Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
muka fara fada, sai ga Allah ya kawo Hafsat.. "Mai ya hadaku kuma."? Cewar Yaya Hafsat, aiko nace mata"Wai ni zata cema jarabatu." Cikin mamaki Yaya Hafsat tace."shine dan kawai tace maki jarabatu shine zaki batama kanki lokaci."? Turo baki nayi ina magana ciki?, cigaba da cewa tayi...."Ku taso mu tafi bani san wanann sakarci, daga yau." Cewa nayi."to amman yaya Hafsat kice mata tabar jana fada."kallon Basma Yaya Hafsat tayi sannan tace...."ke Basma karki sake ce mata jara ba tu." Ciki? Basma tace....."To na daina yi hakuri Salma." Dafata nayi sannan nace...."nayi hakuri, kema yi hakuri Basma." Haka muka tafi fell, ita Basma ta shiga team din yan gudu, ni kuma na shiga team din boli... Munyi wasa yanda ya kamata, da man ni ba daga nan ba wajen boli ina bala'in san boli, dan Hafsat tayi mamakin yanda nike ta buga ball din boli kamar ba ita ba.. Bayan mun taso daga fell aka yi ringing din dinning muka je muka ansa sannan ko wace yarinya ta tafi massalaci, bayan mun dawo daga massalaci muka tafi kwanar wata sabuwar friend da mukayi Sabira can muka tadda Asm'au akaita labarin gida, daga nan muka wuce night... Bayan mun dawo daga night muka zauna muna labarin yan class din mu.. "Ni Basma Ina mamakin yan class dinmu wallahi, sudai sun cika tsoro kamar farar kura." Dariya Basma tayi sannan tace...."Kisan Allah Salma zasu warene har basu ida sabawa da juna ba, kowa dai sitmate dinshi yasani da ita yake labari." Dan shiru nayi sannan nace...."To mai zai hana inmunje class gobe kowa ya tashi yayi introduction din kanshi, kinga ta wannan hanyar zamu sannan juna." "Hakane Salma kin kawo shawara mai kyau Allah ya kaimu goben lafiya.. "Amin, ke ni sai da safe bacci nike ji, kuma nan school din tashi asuba suke yi, "aiko sai da safe.. Washe gari Bayan mun gama potion da duk wani school athorities sannan muka tafi class..Bayan kowa ya gama zuwa class na ta tashi na fara magana.. "Yan class din nan, yau zanyi roster gashi ba kowa na sani class ba dan Allah kowa ya tashi yayi introduction din kanshi.. Nan fa yan class sukayi Naam kowa ya tashi yayi introduction din kanshi, ni kuma ina rubuta sunan kowace a roster har suka gama.. "Basma tashi muje admin block mu dauko check." Tashi Basma tayi tana cewa...."to mu tafi Mau sai mundawo..... Nan muka wuce muka dauko alli harda doster sabuwa muka taho da ita.. Bayan mun dawo daga Admin, nan muka zauna muna ta labari duka ajin ashe da man yan ajin likimo sukayi kowa da kunshin rashin jin maganarshi kunshe a wando=??. Haka muka cika makaranta da surutu sai da wani malami ya shigo yayi masu warning akan surutun mu yayi yawa, sannan ya sa ni naje na kira malamin Math dayake shi muke dashi. Bayan yazo yayi mana lesson ya Kama gabanshi.. Bayan antashi daga class muka wuce hostel.. Yau dai da kanmu muka yi wanki, bayan mungama muka shiga wanka muka shirya muka anso dining sannan muka wuce evening... Yau general muka tsaya bayan antashi daga evening.. "Yaran makarantar! "Naam!"yaran makarantar nan! "Naam! "Dan ubanku bakuji? "Muna ji! "Bakuji! "Munaji! "Uban mai yasa kwana biyu baku yi mana potion har sai an koroku."? Wata prefer ce take wannan bayanin a filin general cleaning.. "To daga Yau kar yar'iskar yarinyar da ta bari muka sake korota yin potion kuna ji? "Eh munaji, haka aka gama bugunmu a ringing sanann suka sallami ko wace ta wuce wajen potion dinta.. "Wai Basma baki daina wannan kukan."? Cikin kuka Basma tace."Salma baki ga yanda akayi mamu bane Wai."? Cikin takaici nace"To ya zamuyi." Tsaki Basma tayi sannan tace man."Ai dole kice ya zamuyi sai da nace maki karda muzo boarding kike ce boarding dadi ai ga dadin nan muna gani.. "Uhmm." nidai na cigaba da potion din na, muma nan gaba zamuyi ma wasu irin abunda aka yi mana Yau Basma. " ```Toh fa jama'a kunji wani dogan guri wajen Salma wai suma zasu yima wasu abunda akayi masu, yarinyar da take JS1 take hangen anbasu prefer =??``` *Muje zuwa.... =ؤ?* *Yar'mutan kankia cec'?* Share Comment Please *BANSAN INDA SUKE BA* _A HALIN YANZUN_ *NA* *Jameelah Jameey* *Yar'mutan kankia cec'?* *MANAZARTA WRITERS ASSOC* *Marubuciyar=?G?* *Nana Jawaheer* *Gimbiya Hakima* *Izzah ko mulki* *Sanadin link* *A gidan haya* *?arawo ne* *Sadaukin burhaan* *Sanadin soyayyar shan minti* *Bayi ma ?a'?ane book 1&2* _AND KNOW_ *BANSAN INDA SUKE BA* _A HALIN YANZUN_ *BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM* *Chapter four nd five??. Bayan ya shiga wani glass ne naga ya dannna shima ga dukan alamu fingerprint ne ya dannan ji nayi door din na cewa "welcome back Barrister Salim.".... Sannan ta bude ya shiga, wooow!!! Masha Allah lakuwata ila billa, wani kallar parlour ne ya shiga dan komai na parlour da glass akayi shi harta kujerun dake jere a parlourn na glass ne, wal'wal suna nuna mix color's kala? su blue, red, purple, ash suke ta haskawa, ga decoration anyi masu da ratsin ruwa da kifaye daga gefe, idan bako yazo yana Iya kasa zama yayi tunanin ruwane a jikinsu da kifaye a kujerun. Wata dattujuwar matace zauna tana kallon N.T.A. News, kuma tana karanta dailytrust a hannunta ga kuma waya ta hau twitter tana jin abunda duniya take ciki, hankalinta baki daya yana kan abubuwan da take, inda taga Abu mai mahinmanci sai ta dauko wata joter da take gefenta tayi wani short note, Wanda ni dai bansan mai take rubutawa ba a jikin wannan joter din, samun waje yayi ya zauna baice komai ba, sai ma maida hankalinshi shima da yayi a wajen kallon da take, sai da aka gama labarai duka a n.t.a.news sannan ta ida karanta dailytrust din tayi note a wannan joter din sannan kuma ta sake shiga wasu page a twitter taga abunda ta gani ta sauka ta ajiye jaridar tare da wayar sannan ta dauki remote ta mai da Manaratv, sannan ta waigo tace a natse"Barrister daga Ina kake cikin daren nan? I said from whare are you? Kasan yanda ka tadaman hankali kuwa." Dukar da kanshi yayi sannan yace...."sorry Mami, Ina wuni."? Harararshi tayi sannan tace.."ba wannan na tambaye ka ba, ce maka nayi daga Ina kake."? Raurau yayi da ido, dan shi baisan gaya Mami tana mashi fada ko ya yake, ji yake har cikin kwakwalwar kanshi, dan baya son hayaniya ko ya take kuma Mami tasan da haka, amman gashi ta kulle ido sae ihu take mashi a kunne, tashi yayi ya koma inda take zaune hannuwanta ya kama yana murzawa a shagwaSe yace....."Mami wallahi yanayin aiki ne shiyasa nayi dare ban dawo ba believe me Mami." Murmushi tayi tana girgiza kai sannan tace...."matsalarka daya Barrister baka Iya karya ba, ko kayi ta, bata yi maka kyau, tabbas ba zan hanaka fita ba Salim tunda kai ba Yaro bane, Amman kasani kaji tsoran Allah a duk inda ka tsinta kanka, ka sani komai kake yana nan yana ganinka idan ni da Abbanka bamu ganinka, dan haka ka tashi kaje kaci abinci, Abbanka ya dawo ya tafi jana'ida cikin unguwar nan." sosa ?eyarshi yayi, yana murmushi dan ya lura koya yayi ma Mami karya sae ta ganoshi ya rasa dalilin haka, cewa yayi.."Insha Allah Mami, zaku samaini mai jin tsoran Allah, amman ina akayi rasuwa kuma wa ya rasu."? Cewa Mami tayi...."Allah sarki, cikin masu aikin gidan nan, Allah yayi ma yarinyarshi rasuwa dazun nan, shine yace tunda baka dawo ba shi ya tafi dan yace ace anje mashi ta'aziya." cikin yanayin damuwa Salim yace."Allahu akabar, Allah ya jikanta, Mami yau kuma mai akace goverment tayi? Dan nasan yan kasar nan tamu ba'a iya masu." murmushin manya Mami tayi sannan tace.....Hmmmm!! "Barrister kenan, har yanzun kai Yaro ne, baka san siyasa ba, ranar da na haifeka aka ba Abbanka chairman, ba tare ba an tambayeshi shawara ba, lokacin da kake S.S one aka ba Abbanka senator, shima bai sani ba, haka akazo aka bashi dan majalisa lokacin ka gama degree dinka shima bai nama ba, asali ba shi da gurin yin siyasa, dan bata burgeshi, yana nan yana nan, yanzun kuma duniya ta daga hannunshi har ya zama prisedent baki daya, kasan mai yasa hakan ta kasance."? Komawa yayi ya zauna, girgiza mata kai yayi sannan yace..."Aa Mami." Kallonshi Hajiya Khadija tayi, tana murmushi sannan tace saboda rike gaskiya da amana, ba yabon kai ba, mahaifinka shi mutun ne mai tausayi da kuma son yaga ya taimaka ma na kasa dashi, shiyasa kullun muna hanyar karanta news kuma muna zuwa gidan tv muna kallo, gami da hawa social media muna jin koken bayin Allah, shiyasa nike rubutawa domin share masu hawayensu, idan bamuyi ma tallakawa ba wa zamuyi mawa? Wannan dukiyar tasu ce idan munci wallahi ranar gobe kiyama sai Allah ya anso masu hakinsu, kaga solution shine karkaci, Kadai kayi tsakaninka ga Allah sannan ka barma Allah sauran, dan haka wannan matsalolin yau ne na dauka wanda Allah ya kaddara zamuji, kuma insha Allah zamu share masu hawayensu, idan Allah ya bamu iko." tabbas yasan yayi dacen iyaye na gari, dan shi har mantawa yake shi daddynshi president ne, dan Dad dinshi baya mashi wasa, kullum nuna mashi yake ya tashi ya nemi halak din shi, cewa yayi...."Allah yasa Mami, shima Abba Allah ya taya shi riko, yasa ya sauka wannan mulkin lafiya, naji yace zamu koma da zama Abuja ko."? ?aga mashi kae Hajiya Hadiza tayi tana cewa...."Eh da haka yace, amman yanzun yace muyi zaman mu anan yobe." Murmushi yayi sannan ya tashi baice komai ba, abinci yaci sannan yace shi ya tafi zai kwanta idan Abban shi ya dawo Mami ta gaida mashi shi.... *Muje zuwa...... =ؤ?* *Yar'mutan Kankia cec'?* *BANSAN INDA SUKE BA* _HALIN YANZUN_ *NA* *Jameelah Jameey* *Yar'mutan kankia cec'?* *MANAZARTA* *WRITERS ASSOC* *BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM* *Chapter eight and nine

Chapter 2 of 5