Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 4
a fusace tana kai masa sara da wafta za ta hadiyeshi shi kuma Zuhairu ya rika gocewa da kai mata sara cikin tsananin jarumta da karfin zuciya, duk inda macijiyar ta sara a jikin jirgin ruwan sai ka ga itacen wajen ya fashe ko ya ragargaje. Da ragowar jaruman da suke tare da Zuhairu suka hangi abin da yake faruwa sai nan da nan suka zare makamansu, gwanayen harbi da kibiya suka rika sakarwa macijiyar ruwan kibbau daga inda suke, masu jifa da majaujawa suka rika jifanta da wasu dunkulallun karafa masu tsini dake huda jikinta, sauran jaruman masu fada da takubba ko mashi suka tafi ga jirgin ruwan don kai dauki gareta, da zuwansu suka far mata da sara da suka babu kakkautawa, macijiyar nan ta kawo wafta cikinsu ta suri daya ta hadiyeshi daga shi har takobi da sulken yakin da ke jikinsa, ta sake kawo sara ta samu mutum uku lokaci guda, iska ta kwashesu ta yi sama da su sabodá karfin saran suka zube a gefe matattu ba su ko shura ba, jikinsu ya rika zagwanyewa yana narkewa kamar jini, saboda masifar dafin da ke jikin macijiyar Da ragowar jaruman suka ga haka sai suka ja da baya a razane, shi kuwa Zuhairu ya sake tasar mata a fusace, ya kai mata wani gawurtaccen sara irin na zaratan sadaukai da dukkanin karfinsa, ya yi sa'a ya sameta a lokacin da take kokarin kai masa sara, macijiyar ta yi wani irin gunji mai tsananin karfi saboda azabar saran da ya kai mata, jini ya yi tsartuwa sama daga inda ya sari jikinta, macijiyar ta yi tsalle ta fada cikin ruwan kogin, masu jifa da majaujawa da harbi da kibiya suka ci gaba da har bin ta har ta nutse a cikin ruwan kogin, jini ya taso sama ya gauraye ruwan kogin daga inda ta nutse. Zuhairu ya tsaya yana saurare ko zai ga macijiyar ta sake tasowa saman ruwa daga inda ta nutse amma har aka shafe lokaci mai tsawo ba su sake ganinta ba, don haka ya yi zaton ta halaka sun gama da ita, daga nan suka kwashe gawarwakin 'yan uwansu da sauran jama'ar da macijiyar ta halaka a cikin jirgın ruwan suka fita dasu suka binnesu, sannan suka share jirgin ruwan suka gura duk abin da ya lalace a ciKinsa, suka zuba kayansu suka hau suka dauki fila-filan da ake amfani da su wajen tuka jirgin ruwan suka soma tukawa suka kama hanya da zasu ketare kogin. Bayan sun yi tafiya mai nisa a cikin kogin har rana ta kusa faduwa ba su kai karshensa ba, can daga bayansu sai suka rika jin wani kugi da gunji yana tunkaro inda suke, iska mai karfi ta soma tahowa daga gabas tana kada ruwan, kogin ya soma tunbatsa yana ambaliya da tsiri sama, igiyar ruwa ta soma kadawa tana girgiza jirgin da suke ciki sannan sai suka ji wata irin tsawa mai tsananin karfi da ban firgici ta sake gauraye wajen, ruwan ya sake hautsinewa yana kadawa da karfi tare da yin tsiri sama kamar zai sha kan jirgin ruwan ya nutsar da su su halaka, jirgin ruwan ya soma tangadi da tangal- tangal kamar zai dulmiyar da su su halaka. Can daga bayansu sai suka hango wannan bakar guguwar ta keto ta saman ruwan kogin tare da iska mai tsananin karfi sun tunkaro inda suke, gaba daya wajen ya yi bakik kirin sararin samaniya, ya yi duhu mafi tsananin gani daga yankin duhun dare, suka sake jin wata tsawa mai tsananin amo da rugugi mai matukar hauhawa da ban firgici, jirgin ruwan ya sake yin girgiza da tangal tangal tamkar zai kife dasu su halaka, har zuwa sanda bakar guguwar nan ta karaso inda suke, daga cikin bakar guguwar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana akan iska, hannunsa rike da gorarsa na aikin sihiri tare da sandarsa ta tsafi, ya dubi su Zuhairu ya bushe da dariya irin wadda ya saba yi a duk sanda zai aikata wani abu na mugunta da zalunci, ya ci gaba da kyakyata dariyar har zuwa tsawon wani lokaci sannan ya ce de su "Halaka ta tabbata a gareku cikin wannan rana babu shakka ba za ku kubuta daga wannan musiba da ku ke ciki ba har sai kun halaka, kamar yadda na sanar daku cewa ajali zai gabata gareku cikin wannan tafiya, saboda babu wani mahaluki a fadin duniya da ya isa ratsa lardin Ashtar bare ya je inda fadata take, saboda ma'abota tsaro da bada kariya dake tare da ita, ya dubi 'yar uwarsa Buniyatu ya ce da ita. "Ke kuwa Buniyatu zan sake bada dama a gareki kafin ku riski inda za ku halaka, ki zama mai neman afuwa a gareni tare da yin rantsuwa da alkaluman sihiri masu girma akan cewa za ki rabu da begen wannan jarumi da ku ke tare da shi, tare da barin addininsu da ki ka yi imani da shi a yanzu, ni kuma na yi miki alkawarin zan kubutar da ke daga wannan halaka da ku ke ciki na maida miki alkaluman tsafi da sihirinki da na rabaki da su, na tafi da ke fadata mu zauna tare cikin salama, da tasirin aikata abin.da ki ke son na daga alkaluman sihiri." Buniyatu ta maida masa raddi da cewa ""Bana bukatar taimako daga gareka ka kubutar dani, ga Allah nake neman taimako kuma ba zan taba juya baya ga abinda na tabbata a kansa yanzu ba, na fita daga addinin Musulunci, ba kuma na neman ka dawo da alkaluman sihirin da ka kwace daga gareni don a yanzu ina neman tsari da su, kuma ba ka isa ka tabbatar da hallaka akan mu ba, komai karfin tasirin tsafi da sihirinka har sai ranar da Ubangiji ya so tabbatar da bakan a kanmu." Matsafi Bahalu ya fusata da jin kalamanta masu tsauri a gareshi ya dubeta ya ce da ita. "Ke dai kina cikin dimuwa da bata wadda ba za ta dawo da ke kan turbar gaskiya ba, kuma tun da kin yi zabi da kasancewa cikin wannan hali tare da jama'ar da ki ke tare da su, to ku yi Saurare da zuwan musibar da za ta riskeku ta kai ku ga halaka, ita ce za ta zama hanyar salwantar rayuwarku ba za ku taba kubuta daga gareta ku ketare wannan kogi da ku ke ciki ba," Yana gama ambaton wannan magana ya sake bushewa da dariya irin ta mugunta da zalunci sannan ya bace cikin bakar guguwar da ya bayyana a cikinta ya bar wajen, daga nan sai suka sake jin wata tsawa da rugugi mai ban firgici ya gauraye wajen can daga gabansu sai suka hangi ruwan kogin nan ya dare gida biyu ya yi tsiri sama, tsayinsa zai iya shan kan jirgin ruwan da suke ciki ya nutse da su su halaka, sannan sai wata iska mai karfi ta soma tura jirgin ruwan yana tunkarar inda ruwan kogin nan ya dare gida biyu za ta dulmiyar dasu su halaka, su Zuhairu suka ci gaba da addu'a don neman kiyayewar Ubangiji ya kubutar da su daga wannan musiba da suke ciki. Jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya yana kara tunkarar inda ruwan kogin ya dare gida biyu zai dulmiyar da su su halaka. Shin me zai faru? Mu hadu a littafi na uku kuma na karshe don jin yadda za ta kasance. Naku har kullum mai fatan nishadantar daku SHEHU USMAN MUHD. 07034668406, 08025433394 Ni Shuraihu Usman dana rubuta kuma na gabatat da shi a shafin dlhausanovels,com,ng ke cewa bissalam mu hadu a kashi na uku wanda zai dau lokaci gaskiya dun yanzu bama da shi a kasa, Ina masu Sha'awar karanta littatafan Hausa, kama daga kan na yake yake, irin na su, Abdulaziz Sani M ginj, Shehu usman Muhd, Muktar Yaron malam, Ashiru Sani Muhd, Nura Iliyasu, Nura sada , isah Muhammad, Sarana mohammed, imrana Musa, Abdurrahman Iliyasu, Kh Abdulkarim Waziri, Sani Yusuf, Rabi'u Muhammad Gumel, ibrahim Adam Usman, Mansur sufi... dama wasu marubutan na da, Nesa ta zo kusa marmaza kuje shafin www.dlhausanovels.com.ng ku downloading duk littafin da kuke da bukata zuwa kan wayarku a kyauta batare da ko sisin ku ba. kada dai ku manta sunan shafin www.dlhausanovels.com.ng Shuraihu Usman 08140419490 2020 - DL HAUSA NOVELS An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 4 of 4