Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
nan sukazo wuccewa ta wani lungu Aifa sae sukaga Lanta da yakubu saurayinta suna iskanci. Kasan cewar Sam mutane basu damu da sama lungun idoba shiyasa har za'ayi abu alungun agama mutane basu ankare Ba Yakubu yadanne lantana yata iskanci da ita. Nafisa tace lantana me yakubu yake miki Nan suka tsaya da jan kaya Lantana tace bansani Kuma wlhi kika fa'da sainaci ubanki kema Fatsima kifa'da kisani. Fatsima tace saina fa'da 'din aini ba Nafisa bace nasan abunda kukeyi itace bata saniba Tace to kifa'da inci uwarki Tace kici uwarki Larai dae Taja hannun Nafisa sukabar gun Nafisat tace iskaci sukeyiko Tace eh man Nafisa tayi mamakin ganin 'dakin babanta fes tatan baye shi yagaya mata komae Nan tahau murna Su hassana da mairo ma suna santin 'dakin amma baba larai cewa tayi bazata shiga 'dakinba Dan 'danshan jinine Amar Nafisa tace jikokin me garine fah Babah Babanta yace shareta Nafisa Larai tace eh tasherenin sae me kwa'dayayye kawae yace nine kwaa'dayayye tace kai'dinfa yace Lalle rashin mutunci nake yakai inda yakai Tace har ya hucce Yace wlhi Larai kikiyayi ranar dazan tashi Tace ai'in Allah yayarda bazaka tashiba haka zaka qare rayuwarka Bae kulata ba Dan kallan mahau kaciya yake mata Nafisa tace kayi hakuri baba yace Ba komae kidae kidinga min Addu'ar Allah yabani lpy tace to Allah...... Bata qarasaba taji am maka duka da takalmi abayanta. Qara tasake tare da miqewa agigice Baba Larai CE Tace harda cewa yayi hakuri yarinya dake kin'iya makirki Tace kiyi hakuri Tace zoki 'dau cincin kifita Nan ta'dauka tafita tana kuka =ؗ=ؓ=ؗ Washe gari Su MARWAN sun gama shirinsu natafiya Amar yace kakale baqo zaiyi halinsa tace wlhi bansan rabuwa daku Yace to ya za'ayi dolene ai Kinga ana leman yah MARWAN gun aiki. Nikuma karatu Tace to kugae damin da kowa. Naha'dama Momyn taku kayanta suna mota Amar yace kae matarnan yanzu zaki cikamana ciki da warin daddawa Tace eh jiyama kacita ai yace inani inacin daddawa Nan suka rabo cikin jin da'di Akan hanyar sune Amar yayi parking kofar gidansu Nafisa MARWAN yace lpy. Yace kayi hakuri mushiga gidan kugaisa da baban nata tunda yanemi alfarmar hakan Baice komae ba yafito daga mortar Amar ya kunkusa kofar gida. Nafisa na wanke wanke baba Larai tace ke jeki duba kiga waye Tace to. Ganin datayi Su MARWAN ne shiyasa koma da gidu cikin gidan MARWAN yakalli Amar shima yakalle shi Yace tunda takoma sae mushiga mutafi ko Amar yace ila taje gayama.... Bae qarasaba sae gata Tace ina kwananku Amar ne ya am'sa Yace kinfito kuma kinkoma da gudu tace Naje gayama babane kunzo Yace kushigo. Nan suka shiga Taje taci gaba da wanke wankenta Baba Larai bata guduba wannan karan ba amma ta la6e kofar 'dakin tana sanjin me za'a fa'da Baba ya musu sannu da zuwa Suka gaida shi. Yace nagode sosae da temakwanku garuni da 'diyata MARWAN yace bakomae Amar yace dama zamu koma gidane yanzu yace ayya kano ko yace eh Yace yanzu ku yaran Abdallane suka eh Yace ikwan Allah Allah ya albarkaci rayuwarku Ameen MARWAN yace Baba yace yanzu yaushe zaku da'da dawowa Amar yace ai sae kunganmu kawae Yace Allah yasa muqara ganin juna sukace Ameen Baba ya tsaida kallanshi akan Amar yace dama inasan rokwan alfarma agunka. Yace to inaji. Yace inbazan takura kaba inasan ka Auri Nafisa dan tunda naganka naji kashiga raina kae da 'dan uwanka. Nasan Kaine zaka riqe Nafisa amana =ؗ=ؓ=ؗ 'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI=ؗ=ؓ=ؗ Tarine Yakama Amar bai shiryaba yayi saurin kallan MARWAN yaga yana murmushi alamar irin yashiga annu Murmushi shimah yayi yace ai baba ya MARWAN yarigani shine yakesan Nafisa yanzuma munzo wajankane da magana Tab.... MARWAN yace azuciyarsa amma Sam bae yarda ya'dago kansaba Da murna baba yace ato aishi kenan wlhi nabaka Nafisa halak malak Idan naji sauqi zanje gun megari da kaina Amar yace basae kasha wahalaba zasuzo da Kansu Yace to Allah ya kawosu Yace Ameen Nan Amar yace to zamutafi Yace to Allah ya kiyaye hanya Ya ajiyemae ku'di yana cewa kakula da shan maganin insha Allah zaka miqe Yace to nagode sosae Allah yayi albarka Yace amin MARWAN yayi mamakin yanda dazasu fita yabi Nafisa dakallo Itama tayi mamaki Amar yayaficuta da hannu Nan tsame hannunta Tabiyosu Kuda tafito wajan tuni MARWAN yashige Mota. Amar yace zamutafi tace shikenan bazan qara ganinkuba Yace aikinzama tamu tace meyasa kace haka Yace haka kawae Tace to yanzu yaushe zaku dawo yace ila In baba yagama yagama shan Magani Tace to Allah yakiyaye Taleqa cikin mutar tace ya MARWAN Allah yakiyaye Da Saudi Amar yajata Dan yasan ka'dan da aikin MARWAN ya falleta da mari Dan yacika yayi fam qiris yake jira ya fashe yace munyi latti Nafisa Tace to ai banyi sallamah da ya MARWAN Ba yace kunyi saikin gamu yafa'da yanamae shigewa motar yafigeta Tabi motar da kallo Allah yasani bataso tafiyansu Ba. Gashi taso MARWAN yayi mata magana dan tanajin da'din muryar shi sosae Sam amota MARWAN bae kula Amar Ba Todama Amar 'din yasan bazae kulashi Ba amma yana tsoran shurunsa Sun isa gida lpy lau Suka samu Momy da dady suna hira afalo zainab na game a laptop Da gudu tazo tataresu tana cewa oyoyo ya MARWAN oyoyo ya Amar Cikin fara'a sukace oyoyo my sis Momy tace sannunku kunsha hanya Amar yace wlhi Dady yace to sannun Ku nasan kan kuqara zuwa garin sae kun'dau shekaru Amar yakalli MARWAN qasa qasa yace Ai dady zamu koma nanda wata 'daya Cikin mamaki momy da dady suka kalli Amar dan sunsan koka'dan basasan zuwa qauyan Momy tace to Allah dae yasa lpy Yace lpy Momy alkairine Yayane yayi mata a can Momy takalli MARWAN tace wae haka Gamamakin Amar sae yaji yace eh Daka tsalle zainab tayi tana murya tace Allah nagodema ma Kae I luv u ya MARWAN naji 'dadi Dady yace masha Allah 'yar gidan waye Amar yace wae 'yar Malam shehu Dady yace Malam shehu Malam kae ban ganeshi Ba Yace yanadafa 'ya Nafisa amma mamanta tarasu tun tana qarama Dogon tunani dady yayi can yagano Malam shehun yace nagane shi To Allah yasa matar alkairice agaresa Amar yace amin Momy da tasaki baki tace Ikwan Allah yanzu MARWAN aure zaka qara ina soyayyar da kakema matarka Amar yace kae Momy kibarshi man Dady yace banda abinki ai so tsuntsune Amar yayi dariya yace hakane dadyna MARWAN ya'dau keey 'din motarshi yace Nina tafi Dady yace to yaushe kakesan ayi bikin Ya kalli Amar Da sauri Amar yace nanda wata biyu yace Yanaso ko MARWAN baiyi magana Ba yafice Momy tace nisae naga kamar matar bata shigeshi Ba Dady yace inbata shige shiba yazaiyi yace yana Santa Kawae halin miskilancin 'dannakine yatashi Tace ina mamakin halin nan nashi ko nawa yayi oho Dady yace Allah yakyauta Amar najinsu yatashi yayi shashinsa yana cewa Momy kayanki namota Wanda Hajiya tabayar abaki Sis kawomin abinci atare sukace to to Zainab na kitchen tana ha'dama Amar abinci Allah Allah take tagama taje dan gulma nacinta Ta'ajiye Mae abincin akan table Yace yauwa sis Tace ya Amar ya'akayi ya MARWAN yafa'da San wata yace Duk shirinane Nan yabata lbr tadinga dariya MARWAN tuqi kawea yake amma tunanishi yazaiyi da auran Nafisa Allah yasani soyayyar matarsa ne kawae azuciyarsa Amma tunda Amar ya matsa zai aureta kawae intagirma tagane bayasanta tarabu dashii Dan ra'ayin shi nazaman mata 'dayane Yayi parking motarsa cikin gidansa yafito Dagudu maryam tazo tarungume shi tana murna shima cikin 'doki yafara kissing dinta Tajashi falo Tace yanzu sae kafara wanka kaci abinci sae kaban lbr Yazareta daga jikinshi yaqare mata kallo Maryam bawata kyakkyawa bace amma kallo 'daya zaka mata gano Abu biyu atare da'ita Nafarko tanada wayewa sosae Nabiyu kallo daya zaka mata katabbatar da bata da kunya Amma ga MARWAN duk duniya bamekyan marwan dakuma kunya Bayan MARWAN ya gama kallanta Riga da wando ne tasa tayi kyauta sosae Yamayar da kallansa kan falan kaca kaca yake yace wae my luv yaushe zaki fara tsaftace gidannan tayi shuru yaci gaba Saiki tsaftace jikinki amma gidanki baxai sami wannan gatan ba =ؗ=ؓ=ؗ Tace haba hony daga dawowarka zaka faramin fa'da Yace ok bazanyi miki magana akan gyaraba Wlhi halin nan naki yana bani haushi Tayi farii da ido tace yadena baka haushi honey Su Habiba ne sukazo shiya gidan yayi datti Kuma wlhi nagyara jiya yace Tun jiya Tace eh Yace banga dalilinki nahanani kawo miki 'yar aikiba Tace inaaaaaaa banasan 'yar aiki sobuda 'yar aikin aunty Zakkiya ita ce tazama kishiyarta Yayi murmushi yana tuna kishi irin na maryam Akwaita da kishi Yace kina tsoran wata takwace miki nine Tace kwarae Ai duk macan da tayi gangancin sanka tota yaudari kanta Ba'dan ka'dan ba Yace danni nakine Tace ato Shiga yayi betroom. Yanda yayi zatan ganinsa hakako yagansa wato aburkice saikace Ba mace agidan Girgiza kae kawae yayi yafa'da toilet nanma takaici kamar ya kasheshi. Dakansa ya tsaftace toilet 'din yayi abin da zaeyi tana kan gado tanajin Shi Yafito yace amma toilet 'dinnan yafi 4 days baiga wanki Ba Tace tunda katafi Dake ba shigarsa nakeyiba Amma ai bae kae 4 days ba Yana zaune a dining takwawo Mae abinci indomie ce da egg Yana kallanta yakauda kae tace lpy Yace ita tajawo hakan Gsky bazanci Ba A duniya baki da abinci sae indomie Gashi itamma baki iyaba. Abu duk qarni Cikin jin haushi tace Nagajifa Wae meyasa kowane lukaci kakesan kusheni Komae nayi ban iyaba Amma ai kasan bana girki agidanmu bare aiki Amma kae ina qoqarin yima komae amma baka gani..... Taja tsaki tabar gun Tashi yayi ya'dau keey din mota ya fita Dan yasan yanzu yana zuwa lallashinta sae tasashi yaci indomie shikuma Allah yasani ba zaeciba Hotel yanufa yaci abincin da yakeso dama yasaba zuwa Dan 'yan hotel 'dinma sunsan shi Sanda yagama yadawo gidan Sam yanda yabar komae haka yazo ya ganshi yayi tsaki Allah yasani MARWAN akwae shi dasan tsafta shiyasa duk ran weknd yake zama yagyara gidan Har zae shiga 'dakinta saidae yafasa. Yashiga nasa. Ya gyara kowane saqo da lungu na 'dakinsa Ya tsaftace yadawo falo ya gyara shi Tare dasa tuarare Nan gidan yafito tsaf Nan gidan ya 'dau kamshi Kitchen yashiga shima yagyara shi sosae MARWAN dama yasaba da wanke wanke maryam nan komae yafito tsaf Ya qara yin wanka Sannan yanufi 'dakin ginbiyar tasa Tana zaune kan gado tana catin rannan 6ace Kallo daya yayi mata Yaga bazae iya jure fushinta ba Nan yajawota jikinsa yana lallashinta Dake itama ahannu take nan warware Maryam tana harkar maganin mata sosae Tabbas dashine takejan hankalin MARWAN yana jin da'dinta sosae amma baya gamsuwa da'ita =ؗ=ؓ=ؗ 'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI=ؗ=ؓ=ؗ Sam MARWAN ya manta da zancan wata Nafisa Yana falan Momy sana hira tsakalin 'da da Uwa Sae ga dady yafito Shima yace ayi dashi Momy tace ai mungama. Yace kundae ganni kunyi shuru wayasani ma ko zancena kokeyi Momy dayi dariya tace wane mu Dady ya gyara zama yace am MARWAN Cikin ladabi ya amsa da na'am dady Yace inasan kasa acigaba da gininka na zoo-roat Dan yanzu kasan sabuwar rayuwa zaka shiga yace hakane. Yace nakira kakanku nace masa kaga ita yarinyar Malam shehu kanaso yacemin har sunyi magana da shi Dama bayajin da'di shi Malam shehun Wae hawan jinine ya kwantar dashi Amma yanzu Cikin ikwan Allah yanzu ya warke Zaiyi magana saiga Amar yashigo da sallama yana cewa ayya dady Baban Nafisa ya warke Yace eh Dada kasan da rashin lafiyan shine yace kwarae Yace to Allah ya bashi lpy Cikin Murna Amar yace to dady ayi ayi ayi Auran nan MARWAN ya watsa mishi harara da sauri yabar gun Momy na dariya Yace yanzu dae anyanke auranku jumma"ar sama Dasauri MARWAN yace haba dady yayi wuri ai Kumafa aikin bazai kammalu alukacinba Yace baiyi wuriba son Dan yanzu haka QAUYE sunacan suna shirin baki Momy tayi gyaran marya tace dady (dake haka itama take cemae) Ni ganina kawae yaha'da matansa awaje 'daya tunda flat biyune agidan inadama kayine shida Amar yace eh Tace kawae yasakata a'dayan part 'din kaga yayi aikin can gidan Cikin nutsuwa. Yace Hmmm kinkawo shawara Amma wajan yananan dakyanshi yafa'da yana kallan MARWAN Yace aa gsky sae angyara dan duk maryam ta6ata kuma da shiginta aciki Momy tace to yanzu inkakoma kace takwashe ina dama kagaya mata maganar aura. Cikin sanyi yace eh. Dady yace to gobe zanturo abdul-salam ya gyara to MARWAN yace Baqaramin da'di MARWAN Yajiba lukacin da Momy tace ya ha'da matansa Dan yasan baqamin yaqi za'ayiba idan maryam taji ita da kishiyarta zasu tare a zooroat Dan asalin gidanma duk ra'ayinta ne Kuma nazaman mutun 'yane Yanzu tunaninsa taza'ayi yagaya mata zaiyi aure Allah yasani basan aurannan yakeba Maryam CE tashigo har tazauna gefanshi Bae saniba dan yayi nisa aduniyar tunani Tashafa gefan fuskarsa Ahankali ya ankare da'ita tace. Tunanin me kakeyi yace bakomae tace banyarda Ba Yace inatunanin wani abune Tace gayamin koshi miye yanzu zan maka maganin shi yace Promise tace yah Yace aure aka 'dauramin da wata 'YAR QAUYEN MU Tace what mekace. Yace yanda kikaji nima haka naji Dan haka part 'dincan da kikasa tarkacanki zaki kwashe akawota ciki MARWAN yace hakanne dan awucce gurin gabaki 'daya Dan yasan inyace mata satin sama za'ayi auran toba shakka saita hanashi auran Ai Cikin razana tatashi tace wae mekake cewane MARWAN kana nufin kayi Aure Yace Ammin bah Tace oho qiyayyar da 'yan uwanka suke nunamin yanzu takoma gun Momy da dady ne Yace ban ganeba tace Nasan bamae maka Aure sae su Ashe suma muna fukaine dama...... Fauuuuu Tassssss gauuuuu MARWAN faffalleta da mari uku ajere Marin ya shigeta ya gigitata Yace dan ubanki iyayan nawa ne muna fukae tace eh Ya kwasheta Jikake tif Tazube Aqasa yamata Dukan tsiya ya kulleta ya bar gidan Yana tuqin mota yana tuna rashin hankali irin na mata Wato indae kace zaka qara aure kanada mata tofa Tunaninta 6acewa yake Sam duk wani abu zata fa'deshi ne kawae kodame zai faru saedae yafaru (Tofah kunji maza. Dan Allah mata mudinga kula mudinga sanin yazamuyi da mazajanmu lukacin da sukace zasuyi. Mudinga bin komae asannu Dan musamu riba me 'dorewa Idan mijinki yace zaiqara aure plx kibarshi yayi Cikin kwanciyar hankali. Idan kika kwantar dakai kikasa Allah agabanki wlhi sae kinfi amaryar kwanciyar hankali Ammafa sae kinyi hakuri akan komae Plx munga kola Amarya da uwar gida kuyi ammani da darasina ) MARWAN gidan aminin shi yawucce kaitsaye wato Aminu Bayan sungaesa sun'danyi hirarsu ta likitoci MARWAN ya gayamae matsalar da yake ciki Yace yanzu dae katabbatar ka shirya kalaman da zaka lalla6a maryam dasu Dan samun kawanciyar hankalinka. Yace Ai Aminu lalla6a maryam yazama dole tunda itace rayuwata. Aminu yayi dariya yace MARWAN na maryam yace kwarae ninatane ka'dai har 'abada yace Togashi Amar nasa mata gaba Yace aibansan meyasa suka tsani maryam ba gashini da'da San matata nake Yace toga wata matar "Yar QAUYE Kuma nasan gaba zaka sota Yace kaeeee barifah maryam CE azuciyarnan Koda maryam tagama kukanta tattara kayanta tahauyi tana cewa wlhi bazata zaunaba Lokacin data mur'da kofa tajita arufe baqin ciki kamar yakasheta Ya kulletane dama Dan yasan tana tashi zatace zatatafi gidansu shikuma bayasan tafiyar tata Haka takoma gado takira babbar aminiyarta Habiba tagaya mata Nan tabata shawarar tsiya tare dacewa zatazo gidan Takira ma momynta tagaya mata ita hakuri tabata Can MARWAN yadawo yabude kofar yana cewa my luv Ta gallamae harara Rungumeta yana cewa wlhi bana Santa my luv keka'dai nakeso 'Yar QAUYE CE fah kucaka Sam batamin Ba bana Santa kuma ma qaramar yarinyace Tace inma miye ita ai kishiyata za'akirata Yace fa'da mun yanzu me kikeso ayi Tace tunda an'daura auran shikenan Sae dae zan kafama sharu'do'di yace inajinki Tace bakae Ba shiga 'dakinta sannan kamin Alqawarin bazaka kusan cetaba Cikin rashin damuwa yace namiki alqawari Tace kayi yace nayi Yanzu me kikesan canjawa a 'dakinki tace no bakomae kawae zakaban wasu ku'dine yace nawa million daya yace angama ginbiyata. Dama ance ba'a shiga tsakalin mata da miji Wan dama ya shiga shizaeji kunya Zainab CE zaune kan kujerun shaqatawar farfajiyar gidansu tare da Amar Tace ya Amar yanzu saura kwana 7 bikin yayah Yace kwarae ni inasan zuwa qauyan amma nakasa zuwa inasan zuwa kafin Auran gashi nasama Nafisat rae wlhi Tace muje tare yace to muje gobe mana tace Allah yakaimu =ؗ=ؓ=ؗ 'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI =ؗ=ؓ=ؗ Nafisa CE 'dauke da farantin tallen kokon safe tana tafiya Cikin qaddara tayi tuntu6e Gabaki 'daya kokon yazube [6:50AM, 01/10/2016] Hajjaju Novel: =ؗ=ؓ=ؗ 'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI =ؗ=ؓ=ؗ Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele =ؗ=ؓ=ؗ =ؗ=ؓ=ؗ 7 =ؗ=ؓ=ؗ Cikin kuka tafara kwashe kwanuka ta nufi gida Kallo 'daya Larai tamata tasan tazubar Tace wlhi ku'dina zaki nemomin Tace Dan Allah baba kiyi hakiri Dama Larai tana ciki da Nafisa akan maganar auranta tana baqin ciki sosae Nan tafa jibgarta Hakan bae mataba sanda tadaka barkono tasa ruwa Nafisa na ihu tana kuka amma Larai bata tausaya mataba sanda tamata tsarki dashi Hassana da mairo Sunsaba ganin azabar da take gana mata amma baza su'iya hanataba Nafisa nacikin kuka saiga babanta yadawo dake yasamu sauqi Hankalinsa tashe yace Nafisa mae yasa meki tace tuntu6e nayi koko yazube shine baba tadaken tamin tsarki da barkono Yace Larai Tafito daga 'daki yayadae Yace wae meyasa baki da imanine tace Banda shi Yace wlhi bazae yuhuba Kinakasa min 'yaba Dama ina barinkine dan rashin lpy amma wlhi yanzu zanbaki mamaki Tace kayimin abinda zakamin. Ai kasaba indae akan 'yar'iskar yarinyar nanne Yace kitafi gidanku na sakeki saki 'daya Tace ai wlhi kayi qarya nida gidan mutu karaba Kokulata baiyiba yasa ruwa abuta ya'daga Nafisa yace Taje tayi tsarki Ana Cikin haka saiga lantana tashigo da gudu Wata mata ma tashigo Baba yace lpy Matar tace Kaine mahaifin yarinyarnan yace eh Tace wannan yarinyar taka bata da hali Yace me yafaru tace Ganinta nayi da wani suna lalata alungu Da sauri baban yakalli Larai Matar taci gaba da cewa Wlhi da'idona nagansu Larai tace kee Kiji tsoran Allah lantana kamilar yarinyace batasan wani lalataba Matar tace to'ai gatanan baqarya namata ba Tace wlhi sharri kika mata Nan tabau masifa Da sababi Babah yace mungode baiwar Allah insha Allah zata dena Matar tatafi Babah yadawo da kallan shi kan larae yace kinga akin iskanci ko Dama idan zaka dinga furucin iskanci akan yaran wasu toko da ikwan Allah saidae kagani akan naka Yayi ficewarsa yabarta tana bambamin masifa Wae sae kace bashi bane ya haifi lantana duk ya tsaneta Bayan kwanaki =ؗ=ؓ =ؗ 'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI =ؗ=ؓ=ؗ Da sallama tashiga gidan Hajjiya matar megari tace 'yar albarka. Yanzu kuma mae aka'dauko Nafisa tace goro. Tace to nanawane duk Tace na ishirin da biyar Tace to jeki kaimin banka'dan filo Tace dukka tace eh Banaso kisha wahalan tallene Hartata shi sae kuma tazauna tace har yanzu ba suzuba Hajjiya tace suwa tace Ambar da qanwar tashi mana Tayi dariya tace yaudae zaki gansu Tace hmm Yau kwana hu'du kenan kikace zasuzo sun miki waya amma basuzo Ba Tace kedae kaimin goran banka'dan filan Nan tatafi da gudu tashiga 'dakin da sallama..... Amar ne zaune da zainab Da sauri tawan cakalar da farantin tana cewa Ambar yace Nafisat Cikin farin ciki taje kusa dashi tazauna tace na'am Yace yaushe zaki iya sunana Tace sae nazama 'YAR BIRNI yace ko tace eh Yauwa kacema Hajjiya zakuzo shekaran jiya waccan amma kukaqi zuwa kullun sae nazo dubaku yace na'danyi ciwone shiyasa amma naso zuwa wlhi Nafisat Zainab tace ya Amar Itace yace yah Tayi shuru. Tayiko yace da ita tace balefi kam Nafisa tace wannan itace qanwar taka Yace eh Tace itama me kyau Zainab tace yanzu jibi zata zama tamu ko Yace kwarae Nafisa tace sae magana kukeyi amma kunqi sani ciki Zainab tace ayya my luvly sis Me kikesanji Tace miye my luvly sis Tace yama zan mata explanation ya Amar Tace meye koma shi Zatayi magana Amar yace Nafisa jibi kin zama tamu Tace kamarya Cikin qasa qasa da murya zainab tace anyako tasan da maganar Nafisa da kunne Tace maganar Mae Amar yace kinsan meye aure Tace eh mana idan mutun yatafi gidan mijinshi shikenan banzai dawoba Atare Amar da zainab suka kalli juna Yace to kinsan ya MARWAN ai Tace mae da'din muryar nan. meyasa bakazo dashiba yace zaizo jibi Tace to Allah yakawo shi Yace Ameen Tace to meyasa ka tambayeni aure Yace Dan ya MARWAN yace yana sanki zai aureki jibi Da sauri tarufe fuska wae adone taji kunya tace shine yafa'da Yace eh ko bakya sanshi tace ina sanshi man gashi da da'din murya Yace ko Tace eh Duk tana maganar ne hannunta akan fuskarta Yace towae miye narufe fuska Batace komae ba Can Tamiqe tana cewa Nina tafi gida Yace kizauna mana tunda kokin koma wani tallan zaki 'dauko tace ai babanane yace indawo da wuri zamuyi hira Yace to kigaishemin dashi kice zanzo tace to Takwashe goran da tazubar tasama Hajjiya a banka'dan filo tafito Hajjiya tace yaudae kinga ambar hankalinki ya kwanta Dariya tayi takar6i ku'dinta tafita Da wake wakenta ta'isa gida taba baba Larai kudinga Tayi gun babanta. Yace Nafisa tace na'am Babah Yace ina wannan saurayin MARWAN Tace nagane shi yayan ambar yace yauwa shine yake sanki da aure Tayi shuru Yace kina sanshi tace Eh yace to shikenan Aranar Hajjiyan megari tasa aka kawo Kayan auran Nafisa... Ansamu tashin hankali gun Larai sosae Dan batayi tunanin abun zaizo Cikin sauqi hakaba Ga 'yarta lantana bayi auranba amma Nafisa zatayi qanwarta Qarara take nuna baqin cikinta =ؗ=ؓ=ؗ Ran jumma'a aka 'daura auran Nafisa da MARWAN Aranar dae Nafisa tayi wanka sosae Dan Hajjiyan megari takawo mata Kayan sawa Masu kyau Ba qaramin kuka Nafisa tayiba lukacin da tatabbatar zata rabu da babanta Haka tanaji tana gani aka tafi da'ita BIRNI Akabar baba Larai da baqin ciki =ؗ=ؓ=ؗ 'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI =ؗ=ؓ=ؗ Gun Momy akakaita Nafisa Ba shakka Momy tayi mamakin Nafisa Batayi tunanin yarinyace haka ba Haka tace akaita gidan mijinta Hakako akayi aka kaita gidan MARWAN Lukacin da akakaita gun maryam ba qaramin kwanciyar hankali tajiba dan ganinta yarinya Tasa azuciyarta MARWAN Ba aure yayiba 'Yar aiki yakawo mata. Shuru Nafisa taga MARWAN bae zoba Dama tasan gae dashine MARWAN ko yanacan 'dakin ginbiyarsa maryam Suna hira Cikin nusha'i Maryam takara kashemae ido tace hony lukaci na tafiya kallifa to 11 Yace wani abune tace eh man Yace to fa'di inajinki Tace ka tashi kaje gun amaryarka Yace bazan jeba tace Kaga bawae ina nufin kaje kazauna bane inasan mudinga nura da ita yanzu tashi muje muga lafiyarta Yaja tsaki yatashi Tana zaune sae raba ido take tana kallan inda akakawota kamar aljanna Saiga Su maryam sun shigo Da sauri tadur kusa qasa tace ya MARWAN ina wuni Aunty maryam ina wuni Maryam CE ta'amsa MARWAN niyar fita yayi Da sauri tace ya MARWAN baka amsaba gaisuwarba Yace ban amsaba. Yafita maryam tabi bayanshi Ganinsun sun fita Hakan yasa Nafisa tayi tunanin ita ka'dan zata kwana Tuni tsoro ya shigeta Atunaninta dukkansu ne zasu kwana waje 'daya Ganin tsoran da yashigeta shi yasata yin shashin maryam tafara kwankwasa musu kofah Maryam dake gefan maryam tace waye tace Nafisa CE Mamaki ya kamata tatashi tabu'de mata kofar Tace wani Abu kikeso Bata kulataba Saima ratsata da tayi tawuce Cikin falun Maryam tabita da kallo 'Dan nesa da MARWAN ka'dan tazauna Yace lpy tace ai bazan iya kwana nika'daiba shine nazo inkwana daku Maryam dake kofa tace dawa Nafisa tace daku mana MARWAN ya daka mata tsawa yace tashi kikoma 'dakinki Tarikice sosae Dan tsawar da yadaka mata Nan tafara kuka tana cewa wlhi bazan iya kwana nika'daiba Cikin fusata MARWAN yafitar da'ita daga falan Jikake tim wurgata farfajiyar gidan ya kulle kofar maryam tace gwara da kamata haka fitinanniyar yarinya kawae Tsoro yaqara kama Nafisat tasha kukanta tashige 'dakinta Atsorace bacci ya'dauketa Asuba nayiko tafarka Basan kan toilet 'dinba saida swn tayi aiwala Bayan gari yawaye maryam takawo mata tii da buredi da kwae Amma fur Nafisa tace bazataci ba Maryam takira MARWAN Yace to mekikesan kici tace koko da qusae Ya dallah mata harara yace to babu anan. In bazakici wannan Ba ki barshi Nan take tasamae kuka harda bubbuga 'kafa Haushi Yakama MARWAN yako nemo igiyar caji Yadinga shau'da mata Tana tsalle tana ihu Sanda ya tabbatar yazaneta sosae sannan yabarta Yatasa mata breakfast 'din agabanta yace taci Tace wlhi bazataci Ba Ita koko da qusae takeso MARWAN ya lura yarinyar 'yar girima CE Ga maryam nagefe tana kallan duk abinda yake faruwa Yaja tsaki yace wlhi kici ko naqara zaneki Cikin kuka tace nidae kokoh da qusae nakeso Tashi yayi yafita Maryam tace amma kekam Allah yayiki cikakkiyar Ba qauyiya Cikin rashi damuwa tatashi takwanta kan kijera Aran maryam tace tsinanniya sae kace kukerar ubanta. tafita shashinta Koda maryam taje falonta Bataga MARWAN

Chapter 2 of 5