Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
zai ce zai shiga, saboda ganin abin da ya faru gareta, shi kuwa Zuhairu cikin karfin zuciya da jarumta sai ya amsa da cewa "Ni zan shiga kogon dutsen na dauko wannan sako, sanar dani inda sakon yake na je na dauko." Buniyatu ta ce da shi "Sakon yana rubuce ne jikin wata fatar bauna dake cikin akwatin bakin karfe da ke ajiye a Karshen wannan kogon dutse, idan ka shiga cikin kogon dutsen kada ka sake ka taba komai sai wannan akwati, kada ka sake ka ji tsoro ko ka razana akan duk abinda za ka ga ya tunkaroka idan ka shiga kogon dutsen, haka kuma kada ka yi magana ko ka yi waiwaye ka Juyo baya har ka isa inda akwatin take, idan ka isa gareta sai ka dauko akwatin ka fito da ita, ni kuma zan bude mu dauki wannan rubutaccen sakon dake cikinta." Da Zuhairu ya gama jin wannan bayani na Buniyatu sai ya tashi ya nufi kofar wannan kogon dutse ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, yana zuwa ya shiga cikinsa da Shigarsa wuta ce ta fara tasowa kansa tana wani irin huci da ruri irin na azaba, Zuhairu ya daga hannu zai kare fuskarsa don kada wutar ta konashi, amma sai ya tuna da maganar Buniyatu cewa duk abin da ya gani kada ya ji tsoro ko ya razana, don haka ya ci gaba da tafiya har wutar ta karaso gareshi ya ji ta wuce ta jikinsa ba tare da ya ji zafinta ko Kuma ta konashı ba. Ya sake ganin wani katon dutse ya taho daga sama zai fado kansa ya halakashi .zunairu bai razana har dutsen ya kusa kansa amma sai ya bace babu shi ya sake jin kamar muryar kakansa Marwan ya kira sunansa ta baya, Zuhairu bai juya ba ya cigaba da tafiya. Haka ya yi ta ganin abubuwa na ban tsoro da razanarwa iri daban-daban, amma Zuhairu bai razana ba har ya isa inda wannan akwatin bakin karfe take ajiye a karshen kogon dutsen, ya dubi akwatin ya ga tana da matukar girma yadda idan mutum ba sadauki bane ba zai iya daukarta daga inda take ba, ya matsa gare ta ya sa hannu ya ciccibeta da kyar ya rabata da kasa ya dora a kansa saboda tsananin nauyi, Sannan ya juyo ya kama hanyar fitowa daga kogon dutseen Bayan Zuhairu ya fito ya nufi inda su Buniyatu da sauran jarumai da suke tare da su suke tsaye suna jiran fitowarsa, ya sauke akwatin a gabansu, Buniyatu ta yi matukar farin ciki da samun nasarar dauko akwatin da ya yi, sannan ta sa hannu ta bude murfin akwatin, wani haske mai tsananin karfi tamkar walkiya ya tashi sama bayan da ta bude, baradan dake tare da su suka ji tsoro suka ja da baya, yayin fitar wannan haske. Bayan lafawar hasken Buniyatu ta sanya hannu a cikin akwatin ta dauko wata bakar fatar bauna dake nannade da bakin zare wadda ita kadaice a cikin akwatin, sannan ta dubi Zuhairu ta ce da shi. "Tunda har mun samu wannan rubutaccen sako na sirri, to kuwa mun samu damar samun nasara akan matsafi Bahalu yanzu zamu tafi ga tsohuwa DIYANNUWA don ta karanta mana wannan rubutaccen sako, ta kuma sanar damu yadda zamu iya zuwa wannan fada ta Darul Sabar da matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima, don babu wanda zal iya karanta wannan rubutaccen sako a fadin duniyar nan idan ba ita ba." Zuhairu ya dubeta cikin mamaki ya ce da ita "Wacece kuma tsobuwa Diyanuwa da zamu tafi gareta don ta karanta mana wannan sako kuma menene alakarta da wannan rubutu da ke jikin wannan fata da babu wanda zai iya karantawa sai ita?" Buniyatu ta ce da shi "Ita wannan tsohuwa Diyanuwa kakata ce ta wajen uwa, kuma a hannunta na girma tun tasowata, bayan mahaifiyata ta rasu, tana matukar kaunata fiye da yadda ta ke son komai a duniya don babu abin da Zan nema a gareta ta gaza mallaka min matukar tana da ikon bani shi, sai dai kuma ba ta kaunar dan uwana Bahalu tare da mahaifinmu Kauwas a rayuwarta ta duniya, ta tsanesu da mafi munin tsana saboda kasancewar halinsu iri daya na tsananin mugunta da zalunci, wannan ne dailin da ya sa mahaifina ya karbeni daga hannunta ya dawo dani gareshi, a halin yanzu ta makance ba ta gani kuma mahaifinmu ne sanadin makancewarta, sakamakon jifanta da alkaluman sihirin sa da ya yi. "Babu wanda zai iya karanta wannan rubutaccen sakon sai ita duk da cewa makauniya ce ba ta gani, kuma idanunta ba zasu warke daga wannan makaranta ta aikin sihiri ba har sai an debo mata ruwan dake cikin rijiyar dake tsakiyar fadar Darul Sabar ta wanke idanunta da shi, idan muka isa gareta muka sanar da ita bukatarmu babu shakka za ta taimaka mana ta kuma sanar damu bayanan da bamu Sani ba, game da ita wannan fada, ko don mu debo mata ruwan dake cikin wannan rijiya ta tsakiyar fadar ta warke daga halin makanta ta aikin sihiri da ke tare da ita." Zuhairu ya sake cika da mamaki ya dubeta ya ce da ita "To ita da take cikin halin makanta ta ya ya za ta iya Karanta wannan rubutaccen sako dake jikin wannan fata?" Buniyatu ta yi murmushi sannan ta ce da shi "Idan muka isa gareta za ka gani har ma da wasu abubuwan ban mamaki da al'ajabi daga gareta, don Allah ya yi mata baiwar gane duk abinda ya kusanceta, koda kuwa tsuntsu ne ya wuce a sama ba tare da ya yi kuka ba, idan ta ji hucin iskarsa za ta fada maka sunansa kuma babu kuskure ka ga shi ne ya wuce." Zuhairu bai sake cewa komai ba ya ci gaba da mamakin wannan al'amari da ta fada masa, daga nan suka tashi suka kama dawakansu suka hau suka ci gaba da tafiya, inda zasu yi tafiyar kwanaki goma sha biyu akan hanyarsu ta zuwa lardin Ashtar kafin su isa inda tsohuwa Diyanuwa take zaune Ita kuwa Gimbiya Hasima tun daga ranar da matsafi Bahalu ya kawota wannan fada ta Darul Sabar ta kasance cikin halin tsananin damuwa da bakin ciki mara misaltuwa babu abin da ta rasa na daga sutura, abinci ko abin sha, a wannan fada bar ma da hadimai masu yi mata hidima, sai dai ba ta iya cin abinci sosai kullum tana cikin tunani da damuwa da bakin cikin rabota da mahaifanta da matsafi Bahalu ya yi, cikin kwanaki kadan ta rame ta yi baki tamkar wadda ta shekara a halin rashin lafiya, ba ta da aiki sai yawaita ibada don ta rika samun nutsuwa, tun da Gimbiya Hasima take a cikin wannan fada ba ta taba fita dąga cikin dakin da matsafi Bahalu ya ajiyeta ba, duk da ya bata damar ta fita ta zagaya cikin wannan fada duk inda take so, wata rana da yanma ta yi tunani ta fita waje don ta dan zaga a harabar fadar ko ta ga wani abin nishadi da zai debe mata kewa. Ta tashi, ta fita daga dakin ya zuwa waje ta ga an zagaye harabar fadar da shuke-shuke masu matukar kayatarwa, ga furanni da ya'yan itatuwa na ababen marmari iri daban-daban. Ta ci gaba da tafiya a cikin harabar fadar tana zagayawa har ta iso wani dan karamin lungu da duhun itatuwa da furanni sulka lullubeshi tana shiga sai ta riski wata kuyanga daga cikin kuyangin dake hidima a wannan fada tana sallah, Gimbiya Hasima ta cika da matukar mamaki don ba ta yi zaton akwai ma'abocin addinin Musulunci a cikin wannan fada ba, ta tsaya daga bayanta har sai da ta idar da sallah ta zauna ta yi addu'a ta shafa, sannan Gimbiya Hasima ta matsa gareta ta yi mata sallama. Kuyangar nan ta dago kai da sauri ta dubi me yi mata sallama da ta ga Gimbiya Hasima ce ta amsa mata cikin mamaki don ba ta yi zaton cewa itama ma'abociyar addinin Musulunci ba ce ba. Gimbiya Hasima ta zo kusa da ita ta zauna sannan ta ce da ita, Ya ke wannan baiwar Allah ina labarinki kuma me ya kawoki wannan waje na ganki a halin yin hidima karkashin wannan shu'unmin matsafi, ma'abocin shirka da sihiri bayan kin kasance Musulma mai bauta ga Allah (SWT)." Kuyangar nan ta sunkuyar da kai hawaye ya zubo daga idanunta sannan ta dago ta dubi Gimbiya Hasima ta ce da ita. "Sunana SANAWIYATUL ASSAD BIN ABDUL NAS mahaifina sarki ne dake sarautar birnin KUBAIRU Gabas da kogin Haisa, kuma jarumi ne da ya shahara a fagen yaki da rundunar mayaka, wanda hakan ta sa sauran sarakunan kasashen kafirai ma'abota bautar gumaka da tsafi suke matukar shakka da tsoron kai hari akan birninsa, ya yi yake-yake da dama na jahadi dan daukaka addinin Musulunci har sai da ya kafa daular Musulunci a wannan yanki, na taso cikin gata da kulawa tare da tarbiyya irin ta addinin Musulunci har na kai girmana. "Wata rana daga cikin ranakun rayuwata wani dan Sarki daga cikin 'ya'yan sarakunan yamma ma'abota bautar gumaka, ya ganni ya ce yana sona ya tafi ya sanar da mahaifinsa bukatarsa ta san a nema masa aurena, da yake yana da gata a wurin mahaifibaa saboda shi kadai ya haifa a duniya, tun a wannan rana sai mahaifinsa ya taso yan aike daga fadarsa zuwa fadar mahaifina akan neman aurena ga dansa, 'yan aike suka iso fadar mahaifina suka nemi iso aka basu damar su shiga bayan sun shiga suka kai gaisuwa sannan suka sanar da mahaifina sakon sarkinsu na neman aurena ga dansa. "Da mahaifina ya ji bayanin dake tafe da su sai ya basu amsa da cewa, su koma Su sanar da sarkin su cewa babu auratayya tsakanin dansa ma'abocin bautar gumaka da 'yarsa Musulma, sai dai idan ya amince zai karbi addinin Musulunci daga shi har jama'ar birninsa su daina bautar gumaka da tsafi, to kuwa zai bada aurena ga dansa. Yan aike suka tashi suka kama hanya suka koma birninsu, da suka isa birnin suke sanar da sarkinsu abinda mahaifina ya ce sai ran sarkin ya baci, ya yi fushi da harzuka mai tsanani ya dauki alkawarin sai ya yaki mahaifina ya rushe birninmu ya daukeni ya tafi dani fadarsa ya aurar dani ga dansa, tun daga sannan suka shiga shirin yaki, sun kawo hari har sau uku birninmu amma ba su taba samun nasarar shiga birnin ba, bare su samu nasarar abinda suke nufin aikatawa kuma a duk sanda suka zo sukan koma ne cikin tsananin rauni da tagayyara, yawan rundunar baradansu ya kan karanta jarumai daga cikinsu su zama raunana, madaukaka daga cikinsu su zama makaskanta. "Bayan da suka dawo daga yaki na uku ne da suka je kai hari birinmu, wannan dan sarki ya fusata da ganin baradan mahaifinsa sun kasa samun nasara akan jama'ar birninmu, ya tafi ya dauki guba ya sha ya halaka da mafi munin mutuwa saboda ni, sarkin nan ya yi matukar bakin ciki mara misaltuwa, saboda hallakar dansa saboda ni wanda shi kadai ya mallaka a duniya. Tun daga wannan lokaci ya sake daukar alwashi akan sai ya halakani ya halaka mahaifina don daukar fansar salwantar dan sa, ko ta wane irinhali don haka ya koma neman taimako daga manyan matsafa da hamshakan bokaye don a samu wanda zai je fadar mahaifina ya halakashi ni kuma ya daukoni ya kai masa fadarsa, amma cikin hukuncin Ubangiji babu wanda ya samu nasara kaina ko kan mahaifina daga cikin jama'ar da yake turowa har zuwa sanda ya hadu da boka Kauwas, wanda shi ne mahaifin matsafi Bahalu wanda ya daukoki ya kawoki wannan waje, shi ne ya daukoni daga fadar mahaifina ya kawoni wannan waje duk da bai samu nasarar halaka mahaifina ba, kuma bai kaini fadar wancan sarki da ya yiwa alkawarin zai daukoni ya kawo ni ba, sai ya taho dani wannan waje ya ajiye ni, "Yadda al'amarin ya faru kuwa shi ne wata rana da yammaci muna zaune a dakina tare da sauran kuyangina muna hira, sai muka ji wata irin tsawa mai tsananin karfi daban firgici ta gauraye dakin, karfin tsawar- kamar faduwar aradu muka razana matuka daga ni har kuyangin da suke tare dani, muka tashi zamu fice daga dakin a figice sai muka ga wata bakar guguwa ta turnuke ta rufe kofofin fita daga dakin, nan take kuma ta gauraye ko ina dakin ya yi duhu mafi tsanani daga yankin duhun dare, sannan sai na ji an wafceni an yi sama dani cikin iska, na yi karaji da kururuwar neman taimako daga sauran kuyangin da suke tare dani amma babu wanda take ganina saboda tsananin duhu da ya rufe dakin kamar yadda bana ganin kowa, daga nan sai na ji kaina ya juye na fita daga hayyacina ban sake sanin abinda yake faruwa gareni ba. "San da na dawo hayyacina sai na ganini a cikin wannan waje da kuma wanda ya kawoni wato boka Kauws mahaifin matsafi Bahalu da ya daukoki, ni ce mace ta farko da aka fara kawowa wannan waje dukkanin sauran daga baya ne aka kawosu. Kuma duk wadda ki ka gani a cikin wannan fada 'yar wani sarki ce ko kuma yar attajiri aka daukota daga hannun mahaifanta aka kawota nan, yau Shekaruna uku kenan rabona da mahaifana da sauran dangina, na yi kukan bakin CikI da takaici mara misaltuwa har na hakura na mika lamarina ga Allah ina mai rokon sa ya kubutar dani daga wannan hali da nake ciki, wannan shi ne labarina da abinda ya faru a gareni." Da Gimbiya Hasima ta ji wannan labari nata sai ta yi matukar tausayawa wannan kuyanga, itama ta bata nata labarin da abinda ya faru tsakaninta da matsafi Bahalu ya daukota ya kawota wannan waje, suka taya juna jimami tare da addu'ar Allah ya kubutar da su daga halin da suke ciki, daga nan suka ci gaba da hira har zuwa faduwar rana, suka yi sallar magariba sannan suka yi sallama Gimbiya Hasima ta tashi ta koma dakinta. Tun daga wannan rana Gimbiya Hasima ta kan ziyarci wannan kuyanga su yi hira, ko kuma ita kuyangar ta je dakinta da haka har suka yi matukar shakuwa da juna *** Su kuwa su Zuhairu bayan da suka ci gaba da tafiya a cikin wannan daji suka shafe tsawon kwanakin shida sannan suka iso inda wata bukka take ita kadai a tsakiyar daji, Buniyatu dake gaba ta dubi Zuhairu ta ce da shi "Wannan shi ne bigiren da Kakata tsohuwa Diyanuwa take zaune, don haka bari mu isa gareta ka ga abin mamaki da al'ajabi cikin hikima da baiwar da Allah ya hore mata. Kuma kada wanda ya yi Magana daga cikinku ku yi saurare ku ga abinda zai faru tsakanina da ita danku zama shaidu da tabbatar da abin da na ambata. Suka tunkari inda wannan bukka take, kafin su isa gareta sai suka hanngi wata tsohuwa ta fito daga cikin bukkar da ta ji takun sahun tafiyar dawakansu sanye da bakaken tufafi hannunta rike da sanda tana dogarawa, ta tunkaro inda take jin motsin tafiyarsu ta tsaya har suka karaso gabanta suka ja linzamin dawakansu suka tsaya, gaba daya babu wanda ya yi magana daga cikinsu, ita kuma idanunta a rufe irin na halin makanta ta ce da su. "Su wanene wadannan jama'a da ku ka zo gareni hafika na ji cewar akwai jikata Buniyatul Hajari a tare da ku. Buniyatu ba ta yi magana ba ta karbi kwari da baka daga hannun wani jarumi daga cilkin jaruman da suke tafee tare da su, ta sanya kibiya a cikin bakar ta ja ta sakar mata kibiyar a saitin kirjinta, kibiyar ta tafi gareta da karfi kafin ta kai jikinta tsohuwa Diyanuwa ta ji hucin tahowarta, ta sanya sandar dake hannunta ta kade kibiyar ta tafi jikin wata bishiya ta cake a jikinta, sannan ta sake yin magana ta ce da su. "Babu shakka wannan harbin kibiyar na jikata ne Buniyatu, marhabin da zuwanki gareni kuma ke da su wa ku ke tafe har ku adadin mutum arba'in da biyu kuma ke kadai ce mace a cikinsu? Su Zuhairu da sauran baradan dake tare da shi suka cika da mamakin abinda ya faru tare da maganar da tsobuwa Diyanuwa ta ambata, wadda babu kuskure a cikinta tamkar idanunta a bude suke tana ganin adadin yawanSu. Buniyatu ta amsa mata da cewa "Babu shakka ni ce jikarki Buniyatul Hajari, na ziyarceki tare da wadansu jarumai da muke tafe tare dasu cikin wata bukata da ta kawomu gareki, amma ya aka yi kika san adadin yawan mu cewa mu arba'in da biyu ne muka zo wannan waje kuma ni kadaice mace a cikinsu? Tsohuwa Diyanuwa ta yi murmushi sannan ta ce da ita "Jikata mantawa ki ka yi dani shi yasa ki ka yi min Wannan tambaya, amma ki sani ina da hikimar gane mace a cikin taron maza komai tsananin yawansu kuma koda ba tai magana ba, ta hanyar hucin numfashi da bil adama suke wanda kunnena yake ji, kuma na gane adadin yawanku tun daga takun sahun dawakanku da na ji sanda ku ka tunkaro inda nake, ta juya ta nufi wajen bukkarta tana dogara da sanda tare da yi musu izinin su karaso, su Zuhairu da Buniyatu suka saki linzamin dawakansu suka karasa bakin wannan bukka suka sauka suka daure dawakansu, tsohuwa Diyanuwa ta gabato musu da abinci da abin sha na daga 'ya'yan itatuwa suka ci suka sha har sai da ya ishesu gaba daya duk da yawansu." Bayan sun huta Sun nutsu tsohuwa Diyanuwa ta tambayesu me ke tafe da su gareta, kamar yadda Buniyatu ta fara sanar da ita da farko. Buniyatu ta kwashe labarin duk abin da ya faru tsalkaninta da Zuhairu da kuma yayanta matsafi Bahalu ta sanar da ita, ta kuma yi mata bayanin abinda ya kawosu gareta, don ta karanta musu wannan rubutaccen sako na sirri da mahaifinsu ya bari kafin ya rasu, saboda su sami damar zuwa wannan fada da matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima su karbota daga gareshi, su kuma debo ruwan da yake çikin rijiyar tsakiyar fadar, don samun waraka daga aikin sihirin da aka yiwa Zuhairu su kuma kawo mata don karya sihirin dake tare da ita, ta warke daga halin makanta da take ciki. Da tsohuwa Diyanuwa ta ji wannan bayani sai ta ce da Buniyatu "Hakika zan taimaka muku ko don na samu waraka daga halin makantar da nake ciki, idan kun cimma nasara, kuma bana kaunar zalunci ba kuma zan taba goyan bayan azzalumi ba a duk inda yake a fadin duniya." Tajuya ga Buniyatu ta ce da ita "Ina rubutaccen sakon yake?" Buniyatu ta dauko wannan fata ta mika mata, tsohuwa Diyanuwa ta karba ta warware fatar, ta shafi rubutun dake jikinta da tafin hannunta, ta sanya dan yatsanta tana shafar tsawon rubutun sannan ta soma karantawa tana sanar da su ma'anar rubutun kamar haka: Darul Sabar wata shahararriyar fada ce da aka ginata a lardin Ashtar tsakanin wasu manyan tsaunuka guda uku, BAKAR GUGUWA littafi na biyu 2 Na Shehu Usman Muhd typing by Shuraih Usman post by Shuraih 99% Part E . . tana da matukar kariya da tsaro na dalasumai na aikin tsafi da sihiri dake zagaye da fadar, kuma kafin ku isa inda wannan fada take da zarar kun shiga lardin Ashtar za ku fara gamuwa da fitintinu iri daban-daban, na abubuwan cutarwa da zasu taso gareku da nufin halakaku, sai kun yi da gaske waje samun nasara a kan su, don shi kansa lardin Ashtar yanayinsa ya bambanta da sauran yanayin da ku ka saba ji a cikin wannan duniya, akwai masifu da wahalhalu masu tsananı a cikinsa, wanda zai yi wahala ace wani bil Adama ya shiga cikinsa ya fito ba tare da ya halaka ba." Idan kun shiga lardin Ashtar kafin ku isa inda wannan fada take, za ku fara tarar da wasu manya-manyan sansasanin barada kuma jarumai ma'abota aikin sihiri har guda uku, mahaifinki boka Kauwas ne ya samar da wannan sansanin baradan, kuma sai da ya shafe shekaru uku cur yana tattaro manyan sadaukai da suka shahara a fagen jarumta, sannan ya kafa wadannan sansanoni karkarkashin alkaluman sihirinsa, don su zama masu bada kariya da tsaro ga dukkan wanda zai kawo farmaki akan fadarsa, ya sanyawa kowane sansani shugaba daga cikinsu da kuma Sunan da yake kiran sansanin da shi, sansani na farko sunansa DARUL UKUB, sai na biyu DARuL MUSIBA naa karshe shi ne DARUL MAUTU babu abinda wadannan barada suke aikatawa a kowane sansani illa bauta ga wasu manyan gumaka dake kusa da tsaunukan nan guda uku da Suka zagaye fadar, tun daga farkon hudowar ranar har faduwarta, kuma sukan ci su sha ne daga abinci da abin sha da yake zubowa daga saman wannan tsaunuka da zarar sun fara bauta ga gumaka da suke kUsa da su, wannan wata hikima ce ta zubowar abincin daga saman tsaunukan dága mahaifinku da ya tara wadannan jarumai, cikin alkaluman Sihirinsa don su kara karfin imaninsu ga gumakan da suke bautawa. Babu wata halitta mai rai da zata gifta ta wannan waje baradan basu farmaketa sun halakata ba, koda kuwa tsuntsu ne dake shawagi a sararin samaniya, don haka babu wani mutum da zai wuce ta wajen ba su farmakeshi da nufin halakashi ba, don haka ya zama dole kenan sai kun yi yakk da wadannan sansanonin barada guda uku, kun halakasu kafin Ku samu damar zuwa fadar. Idan kun samu nasarar halaka wadannan barada ku ka isa inda fadar take, za ku tadda tana kewaye da manyan kofofi guda uku, ban san yadda za ku iya bude kofofin ku shiga cikin fadar ba, saboda ba a rubuta a jikin wannan sako na sirrin zuwa fadar ba, sai dai na yi sani da cewa kofofin suna tare da tsaro na dalasuman aikin sihiri, wanda ba za ku iya tunkarar kofar kai tsaye ku bude ku shiga cikinta ba, ku yi kokarin neman hanyar da zaku bude kofar da kanku, idan kun samu nasarar shiga cikin fadar shi kenan babu wani aikin sihiri da zai yi tasiri a kanku, daga nan kuma ya rage tsakaninku da shi wanda yake zaune a fadar ku yakeshi don samun nasara a kansa." Da ta gama karanta wannan rubutaccen sako da suka kawo mata tare da yi musu bayanin abin da sakon ya kunsa ta kara da cewa "Kada abin da na sanar daku na daga wahalhalu da musibar dake tare da wannan tafiya da zaku yi ta sa ku karaya ko ku zama masu rauni da fargaba, ku yi imani da cewa za ku iya samun nasara akan abinda ku ka sa gaba a ukatanku, za ku ga nasarar tana tare da ku ku kai ga Cimma kudirinku akan duk abin da ku ka sa gaba." Su zuhairu suka yi mata godiya a bisa wannan shawara da ta basu, da kuma karanta musu rubutaccen sakon da ta yi ta sanar da su yadda za su iya zuwa Darul Sabar fadar da matsafi Bahalu ya tafi da (Gimbiya Hasima da yake yamma ta yi sai suka yada zango a yannan waje suka kwana, da gari ya waye suka yi shiri suka yi bankwana da tsohuwa Diyanuwa suka kama hanya suka ci gaba da lafiya, suka tunkari inda da zai kai su lardin AShtar inda wannan fada ta matsafi Bahalu take Bayan Su Zuhairu sun bar inda tsohuwa Diyanuwa take zaune ita kadai a cikin daji suka ci gaba da tafiya har suka shafe tsawon kwanaki takwas, sannan sulka iso bakin wani katon kogi ma'abocin girma da fadi, ruwan cikinsa na kadawa daga gabas zuwa yama, iska na turashi da karfi yana ambaliva da toroko ya yi tsiri sama, daga gefen kogun suka ga wani katon jirgin ruwa a tsaye tamkar ana jiran isowarsu su shiga dan ketare ruwan, suka ja linzamin dawakansu suka tsaya a bakin wannan kogi Buniyatu ta dubi Zuhairu ta ce da shi. "Wannan shi ne ruwan da zamu ketare mu shiga lardin Ashtar da mun wuce wannan kogi tatiyar kwana biyu zamu yi mu shiga cikin lardin, kuma mun yi sa'a jirgin ruwa a bakin kogin da zamu iya shiga ciki ya ketare, anan zamu bar dawakanmu har zuwa sadda zamu dawo, don dukkanin tafiyar da zamu yi a cikin lárdin Ashtar zamu yi ta ne da kafarmu." Da Buniyatu ta yi musu wannan bayani sai Zuhairu da sauran baradan suka sauka daga kan dawakansu suka daure su a bakin wannan kogi, sulka tunkari jirgin ruwan Za su hau, sai Zuhairu ya dakatar da su, ya zare takobinsa ya nufi wajen da jirgin ruwan yake don ya tabbatar da cewa babu wani abin cutarwa a cikinsa kafin su shiga yana zuwa ya shiga cikinsa tun daga farko ya fara ganin jini face-face a jikin jirgin ruwan ko ina, ya rika tafiya a hankali yana kara shiga ciki, sai ya soma ganin kasusuwa da gawarwakin bil Adam birjik a cikin jirgin, ya ci gaba da tafiya yana dube-dube ko zai ga abin da ya halaka Wannan jama'a sai ya soma jiyo wani gunji da huci tamkar na wata halitta da ke da rai Cikin karshen jirgin ruwan Zuhairu ya gyara rikon takobinsa ya ci gaba da tunkarar inda yake jin wannan gunji da huci don ya ga abinda yake yin sa, har ya isa karshen jirgin ruwan, da zuwansa sai ya tarar da wata katuwar macijiya a nannade ta fasa kai tana wannan huci, girmanta kamar wani karamin dutse za ta iya hadiye mutum ya halaka lokaci guda, a gabanta ga gawarwakin mutane nan da ta halaka take hadiya a matsayin abinci, nan take Zuhairu ya fahimci. Macijiyar nan ce ta halaka jama'ar dake cikin jirgin rowan gaba ki daya. Da ganin Zuhairu sai macijiyar nan ta yi wani huci mai karfi ta taso kansa ta kawo masa sara, Zuhairu ya kauce ta samu jikin itacen jirgin ruwan ya daga takobinsa ya kai mata sara ya samu jikin ta amma sai ya ji kamar ya sari dutse takobinsa ta tashi sama ba tare da ta yanki jikinta ba, Macijiyar ta sake kawo masa sara Zuhairu ya goce, ta sake kai masa sura za ta hadiye shi, Zuhairu ya kai mata sara ya samu bakinta, macijiyar ta yi gunji da girgiza saboda azabar saran da ya yi mata, jirgin ruwan ya yi tangal-tangal kamar zai kife, sauran baradan da ke bakin kogin suka ja da baya saboda jin wannan gunji. Shi kuwa Zuhairu ya sake jan daga don tunkarar ta, da ya lura sosai sai ya ga ya ji mata rauni a inda ya sareta a baki, don haka ya kara azama da kai sara a wannan waje don ya halakata: Macijiyar ta sake taso masa

Chapter 3 of 4