Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
yace Bbu Nafisatu saidae inasan nayi aure Nafisa tawaro ido tace aure babah Yace eh Inaneman kwanciyar hankali To kinga bana samu agun Larai Shuru tayi dan itama shedace can tace to wazaka aura Kuma a'ina take Yace nan qauyan kusa damu take sunanta maryama bazawarace yaranta 3 mijinta rasuwa yayi amma yaran suna gun dangin mahaifinsu Tace to babah inkayaba da hankalinta ka'aureta yace Jumma'arnan ma auran tace inananma za'ayi kenan tunda rana 'dayane dana Adamu Yace kwarae Haka sukadinga hira cikin farinciki Canyace tatashi yarakata gidan megari Tayi dariya tace baba korata kake Shima dariyar yayi yace aa Tace to kamanta momy tace Amar zaizo ya'daukeni yace au namanta....... Bae qarasaba Amar yashigo da sallama Yana cewa gani nazo Nafisa tace yanzu babah yake cewa muje yarakani Yace toh baba kasha zamanka gani nazo Murmushi yayi Nan Nafisa tamusu sallama suka tafi Lukacin da Nafisa take qoqarin fita daga motar Amar yace amma Aunrynmu kinyi kwana biyu bakuyi waya da leemat bako Tace wlhi kam munkwan biyu bamuyi waya ba amma zankira anjima yace OK tafita tana shiga falan Hajjiya momy tace sannu kindawo Tace eh momy Hajjiya tace bakijin nauyin jikinkine ko Zainab tace aiko tanaji inda ayanzu zakice tazo kuje wanigu toko binki zatayi Nafisa taharareta Agaskiya Nafisa taji da'din qauyen sosae Fatsima qawarta ma taxo sungaesa sunsha hirar yaushe gamo Harma tarakata gidan Lantana Ayau aka'dauran Adam da Hafsa Gidan megarin akakawota Baban Nafisa ma an'daura auransa Inda baba larai kawae taganta da kishiya A'dakin isma'ila akasa amaryar Baqamin hauka baba Larai tayi ba amma bawanda yakolata Anasaura kwana biyu Sukoma Kwatsam saiga MARWAN wae yazo tafiya da Nafisa za'amata wata allura Momy taqura mishi ido tace wata allurace wannan wacce bamusanta ba Sosa qeya yayi yace yanzu'akayi momy Murmushi kawae tayi tace to Allah ya kaiku lpy amma kar kakuskura kakaita gidanka Yace toh Cikin takaici da baqin ciki Nafisa tashirya dayima kowa sallama sukatafi hardasu Zainab da Amar Momy da Dady kawae suka bari aqauye Tun'amota MARWAN yaketa jifan Nafisa da shuqumin kallo Sarae talura sharewa tayi Sunako sauka yawucce da'ita gidansa. Dama tasan abuqace yake danhaka batayi tunanin zaisaurara mata tada'diba Sanda suka gama abinda zasuyi yadawo da'ita gidan momy Yace my FEENAH INA sanki ina qaunarki Wlhi akowane lokaci inasan kasan cewa dake Tawatsa mishi wani kallo Mae saqo kalakala Tace inasanka mijina sosae plx kasoni Wlhi inbakae bazan iya rayuwaba Yarungumeta yace ninakine keka'dae my FEENAH Su momy sundawo Ayauzo cikin Nafisa yana cikin wata fitansa Shiyasa Sam momy bata wasa da kula da lafiyarta Akoyaushe hankalinta nakanta Yau cikin dare Nafisa tatashi dawani gigitaccan ciwan ciki da Mara afurgice tatashi tana juyi ha'de da salati Motsinta ne yatashi Zainab Ganin halin datake ciki yasa tayi 'dakin momy Kira daya tamata tatashi Dake a'ankare take Dagudu sukayi dakin momy tace maza auta jekitada mota mutafi asibiti Da sauri zainab tafita Tanako fita saiga kan yaro yafito Nan momy tadinga temaka mata Cikin lokaci qanqani Nafisa tahaifi danta kyakkyawa mai kama da MARWAN sak Momy tagyarata da 'danta zainab sae murna take dan akwaeta dasan Yaro Washe gari kallo daya zakuma Su momy da Dandy Amar zainab kaga gamshash shan farin cikinsu Dady yace bari nakira MARWAN Amar yace ainarika dady.... MARWAN ne yashigo falan Kallo 'daya sukamae suka hango nashi farin Cikin na musam manne Birni da qauye bawanda baiji aihuwar Nafisa ba Ana saura kwana uku suna 'yan qauye sukazo cikiko harda Su baba Larai da lantana Baqamin tsurewa baba Larai tayi ba dangain irin daular da Nafisa tashiga ciki Ranar suna Hmmmmmm dole ni Rahamat naja numfashi dan bazan iya fa'din budirin da akayiba Yaro dae yaci suna abakar S@DIQ Nafisa tasamu alkairi bana wasaba Kowa yawatse cikin farin ciki da annushuwa Lantana bataso tafiyaba dan daqer baba Larai tamatsata suka tafi Momy ko tacikasu da abin arziqi Yau sati biyu kenan da aihuwar Nafisa Amma MARWAN baisamu sakewa da Nafisa ba Dan momy tamishi katanga da'ita Ba kunya yace wae momy yaushe zakiban FEENAH ne tace sae tayi sittin yawaro ido Yace ina arba'in akeyi tace Ashe kasani Shuru yayi Yaukam yashigo gidan momy bataan wae taje gaisuwar rasuwa ayanda zainab tagayamae afarfajiyar tana zance Dan haka 'dakin da Nafisa take yayi kansa tsaye Tana kwance bacci takeyi hankali kwance itada da baby Sadiq Qura mata ido yayi dan tamishi kyau sosae saiqamshi sukeyi Yakae bakinsa cikin nata yana yana tsotsa Furgigigit tatashi yajawota Jikinsa yana kissing 'dinta yace nayi missing dinki Shru tamishi dan taga nutsuwrshi tafara tafiya Yafara qoqarin cire mata riga tafara hanashi ya watsa mata wani kallo tuni tabarshi Yayi nisa cikin San burin shi yacika Kawae saejin sallamar momy sukayi afalo Ahankali yasaketa yajah tsaki Da Sauri Nafisa tasaka rigarta Takwanta da juyama MARWAN baya Yayi mamakin hakan da tayi zaimata magana momy tashigo. Yace sannu da dawowa tace yauwa Nafisan Bacci take Yace eh nima shigowata kenan tace gud Fitotoh Ya miqe amma ko ka'dan bae yarda ya ha'da ido da itaba Dan yasan kallo 'daya zatamae tagane wani abu Muleqa maryam Tunda MARWAN yasaki maryam tashiga damuwa sosae dan baqaramin sanshine yaqara shigarta ba Ga wani bakwan lamari da yake damunta Dan Habiba taha'data da wani Alhaji a Abujah Baqamin sake mata ku'di yakeba amma kash Ta'deboma kanta ruwan dafah kanta Dan Alhajin matsafine nagaske Yanzu haka kasheta yakesanyi Dan sae mugun mafarkae takeyi kuma dashi takeyi Abunma yanzu yayi tsamari dan har ganinshi takeyi azahiri yabiyota da wuqa zae caka mata Nan take kwalla ihu sae ya6ace Duk tarikita 'yan gidansu sunyi mata tambayar duniya amma taqi cemusu komae Ahaka suka gaji suka barta Amma tana kwalla ihu zasuyi kanta Toyauma Tagama kwalliyarta dan tanasan ha'duwa da habiba su tattauna akan matsalar da suke damunta Tanasan fa'dama iyayanta abinda yake damunta Amma sam habiba tahanata fa'da musu batasan dalilinta ba Shine yau takesan jin dalilinta Kuma talura da habiban yanzu tafaraja baya da ita sosae Lokacin da taje gidansu habiban tatarar batanan Taja tsaki dan sanda tafa'da mata zasu ha'dun Tunani tayi taje gidansu basmah qawarsu dake makwafta dasu hababi ko tanacan Lokacin da tayi sallama gidansu basmah bawanda ya'amsa saima jin muryar habiba datayi itada basmah suna shewa Inda ita habiba kecewa Ba maryam mery kike fa'daba Cak maryam tatsaya daga tsakar gidan tanajinsu Habiba tacigaba dacewa Wlhi Alhaji barau yagama da'ita Dan yanzu ranta kawae yake nema Kinsanko tsawan da ya'dauka yana San yayi amfani da ita Basmah tace aa Tace tun dana 'dakin mijin Dan akwae ranar da tarakani gunsa yaganta shinefah yace min wae dodan tsafinsu yana bukatar mace kamarta Saboda jininta zaiqara mishi sukuni fiye da sauran abokana yansa Basmah tazaro ido Tace toh=3 Habiba tace kinsan menayi Tace aa Qoqari nayi narabata da mijinta MARWAN sannan kuma naha'data dashi Alhaji barau 'din Basmah tace Shegiya kae amma ke muguwace Habiba tace abinda maryam bata ganeba kenan axamanmu Suka bushe da dariya. Basmah tace Allah kin cuceta da yawa gashi kuma tabaki yarda Tace kinsan miye Basmah tace sae kinfa'da Tace Allah farkwan dangan takata da mery maryam nasota amma datayi Aure yanda MARWAN yakesanta yake bata kulawa shine naji baqin cikin hakan sosae. Tare takaici Basmah tace hmm toyanxu yaushe zae kasheta shi Alhaji barau din tace inazan sani nidae badae yaban kwabbae naba Basmah tace banganeba Tace zaki gane yanxu. Alhaji barau fah ku'di yacakkemin miliyoyi Shiyasa nasan yanda nayi naha'dashi da'ita takota Ina Basmah tace Lalle mutun mugun icene kalli yanda kuke da maryam amma kiga yanda kika shirya mata gadar zare da mugunta. Azahirin gaskiya taban tausayi Cikin 'dan daure fuska Habiba tace toko zaki gayamatane Tace wace ni dama ina shiri da itane toko ba'abinda zae hanani gaya mata Habiba tace dako naha'da dake Wlhi duk ashanye jininku Basmah tayi dariya tace aini nafi qarfinki Wlhi Habiba danda nice maryam da tuni nada'de da harbo jirginki kalleni dakyau fatata da jininda yake cikinta tafi qarfin wani maye ko matsafi Saboda kawae narike Allah da manzansa duk abinda yayi hani dashi banayi sannan koma ina koyi da 'dabi'un ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIYUWA SALLAM Itama maryam 'din abinda yasa har kikaci galaba akanta shine Tunfarko bata gina rayuwarta tafarkin Allah ba Tagina rayuwarta ne tasan kasancewa da mace Abinda yakasance qaxamin Abu amanyan lefuka Inasan kiyima Allah Habiba kidena aikata abinda kikeyi Habiba taja tsaki tace Kinsan abinda yasa tunfarko bana San kasan cewata dake Basmah tace nasaniman bakisan nakasance cikin fa'da miki gaskiya Tace kwarae Wlhi plx kiriqe gaskiyarki banasan jiiii Kinga lukaci natafiya bari nayi waya da sahibina kan maryam tazo dantace min zataxo Basmah taja tsaki Hawaye Baqin ciki Takaici Nadama Dana sani Rashin sani Allah da rayuwa sune suka cafki maryam lokacin da tagama jin dukkan abinda yake fitowa daga bakin Habibi Ahankali tajuya tafita daga gidan cikin tashin hankali Dake bata tare da nutsuwarta Sam Shiyasa har ya haifarmata da tuqin ganganci hartayi hatsari Nantake tasume Mutane suka bata temakwan gaggawa cikin sauri sukajaita Asibiti tare da kiran wayar iyayanta tawayarta suka gaya musu Anan take sukayi asibitin Lokacinko likitoci sunyi aikinsu danko har tafarfa'du Saidae maryam inbanda kuka ba'abinda takeyi sun mata tambayar duniya amma taqi cedasu qala Bayan kowa yafita daga 'dakin sae kawae Aunty Khadija Tamatsa kusa da maryam tace kiyima Allah maryam kigayamin Mae yake damunki Nan take maryam tazube ajikinta tace nacuci kaina Aunty banyima kaina adalciba inasan 'daukar fansa Aunty Khadija tace wae lpy Mae yafaru. Anantake maryam takwashe rayuwar dasukayi da Habiba tundaga gidan MARWAN da sanadin sakintan dayayi da kuma jin kalaman datayi yanzu Aunty khadiya tafara salati tana cewa tab munshiga uku Kae mutun mugun ice Toyanxu ya'ayi tace Sonake kifahimtar dasu dady cikin hikima dan sunemamin Magani Arabani da shi Alhaji barau din PLX Aunty karya kasheni Tace toh Hakako akayi baqamin Magani akanemama maryam ba hartasamu tafita daga tarkwan Alhaji barau din 'dan daqer Sannan tace ma Aunty khadija zata'dau fansan abinda habiba Tamata Nantake tace kartafara tabarta da Allah kawae ya'isheta Itako Habiba yaushe takira maryam bata 'dauka Ranardae maryam ta'dauka taja mata kunne akan kartaqara kiranta tare damata zagin cinmutunci da kuma sanar mata dacewa taji komae abinda take shiryawa akanta Da farko jikin habiba yayi sanyi amma daga qarshe tata6e baki Tace ko banxa dae 'dan koli yaci ribah =ؗ=ؓ=ؗ 'YAR QAUYE KO 'YAR BIRNI=ؗ=ؓ=ؗ Saura kwana biyu 2 yau Nafisa takoma 'dakinta Farin ciki gun MARWAN abin ba'a magana Yanzuma yana cikin sabon gidansa na Zoo-roat shida Amar da zainab Sae santin gidan Amar da zainab sukeyi Dan angama gidan tsaf dashi Komae yaji babuce kawae babu agidan Sundawo gidan momy agajiye tace yadae Amar yace yace Wlhi gidan yayah yayikyau bana wasaba Zainab tace momy kinga gidan kuwa Wlhi daqer nafito saboda ni'imarsa Momy tace nida Dadyne zamubaku lbr tunda munrigaku zuwa harsuna ha'da baki wajan cewa LA munmanta Momy tayi dariya MARWAN yace plx momyna Dan Allah inasan naga FEENAH tace kafita daga idona Yamarairaice da cewa dan Allah momy tambayarta kawae zanyi Tace toh minti 'daya nabaka Da sauri yatashi ya nufa 'dakin datake Tanako zaune tana game a laptop 'din zainab Qamshin turaransane yasata dago dakanta takalleshi Ware hannayansa yayi Tako tashi dagu taje ta rungumeshi Ya qamqameta tsam ajikinsa Yace ina missing 'dinki FEENAH Tace nima haka MY D Ya'dago fuskarta yace qaryane Kalleki yanda kike qiba tare da kyau. Niko sae ramewa nake Taturo baki cikin shagwa6a tace Banafah iya bacci fah saboda bana samun sukunin bajewa yanda nakeso. Yace hmmmm Tace Allah MY D idan ba aqirjinka nakwantaba bana iya yin bacci Yaqara qanqameta ajikinsa yace Kina buqatata Tace ssae mah Yace to yau inasanyin...... Bae bari yaqarasa afiliba sae gani nayi yara'da mata qarashan akunnanta Tawaro ido tace . Gobefah za'a kaimaka niii Yace nasani'ai Tace to nibansan yanda za'ayiba yace ninasani takwa6e fuska tace plx yahyana. Kabari kawae sae ankawo maka niii Yace matsora ciya nabari Yacaf ke bakinta yana kissing ssae can qafarta tafara rawa hakan yasa yasaki bakin tamaida kanta qerjinsa tace ina sanka majina Yace ssae Tace eh Rabata yayi da Jikinsa yace minti 1 momy tabani Inasan cin abincinki yau FEENAH Duk yanda za'ayi kimin abinda zanci da hannunki Tace toh MY D idan momy taganni a kitchen nace mata Mae yace kice zakiyima yahyanki abinci Zatayi magana yace Kinsan Allah...... Sae kuma yayi shuru yafita Ahankali tazauna tadafe kanta Abaeyane tace o Allah MY D kanada futuna qiri qiri kakesan koyamin rashin kunya Can jimawa zainab tashigo tace Yanaganki haka tace Wlhi my d ne yakesan namishi girki Tace hmm soyayyarku tana birgeni Tace banda sharri dae tace aiba sharri bane Tashi tayi tace Kinga bari naje naji da umarnin mijina Zainab tace tomae miji Tana kitchen tana ha'damae abincin Momy tashigo tana cewa wayasaki girki Cikin kunya tace Wlhi yayane Murmushi tayi tafita Hakan yaba Nafisa damar zagewa tayimae girki lafiyayye Bayan isha'i yashigo gidan Yasamin abinda yakeso dan Nafisa tashirya mae komae Yaciki cikinsa dam yana hamdala shida Amar Zainab ce Mae ha'dama Nafisa kayanta Takalleta tace wae miyene dan Allah kidena tunaninnan haba Sae kace bazaki dinga ganinmu dukkin wani damu Tace Wlhi zainab banasan tafiya Tace hakuri zakiyi dan ya MARWAN yafimu buqatarki Momyce tashigo tace haryanzu baku gama ha'da kayanba Zainab tace nagama momyn tace toh maza kaimata mota Tace toh Tamaida kallanta kan Nafisa tace kizo 'daki kisamaini. Tace to Tana fita tabi bayanta Momy taqarema Nafisa kallo tace Dady bayanan bare kuyi sallama kikwantar da hankalinki 'Yata Tace toh Momy taci gaba Kiqara ladabi da biyayya agun mijinki Kikasance mae tsafta Iya kwalliyar 'daukar hankali Ki'iya kissa da shagwa6a Nasanki gwanace wanjan girki inasan kiqara dagewa wajan sarrafa kowanne iri Kinji 'yata Tace toh momy Tace yauwa idan magun gunanki sunqare kimin magana. Maza tashi kije mijinki na mota yana jiranki cikin jin kunya tace toh zata fita momy taqara cewa kikulamin da Sadiq tace toh Tafita Afalo taga Amar da Sadiq a Hannunshi yace Auntynmu kinfito tace eh Yace gud zainab nawaje Tace toh suka fita atare Amota sukaga MARWAN yana wayana tashiga motar Amar yamiqa mata Sadiq yace saimunzo da Leemat Nafisa tace a'ina zaka ganta yace batadawo gidan Auntyn taba Tace hakane To saekunzo Zainab tace nidae akulamin da sweet Sadiq 'dina adena barinshi yana kuka Harararta Nafisa tayi MARWAN yaja motar Sunyi nisa da tafiya yace ba maganane Tace Wlhi jina nake wani iriii Yace saboda zaki koma guna ko Tace aa bafah haka bane Yawatsa mata wani kallo wanda yasa lukaci 'daya jikinta yamutu Baqaramin sake baki Nafisa tayiba taganin tsantsararran gidan nata Tunda take aduniya bataga gida maikyan shiba Kowane lungu da sa'ko saida yanuna mata Tarungume shi tabaya Tace MY D I luv...... Juyo da'ita yayi gabansa yace basae kinqarasa ba matata Inasanki Takwantar dakanta girjinsa tace Allah yada'da albarkar duk wani abu naka Yace ameen Bangaya mikiba Yauwa naje qauye na'dauko babah nanuna mae gidannan saboda yasan inda kike zama Kinsan halin rayuwa 'Dago dakanta tayi tana kallansa Tace hakane amma meyasa baka ha'dani dashiba yazo haryatafi bayan kuma kasan bana samun ganinsa inba zuwa nayiba Yamata kiss =؋yace afuwa ayafemin Tace to zakabarni naje Yace ina Tace qauye yace no bayanzu bah Tace a al'ada duk wacce ta'aihu bayan Arba'in tana zuwa gaida iyaye da 'yan Uwa Yace kinsan miye Tace aa Yace yunwa nakeji bata wasaba Tawaro ido tace kae MY D meyasa kakesan illatamin kanka Kaga banga tazamaba dole nanema ma cikinka abinci. Tafa'da tanamae zare kanta daga jikinsa Ya'dau Sadiq yanamae wasa Tana kitchen taji yana cewa kinyi isha'I ko Tace nayi Yace Baby Sadiq yanasan yin bacci bari nashiga wanka Tace toh Yace bansan yayi kuka dan haka kikula Shuru tamae tana mamakin irin 'kaunar da sukema Sadiq Sam basasan kukanshi Gashi dakuka ba'dan ka'danba Ahaka tagama komae tajera a dannin Lokacin MARWAN yafito dakayan bacci ajikinsa Yace tnx FEENAH har kingama tace duk wani Abu idan yakasance nakane bana 'daukarsa da wasa Yagya'da kae yace gud' Tashige tana cewa nima bara nayi wanka Yace kitabbatar kinsaka rigar da na'ajiye miki Tace nina'isa kaucema umarninka Wankatayi tasaka rigar da yace tasa Shigiyar rigace iyakarta cinyarta amma tayi kyau ssae Tafeshe jikinta da turare dama tashafe kowane lungu da sa'ko najikinta da humra Ahankali take fitowa Idan MARWAN tsaf akanta Baisan lukacin da yaje yakwantar da Sadiq ba yaxo ya rungumeta yace kinyi kyau ssae FEENAH Tace kaima haka MY D inafatan kaqoshi yace ssae mah Sae dai ina buqatarki yanxu Tace OK Ya'dauketa yakaita bet zaifita kuma tace zuwa ina kuma Bae kulataba Sae ganinshi da Sadiq tayi yakwantar dashi a nashi bet 'din Sannan yadawo kanta Yace duk halin da xanshiga baxana manta da 'Dana ba Nan yafara kissing 'dinta Duk yarikice mata Lalle tasan yayi missing 'dinta Ajiyar zuciya yaketa sauke mata lokacin da yake shan breast dinta Bae tashi rikice mata ssae saida yafara aiki ihu da kuka yasa mata Yanayi tanayi Duk hankalinshi yafita daga jikinsa Sae sambatu da samata albarka yake Itadae jinshi take tana qara rikitashi da kukan shagwa6a Baqamin wahala tashaba Dan daqer tasamu kanta agunsa Washe gari yagabatar mata da 'yan aikin gidan 'daya bayan 'daya bayan tagama breakfast suna zauna suna ci Sadiq ne yaketa mata rikici tana bashi nono MARWAN yaqura mata ido Tahura fuskarsa Ya'dan lumshe ido yace my FEENAH kigaya min sirrinki Tace aiduk sirrina bawanda baka saniba MY D Yace FEENAH kinyi baka 'danba Kmae kikayi maekyaune abin sone Kmae kikayi kyau yakeyi miki ina farincikin kasan cewarki matata Allah yabarmin Tace nagode MY D Kaine kacancanci kalmomin nan Yace ko Tayi mae fari da ido tace dagaske Tashi yayi ya saqale kansa akafa'darta Yace dan Allah kiqara ban nayi Tace mene Yaxura hannunshi arigarta yana shafa breast 'din yace Abin nan najiya Tace kashiryafah yahyanah fita zakayi Yace baxan 'dau lokaciba. Kwanciyar hankalina Tace toh kayi MY D ainakane Cikin murna yakar6i Sadiq yaja hannunta xuwa betroom Itadae sae godema momy take =ؗ=ؓ=ؗ er 'kauye ko er birni=ؗ=ؓ=ؗ Haka rayuwar tasu taci gaba da tafiya cikin so da qaunar juna Baqamin so da 'kauna MARWAN yakema Nafisa bah Haka momy kullun qara santa take Yanxo shekaran Sadiq 3 da 'dan watanni Yaro Mae kuxari da lpy Soyayya tsakanin Halima da Amar abin ba'a magana Ssae kowa yasan da zaman soyayyarsu Hakama zainab da Aliyunta suma ba'a magana Dady yayanke Auransu cikin wantan nan Wae tare xaiha'da Auran Amar da zainab Shiyasa aketa hidimar ha'de ha'den biki Nafisa tana zuwa qauyansu amma tare da MARWAN danko ka'dan bayasan tayi nisa dashi kuma idan sukaje aranar suke dawowa Sadiq yazama 'dan gidan momy Sam bayasan xama dasu Nafisa yafisan xamansa gun momy Shiyasa komae nasa yake gunta Inkunga yaxo gunsu Nafisa to kwana 'daya yakeyi inyayi tsamari 2 MARWAN ne zaune amaxaunin direba yana jiran Nafisa tafito Dan gidan Aminu abokinsa xasu Tafito cikin shigarta tadoguwar riga black da ratsin jaah da 'dan hijab 'dinta qarami daka'dan yafi hijabu gayu shima jaah. Sae takalminta Mae tudu black Sae qamshi take zubawa Baqamin kyau tamishi ba har tashi motar idanshi nakanta Yaja motar Sunyi nisa da tafiya yakalleta sukako ha'da ido yace kinyi kyau Tayi murmushi Yaci gaba Yanxu supermarket 'din zamu fara zuwa tace eh Ya'dan rage murya can qasa yace plx kiqaraban baby Dan Allah saboda.... Saikuma yayi shuru Ta'dan kalleshi tace sabodame Yace saboda nagaji daganinki haka Taturo biki gaba Tace bakaso nahuta ko Yace indae hutu irin wannanne bana sanki dashi my FEENAH Akoda yaushe inasan na ganki kina shayar da 'yayana inasan hakan Wlhi FEENAH inasan yara koda 50 Tawaro ido=3 tace 50 MY D yace yah Tace tab Yace sunyi yawane Tace ssae mah Amma kaima kasan kwan mutun baya kaiwa haka Yace waya gaya miki Anasamu ssae Tace to waye zae aifama Su Ya watsa mata wani kallo yace kee Tace mutuwa xanyi Yace OK naqara Aure Aburkice tace tab ai Wlhi gwara ko'dari nahaifema dakamin kishiya taqara she maganar cikin jin haushi da takaici Yakalleta Aiko qarara yahango kishi mexafi afuskarta Yada'de da sanin xafin kishi irin nata Murmushi yayi Dae dae nan sukayi faking motarsu Aharabar supermarket 'din jifatu Kuma dae dae nan maryam itama ta perka momtarta Harsu MARWAN suka fito daga motarsu suka shiga supermarket 'din basu lura da maryam ba Suna cikin za6an kayane Maryam tasha gaban MARWAN tace Barka da ranah Qare mata kallo yayi ya'dauke kansa Yayinda Nafisa duk tarikice Cikin sanyin murya tace Aunty ina wuni Gamamakinta sae taga ta'amsa mata cikin kulawa Maryam taqara matsawa kusa da MARWAN tace wae yau nice MARWAN zaka gani ina maka magana amma kashareni Yanda ta kusanto shi Abin yabashi haushi dan haka baisan lukacin da wanke mata fuska da mari ba Yaja hannun Nafisa sukayi wanigun Nafisa dae gabaki 'daya tagama rikicewa Dan takasa 'daukar abinda yakawota Tsaf MARWAN yalura da ita dan haka ya'dibi abinda yadace yace sutafi Abin mamaki maryam najikin motarta Ganin datayi bakulata zaiyiba shiyasa tace MARWAN kaji tsoran Allah kaji tausayin xuciyar da take sanka Kayi hakuri kadubeni kamin afuwa mudawo kamar da Sam bae kulataba suka shige mota Sukabarta nan Da cixan yatsa tabar gun Amota Nafisa tayi 'daf jiki asanyaye MARWAN ya'dan kalleta yace FEENAH tace na'am Yace yadae Tace zaka dawo da Aunty maryam ko Yace maekika gani tace bkmae Shuru bamae magana har suka isa gidan Aminu Baqamin murna Zakkiya da Aminu sukayiba daxuwansu Aminu yace yada zuwan baxata MARWAN yace naso nakiraka FEENAH tace aa mumuku baxata Zakkiya tace kinkyauta Nafisa Hirar dasukeyine cikin nisha'di. Shine yasa Nafisa 'dan warwarewa Tace Aunty Zakkiya kuban yarannan naki Aminu yace ambaki Nafisa MARWAN yayi murmushi yace Allah kasan Allah xamu gudu dashi Cikin dariya Zakkiya tace Allah kutafi dashi munbaku MARWAN yace kamar gaske Duk sukayi dariya Zakkiya taja Nafisa betroom 'dinta. Bayan sun'dan xauna Zakkiya tace Intambayeki man Nafisa tace inajinki Aunty Tace Mae yasa bakisan kisami ciki yanxu Tawaro ido tace Wlhi inasan nasamu amma inajin tsoran aihuwane daxafifah Tayi dariya tace hakka zakiyi hakuri Nafisa Nima naji kwanaki MARWAN yana magana da Aminu ne Akan yanxu yanasan yaganki da ciki amma ya fuskanci kamar bakiso Shine nakesan fahimtar dake ba'abinda xakima MARWAN wanda xaiqara mishi sanki kamar kema kinunamae kinasan yara kuma akoda yaushe sukaxu kina maraba da xuwansu Plx karki qara nunamae bakiso Nasan halin MARWAN Nafisa Wlhi dan yaqara aure akan yara bawani abubane Agigice Nafisa taqara tsaida idanta akan Zakkiya tace aure Aunty tace kwarae dan tunkan na'auri Aminu nagane MARWAN yanasan yara Cikin sanyi Nafisa tace Aunty inada kishi Wlhi baka'dan ba Tace baki kaini kishiba Nafisa shiyasa duk wani wanda nasan innayi xaiqaramin martaba agun mijina shinakeyi Dukkan abinda xaifaranta mae rai shinakeyi Duk inda naje to kitabbata sae naxakulo abinda nasan xaifarantama mijina rae Nafisa tasauke ajiyar xuciya Tace Aunty ina 'kukarin yin dukkan abinanan dakika fa'da Tace Nafisa kiqara banasan kiqara tarayya da wata mace acikin xamanki da MARWAN Tace insha Allah xanqara qaimi Tace to Allah yasa Ahaka Zakkiya tadinga da'da wayarma da Nafisa kae ssae wajan xamanta da MARWAN Nafisa tayi farincikin xuwa gidan ba'dan ka'dan ba Dan baqaramin qaruwa tayiba da Zakkiya Tabata magungunan mata masu inganci da kyau Ahaka sukabar gidan Acikin mota ne MARWAN ya lura da farincikin da Nafisa take ciki yace Kinata farin ciki Mae kuka kitsa da Zakkiya tace bkmae Yata6e baki yace OK cikin dare maryam takira MARWAN xagin da yake matane yatashi Nafisa Harya gama yayi cilli da wayan Ahankali tamaida kanta qirjinshi talafe Yanajinta Washe gari suna break yace Wlhi my FEENAH inasan kan bikin Su Amar naganki da ciki Shuru tamae Sanda tatabbatar yagama komae Taje rakashi mota sannan takae bakinta kunnansa tace Aidaga Kaine MY D Yace hmmm Tace daxaka dage nasan cikin satinnan xansamu Yace ko Tace Allah Yace xakisani Wlhi yau kitanadi hawayanki da yawa Tace harkaima Sanda yamata kiss ssae sannan yabarta badan yasoba Dagaske MARWAN ya riqe wuta yayinda Nafisa tajama kanta dan yanxu har tsoranshi take Amma dake ta'daura 'dammarae jure duk wani abu da mijinta yaxomata dashi Sam bata nunamae komae ba Yau Halima da SafiYYa da saudat suna gidan Nafisa Bayan sunci sunsha suna maganar biki Nafisa tace gsky Halima kinyi kyau jiyanda fatarki tayi sharr Saudat tace badole fata tayi kyauba kinsan wacece tamata gyaran fata Nafisa tace aa Saudat tace Rahamat Tace wacece wannan tace a jos take Tace xaki ha'dani da ita tace ok SafiYYa tace kewane gyaran fata kike lema kinganki kuwa Halima tace ina ganin bata ganin madubi Nafisa tace aiduk inda gyara yake xanso nakasance agun Saudat tace takaimiki 'yar hannuna Halima tace inasan Amar so ba'dan ka'dan ba sisters Nafisa tace to gashi xaixama mallakinki Tace ina miqa godiyata gareki Nafisa dan kece silan komae Tace kigodema Allah Tace kullun cikin godemae nake

Chapter 4 of 5