Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
dauketa tana karaji da kururuwar neman taimako har ta daina hangensu saboda nisa da suka yi da wajen, sannan matsafi Bahalu ya turo wani farin hayaki daga bakinsa ya bugi fuskarta, nan take Idanunta suka daina ganin komai, barci mai nauyi ya dauketa, ta fita daga hayyacinta daga nan ba ta sake sanin abinda yake faruwa a gareta ba. Matsafi Bahalu ya ci gaba da tafiya da ita cikin alkaluman sihirin rage nisan tafiya, sai da ya shafe tsawon kwanaki goma yana tafiya ba tare da yada zango ya huta ba sannan ya isa lardin Ashtar inda wannan fada ta Darul Sabar take, ya wuce cikin fadar dake tsakanin wasu manyan tsaunuka guda biyu a tsakiyar daji Fadace da aka ginata da kananan duwatsu abin yiwa ado da jauhari, an zagayeta da manyan katangu masu matukar girma da tsayi tare da kariya ta alkaluman sihiri da babu wani mahaluki da ya isa shiga cikinta matukar ba da izinin wanda ya mallaketa ba. Akwai itatuwa da furanni masu matukar kyau da suka kayata wajen tamkar lambu, ga rafuka da koramu masu gudanawa a tsakiyar wajen kana zuwa inda fadar take za ka tabbatar da cewa ka zo wata kasaitacciyar fada, irin ta manyan sarakuna da suka shahara a fagen tarin dukiya da karfin iko. A cikin fadar akwai hadimai mata kyawawa wanda dukkaninsu an daukosu ne daga hannun iyayensu aka kawo su wannan fada aka ajiyesu don yin hidima ga wanda ya mallaketa, kuma da yawansu 'ya'yan sarakuna ne da manyan attajirai, sai dai daga cikinsu babu wadda matsafi Bahalu yake ganin ta dace ya zauna da ita a matsayin matarsa ban da Gimbiya Hasima, don haka dukkanin matan da ya tarar an tara a fadar suna zaman kuyangi ne don yin hidima a gare ta. Matsafi Bahalu yana shiga cikin fadar ya wuce da Gimbiya Hasima wani daki mafi kyawun ado daga cikinya'yana da nake fatan su gajeni a fagen tsafi da sihiri, za ki kasance a karkashin ikona kuma mai yin biyayya a gareni har karshen rayuwar ki." Hasima ta ce da shi "Allah ya yi mini tsari da dukkanin sharri da mugun nufinka a kaina, ya kuma kubutar da ni daga wannan hali don shi mai karfin iko da isa ne Cikin buwayarsa akan kowane tasirin tsafi da sihiri da kake dagawa da shi, kuma kiyayata na tare da kai har Karshen rayuwata ba zan taba kaunarka ba, bare na yi biyayya a gareka." Bahalu ya sake bushewa da dariya sannan ya ce da ita "Ai lamarina ya yi nisa a gareki daga fita daga wannan fada, kuma bakin alkalami ya riga ya bushe tunda har na riga na kawoki cikinta, ki sani cewa babu wani mahaluki da ya isa shigowa wannan lardi komai jarumta da sadaukantakarsa bare ya kubutar da ke daga hannuna." Ya tafi jikin wata karamar kofa dake saman dakin ya budeta sararin samaniya ya bayyana, a lokacin dare ne kuma babu hasken farin wata sai tsananin duhu sannan akwai wasu taurari masu matukar haske guda biyu daga daidai kofar da ya bude, ya dubi Gimbiya Hasima ya ci gaba da cewa. "Ki yi duba ya zuwa wadannan taurari guda biyu dake sararin samaniya, sune taurarin da na dade ina jiran bayyanarsu, don samun nasarar daukoki daga birninku na kawoki wannan fada, kuma da suka bayyana na samu nasarar aikata hakan. Saboda haka ki ci gaba da duba ya Zuwa wannan taurari tsawon kowane dare, a duk sanda ki ka ga taurarin sun taho sun hade da juna sun zama daya, to wannan rana ce da take bayyana kasancewarki matata da tabbatar aure a tsakaninmu, kamar yadda bayyanar taurarin ta tabbatar da samun nasarar daukoki daga birnin ku. Ya sake bushewa da dariya irin ta mugunta da zalunci kamar yadda ya saba sannan ya juya ya fice daga dakin ya bar ta. Gimbiya Hasima ta sake fashewa da kuka saboda bakin ciki da takaicin halin da matsafi Bahalu ya sanya rayuwarta a ciki, ta dade tana wannan kuka don tausayawa kanta har kusan asubahi, sannan ta hakura ta mika lamarinta ga Ubangiji, ta duba hannunta ta ga zoben nan na Zuhairu yana tare da ita ba ta jefar da shi ba, ta daukeshi ta saka a dan yatsanta ta sumbaci zoben kuka don sannan ta daga hannunta sama ta yi addu'a don neman Allah ya kubutar da ita daga hannun wannan shu'umin matsafi da ya daukota daga birninsu ya rabota da 'yan uwanta ya kawota wannan waje. Shi kuwa Zuhairu cikin kwanaki biyar ya gama shirinsa na tafiya lardin Ashtar don 'yanto Gimbiya Hasima daga hannun matsafi Bahalu tare da neman makarin aikin sihirin da Bahalu ya yi masa ya maida siffarsa irin ta tsoho mai tarin shekaru. A ranar da Zuhairu zai tafi ya fito cikin shiri na sulken yaki, ya yiwa dokinsa damara da shiri na sosai, haka itama Buniyatu an bata doki tare da sauran kayan yaki daga fadar Sarki Shaiban, ta gama nata shirin cikin sulken yaki ta fito idan ka ganta za ka yi zaton wani hamshakin jarumi ne sadauki da ya shahara a fagen fama ba mace ba ce ba, kafin su tafi suka yi bankwana da dattijo Marwan kakan Zuhairu ya yi musu addu'a ta tatan samun nasara sannan suka yi sallama suka kama hanyar birnin Bahazum. Da isar su Birnin suka wuce fadar Sarki Shaiban, suka tarar da an shirya wasu manyan jarumai cikin shirin yaki, su kimanın mutum arba'in da zasu yi musu rakiya cikin BAKAR GUGUWA littafi na biyu 2 Na Shehu Usman Muhd typing by Shuraih Usman post by Shuraih 99% Part C . . tafiyar da za su yi, Zuhairu ya sauka daga kan dokinsa ya tafi gaban Sarki ya kai gaisuwa, sarki ya amsa masa sannan ya ce da shi "Allah ya baka nasara na gama shiri dan yin tafiya bisa ga alkawarin da na dauka, na neman Gimbiya Hasima duk inda take a fadin duniya." Sarki Shaiban ya ce da shi "Na shirya wasu jarumai da zasu yi maka rakiya adadin mutum arba'in, daga cikinsu akwai mutum goma kwararru a fagen iya harbi da kibiya, sannan akwai wasu mutum goma da suka kware a fagen iya fada da mashi, sai kuma mutum goma masu iya jifa da majaujawa, sauran mutum goma na karshe sune kwararru a fagen iya fada da takobi, wadannan sune adadin mutumn arba'in da zasu yi maka rakiya, don haka za ku tafi tare dasu su taimaka maka, ni kuma zan sanya malamai su ci gaba da addu'a Allah ya baku nasara cikin tafiyar da za ku yi." Zuhairu ya yi godiya sannan Sarki Shaiban ya sa aka yi musu addu'a ta fatan samun nasara ya kuma umarci baradan da zasu yiwa Zuhairu rakiya su kasance masu yi masa biyayya a matsayin shugabansu har su je su dawo, daga nan suka yi sallama da sarki, aka yi musu rakiya zuwa bayan gari suka kama hanya suka ci gaba da tafiya. Buniyatu tana gaba don yi musu jagora zuwa bigiren da suke zaune tare da yayanta matsafí Bahalu, don dauko rubutaccen sako wanda zai shiryar da su hanyar da za ta kaisu lardin Ashtar inda fadar da matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima take. Kwanci tashi suna tafiya a cikin wannan daji tun daga ranar da suka baro gida, har suka shafe kwanaki ashirin daga cikin kwanaki arba'in da za su yi kafin su isa bigiren da Buniyatu suke zaune a cikinsa, sukan yi tafiya daga bayan ketowar alfijir har zuwa faduwar rana sallah da cin abinci ne kawai yake 'tsayar da su sai dare ya yi su yada zango don su kwana kafin gari ya waye su ci gaba da tafiya. A rana ta ashirin da daya daga cikin ranakun tafiyarsu da La'asar sakaliya, suna tsakiyar tafiya sai suka hangi wasu rundunar mahaya cikin shirin yaki, suna dauke da tutoci na mabiya addinin bautar rana, su Zuhairu suka yi nufin Su ratse musu su ci gaba da tafiya, don kada baradan su tsayar da su su bata musu lokaci cikin tafiyar da suke yi, amma sai wadannan ayarin baradan suka hangesu suka sha kansu suka tsayar da su, daya daga cikin baradan wanda kuma shi ne babbansu ya dubi su Zuhairu ya ce da su. "Kai wadannan matafiya daga ina ku ke kuma ku jama'ar wane birnine da inda ku ka nufa? Sannan ina labarin dukiya da guzirin da ku ke tare da shi. Ku yi gaggawar mikoshi garemu don a yanzu kun zama ribatattu a garemu ababen tafiya da ku ya zuwa birninmu don kaiwa sarkinmu ku zama bayi, kamar yadda mukan yi ga duk jama'ar da muka hadu da su a wannan daji cikin tafiyar da muke yi." Zuhairu ya ce da shi "Ba ma tare da wata dukiya ko guziri da zamu baku bisa ga bukatarku, cewa dai mu mun kasance matafiya ne cikin wata bukata da take tare damu, kuma bamu fito dan yin fada da kowa ba sai don tunkarar abin da muka sa a gaba saboda haka muna neman afuwa a gareku, ku bamu hanya mu wuce ya zuwa inda muka nufa." Wanda ya fara magana ya dubi Zuhairu ya ce da shi "Kai dattijo ma'abocin rauni da gazawa ka sani cewa ba zaku kubuta daga hannunmu ba har sai kun zama ribatattu a garemu, don na ga alama kun kasance daga cikin mabiya addinin Musulunci ba masu bauta ga rana ba. Za mu tafi daku ya zuwa biminmu don mu bautar da ku kamar yadda muke bautar da duk wanda bai zamo daga jinsinmu ba. Kuma baya bauta ga rana abar bautawa da gaskiya, to kuwa Sunansa bawa a garemu kuma ya halatta mu bautar da shi ko ko mu halakashi mu shayar da jininsa ga rana abar bautarmu bisa ga tsarin addininmu" Zuhairu ya fusata da jin maganar wannan mutum ya ce da shi, kaicon rayuwarka da abin da ka ke ambatawa cikin zantukanka masu munin ambato, wadai da miyagun kalamanka na zalunci da ke bayyana tsantsar shirka da bata mabayyani na bauta, gara na abar halitta, da shayar da jinanan Musulmi a gareta da nufin yin bauta don girmamata, ka sani cewa halaka ta gabata gare ka da rundunar baradan da kake jagoranta sababin abin da kake aikatawa na zalunci a doron kasa, don sha fe ruhinka daga bayan kasa shi ne mafi alkairi ga sauran jama'ar Musulmi." Barden nan ya bushe da dariya saboda jin abin da Zuhairu ya ce sannan ya dubeshi ya ce da shi "Kai dattijo ma'aboCin rauni da gazawa saurara ga ambaton wadannan kalamai naka da ka ke ambatawa, ka bari natasa masu ragowar jini a jiki da jarumta su yi magana, ba kai dattıjo raunanne ka yi magana ba, don haka ko dai ku mika wuya a garemu ko kuma mu tursasaku ga aikata abin da muka umarceku ta hanyar karfi da tsananin yawanmu." Zuhairu ya zare takobinsa ya fita gaban rundunar baradan ya ce da su Ba zamu zama masu soro ko karaya da ganin yawan rundunarku da ku ke alfahari da ita ba, don Allah da muka yi imani da shi muke bauta masa zai iya bamu nasara a kanku koda kun fi yawan adadin kasa, don haka idan da mai karar kwana ya fara fitowa gareni ya ga yadda zan aika da ruhinsa barzahu, idan kuma kun ki fitowa ni na gabata cikinku na hau ku da sara da kisa irin na kare dangi, har sai na tarwatsa rundunarku na sanyaku nadamar halittarku a bayan kasa da abinda ku ke aikatawa." Jarumin nan ya sake fashewa da dariya lokaci guda kuma sai ya turbune fuska, irin na mugunta da zalunci ya dubi Zuhairu ya ce da shi. "Ban zamo daga cikin mutane masu imani da zan ji tausayin tsufanka na kyaleka ba, tunda har kana jin ka isa jarumi bari ni na halakaka da kaina, don ya zama izina ga Sauran jama'ar da ke tare da kai." Ya zare takobinsa ya taho ga Zuhairu sai kuma yasa ke shawara ya maida takobin yana mai fadin cewa "Ai halaka ka da takobi ma nuna rashin jarumta ne, da gazawa, don kuwa iskar gudun dokina kadai ta isa waftoka daga kan dokinka ka fado ka halaka." Kafin ya gama maganar Zuhairu ya fusata ya daga takobinsa ya kai masa sara, Jarumin ya yi sauri ya sanya wata garkuwa ta bakin karfe ya kare saran, kaifin takobin Zuhairu ya keta garkuwa gida biyu ta tarwatse, jarumin ya yi baya taga-taga kamar zasu fadi daga shi har dokinsa da kyar dokin ya tirje ya tsaya saboda karfin saran da Zuhairu ya kai masa irin na sadaukantaka, jarumin nan ya dubi Zuhairu cikin tsananin mamaki kafin ya kare mamakinsa Zuhairu ya sake kai masa wani saran cikin karfin zuciya da zafin nama, jarumin ya yi sauri ya zare takobinsa ya kare saran, a wannan karon ma sai da ya sake yin baya kamar zai fado daga kan dokinsa saboda karfin saran. Zuhairu bai saurara masa ba ya ci gaba da kai masa sara a fusace, barden nan ya yi kokarin ya kare amma tuni ya makara kaifin takobin Zubairu ya sari tirken dokin wuyansa, kansa ya fita daga gangar jikinsa, ya yi tsalle sama ya tafi ya fadi a gaban sauran baradan da ke tare da wannan jarumi. Da ganin haka sai ragowar baradan dake tare da wannan jarumi suka harzuka suka taso kan Zuhairu cikin karaji da gunjin fusatuwa, suka far masa da sara da suka kamar zasu halakashi, Zuhairu ya shiga karewa da maida martani yana saransu da halakasu, suma ragowar jarumai da suke tare da shi tare da Buniyatu suka zare makamansu suka farwa baradan nan da sara, nan take waje ya yamutse kura ta turnuke ta tokare sararin samaniya, karar haduwar takubba ta cika wajen kururuwar mazaje da haniniyar dawakai ta yawaita. Kafin wani lokaci su Zuhairu sun ragargaza rundunar baradan nan da suka taso kansu, suka tarwatsa su, madaukaka daga cikinsu suka zama makaskanta, manyan jarumai da ke ji da kansu suka zama masu rauni, da yawansu suka halaka sai 'yan kalilan daga cikin su ne suka arce don su tsira daga halaka, a sanda ake tsakiyar gabza yaki Bayan su Zuhairu sun tarwatsa rundunar baradan nan suka yi godiya ga Allah a bisa nasarar da suka samu cikin iko da kiyayewarsa, kuma babu wanda ya halaka daga cikinsu, daga nan suka kada linzamin dawakansu suka ci gaba da tafiya ya zuwa inda suka nufa. Al'amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya fice daga dakin da ya ajiye Gimbiya Hasima ya tafi ya zuwa nasa dakin cikin murna da farin cikin samun nasarar dauko Gimbiya Hasima, tare da mallakar wannan fada ta mahaifinsa da ya gada, hankalinsa ya kwanta don a yanzu babu abinda ya ke jira illa bayyanar hadewar wannan taurari na alkaluman sihiri da zasu tabbatar da kasancewar Gimbiya Hasima matarsa ya samu damar kusantar ta, ya yi sani da cewa mahaifin Gimbiya Hasima zai tura wanda za su shiga duniya neman ta, saboda irin kaunar da yake yiwa yar tasa, amma ya san babu wanda zai iya shigowa lardin Ashtar bare ya samu nasarar shiga fadarsa, ko ya karbi Gimbiya Hasima daga hannunsa, saboda ma'abota tsaro da kariya dake tare da fadar. A kowace rana ya kan ziyarci dakin da Gimbiya Hasima take, don ya ganta ya ji sanyi a ransa saboda kaunar da yake yi mata, sai dai bashi da ikon kusantarta ko ya tabata, saboda alkaluman sihiri da ya yi imani da su basu bashi damar aikata haka ba, har sai ranar da wannan taurari na aikin sihiri suka hade da juna suka zama daya, saboda haka a kowane dare ya kan zauna a daidai kofar da taurarin suke ya zira ido yana dubansu da sauraron ya ga sun hade da juna har zuwa wayewar gari, sai ranar ta fito ya tashi ya koma dakinsa, haka yake yi a cikin kowanne dare tun daga ranar da ya kawo Gimbiya Hasima wannan fadar Bayan wasu kwanaki matsafi Bahalu ya yi tunanin va yi bincike don ganin halin da 'yar uwarsa Buniyatu ta ke ciki, ya tashi ya tafi ga tarkacen kayan bokancinsa na aikin sihiri, ya zauna a gaban wani kasko na lu'u-lu'u a cikinsa akwai farin rairayi, ya sa hannu ya yi zance akan farin rairayi sannan ya rufe idanunsa yana karanta wasu dalasumai na aikin sihiri, bayan wani lokaci bayanai suka bayyana gareshi, a saman farin rairayin sai ga siffar kanwarsa Buniyatu tare da Zuhairu da sauran baradan dake tare da su sun bayyana tafe akan dawakansu kan hanyarsu ta zuwa bigiren da suka zauna tare da mahaifinsu kafin ya rasu. Matsafi Bahalu ya yi mamaki da ganin wannan al'amari, ya sake share rairayi ya yi wani zanen a kansa, bayanai suka sake bayyana a gareshi cikin alkaluman sihirinsa ya ga cewa za su je wannan kogon dutse ne don dauko wani rubutaccen sako na sirri da zasu samu damar sanin inda wannan fada take, hankalinsa yayi matukar tashi nan take ya tashi cikin sauri ya shiga shiri, dan tafiya wannan kogon dutse ya rigasu zuwa ya dauke wannan rubutaccen sako da zasu je daukowa a cikinsa. Bayan ya gama shiri ya fice daga fadar ya kama hanya, ya yi tafiya har ta tsawon kwanaki shida cikin alkaluman sihirin rage nisan atfiya, sannan ya isa inda wannan kogon dutse yake, da zuwansa ya shiga cikin kogon dutsen ya soma duba da binciken inda wannan rubutaccen sako yake, amma ya rasa inda aka ajiyeshi, babu abin da matsafi Bahalu bai duba ba ko bincika cikinsa a cikin kogon dutsen amma ya rasa inda rubutaccen sakon yake, ya yi bincike cikin alkaluman sihirinsa baya nan suka tabbatar masa da cewa babu shakka rubutaccen sakon yana cikin wannan kogon dutse amma ya yi duk binciken da zai yi ya kasa gano inda rubutaccen sakon yake. Da matsafi Bahalu ya gaji da nema sai ya hakura ya fita daga kogon dutsen, sannan ya yi wani aikin sihiri akan kogon dutsen yadda Buniyatu ba za ta iya samun damar shiga cikinsa ba, bayan ya kammala ya yi dariyarsa da ya saba yi irin ta mugunta da zalunci sannan ya bace ya bar wajen. Su Zuhairu suka ci gaba da tafiya har suka shafe sauran kwanaki goma sha tara da suka rage musu, kafin su iso inda wannan kogon dutse yake, a ranar da suka iso wajen da sanyin safiya suka tunkari inda kogon dutsen yake. Da isarsu wajen kafin su kai ga shiga cikin kogon dutsen, sai suka ji wata irin tsawa mai tsananin karfi da ban firgici ta gauraye wajen tamkar faduwar aradu, kasa ta soma girgiza tana raurawa tamkar za ta tsage, Zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi su afka cikinta su nutse, can daga nesa sai suka hangi iska mai tsananin karfi tare da bakar guguwa sun keto daga bangaren yamma, aka sake yin tsawa da rugugi mai matukar ban firgici kamar sau uku, gaba daya dajin ya yi bakikkirin sararin samaniya ya yi duhu mafi tsanani daga yankin duhun dare. Baradan da suke tare da su Zuhairu suka yi matukar razana da ganin wannan yanayi da kuma al'amarin da yake faruwa mai matukar firgitarwa shi kuwa Zuhairu ko a jikinsa don ya saba da ganin irin wannan yanayi a duk sanda matsafi Bahalu zai bayyana, kuma ya san wannan ba komai ba ne face aikin tsafi da sihiri irin na ma'abota shirka da tabewa Wa iyazu billahi ya ce a zuciyarsa yana duban wannan bakar guguwa da ta tunkaro inda suke cikin jarumta da karfin zuciya har ta karaso ta tsaya a gaban su ta sauka. Da tsayawar iskar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana Cikin bakar guguwar a wannan karon ya sha babban da yadda suka saba ganinsa a baya, a yanzu yana sanye ne da sutura irin ta alfarma ta manyan sarakuna da suke ji da kansu a duniya suke sanyawa, hannunsa na hagu yana rike da kurtunsa na sihiri a dama kuma yana rike da sandarsa ta tsafi, ya dubi su Zuhairu ya yi magana da murya irinta nuna kaskanci a garesu ya ce da su. "Ban yi zato ga samun nasara cikin abinda ku ke nufin aikatawa ba, don kuwa a yanzu lamarina ya ta'azzara akan wani abin halitta ya samu nasara a kaina komai karfin tasirin tsafi da sihirinsa, na san za ka fito neman Gimbiva Hasima da nufin zuwa fadata ku karbota daga hannuna, sai dai ina mai sanar da ku cewa abune da ba za ku taba samun nasara a kansa ba ne ku riski inda fadata take, bare ku karbi Gimbiya Hasima daga hannuna, kuma halaka ta tabbata ga duk wanda ya shiga lardin Ashtar da nufin zuwa fadata saboda ma'abota tsaro da masu bada kariya dake tare dani, babu wata jarumta ko aikin sihiri da zai yi tasiri a kaina, kuma babu wani masani na ilimin bokanci da zai iya sanar da ku yadda za ku samu nasarar zuwa fadata. Ya dubi 'yar uwarsa Buniyatu ya ce da ita "Ke kuma kin yi zabi ga abinda zai kai ki ga halaka, kasancewar ki tare da wannan jarumi da ki ke son taimaka masa idan har ba ki rabu da shi ba, don kuwa ba za ku taba samun nasara ba, kuma hallaka ta kusanta ta gabata gare ki matukar kina tare da shi cikin wannan tafiya da ku ke yi, ki zama mai neman afuwarm a gareni tare da yin rantsuwa da alkaluman Sihiri masu gima akan za ki rabu da wannan jarumi ki dawo gareni, ni kuma na yi miki alkawarin zan maida miki alkaluman sihirin da na kwace daga gare ki, na tafi da ke fadar mahaifinmu da na mallaka a yanzu, mu zauna tare da ke cikin salama da aminci kamar yadda mahaifinmu ya so mu kasance kafin ya rasu. Buniyatu ta amsa masa da cewa "Ai babu juya baya ga abin da na tabbata a kansa, na taimakawa abin begena da kasancewa tare da shi har abada, kamar yadda mahaifinmu ya bar duniya abadan ba zai sake dawowa cikinta ba, haka na inganta rabuwa da kai abadan ba zan sake komawa gareka ba, kuma ka sani a yanzu na karbi addinin Musulunci tare da yin imani da Allah mahaliccin kowa da komai, don haka ba zan sake komawa ga alkaluman sihiri da bautar gumaka da tsafi ba, wanda a yanzu na yi sani da cewa aikata hakan shirka ce da bata mabayyani, Allah ya kiyashemu da sake afkawa a cikinsa. Matsafi Bahalu ya ce da ita "Ke dai kina cikin fagamniya da bata saboda makancewar zuciyarki akan begen wannan jarumi, kin zabi kasancewa da shi cikin halin wahala da kunci wanda karshensa halaka. Fiye da kasancewa dani dan uwanki cikin salama da tasirin aikata abin da ki ke so na alkaluman sihiri, to kuwa za ki kasance abar yiwa kaico da danasani mara misaltuwa ckin wannan hali kuma ba za ka taba samun nasara a kaina ba, cikin kudirinku, idan ma kina da wani sirri da ki ke son dauka a cikin wannan kogon dutse kamar yadda bayanai suka tabbatar mini to kuwa ba za ki samu nasarar shiga cikinsa ba, bare ki dauka, don na daure kogon dutsen da dalasumai na aikin sihiri da ba za ki iya shiga ba, tun da ba kya tare da alkaluman sihiri a yanzu. Zuhairu ya zare takobinsa cikin fushi yana mai maida masa raddi da cewa "Mu mun yi sani da cewa samun nasara ko rashinta daga Allah ne, kuma a gareshi muke neman taimako don haka muka yi imani da cewa zai bamu nasara a kanka, ko don ya tabbatar da karfin iko da buwayarsa akan duk wani aikin sihiri da ya sa ka ke inkarin samun nasara a kanka, kuma bari na fara tabbatar maka da cewa kai ba komai ba ne a cikin rayuwar duniya, na hallaka ruhinka da Salwantar da rayuwarka, wata kila san da zamu isa fadarka mu dauko Gimbiya Hasima kai ka dade da tafiya barzahu. Ya saki linzamin dokinsa a sukwane ya iso gare shi, ya kai masa sara a fusace da dukkanin karfinsa, matsafi Bahalu ya bace saran ya wuce shi kuma ya bayyana a baya, zuhairu ya sake juyowa gareshi ya kai masa wani saran, Bahalu ya sake bacewa bai sake bayyana ba sai da ya yi nisa da inda Zuhairu yake sannan suka hangeshi ya bayyana akan wani karamin dutse dake gabansa, ya dubi Zuhairu ya ce dashi. "Ai yanzu girman matsayina ya fi gaban na yi arangama da kai dan fafatawa, ka sani a yanzu ni ne shugaba na duk wani ma'abocin aikin bokanci da sihiri da ke wannan yanki a duniya, don haka yin mubazara da kai nuna kaskancine a gareni, kuma idan na halaka ka da kaina zaj zama nuna gajiyawata cikin aikin shihirina, don haka zan bar ka ka halaka ne cikin wannan tafiya da ku ke yi daga kai har sauran jarumai da ku ke tare da su." Yana gama fadar maganar sai bakar guguwar nan ta sake turnukewa ta gauraye wajen, iska mai karfin ta taso ta yi sama da guguwar ta nufi bangaren yamma inda bakar guguwar ta bullo tunda farko, suka rika duban wannaan bakar guguwa har ta bacewa ganinsu sannan sai suka ga wajen ya washe duhun da ya lullube sararin samaniya ya yaye, komai ya koma yadda yake alamar matsafi Bahalu ya tafi yi. Bayan tafiyar matsafi Bahalu sai Buniyatu ta sauka daga kan dokinta, ta nufi kofar kogon dutsen za ta shiga cikinsa, da zuwanta bakin kofar kogon sai suka ga wata irin iska mai tsananin karfi ta fizgeta ta yi sama da ita ta makata da jikin wani karamin dutse dake kusa da wajen, Buniyatu ta yi kara a firgice sannan ta zube a kasa sumammiya sulken jikinta ya kama da wuta za ta ta halaka. Zuhairu da sauran jaruman da suke tare da shi suka diro daga kan dawakansu cikin sauri suka tafi gareta don kai mata dauki kada ta halaka, suka yi kokarin kashe wutar BAKAR GUGUWA littafi na biyu 2 Na Shehu Usman Muhd typing by Shuraih Usman post by Shuraih 99% Part D . . da ta kama jikinta har ta mutu. kafin ta fara konata, daga nan Zuhairu ya ci gaba da shafa mata ruwa a goshinta yana yi mata addu'a har ta farfado daga suman da ta yi, bayan ta dawo hayyacinta ta tashi ta dubi Zuhairu ta ce da shi "Hakika ba zan iya samun nasarar shiga wannan kogon dutse ba, saboda aikin sihiri da yayana matsafii Bahalu ya aikata akan sa, don haka sai dai wani daga cikinku ya shiga saboda ni bani da damar shiga cikinsa. Da jin haka sai ragowar baradan dake tare da su suka yi shiru, babu wanda ya yi magana bare a samu wanda

Chapter 2 of 4