Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 4
bakin kofa masu tsaron kofar uk fara duban Zuhairu cikin mamaki da al'ajabin ganinsa tare da Gimbiya Hasima ba tare da ya hallaka ba, kamar aydda suke da masaniyar cewa duk wani namiji da ya kusanci inda takc sai wannan matsafin ya halaka shi, matukar ba mahaifinta ba Da suka shiga cikin birnin duk inda suka wucc sai jama'ar gari su bi Zuhairu da kallo saboda ganin sa tare da Gimbiya Hasima suna masu mamaki da ganin wannan al'amari, shi kuwa Zuhairu bai damu da abinda yake faruwa ba. suka ci gaba da tafiya har suka isa fadar Sarki Shaiban Bayan sun isa fadar Gimbiya da suaran kuyanginta suka shiga ciki, ta je ta sanar da mahaifinta sarki Shaiban zuwan Zuhairu ta yi masa iSo. Sarki ya bada umarmin Zuhairu ya shigo aka je aka shigo da shi har cikin fadarsa. Tun da aka shigo da Zuhairu cikin fadar, Sarki Shaiban ya dubeshi sai ya sake cika da matukar mamaki saboda ganin shi ne jarumin da ya yi mafarki dashi mahayin doki da ya yaki matsafi Bahalu ya halakashi a cikin mafarkinsa, gashi yanzu ya ganshi a zahiri kuma shi nc wanda ya dauki alkawarin taimaka wa yarsa. Zuhairu ya kai gaisuwa gaban Sarki Shaiban, Sarki ya amsa masa, aka yi masa ishara da wajen zama, ya zauna suka kadaita daga shi sai Sarki a fadar sannan Sarki Shaiban ya ce da shi. "Labari ya isheni game da taimakon da ka yiwa 'yata Gimbiya Hasima, tare da alkawarin da ka yi na kubutar da ita daga halin da ta ke ciki, shi ya sa na umarceta cewa idan ta koma inda ku ka hadu da ita ia sanar da kai Cewa ina son ganinka." Ya inganta na sake yin godiya ga Ubangijna bisa baiwa da ni'imar da yake saukarwa akan bayin sa, don kafin faruwar wannan lamari na yi ma farki da zuwan wani jarumi mahayın doki da ya zo ya halaka wannan shu'umin matsafi ya kubutar da 'yata daga halin da take ciki, sannan a yanzu da aka shigo da kai fadata sai na ga cewa babu shakka kaine jarumin da na yi mafarki dashi ya halaka wannan matsafi, don haka nake mai kyakkyawan zato na samun nasara nafarkina va zama gaskiya. Ba zamu zama masu yaw aita mamaki akan abin da ya faru ba don buwayar Ubangiji da ikonsa ta wuce haka. sai dai mu yawaita godiya gareshi da addu'ar neman nasara, kuma na yi maka alkawarin cewa matukar ka raba 'yata Gimbiya Hasima da wannan shu'umin matsafi da ya sanya rayuwara cikin kunci, to kuwa zan baka aurenta tunda itama tana kaunar ka, wannan shi ne dalilin da ya sa na ce ta sanar da kai ina son ganinka, Allah ya yi maka albarka. Zuhairu ya yi matukar farin ciki da jin wannan bayani na sarki Shaiban saboda kaunar da yake yiwa Gimbiya Hasima, ya yi masa godiya cikin girmamawa Lare da tabbatar masa da alkawarin da ya dauka na taimakawa Bahalu. ka, Gimbiya Hasima akan sha'anin matsafi Daga nan suka yi sallama da Sarki Shaiban Zuhairu ya tashi ya fita daga fadar, ya koma wajen su Gimbiya Hasima ya sanar da ita abinda ya faru tsakaninsa da mahaifinta, Gimbiya Hasima ta yi matukar murna da farin ciki, sannan ta sa aka kai Zuhairu wani daki na hutawa, abin kawatawa da kayan ado nau'i daban-daban, suka zauna suka yi hira irin ta masoya aka kawo masa abin sha na 'ya'yan itatuwa na marmari dangin su tufa, inibi da kayan ciye-ciye na karrama masoyi, Zuhairu ya ci ya sha daga abin da aka kawo masa sannan suka yi sallama a bayan gama hirarsu ya tashi ya fita, ya je ya kama dokinsa ya hau, ya kama hanyar komawa gida. Tun daga wannan lokaci Zuhairu ya ci gaba da ziyartar Gimbiya Hasima cikin wannan lambu da take zuwa a kowane yammaci suna hira, wani lokacin kuma ya kan tafi har birnin Bahazum fadar mahaifinta ya Ziyarceta a can su yi hirarsu irin ta ma'abota begen juna. Sannan Zuhairu ya sanar da kakansa Marwan dukkanin abinda yake faruwa game da soyayyarsa da Gimbiya Hasima, da yadda mahaifinta ya karbeshi da martaba, kakan nasa dattijo Marwan ya yi mamaki da wannan labari sannan ya gargadeshi cewa, ya guji shiga abinda bai shafeshi ba, matukar ba taimako zai yi akan dan uwansa Musulmi ba, sannan kada ya sake ya cire Zoben da ke yatsansa ko kuma ya taka sahun wani matsafi da ya taso masa da nufin halakashi a duk inda yake, idan ya kiyaye wannan sharadi babu shakka zai samu nasara akan kowane irin shu'umin matsafi komai tasirin tsafi da sihirinsa. Al-amarin matsafi Bahalu kuwa bayan da ya koma bagiransa da suke zaune tare da 'yar uwarsa Buniyatu, a cikin wasu manyan tsaunuka da suke nesa da Birnin Sinar, tafiya ce mai nisa tsakanin inda suke da birnin Bahazum, sai dai sukan yi tafiyar cikin alkaluman sihirin rage nisan tafiya, su je bimin cikin kankanin lokaci, kuma idan suka je yankin da birnin yake sukan shafe kwanaki masu yawa wani lokacin ma har watanni kafin su sake komawa bigirensu. A sanda matsafi Bahalu ya fara kaunar Gimbiya Hasima ya kan zauna kusa da birnin Bahazu cikin halin 6ata na alkaluman sihiri yana lura da duk wanda zai ce yana kaunarta ya halakashi, kamar yadda ya halaka 'ya'yan sarakuna da dama. Bayan matsafi Bahalu ya yi jinyar raunin da Zuhairu ya ji masa a hannu tsawon kwanaki masu yawa har ya warke, sannan sai ya sake yin shirin dan komawa birnin Bahazum da nufin halaka Zuhairu yana mai tusatuwa da abin da ya aikata gareshi Ya tafi ga taskarsa ta ajiyar kayan sihiri da tsafi da ya gada a wajen mahaifinsa, ya budo, ya dauko wani kurtun sihirin daga cikin taskar ya maida taskar ya rufe, ya koma gaban wani farin dutse mai haske dake tsakivar dakin ya fadi ya yi sujjada, sannan ya daga kurtun sihirin ya girgiza shi yana mai surutai da sambatu irin no aikin sihiri, wani farin hayaki ya soma fita daga cilkin kurtun zuwa jikin farin dutsen, nan take sai ga zanen siffar Zuhairu ya bayyana a jikin farin dutsen tamkar madubi. Matsafi Bahalu ya nuna wannan sura ta Zuhairu da ta bayyana a jikin dutsen da tafin hannunsa, yana mai ci gaba da ambaton wasu kalamai irin na aikin sihiri, da nufin neman sa'a a kansa ya halakashi idan ya sake komawa gare shi. Yana cikin wannan hali na aikin sihiri sai ga 'yar uwarsa Buniyatu ta shigo cikin kogon dutsen, ta dubi jikin farin dutscn nan dake gaban matsafi Bahalu, sai ta ga zanen surar masoyinta Zuhaira tamkar a jikin madubi. Nan take. farin ciki ya lullubeta, ta gabata gareshi tana mai yin yabo da begen wannan sura. Da jin abinda ta ke cewa sai Bahalu ya da kata da abin da ya ke yi, ya juyo ya yi mata magana da cewa "Shin ko kin yi sani da wannan jarumi, da ki ke yabo da ambaton kyawun surarsa." Buniyatu ta amsawa yayanta matsafi Bahalu da cewa "Babu shakka na yi sani da wannan jarima sunansa Zuhairu bin Safuwan, yana zaune a birmin Samaras dake karkashin masarautar birmin Bahazum, na kasance mai bibiyar rayuwarsa cikin bege tun daga ranar da na fara ganinsa, cikin wasu ranaku da na ziyarci yankin birnin Bahazum, shi ne wanda zuciyata take bege da mafi kyawun ambato dan kasancewa tare dani, shi ne wanda na kyautata ranisuwa a akan alkawarin aurcnsa duk da ya nuna rashin amincewarsa akan muradina. Matsafi Bahalu ya cc da ita "Ni kuma na kasance mai nuna tsananin gaba da kiyayyata gareshi sababin abinda ya aikata a kaina, ya kasance mai kaunar wata 'yar Sarki da nake so da muradin aurenta, na kuma yi alkawarin halaka duk wanda ya ce yana kaunarta don ta Zama mallakina duk da ta ce ba za ta auri ma'abocin tsafi da sihiri irina ba. Shi ne mutum na farko da ya taba daga makami a kaina da nufin yin gogayya dani har ya fidda jini daga jikina. Shi ne wanda ya fasa daya daga cikin kurtun sihirin da na gada a wajen mahaifinmu har karfin tsafi da Sihirina ya raunana. Wannan ne dalilin da ya sa na dauki alkawarin halakashi dan yin ramuwa a kansa bisa ga abinda ya aikata a kaina a duk sanda na sake komawa Bahazum." birnin Buniyatu ta ce dashi "Ina mai neman afuwa gareka kada ka halaka masoyina bisa ga abinda ya faru, cewa ni na kasance mai yawan bege da kaunarsa gwargwadon bugawar zuciya da fitar numfashina, kuma zai zama abin kaico gareni da wanzuwa cikin kunci da bakin ciki idan na rasa wannan jarumi ban ma san yadda makomar rayuwata za ta kasance ba." Bahalu ya ce da ita "A rayuwata bana afuwa kuma bana fasa daukar iansa, ba an saurara ga duk wanda ya daga makami gareni ba da nulin halakani har sai da naga Dayansa, kuma bani da kaico akan kowane irin hali da rayuwarki za ta kasancc idan na halaka wannan jarumi, Bakin alkalami ya riga ya bushe garcki don na yi rantsuwa da ababen bautata tare da yin yanka garesu akan hakan ba zan fasa abinda na yi niyya ba, sai ki yi hakuri. Buniyatu ta fusata da jin maganarsa ta ce dashi idan kuwa har ka halaka masoyina kamar yadda ka ambata na rantse da duk abinda nake yin rantsuwa dashi, sai na ie na halaka Gimbiya Hasima 'yar Sarki Shaiban bin Yasar da ka ke son ka halaka masoyina saboda ita." Tana gama fadar maganar ta tashi cikin fushi ta fice daga kogon dutsen ta bar shi, Bahalu bai damu da maganarta ba, ya ci gaba da abin da ya ke yi na aikin Sihiri, dan neman nasara a kan Zuhairu ya halakashi, duk da cewa ya san Buniyatu za ta iya aikata abin da ta ambata akan Gimbiya Hasima. Bayan fitar Buniyatu daga kogon dutscn ta tafi ta nuna ta rasa abinda yake yi mata dadi a duniva, ta shiga tunanin maganganun da yayanta ya ambata na cewa sa ya halaka masoyinta Zuhairu, damuwa ta yi mata yawa har ta rasa abinda yake yi mata dadi, ta san cewa tun da yayanta ya yi nufin halakashi to kuwa babu shakka rayuwarsa tana cikin hadari, ta ji ta kamu da kewar son ganinsa nan take ta tashi ta kama hanyar tafiya birnin Samaras dan ta ga Zuhairu, duk da ta yi alkawarin cewa ba za ta sakc zuwa gare shi ba har sai ranar da za ta tabbatar da cikar burinta na aurensa ko da bai amince ba. Ta yi tafiya mai nisa, a cikin alkaluman sihirin rage nisan tafiya har ta iso birnin Samaras da tsakiyar dare gari ya yi shiru babu motsin kowa. ta nufi gidansu Zuhairu kai tsayc ta shiga ta wuce har dakinsa, ta sameshi a kwance yana barci a kan gadonsa ta tsaya a gabansa tana dubansa cikin bege da kauna har tsawon wani lokaci, shaukin sonsa ya kara ratsa Zuciyarta anan ta sake daukar alkawarin cewa ba za ta bari yayanta ya halaka masoyinta Zuhairu ba matukar tana raye, idan kuwa ya samu nasarar halakashi ba da saninta ba, ko kuma ya yi masa wani aikin sihiri na cutarwa to kuwa ta yi alkawarin sai ta halaka Gimbiya Hasima 'yar Sarki Shaiban dan ta rama. Bayan ta gama wannan tunani na ta ne ta kai hannu za ta shafi jikin Zuhairu saboda shaukin kaunar sa dake kara ratsa zuciyarta. Kafin hannun nata ya kai jikinsa sai zoben da ke dan yatsan Zuhairu ya yi motsi da karfi, Zuhairu ya farka daga barcin da yake yi saboda motsin da zoben ya yi alamar wani matsafine ko ma'abocin aikin sihiri ya kusanceshi, ya duba ko ina a cikin dakin bai ji motsin komai. ba, bare ya ga wani abu ya yi shiru yana saurare jikinsa ya bashi cewa akwai wanda ya shigo cikin dakin duk da baya ganin komai, dan ya san cewa babu yadda za a yi zobensa ya yi motsi ba tare da wani ma'abocin aikin sihiri ya kusanceshi ba. Ya tashi zaune ya yi addu'a sannan ya tafi ya dauko takobinsa dake rataye a jikin bango da Buniyatu ta ga haka sai ta ja da baya sannan ta juya ta fice daga dakin cikin aikin sihiri yadda ba zai ji takun sawunta ba bare ya ganta. Bayan fitar Buniyatu sai Zuhairu ya ji kamar motsi a Waje, ya bude kofar dakinsa cikin sauri ya fito. ya duba bai ga kowa, ya sake jin kamar takun sahu an nufi wajen DUK MAI BUKATAR AUDIO NA LITTAFIN SAI YA DANNA HOTON DAKE NAN KASA https://youtu.be/YSYyhta02NI BAKAR GUGUWA littafi na daya 1 Na Marubuci Shehu Usman Muhd Typing by Shuraih Usman Part E ka zama miji a gareni ta kowane irin hali, dan haka ba zan diana kaunarka ba kamar yadda ba zan rabu da abinda na gada a wajen mahaifina ba na sirTin tsafi da sihiri. Zuhairu ya ce da ita "Ke dai kina cikin rudani da bata mabayyani, kasancewarki mai yin imani da bayyanar wasu bayanai na alkaluman sihiri akan cikar kudirinki, kuma cikin yardar Allah ba za ki taba cimma kudirin naki ba, cewa ni na kasance mai dogarO dashi akan ya kiyayeni daga duk wani sharri ma'abota tsafi da sihiri irin ki." Buniyatu ta ce da shi "Kaine rayuwar ka take cikin tasku da razani na kusantar halaka, sababin alkawarin da dan uwana ya dauka na halakaka, akan soyayyar Gimbiya Hasima dake kalamansa sun munana akan ambaton salwantar da wanzuwa a tsakaninku, rayuwarka cikin aikin sihirin da yake shiryawa a yanzu dan zuwa gare ka, wannan ne dalilin da ya sa zuciyata ta ka samun nutsuwa akan maganarsa. kuma na shiga halin damuwa da begen son ganinka, don haka na taso na taho garcka cikin wannan dare, na yi alkawarin bada kariya garcka akan duk wani aikin tsafi da sihirinsa, kuma idan har wani abin cutarwa na daga cikin sihirinsa ya sameka to kuwa na yi alkawarin sai na halaka Gimbiya Hasima yar sarki Shaiban bin Yasar da yake son cutar da rayuwarka saboda ita. Zuhairu ya fusata da jin maganarta ya maida mata raddi da cewa. Har ke kina da tasirin bada kariya ga wanda ya dogara ga Allah cikin lamarinsa, ke kanki ba ki da ikon Kare kanki daga duk abinda Allah ya hukunta zai faru garcki, kuma ina mai gargadinki da gargadi mai tsauri kan cewa duk abinda ya faru ga Gimbiya Hasima na rantsc da wanda raina yakc hannunsa sai na halakaki daga ke har dan uwan naki na sharc ruhinku daga dogon kasa. Yana gama fadar maganar Buniyatu ba ta ko tanka masa ba, ta bace cikin alkaluman sihirinta ta fice daga gidan ta yi tafiyarta ta barshi, Zuhairu ya tafi ya koma dakin sa ya yi addu'a ya kwanta yana tunanin maganar da Buniyatu ta fada akan Gimbiya Hasima har barci ya dauke shi. Tun daga wannan rana da Buniyatu ta je wajen Zuhairu ta sameshi a gida da tsakiyar dare, Zuhairu bai sake ganinta ta bayyana gareshi ba, kuma babu wani abu da ya faru gareshi na daga aikin sihiri daga yayanta matsafi Bahalu da ya dauki alkawarin sai ya hallakashi. Sannan Zuhairu bai sanar da Gimbiya Hasima abinda ya faru tsakaninsa da Buniyatu ba, akan alkawarin da ta dauka na cewa idan wani abu na cutarwa ya same shi daga yayanta itama za ta maida martani a kanta. Al'amarin Gimbiya Hasima kuwa ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali, akan lamarin matsafi Bahalu, tun tana fargaba da tsoron kada ya halaka Zuhairu kamar yadda yake halaka duk wanda ya ce yana kaunarta, har ta daina fargabar komai saboda ganin matsafi Bahalu bai sake bayyana gareta ba, tun daga ranar da suka yi artabu da Zuhairu ya fasa kurtun sihirin da yake hannunsa, kuma ta daina yin munanan mafarke-mafarken da take yi a kansa, tare da ganin ababen ban tsoro da firgitarwa dake sata zaran1 a duk sanda zai bayyana gareta. Sukan hadu da Zuhairu a duk sanda ta ziyarci wannan lambu da take zuwa tare da kuyanginta su yi hira irinta ma'abota bege da kaunar juna har zuwa faduwar rana, sannan Zuhairu ya yi mata rakiya, har kofar shiga birninsu daga nan ya juya ya kama hanyar kamawa gida. Duk wannan abin da ya ke faruwa Buniyatu ta kan kasahce tare da Zuhairu a duk inda yake. Saboda alkawarin da ta dauka na bada kariya gareshi don kada yayanta matsafi Bahalu ya halakashi kamar yádda ya sha alwashi, sai dai ta kan yi nesa da Zuhairu yadda ba zai ji motsinta ba, don ta san idan ta kusanceshi zai gane cewa tana tare da shi saboda zoben dake yatsansa. A duk sanda Zuhairu suke cikin lambu suna hira tare da Gimbiya Hasima Buniyatu ta kan ji kishi da bakin ciki kamar ta je ta halaka Gimbiya Hasima, sai dai ba ta da ikon aikata hakan saboda sanin cewa idan ta halakata babu shakka sai yayanta ya halaka Zuhairu, don haka ta kan yi nisa da bakin lambun dan kada ta ji ko ta ga abinda suke yi na soyayya da begen juna. Wata rana daga cikin irin wadannan ranaku na rayuwarsu, Gimbiya Hasima tare da Zuhairu suna zaune cikin lambu suna hira, kuyanginta, sun basu waje suna zantawa irin ta ma'abota begen juna, Gimbiya Hasima ta caba ado da kayan ado mafi daraja da 'ya'yan Sarakuna suke sanyawa, suna zaune akan wasu kuferu na alfarma dake tsakanin wasu filawoyi da furanni masu kayatarwa da kyan tsari, kamshin turaren wuta ya gauraye wajen mafi dadin kamshi daga turaren almiski. Buniyatu da ta kasance mai bibiyar Zuhairu a duk inda yake, ta yi nisa da bakin lambun ya zu wa cikin wasu duwatsu dake bayan lambun dan kada ta riski hurar da suke yi ta masoya saboda kishi. Gimbiya Hasima ta dubi zoben nan dake dan yatsan Zuhairu sannan ta ce dashi. "Na dade ina muradin mallakar zoben nan na azurfa dake hannunka, tun daga lokacin da na fara ganin sa tare da kai, sai dai ban yi sani ba ko cewa ba irin zoben da za ka bada kyautarsa gareni bane, kasancewar ko yana tare da wani sirri na daga rayuwarka a tare da shi. Zuhairu ya murza zoben sannan ya ce da ita "Hakika wannan zobene ne mai daraja a gareni, kuma yana tare da wani sirri da ya shafi rayuwata, don haka ba zan iya bada kyautarsa gareki ba, kamar yadda wanda ya mallakeshi gareni ya umarceni cewa kada na sake na rabu da shi a duk inda nake cikin kowane irin hali." Gimbiya 1Hasima ta ce da shi za ka iya bani shi ha gani don na karewa irin kirarsa kallo, idan na koma birnin Bahazum na sanya kwararrun makera su Kera min irinsa." "Zan iya baki ki gani." In ji Zuhairu ya cire zoben daga dan yatsansa ya mika mata, Gimbiya Hasima ta karba ta karewa zoben kallo na irin kyawun kirar da aka yi masa, sannan sai ta sanya a dan yatsanta dan ta gwada, zoben ya yi mata kyau matuka kamar saboda ita aka kerashi, shi kansa Zuhairu sai da ya yi bege ga kyawun zoben a jikin dan yatsanta, ya ji ba don wasiyyar da aka yi masa ba cewa kada ya sake ya rabu da zoben da kuwa ya bar mata 7obcn ta sanya a hannunta. Suna cikin wannan hali e kafin Gimbiya Hasima ta cire zoben daga hannunta ta bawa Zuhairu sai suka ii wata irin kara mai tsananin karfi da rugugi mai ban firgici kamar fadowar aradu ta cika wajen, kasa ta rika girgiza tana raurawa kamar za ta tsage su rufta cikinta. wani bakin gajimare ya taho daga gabas ya lullube sararin samaniya tamkar hadari, gaba daya wajen ya yi duhu mafi tsanani daga yankin duhun darc, rugugin da suke ji ya ci gaba da hauhawa yana kara kusanto inda suke har sai da suka daina jin komai sai shi, tamkar kokon kawunansu zai fashe saboda tsananinsa. Kuyangin Gimbiya Hasima suka razana suka rugo inda su Zuhairu suke cikin firgici, ita kanta Gimbiya Hasima sai da ta tsorata ta shiga halin rudani da kidima, saboda ta san cewa matsafi Bahalu ne zai bayyana, cikin wannan hali mafi munin yanayi daga alamomin bayyanarsa. Shi kuwa Zuhairu duk da ganin abinda yake faruwa bai razana ba, sai ya mike tsaye yana duban wannan yanayi cikin tsananin jarumta da karfin zuciya, kuma ya san wannan ba komai bane face aikin sihiri da tsafi irin na ma'abota shirka da tabewa, Wa iyazu billahi. Ya ce a ransa, yana mai hasashen cewa matsafi Bahalu ne zai sake bayyana garesu. Bayan Bayan wani lokaci sai suka hangi bakar guguwar nan ta danno daga bangaren yamma, tare da iska mai tsananin karfin, feshin wuta yana tartsatsi, da zubowa daga cikin bakar guguwar. Kamar dai yadda matsafi Bahalu ya ke yi idan zai bayyana. Guguwar ta ci gaba da tahowa har sai da ta iso gaban Luhairu sannan ta tsaya, aka sake yin tsawa da rugugin radu mai tsananin karfi da ya zarce wanda suka ji da farko, wani farin haske ya keto daga cin bakar guguwar daga cikin hasken sai ga Matsali G1Ziyanu ya bayyana sanye da kaya irin na mashahuran matsafa, ma'abota aikin sihiri, hannunsa na hagu yana rike da sandarsa ta tsafi, na dama kuma yana rike da wani kurtun sihirin bayan wanda Zuhairu ya fasa a wancan haduwar da suka yi sanda suke fa fatawa a tsakaninsu. Matsafi Bahalu ya dub Zuhairu cikin tsananin fushi da fusatuwa ya ce da shi. "Kaicon ranar dana-6ani marar amiani gareka, da za ka hallaka sababin bijiréwa umarni da gargadin da na yi garcka, akan ka rabu da Gimbiya Hasima amma ka ki ji. Yau ne ranar da zan tabbatar da isa da karfin ikona a kanka. Yau ne ranar da za ka tabbatar da tasirin tsafi da sihiri da ka ke inkarinsa ya zarce tasirin duk wani abin dogaronka. "Yau ne ranar da za ka halaka da salwantar ruhinka daga doron kasa ta hanyar kis amafi muni da ukuba mai tsanani kafin fitar ranka. K uma yau ne ranar da na jima ina sauraron zuwanta da alamomi zasu bayyana gareni na mallakar Gimbiya Hasima ta zama matata, idan na hallakaka zan dauketa na tafi da ita DAHRUL SABAR dake lardin ASHTAR mu zauna tare da ita har abada, fada ce da mahaifin yasa aka gina masa a wannan lardi da babu wani mahaluki da ya isa zuwa inda take ya shiga cikin ta idan ba mamallakinta ba, kuma shima kafin ya kai ga tarewa a cikinta ya rasu, don haka ni ne zan tare a cikinta tare da Gimbiya Hasima. Zuhairu ya amsa da cewa kada ka zama mai alfahar da bayyana abinda ba za ka iya aikatawa ba, cewa kai ka kasance mai yawan alwashi da yawan rantse-rantse bisa ga abinda ka ke hasashen samun nasara a kansa, kuma tun wancan lokacin har ya zuwa yanzu ababen bautarka da ka ke yin rantsuwa da su sun kasa baka nasara bisa ga tasirin tsafi da sihirinka. Bahalu ya fusata da jin maganarsa ya yi karaji da gunji dake tattare da aikin sihiri gaba ki daya wajen ya yi amsa kuwwa da amo mai hauhawa, ya zaro wasu kibiyoyi irin na aikin sihiri ya jefi Zuhairu da su, kafin kibiyoyin sukai kansa sai wani farin haske ya ratso ya shiga tsakaninsu,d aga cikin farin hasken sai ga Buniyatu ta bayyana a gaban Zuhairu ta sanya wata garkuwa ta kade kibiyoyin suka zube kasa, wajen da kibiyoyin suka fadi ya kama da wuta kasar wajen ta kone ta yi baki. Bahalu ya fusata da ganin abinda ya faru ya dakawa Buniyatu tsawa ya ce da ita, "Me ya sa ki ka kare abinda na aikata cikin alkaluman sihirina da nufin halaka wannan jarumi, ki sani cewa ba zan fasa abinda na yi niyyar aikatawa ba, n: halaka wannan mutum ko ta wane irin hali." ga Buniyatu ta ce da shi "Na yi rantsuwa da duk abinda nake yin rantsuwa da shi ba zan bari ka halaka masoyina ba, idan kuwa wani abu na cutarwa ya sameshi daga garcka to kuwa sai na halaka Gimbiya Hasima wadda ka ke son hallakashi saboda ita." Matsafi Bahalu ya ce da ita "Idan kin zama mai bada kariya a gareshi to kuwa ba za ki iya kubutar dashi daga abinda na yi niyyar aikatawa a kansa ba, na yi rantsuwa da tasirin tsafi da silhiri na tare da yanka ga ababen bauta 4 na kuma nemi sa'a daga garesu ina mai fatan samun nasara a kansa. Ya sake turawa Zuhairu wani aikin sihirin wuta ta vi kansa za ta kama jikinsa ya kone, Buniyatu ta yi nata surkullen ta tare wutar, nan take wutar ta mutu kafin ta kai kan Zuhairu. Ya sake jifansa da wani irin mashi na aikin sihiri ja jawur dashi kamar karfen da aka curoshi daga wutar makera, Buniyatu ta tura wata 1ska ma1 tsananin karfi ta ture mashin ya tafi ya fada cikin wata korama dake gudanawa a tsakiyar lambun, ruwan cikin koramar ya kama tafasa saboda masifa nan take launin ruwan ya sauya ya koma ja jawur kamar jini. Matsafi Bahalu ya sake fusata da fushi mai tsanani ya yi karaji da kururuwa mai matukar karfi, ya daki kasa da sandar tsafin dake hannunsa, iska da bakar guguwa suka turnuke suka rufe wajen har sai da su Zuhairu suka daina ganin junansu, ya biyo ta cikin duhun bakar guguwar da nufin halaka Zuhairu, Buniyatu ta tura wani farin haske cikin bakar guguwar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana tana ganinshi, ya daga sandarsa ta tsafi dake hannunsa zai makawa Zuhairu Buniyatu ta sanya hannunta ta ade Sandar bai same shi ba. Bahalu ya sake fusata ya kai mata sura cikin sa'a ya fizge kurtun sihirin da yake hannunta, wanda a tare da shi ne duk wani abu da ta gada na daga alkaluman sihiri yake ciki, Buniyatu ta yi karaji da kururuwwa ma tsananin karfi, saboda subucewar kurtun sihirin daga hannunta zuwa hannun matsafi Bahalu. Ku yi min afiuwa domin jin yadda za ta kasance mu hadu a littafi na biyu. Na ku har kullum mai fatan nishafantar da ku. Shehu Usman Muhd Littattafain Marubucin: MAZAN FAMA JARUMTA BAJINTA HARGITSI GWAGWARMAYA DAUKAR FANSA BAKAR GUGUWA JAHURUL KARNI An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi

Chapter 3 of 4