Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 4
halaka ka har da kai sai kayi hattara. Zuhairu ya cika da matukar mamakin najin labarin abinda yake faruwa akan gimbiya Hasima tare da gasgata maganar da Muzaffar ya sanar da shi. Saboda abinda ya gani da idanunsa, sai dai lamarin baisa Zuciyarsa ta karaya ga barin kaunar gimbiya Hasima ba, sai ma ya ji ya kara bcgenta aransa ya kuma dauki alkawarin taimaka mata ya rabata da wannan shu'umin matsafin iya kacin iyawarsa. Ya dubi Muzaffar ya ce da shi "ldan har abinda ka ambata ya tabbata gaskiya babu shakka na dauki alkawarin kasancewa wanda za1 raba tsakanın gimbiya Hasima da wannan shu'umin matsafi ko wanene shi, zan sadaukar da rayuwata dan na taimaka mata takubuta daga makircin wannan matsafi matukar ina raye." Muzaffar ya sake dubansa cikin mamaki ya ce da shi "Kaicon zuciyar da tamakance akan soyayya har take neman kai ruhi da gangar jiki ga halaka. Ka sani cewa rayukan mazaje da dama sun salwanta akan kaunar gimbiya Hasima kamar yadda kai ma zaka halaka matukar baka nisanta zuciyarka da begenta ba. Menene dogaronka na tunkarar hamshakin matsafi da ya halaka manyan jarumai ya'yan sarakuna da attajirai masu ji da kansu akan gimbiya Hasima." uhairu ya ce da shi "Kai dai bari ga ambaton irin Wannan zance kada imaninka ya raurñana, cewa ni na dogara ga Allah ubangijin musulunci, gareshi nake neman taimako kuma nayi imani da cewa shi mairinjayene akan kowane irin karfin tsafi da sihiri, dan haka bazan taba zama mai rauni ba akan shakkar wani mutum ma'abocin tsafi da sihiri, kuma da sannu zan zama mai cimma nasara akan abinda na dauki alkawarı akansa cikin yardar Allah." Yana gama fadar maganar ya yiwa Muzaffar sallama ya kada linzamin dokinsa ya wuce. Muzaffar ya bishi da kallo har va bace sannan shima ya saki nasa linzamin dokin ya ci gaba da tafiya ya zuwa inda ya nufa. Da Zuhairu ya isa gida bai sanar da kakansa Marwan abinda ya faru garcshi a ftarsa ta wannan rana ba, dan gudun kada ya ce yarabu da gimbiya Hasima saboda wannan da shu'umin matsafi, ya bar maganar aransa tare da daukar alkawarin cewa idan har ya koma bakin wannan lambu da gimbiya Hasima take zuwa, idan ya ganta zai tunkareta ya sanar da ita yana kaunarta kodan yaga wannan shu'umin matsafi da aka bashi labarinsa. Bayan wasu kwanaki da faruwar wannan lamarı, Zuhairu ya sake yin shiri ya nufi bakin wannan lambu da gimbiya Hasima take zuwa da isarsa wajan ya tadda gimbiya Hasima bata karaso ba, ya sauka daga kan dokinsa ya daure shi, sannan ya koma inda ya saba zama ya zauna yana jiran zuwanta. Bai dade da zama ba sai ga gimbiya Hasima tare da kuyangunta sun nufo bakin wannan lambu da take zuwa. Zuhairu ya yi farin ciki da sake ganinta, yana dubansu har suka iso bakin wannan lambun suka sauka daga kan dawakansu sannan sai ya tashi ya tunkari inda suke dan ya sanar da gimbiya Hasima abinda yake ransa na daga begenta. Ko dan yaga wannan matsafi da aka bashi labarin kamar yadda ya yi alkawarin aransa. Tun da ya tunkari inda suke sai yaga sunja sun tsaya suna dubansa a tsorace kamar wanda suka ga wani abin cutarwa ya tunkaro inda suke. Zuhairu bai karaya ba saboda sanin labarin da aka bashi, ya isa garesu ya yi musu sallama kuyangin gimbiya Hasima suka amsa masa ita bata yi masa magana ba, ta ma kauda kai gabarin dubansa kamar yadda tayi a waccen lokacin day a taimakesu. Ya ci gaba da magana garcta yana nai ladin cewa "Idan har nayi dace da zuwana garcki bai zama laifi ga gimbiya ba, ina mika gaisuwata garcki cikin girmamawa da martaba 'yar sarki jikan sarki abin bibiya da koyi a fagen adalci ga sauran sarakunan duniya, nazo gareki ne (dan neman yarda bisa ga begenki da yake zuciyata idan kin aminta dani cikin lamarinki." Yana fadar wannan magana sai yaga gimbiya Hasima ta dago kanta da sauri ta dubeshi cikin yanayin tsoro da razana, kamar wadda ya fada mata mummunan kalami mafi munin ambato, amma bata yi masa magana ba. Kafin Zuhairu ya sake yi mata magana sai suka j wata irin tsawa mai tsananin karfi tare da wani rugugi mai hauhawa tamkar fadowar aradu ya gauraye wajan. Kasa ta soma girgiza tana raurawa tamkar zata tsage su nutse a cikinta su hallaka, iska mai tsananin karfi tare da bakar guguwar nan mai fesar da wuta daga cikinta, irin wadda Zuhairu ya gani a wancan karan ta keto daga bangaren yamma ta nufo inda suke. Zuhairu ya ji zoben dake hannunsa ya yi motsi alamar wani matsafine ya tunkaro inda yake. Bakar guguwar nan ta taso kan Zuhairu kamar zata rufeshi ya halaka, da ganin haka sai gimbiya Hasima da sauran kuyangun da suke tare da ita hankalinsu ya tashi, suka shiga halin kidima da rudewa, shi kuwa Zuhairu sai ya ci gaba da duban bakar guguwa dake tafe da feshin wuta cikin jarumta da karfin zuciya, kuma yasan wannan ba komai ba ne lace aikin tsafi da sihiri irinna ma'abota shirka, wa'iyazubillah ya ce aransa yana duban guguwar har ta karaso inda yake. Da guguwar ta karaso bata rufe shi ba kamar yadda ya yi zato sai yaga ta tsaya agabanza tayi tsiri sama tana juyawa, sannan ta sake yo kasa har sai da talafa wajan ya washe sai wani farin hayaki da ya tsaya a gaban Zuhairu, suka sake jin wani karaji mai ban firgici daga cikin hayakin, sannan suka ji anyi zagi da kalma mafi munin ambato akan Zuhairu, aka ci gaba da yi masa magana cikin kakkausar murya mai hauhawa da fadin cewa. "Kaicon rayuwarka da kusantar ajali sababin abinda ka ambata na begen gimbiya Hasima, zai zama mafi munin karshen garcka da mutuwar kaskanci akanka saboda abinda ka ambata ka sani cewa gimbiya Hasima mallakina ce. Kuma nayi alkawarin hallaka duk wani namiji da ya kusanci inda take matukar ba mahaifinta ka ba, bare ya ambata yana kaunarta kamar yadda ka ambata na rantsc da karfin tsafi da sihiri na sai na halakashi kamar yadda na halaka wasu mazaje da dama suboda begenta." Zuhairu ya maida raddi ga inda yake jin maganar cikin karfin zuciya da cewa. "Da zanyi gani da mai ambato dake 6oye cikin aikin sihiri, da kuwa nayi jahadin kawar da mushiriki ma'abocin aikin tsafi daga doron kasa, wancenc kai kumna ka bayyana gare ni ko kazama daga wanda suka 1sa sufada aji ba masu boyuwa cikin aiki sihiri ba." Yana fadar maganar sai ya sake jin wata tsawar mai matukar razanarwa ta sake cika wajen sannan iskar da take kadawa mai matukar karfi ta tsaya cak. daga cikin farin hayakin nan dake tsaye a gabansa, sai yaga want mutum ya bayyana ta cikinsa, katone kakkarfa babu... DUK MAI BUKATAR AUDIO NA LITTAFIN SAI YA DANNA HOTON DAKE NAN KASA https://youtu.be/YSYyhta02NI BAKAR GUGUWA littafi na daya 1 Na Marubuci Shehu Usman Muhd Typing by Shuraih Usman Part C alamar tausayi ko imani a tare dashi. Yana sanye da sutura irinta mashahuran matsata, hannunsa nadama yana rike da 'yar kakramar sanda wadda akayiwa ado da zinari na hagu kuma.yana rike da wani gora irin wanda ya gani a hannu matsfiya Buniyatu, an zagaye bakin goran da wasu gurayc da kambuna irinna aikin sihiri, ya dubi Zuhairu ya ce da shi. "Ahir "Ahir dika da ambaton wadannan kalamai akan wadda ya buwaya cikin aikin sihiri, nine matsafi BAHALUL HAJARI BIN KAUWAS, mahaifina shine sarkin bokaye da matsafa ma'abota bautar gumaka da ke yammacin birnin Sinar, bayan rasuwar na gaj1 kashi casa'in da tara na sirrin tsafi da sihirinsa yar uwata ta gaji kashi daya, dan haka yau duniya babu wani masani cikin alkaluman sihiri da yasan kashi goma cikin dari na abinda na gada wajan mahaifina. Sannan ina kaunar gimbiya Hasima ne da nufin ta Zama matata saboda na yi bincike a cikin alkaluman Sihirina bayanan sun tabbatar da cewa, babu wata mace da ta kai ta kyau da cikar halitta a wannan zamani, don haka na yi alkawarin aurenta ko ta wane irin hali, duk da ita ta ce ba za ta auri ma'abocin tsafi da sihiri irina ba, kuma na sha alwashin hallaka duk wanda ya kusanci inda ta ke bare ya ambata yana kaunarta. Na halaka mutane da dama a kanta wasu ma ba ta san da su ba wucewa ta zo yi suka yaba kyawun surarta na halakasu, kuma na yi rantsuwa da abin bautata tare da karfin tsafi da sihirina sai na hallaka duk wanda ya ce yana kaunarta ko wa ye shi, har zuwa ranar bayyanar wasu bayanal Cikin alkaluman sihirina da zasu tabbatar da mallakar Gimbiya Hasima garenı ta zama matata." Da jin wannan bayani na matsafi Bahalu sai Zuhairu ya gane cewa shi ne yayan Buniyatul Hajari da ta taba uwa gareshi cikin halin aikin sihiri ta ce dashi tana Kaunar sa da muradin ya aurcta. Zuhairu ya sake madia masa raddi da cewa "Kaiconka ya kai wannan fajirin mutum da irin kalamanka masu munin ambato, zan yi ishara garcka da zuwan karshen wannan ta'asa da zalunci da kake aikatawa, idan har ba ka rabu da Gimbiya Hasima babu shakka ajali zai gabata garcka sababin haduwar ka dani. Bahalu ya fusata dajin maganar Zuhairu ya ce da shi "Da ka yi sanin makoma da karshen wanda ya ambata irin wannan kalamin gareni da ba ka yi sha'awar ambatashi da bakinka ba, na yi rantsuwa da ni kaina saina halaka ka da kisa mafi muni ta hanyar karfin tsafi da sihirina." Ya yi karaji da kururuwa mai karfi da ke tattare da aikin sihiri, da jin ya yi amsa kuwwa da hauhawa Kasa ta ti girgiza, ya juya sandar sihirin da ke hannunsa nan takc ta rikida la zama shafceciy ar takobi tana sheki kaifinta kamar zai zuba a kasa, ya taso kan Zuhairu a fusace bakar guguwar nan ta biyo bayansa. Zuhairu ya zare tasa takobin ya tareshi suka yi karon battar karfe, takubbansu suna haduwa wata kakkarfar iska ta yi jifa da Zuhairu har sai da ya tafi ya fadi a kasa, Bahalu ya kai masa sara Zuhairu ya goce, sannan ya mike cikın sauri da azama, shima ya kai masa nasa saran, babu abin da ya tare kaifin takobin Zuhairu amma amo mai tana shiga jikin Bahalu sai va kece gida biyu sara takobin ya wuce. Suka ci gaba da fafataWa cikin mugun nufi na san halaka abokin karawa. Da matsafi Bahalu yaga ba zai iva halaka Zuhairu ta hanyar karfi da jarumta ba sai ya koma ga aikin sihiri da tsafinsa. Ya yi karaji ya nuna Zuhairu da tafin hannunsa yana surutai da sambatu irin na aikin sihiri, nan take wuta ta kama ta taso kan Zuhairu za ta konashi, Zuhairu ya yi tsalle da maujajawa ya goce wutar ta wuce ba ta samu jikinsa ba, ya watso masa wzsu kibiyoyi irin na aikin sihiri Zuhairu ya sanya takobin ya ya kade kibiyoyin suka tafi suka zube a kasa wajen ya kama da wuta. Matsafi Bahalu ya sake yin wani siddabarun cikia alkaluman sihirinsa, nan take sai ga wani katon dutse daga sama yana ci da wuta, ya mirgino ya nufo kan Zuhairu zai danneshi ya halaka, Gimbiya Hasima ta kwala kara mai tsananin karfi saboda razana, don ta sha ganin da irin wannan sihirin ya hallaka wasu daga cikin masoyan ta. Zuhairu ya ji hucin tahowar dutsen daga samansa ya yi tsalle ya kauce dutsen, ya fadi a wajen ya kama da wuta kasar wajen ta kone kurmus. Ta yi baki. Bahalu ya fusata da ganin Zuhairu bai halaka ba, ya sake yin wani siddabarun cikin alkaluman tsafinsa. Ya sari kasa da takobin da take hannunsa, nan take kasar ta rika darewa tana ruftawa da duk abin da yake kanta ta nufo inda Zuhairu yake za ta rufta dashi ya halaka. Zuhairu ya sake gocewa kasar ba ta rufta da shi ba. Matsafi Bahalu ya sake yin wani karaji dake tare da aikin sihiri, iska mai tsananin karfi tare da bakar guguwar nan suka sake turnuke wajen. Bahalu ya biyo ta cikin bakar guguwar ya taso kan Zuhairu zai halakashi, idan ya yi karaji sai ka ga feshin wuta yana zuba daga cikin guguwar saboda aikin sihiri. Gimbiya Hasima ta sake kwala wata razananniyar kara saboda firgita, don ta sha ganin a gabanta ya halaka wasu daga cikin wanda suka ce suna kaunarta da irin wannan aikin sihirin. Kafin bakar guguwar ta isa kan Zuhairu sai ya yi kabbara da madaukakiyar murya mai karfi, tare da ambaton sunayen Ubangiji yana mai tasbihi gareshi dan yin tawassali da neman kariya daga gareshi akan wannan aikin sihiri. Guguwar tana karasowa gareshi ya kai sara cikinta da dukkanin karfinsa, cikin sa'a ya samu matsafi Bahalu a hannu kurtun sihirin da yake hannunsa ya fashe. Bahalu ya yi wata razananniyar kara mai karfi saboda azaba, guguwar da ta tunkaro Zuhairu ta koma baya ta bace, sannan wajen ya washe Zuhairu ya duba bai ga matsafi Bahalu ba ya shiga nemansa cikin taka- tsantsan amma bai sake ganin ya bayyana gareshi ba. Bayan wani lokaci sai ya ji maganar matsafi Bahalu yana cewa dashi cikin kakkausar murya. "Azaba ta tabbata gare ka ya kai wannan jarumi,.. dake nufin tozarci ga girman matsayina. Na yi rantsuwa da taurari tare da karfin tsafi da sihiri sai na halakaka da kisa mafi &askanci da azaba mai tsanani sababin abin da ka aikata gareshi." Zuhairu ya ce dashi "Babu razanarwa ko ban tsoro ga wanda ya zama gajiyayye ma'abocin rauni da rashin tasiri, kaicon wanda yake gudun ceton rai cikin tsoro da firgita akan abin da ya sha alwashin ganin bayansa. Wadai da mai alfaharin da ya zama kaskantacce abin dogaronsa ya kasa tasirin bashi nasara, idan kana inkarin abinda na ambata ka sake bayyana a gare ni, na rantse da' wanda raina yake hannunsa sai na halakaka da shafe ruhinka daga doron kasa, kamar yadda ka halaka wadanda ka samu nasara a kansu. Kake alfahari da hakan. Matsafi Bahalu ya bayyana cikin fushi amma nesa da inda Zuhairu yake jini yana zuba a inda kaifin takobin sa ya sareshi sannan kurtun sihirin da yake hannunsa ya fashe, ya dubi Zuhairu ya ce da shi. "Zai zama abin kaico gareni idan na bar wannan waje ba tare da na hallaka ba, sai dai ya zama dole gareni na koma ga bagırena don sake yin shiri a kanka, sababin fashewar kurtun sihiri da yake hannuna, amma ina mai sake yin rantsuwa da duk abinda nake yin rantsuwa dashi, halaka za ta tabbata gare ka a duk sanda na sake bayyana gareka. Sababin abinda ka aikata a kaina. Yana gama fadar wannan maganar sai suka ga ya bace, sannan bakar guguwar nan da ya bayyanata cikinta ta sake turnukewa ta yi tsiri sama, ta nuasa ta nufi inda ta fito har ia bi iska ta bace. Duhun day a rufe wajen ya washe komai ya koma yadda yake. Da Zuhairu ya ga matsafi Bahalu ya tafi sai ya yi ajiyar zuciya irin na jarumta sannan ya maida takobin sa, ya juya wajen da Gimbiya Hasima da sauran kuyaginta suke tsaye suna kallon abin da ya faru tsakaninsa da mastafi Bahalu, suna hada ido da ita sai ta fashe da kuka sannan ta soma yi masa magana cikin wata tattausar murya mai ban tausayi ta ce da shi. "Wannan shi ne abin da yake damuna a rayuwata ta duniya, tun daga ranar da wannan matsafi ya ce yana kaunata na rasa sukuni da farin ciki har ya zuwa yau, babu shakka duk abin da ya fada haka yake wannan matsafi ya halaka jama'a da dama saboda ni tun daga yayan sarakuna da manyan attajirai da suka ambata suna neman aurena, har ta kai a yanzu babu wani namiji da ya isa kusantar inda nake bare ya yi min magana matukar ba mahaifina ba, har sai wannan shu'umin matsafi ya halakashi, wannan ne ya sa ban yi maka magana ba barc godiya a snada ka taba taimakona a farkon haduwata da kai, don haka ina rokonka ka nisanta kanka da kusantar inda nake matukar ba kana so wannan matsafi ya halakaka ba kamar yadda ya halaka wasu mutanen a baya. Zuhairu ya ce da ita "Ka da ki zama mai raunin zuciya da zai sa imaninki ya raunana, ki sani cewa tsafi da sihiri shirka ce wadda ba ta tasiri akan gaskiya, wato addinin Musulunci, kuma Allah yana tare da duk wanda ya dogara dashi zai kuma kareshi daga sharri ma'abota tsali da sihiri komai tasirin tsafin sa, garcshi na dogara kasancewar shi mai rinjaye ne akan duk wani aikin sihiri,.na samu labarin abinda yake faruwa gareki.game da wannan shu'umin matsafi, wannans hi ne dalilin da ya kawoni gareki har na ambata ina kaunarki dan na ga kowane ne shi, kuma na dauki alkawarin cikin yardar Allah sai na rabaki da wannan matsafi na kubutar da ke daga halin da ki ke ciki. Gimbiya Hasima ta sake cewa da shi "Ka yi hakuri ya kai wannan bawan Allah, ba na so ka halaka a kaina kamar yadda wasu da dama suka hallaka saboda ni." Zuhairu ya ce da ita "Idan ya samu nasarar hallaka wasu mazajen saboda ke a baya Allah ne ya kaddara faruwar hakan a kansu, kuma wannan ba yana nufin cewa ya fi kartin hukuncin Ubangiji ba, cikin yardar Allah ni zan žama sanadiyyar halakarsa matukar bai rabu da ke ba. Daga kaina ba zai sake halaka wani ba." Gimbiya Hasima ta yi shiru ba ta sake yin musu akan maganarsa ba, bayan wani lokaci ta dago kanta ta ce dashi, ya ya sunanka kuma ina labarin garinku da abinda yake kawoka wannan waje. Zuhairu ya ce "Sunana Zuhairu bin Safwan kuma na kan zo wannan waje ne daga birnin SAMARAS dake karkashin masarautar mahaifinki, ya sanar da ita dukkanin labarinsa sannan suka yi sallama, ta kama dokinta ta hau sauran kuyanginta suma suka kama nasu dawakan suka hau suka yi masa sallama suka hanyar komawa binrin Bahazum, sai da suka yi nisa sannan shima ya kama nasa dokin ya hau ya nufi hanyar kama komawa gida. Da isar Gimbiya Hasima gida ta sauka daga kan dokinta, ba ta tsaya a ko ina ba sai cikin dakin mahaifinta, ta shiga cikin matukar murna da farin ciki ta sameshi a zaune cikin halin damuwa, saboda bakin cikin halin da 'yarsa take ciki Da shigowarta Sarki Shaiban ya ganta cikin murna da farin ciki, abin da ya dade rabon da ya ga yarsa Gimbiya Hasima a cikin irin wannan yanayi, tun daga sanda matsafi Bahalu ya ambata yana kaunarta, ya mike cikin sauri yana mai matukar mamaki tare da tambayarta abin da ya sanyata wannan farin ciki. (Gimbiya Hasima ta ce dashi "Ya kyautu gareni na yi godiya ga Ubangijina Allah mabuwayi a bisa taimako da rahamarsa da ya saukar gareni, ta kwashe labarin abinda ya laruu gareta tsakanin matsafi Bahalu da jarumi Zuhairu, a bakin lambun da take zuwa ta sanar da mahaifinta. Ta ci gaba da cewaYa samu nasara akansa har sai da matsafi Bahalu ya gudu da kansa dan neman tsira, ya kuma dauki alkawarin taimakona da raba tsakanina da wannan shu'umin matsafi cikin yardar Allah. Sarki Shaiban ya yi matukar mamaki da al'ajabi na jin wannan labari, tare da yabon jarumta da bajintar jarumi Zuhairu, tare da farin cikin jin ccwar ya dauki alkawarin zai taimakawa yarsa Gimbiya Hasima ya rabata da wannan shu'umin matsafi,ya daga hannunsa ya yiwa Allah godiya, sannan ya juya ya dubi Gimbiya Hasima ya ce da ita. "Hakika Allah bai saukar da cuta ba har sai da ya saukar da maganinta, babu shakka na yi mafarki da zuwan wani jarumi mahayin doki a cikin mafarkin nawa na ga wannan jarumi vana yakar matsafi Bahalu har sai da ya hallaka shi ya kubutar da ke daga halin da ki ke ciki. Gashi ayanzu mafarkin nawa yana shirin Zama gaskiya. Lallai rahamar Ubangiji akan bayinsa tana da yawa, ya sake yin godiya ga Allah, sannan ya ce da Gimbiya Hasima. "Idan kin koma bakin wannan lambu da ki ke zuwa ki ka hadu da wannan jarumi ki ce masa ya zo birnin Bahazum ni sarki Shaiban ina son ganinsa. Gimbiya Hasima ta amsa masa da cewa za ta sanar da Zuhairu abin da ya umarceta sannan ta tashi ta koma cikin gida wajen mahaifiyarta. Shi kuwa Zuhairu da ya koma gida bai sanar da kowa abinda ya faru tsakaninsa da Gimbiya Hasima ba, ya ci gaba da harkokinsa kamar yadda ya saba. Washe gari da yamma ya sake yin shiri ya tafi bakin wannan lambu kamar yadda ya saba, yana zuwa ya sauka daga kan dokinsa ya daureshi sannan ya koma inda ya saba zama ya zauna. Bai dade da zama ba sai ya hangi Gimbiya Hasima tafe ta nufo inda yake, ya cika da mamakin ganinta ita kadai ba tare da kuyanginta ba, kamar yadda ya saba ganinta. Wani abu da ya kara bashi mamaki shi ne bai ganta akan doki ba, kuma ya san ba zai yiwu ta taho daga birninsu zuwa bakin wannan lambun da kafarta ba. Zuhairu ya ci gaba da dubanta har ta karaso inda yake tana mai yi masa murmushi, sai dai ya sake yin mamaki da ya ga bata yi masa sallama ba, kamar yadda yake a shari'ar Musuluci ga duk wanda ya zo ga dan uwansa Musulmi. Sai ya ji ta ci gaba da yi masa magana da cewa. "Zuciyata na cike da farin cikin sake ganinka masoyina, marhabin da 7uwanka abin. begena, cewa dai ni na kasance mai ni imtuwa da kaunarka a raina tamkar buguwar numfashi ga dukkan mai rai." Duk da Zuhairu ya ji murya tare da ganin surar mai yi masa magan tamkar ta Gimbiya Hasima, amma sai ya ji yana kokonton tabbatar da cewa ita ce, ya ci gaba da dubanta bai yi magana ba, zuciyarsa tana shakkar ace Gimbiya Hasima ce, ya ji a jikinsa cewa akwai yaudara a cikin lamarin don haka ya yi taika-tsantsan. Ta sake matsowa gareshi tana mai yi masa magana Cikin tattausar murya da cewa "Ya ya na ga ka yi shiru ba ka yi magana ba, kuma ka ki sakin jikinka da ni kamar kana cikin wani hali na damuwa." Ta kai hannu za ta taba jikinsa a sannan ne ya ii zoben da yake hannunsa ya yi motsi. alamar wani ma'abocin sihiri ne ya kusanceshi, cikin sauri ya mike daga inda yake zaune, ya zare takobin da take daure a damararsa ya dubeta ya ce da ita. Duk da jin murya da ganin sura irin ta Gimbiya Hasima ban yi imani da cewa ke ce Gimbiya Hasima ta gaskiya ba, don haka ki sanar dani wace ce ke kuma daga wane jinsi ki ka kasance, idan ba haka ba kuma na halakaki. Dan na ga akwai aikin sihiri irin na ma'abota shirka da bata a cikin lamairnki." alamar wani Matar nan dake tsaye a gabansa cikin surar Gimbiya Hasima ta dubeshi ta bushe da dariya sannan lokaci guda sai ta rikida daga wannan sura ta koma surarta ta asali wato Buniyatul Hajri kanwar matsafi Bahalu dake hallaka duk wanda ya ce yana kaunar Gimbiya Hasima. Ta sake dubansa ta ce da shi. Lallai ka yizurfi cikin begen Gimbiya Hasima yadda har ka ke iya ganc cewa ba ita ba ce koda an suffantu da irin surarta, da ni kake bege kamar yadda ka ke begenta a zuciyarka babu shakka da na yi farin cikin da babu wata halitta da ta taba yin kamarsa a duniya. Zai kyautu gareka ka cire kaunarta daga zuciyarka dan ita yar Sarki ce, mafi girman daraja daga 'ya'yan sarakunan duniya, ba za ta auri wanda ba dan sarki kamar ta ba. Zuhairu ya cc da ita "Ba zan so ki ba, ba zan aminta da maganarki ba, kuma babu shiriya tsakanina da duk wani mutum ma' abocin tsafi da sihiri a duk inda yake, ina ma sake jaddada nasiha gareki ki gaggauta tuba daga halin da ki ke ciki dan samun rahama, idan ba haka ba kuma ki nisanta da inda nake ko kuma na salwantar BAKAR GUGUWA littafi na daya 1 Na Marubuci Shehu Usman Muhd Typing by Shuraih Usman Part D da ruhinki da kaifin takobina." Buniyatu ta sake yin dariya sannan ta ce da shi "Mai ya haddasa irin wannan gaba da kiyayya tsakanina da kai maosyina? Me Gimbiya Hasima ta fi ni da ka ke matukar kaunarta har ka kasa amincewa ka so ni kamar yadda ka ke sonta." Zuhairu ya ce da ita "Shirka, tsafi da sihiri sune suka haddasa gaba da kiyayya tsakanina da ke. Kuma ba zan taba aminta da ke ba cikin wannan hali da ki ke ciki har abada, ita kuma Gimbiya Hasima ta fi ki da daraja ta addini da hasken Musulunci. Ta fi ki nasaba ta daukaka da daraja, sannan ke najasace a bar ki kasancewar kina halin bata da tabewa, kuma za ki zama mafi munin makoma idan ki ka mutu cikin halin da ki ke ciki a yanzu." Buniyatu ta fusata da jin maganar da ya fada, ta ce da shi "Hakika ka zama mai muzanci da tozarta matsayina akan wadda ka ke bege, na rantse da girman darajar abin da na gada na sirrin tsafi da sihirin mahaifina, ba don na yi alkawarin aurenka ba, kuma ba na so ka shiga halin darnuwa daizai sa ka halaka nima na rasaka ba, da sai na dauke Gimbiya Hasima na hallakar da ita yadda ba za ka sake ganinta ba, har abada. To amma ka sani na yi alkawarin aurenka ta kowane irin hali, kuma ko ba ka amince ba sai ka zamo miji a gare ni, har karshen rayuwarka, ba za ka auri Gimbiya Hasima ba, ka yi saurare da zuwan abin da zai faru garcka nan gaba a duk sanda na sake dawowa muka hadu." Tana gama fadar maganar a bace a fusace cikin alkaluman sihirinta. ba tarc da ta saurari abinda Zuhairu zai sake cewa ba, da Zuhairu ya ga Buniyatu ta tafi sai ya maida takobin sa sannan ya koma wajen da yake zama ya zauna yana tunanin abinda ta ce cikin kalamanta. Bayan tafiyar Buniyatu ba da dadewa ba, sai ga Gimbiya Hasima tare da kuyanginta sun iso bakin wannan lambu, da zuwansu ba su shiga ciki lambun ba kamar yadda ta saba sai Zuhairu ya ga sun tunkaro inda yake zaune, suna zuwa Gimbiya da kanta ta yi masa sallama Zuhairu ya amsa mata sannan ta ce dashi. "Na zo gare ka nc domin na sanar da kai sakon mahaifina sarki Shaiban ya ce na shaida maka ka zo yana son ganinka a bisa ga taimakon da ka yi min." Zuhairu ya dan yi shiru kamar yana tunani sannan ya cc da Gimbiya Hasima to, ya tashi ya je ya kama dokinsa ya hau, suka juya baki daya suka kama hanyar komawa birnin Bahazum, suna tafe suna hira har suka isa kofar shiga birnin. Tun daga

Chapter 2 of 4