Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT __ BAKAR GUGUWA littafi na daya 1 Na Marubuci Shehu Usman Muhd Typing by Shuraih Usman Part A posted by Shuraih 99% . Zuhairu yana tafe akan ingarman dokinsa cikin sassarfa da hanzari, ya nufn bakin wani makeken lambu ma'abocin ni'ima ta 'ya'yan it'atuwa furanni da koramu masu gudanarwa a cikinsa. Zuhairu jarumi ne na gasken gaske wanda jarumta da bajintarsa ta shahara a dukka nin fadin alkaryun dake kusa da brinin su, yana da karfin zuciya da rashin tsoro na ban mamaki. Shi kadai yakan fasa rundunar mahara da masu tare hanya suyi fatake masu tafiya a daji fashi. Al'addar Zuhairu ce yakan ziyarci bakin wannan lambu ako wane yammaci dan yaga wata 'yar sarki da ke zuwa lambun tare da kuyangunta ako wace rana. Tun daga ranar da ya fara ganinta cikin wasu ranaku da yake yawo a wannan waje, ya ji zuciyarsa takamu da tsananin begenta, irin wanda bazai musaltu ba, sai dai baisan makomar rayuwarsa ba. bisa ga kaunar da yake yiwa wannan 'yar sarki, kasancewarta mai girma da daraja daraja cikin man'yan 'ya'yan sarakunan duniya. ° Ya yi sani da cewa 'ya'yan sarakuna a wannan lokaci' basa auran wanda ba dan sarki kamar su ba. Ko kuma attajiri wanda dukiyarsa ta shahara. Shi kuma gashi ba d‘an sarki ba, dan haka ya kauda kai gabarin tunkararta ya bayyana mata abinda yake zuciyarsa, na daga begenta saboda girman matsayinta da ya wuce nasa. Sai dai yakan ziyarci bakin wannan lambu da take zuwa akowanne yammaci dan ya ganta. Da isarsa bakin wannan lambun ya sauka daga kan dokinsa ya kaishi gefe ya daure. sannan ya koma gindin wata itaciya dake fuskantar kofar lambun ya zauna ya dauko wata Sarewa ta azurfa da ya gada a wajen mahaifinsa ya Soma busawa cikin nishadi yana mai sauraran isowar wannan 'yar sarki dan ya ganta. Zuhairu yana zaune a wannan waje har rana ta kusa faduwa wannan yar sarki bata zoba, ransa ya baci saboda kewar rashin ganinta ya yi shiru yana tunani da sake-sake a ransa. Yana cikin wannan hali kamar daga sama sai yaji anyi masa magana dawata irin zazzakar murya mai sanyi daga ababan sauraro. Muryar tace dashi. "Da kazama mai yiwa zuciyarka adalci da babu shakka da ka rabu da begen wadda bata san kana begenta ba. Da ka rabu da tunanin wadda bata san kana tunaninta ba, da ka sauya lamarinka daga kuncin kaunar wadda baza ta soka ba, saboda girman matsayinta da ya wuce naka." Zuhairu ya dago kansa cikin sauri ya dubi inda ya ji muryar da ta yi masa magana amma baiga kowa ba, ya duba kowane bangare na daga inda yake baiga mai maganar ba. Muryar ta sake cewa da shi "kada ka damu ko kaji tsoro mai kaunarka ce take yin magana da ka, ko kana inkarin abinda na ambata na bayyana gare ka dan tabbatarwa." Zuhairu ya dubi inda ya kejin muryar ya ce "ldan kin kasance tare da alhairi ki bayyana gare ni don nasan wacece ke da kuma dalilin zuwanki gareni har ki kayi sani da halin da nake ciki da fadar Magana mafi munin ambato, 1dan kuma bakya tare da alhairi to kuwa ina mai neman tsari dake tare da rokon kinisanta dani ko waccce ke Zuhairu ya ji anyi dariya cikin tattausar murya. sannan muryar ta ce dashi "Zan kasance alhairi gareka tunda ina tare da dumbin kaunarka a zuciyata, dan haka zan bayyana gareka nasanar dakai koni wacece da kuma abinda ya kawoni gare ka kamar yadda ka ce." . Ana gama fadar maganar sai yaga wani farin haske ya bayyana a gabansa daga cikinn farin hasken sai ga wata mace ta bayyana kyakkyawar budurwa tana sanye da fararan tufafi hannunta rike da wani dan karamin gora abin zagayewa da gura ye da kambuna irin na aikin sihiri. Ta dubeshi tayi murmushi tare da juya fararan idanunta dan jan hankali. Zuhairu ya kare mata kallo sannan ya ce da ita "Wacece ke kuma meya kawoki gareni cikin wannan yanayi na aikin sihiri, ki sani cewa babu aminci tsakaniin Musulmi da duk wasu mushiriki ma'abota tsafi da sihiri, matukar basu tuba sunbi Allah ba." Kyakkyawar budurwan nan tayi dariya sannan ta ce da shi "Da dai kayi sani da irin martaba da daraja da take tattare da alkaluman sihiri, da kuwa kayi biyayya ga ma'abota mallakarsu dan kazamo daga cikinsu. Shine abin tunkaho da alfaharin mu dan a yanzu duniyar ma'abota sani na alkaluman sihiri ne keda tasiri akan komai." Ta sake yi masa murmushi irin na jan hankali sannan ta ci gaba da cewa "Suna na BUNIYATUL HAJARI BIN KAUWAS mahaifina shine shugaban bokaye da ma'abota aikin sihiri dake yammacin bimin SINAR. Ya rasu cikin wannan shekarar yana tsakiyar tafiya ba tare da wata rashin lafiya ko cuta ba, bayan rasuwar sane muka gaji sirrin tsafi da sihirinsa ni da yayana da ya rasu ya barmu a duniya, na gaji kashi daya cikin dari na alkaluman sihiri. Mahaifina yayana kuma ya gaji kashi casa'in da tara daga ciki. Dalilin zuwa na gareka kuwa shine na kasance mai bibiyar rayuwarka tun daga lokacin da na fara ganinka zaune a wannan waje kana busa sarewa, tun daga busar sarewar da kake yi mai sanyaya zuciya har wannan rana nakan ziyarci wannan waje dan na saurari zuciyata ta kamu da tsananin begenka. Sai dai bantaba bayyana gareka ka ganniba sai a yau, kuma na lura cewa zuciyarka ta kamu da kaunar wata 'yarsarki da take zuwa wannan lambu, dan haka na baiyyana gareka dan na raba tunaninka da begen wadda bata san kana begenta ba." Zuhairu ya fusata dajin wannan magana ya ce da ita "Da kinsan yadda nake tsananin gaba da kiyayyar mushirikai ma'abota tsafi da sihiri da ko kusa baki tunkari inda nake da bukatar na kaunace ki ba, kiyi alkawarin zaki musulunta dan samun cabo da kaucewa bata na aikin sihiri da kike aikatawa, ko kuma ki nisanta da inda nake. Idan ba haka ba kuwa na rantse da wanda raina yake hannunsa sai na halakaki da kisa mafi muni da azabar kaifin takobina." Buniyatu tayi dariya sannan ta ce da shi "Babu kiyayya ko gaba a tsakanina da kai masoyina, idan da ina gaba da kai zai zama mafi sauki gareni na halakaka ta hanyar karfin tsafi da sihirina." Ta daga kurtun sihirn da yake hannunta ta girgiza shi ta soma wasu irin surutai da sambatu irinna aikin sihiri nan take wuta takama daga kowace kusurwa hudu dake zagaye da Zuhairu. Sannan wutar ta taso kansa gadan-gadan zata konashi ya halaka Zuhairu yayi niyyar Kaucewa amma yaji ya kasa koda motsi daga inda yake kamar wanda kasa tarikeshi Wutar ta taso masa haikan zata koneshi ya halaka sai da ta kusa zuwa inda yake ya soma jin zafin da hucinta, sannan sai yaga wutar ta mutu ta kuma bace ya dena ganinta. Buniyatu ta sake bushewa da dariya sannan ta ce da shi "Wannan kadan kenan daga tasirin tsafi da sihirin da na gada a wajen mahaifina wanda zan iya halakaka dashi idan naso. Sai dai bani da nufin cutar da kai bare aje ga batun halakaka, saboda kaunar da nake yi maka. Kai dai kayi azama ga zurfafa tunani dan amincewa da kaunar mai kaunarka, zai zama mafi kyautuwa gareka ka ka amince da bukatata muyi aure. Wannan shine kudirina akanka kayi tunani akan maganar. Na barka lafiya." Tana gama ladar maganar sai yaga ta bace daga wajen ya dena ganinta. Sannan yaji shuru bata sake yin magana ba bare motsinta. Dan haka ya tabbatar da cewa ta tafi tabar wajan, da ganan ya tashi ya kama dokinsa ya hau ya nufi hanyar komawa gida. Da isar Zuhairu gida ya daure dokinsa ya tafi wajan kakansa MARWAN BIN HADIS wanda shi kadaine ya rage masa a duniya. lyayansa sun rasu tun yana karami, a hannun kakan nasa ya taso. Ya zauna kusa da shi ya gaisheshi sannan ya kwashe labarin abinda ya faru gareshi tsakaninsa da wannan shu'umar mace da suka hadu da ita a fitarsa ta wannan yammaci, ya sanar da shi. Dattijo Marwan ya cika da mamakin wannan labari sannan ya ce da Zuhairu "Babu shakka duniya ta kara kazanta da shu'uman mutane mushirikai ma'abota tsafi da sihiri a doron kasa." Ya tashi daga inda yakezaune ya nufi wata akwatin bakin Karfe dake karshan dakin ya bude, ya bincika kasan akwatin ya dauko wani zobe na azurfa ya dawo ya bawa Zuhairu sannan ya ce da shi "Ka sanya wannan Zoben a dan yatsanka cikin yardar Allah zai zama kariya gareka daga sharrin ma'abota tsafi da sihiri, babu wani aikin sihiri da zaiyi tasiri akanka kuma komai rintsi kada ka sake ka cireshi daga hannunka, a duk sanda wani matsafi ya tunkareka ko mai aikin sihiri zakaji zoben yayi mosti a hannunka koda kuwa baka ganinsa, haka kuma idan kaji dokinka yayi haniniya to ka lura akwai Wani abin cutarwa kusa da kai, dan shi yana ganin abinda kai baka gani, kuma kada kasake kashiga inda dokinka yayi gardamar shiga, haka kuma kada kaji tsoron duk abinda dokinka baiji tsoron ganinsa ba. Kada kamanta yawan addu'a aduk inda kake dan neman tsari da kariya daga wajan Ubangiji, ka kiyaye da abinda na sanar da kai." Zuhairu ya karbi zobe ya saka a hannunsa sannan ya yiwa kakansa dattijo Marwan godiya ya tashi ya fita Washe gari da yamma Zuhairu ya sake yin shiri ya kama dokinsa ya hau, ya nufi hanyar wannan lambu da Gimbiya Hasima take zuwa akowane yammaci dan ya ganta. Ya ci gaba da tafiya cikin sassarfa da hanzari har ya Soma hango bakin lambun da Gimbiya hasima take zuwa. Kafin ya karasa bakin lambun sai ya hangi wasu barada su kimanin arba'in sanye da kayan fada da makamai, sun zagaye wasu yammata sun kamasu sun dora akan dawakansu zasu tafi da su, yammatan suna kuka da kururuwar neman taimako amma babu wani wanda zai iya taimaka musu a wajen. Zuhairu ya saki linzamin dokinsa ya kara azama dan ya isa garesu yaga abinda yake faruwa da isarsa wajan sai yaga gimbiya Hasima ce tare da kuyangunta baradan nan suka kama zasu tafi da su. Zuhairu ya fusata da ganin wannan aikin zalinci ya dakawa baradan tsawa ya ce da su "Kai fajirai kaskantattu ma'abota zalunci da rashin imani, me kuke nufin aikatawa ga wadannan bayin Allah da ku ka "Kai kama." Baradan nan suka juyo suka dubi Zuhairu, da suka ga shi kadaine tsaye akan dokinsa sai suka bushe da dariya irinta mugunta da zalunci, sannan daya daga cikinsu ya bashi amsa da cewa " Babu shakka ajaline ya Kusanto da kai wannan waje, har kake tambayar abinda muke nufin aikatawa ga wadannan yammata, bari mu sanar da kai dan ya zama guzirinka na tafiya barzahu, zamu tafi da su ya zuwa ga shuwagabannin mu dan,su zama bayinmu bukatarmu dasu duk sanda mu kaga dama idan mungaji dasu ko kuma ansamu kata daga cikinsu tasamu ciki, sai mu sare kanta dan shayar da jininta ga ababan bautarmu, wannan shine makomarsu da abinda zamu aikata garesu masu yi mana hidima da biyan Idan mun tafi dasu." Zuhairu ya fusata dajin wannan magana ya ce da su "Kaicon rayuwarku da abinla kuke aikatawa mafi munin makoma na zalunci da rashin Imani. Kuma idan wannan shine kudirinku a rayuwa to kuwa zan halakaku da shafe ruhinku daga doron kasa dan kawar da wannan zalunci."... TOFA MUN FARO KENAN MASU SON LITTAFIN COMPLETE SAI SU DANNA HOTON KASANNAN https://youtu.be/YSYyhta02NI BAKAR GUGUWA littafi na daya 1 Na Marubuci Shehu Usman Muhd Typing by Shuraih Usman Part B post by Shuraih 99% . Baradan nan suka sake bushewa da dariya sannan daya daga cikinsu ya fita gaban Zuhairu ya tsaya yana sanye da sulke da kayan fada hannunsa rike da bakar takobi yayi huci ya daga takobin sama cikin karaji ya taso kan Zuhairu. ZUhairu ya zarce tasa takobin ya tare shi suka hadu, ta kubbansu suka yi karciya tartsatsin wuta ya tashi sama, zuhairu ya sake kai masa sara bardan ya goce kaifin takobinsa ya tafi ya zuwa wuyan dokinsa nan take ya sare wuyan dokin suka tafi suka fadi kasa gaba daya. Bardan nan ya mike a fusace kafin yayi wani yunkuri Zuhairu ya cimmasa ya sanya takobinsa ya yi masa saran karan tsaye nan take ya tsarge shi gida biyu duk da sulken karfe da yake jikinsa, ya zube kasa matace bai ko shura ba. Wani daga cikin baradan mai karfin zuciva ya sake zaburowa.cikin karajin fusata. Zuhairu ya tareshi da zamiya ta salon iya fada irin na zaratan sadaukai, ya kai masa wani gawurtaccen sara da karfin karar da ruhi, bardan nan ya sanya garkuwarsa ya kare, garkuwa ta kece gida biyu saboda tsananin karfin saran, kafafun dokin bardan na gaba suka durkushe dokin ya yi haniniya wadda ta hadu da hucin saran da Zuhairu ya sake kaiwa bardan ya sameshi a tirken wuya, nan take ya sare masa kai ya fadi kasa matacce Da gani haka sai ragowar baradan suka fusata suka sauke su gimbiya Hasima da kuyanginta daga kan dawakansu suka zare makamai, suka tasar ma Zuhairu baki daya cikin karaji da gunjin lusata. Shima Zuhairu ya karkata garesu ya taho suka hadu yana mai kai sara a tsakaninsu irinna karar da san sanin abokan gaba, baradan nan suka zagayeshi ta ko ina suka yi masa kawanya, amma duk inda Zuhairu ya keta sai dai kaga yana saransu suna zuba kasa matattu, haske takobinsa ya koma ja-jawur saboda keta jinin azzaluman baradan nan. Gaba daya wajan ya yamutse aka shiga artabu da bakin gumurzu wanda ya kawo salwantar rayukan barada masu dama. Da baradan an suka ga haka sai wasu daga cikinsu suka razana suka soma arcewa suna gudu dan sutsira da rayuwarsu saboda azaba masu karar kwana suka ja daga aka ci gaba da kafsawa har sai da Zuhairu ya karesu baki daya. Bayan Zuhairu ya gama da wadannan azzaluman barada ya tsaya akansu yaga babu sauran wani ma numfashi a cikinsu, sannan ya juya ga su gimbiya Hasima, ya hangeta tsaye agefe daga ita sai doguwar riga jikinta babu mayafi ya yi sauri ya sauko daga kan dokinsa ya dauki mayafi ta dake yashe a kasa ya tafi inda take ya mika mata. Gimbiya Hasima tasa hannu takarbi mayafin ta rufe jikinta da shi, bata ko yiwa Zuhairu magana ba barce godiya abisa taimakon da ya yi masu, sai ma ta kauda kai gabarin duban inda yake, ta tafi takama dokinta ta hau sauran kuyangunta suma suka kama nasu dawakan suka hau, ta kada linzamin dokinta suka kama hanyar komawa birnin Bahazum ba tare da ta sake duban inda yake ba bare tayi masa goriya. Wannan lamari ya kara karya Zucivar Zuhairu game da begen da yake yiwa gimbiya Hasima, ya duba duk da irin irin taimakon da ya yi mata bata ko yi masa magana ba bare godiya. A tunaninsa saboda girman matsayinta da ganin shi ba dan sarki bane yasa bata ko yi masa magana ba. Ya bisu da kallo har suka bace sannan ya kada kansa ya juya ya kama dokinsa ya hau, ya saki linzamin dokin ya fara tafiya. Kafin ya yi nisa da wajan sai yaji wata irin tsawa mai tsananin karfi da ban firgici tamkar faduwar aradu ta gauraye wajan, sararin samaniya ya yi duhu mafi tsanani daga yankin hudun dare kasa ta soma girgiza tana raurawa kamar zata tsage. Zuhairu da dokinsa su afka ciki, can daga nesa wata bakar guguwa tare da iska mai tsananin karfi suka keto daga bangaran yamma, guguwar tana tafe feshin wuta yana zuba daga cikinta, ta tafi wajan da ya halaka azzaluman baradan nan ta wuce ta kansu, gaba daya gawarwakin baradan suka kama da wuta suka kone kurmus hadda sauran dawakansu sa suke da rai duk suka hallaka. Zuhairu yaja linzamin dokinsa ya tsaya yana duban wannan abin al'ajabi da yake faruwa, ya ji zoben dake yatsansa ya yi motsi alamar wani ma'abocin aikin sihirin ne ya kusanceshi, ya duba kusa dashi baiga kowa ba, Kuma baiji dokinsa ya yi haniniya ba. Ya dubi cikin bakar guguwar nan na irin abinda yake faruwa, nan take ya tabbata cewa wannan ba komai bane face aikin tsafi da sihiri irin na ma'abota shirka. Wa'iyazubillah ya ce aransa yana mai neman tsari da wannan lamari. Sannan sai yaga wannan bakar guguwar ta taso ta nufo inda yake tsaye tana cigaba da feshin wuta, duk abinda ta wuce takansa tun daga itatuwa har civayi sai kaga ya kama da wuta ya kone kurmus. Da farko Zuhairu ya ji tsoro ya razana amma sai karfin zuciya da jarumta suka dawo masa saboda ganin dokinsa bai razana ba. Ya ci gaba da addu'a yana mai neman tsari da wannan aikin sihiri, guguwar tana zuwa kusa dashi sai yaga ta ratse tabi gefe bata bi ta inda ya ke ba ta nausa nayi gabas. Zuhairu ya bita da kallo har tabacewa ganinsa sannan ya saki kinzamin dokinsa ya ci gaba da tafiya. Akan hanyarsa ta komawa gida kafin ya isa garinsu yarika ganin gawarwakin baradan nan da suka arce suka guda asanda yake fafatawa dasu, bakar guguwar nan ta biyosu ta halakasu baki daya daga su har dawakansu sun kone kurmus. Zuhairu ya sake cika da matukar mamaki tare da neman tsari da irin wannan aikin sihiri. Ya wuce ya ci gaba da tafiya yana tunani da sake- sake aransa, babu shakka duk abinda ya faru na wannan aikin sihiri yana da nasaba da gimbiya Hasima sai dai. baiyi sani da dalilin faruwar hakan ba. Gashi dai duk baradan da suka kama su gimbiya Hasima da kuyanginta da nufin cutar da su sun hallaka hatta gawarwakin wanda ya halaka duk sun kone kurmus. Shi kadai ne da ya yi nufin taimakonta bai halaka ba. Yasan sarki Shanban bin Yasar musulmi ne kuma mai ilimin addini bazai yuwu ace daga shine yake aikata irin wannan shirka da sihiri ba. Yana cikin tafiya yana wannan tunani aransa, kalin ya isa garinsu sai ya hangi wani mahayi tafe akan doki ya fito daga garinsu zai kama hanyar tafiya birnin Bahazum. ya iso inda yake sai Zuhairu yaga ashe abokin sane MUZAFFAR dake tafiya birnin Bahazum dan yin fatauci, suka hadu suka gaisa Zuhairu ya yi nufin sanar dashi abinda ya laru gareshi., ko zai samu wani labari gamc da gimbiya Hasima 'yar sarki Shaiban bin Yasir da ya ke zuwa birnin Bahazum da mahaifinta yake sarauta yawan fatauci. Zuhairu ya ce da shi "Ya kautu gare ni in sanar da kai abinda yake faruwa gareni game da begen gimbiya Hasima 'yar sarki Shaiban binYasar da kake zuwa bimin Bahazum da mahaifinta yake sarauta danyin fatauci, wata kila ko kayi sani da abinda zaka labarta min game da ita." Ya kwashe labarin dukkanin abinda ya faru gareshi ya sanar da Muzaffar yana mai fadin cewa "Abinda ya bani mamaki shine duk irin taimakon da nayi mata bata ko yimin magana ba bare godiya, takama dokinta ta hau ta tafi, nayi zaton ko saboda girman matsayinta ne yasa bata yi min magana ba kasancewarta mafi girman daraja daga'ya'yan manyan sarakunan duniya. Ni kuma gani ba dan sarki ba kuma ba attajiri ba, dan haka zuciyata ta kacaya ga ainbatan kaunarta gareta. A bayan yafiyarta kuma naga wani abin mamaki da bar al'ajabi, wata bakar guguwa irinta aikin sihiri dake ci da wuta data halaka dukkanin baradan nan da suka tare gimbiya Hasima da nufin cutar da ita. Babu shakka duk abinda ya faru yana da nasaba da ita. Ina labarin wannan lamari. Muzaffar ya dubi Zuhairu da duba irin na mamaki da al'ajabi sannan ya ce da shi "Kaicon 1ashin sani dake sanya zuciya afkawa a bcgen wadda ajali yakan kusanta ga duk wanda ya amabata yana kaunarta, na san baka da masaniyar abinda yake laruwa game da gimbiya Hasima shiya sa har ka ambata kana kaunarta, amma labari ya Ishe duk wanda yake da masaniyar maganar cewa, wani hamshakin matsafine daga cikin manyan Inatsafa ma'abota aikin sihiri dake yamma cin birnin SINAR ya ke kaunarta. Kuma ya sha alwashin auranta kota wanc irin hali dan haka yake halaka duk wanda ya ce yana kaunarta, duk da ita tace bazata auri mushiriki ma'abocin tsafi da sihiri ba, 'ya'yan sarakuna da dama tare da manyan attajirai masu yawa sun hallak akan neman aurcta, kuma wannan matsafi shine ya halakasu." A yanzu gimbiya Hasima ta zama tamkar hanyar kusantar ajali ga duk wanda ya ce yana kaunarta, hasalima babu wani namiji da ya isa tunkararta bare ya yi mata magana matukar ba mahaifinta har sai wannan matsafi ya halakashi, shi yasa zaka ga a duk inda za taje babu wani namiji mai yimata rakiya daga cikin baradan mahaifinta daga ita sai kuyangunta mata take tafiya, kuma duk abinda ya faru akan wanna barada na aikin sihiri suka halaka wannan matsafinne ya halakasu. Kaima saboda ilyar tamaka mata kayi shiyasa bai halaka ka ba. Wannan shinc dalilin da yasa gimbiya Hasima bata yi maka magana ba bare godiya a sanda ka taimaketa, babu shakka da ta budi baki ta yi maka magana da kuwa wannan shu'umin matsafi ya

Chapter 1 of 4