Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
ji yanda yaga Mala yana janmu a jiki,shiyasa yake jin haushi idan mukace Mala da matarshi sunyi mana wani abu ,bayan mun ida raka Baffah bakin mota mukace ya sawo mana ice cream sannan muka dawo part dinmu,muna sane da kallon banzan da Mala yake mana tun Baffah na nan har ya tafi,Amman mudai mun nemi tsari wajen ubangijinmu Allah. Bayan mun dawo daga rakiyar Baffah muka shigo parlour muka iske Momy zaune tayi tagumi duk abun duniya ya isheta. Dafata mukayi na fara cewa."Momy dan Allah kiyi hakuri insha Allah ba zamu sake ba munyi maki alkwari." Cigaba da cewa Basma tayi."Momy munsan duk mune muka saki cikin wannan yanayin daga dawowarmu, amman insha Allah ba zamu sake ba." Kallonmu tayi sannan ta mike tsaye ta shiga room dinta ta barmu tsaye a parlour muna kallon juna. Cema Basma nayi."Basma please dan Allah kizo mu bita room dinta mu bata hakuri wallahi ko yau ban iya bacci idan har bata yafe mana ba." Kallona tayi itama sai kawai naga hawaye yana zuba a idanun Basma, dan ita Basma kuka bai mata wahalar yin, cikin kuka tace. "Mun bani Salma mahaifiyarmu tana fushi damu, fushi mai tsanani, idan muka mutu yanzun mai zamu cema ubangijinmu."!? Bance mata komai ba kawai hannunta naja muka nufi room din Momy dan maganar da Basma tayi ta tada man hankali sosai haka mukayi ta maza muka shiga room din.... Muna shiga muka iske Momy zaune bisa bed dinta tana tunani dan abun duniya duk ya bi ya isheta, abunda yafi tada mata hankali furuncin da Mala yayi kaimu sannan kuma ga Baffah ya daura mata laifi, bayan bata san abunda tayi ma su Mala ba har haka, da zasu gaya mata da ta basu hakuri. Zaunawa mukayi muna kuka, dan mun tsorata a yanayin da muka ganta, dan ni irin kallon da naga tana yi mana sai da naji gabana yana faduwa, Basmace tayi karfin halin cewa."Momy please, wallahi.... Tas! "Momy ta wanke Basma da Mari tana nunata da yatsa gami da kulle ido tace."wallahi idan har baku banma room ba har na bude idona sai na tsine maku albarka." Da sauri muka, Wago kanmu a tare muna kallon Momy da idonta yake a kulle, sake cewa tayi...." zaku fita ko sae na tsinemaku uban kowa ya huta." cikin kuka na girgirza kae nace... NOTE _A bisa a wani dalili litafin BANSAN INDA SUKE BA A HALIN YANZUN ya koma na kudi farashi maifi sauki, Yar'uwa shin kin shirya jin yanda labarin SALMA zai kasance da kuma sanin shin ina su BASMA da BAFFAH suke, ko kuwa wani abun Mala yai masu."!?_ _Kamar yanda nace maku da farko ba sae nace komae ba, da kanku zakuce komae a cikin novel din BANSAN INDA SUKE BA, dan yanzun aka fara wasan kuma naga kuna cewa komae din=??_ _anata biyoni ta private ana cewa yar'mutan kankia kin iya novel dan salonki daban yake, ni masoyiyarki ce ta asali dan kuwa ko wani novel kika saki baya wuce ni sae na karanta shi, to tanan zanga kaunar ta gaskiya wajen paid din novel din nan, dan nasan soyayyarce zata a saya har aji dadi>?p?_ *Yanda zaki biya=?G?* NORMAL GROUP #400 VIPS KUMA #800 Via acc num 0777512438 access bank Jamila Abubakar Bello, idan kuma kati zaki turo kiyi man magana ta wannan numbers din 07034464517 /08160508316 Share pls=?O? *BANSAN INDA SUKE BA* _A HALIN YANZUN_ *NA* *Yar'mutan kankia c'?* *MANAZARTA WRITERS ASSOC* *BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM* *Free page ya kusa karewa kiyi maza kije kiyi subscribe https://youtu.be/oP9HIZhDPaA kiyi screenshot ki turo ta wannan numbers 07034464517 /08160508316 sae nayi adding dinki a paid group, Vips kuma #500* *Chapter 14&15?z?niko nace anya Momy ta dauko hanyar gsky kuwa?)* Haka muka tafi Doctor Dara, dan shine asibitin Baffah Doctor Dara friend din Baffah ne sosai, bayan munje mun gaidashi Baffah yace yayi mana duk abunda ya dace, dan mu duka bamu lafiya, amman ita Basma ciwon kai yafi damunta. Haka aka fara zuba mu dan harda awon B. P akayi mana, bayan angama komai muka zauna muna jiran fitowar Doctor. Kallonmu kawai Baffah yake yana mamakin abunda ke damunmu, amman tunda muka dawo hutu bamu sakin jikinmu sosai, kamar da amman shidai yasan ba abunda yake mana haka ma Momy, balle Baba Mala da yake tsananin kaunarmu, amman yasan abunda zai mana dan ya samu farinciki, muna cikin haka Doctor ya shigo office din ya tadda mu, sai da ya zauna yace."Umma Salam(Sunan Basma na gaskiya kenan Umma Salam) damuwa ce tayi mata yawa, sai ta rage tunani sosai dan yana gab da haifa mata matsala, sai kuma Umma Salma." Shiru yayi da yace Umma Salma dan bai san ya ma zaice ba, daurewa yayi yace."Umma Salma maganar gaskiya jininta ya hau sosai, idan ta cigaba da sama ma ranta damuwa to zuciyarta yana gab da fashewa." Tashi Baffah yayi tsaye gumi duk ya keto mashi. Cewa yayi."inalillahi wa'inna'alaihirajiun, Salma gaya man matsarku dan Allah, ban shirya rasa ku ba, hawan jini? Mai ke damunku ku gaya man nifa mahaifinku ne, idan baku gaya man waya zaku gaya ma wa."!? Kallon Baffah da Doctor nike na rasa abunda zance masu, tashi nayi, nayi hanyar fita, koda Basma taga zan fita itama biyo bayana tayi, Baffah mike ma Doctor hannu yayi sannan ya biyo bayan mu, bakin mota ya tadda mu, muka wuce gida, tunda muka shiga cikin motar ba wanda yayi magana, kowa da abunda ke cikin zuciyarshi, ba kamar Baffah da yake ji kamar ya kurma ihu, ace yarinya karama kamata tana da hawan jini was ma. Yana yin parking na balle marfin motar nayo part dinmu. Muna shiga ciki, room din mu na shiga, na fada kan gado na fara aikin kuka, dan maganar gaskiya a lokacin ina cikin tashin hankali wai ni Salma nice yau nike dauke da hawan jini, abunda da ban tsoro, ina cikin kuka naji an dafani, dago kaina nayi ina kallon Basma dake hawaye, mu duka kasa cema junanmu komai mukayi, Baffah ne ya shigo yace mu samai shi a parlour. Toilet na fara shiga na wanke fuska ta, sannan muka tafi, kallo daya nayi ma Baffah jikina yayi sanyi, dan banga sauki a fuskarshi ba, shiru muka yi na wani lokaci sannan Baffah yace."Umma Salma, gaya man matsalarku a gidan nan, gaya man maike damunku har haka."!? Shiru muka yi dan har ga Allah bamu san abunda zamu ce mata shi ba, tsawa mukaji yayi yana cewa."Salma ba tambayarki nayi ba, zaki yi shiru zaki saman ido."!? Cewa nayi."Baffah ba abunda ke damun mu, am... "Karya kike Salma, nace Karya kike."Baffah ya katseman magana yana cewa karya nike, kallonshi nayi sai kawai na fara hawaye, dan nayi ma Momy alkwarin bamu sake yi ma Baffah maganar su Mala, dan ko bamu so ta rasa aurenta saboda damu." Cigaba da cewa yayi."Salma tunda baku gaya man matsalarku, ban isa nasan maike damunku ba, ku tashi ku tafi ni nasan maganin abun." Cewa nayi."Baffah ma yar... "Ya isa haka Salma, nace ku tashi ku tafi, Amman ku dunga shan maganinku." Tashi muka yi jiki duk a sanyaye, muka shiga room, kallonmu Baffah yayi sannan ya girgiza kai yace ma Momy."Dear yaranan suna cikin matsala, kuma naga ba gaya man zasuyi ba, ko ke kinsan abunda ke damunsu."!? Kallonshi Momy tayi, tashi tayi ya dawo kusa dashi ta zauna sannan tace."Nima bansan abunda ke damunsu ba, Amman Abu daya za'ayi shine muta addu'a." Murmushi yayi sannan yace."hakane, Amman dole muringa yi masu abunda zai sasu farinciki, kisan su kadai Allah ya bani inasan farincikinsu." "To Insha Allah." Tunda muka shiga room ba Wanda tace ma kowa komai, dan ni wanka na shiga ma, Kafin na fito Basma ta fiddo mana da kayan da zata sanya, itama wanka ta shiga tana fitowa ta shirya kallona tayi tace."Salma karki damu, mu cigaba da hakuri kinji Sis." Daga mata kai kawai nayi sannan na kwanta bacci nayi ban tashi ba sai 5pm, wanka kawai nayi sannan nayi sallah parlour natafi na tadda su Momy suna kallo, zaunawa nayi na fara kallo, muna cikin kallo Baffah ya dawo, cewa yayi." My twice girls, close ur's eyes." Kulle idanuwanmu mukayi, ji mukayi ya sanya mana wani abu a hannu, sannan yace."open."muna dubewa muka ga makulin mota da ya ba ko wancan mu, kowa da tata kuma sabuwa dal." Tashi mukayi lokaci guda, muka rumgumeshi muna cewa."Thank you Baffah."dan rasa abunda zamu ce mukayi, fitowa mukayi dan zuwa ganin motors din, muna fitowa muka hadu da Baba Mala dan da alama daga wajen motar yake, murmushi yayi sannan yace."Alhaji Allah yasa alkhari, ai shigowa ta Kenan naga kayi sabuwar mota kai da Hajiya." Cikin farinciki Baffah yace."ai Alhaji Mala, ba motarmu bace,motar Yarankane Salma da Basma." Take fuskarshi ta sauya, ?a?aro murmushi yayi yace."masha Allah, gaskiya natayasu murna, motar sunyi kyau sosai, Allah yasa akashe lafiya." "Amin ya Allah, Alhaji Mala." Nan muka wuce dan ida zuwa ganin mota, shi kuma ya shige part din shi, yana shiga yace ma matarshi."Zulai tabbas dole na tashi tsaye cikin kwanankin nan, naga na kashe Alhaji Muhammad shida iyalanshi." Kallonshi tayi ta watsar, sannan tace."ai ni na haddace wannan maganar taka Mala, halan wani abu kaga yayi ma wannan tsinannun yaran nashi."!? Kallonta yayi yace."Zulai Mota sabuwa fal ya saya masu, yau din nan, kuma yana sane da Dahira bai saya da ita ba." Tashi tayi daga zaune tana dafe kirji tace."mota ya saya masu? Tabbas Mala kana da aiki gabanka, tsaya kallon ruwa kwaWo yayi maka ido." Dariya ya fashe da ita yace zan baki mamaki ne, kin san waye Mala, wallahi yau din nan sae sun bakunci lahira.... Itama dariyar tayi tana cewa..... *Wannan shine second to the last freee page=??* *Yanda zaki biya=?G?* *NORMAL GROUP #https://youtu.be/oP9HIZhDPaA * *VIPS KUMA #800* via acc num 0777512438 access bank Jamila Abubakar Bello, idan kuma kati zaki turo kiyi man magana ta wannan numbers din 07034464517 /08160508316 Share pls=?O? *BANSAN INDA SUKE BA* _A HALIN YANZUN_ *NA* *Yar'mutan kankiac'?* *MANAZARTA WRITER'S ASSOC* *BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM* *LAST FREE PAGE

Chapter 4 of 5