Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ BAKAR GUGUWA littafi na biyu 2 Na Shehu Usman Muhd typing by Shuraih Usman post by Shuraih 99% Part A . . Kafin Matsafi Bahalu ya bar wajen Buniyatu ta tasar masa da nufin karbe kurtun sihirinta daga hannunsa, ta kai masa sura za ta fizge kurtun sihirin shi Kuma ya sanya sandar tsafin dake hannunsa ya maketa. Buniyatu ta yi karaji ta tafi ta bugu da jikin wata itaciya dake tsakiyar lambun nan take ta zube kasa sumammiya, Jini na zuba ta hanci da bakinta. zuhairu ya fusata da ganin wannan al'amari ya zare takobinsa cikin kabbara ya tasarma matsafi Bahalu da nufin kai dauki gareshi ya ketashi gida biyu ya halaka, shima Bahalu ya juyo gareshi a fusace, ya tasar wa zuhairu cikin karaji da gunji mai tsananin karfi dake tattare da aikin sihiri gaba daya dukkanin wajen ya yi amsa kuwwa da amo mai hauhawa da ya gauraye ko ina, suka hadu a tsakanin fusatuwar su suka kaiwa juna sara da bugu da makaman da yake hannunsu, kaifin takobin Zuhairu ya hadu da sandar sihiri dake hannun matsafi Bahalu wani farin hayaki ya tashi sama tare da tartsatsin wuta tamkar haduwar karfe da karfe. Zuhairu ya sake kai masa sara a fusace kafin matsafi Bahalu ya kare kaifin takobin ya sauka a jikinsa amma abin ka da shu'umin matsafi sai Bahalu ya zama hayaki saran ya wuce ta jikinsa ba tare da ya ji masa rauni ko wata illa ba, ya sake bayyana a gabansa dasaran ya wuce Zuhairu ya sake maida kaifin takobin a tsakiyar kansa Bahalu ya kare saran da sandar sihirin dake hannunsa, suka kaiwa juna sara rin ta neman makasar abokin karawa kaifin takobin Zuhairu ya wuce ta gefen an matsafi Bahalu da karti kadan ya rage ya sare kansa daga gangar jikinsa, suka yi tirjiya irin ta arangama sannan suka sake zaburowa suka yi wata bahaguwar haduwa irin ta zaratan sadaukai dake sanya halaka da matukar tsoratarwa ga kananan jarumai masu raunin zuciya. Makaman dake hannunsu suka hadu da karfi har sai da dukkaninsu suka yi baya taga-taga kamar zasu fadi sannan suka tirje suka tsaya. Suka sake zaburowa suka kai dauki ga juna, Zuhairu ya suri matsafi Bahalu ya cirashi sama da dukkanin karfinsa ya makashi da kasa, ya bi shi da sara cikin azama da zafin nama, kafin kaifin takobin ya sauka a kansa Bahalu ya bace, takobin ta sari kasa, ya sake bayyana a gefe Zuhairu ya sake yin kansa da sara cikin fusatuwa ya rika kai masa saran cikin jarumta da kwarewa irin ta sadaukantaka, shi kuma matsafi Bahalu ya rika karewa da sandar sihirin dake hannunsa ko kuma ya goce, wani lokacin ya kan tsage kashi biyu saran ya wuce, ta jikinsa ko kuma ya bace ya zama iska. Haka suka yi ta fafatawa da arangama a tsakaninsu har sai da kaifin takobin Zuhairu ya dakushe haskenta ya dusashe, saboda yawan kai sara da haduwar da take yi da sandar sihirin da take hannun matsafi Bahalu. Da Bahalu ya ga lamarin ya ta'azzara a gareshi Zuhairu ya tsanan ta masa da kai sara yana shirin halakashi, sai ya yi wani irin karaji da kururuwa mai ban firgici dake tattare da aikin sihiri, wata bakar guguwa ta turnuke a tsakaninsu, sannan ya nunashi da sandar sihirin da take hannunsa yana ambaton wasu dalasunmai na aikin sihiri, wata irin iska mai tsananin karfi ta yi sama da Zuhairu ta makashi da kasa, Zuhairu ya yunkura ya tashi matsafi Bahalu ya sake nunashi da sandar sihirin iska ta sake yin sama dashi ta makashi da jikin bishiyar dake tsakiyar lambun ya bugu da buguwa mai tsanani har takobin da take hannunsa ta subuce ta fadi kasa. Haka matsafi Bahalu ya ci gaba da nuna Zuhairu da sandar sihirinsa iska mai karti tana wujijjigashi ta maka da jikin itatuwan da ke cikin lambun har sai da Zuhairu ya yi matukar jigata, ya fadi kasa jini na zuba ta hanci da bakinsa, matsafi Bahalu ya dubeshi ya bushe da dariya sannan ya ce da shi. "Ahir din ka, da yin jayayya da hamshakin matsafi da ya buwaya cikin lamarinsa kamata, Bahalu na ke bin Kauwas cikamakin ma'abota sani na ilimin bokanci da sihiri da ke raye a doron kasa, ka sani cewa na yi yanka ga ababen bautata don neman nasara a kanka kuma ina da tabbacin samun nasara akan hakan. Babu shakka ka cika namiji ma'abocin jarumta da sadaukantaka don duk a cikin masoyan Gimbiya Hasima da na halaka babu wanda ya kai ka jarumta da karfin zuciya. Sai dai wannan rana ita ce sa' arka ta karshe a rayuwar duniya da zan halakaka kamar yadda na dauki alkawarin halaka duk wanda ya ambata yana kaunar Gimbiya Hasima Ya daga sandar sihirin dake hannunsa zai daki Zuhairu da ita a tsakiyar kansa ya halakashi Gimbiya Hasima da ke tsaye a gefe tana gani abin da yake faruwa ta yi karaji da kururuwa irin na firgita da ganin matsafi Bahalu zai halaka Zuhairu a sannan Buniyatu ta farfado daga suman da ta yi ta hangi abin da yake shigin faruwa yayanta matsafi Bahalu ya daga sandar sihirinsa zai daki Zuhairu da ita, ya halaka Nan take ta mike cikin sauri ta shiga tsakaninsu ta kare Zuhairu kafin ya dakeshi da sandar tana mai fadin cewa. "Kada ka halaka abin begena dan kuwa ba zan iya rayuwa a duniya ba batare da shi ba, idan kuma ka ce sai ka halakashi to kuwa sai dai ka halakamu gaba daya ni da shi." Matsafi Bahalu ya fasa dukan Zuhairu da sandar Sihirin ya dubı "yar uwarsa Buniyatu ya ce da ita. "Tunda kin zabi kare abin begenki akan zama da nj dan uwanki to kuwa zan barki tare da shi ba zan halakashi ba, duk da na yi rantsuwa da ababen bautata akan aikata hakan, sai dai ki sani daga yau babu ke babu sake aikata wani aikin sihiri tunda na kwace kurtun sihirin dake hannunki, kuma ba zan sake maidashi a gareki ba har abada. Za ki ci gaba da zama a wannan birni tare da wanda ki ka zabi zama dashi fiye da ni dan uwanki na jini, ni kuma zan dauki Gimbiya Hasima na tafi da ita Darul Sabar fadar da mahaifinmu ya gina kafin ya tare a cikinta ya rasu, mu zauna a can tare da ita. Kuma har abadan ba za ki iya riskar inda wannan fadata ke ba, bare ki dawo gareni har karshen rayuwarki, saboda ba kya tare da duk wasu dalasumai na aikin sihiri da za ki yi amfani da su don zuwa wannan fada." Yana gama fadar maganar ya juya ga Zuhairu ya nunashi da sandar sihiri da take hannunsa ya soma karanta wadansu dalasumai na aikin sihiri wani farin haske ya fito daga jikin sandar ya shiga jikinsa. Nan take Zuhairu ya soma tsuma da makyarkyata irin ta rawar sanyi har sai da ya durkushe a kasa, sannan sai kamanninsa suka soma sauyawa daga siffarsa ta saurayi maji karfi ya zuwa siffar dattijo mai tarin shekaru ma'abocin rauni, gaba daya gashin jikinsa ya koma fari fat irin na furfura tamkar dattijo da ya haura shekaru tamanin a duniya, daga nan ya fadi kasa a sume. Buniyatu da Gimbiya Hasima suka kwala wata razananniyar kara saboda ganin abinda ya faru akan zuhairu, matsafi Bahalu ya bushe da dariya irin ta mugunta da zalunci sannan ya dubi Buniyatu ya ce da ita "Wannan shi ne yadda abin begen naki zai kasance har karshen rayuwarsa kuma haka za ki kasance da shi cikin wannan siffa ta dattijantaka, har abadan ba zai dawo siffarsa ta asali ba, ko matukar bani ne na karya wannan aikin sihirin ba kuma aka bashi ruwan da ke cikin rijiyar BASRA dake tsakiyar fadar Darul Sabar da zan tafi da Gimbiya Hasima, kuma babu wani mahaluki da ya isa ya shiga cikinta komai karfin tsafi da sihirinsa idan bani da na mallaketa ba ko kuma wanda na yiwa izinin ya shigeta. Ya sake kyakyacewa da dariya sannan ya daki kasa da sandar sihirinsa, iska mai karfi ta keto daga bayansa tare da bakar guguwa suka hadu suka turnuke wajen suka yi tsiri a sama, matsafi Bahalu ya bi ta cikin bakar guguwar ya bace, sannan ya biyo ta inda Gimbiya Hasima take a tsaye cikin kuyanginta ya sureta ya yi sama da ita Gimbiya Hasima ta yi karaji da kururuwa mai tsananin karfi sanda matsafi Bahalu ya sureta ta cikin bakar guguwar nan ya tashi sama da ita. Buniyatu da sauran kuyanginta suna ganin sanda guguwar ta yi sama da Gimbiya Hasıma tana karaji da kururuwar neman taimako amma duk cikinsu babu wanda za ta iya taimaka mata. Tun suna hangenta da jin karajinta har ta bace Cikin bakar guguwar nan matsafi Bahalu ya tafi da ita. Bayan tafiyar matsafi Bahalu sai wajen ya washe duhun da ya lullube sararin samaniya ya yaye suka daina Jin karaji da rugugın da suke ji tun da farko. Buniyatu ta dubi Zuhairu ta ganshi cikin halin suma ta tafi gareshi cikin sauri ta dago kansa tana girgizashi taga babu alamar motsi a tare da, shi, hankalinta ya kara tashi. Ta tashi cikin sauri ta tafi bakin kogin dake gudanarwa ta tsakiyar lambun ta debo ruwa ta dawo ta zauna ta rika shafa masa ruwan tana girgizashi cikin kuka. Sai da ta dauki lokaci mai tsawo Zuhairu yana cikin wannan hali sannan ya farfado daga suman da ya yi. Da farfadowar Zuhairu ya tashi zaune a firgice, ya duba bai ga matsafi Bahalu da suka fafatawa a kusa da shi ba, ya dubi jikinsa ya ga yadda kamanninsa suka koma irin na tsoho tamkar dattijon da ya shafe shekaru casa'in a duniya, ya sake duban inda kuyangin Gimbiya Hasima suke tsaye bai ganta a cikinsu ba, hankalinsa yai matukar tashi, duk da irin halin da yake ciki na komawar kamanninsa irin na tsufa, babu abin da ya fara tambaya sai ina Gimbiya Hasima. Daya daga cikin kuyangin nan ta amsa masa da cewa wannan shu'umin matsafin ya dauketa, ya tafi da ita. Zuhairu ya mike tsaye cikin karaji duk da siffa irin ta tsufa da kamanninsa suka koma yana jin karfin jikinsa kamar yadda ya ke ji tun da farko. Kafin matsafi Bahalu ya yi masa wannan aikin sihiri a jikinsa, ya dauki takobinsa ya tasarwa Buniyatu cikin fushi daharzuka yana mai fadin cewa "Sanar dani inda yayanki matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima. Idan kuma ki ka bijirewa ambatona na rantse da sarkin da raina yake hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni da kaskanci, kafin na kai ga gano inda yayan naki yake na tafi gareshi shima na halakashi akan daukar Gimbiya Hasima da ya yi. Buniyatu ta amsa masa da cewa "Ya abin begena Zuhairu ka yarda dani da abinda zan ambata gareka, da BAKAR GUGUWA littafi na biyu 2 Na Shehu Usman Muhd typing by Shuraih Usman post by Shuraih 99% Part B . . nake yi maka ya zarce yadda nake son komai a duniya. Zuhairu ya ce da ita "Ba zan amince da maganarki ba, har sai kin yarda za ki yi imani da Allah ki karbi addinin Musulunci, ki daina bautar gumaka da tsafi ki rabu da duk wata shirka da sihiri da ki ke aikatawa." Buniyatu ta ce da shi "Na amince zan karbi addinin Musulunci idan har za ka yarda dani na zama abar gasgatawa a gareka, maganar aikin sihiri kuwa a yanzu bani da ikon aikatawa tun da dan uwana ya kwace kurtun sihirin da yake hannuna wanda a cikinsa ne alkaluman sihirin da zan iya amfani da su don yin wani aikin sihiri suke ciki, kuma a yanzu ya yi fushi dani saboda ina kokarin baka kariya daga abinda yake son aikatawa a gareka, ya kuma yi alkawarin ba zai sake maidashi a gareni ba har abada." Da ta gama yi masa wannan bayani Zuhairu ya sata ta yi kalmar shahada ta shiga addinin Musulunci tare da sanar da ita abinda ya wajjaba akan kowane Musulmi, daga nan ya tambaye ta cewa yanzu ta wacce hanya zamu iya riskar inda matsafi Bahalu ya tafi da Gimbiya Hasima dan na kubutar da ita daga hannunsa. Buniyatu ta amsa masa da cewa "Ban san inda fadar take ba, a fadin duniya amma na yi sani da wani rubutaccen sako na sirri da mahaifinmu ya bari, wanda ke kunshe da tarihin yadda aka gina fadar da dukkanin Siminta, sai dai a yanzu rubutaccen sakon baya tare da ni yana cikin kogon dutsen da muke zaune tare da dan uwana da mahaifinmu kafin ya rasu. Zuhairu ya sake tambayarta "A ina wannan kogon dutsen ya ke." Buniyatu ta ce da shi "Yana can kusa da birnin Kisira tsakanin wasu manyan tsaunuka a gabar kogin bahar Sugaira, tafiyar kwanaki biyu muke yi cikin alkaluman sihiri na rage nisan tafiya. Kafin mu iso wannan kogon dutse amma a yanzu sai D mun yi tafiyar kwanaki arba'in saboda bada alkaluma sihiri zamu yi taiyar ba." Zuhairu ya ce "Na dauki alkawarin sai na kubutar da Gimbiya Hasima daga hannun matsafi Bahalu da ya tafi da ita ta kowane irin hali matukar zan yi sani da inda wannan fada take a fadin duniya, don haka mu tafi ya zuwa birnin Bahazum fadar sarki Shaiban mahaifin Gimbiya Hasima, na sanar da shi abin da ya faru gare ta, sannan mu wuce alkaryarmu na sanar da kakana abin da ya faru gareni daga nan na yi shiri don tafiya wannan fada." da ya Da nan ya juya ga kuyangin Gimbiya Hasima ya umarcesu da su kama dawakansu su hau don komawa gida su sanar da Sarki abin da ya faru, kuyangin suka kama dawakansu suka hau ita kuma Buniyatu ta hau dokin Gimbiya Hasima, Zuhairu ya hau nasa dokin suka kama hanyar komawa birnin Bahazum Da isar su Birnin Bahazum suka wuce fadar Sarki Shaiban don su sanar da shi abinda ya faru ga 'yar sa Gimbiya Hasima, suna zuwa kofar fadar kuyangin Gimbiya Hasima suka shiga ciki Zuhairu da Buniyatu suka dakata daga waje don neman iso kafin a basu damar su shiga ciki Da shigar kuyangin cikin fadar suka tarar da Sari Shaiban a zaune cikin fadawa ana fadanci Sarki Shaiban ya yi duba ya zuwa kuyangin bai ga yar sa Gımbiya Hasima a tsakanınsu ba, kuma yanayin kuyangın suna cikin wani hali na firgici da rudewa, nan take hankalinsa ya tashi ya ji a jikinsa cewa wani abu ne ya faru gare ta, ya mike cikin sauri daga kan kujerar sarautar da yake zaune yana mai tambayarsu cewa ina Gimbiya Hasıma ta ke. Kuyangin nan suka fashe da kuka sannan daya daga cikinsu ta amsa masa da cewa wannan shu'umin matsafin ya dauketa ya tafi da ita.... Tun kafin ta karasa maganar Sarki Shaiban ya fadi kasa sumamme saboda jin mummunan labarin abinda ya faru akan 'yarsa, jama'ar da ke fadar suka taso kan Sarki Shaiban don kai masa dauki, aka rika shafa masa ruwa da yi masa addu'a sai da aka dauki lokaci mai tsawo sannan ya farfado daga suman da ya yi. Bayan da Sarki Shaiban ya dawo hayyacinsa ya nemi sanin yadda al'amarin ya faru, kuyangar nan ta kwashe labarin yadda matsafi Bahalu ya dauke Gimbiya Hasima ya tafi da ita da abinda ya faru tsakaninsa da Zuhairu ya maida shi siffa irin ta tsoho cikin alkaluman sihirinsa ta sanar da sarki. Sarki Shaiban ya tambaya "Yanzu ina Zuhairu yake?" Kuyangar nan ta amsa da cewa "Yana kofar fada don neman iso a gareka kafin ya shigo." Nan take Sarki ya umarci wani bafade da cewa aje a kira Zuhairu ace masa ya shigo. Bafajen ya tashi cikin sauri ya fita don cika umarnin Sarki, ya je ya sanar da Zuhairu cewa Sarki ya ce ya shigo. Zuhairu ya biyo bayan bafajen suka shigo tare da Buniyatu. Da shigowar Zuhairu cikin fadar, Sarki Shaiban ya dubeshi cikin matukar mamaki da tu'ajjibin ganin yadda kamanninsa suka jirkita daga siffar matashin jarumin sadauki ya zuwa siffar dattijo mai tarin shekaru, kamar yadda kuyangar nan ta sanar da shi, gaba daya duk wani gashi dake jikinsa ya zama fari fat, irin na furfura ta tsufa. Zuhairu ya fadi gaban Sarki ya kai gaisuwa cikin murya mai rauni irin ta dattijontaka, Sarki Shaiban ya amsa masa sannan ya sake tambayarsa abin da ya faru, Zuhairu ya sake sanar da shi kamar yadda kuyangar nan ta sanar da shi da farko, daga nan ya kara da cewa. Ya kai wannan Sarki mai tarin daraja da Martaba ta hasken addinin Musulunci da adalci ga jama'ar ka, ka sani cewa na dauki alkawarin sai na kubutar da Gimbiya Hasima daga hannun wannan matsafi cikin yardar Allah, zan bi shi duk inda ya shiga a fadin duniya na karbota daga gare shi. Ya juya ga Buniyatu ya gabatar da ita gaban Sarki Shaiban ya ce da shi "Wannan ita ce Buniyatul Hajari bin Kauwas, yar uwace a wajen matsafi Bahalu sai dai a yanzu ta karbi addinin Musulunci, kuma ta yi sani da yadda zamu samu nasarar riskar inda wannan shu'umin matsafi yake da yadda zanmu samu nasara a kansa, ta Kuma yi alkawarin za ta taimaka min na cika alkawarin da na dauka cikin yardar Allah." Sarki Shaiban ya yi shiru hawaye na zuba daga idanunsa sannan ya dago kansa ya dubi Zuhairu ya ce da shi. "To Zuhairu na amince da wannan shawara da ka yanke, sannan zan hadaka da jarumai da zasu yi maka rakiya, zan kuma ba ka duk abinda kake bukata daga gareni na guziri yayin Wannan tafiya. Ni kuma zan sanva malamai su ci gaba da yi muku addu'a tare da fatan Allah ya baka nasara ka kubutar da ita daga hannun wannan shu'umin matsafi da ya dauketa." Zuhairu ya yi godiya ga Sarki bisa ga amincewar da ya yi a kan shawarar sa, sannan suka yi sallarma ya tafi ya fice daga fadar tare da Buniyatu suka kama hanyar tafiya alkaryar su. San da suka isa garinsu babu Wanda ya gane Zuhairu daga cikin jama'ar da suka san shi, saboda canzawar da kamaninsa suka yi ya zuwa siffar tsoho. Suka wuce har suka isa gidansu suka shiga shi da Buniyatu. Suka tadda kakansa dattijo Marwan zaune a tsakiyar gidan kan buzu yana jan Casbaha. Shi kansa kakansa MarWan bai gane Zuhairu ba, saboda sauyawar da kamanninsa suka yi ya Zuwa siffar tsoho, ya rika dubansa cikin mamakin ganin wani dattijo sa'an shekarunsa akan dokin jikinsa Zuhairu tare da Buniyatu wadda suka shigo gidan tare da ita, har ya sauka daga kan dokinsa ya karaso gareshi. Da Zuhairu ya ga ya yi masa duban rashin sani bai gane shi ba sai ya yi masa magana ya ce da shi "Ya kakana Marwan ni ne jikanka Zuhairu na kasance cikin wanna hali da ka ke ganina, kuma hakan ta faru ne sakamakon aikin sihiri da matsafi Bahalu ya aikata a kaina ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsu ya sanar da shi, har ya zuwa yadda ya samu nasara akan sa ya maidashi irin wannan siffa ta dattijo da yake a yanzu. Dattijo Marwan ya cika da matukar mamaki da al'ajabin wannan al'amarin da ya faru gareshi, sannan ya dubi Zuhairu ya ce da shi Hakika ka aikata babban kuskure na mantawa da abin da na umarceka, ka sani cewa na haneka da cire zoben da na baka daga dan yatsanka, kuma na sanar da kai cewa ka rika lura komai rintsi kada ka sake ka taka sawun duk wani ma'abocin tsafi da sihiri da ku ke artabu da shi yayin kafsawa. Idan da ka kiyaye wannan sharadi da na sanar da kai na yi imani da cewa ba zai taba samun nasara akan ka ba, cikin yardar Allah. Sai dai a yanzu bakin alkalami va bushe a gareka tunda har wannan lamari ya faru, kuma ita Gimbiya Hasima da wannan zobe yake hannunta na yi imani da cewa ba zai sami nasarar kusantar ta ba matukar zoben yana tare da ita. Zuhairu ya yi shiru yana mai nadamar abin da ya faru na yin mantuwa ga abinda kakansa ya sanar da shi sai dai ya yi matukar farin ciki da ya ji cewa matsafi Bahalu ba zai samu nasarar kusantar Gimbiya Hasima ba, matukar zoben yana tare da ita. Kakansa Marwan ya ce da shi "Yanzu menene kudirinka game da abin da ya faru." Zuhairu ya amsa da cewa "Kudirina shi ne zan bi wannan shu'umin matsafi duk inda ya shiga a fadin duniya, don na kubutar da Gimbiya Hasima daga hannunsa." Ya nuna Buniyatu ya ci gaba da cewa "Wannan kanwace a wajen matsafi Bahalu kuma ta yi sani da yadda zamu samu nasarar zuwa inda ya tafi da Gimbiya Hasima don kubutar da ita, da kuma yadda za a karya wannan sihiri dake tare da ni, ta kuma yi alkawarin Za ta taimaka mini akan haka." Dattijo Marwan ya amince da shawarar da Zuhairu ya yanke, sannan aka bawa Buniyatu masauki inda za ta zauna kafin Zuhairu ya gama shirinsa na tafiya. Al'amarin Gimbiya Hasima kuwa bayan da matsafi Bahalu ya dauketa cikin bakar guguwar nan ya yi sama da ita, tun tana hangen kuyanginta da sauran jama'ar dake cikin lambun da ya

Chapter 1 of 4