allah ya gafarta mini bisa ga wannan kuskure da na yi." Bayan wasu watanni da faruwar wannan al'amari, Shamsuddin ya nemi auren wata yarinya 'yar wani babban attajiri na Misira. Da ranar daurin aure ta zo, aka yi shagalin buki irin na Sarkuna da manyan attajirai. Da dare ango ya shiga gun amaryarsa, bisa ga al'ada da kuma addinin Musulunci, suka kwana suna marunguma junansu. Bisa kaddarawar Allah, yayin da ya zartar da hukuncinsa a kan halittu, shi ne mai yin yadda ya so, mai karbar addu'ar talikai. Allah da ikonsa ya karbi fatar wadannan 'yan uwa biyu. Aka yi gamo da katar, daren da Shamsuddin ya shiga dakin amaryarsa a birnin Misira ya zo daidai da daren da Nuruddin ya shiga dakin tasa amaryar a birnin Basara. Dukkan matan suka dauki ciki a daren farko na amarcinsu, tamkar yadda 'yan uwan biyu suka yi fata. Bayan wata tara, matar Shamsuddin ta haifi 'ya mace, wacce a fagen kyau, ba a taba ganin tamkarta ba, duk fadin Misira. Matar Nuruddin ta haifi yaro, babu tamkarsa a kyau, duk fadin Basara, kamar yadda wani mawaki yake fada, cewa: "Sassauka ne mai wadatar da abokin shansa daga yawun bakinsa, Yakan wadatar da mai gani da ganin kwayar idonsa da kundukukinsa, Idan an ce kykkyawa to babu shi a wurin, da zarar ya zo maganar kyau ta kare, Dukkan kyakkyawa yakan koma mummuna a gabansa." Aka rada wa wannan yaro suna Hassan Badaruddin a ranar sunansa. Aka yi kasaitaccen buki tare da walima, aka ci aka sha mai tsada da daraja. Tun ranar da aka daura musu aure da 'yar Waziri, aka nada Nuruddin a matsayin Wazirin Basara, ya ci gaba da zuwa fada kullum. Sarki ya yi murna da shi domin iya lafazinsa da fasaha tasa, ya so shi, ya kusata shi gare shi. Aka kara masa albashi mai tsoka. Waziri Nuruddin ya rika tara kudin albashinsa, da ya ga sun yi kauri, ya sami amintaccin yaransa ya rika tura su, suna shiga lungu-lungu da sako-sako na duniya domin yin fatauci. Cikin dan kankanen lokaci, Waziri Nuruddin ya mallaki jirage, da gonaki da filaye, ya zama babban attajiri daga tajiran birnin Basara. *** Za mu ci gaba gobe iñsha allahu YuSUF A JIBAGA. ke gaisheku04. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN Waziri Nuruddin ya rika tara kudin albashinsa da yake samu, da ya ga sun yi kauri, ya sami amintaccin yaransa ya rika tura su, suna shiga lungu-lungu da sako-sako na duniya domin yin fatauci. Cikin dan kankanen lokaci, Waziri Nuruddin ya mallaki jirage, da gonaki da filaye, ya zama babban attajiri daga tajiran birnin Basara. Farin jinin Waziri Nuruddin ya karu ga Sarkin Basara da jama'arsa, kowa yana son shi da yabon kyawawan halayensa. Ya kasance dare da rana Nuruddin na tare da Sarki, bacci kawai ke raba su. Dansa kuwa, wato Hassan Badaruddin, tun da aka yaye shi, kakansa tsohon Waziri ya ci gaba da renonsa a gidansa. Lokacin da yaro ya cika shekara hudu da haihuwa, a lokacin ne kuma Allah ya yi wa kakansa, mai rikon shi, rasuwa. Aka yi masa jana'iza irin ta manyan mutane, aka kai shi makabarta da ke bayan gari aka rufe. Bayan kwana arba'in aka yi sadaka, Hassan ya koma gidan ubansa Nuruddin, ya ci gaba da rayuwarsa. Lokacin da ya cika shekara biyar da haihuwa, mahaifinsa ya nemo wani babban Malami yana koya masa karatu da rubutu. Cikin shekara biyu ya haddace Alkur'ani mai tsarki, malaminsa ya shiga koya masa sauran fannoni na ilimi, irinsu fikihu, hadisai, wakoki da lugga. Hassan Badaruddin yaro ne mai hazaka da fahimta, duk abin da aka koya masa sau daya, to ya rike shi ke nan. Hassan na kara girma kyawunsa na kara bayyana, tamkar da wani mawaki yake cewa: "Yana dada girma yana dada hankali da farin jini, tamkar farin wata. Rana tana samun haskenta daga hasken kundukukinsa. Hasken farin wata yana cikin kundukukinsa. Marecen Miriha yana daidaita da kundukukinsa. Baka na harba kibau daga makyabtansa. Kyawun tsarin taurari na cikin dare ya bayyana a gare shi. Madaidaiciyar tsayuwa da haske sun tabbata a gare shi. Jauza'a suna hudowa ta cikin goshinsa. Ya mallaki kyawo dukkansa, ka ce shi ne ya tattara kyawun dukkan halittu. Dukkan baiwa cikakkiya ta taru gare shi." Malamin nan bai gushe ba yana koyar da Hassan dukkan fannoni na ilimi a cikin gidan ubansa har tsawon shekara goma sha biyu, ya hardace dukkan kome da aka karantar da shi. Duk tsawon wadannan shekaru Hassan bai taba fita waje ba, wannan ne ya sa ba kowa ne ya taba ganin shi ba. Yayin da ya cika shekara goma sha biyar, mahaifinsa ya yi nufin fara tafiya da shi zuwa fada, domin ya fara koyon sha'anin mulki. Ya tufatar da shi tufafi na alfarma, ya aza shi bisa wata alfadara, zababbiya daga cikin alfadaransa, ya tafi da shi zuwa fada. Duk inda suka wuce, sai mutane su tsaya suna kallon Hassan, suna shauki da begen kyawunsa, har suka isa fada. Lokacin da Sarki da sauran fadawa suka ga Hassan Badaruddin dan Waziri Nuruddin suka dimauta da ganin kyawu da cikar halitta tasa. Sarki ya yaba da shi, ya sa masa albarka, ya umurci Nuruddin ya rika zuwa da shi fada kullum. Tun daga wannan rana, sai ya kasance Waziri Nuruddin yana zuwa da dansa fada kullum, har yaro ya kai shekara goma sha takwas, ya isa mutum sosai. Da Nuruddin ya ga dansa ya fara mallakar hankali, shi kuma ya fara tsufa, sai ya kira shi ya zaunar da shi, ya ce, "Ya dana, ka sani cewa duniya gida ce mai karewa, lahira ita ce gidan tabbata. Ina so in wasice ka da wasiyya, ka fahimci wadannan abubuwa da

Chapter 1 of 4