Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels  Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 MAYA’UDARA-Page-1- to-end OCTOBER 20, 2016 | RASHIDATKARDAM | 3 COMMENTS [10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [6/5/6:30pm] RASH KARDAM & SADEEY S ADAM WITH BEEBAH LUV YAUDARA ( Bismillahir Rahmani Rahim) {Allahumma Salli Ala Muhammadin Wa Sallim} Ranshi a bace yake sosai, ya rasa meke masa dadi,, duniar tayi masa zafi,, ya ciji lebe, ya ciji yatsa, duk shi kadai, yayi zagayen a daki ya koma Parlour, sai gumi ke keto masa duk da sanyin Ac,, kamar wani zautacce. Ba kowa bane illa “”AREEF”” Daukan waya yayi ya kirata yafi sau 20 amman bata dauka ba,, wai me yasa Teemahluff ke mishi haka,, Kodan taga yana bala’ in sonta ne?? Ya kuma dialing wayar frnd dinsa farouk,,bugu daya ya dauka, bayan sun gaisa ne yake ce masa, ya akai ne abokina ya gidan ya akwai labari ne? Yayi tsaki tare da cewa whl kasan matsala ta guda daya ce akan teemah,, nayi kiranta but she refused to answer my calls.. Farouk ne ya girgiza kan shi, tare da tausaya wa aminin nashi, don kuwa yasan yana cikin matsala,,, baisan me zaice mishi ba wanda ya wuce ya bashi hakuri,, tun farkon soyayyar su da yarinyar shi daman batai masa ba,, kuma yasha bashi shawara akanta, amman yaki ji, har fada sunyi akan teemah. So daga baya sai ya yanke shawarar zuba mashi ido akanta, inya kawo masa kukanta sai dai kawai ya bashi hkr ya kwantar masa da hankali,, amman yasan yarinyar kawai cheating take ma abokinsa, yasan ba son shi take ba, sai dai yace Allah ya ganar dashi gaskia.. Kamar kullum yanda ya saba bashi hakuri yau ma hakan ce ta faru, yace ya sake kiranta may be, bata kusa da phone din ne,, haba farouk I called her more than 20 tyms fa.. Bari kawai naje gidan su,, yanzu. Ya dire wayar yana ajiyewa ya sake kiranta still no answer,, ya dauki key din motar sa ya fice daga gidan.. A bangaren Teemah kuwa,, tana ganin calls din sa taki dauka, don kuwa yau batai niyar ganin shi ba,, kuma tasan shi da dan karan naci zai iya ce mata zai zo.. Mstwww tayi tsaki aikin banza kawai, sai shegen nacin tsiya. Hmmm masu karatu last week fah ta gama tarairayar shi, ta amshe masa yan kwabban sa, wai za ai bikin kawarta nxt week,,, Yanxu haka wani take jira, zai zo yau kuma shi zata wanka. Areef bai zame ko ina ba sai kofar gidan su teemah, nan ma yayi kiran dunia taki dauka, ya kira wani yaro ya aike shi cikin gidan, ya kira mashi ita,, ai kuwa yana zuwa ta balbale shi da masifa, dallah je kace mishi bana nan na fita unguwa,, yace toh har kama hanyar tafia tace zo nan, ya dawo ta kama kunnen sa kuma sauran in kaje kace nice nace bana nan,,, whl sai nayi maka dukan tsiya in muka gamu,, kuma in ya tafi ka dawo ka gayan,, yace toh daman yasan hali. Bayan fitar shi ummanta tace,, anya teemah baza kima kanki fada ba ko?,, whl duk ranar da Allah ya tashi kamaki baza kiji da dadi ba. Bata ce komai ba tayi wucewar ta daki, tana kunkuni,, uwar tace hmmm ayi dai mu gani.. Bayan an gaya masa bata nan,, ya dauko naira 100 yaba dan Aiken,, sannan ya zauna cikin motar yayi tagumi, ya kulla wancan ya kunce wancan duk shi kadai,, yakai har kusan 10 to 15 mins bai tafi ba,, sai can ya tada motar shi ya tafi… Har yanzu bai ji ya tsaneta ba,har yanzu ji yayi kamar kara rura mashi wutar son ta ake a cikin zuciyar shi,, Allah sarki daman ance so hana ganin laifi.. After tafian shi da 10 minute kuwa sai ga wanda take jira yazo me suna Haydar, daman tana ta Allah2 Areef ya tafin kar su hadu… Nan aka chanchada kwalliya,, me jan hankali aka fito ana yatsina ita a lallai ga me saurayi.. Teemah fara ce doguwa, amman bata da wani kyau,, tana da dukiyar fulani daidai gwargwado,, amman kuma kasan sha6al yake don kuwa sungul ta tafi,, abinda ya Cece ta farin da take dashi,, don ko gashi bata dashi, ita dai wannan farin da iya kwalliya da kwalisa da kuma shagwa6a da kwarkwasa,, shine yake jawo mata samarin, har take samun damar yaudarar su.. Tasan duk wata salon hanya ta yaudara da iya kwacewa samari abin hannun su,, don kuwa indai har Allah ya hada ku, toh ka shiga uku a wurinta sai tasan duk wata hanya data amshe maka kudin ka sannan ta rabu dakai…. Toh masu karatu ga dai Haydar nan a gaban teemah,,, bamu san ta yanda zata bullo masa ba don shima wankar sa take son yi… Ku biyo mu don jin yanda zata karshe,,, don yanzu aka fara yanzu aka diga damba a wannan lbrn me suna YAUDARA don kuwa akwai gwagwarmaya a cikin sa sai kun jimu… Daga masu kaunar ku. S B R Marubuta Uku [truncated by WhatsApp] [10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [7/5/6:47am] RASH KARDAM & SADEEY S ADAM WITH BEEBAH LUV YAUDARA Pg Hydar tunda ya hango ta yake smiling,ita kuwa sai gwargwasa take a hankali take tafiyar kamar mai tausayin k’asa haka dai ta k’araso gurinsa cikin kisisina irin ta mayaudaran Mata. Jingina tayi da motar sannan tad’an had’e rai ba tare da ta kalli hydar d’in ba. Murmushi yayi sannan ya rage glass d’in motar ya kuma bud’e Mata “Allah yasa dai banyi laifi ba”,murmushin makirci tayi Wanda shikesa samarin nata su rud’e suna kallon duk duniya ba Wanda yakai teemaluf iya soyayya da kuma kyau. “laifi ai ka gama yinsa my D kasan awowin da na d’auka ina jiranka kuwa? amma kak’i xuwa a lokacin da kace zakazo” tad’an k’ara b’ata rai “ka koma wajen wacce kake so tunda yanzu ni baka sona”, a gigice ya kalleta “haba teemah kinsan kuwa duk duniya ba wacce nake so kamar ki,wlh bani da wadda ta fiki,na b’ata lkci ne wajen siyo Miki kayan da kika buk’ata pardon me pls ” “murmushi tayi najin dad’i “dan kasan baka laifi a guna shiyasa kake min haka but next tym in ka kuma I wl punish u”, bazan kuma bama” tayi dariya sannan ta Shiga cikin motar ta zauna, ya kake ya mummyna(mamanshi)?”, lafiyanta k’alau tace a gaida surukarta kuma Yana son ganinki yaushe zakije mata?” , hmmm “zan duba ko da week-end ne Sai naje kasan yanzu Ina busy ga bikin bestyna ga kuma skul”, ok Allah kaimu” “Ameen my D”. Sunyi hira sosai yasha kisisina da iyayyi da shagwab’a shi kuma hakan ke burgesa ga teemah Ta wankensa sosai d’an kuwa Sai da ya rubuta mata cheque na 50k sannan ya mik’o mata Manya manyan leda guda 2 sukayi sallama ta fito daga motar sannan ta juyo ta kalleshi “Am vry proud of u my D,Allah barmu tare har k’arshen rayuwarmu”, “Ameen teemah” ya amsa a tak’aice. “to ni zan shiga gida sbda magrib tayi ya kamata muje muyi sallah ko?” murmushi kawai yayi baya gajiya dajin zazzak’ar muryar teemah da kallon kyakkyawar fuskarta”(hmmm mukuwa SBR cewa mukai “kallon kitse akewa rogo “) “My D ya kayi shiru?”, hmmm “nothing”, hmm badai zaka fad’a ba nizan shiga gida my regards 2 mumcyna”Tana Gama fad’a ta shige gida, yad’an jima dan har Saida yaji an fara Kiran sallah sannan ya ja motarsa ya tafi cike da kewar teemahluff d’insa. ******** Misalin k’arfe 02:30am Areef ne keta juyi kan makeken gadonsa ya rasa me keyi masa dad’i anya kuwa teemah unguwa taje? Ya tambayi kansa To kodai bata da lafiya ne shiyasa tak’i d’aga wayar kuma basa so su tada mai hankali suka k’i fad’amai gaskiya da yaje?, amma yasan teemansa bata tab’a k’in d’aga wayarsa ba saidai in Bata gurin ko a silent ta saka wayar kuma data ga missed call d’insa take kiransa Gskya ba lafiya ba dole gobe na koma gidan dan ganin meke faruwa Allah yasa dai lafiya duk a zuciyarsa yake tunanin Tashi yayi ya Shiga toilet ya d’auro Alwallah yayi ta jero nafiloli tare da yiwa teemansa addu’a,sai da yayi sallar subhi sannan bacci mai nauyi ya d’aukeshi. ********** Tun k’arfe 11:00am teemah tayiwa bestynta waya tace dan Allah tazo yanzu2 akwai Magana Futha na break fast taji Kiran bestynta dan haka ko gamawa batayi ba taje ta watso ruwa,tayi sauri tad’anyi makeup taja hijab tace wa mamanta tayi gidansu teemah yanzu zata dawo “Karki dad’e Futha saboda d’aura abincin rana”, “insha Allahu baxan dad’e ba” ta fad’a tare dayin waje har tuntub’e take don son zuwa taji gulma dan kuwa tunda taji teemah tayi Mata Kiran sassafe tasan da Magana. Tana Shiga gidan teemah taja Futha d’aki ta d’ebo ledojin ta juye a gabanta,atamfofi guda 4 da Swiss lace guda 3 sai veils da kayan makeup da kuma turaruka masu sanyin k’amshi Futha ta saki baki tana kallon kayan cike da mamaki tace “kina cutar Areef da yawa teemah ko wlh kiji tsoron Allah bafa sonshi kike ba amma kike Yi masa muguwar YAUDARA ina tausayinki Randa Allah ya tashi kamaki” Hmmm “ya tashi kama mu dai kema ai kina YAUDARAr samarin,samarinki nawa, dariya Futha tayi sannan tace “dama in kanayin Abu sai kayi tunanin kowa ma nayi to wlh k’arya kike min besty Samarina biyu kacal kuma in kinga sun yimin kyauta su suka Sa kansu ni bana YAUDARA Kawai dai duk Wanda Allah ya zab’amin a cikinsu zan aura” “sai kiyi tayi kuma in fad’a Miki yanxu duniya ta canza ni samarina basa k’irguwa uncountable ne wasu ban sansu ba sai recharge card ake watso min,Areef kuma tuni na gama yayinsa na wankesa sosai na yadda shi, yanxu wani hydar ne on top,in fad’a Miki bayan kayannan har cheque ya rubuta min na 50k kuma da sunanki na wankesa nace bikin bestyna za’ayi,futha wayake tausayin maza yanxu ca6 wlh wankar banxaye zanyi dariya Futha tayi “ba dama teemah yanxu dai a karb’o kud’in a bani kaso na tunda da sunana aka wankesa”, “kinma Isa keda kikace ina YAUDARAr samari to bazan bada ba” “wlh dole na fad’a Miki gskya besty ko xaki mutu,kuma sai kin bani Swiss d’aya da 5k” Dariya sukayi su duka teemah tace “kin manta sunana TEEMAHLUFF tun muna sec skul kuka samin sunan shiyasa LUV d’in ya bini har girmana dashi na samu damar wankar samari” “hakane kam k’awata nima dazan samu damar wanka da na wanka saboda ba kyaune dake ba makeup ke taimakonki ni kuma ga kyau ga makeup but ban iya YAUDARA ba amma nima zan Maida sunana FUTHA LURV dan na d’an wankesu kad’an ba kamar naki ba”. dariya sukai sosai teemah tace “Ashe kema kinason wankar samarin dama ce baki samu ba” futha tayi dariya sosai sannan tace ” am joking fa wlh ban tab’a Jin son inyi yaudara ba” teemah tace “ohh kenan ni mayaudariya ce?”, “oho Miki” suka sake yin dariya sannan suka ci gaba da hirarsu. Urs… S B R (Triple Writer’s) [[truncated by WhatsApp] [10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [8/5/2:19pm] RASH KARDAM & SADEEY S ADAM WITH BEEBAH LUV YAUDARA Pg 3⃣ Sunyi hira sosai da Futha, can Teemaluff Tace”ke yar gari, tsaya muga miye a cikin laidan nan da ya kawo, suka zazzage kayan ciki, Riga da skirt ne, masu ‘kyan gaske, sai dogayen riguna, masu duwatsu, ajiki, sunji ado sosai, sai wasu takalma da turaruka masu kyan gaske designers. Shewa sukayi tare da tafawa Futha Tace”Teema kinyi wuta fa, Teema ta rausaya idonta, tare da juyasu, hmm ke ae bamuyi komai ba. Yanzu nafara wankan garori. Futha ta kaleta Tace”Allah yasa ki gane ki dawo hanya. Dariya sukayi dukansu, sai dab magriba Futha tayi shirin tafiya, Teema ta d’eba mata, turare da su powder, da su lip gloss, masu kyau ta bata. Sai da tayi make-up kafin ta rako Futha, tafiya takeyi, kamar bazata taka kasa ba, tana karairaya, wanda duk d’a namiji in ya ganta, sai ya kyasa. Sun fito bakin titi, suna jiran mai Napep ke nan, wata katuwar jeep ce tazo wucewa, har ya tafi ya dawo, dai-dai inda suke ya rage glass d’in motarsa, yana kalon Teema da ke kwar-kwasa, tana juyi tamkar sarauniyar kyau. Cikin sanyin murya Yace”Hajiya ya kk? Ina zuwa haka?. Sai da ta rausaya ido ta jujjuya jiki, ta bud’e baki, ta fara magana cikin salon YAUDARA da kisisina irin na wayyayun mata, kawar da fiskanta gefe tayi, kafin Tace”k’awata ce mai tafiyar, shikam baki yasake yana kalonta, don ta matukar tafiya da tunaninsa. “Ok! To kefa? Sai da ta d’anyi fari da ido, Tace” tazo gaidani ne, na mata rakiya. Futha da ke gefe, saki baki tana kalon ikon Allah. Teema lokaci d’aya, ta sauya salo, kamar ita bace suka fito tare ba, a zuciyarta, Tace”eh! Tabbas Teema ta ‘kware taci sunanta Teema lurv. Mai mota ya kali Teema Yace” Hajiya zan iya samun phone number ki? Sai da ta fari da ido, cikin da barata boye babban wayarta, ta ciro ‘karaman ta mika masa, yana karba ya juya wayar a hannunsa,Yace” kina babban Yarinsa kamar ki ace wannan ne wayarki?. Wani murmushin YAUDARA Tace”ya zanyi wayar tawa kenan, tana kwarkwasa. Kansa ya gir-giza, Yace” dole na san abinyi, kamarki ace kina rike wannan wayar, ba girmaki bane. Murmushi ta masa, Tace” Ranka shidad’e ayi haka?. Murmushi ya mayar mata, “karki damu ae kinfi haka a gurina. Futha da ta tsaya tana kalo, Yace” ko zan sauke k’awar taki a gida, “ok! ba matsala da ka kyauta. Da ‘kyar Futha ta, tashiga motarsa ya kaita gida. Wa she gari da yamma, “Khalid ne ya wayar Teema, ya sanar mata yana zuwa, yau da daddare. Cike da murna da rawan kai, ta shirya, cikin kayan da Haiydar ya kawo mata, riga da wando tayi kyau sosai, tayi zaman jiran zuwansa. Sai da karfe ta’kwas da rabi ya iso k’ofar gidandu Teema cikin motarsa mai glass baki. Wayarta ya kira ya saida mata, yana ‘kofar gida, Tace” gani fitowa My Sweet Heart. Sai da ta ‘kara yin ‘kwaliya kafin ta fito, cikin yanga da kwar-kwasa, Khalid tun daga nesa, ya zuba ma ‘kirjinta ido, wanda suke tsatsaye kamar biro, fiskanta nan ya sha make-up. Har ta k’araso gurin bai san ta iso ba, sai da ta zo dai-dai fiskansa, ta hura masa iska, wani sassayan ajiyar zuciya ya saki, tare da bud’e mata ‘kofar motar ta shiga ya zagaya shima ya shiga. Zama yayi, ya k’ura mata ido, tare da sunkuyo da fuskan sa dab nata, yayi ‘kasa da murya Yace”Beb kinyi kyau sosai, har kinfi kulum. Rausayar da da ido tayi Tace”nagode amma kafi ni kyau. Haccinta ya lakace, Beb baki da dama fa.murmushi tayi mai k’ayatarwa. Hannuta ya kalla, ya sha lale, Yace” Teema inga hannu ki?, ‘boye hannu tayi, ni bazaka gani ba. Haka kika ce ko? Ni kuma yau sai na gani. Ta ‘boye hannu tayi, yayi ya gani ya kasa, ya kaleta Yace”dole na miki hukunci tunda kika hanani gani, kafin tace komai, sai ji tayi ya gantsara mata cizon wasa a kunneta. ‘Kara tayi irin na shagwab’a, ta murgud’a masa baki, lah! lah!, lalle yau kin tsokanoni, sai nayi maganin bakin, da kike murgud’awan, kama hab’arta yayi, yasoma shan janbakin, har sai da ya shanye duka, ya riko hannunta, mai da numfashi suka rinka yi, hirarsu da Khalid yawanci shafe-shafe ne saida suka gaji dan kansu, yari ko hannuta don ya mata rakiya. Wayar ta ne tasoma k’ara, sunan Areef ta gani, sai da ta faki, idon Khalid taga baya kalonta, da sauri tasaka wayar a silent, don yanzu Areef baya gabanta, ta gama da shi. Duk ta shagwab’e masa a jikinsa, sai shafa ta yakeyi, yana zuwa kan k’irjinta ya kira sunanta a hankali, Teema!, ta amsa a kasalance, Yace”ina son nan gun, k’irjita a shafa, yana birgeni sosai. murmushi tayi Tace” Allah ko? Ya gyad’a mata kai alamar eh!.(Yan matan Zamani, mafi yawanci yanzu irin soyayyan da kukeyi kenan, na tab’e tab’e, kusani namiji yana gama latsaki, daga lokacin darajanki, ya ragu a gunsa. Ina mai shawartan ku, da ku kiyaye, guys abunda suke so kenan, ba soyayyan gaskiya, suke maki ba). Urs… S B R. (Triple Writer’s). [[truncated by WhatsApp] Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: 07039625239 [10:14PM, 9/21/2016] Rash Kardam: [16/5/8:30pm.] BEEBAH LUV & RASH KARDAM WITH SADEEY S ADAM MA’ YAUDARAH 06~10 Note: Pls fans, sakamakon jin da mukai anyi novel me suna YAUDARAH, shi yasa muka chanxa ma namu suna ya koma MAYAUDARAH,. Tnx Sun isa babu dadewa, don daukan Futha, su tafi batai tunanin wani ne zai kai su ba, tayi tunanin a keke napep zasu tafi, daman bata shiga ba a kofa ta tsaya tayi mata waya, futha tayi ma ummanta waya sallama, tace sai sun dawo Allah ya kiyaye hanya, su gaishe da Amaryar tace toh. Bayan ta futa ne ta gansu a cikin mota, ta shiga da sallamar ta, ta gaisar dashi daga nan bata sake cewa komai ba, sai dai in teemah tayi mata magana takan bata amsa a takaice, don Futha akwai kamun kai. Bayan sun isa shima da zata futa tace mashi sai anjima, kai wannan kawar taki akwai ta da girman kai, sai wani shan kanshi take,, ayya whl baka fahimceta bane haka take bata fiya magana ba,,, ok sai yaushe zanzo daukar ki, tace zadai muyi waya ok sai ltr din kenan, ok bye. Hmmmm kedai teemah bazaki taba jin magana ba, kullum cikin kula samari kike, wannan kuma daga ina kika kwaso shi,, daga ganinshi ba mutumin kirki bane,, don Allah teemah ki ringa tunani whl wannan rayuwar ba mai bullewa bace, ki nitsu kiyiwa kanki fada pls kinji kawata, ta kama hannunta, toh naji matar liman zanyi, ni muje dallah. Matar soja kam ba karamin dadi taji ba,, tayi masu tarba me kyau,, sunci sun sha, sunyi hani’an. Nan kuma aka dosa hirar school, after nan kuma aka fara ta samari, kowacce na bada nata lbrn, da irin yaudarar da take ma samari,, hmm nan fah teemah aka soma fede biri harda wutsiyar sa, ai duk naku wasa in gaya muku, nifa yanzu indai zan fita unguwa to alkawari ne sai nayi saurayi, kuma daman in naga kalar ka batai mun ba ko sauraranka bazan yiba, don kunsan ni sai mai kudi,, gwara wanda zan wanke shi, ba wanda zaizo yana mun karyar baya dashi ba. Heeeeh whl kuwa yar uwa kinmin daidai, don kuwa yanzu sai da hakan inji Sumayya Gireii, don kunsan suma fa mazan yanzu dan karan yaudara ce dasu, yo kun manta ni da Ahmad ya yaudaran yazo ya kawo kudin aurena, ashe ba iyayen shine na kwarai ba, na karya ne tsabar yaudara ce irin ta maza,, ai shiyasa yanzu na Daura damarar yaudarar maza son raina, don nama daina tunanin aure yanzu, sai na gama cin dunia ta da tsinke tukunna. Futha ce da ummilele suka gyara zama, hmm yanzu kukam kuna ganin hakan yafi maku ko? Whl kuyi ma kanku fada yaudara babu kyau, gwara ku tsaida guda daya nagari, yanzu dunia ta lalace, wasu samarin fa ba sonku suke tsakani da Allah ba, sai dai su zo su kashe muku kudi, in sun samu abinda suke so a gurin ku su gudu su barku, ai kuwa sun cuci rayuwar ku.. Whl kuwa fada musu ummi don kullum sai na gayawa teemah ta daina amman gani take burgewa ne, whl ba abin burgewa bane kuna cutan kanmu ne… Can kuma rash ta amshe chab wai wa’azi zukuyi mana?? Ai gwara ma ku daina, don yanzu kam bazai shige mu ba, yanda ake yaudarar mu, muma sai mun dana, donni inda aure kazo mun ma tuni nike korar ka don ban shirya ba, sai na tatsi na tatsa son raina, in baka red card,, dakyau kawata ban mu kashe,,, inji sadeey, ai sai da hakan, don ni yanzu akwai me sanya mun credit, akwai me siyan kayan make up,, akwai me sai mun anko, akwai kuma driver na wanda duk inda zanje shi yake kaini,, kuma duk yanda nace ana yi mun, koya kika ce kawas,, kwarai kuwa,, Matar soja tace ayi dai a hankali don kuwa a wannan zamanin ba kasa fai samari ke bama yan mata kudi haka kawai ba, sai kema in kina bada gudummuwa,, To ai ba wani abu bane baya wuce shan minti, kawai meye a ciki don an dan sha minti ai ba wani abu bane inji teemah duk teemah tafi zaqalqalewa a cikin su don kuwa idon ta ya bude sosai sai dai gyaran Allah kawai… Ai kuwa whl wani abu ne babba ma kuwa don kuwa kunsan babu kyau Allah ya haramta hakan,, kuma sai sun gama shafe ku sannan su arce su barku anan, su kara wuta, wani ma daman da matar shi, wani kuwa da wadda aka sa musu rana, tunda yaga kin sakar mashi sai yazo yayi abinda zai yi ya gudu, Allah dai ya kara shirya mana zuri’ a amin.. Ohoo sudai ina ai wanda yayi nisa yayi nisa, sai dai gyaran Allah kawai Allah ya gyara amin. Sai dab da maghrib suka tafi ansha hirarraki kala kala.. Wacece Teemah Teemahluff diya ce ga Alh Rislan da Haj Raudha, Alh rislan haifaffan garin kano ne a wata unguwa da ake kira Hotoro Dan Marke,,, malamin makaranta ne govt, sec, school dake hotoro, ya dade yana teaching, har ya samu mukamin principal a makarantar. Alh rislan mutum ne me kirki da kawai ci, da rikon a mana, da sanin ya kamata,, baya karbar cin hanci, yana da bala in kirki da rikon addini.. Matar shi daya, raudha me bala’in hakuri da addini, yayan su uku Fauzan, shine babba sai Teemah itane ta biyu, sai kuma mukhtar shine autan su. Sun taso cikin gata da tarbiyya, don kuwa Alh rislan yana kokari Sosai wurin basu tarbiyya da ilimi, both side, islamiyya da boko, yana son yaga sunyi karatu me taho, farko sun fara govt school daga baya ya cire su ya saka su a private school tun suna primary 4 suke Private school har secondary school. Yana bala’in kokari duk abinda ya samo akan iyalin shi suke tafia, ba wani me kudi bane rufin asiri ne kawai da zuciyar nema. Akwai wani makwocinsa Alh Faisal yana da kudi sosai,, kuma suna shiri da Alh rislan don kuwa shike bashi shawara, ya zama kamar dan uwan sa,, yakan taimaka mashi sosai bawai don ya gaza bane a ah yana dai taimakon shine tunda ya fishi kudi nesa ba kusa ba. Akwai wata shekara ya hada da nashi iyalin da Alh rislan da raudha ya kai su aikin hajji,, shi yasa ake kiransu Alh rislan da haj raudha.. Alhamdulillah komai yana tafia daidai a rayuwar gidan Alh rislan, su teemah da Fauzan har sun sauke Qur’an don ba wani tazara ke tsakanin su ba, shekara daya ne tsakanin su.don haka komai tare suke yi, hatta a school ma aji daya ya bata, kuma shi baya da jikin girma, ita kuwa tana da tsaho ana yawan cewa ita ce babba akan shi.. Teemah ta tashi cikin tarbiyya da nitsuwa tun tana Karama amman tana shiga SS1 a school ta zama fitinanniya kamar ba ita ba, Don kuwa yan mazan ajin su da yan matan ma yawancin su duk kangararru ne yayan masu kudi, shi yasa fitinar tayi yawa, su suka bata tarbiyya teemah,, tun tana kin biye musu har dai ta fara shiga layi. A lokacin bata wani kware ba, kuma bata kula samari don bata fara zuwa zance ba, babanta yace karatu zatai har sai ta fara higher institution sannan zai aurar da ita don yana son yaga sunyi karatu, tunda sun sauke na muhammadiyya, kuma yasan yarsa tana da tarbiyya zata rike mutuncinta a duk inda take. Ayyah baba rislan kayi kuskure don kuwa,, abokai da kawaye sun lalata maka tarbiyyar da ka dade kana yi tun fil’azal, teemah kam ta fara nisa yanzu sai dai gyaran Allah. A kwana a tashi ba wuya wurin Allah su teemah har an gama secondary school, kuma Alhamdulillah tayi passing exams din ta gaba daya, a waec neck ne tayi losing subject biyu. Tana da kokari sosai da maida hankali sai dai kawai rashin jin da ta zunduma kanta yanzu a ciki,,. Bai wani bata Lokaci ba ya samar mata admission a Bayero university, kuma ta samu a fannin sociology, yayi mata fada sosai akan ta maida hankali akan abinda ya kaita baya son kula yayan banza, tayi abinda ya kaita tace to kamar da gaske.. Shi kuwa fauzaan yana ABU ZARIA can ya sami admission shi kuma mukhtar Auta yana JS one don akwai tazara tsakanin shi da

Chapter 1 of 5