Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
iya ba Gumi ne yake keto mata salati kawai take yi wani irin ne shine taji yazo mata sake kenkeme Nabil tayi gem Hadim sai yanzu ta tsorata dan bata taba ganin haifuwa ba azaton ta fitan raine ganin yanda Fandau take yun kuri cikin karfi Abin ya bata tsoro tace "Nabil idan ta mutu yaza muyi Tafa de haka tana cikin riki cewa Shiko Nabil yanda Fandau da danke shi ko halin magana ba shida shi balle yayi yunkurin ta shi Shikan sa gumi ne yake keto masa duk addua da yazo bakin shi yake tofa mata Cikin sa a Wani yunkurin tayi da karfi sai gawata sun guceci y'a ta fado dama yau riga da zani tasa zanin dama ya dade da kuncewa sai ciket din ta na ciki ajiyan zuciya ta sauke ta saki Nabil Shima jahota yayi jikin sa ganin yanda take sauke ajiyan zuciya ya rungume ta gyam yana sakin ajiyan zuciya bai masan me aka haifa ba Sai jiyayi Hadim tana tace"kutuma macce macen ma baka me kamar ki kika haifa mana Nabil Yace "alhamdulilah alhamdulilah sai faman shafa kan Fandau yake yace "yanzu ina ne yake miki ciwo sai a sannan Fandau ta bude ido tace ruwa zan sha da sauri Nabil ya saketa yayi hanyan kitchen yana zuwa ya bude fridge ya dauko roban ruwa ya daga kanta yaba ta kurba daya tayi ta tuno da mejego bata shan ruwan sanyi asanin ta ta zare bakin ta tace na zafi nake so Ya juya zai hanyan kitchen Hadim da take ta faman fadan anhafi macce kuma baka amma kuma ta daga yar ta daura ta a cinyar ta na goge bata furka Tace "Nabil kaga macce ta haifa fa Yace "good mekyun kenan Tasake cewa "amma fa tafita kyu zo kagan ta Yace ina zuwa Hadim Zanin Fandau da yake cikin jine Hadim ta jawo ta kwan tar da yar ta nufi lokan gadon fandau inda dama ta tana di almaka shin ta zare duk takawo part din ta ajiye ta dauko ta seta yatsanta kamar yanda aka mata bayan yankan cibiya ta yanke ta daure ta dauko wani zanin a whardrob din Fandau ta nade yar dai dai lokacin Nabil yafito da cup ahannun ya tashi Fandau ya bata Hadim ta kalle shi ta bata rai tace wai Nabil mehaka ruwan ma sai kai zaka bata Cikin tsawa tace keee kalle ni idan zaki ware maki ware ki temaki kanki dan mu muna fita adakin nan ba kara shigo miki zamu yiba sai munje mun dawo kafin nan kin gama jegon dan muna zuwa zamu daura daga inda muka tsaya kin haihowa mijina abin da yake so macce ni namiji nake so dan haka baki kubuta ba da namijin kika haifane ma wata kila shi ya hakura mu sallame ki inkinga mun barki to kin haifi namjiji Amma abin da zan gaya miki ki temaki kanki kicire ragonci ki kasa jikin ki da ruwan dimi dan inda wanan sun kucece yar ta fito ba karamin budewa yayi ba Inba haka ba kirube Wllh tana gama fadan haka ta dauki zanin Fandau da yake cikin jini ta daura ajikin ta cire siket din ta ta zauna dabar acikin jinen da kazan tar haifuwan ta na Goggo ga cinyar ta take tayi jagab kamar ita ta haihu ta meke ta kalle Nabil tace "zomu tafi Mu nunawa yasmin ko Nabil ya kalle Fandau da kanta yake sunkuye tana zaune cikin jinin har yanzu yakalli Hadim data rungumi jaririiya tana jiran sufita Yace"haba yaza mufita mutar ta cikin wannan hali mu temaka mata da koda gyaran wajen ne mana yamutsa fuska Hadim tayi tace wllh bazan iya ba zuciya ta bakaga yanda yake tashi ba ko wannan tsayuwan karfin hali nake Gazanin ta dana daura dan yazama sheda awajen yasmin da ma aikatan gidan nan ya dameni da wani irin garni sona ke muje na kunce zuciya ta sai haurowa yake Nabil yace " toki tsaya ni zan gyara daukan Fandau yayi yayi hanyan bathroom da ita wani kishine ya kama Hadim cikin tsawa tace "my star a gabana kake daukan wata Yajuyo ya mata wani irin kallo yace "meyasa wani lokaci imanin ki bashida yawane idan ban dauke taba kina ga zata iya tafiya ne aga ban idon ki taci wannan a zaban Itama cikin bacin rai da kishin yanda Fandau tayi wani lif ajikin Mijin ta Tace"to meye wani a zaba a haihuwar macce macce fa ta haifa Nabil wani kallo ya mata yace "in fisari kayan ragone kaza ma tayi mana yana fadan haka ya shige da Fandau bathroom ya sauketa abakin bathtub ya hada mata ruwan wanka me dimin ya sata yace "zaki iya yin wankan ko gyada masa kai tayi Yace yawwa kidin ga kula da kanki dan mu ayau zamu tafi dan su ummi dama basu so Hadim ta haihu a nan ba sai cewa mukayi doctor yace ba ason tayi zaman jirgi cikin zai iya samun matsala dan haka muka musu alkawarin aranan da ta haihu aranan zamu taho dan haka ki kula da kanki kinji abin da tace ai zaki iya rubewa dan ki kula nima ina kaisu zan dawo cikin kwana ukku nan zaki ganni Bata ce komai ba shikuma har yaje bakin kofa ya sake dawowa yarugume Fandau yace "wllh ko ban zauna da keba kina da mushin manci arayuwa ta daga nan har karshen ta Kin bani abu biyu arawuwa wanda bazan taba mantawa da shiba *Budurcinki* Dakuma *Y'ata ta fari* Kissing din lips dinta yayi yace "ke ta musamman ce Ita ko Hadim Nabil yana gaya mata wannan maganan tayi tsororo a tsaya ta bisa da kallo tana mai maita _idan fisari kayan ragone kaza ma tayi mana_ Idan ta fashince shi gatse ya mata ne ko gori yanzu ni Hadim har nayi saken da Nabil zai gaya min wannan maganan kuma yasa hannun sa agaba na yadauki macce wanda ni bai taba dauka naba koda bani da lafiya sai yace nayi girma Me hakan ke nufi Kwaban zuciyar ta tayin da cewa tausayin ta yaji ganin ta wahala ita ma kan ta lokacin da Fandau take cikin nakudan ta tausa ya mata balle Nabil sarkin tausayi Kukan baby ne yadawo da ita haiyacin ta tayi saurin kijjigata Alokacin Nabil yafito ko kallon inda jaririiya da Hadim bai yiba yafara gyara wajen Hadim cikin mamaki take binsa da kallo yau *shidmas* guda da sa hannu cikin jine yana aiki tukuru tas ya goge wajen yashiga yafita yana cikin wanke kayan jinen ne yaju ya yakalli Fandau da take ta faman gasa jikin ta da towel sai da ya gama wanke komai na kayan da ta haifu mabiya kuwa dakyar yasa mu yayi fishing din sa Ya karasa inda take yace "wankan ya isa haka kodan kin wahalu fa ba keba ai koni sai nayi wankan sati ina ga wannan matsa da akamin Duk jikina ciwo yakeyi a tare suka fito yasa mu Hadim tacika fam Sai faman jijiga jaririiya take abakin gado fandau da zauna shikuma yayi hanyan kitchen Tace ina kuma zaka sake Komawa Bai kalle taba yace" zan hada mata tea me kaurine Aiko Hadim tasake cika cikin fusata tace wai me kake nufine Ko juyowa bai yiba ya wuce kitchen Bayan yaka wowa Fandau tea din yabata karba tayi ta fara sha Yaka rasa wajen Hadim da bakomai cikin idon ta sai tsabar bala i Yasan idan bai yin lallami ba sauki dafa ta yayi yace maman baby girl ya akayi ne muga yartaki kinwani kan kame ta dan rowa Bata rai Hadim tayi Tace"Nabil kasan me kayi kuwa Cikin salon sa na yaudara yace "menayi? Tace"baka ma san me kayi ba a gabana fa kake tattalin wata macce Yace ba tattalin ta nayi ba kinsan ance dan tuwon gobe ake wanne tukunya Duk magan ganun su cikin kunne Fandau dan bawani nesa suke ba hima kansa yana fadan haka yaji wani iri azuciyar sa yace Allah yasa bata ji ba amma yana juyawa ya ga idon ta da hankalin ta duk akan su da gani yanayin kallon da Take musu taji komai Hadim tace "aisai kai karbi yar karike yasa hannun yakarbi yar ita kuma Hadim jagaf jagaf da jine ajiki ta fara ta fiya wanda baisa nima zaice haifuwan gaske yi Dariya yakama Nabil daya tuno lokacin da hadim ta zage ta na ta shafa kazan tan haiwuwa ajikin ta Ga zanin Fandau Daga nan suka fito Hadim tana takawa Ahankali sai wani cicci je baki take Aiko kamar yanda suka zata a man falon ko suka samu Yasmin tana kallo Ai tana hango su dagudu tayi inda suke aunty karde haifuwa kikayi ne ina tan take tayi kan ai tama manta dawani tsoron Nabil da suke yi wanda ko waje yaje tofa basa zama awajen dan shi ko kamal wanda yabiyo bayan sa soron sa yake Kai har yayinsa mata su zainab wada suke uba daya suna tsoron sa dan Iya uwar gida maman su zainab cewa take kar karaga musu ai kaine babba tunda kaine namiji amma sai ga yasmin taca muko ya baby ha hannun sa tana tace "memuka samu mugani meka mata yayi Yajuyo yana yiwa hadim sannu harda riketa kamar wanda ita tayi nakudan Yasmin tace lahhhhh anty kin haifi me kama da Kala wllh suna kama da kala Hadim sake kallon jaririya ta tana murmushi dan mata so yariyar tayi baki ma amma taji dadi da aka dan ganta tada Kala Kala kanwar Nabil ce uba daya ita ma yar gakin iYa ce Wow amma fa hancin ta irin na yashid dakum.. ... Hararan ta Nabil yayi tayi gum da bakin ta Tabi bayan su suka haye sama Toilet hadim ta wuce ta tayi saurin yin jifa da zanin duk jikin ta karni yake wani irin amai ne taji yana taso mata wanka tayi yafi so 5 turare kam bawan da ba ta fesa ba tafito daure da towel bata ga Nabil ba dan tasan yaje daya dakin wanka ne yanda jikin sa ya baci Yasmin ce da waya ahannu sai kolotun ihu ta ke takira wannan idan tafa da ko amsa bata sayawa ji zata kashe takira wani Hadim ce tazo ta zauna abakin gadon yasimin tace"aunty kin ganki uwa ras kaman bake kika haifu ba Amma ANTY tare kuka haifu da yashid ko yanda naga duk jikin sa jine har yafiki baci Gaban hadim ne yafadi ras tace ban gane kamar bani na haifuba Yasmin tace "wllh anty fuskan ki tayau kamar baki sha wahalan nakuda ba sai tafiyan ki da ya canza kawai anty Hadim tace"yasmin kinada yawan shirme a maganan ki mekomin wayata naki ra Habiba da su faridan Amjad Suzo suga baby dan yanzu zamu wuce Kita shi ki hada mana kayan mu Yasmin tace "yawwa anty ina siyayyan kayan baby da mukayi kinga kamar nida yashid munsan macce zaki haifa muka dinga iban kayan baby girl keko kikayi ta jidan na baby boy Wai ina suke ma wllh akwai wani mekyu dama na nace idan macce ce shi za afara sa mata Hadim tace "inaga fa anwuce da shi 9ja dan kayan da muka bari anan ba yawa duk mun aika anty yanzu wazai mata wanka Hadim tace "bana jin za ayima ta wanka anan sai munje gida dan awai wasu abubuwan da ake yiwa diya macce a wankan fari a al adan muna shuwa Yasmin tace "shuwa iyayen.... Keee bani man zaitun da auduga na goge mata jiki dashi tana maganan tana kiran wayan Habiba babbar amini yar ta Aiko habiba cikin ihu itama da murna ta kaye waya kawayenta zallah nanan London take kira dan su zo suka baby kafin suta fi tana ganin kitan yangida amma bata dau ka Tafijin kawayen baye idan ta tuna kyutan da kungiya su tayi akan abin da a ka Haifa baki yaki rufuwa Nabil kwance cikin Bathtub yayi shiru nunani yakeyi wai dama haka nakuda da haihu yake da azaba Lalle annabi yayi gaskiya da yace abi uwa uwa uwa ummattii Akwai wani hassari da akayin agaban sa ankayi ta mutuwa da raunuka manya harda wanda kafansa ya fille yabar gan gan jikin sa amma mai ga yashiga halin da Fandau tashiga ba Anya yayiwa uwar Fandau a dalci da yara bata da yarta gashi ita ma Fandau din zai rabata da yar ta Yar fa nima tawa yar ta girma a mata haka Tsaki yayi afili yace aine y'ata tafi karfin haka yata Wllh ina ma wani zai ganta tana yawo a kafa balle ya yaudareta kofilin wasa zan shiga aisai na hada ta da body gard sannan baza tayi Rayuwar Nigeria ba Da wannan karfin guiwan yafara gasa jikin sa da yake masa ciwo baye kafadun sa inda nan Fandau tafi matsewa Sun samu rakiyan dinben mutane wada yafi na da zuwa airport doctor Muktar ko kin zuwa yayi dan yaji mugun haushi da wai Hadim haifuwan gida tayi kuma bayan hakama yayi yayi subari aduba lafiyan ta amma sunki shiya fijiye mata ma karuwa dan yar da girman ta Haka agidan ma Hadim kin yarda tayi kowa ya bata wanka sai fada suke da mamar ta sai tace ita zata iya ai ita ba yarinyar bace ummin Nabil ma tasa baki tace Hadim kibari a koya miki abubuwan kinga haifuwan farine Ai ita kanta ummi ce mata tayi ita fa bame kanin siraicin ta dan bakyu wani yaga siraicin wani _Niko nace keko kika gama ganin na Fandau_ _a he kinsan da haka_ Haka suka rabu da ita ga hade haden na shuwa ba kadan ba amma haka suka bata ta shiga dashi idan na tsugun none zata zuba tana gani zai gama hayakin sa yagama idan na wanka ne ko wanke wajen tayi floshing dinsu da wayan ta ma take shiga tayi zaman ta tana chatting dinta da kawayen ta akan baby Nabil ya sake sunkurar da kai a gaban Maman Fandau yace"yauwa mama idan macce ta haifu me dame ya ka mata abata Mama tace kowani irin abinci ne inde megina jikine da kuma wanda zai sa ruwan nono ya gudano zata iya ci Shiru Nabil yayi dan yagane mama bata gane meya ke nufiba yanda yaga anayiwa Hadim shidema ya tabbatar idan macce ta haifu ba abarinta haka dan yaji su ummi sunayiwa Hadim fada ta dage da abinda zai gyarata Dan haka ya yir yawa kansa tafiya London a gobe in yaso ya dawo kafin suna Sunkurar da kai yayi cikin kunya yace "ina nufun wada zai gyara mata jiki Mama murmushi tayi tace "inban da abin ka Malam k'arami ai shuwa sun san irin wanan abubuwan ai Sake sunkuyar da kai Nabil yayi Yace"basu bata ba ita kuma tace naki take so Murmushi mama tasake yi tace Allah sarki Halima y'ata wllh nima ina sonta tana da kirki da iya gimama mutum insha ALLAH gobe idan zanje duba yar jikalle zankai mata Nabil yace "Mama ai kunyan ki take ji ni zaki bawa na kai mata ko kinje kar kimata zance ta ce kunya ta keji Mama tace"shikenan idan naba da antsayo abubuwan sai nakira ka awayan ko yace to" mungode mama tace rufe min baki har kai zaka bude baki kace zaka min godeya akan wani kan kanin abu Nabil dubi yanda ka mayar ni kamar nina yi cikin ka da haifuwan ka bangare na ya ban ban da dana kishiyoyi na dubi yanda ka ajiyenin komai na rayuwa kullum sai kakira ne mun gaisa ga yaron dakin ka kullum sai kace yazo yaduba abinda nake bukata amma abin da nake soda kai sauran matan ma kana musu baka gafa yanda ban isa fitowa tsakar gida ba za afara min gorin na shanye zubiyar ka har taka nas suka je gidan ku suka gayawa Hjjy hajara dan ma ita bane daukan irinwanan bane sai tace musu haka halin danta yake da kyuta suyi hakuri ran da yajiyo kuma zai muku kaga duk suma kana musun amma Gaskiya bai kai nawa ba, ni kaina ina mamakin yanda kake nuna ban ban ci a tsaka nen mu kaga dole su zargi wani abu, Shidi man nawan ne yafina su dan haka nake neman alfar ma wajen ka kana mana komai dai dai Nabil ransa ne yabaci yadade dagano matan nan basa son mama shiya sa ma yake jin haushin su yake kuma nuna ban dancin amma idan ba haka ba shi kishiyar uwar sa ma amatsayin Uwa yadauke ta bai taba ban ban ta iya da ummi ba Yayi kwafa badan mama tace alfarma tane maba da abin da ya saba musun ma de nawa zai yi dan shi a rayuwan sa ya tsani mutum me hassada Yameke yana cewa to shikenan mama Hada komai kafin na dawo agidan ABBA musa sai nabiyo ba karba dan ni gobe fitan asuba zanyi Har kofan babban falon ta tara kosa tayi saurin komawa kafin afara yada mata mgn dan tana jin muryoyin mutan gidan Yanzu dan Allah baza suma ka alfarman wasan nan daya ba abari idan anyi suna katafi zaka tafi ka barmu duk yanda kake son babyn ka Nabil da yake wasa da baby yace"baby wai kinji Momin ki tana hanawa naje nema muku kudi bayan da mun nemi na banza ma balle yanzu gaku masu bukata kun fara zuwa Dariya tayi tace" wai kai yanzu meyasa baka fiye son mgn dani ba komai sai kagayawa baby shima dariya yayi yace ai ke komai na fada sai kinmin musu ita ko bata yimin komai nayi tana so Dariya ta sake yi tace "amma Wllh ABBAn fujjirat zaka haukace Yaci ro wayan sa yana daukan baby da su kansa ma Hadim tace "yanzu idan katafi saifa ran gobe suna yace "eh Kamal da Girema zasu yikomai da kuke buka ta Nima da baki zanzo Hadim cikin zunudi tace har da su Sir ko dan da alkawarin mu zai zo nabil yace "eh mana ni abubuwan su ma mamaki yake bani baki ga yanda suke zumudi babyn nan ba, Yanzu haka Duk sunce sai sunjo da yawan suma basu taba sanin ida Nigeria yake ba Fandau suna fita ta sauke cup din abakin ta kala man Nabil yana mata daci wai _dan tuwon gobe ake wanke tukunya_ Kuka ne ya kwace mata wane irin Duniya take cikine meyake faruwa da ita kamar a farki amma yaki karewa Afili tace sakai yar mama banga komai ba ma inde wanan azaban nakudan mama ta sha nazo Duniya na gujeta to banga komai ba Gashi nan tun ba ayi nisa ba Allah ya fara saka mata naguje ta nema gashi nan an raba ni da abin da na haifa wanda ko ganinta banyi ba baza ta masan ne na haifeta ba amma ALLAH kai kasan manufa ta akan haka banyi dan na kuntata mama ba nayine dan zuwa gaba musa mu yanci na mema mata jin dadi na har abada ahe ni kuskure nayi bansa niba, dan yanzu nasan dacin rabuwa da d'a nima da ba shakuwa nayi da ita ba ba wahalan renon ta nayiba naji d'acin rabuwa da ita balle mama yata ji da ta rasani ALLAH kayafeni Haka Fandau tayi tashiga ruwan zafi tayi kokarin da cikin kwana ukku ba kace ita ta haifi wannan yar ba ga abinci wanda taga dama zata tafa taci tacika cikin ta daruwan tea mezafi sosai wani lokacin yana kona ta har kuka take amma sabar wayo irin na Fandau tasan shine kadai magani awajen ta dan haka bata wasa dan yaran kanuri bade sani ciwon kai Yarinya karama amma za kaga tasan komai Yasmin kwance acinya uwar ta inna ZAINABU uwar danja kenan inji Hadim Tace"inna nifa naga abubuwan mamaki a haifuwan nan na Aunty ciki kamar na aljanu wataran ya girma wataran yazama kara mi kai wata ran ma babu zan gani dan nasha kamata ba cikin abin da yafi ban mamaki saman sakiya tun rar da muka je suka hanani shiga wai da aljanu basa son bako amma su kullum sai sunyi ta shiga tunba ma yashid ko anty tayi Baccci haka sai yashiga ko idan anty ta tafi anguwa sai ya shika kuma ya dade idan su biyu ne kuma ba sosai suke jimawa ba Amma abinda yafibani mamaki asaman anty ta haifu Kuma ai idan macce ta haifu bata sallah meyasa ita anty naka tayi sallah ranan da ta haifu Inna da abin dubawa fa awannan haifuwan nasu da kinga shikara da shekaru suna neman haifuwan ba ayita ba sai da kikace tunda baza ta haifu ba zaki sashi yayi aure sannan aka samu ciki nede jikina yana bani akwai wani abu tabbasas kuma hak.... ... Wani irin tsawa inna ZAINABU ta....... *Tofa nima nayar da* *Da maganan Hadim *yasmin dinnan muguwar yar sa ido ce* _B JATTKO_ DAMA TA NA BATUL ADAM JATTKO GODIYA TA MUSAMMAN GA WADANDA SUKA KIRANI DA WANDA SUKAYIMIN TA'AZIYYA THOUGH ONLINE NAGODE NAGODE ALLAH YABARMU DA SOYYAYAR JUNA, ANA TAREšŸ¤ 30 Tace ashe yasmin bakida hankali, wanne irin maganane wannan din? Daza kice kinada shakku akan haihuwarta kodazu danaje gidan tana bawa 'yarta nono, yasmin tace "Allah inna kiyarda maganata kinsan yanda akayi aka samu ruwan nonon ne shinema yakara sakamin shakku don likita dinda take cikin jirgin takira tace yau kwananta 3 da haihuwa amma haryanzu ruwan nono bai sauko mata ba matar sai tace mata meye dalili sai takalleni tacemin inkoma gurin zamana toh day anan bansan ya akayi ba sai naga tana bawa 'yar nono sai inna zainab tayi shuru cande sai tace wasu daman ruwan nono baya sauko musu dawuri balle ita da kikace randa tahaihu nema, Tasake sai tace "toh inna meyasa tace kwananta 3 da haihuwa Inna ZAINABU cikin fada takoreta agurin tacemata kedan Allah kitashi kibani guri banason surkullen zance ni bana daukan magananda bashida ma'ana kinsan halina sarai yasmin de tatashi tana zumbure zumburen baki Nabil tsugunne gaban mama tana fada masa yanda za'ayi amfani da magungunan shiko dayaga bazai iyaba kawai sai yaciro pen yake rubutawa tana masa bayani a tsinake idan yarubuta sai yajefa acikin ledan ahaka tagamama sa bayayin yatashi ya bata salama Hadim ko ajikin ta da Nabil zaitafi dan tasan Fandau tana jego Kuma ma ita haryanzu bata wani dauki fandau din da mushin manci sosai ba Fandau ta shafa nonowan ta da sukayin hulu hulu dan cikan ruwa acikin yau kwannan ta 4 da haifuwa amma ciwon ta keji agaban ta yanzu ta dena Yanzu cikan nonon ne kawai yake

Chapter 17 of 39