Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
makaranta, an nemo mata B.U.K level 1 inda su hidaya ke level 2 hundred, sun fita da aji daya. Komai nata na tafia neat a gidan ta kara kiba ta kara fari da kyau kamar ba ita ba. Mamyn su farouk ce zaune tana shan fruits, ta wani bangaren kuma tana hango dacewar farouk ya auri Rufaidah, sai dai bata son ta gaya masa ko ta sanya shi yayi Dole tafi son ya furta da kanshi. Zata ci gaba dayi masu addua in Akwai alkhairi Allah yasa masu son junan su, in hakan ta kasance sai tafi kowa farin ciki. Areef kam abu kamar wasa wai karamar magana ta zama babba tun ranar da umman su tayi mashi maganar hameedah ya kasa sukuni, karshe dai har sai da ya kwanta a asibiti, umma kuwa cewa tayi whl Areef ko zaka mutu ka dawo sai anyi auran nan,, ka yarda ko kar ka yarda babu fashi indai nina haife ka bakai ka haife ni ba. Bayan sati biyu ne da fitowar shi daga asibiti, yaje har gida ya samu farouk yake gaya masa ya taya shi addua ga abinda umma tace,, farouk ne ya taso yazo dab dashi yace abokina don Allah ka saurare ni da kunnen basira, umma fa uwa ce a gareka kuma nayi imani baza ta cutar dakai ba, kayi hkr ka faranta mata, kaga ita kadai kake da ita baba ya rasu, kayi kokarin faranta mata har ranar da zaku rabu, kayi mata biyayya don Allah, whl baza ka tabe ba, Amman rashin yi mata biyayya akan auran nan da take son hada ku babban kuskure ne kayi hakuri kaci gaba da addua Allah ya sanya albarka a cikin auran. Whl ka ganni nan ni har so nike ace mamy ta hada ni da watan ma don kuwa yan matan yanzu sai a hankali har gwara ma ka auri ta gida, wadda kasan halin ta, akan ta wajen duk mayaudara ne akasarin su. Nan dai Areef yayi ajiyar zuciyar yace a gaskia farouk ko da zan auri hameedah to whl ba dan ina so ba zan yarda da auran amman fa ba zata samu soyayya taba, don teemah kawai nike so kuma ita zan so, babu wata mace da zata samu soyayya ta bacin ita. Kayi hakuri Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, yace amin. Yana komawa gida direct dakin umma ya wuce yake gaya mata ya amince da auran hameedah, umman taji dadi sosai ta ringa sanya mashi albarka, yanzu yaushe kake ganin za saka ranar? Yace ai komai yana wajen ta duk yanda tayi, sai in suna bukatar kudi suyi magana zai basu tun daga hada lefe da sauran abubuwa, tace Allah ya kai mu lokacin, ai wata daya za a saka yace yayi ummina tace yau babana Allah ya maka albarka. Nan dai ya tashi ya dakyar don baijin kwari a jikin shi ya nufi dakin shi. Umma kam komai yayi daidai harta fara shirin biki, ankai kudin aure gidan su hameedah,, ranar Friday ma zasu tafi Dubai ita kawarta don zuwa hada lefe da abinda ya kamata. Hameedah kam sai murna take Allah ya amsa adduar don tana kaunar yaya Areef sosai shine dai baya sonta, kuma ta dau alwashin sai ta bi duk wata hanya da zata bi,, don ta shawo kansa ya sota fiye da kowacce mace. Toh masu karatu muje zuwa dai don jin yanda zata kasance ku biyo ….. S B R [truncated by WhatsApp] [10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [30/7/08:11pm] SADEEY S ADAM & RASH KARDAM WITH BEEBAH LUV MA’YAUDARAH 55~58 Bikin Hameedah da Areef ya kankama dan an Gama shirya komai lkci kawai ake jira… Areef kuwa hankalinsa a tashe yake duk da dai yayi biyayya amma har yanxu baya jin ko k’wayar son hameedah a ransa. **************** Teemah harka ta k’ara kankama karuwanci ba Kama hannun yaro,ta k’ara goge Wa a fagen yaudara.. ta zama hajjaju, yanxu gani take tafi k’arfin duk Wanda baya da ‘ya’yan banki(kud’i) Idan ‘yan mutuncinta sun motsa takan ziyarci futha kuma duk lkcin da taje Sai taji kishi kuma tayi sha’awar dama itace futha amma idan ta hango zaman guri d’aya kullun Sai taji auren ya gundireta… Ji take bazata iya zaman guri d’aya ba saboda ta Saba samari na d’aukar suje guraren shak’atawa kala2,dan hka gidansu ma bata fiya zamansa ba. Yau ma kamar kullun ta Gama shirinta tsaf Tana jiran azo a d’auke ta su tafi yawon shashancin Ummanta ce taxo ta zauna kusa da ita tace “inaso ki nutsu muyi mgna” “Ina jinki”ta fad’a ba tare da ta kalleta ba dan kuwa tasan da wacce taxo. “Fatima inaso ki nutsu ki gane cewa ita duniyar nan ba Aljanna bace,ya kamata ki gane kuma ki dawo hayyacinki” tad’an yatsina fuska tace “umma wai me kuma akace na yi?su fa mutane basa son ganin cigaban mutum sunfi son kullun su ganshi cikin bak’in ciki” “cigaban wace Mace ce kamarki xa’ace har yanxu bata da ko tsayayyen mijin Aure?tirr da irin wannan cigaban wlh wannan ci bayane” “Amma umma……….ki rufamin baki fatima” Ta dakatar da ita sannan taci gaba da fad’in “yau kusan wata 3 dayin bikin k’awarki amma ko a jikinki,duk sa’oinki sunyi Aure wasu ma harda ‘ya’yansu amma ke na rasa abinda ke damunki,shin Ina kike xuwa kullun dan kinga na zuba miki ido ko?to wlh kiyi a hankali duk wannan tarin samarin ace kin rasa Wanda zaki fidda a ciki?karki Manta idan an ciza……dole a hura..ki bi duniya a hankali dai” “Umma sanin kanki ne nima inason in ganni a d’akin mijina to ai komai yanada lkcin umma lkcina ne har yanxu Allah bai kawo ba” “Allah ya kawo mana ke dai kikai watsi da damarki sbda ‘ya’yan masu hunnu da shuni sun hure miki ido,ki dai bi a sannu Kar kixo ki rasa mijin Aure kinsan dai hak’orin dariya shi ke cizon yatsa” Duk da dai ta ji haushin kalaman umman tata amma Sai ta daure tayi dariya tace “Umma karki damu kinsan guga inta dad’e a ruwa tafi d’ebo da yawa,na tabbata akwai Wani tanadi da ubangiji yamin Wanda Sai kunsha mamaki kedai Kisha kurumin ki” (mudai cewa mukai a hakan ) “Allah ya tabbatar da alkhairi” “Amin umma hka nake so ki tayani da addu’a” “Inayi ai kullun cikin yi muku nake” Haka suka b’arke da hira har xuwa lkcin tafiyar Teemah sannan tayi Wa umma sallama ta tafi. Written by S B R [Truncated by whatsapp]. [10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [7/5/6:47am] RASH KARDAM & SADEEY S ADAM WITH BEEBAH LUV MAYA’UDARA 58-60 Teemah tayi sallama wa Umma ta fito daga gida wani had’add’e mota ne ya faka a gabanta tare da zuuge glass d’in motar fiskansa d’auke da murmushi ya sakar ma Teemah. Cikin ta kun k’asaita Teemah ta iso gefen motar ta kallesa ta ce”ai na d’auka bazaka zo ba ne”. Sai da yayi murmushi ya ce”hajjaju ayi hak’uri go slow na samu a hanya shiyasa”. Fitowa yayi ya bud’e mata k’ofar gaban motan tashiga ciki suka bar unguwan. Tafiya mai nisa sukayi kafin suka iso k’ofar wani makeken hotel nan ya danna hanci motarsa suna zuwa suka fito d’aki mai lamba goma suka shiga ba laifi d’akin ya mugun had’uwa bana wasa ba. Teemah suna Shiga tayi jifa da Jakarta ta cire hijab d’in dake jikinta wani riga ne mai hannu best ko cibi bai sauk’a mata ba, sai wando wanda zamu iya kiransa da shi da babu duk d’aya ne. A hankali Nass ya tako gunta tare da janyota jikinsa nan ta fara aika mata da sak’onninsa ganin sun shagala da yawa muka bar d’akin. Teemah basu bar hotel d’innan ba sai da magriba ta koma gida cikin ladabi in ka ganta ka d’auka Ustaziyan gasky ne hijab har k’asa ga nikaf Umma har tana alfahari da Teemah tana da nutsuwa, hankali ga kamun kai.************ 3 months latter. Teemah na hango kwance ta rame tayi bak’i bakintan nan yayi ja-jazur da shi ya d’an kwaile, Umma ne ta shigo tana fad’a “Fatima nikam nagaji kulum kina kwance a gida ga ciwo sai cinye ki yakeyi jibi fa yanda kika dawo duk ki banki kin gama ramewa”. Da kyar Teema ta d’ago kai ko da muka kalleta sai da mikayi baya da sauri wannan kamar ba Teemah ba. Kasa juran d’aga kai d’in tayi ta koma ta kwanta Umma ne ta fita ta kira mai Napep ya zo har k’ofar gida ta shiga ta d’auko Teemah da ta dawo kamar kwarangwal suka shiga Napep suka tafi Asibiti. Suna zuwa aka basu gado nan aka d’ibi jininta da fitsarinta aka gwada gwajin farko ya nuna musu cutar k’anjamau take d’auke da shi, Likitan da kansa yazo ya samu Umma sai da ya mata nasiha kafin ya juya ya kalli Teemah cikin ta kaici da yaji budurwa ce ya ce Fatima kina s’auke da cuta mai karya garkuwan d’an Adam, take Teema ta zaro ido Umma kam yankan jiki tayi ta fad’i a k’asa sumamiya, Teema jiki ba k’arfi ba halin mik’ewa sai dai kuka takeyi, Dr ne ya kira nurse sukazo bata taimakon gaggawa. Cikin ikon Allah ta far-fad’o nan ta fara tuna mai ya faru kuka ta saki tana fad’in Fatima ta cucesu ta zubar musu da mutunci yaushe ta yarda tarbiyan da ta bata da wannan tunanin bacci ya sake d’aukanta. Gidansu Areef biki ake ba sanya Walima kawai hajiya ta shirya sai dinner ranar jumma’a bayan Sallah jumma’a dubban mutane suka shaida auren Areef da Hameeda auren da ya tara manyan mutane bayan d’aurin aure maza suka wuce hotel dan gabatar da liyafa da yamma kuma akayi waliman mata, waliman da ya tara jama’a anyi wa’azi mai ratsa jiki wanda yasaka Hameeda jin zatai ma Areef biyayya koda zai wukanta ta don niman aljannata. Da daddare angwaye suka fito cikin shirin dinner ko da na kallo Areef shima yasha kyau ana haka a ka kwashi kawaye suwa gun Hafcy na hango ta rik’o hannun Hameeda cikin wani cut less mai tsada sai kyalli takeyi ko da Areef ya hango ta sai da k’irjinsa ya bada rass!!! Cikin zuciyarsa ko cewa ya ke”tsarki ya tabbata ga ubangijin halita tabbas Hameeda tayi kyau ba na wasa ba”. Kasa d’auke idonsa yayi ko mai ya tuna take yayi tsaki yana mai jin haushin kansa da irin kallon da yake mata. Written by S B R [Truncated by Whatsapp]. [10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [10/08/08:41] _SADEEY S ADAM_ & _BEEBAH LUV_ WITH _RASH KARDAM_ *MA’YAUDARAH* *66-70* Teemah ce zaune a falon gidansu tayi tagumi da hannunta duka biyun.. tsantsar nadama take, tayi nadamar abubuwan da ta aikata a rayuwarta… Yanxu Ina samarin?Ina gayun?Ina ado da kwalliyar??, Duk babu kowa ya gujeta k’awayenta duk sun gujeta idan ka d’auke Futha da take k’aunarta saboda Allah… Umman ta ce ta shigo taga halin da take ciki,ga abincinta a gefe har ya fara hucewa.. Nasiha da rarrashi ta zauna tana yi mata wanda sai da ta zubda hawaye sosai.. Ina ma ace tun kafin wannan larurar ta sameta ta nutsi… Kaii d’an adam yaji tsoran Allah dan kuwa ita darasi ce ga duk wata wadda take biyewa samari da wadda take cewa sai ta wanki gara.. Tabbas gara zai wanke ta ya barta a banza.. A yau Umma kam taji dad’i tunda har teemah tana kuka sbda nadama…. ********************** Ta gama shirya komai na lunch akan dining table.. Sannan ta Shiga d’aki tayi wanka ta cancad’a kwalliya cikin wani _Orange lace_ d’inkin _towel work_ ne yayi mata d’as a jiki tayi kyau sosai…. Ita kanta saida ta tsaya a gaban _mirror_ tana fad’in Anya nice kuwa..?? Falo ta sake dawo wa,taga har yanxu bai fito ba kusan awa uku da gama girkin har taje tayi wanka amma shiru kamar baya gidan?? Cikin fargaba ta nufi d’akinsa, Da sallamarta ta Shiga Yana zaune a k’asa Yana danna laptop,ba mamaki _chatting_ yake a _Facebook_ dan kuwa sai smiling yake yana ganin ta ya had’e rai kamar ba’a tab’a halittar annuri a fuskarsa ba.. A tsorace ta tsugunnan tace “Yaya an kammala abinci fa” *Mtswww* yaja tsoki ya cigaba da abinda yake… irin Mai mijin nan sai ta saka hannu ta rufe laptop d’in cikin tsokana tace “ka gama cin abinci kafin ka cigaba,kasan bana son ka zauna da yunwa” Mari ya kifa mata har sau biyu “ke wace irin jahila ce da xaki rufe Abu ba tare da an kashe ba,uban wayace ki shigomin d’aki,to baxan ci abincin ba dole ne? stupid” ya fad’a cikin d’aga murya… Rik’e kuncinta tayi sannan ta tashi ta fita tana kuka. _By S B R _ [Truncated by Whatsapp] [10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [6/8/2:00pm] BEEBAHLUV & RASH KARDAM WITH SADEEY S ADAM MA’YAUDARAH 60~65 Dinner tayi dinner anci, ansha, kuma anci uban nera don kuwa tayi kuka sosai,, ba a tashi ba sai karfe sha biyu na dare, amarya kam tayi farin jini kuma tayi bala’in kyau, kowa yabon ta yake kamar wata Queen,, abokan shi kuwa sai yabon ta suke suna cewa yayi dacen mata, yakan ji dadi a lokacin da aka yaben ta, shima tana birge shi kuma yakan ji wani abu a zuciyar shi sai dai kuma kome yake tunawa sai yaji yatsane ta. Angwaye sun maida amare gida akan zuwa gobe za a zo daukan amarya, a mota ango yakan dan janta da hira kadan badan yana so ba. Washe gari ankai amarya gidanta, kawayen da abokai sunyi chilling masu yin yan mata nayi ansha Cece kuce shidai ango ba ehm ba ehm ehm, yana ta imagining dama teemah shi ce abar kaunar shi da yafi kowa jin dadi, haka dai suka watse aka bar amarya da ango, bayan rakiyar abokan shi ya dawo ya wuce dakin shi ya shiga wanka bai kuma waiwayen ta ba ya kwanta baccin ma dai sai barawo ne ya dauke shi. Itama bayan fitar su bata wani damu da dawowar shi ba tayi wanka tayi Sallah tayi addu a ta kwanta daman akwai gajia a tare da ita bata farka ba sai 6 har sai da tayi lattin sallar asuba. Da safe ta cancada kwalliyarta, tace bari ta zagaya gidan ta gani tayi deciding abinda zata nemar masu su ci, ta fita tayi zagayen gidan yayi kyau sosai ta gode ma Allah ta daya kaita wannan matsayin,, taji ana knocking tana budewa taga yan aike daga gidan su an kawo abinci,, ta jere su bisa dining table ta dauko duk abinda za a bukata ta zauna jiran megidan bai tashi fitowa ba sai kusan 12 saura yayi wanka sai kanshi yake, yana fitowa taje ta tare shi ya Areef ina kwana ya amsa a takaice, da fatan an tashi lfy tace lfy kalau, ga abinci umma ta aiko mana, ok na koshi yayi hanyar waje nizan fita bai jira amsar taba yayi waje,. Umman teemah ta dade bata farka ba, wannan ta farfado har a lokacin kuka take tana Allah wadai da halin da teemah ta tsinci kanta. Nan dai likita ya bata baki akan tayi hakuri jarabawa ce ta ubangiji haka Allah ya kaddaro, ta kwantar da hankalinta zai dora teemah akan maganin dazai bata, zata dade sosai a dunia akwai masu cutar in ta gansu ma baza tace suna da cutar ba, sai sanda kwanan su ya kare, yanzu ma dasun zo da wuri asibitin ya daura ta akan maganin tun wuri da bai nuna a jikin ta ba haka, sai dai addua Allah ya kara kare wa, nan dai yayi tayi wa teemah fada tana ta zubar da kwalla tana dana sanin rayuwar datai a baya, Allah ya yafe mata tana ta kuka. Nan dai doctor ya bata gado don samun karfin jikin ta da kuma lfyr ta. Su Futha amare ana can ana tashan luv, don kuwa komai bata nema ta rasa ba haka duk wani motsi nata sai ya tambaya any problem? An sai mata wata arniyar mota “BENZ” sannan sunje honeymoon kusan 4 months sukai acan kasa she 4 suka je DUBAI, LONDON, INDIA, sai kuma suka wuce umara wato SAUDIA,, kai!!! A gaskia Futha tayi dace Allah yaba yan baya ma haka,, sun dawo 9ja a lokacin da karamin cikin ta wata 4 cip cip,, tayi zagayen dangi daga nan ta kira teemah tace zata zo ta kawo mata tsaraba tace sai tazo bata da lfy ma. Ta wuce daga gidan su, ta shiga da sallamar ta,, ta tarar da umman su a tsakar gida tana zaune ta gaishe a a Futha yaushe kuka dawo ne? Tace yau kwana 5 umma Allah sarki an dawo lfy, tace lfy kalau umma ya mai jiki ? Hmmm umma tace da sauki ta nuna alamar damuwa ai sai dai addua Futha Allah dai ya shirya mana zuri a tace Amin,, Futha dai bata gane me umma ke nufi ba don bata san meke faruwa ba, Ta mika mata tsarabar data kawo mata sannan ta shige dakin, Allah sarki umma harda kwallar ta dama tata yar itama bata jefa kanta cikin ukuba ba gashi nan yanzu tana dana sanin rayuwar ta. Futha na shiga da gudu ta taso ta rungume ta tana murna,, Futha tace teemah wannan wane irin ciwo ne lokaci kankani kika koma haka kinyi baki,, kin kwanjame, kin rame, kamar bake ba,, hmmm nan fa suka zauna teemah ta fara kuka me tsuma rai hmm kedai bari yar uwa, kiga dai yanda na koma naki jin shawarar da kike ban da umma take ban da sauran mutane keban, yanzu ga halin dana saka kaina a ciki nan dai ta bama Futha labarin komai game da ciwon ta har yanda DR ya bata magani shine fa dalilin samun lafiyar ta har ta fara murmure wa,, yanzu dan kudin data tara dasu take siyan magani,, amman da kam whl da ta ganta baza ta gane taba,,, gashi yan unguwa da yan gari duk sunsan halin da nike ciki duk inda nayi sai daria ake min nikam na shiga uku na lalace,, kuma kinsan waya saka mun wannan cutar Khalid ne,, sai gashi mun hadu dashi a wurin blood test,,, yace zaizo gida muyi magana har yau bai zoba.. Futha tayi kuka tayi kuka sosai ta kuma tausaya wa kawarta,, nan dai tayi mata nasiha me shiga jiki, (“Toh yan uwa maza da mata kundai ga halin da kawata kuma aminiya ta futha yau yanda Allah ya maida ita kundai ji yanda take ada tana ganin rayuwar banza ita ce rayuwa har gani take ni ban waye ba, rayuwar banza lyk tara samari wannan yazo wancan yazo, aje ayi masha ‘a a dawo ba a tsoron Allah ba a tunanin gaba,, kece wancan hotel wancan gida duk kina tunanin birgewa ne, whl ba birgewa bane karshe dai sai mutum yayi dana sanin rayuwa ko baka dauki cuta ba sai kayi dana sani,, don haka ina me bamu shawara yan uwa akan mubi dunia a sannu ba madauwama bace kuma abinda ka shuka shi zaka girba,, yar uwa kar kiyi ikirarin cewa sai me kudi zaki aura, da talauci da arziki duk na Allah ne, kedai kiyi adduar Allah yayi maki zabi nagari a duk abinda kika sa gaba,, Allah yasa mu dace dunia da lahira.”) Ta bata shawarwari masu amfani a gareta da sauran yan uwa musulmai tace taci gaba da istigfari Allah yana son mai neman yafiya a gareshi,,, Ya Allah ka yafe mana dukkan kurakuran mu amin..sai kusan maghrib tabar gidan akan sai ta dawo duba ita nxt tym.. Kai teemah ranar tayi dana sanin rayuwa tayi kuka tayi kuka har ta gaji ta kuma dau alkawarin duqufa ta nemi aljannar ta, dayin biyayya ga mahaifiyar ta da tilon yayan ta wanda yake uba a gareta a yanzu. **Bayan shekara daya** Sai muka leka gidan su farouk inda muka hango su Rufaidah an zama yan gida hankalinta a kwance ta murmure abinta tana ta zuwa skul,, gata da kokari,,, tana birge farouk kullum ji yake yana kara kaunar ta a ranshi, komai take so shi ake mata a gidan tun daga kan mummy har su farouk,,, farouk ya kasa sanar da ita har yanzu yana sonta sai dai mummy ta gano shi kuma ita ma ta gano akwai wata a kasa don kullum suna tare in bata je skul ba daga ya dawo daga aiki,, mummy tayi deciding tayi musu maganar tunda taga alamar a tartare dasu,. Hakan kuwa akai ta tara su a parlour, take ce akwai magana duk suka saurare ta, tace so take ta aurad da kowa daga cikin su,, shi tayi mashi mata itama tayi mata miji,, nan fa suka fara kallon kallo,, toh fa me mummy ke nufi su dai sunsan suna son juna Amman basu gayawa juna ba gashi mummy na shirin yi masu tabargaza yaya kenan?? Mummy tace kai farouk yar gidan Anty Laura, ke kuma rufaida dan gidan baba sani wato haisam,, nan gumi ya fara aikinsa a jikin su, ita dai rufaida baza ta iya musawa ba duk wanda mummy ta bata zata karba, Amman fa tana kaunar ya farouk,,,. Farouk ne yayi gyaran murya mummy…… mummy….. ya kasa magana, tayi daria menene akwai magana ne? Yace ehhh tace ina jinka, daman… daman… ya kasa maganar ka fadi maganar ka ina jinka. Whl mummy ina da wadda nike so,, tayi murmushi irin na manya,, tace wacece wadda kake so din baka gayan ba sai yanzu danai maka matar ai babu fashi. Da sauri ya kalli rufaidah,, don Allah mummy kiyi hakuri whl inban aure ta ba zan iya shiga wani hali, ina sonta kamar raina,, wai wacece ne a ina take yar waye yar wata unguwar ce? Sai da ya gyara zama sannan yace mummy ba wata bace a cikin gidan ki take gata ma a kusa dake ya nuna Rufaidah.. Mummy tayi daria take YAN QOTA ai daman so nake na tabbatar da abinda nike gani kuma nike ji a wurin kannan ku, toh Alhamdulillah daman haka nike son ji komai ya yi Allah ya sanya alkhairi a cikin lamarin,, yanzu sai muje neman auran ta a wurin yayarta ko,, Rufaidah da sauri tace a a mummy whl sai dai a tafi katsina daga baya a gaya mata in anje. Nan dai suka tsara yanda abun zai kasance zasu je katsina neman auran nata, don mummy bata son aja abun da sauri take so ayi wata daya kacal za a saka, murna a gidan ba a magana har fa yar walima aka hada…. Urs….. S B R [truncated by WhatsApp] [10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam: RASH KARDAM & SADEEY S ADAM WITH BEEBAH LUV *MA’YAUDARAH* _71-75_ Areef wulak’anci kala-kala yake ma Hameeda tana hakuri da shi in ya kuntata mata sai ta shiga d’aki tayi kukanta ta share hawaye, addu’ar ta kulun Allah ya karkato mata da hankalin mijinta gareta. Bikin farouk ya kan-kama yau saura sati guda duk wani abunda ya dace sunyi Hajiyar Farouk da kanta ta ke gyara Rufaida. *6 DAYS LATER* Yau juma’a dubban mutane suka shaida d’aurin auren Umar Farouk da Rufaida abun sai fatan Allah ya basu zaman lfya , abin sai son barka, basuyi wani shagalin k’arya ba Hajiya ce ta shirya musu walima da yamma aka gabatar. Da dadare aka kai Amarya d’akinta, zuwa tara na dare abokai suka rako ango suka musu nasiha gami da barkwanci daga nan suka musu sallama, muma kuma muka mik’e tare da basu guri don wannan lokacin sirrinsune… Aunty Farha kuwa tayi nadama sosai kuka taxo tana yiwa Rufaida kan ta yafe mata abinda tayi mata dan kuwa batayi mata rik’on kirki ba… ‘yar Tata da take tak’ama da ita ta kwaso musu cikin shege ga mijin aunty Farha ya saketa ya kora su yace baxai iya zama dasu ba… Ga yarinyar kullun laulayi take tana kwance ba lfya… Tana kuka tana bawa Rufaida hkri kan ta taimakesu da ko dubu biyu ce suci abinci… Kuka sosai Rufaida take ta Shiga bedroom d’inta ta d’akko dubu goma ta bawa Aunty Farha… Sannan tace zata xo ta dubasu idan yaya Farouq ya dawo… Haka Aunty Farha ta tafi tana kuka tana regretting abinda ta aikata ma Rufaida,yanxu gata cikin daula su suna cikin tsumma…(Duniya budurwar wawa). *********** Areef ne zaune a office wayarsa tayi k’ara yana dagawa yaga abokinsa Dr Saif ne ya ke kiransa. Ya d’aga tare da fadin” Allah ya kare mana likitan zamani”. Dr Saif ya ce”kana inane Areef maza kazo yanzu kaga wani abun mamaki ina cikin asibiti”. Kashe wayar yayi ba tare da ya ji abunda Areef zai ce ba. Cikin fargaba Areef ya dauko key din motarsa ya nufi asibiti. Office din Dr Saif ya nufa yana zuwa ya basa hannu suka gaisa. dr Saif ya d’akko wani file ya turo gaban Areef ya ce “duba ka gani” Cikin fargaba ya ce”na menene wannan file din?” Dr Saif ya ce” in ka duba zaka gani”. Da sauri Areef ya bude, rass!! K’irjinsa ya buga, ba komai ya gani ba illa takardan gwajin Teemah da cutar da take fama da ita har yayi worse sosai. Hawaye ne ya ke zuba daga idonsa “tabbas Teema kinci amana ta ni inanan ina fama da soyayyarki ko matana naki kusantarta sabida sonki”. Dr Saif ya ce”zo ka gani” haka Areef ya rink’a binsa sukaje gun da ake taron k’anjamau nan yaga Teema ido-da-ido ana raba mudu gani kyauta. Take yaji kansa ya sara godiya yayi ma Dr Saif ya shiga mota kasa komawa office yayi ya nufi gida. Yana zuwa ya samu Hameeda tana kuka ta kifa kanta akan kujera bata san da zuwan Areef ba. Jikinsa yayi sanyi sai yanzu ya tuna da ita marainiyace gashi Hajiyarsa ta basa amanarta. Jikinsa yayi sanyi a hankali ya taka yaje gun da ta kwanta ya sanya fuskarta akan nata shima sai yaji hawaye na sauka masa. Kamshin turarensa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take yi sai tajishi a jikinta kaman a mafarki. a hankali ta daga fuskarta ganin hawaye a idonsa abun ya bata mamaki, Areef na ganin ta dago ya durkusa akan gwiwansa ya had’a hannayensa yana rokonta gafara nan tasaki kuka tafad’a jikinsa… tun daga lokacin suka shirya don bata da wasu gatan da ya wuce su. Rayuwa mai dadi su ka gina cike da ban sha’awa har yana mamakin irin kaunar da yakeyi ma Hameeda ba yaso yayi nisa da ita. Teema a irin taron masu ciwon kanjamau da take zuwa wani zuwan da tayi suka had’u da Khaleed nan yaba ta hakuri nan suka dai-dai ta kansu akan zatayi Istibura’i sai ya aureta tun daga lokacin ta bar gari ta tafi gun yan uwan Ummata…. *********** FIVE YEARS LATER… Hameeda na hango da yan ‘ya’yanta sun fito cikin super market Areef na rike da key din motansa, Teema da Khaleed suma sun zo, nan suka gaisa Teema taga matar Areef ta hadu iya haduwa amma ina yanzu ya mata nisa gata matar wani fatan alkairi sukayi majuna su Areef suka shiga mota suka tafi. *ALHAMDULILAH!* ala kulli halin.. _komai yayi farko zaiyi k’arshe_ _Anan muka kawo k’arshen wannan littafin mai suna *MA’YAUDARA* kuskuren ciki da mukayi Allah ya yafe mana_ Ameen *SADAUKARWA* Mun sadaukar da wannan littafin ga ‘Yan Mata da Samarin Zamani… *WANNAN LITTAFIN TUKWICI NE GA* _’Danmu Abin Alfaharin mu our luvly *AREEF* Allah ya raya mana Kai cikin tafarkin gskya tare da sunnahr manxon Allah (S.A.W)_ *Godiya ta musamman ga* _dukkan group din *Online Hausa Writers* Allah ya barmu tare. *TSOKACI* Yan Mata da Matasan zamani kun mai da yaudara ya dawo abin ado a gare ku kunga kadan daga illan masu yaudara da kwadayin abun hannu saurayi ya kai Teema ga fad’awa halaka da nadama mai tarin yawa Allah ya kyauta yasa mu gane gsky Ameen. Urs S B R.. Munai muku fatan alkhairi…. Luv u alot swi[truncated by WhatsApp] Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu

Chapter 4 of 5